A lokacin wannan ziyarar Shugaba Xi zai gana da Shugaban kasar Kongo Brazaville Denis Sassou Nguesso inda za su yi musayar ra'ayi game da al'amurran da suka shafi dangantakar kasashen biyu da hanyar da za su inganta shi.
Kasar Sin dai ita ce abokiyar huldar kasuwanci mafi girma da kasar ta Kongo,wannan huldar kasuwancin a tsakanin su ya haura zuwa kudi dalar Amurka biliyan 5 a 2012 daga dalar Amurka miliyan 290 a 2002,wato cikin shekaru 10.
Shugaba Xi dai ya taso ne daga kasar Afrika ta Kudu inda ya halarci taron BRICS karo na biyar da aka kammala a birnin Durban,kuma kafin haka sai da ya ziyarci kasar Rasha,Tanzania.
Wannan ne ziyarar aiki ta farko ga Shugaban na Sin tun darewarsa karagar mulki, abin da ya nuna aniyar kasarsa na son inganta zumunci da kasashen Afrika. (Fatimah Jibril)