Xi Jinping ya fadi haka ne lokacin da ya gana da shugaba Alain Merieux na asusun Merieux na kasar Faransa, Xi Jinping ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin na mai da hankali sosai wajen bunkasa harkokin kiwon lafiya, kuma ta kan mayar da batun kula da lafiyar jama'a da tsaron rayukansu a matsayin wani muhimmin al'amari matuka. Kasar Sin za ta ci gaba da raya aikin yin gyare-gyare kan harkokin kiwon lafiya, wato kafa tsarin kiwon lafiya da zai shafi kusan dukkan jama'ar kasar, kyautata tsarin ba da tabbaci na kiwon lafiya, da tsarin ba da hidima ga jama'a na kiwon lafiya, ta yadda za a kara kyautata ingancin rayuwar jama'a. Sannan yana fatan asusun Merieux na kasar Faransa ya ci gaba da nuna goyon baya ga aikin kiwon lafiya na kasar Sin.
A nasa bangaren, Mr. Alain Merieux ya bayyana cewa, asusun zai kara yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannin kiwon lafiyar jama'a, ta yadda zai iya bayar da gudummawa wajen rigakafin aukuwar cututtuka da kula da lafiyar jama'ar kasar Sin. (Sanusi Chen)