in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu ta yi asarar dalar Amurka biliyan 1.69 sakamakon yajin aiki
2013-04-12 14:13:56 cri

Cibiyar dangantakar kabilu ta Afirka ta Kudu SAIRR ta bayyana ranar Alhamis cewa, kasar ta yi asarar rands sama da biliyan goma wanda ya yi daidai da kusan dalar Amurka biliyan 1.25 a harkar hako albarkatun gwal da platinum sakamakon yajin aiki tsakanin shekarar 2012 da 2013.

Rahoton da cibiyar ta bayar a birnin Johannesburg ya ci gaba da nuna cewa, kasar har wa yau ta yi asarar rand miliyan 180 wanda ya yi daidai da kusan dalar Amurka miliyan 21 a masana'antar kwal a daidai wannan lokaci.

Babban mai binciken cibiyar SAIRR Boitulome Sethlatswe ya ce, baki daya an yi asarar rand biliyan 15.3 wanda ya yi daidai da kusan dalar Amurka biliyan 1.69 a masana'antun hako ma'adinai na kasar bisa binciken da aka yi a baitulmalin kasar.

Cibiyar binciken ta yi nuni da kididdiga da aka samu daga baitulmalin dake nuna cewa, dakatar da harkar hako ma'adinai ya kawo raguwar adadi riba da aka yi hasashen samu daga albarakatun kasa na GDP da kashi 50, inda maimakon kashi 3 cikin dari an samu kashi 2.5 cikin dari na shekarar 2012.

Rahoton ya ci gaba da nuna cewar, wannan hasara ya shafi sauran sassan tattalin arzikin kasar, musamman ma masana'antu na karafa, kere-kere, na'urori da kuma na roba.

An kuma yi hasashen cewa, kudade da za'a samu daga fitar da kayayyaki zuwa wajen kasar za su kasa da rand biliyan 12 wato kusan dalar Amurka biliyan 1.32, a shekarar 2012, wato ke nan fiye da yadda za'a samu, da ba'a fuskanci yajin aikin ba.

Saboda alaka dake tsakanin harkar ma'adinai da wasu sassa, asara da aka samu daga fitar da kayayyaki waje sun wuce wadanda aka samu kai tsaye.

Sethlatswe ya ci gaba da cewa, sauran abubuwa da yajin aikin ya haifar su ne rage kimar kasar Afirka ta Kudu a fuskar kudade a wajen bankuna na kasa da kasa kamar Moody's, Standard da Poors, da kuma Fitch a karshen shekarar 2012 da kuma farkon shekarar 2013.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China