logo

HAUSA

Babi10: Taiwan

0001-01-01 08:00:00 CRI

>>[Me ka sani]

Me Ka Sani game da Taiwan

A Ina Taiwan yake

Taiwan wani lardin kasar Sin ne wadda ke kunshe da tsibirai da yawa kuma ke tekun Pacific. Taiwan kuma yana kudu maso gabashin kasar Sin. Duk lardin Taiwan ya kunshi tsibirai fiye da 80 ciki har da tsibirin Taiwan da wasu kananan tsibirai wadanda suke kewaye da tsibirin Taiwan da tsibirai na Penghu. Yawan fadin lardin Taiwan ya kai wajen muraba'in kilomita dubu 36.

Lardin Taiwan yana kudu da tekun Gabas na kasar Sin, a arewa maso gabashin Taiwan shi ne tsibirai na Ryuku, shi kuma yana yamma da tekun Pacific. A kudu, lardin Taiwan yana kusa da mashigin tekun Bashi kuma yana makwabtaka da kasar Philippine. Ban da wannan, mashigin tekun Taiwan yana wurin da ke tsakanin tsibirin Taiwan da lardin Fujian na babban yankin kasar Sin. layi mafi gajerta a tsakanin tsibirin Taiwan da lardin Fujian ya kai kilomita dari 1 da talatin kawai. Lardin Taiwan kuma yana kan tsakiya hanyar yammacin tekun Pacific. Saboda haka, a fannin ilmin yaki, Taiwan yana da muhimmanci sosai.

Mashigin Teku na Taiwan

Tsawon mashigin teku na Taiwan daga arewa zuwa kudancinsa ya kai wajen kilomita 380. Matsakaicin tsawonsa daga gabas zuwa yamma ya kai wajen kilomita 190. layi mafi gajerta a tsaye, wato daga Xinzhu na lardin Taiwan zuwa Pingtan na lardin Fujian ya kai wajen kilomita 130 kawai. Yayin da iska ba shi da karfi, kuma babu gajimare a cikin sararin sama, sa'an nan kuma ana jin dadin yanayi, idan an hau kan wani dutsen da ke bakin teku na lardin Fujian, za a iya kallon gajimaren dake duwatsun lardin Taiwan, har za a iya ganin Dutsen Jilong da ke arewacin lardin Taiwan.

Labarin Kasa na Taiwan

Yawan fili na tsibirin Taiwan, wato tsibiri mafi girma a nan kasar Sin, ya kai kashi 97 cikin kashi 100 daga cikin duk yawan filin lardin Taiwan. Manyan Duwatsu masu dimbin yawa suna can tsibirin Taiwan. Yawan filin duwatsu da na tudu ya kai kashi 2 cikin kashi 3, amma yawan filin sararin kasa bai kai kashi 1 cikin kashi 3 ba. Dutsen Tsakiya da Dutsen Yushan da Dutsen Xueshan da dutsen Ali kuma da dutsen Gabas ta Taiwan su ne duwatsu biyar a tsibirin Taiwan. Wuraren da ke kusa da layin tsakiyar Taiwan sun fi tsayi, amma wuraren da ke layin tsakiya zuwa gabas ko zuwa yammacin tsibirin Taiwan sun yi kasa-kasa. Ruwan sama ya nufi yamma ko ya nufi gabas a kan dutsen Tsakiya wanda ke zama daga kudu zuwa arewacin lardin Taiwan. Wuri mafi tsayi a Taiwan yana dutsen Yu Shan, inda kwatancin bakin teku kan dutsen Yu Shan ya yi sama da wajen mita 3997.

Yanayi da Kayayyakin Taiwan

Lardin Taiwan yana tsakanin zirin dumi da na zafi. Bugu da kari, domin teku yana kewayen tsibirin Taiwan, iskar teku ta kan daidaita yanayin Taiwan. Ana jin dadin yanayin Taiwan kwarai. A lokacin sanyi, babu sanyi kamar yadda muke nan Beijing, amma a lokacin zafi ma ba a ji zafi sosai ba. Matsakaicin yawan zafi na kowace shekara a tsibirin Taiwan ya kai wajen 22℃. A galibin wuraren Taiwan ba a iya ganin daskararriyar iska mai laima ba sai a wuraren da bakin teku suka yi sama fiye da mita dubu 3. Amma a Taiwan ana ruwan sama kwarai. Iskar Typhoon ma ta kan isa Taiwan.

Yawan filin gandun daji na Taiwan ya kai kashi 1 cikin kashi 2 na duk fadin lardin Taiwan, inda ya ninka kasar Switzerland, wato ana kiranta "kasar daji da ta duwatsu" biyu. Duk yawan gandun daji na Taiwan ya kai cubic mita fiye da miliyan dari 3. A tsibirin Taiwan, domin yanayinsa daga kan duwatsu zuwa kasa suna da bambanci kwarai, yawan ire-iren itatuwa na lardin Taiwan ciki har da itatuwa irin na zafi da na dumi da na sanyi ya kai kusan dubu 4. Saboda haka, ake kiran tsibirin Taiwan wurin ajiye tsire-tsire da itatuwa na halitta a nahiyar Asiya. A lardin Taiwan yawan itacen kafur da aka shuka ya fi yawa a duk fadin duniya. Kafur da man kafur da aka samu daga itacen kafur sun zama kayan musamman na Taiwan da yawansu ya kai kashi 70 cikin kashi 100 da aka samu a duk fadin duniya.

