Shugaba Zuma ya bayyana cewa, wadannan sojoji guda 13 sun rasa ranyukansu ne a aikin bin manufofin diplomasiyya na kasar Afirka ta Kudu da kuma kiyaye zaman lafiya a nahiyar Afirka, don haka ya kamata kasarsu ta nuna yabo gare su.
A watan Janairu na shekarar bana, kasar Afirka ta Kudu ta tura sojoji guda 200 zuwa kasar Afirka ta Tsakiya don taimakawa sojojin gwamnatin kasar wajen yaki da dakaru masu adawa.
A kuma ranar 24 ga watan Maris, dakaru masu adawa a kasar Afirka ta Tsakiya sun mamaye babban birnin kasar, inda sojojin kasar Afirka ta Kudu 13 suka mutu a sakamakon musayar wuta, kana sojoji fiye da 20 suka ji rauni. Wannan shi ne karo na farko da kasar Afirka ta kudu tayi asarar sojoji da suka kai hakan yawa a cikin shekaru 20 da suka gabata. (Zainab)