Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma ya sanar da isar da sako a ranar Laraba ga majalisar dokokin kasar kan matakin da ya dauka na kara wa'adin tawagar rundanar sojojin kasar (SANDF) dake jamhuriyar demokaradiyyar Congo (DRC) da Sudan.
Kara wa'adin shi ne don cika alkawarin ayyukan kasa da kasa, kuma zai ci gaba har watan Afrilun shekarar 2014, in ji mista Zuma a cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar.
Mista Zuma ya bayyana cewa, wannan mataki ya kunshi jibge sojojin kasar 850 a yankin Darfur bisa alkawuran kasa da kasa da Afrika ta Kudu ta yi zuwa ga kungiyar tarayyar AU da kuma MDD.
An jibge sojojin a kasar DRC-Congo daga ranar 1 ga watan Afrilun shekarar 2012 zuwa 31 ga watan Maris na shekarar 2013 domin shiga aikin tawagar samar da zaman lafiya ta MDD a kasar, kuma za su cigaba da wannan aiki, in ji Jacob Zuma. (Maman Ada)