Yau Jumma'a 17 ga wata a nan birnin Beijing, an ba da rahoto kan tsarin tabbatar da lafiyar jikin Sinawa kafin shekarar 2020, inda aka nuna cewa, a cikin shekarar 2020, ma'aunin kasar Sin a wannan fanni zai kai matsayi na matsakaicin kasashen masu wadata.
A wajen dandalin kiwon lafiya na kasar Sin na shekarar 2012 da aka bude a wannan rana a nan birnin Beijng ne a aka bayyana wannan rahoton da masana fiye da 100 na hukumar kiwon lafiya suka rubuta, wanda yayi nazarin zarafi da kalubale da Sin za ta fuskanta kafin shekarar 2020 ta fuskar kiwon lafiya, tare kuma da gabatar da burin da za a cimma.
Rahoton ya ce, kafin shekarar 2020,kiwon lafiyar jikin Sinawa zai kara samun kyautatuwa, matsakaicin tsawon shekarun rayuwar mutane kuma zai haura zuwa shekaru 77 daga shekaru 73 na shekarar 2010.(Amina)