ECDC za ta tallata albarkatun noma na Afirka ta Kudu a kasar Sin
Cibiyar ECDC ta kasar Afirka ta Kudu wato cibiyar raya lardin gabashin Cape na kasar ta bayyana ranar Litinin cewa, za ta mara bayan kamfanonin kasar Afirka ta Kudu wajen tallata albarkatun gona a shirin baje kolin din-din-din na kasa da kasa da za’a yi a birnin Ningbo na lardin Zhejiang a kasar Sin wanda za’a shafe watanni 30 ana yi.
Cikin wata sanarwa da cibiyar ta buga a shafinta na intanet, ta ce, wannan mataki zai kara bunkasa harkar cinikayya tsakanin Afirka ta Kudu da kasar Sin da kuma ma tallata albarkatun kasar Afirka ta Kudu a kasar Sin.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, shirin zai kuma samar da wata dama ga kamfanonin kasar Afirka ta Kudu na sayar da kayayyakinsu a kasuwannin kasar Sin.
Kasashen Afirka ta Kudu da Sin mambobi ne na kungiyar BRICS da ta kunshi kasashen Brazil, Rasha, da Indiya.(Lami)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku