Hukumar sufurin jiragen kasa ta kasar Afirka ta Kudu PRASA ta bayyana ran Alhamis cewa, za'a samar da wata na'ura mai inganci ta sadarwa daga kasar Sin don aikin ba da sigina.
Yayin jawabi ga manema labarai, shugaban sufurin jama'a ta jiragen kasa ta Afirka ta Kudu Lucky Montana ya bayyana cewa, kamfanin samar da kayayyakin sadarwa na duniya, Huawei shi ne zai samar da wannan na'ura bayan ya cimma nasarar samun wannan aikin kwangila.
Nau'rar za ta samar da kariya a sufurin jiragen kasa da kuma bullo da sabbin dabaru na tuki mai tafiyar da kansa, inda hakan zai sa a samu raguwar hadduran jirgin da ake fuskanta saboda kuskure wajen tuki.
Wannan fasaha za ta zamo ita ce ta farko a nahiyar Afirka baki daya kuma za ta shafe tsawon kilomita 1200 a cikin kasar Afirka ta Kudu.
Shugaban na PRASA ya ce, aiki zai lashe rand miliyan 485 wanda ya yi daidai da dalar Amurka miliyan 52.
Da yake Magana, jami'in kamfanin Huawei Eman Liu ya nuna farin ciki kan wannan hadin gwiwa da kamfanin sufurin jiragen kasar ta Afirka ta Kudu, inda ya kara da cewa, burin kamfanin na Huawei shi ne samar da kayayyaki da fasaha masu sauki ga jama'a da abokan huldarsu a kasashe da ma yankuna baki daya.(Lami)