in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tabbatar da mutuwar mutane 9 cikin Sinawa 33 da suka kamu da cutar murar tsuntsaye nau'in H7N9
2013-04-11 10:36:02 cri

Hukumar kiwon lafiya da kayyade haifuwa ta kasar Sin ta gabatar da wani rahoto a ran 10 ga wata, wanda ke cewa, ya zuwa karfe 5 na yammacin wannan rana, adadin mutane da suka kamu da cutar murar tsuntsaye nau'in H7N9 ya kai 33, inda daga cikinsu mutane 9 suka rigamu gidan gaskiya.

Hukumar ta ce, daga karfe 5 na yammacin ranar 9, zuwa karfe 5 na ranar 10 ga wata, karin mutane da suka kamu da wannan cutar ya kai biyar, cikinsu mutane biyu mazauna birnin Shanghai ne, yayin da guda 1 ke zaune a lardin Zhejiang, sai kuma guda 2 daga lardin Jiangsu.

Rahoton ya kara da cewa, wani karamin yaro dan shekaru hudu a duniya, ya tsira da ransa, bayan kamuwa da cutar da ya yi, inda a yanzu yake cikin koshin lafiya bayan barinsa asibiti a wannan rana. Ya zuwa yanzu, mutane da suka kamu da wannan cuta suna wurare daban daban a birnin Shanghai, da lardin Jiangsu, da lardin Anhui, da kuma Lardin Zhejiang.

Rahoton ya kuma tabbatar da cewa, wannan kwayar cuta ba za ta iya yaduwa tsakanin Bil Adam ba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China