A kwanan baya, masanan kasar Sin sun yi nazari kan kwayar cutar murar tsuntsaye nau'in H7N9, sun kuma bayyana cewa, kila wannan kwayar cuta ta samo asili ne daga tsuntsaye dake zaune a yankin gabashin Asiya, kuma ta hadu da kwayar cutar dake jikin kajin birnin Shanghai, da lardin Zhejiang da na Jiangsu, watalika canjawar wannan kwayar cuta, shi ne dalilin yaduwarta daga kaji zuwa Bil Adam.
Hukumar kimiyya da fasaha ta yi hadin gwiwa da hukumar kiwon lafiya da kayyade haifuwa ta kasar Sin, domin gabatar da shirin magance wannan cuta a ran 10 ga wata, ta yadda za a mai da hankali kan fitar da magunguna da alluran rigakafi da sauransu, shirin da ake sa ran cimma nasararsa nan da watanni 7 masu zuwa.
A wannan rana kuma, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jagoranci wani zaman majalisar gudanarwa, inda ya nemi a ba da bayyanai kan wannan aiki cikin lokaci, tare kuma da ba da kulawa ga wannan cuta yadda ya kamata. (Amina)