in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a mai da hankali kan rigakafin kwayoyin cutar H7N9
2013-04-10 15:03:47 cri

Ran 9 ga wata, kakakin hukumar kiwon lafiya ta duniya Gregorie Hartle ya bayyana a birnin Geneva cewa, ya zuwa halin yanzu, ba a gano asalin kwayoyin cutar H7N9 ba, dalilin haka ne hukumar ba ta iya fitar da tabbatattun shawarwari na kawar da cutar ba, hanya mafi muhimmanci a halin yanzu ita ce daukar matakan rigakafi da suka dace yadda ya kamata.

Mr. Hartle ya kuma kara da cewa, kasar Sin ta gabatar wa hukumar bayanin wannan cuta nau'in H7N9 cikin sauri, amma yanzu hukumar ba ta shirya aike da ma'aikata zuwa kasar Sin ba, kana ta gargadi mutanen kasa da kasa da su mai da hankali kan harkokin rigakafi cikin zaman rayuwarsu na yau da kullum, tare da kaucewa cin naman dabobbin da suka mutu ko masu rashin lafiya, da dafa abinci sosai kafin a ci. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China