Sin ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa ofishin jakadancin kasar Faransa dake kasar Libya
A jiya ne wasu boma-bomai da aka ajiye su a cikin mota suka fashe a ofishin jakadancin kasar Faransa dake kasar Libya. Game da wannan hari, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a ranar 24 ga wata a nan birnin Beijing cewa, Sin ta yi Allah wadai da wannan mugun hari. Kana kasar Sin tana fatan gwamnatin kasar Libya za ta dauki matakai don tabbatar da tsaron hukumomin diplomasiyya na kasashen duniya dake kasar Libya da ma'aikatansu. Hakazalika kuma, kasar Sin tana fatan za a gudanar da ayyukan sake gina kasar Libya a fannonin siyasa da tattalin arziki yadda ya kamata, ta yadda za a samu zaman lafiya da wadata a kasar cikin hanzari. (Zainab)