An kira taro karo na hudu na karamar kungiyar jagorantar aikin rigakafi da ba da kulawa wajen dakatar da yaduwar cutar murar tsuntsaye nau'in H7N9 na kwamitin kiwon lafiya da kayyede haifuwa na kasar Sin a ran 7 ga wata, inda aka jaddada wajibcin ba da jiyya ga wadanda suka kamu da wannan cuta domin tsirar da rayukan mutanen da suka kamu da cutar.
Karamar kungiyar ta kuma nemi da a kafa tsarin hadin gwiwa tsakanin wuraren da aka gano cutar ta yadda za'a dakatar da yaduwar wannan annoba da kuma kokarin ba da jiyya ga wadanda suka kamu da cutar kuma suka kasa karfin biyan kudin jiyya. Hakazalika da kokarin gano daga inda wannan cuta ta tashi. Kana kuma karamar kungiyar ta bukaci kwararru su rika ba da bayyanai kan wannan cuta ta yadda al'ummar kasa za su fahimci wannan cuta. Har ma da yin hadin gwiwa da wasu kungiyoyin kasa da kasa ciki hadda kungiyar WHO da na sauran kasa da kasa da shiyya-shiyya ta yadda za'a yi musanyar kimiyya da fasaha a tsakaninsu.
A halin yanzu, Sinawa 21 da aka tabbatar sun kamu da wannan cuta daga cikinsu mutane 6 suka mutu. (Amina)