in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu za ta tura sojojin wanzar da zaman lafiya zuwa DRC
2013-04-08 11:03:51 cri

A ranar Lahadi 7 ga watan nan ne gwamnatin kasar Afirka ta Kudu, ta tabbatar da kudurinta, na tura dakarun wanzar da zaman lafiya DRC jamhuriyar kasar Congo, a wani mataki na ba da tallafi ga shirin da MDD ke goyon baya a kasar.

Kakakin rundunar sojin kasar Birgediya Janar Xolani Mabanga ne ya bayyana hakan, yana mai cewa, asarar rayukan wasu dakarun kasar 13 da ya auku kwanaki 10 da suka gabata, ba zai hana Afirka ta Kudun sake tura karin dakaru DRC ba, ko da yake bai bayyana yawan sojojin da za a tura a wannan karo ba.

A ranar 28 ga watan Maris din da ya gabata ne dai kwamitin tsaron MDD ya yi umarnin tura dakarunsa kai zuwa DRC, a wani mataki na murkushe ayyukan 'yan tawayen dake dauki ba dadi da tsohuwar gwamnatin da ta shude, musamman a yankunan dake gabashin kasar.

Masu fashin baki dai na ganin wannan mataki da mahukuntan kasar Afirka ta Kudun suka dauka, zai fuskanci tirjiya daga masu ruwa da tsaki, musamman ganin yadda ba da jimawa ba kasar ta yi asarar dakarunta 13, baya ga wasu 27 da suka samu raunuka, a ranar 23 ga watan Maris din da ya gabata, yayin wata arangama da ta wakana tsakaninsu da dakarun 'yan tawayen kasar Afirka ta Tsakiyar a birnin Bangui.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China