Domin teku ya kewaye Taiwan, ire-ire na kayan teku suna da yawa, kamar misali ire-iren kifi kawai sun kai fiye da dari 5. Biranen Gaoxiong da Jilong da Suao da Hualian da Xingang kuma da Penghu dukkansu sanannen wuraren masunta ne. Ban da wannan, gishirin teku na Taiwan ma ya yi suna sosai.

>>[Yawan mutane da Kabulu]

Yawan Mutanen Taiwan

Kodayake fili ba shi da girma sosai, amma mutane suna da yawa a yankin Taiwan. Ya zuwa karshen shekara ta 2001, duk yawan mutanen Taiwan ya kai miliyan 22 da dubu dari 4, wato akwai mutane 619 a kowane murabba'in kilomita.

Yanzu Taiwan ya riga ya zama yanki mai tsafoffin al'umma. Ya zuwa karshen shekera ta 2001, yawan mutane wadanda shekarunsu da haihuwa yake tsakanin sifiri da 14 ya ragu, wato ya kai kashi 25.8 cikin kashi dari 1 kawai, mutane wadanda shekarunsu da haihuwa suke tsakanin 15 da 64 sun karu sun kai kashi 67.4 cikin kashi dari 1. To, haka kuwa, tsofaffi wadanda shekarunsu da haihuwa ya kai fiye da 65 sun karu har ya kai kashi 6.8 cikin kashi dari 1.

Kimanin yawan mutanen da suke da zama a wurare daban-daban a yankin Taiwan bai kasance daidaici ko balas ba. A yankin Duwatsun da duk filinsu ya kai sulusi da kwatancin bakin teku nasu ya yi sama da fiye da mita dubu 1, mutane fiye da 20 kawai suke da zama a can a kowane murabba'in kilomita. Amma a wasu birane, yawan mutanen da suke da zama a kowane murabba'in kilomita ya kai fiye da 4800, musamman a birnin Taipei da na Gaoxiong da na Taizhong da na Jilong da na Xinzhu da na Jiayi kuma da na Tainan, mutane suna da yawa suna da zama a cikin wadannan birane 7. Duk yawan filin wadannan birane 7 ya kai kashi 2.9 cikin kashi dari 1 kawai, amma duk yawan mutanensu sun kai kashi 31 cikin kashi dari 1.

Hukumar Taiwan ma ta kan gyara manufar yawan mutane domin bunkasuwar zaman al'umma da ta tattalin arziki. Tun shekarar 1965, an fara tafiyar da "Shirin Gida", inda aka kayyade shekarun haihuwar auren mata da maza da ta haihuwa. Ban da wannan kuwa an sa kaimi kan tafiyar da manufar "Yaro daya bai yi kadan ba ne, yara guda biyu sun yi daidai". Daga baya, kimanin yawan haihuwa a Taiwan ya yi ta raguwa a hankali a hankali. Wannan manufa ta ba da gudummawa sosai kan raguwar saurin karuwar yawan mutane a yankin Taiwan. Amma domin saurin karuwar yawan mutane ya ragu, matsalolin karuwar yawan tsofaffi da raguwar leburori sun fito sun kasance a gaban hukumar Taiwan. Saboda haka, a shekarar 1990 ce hukumar Taiwan ta gyara manufar haihuwa, inda aka tsara manufar "Yara Guda biyu sun yi daidai, amma guda uku ba su yi yawa ba". A cikin 'yan shekarun nan, hukumar Taiwan ta sake daukan manufar sa kaimi ga haihuwa.

Kabilun da ke da zama a Taiwan

 

Ana da kabilu da yawa a yankin Taiwan. Amma manyan kabilu suna kunshe da kabilar Han da ta Mongolia da ta Hui da ta Miao da ta Gaoshan. Yawan mutanen kabilar Han ya kai fiye da kashi 97 cikin kashi dari 1 na duk yawan mutanen Taiwan. Kabilar Han kuma ta kunshi mutanen Kejia da mutanen Min. Yawancin kakannin mutanen Min sun zo Taiwan ne daga Quanzhou da Zhangzhou da ke kudancin lardin Fujian na babban yankin kasar Sin. A sa'I daya, yawancin kakannin mutanen Kejia sun je Taiwan ne daga Meizhou da Chaozhou na lardin Guangdong.

Kabilar Gaoshan ita wata muhimmiyar karamar kabila ce a yankin Taiwan. Kodayake har yanzu ba a san ainihin kabilar Gaoshan ba, amma nazarin da aka yi sun fi bayyana cewa, kakannin kabilar Gaoshan sun zo Taiwan ne daga babban yankin kasar Sin. Wasu kabilar Gaoshan suna zaune a filin sararin kasa, wasu kuma suna zaune a yankunan duwatsu daban-daban. Yanzu yawan mutanen kabilar Gaoshan yana ta karuwa. Ya zuwa shekara ta 2001, yawan mutanen kabilar Gaoshan ya riga ya kai dubu 415.

Kabilar Gaoshan tana da sassa daban-daban, wato ta kunshi kabilar Amei da ta Taiya da ta Paiwan da ta Bunong da ta Beinan da ta Lukai da ta Zou da ta Yamei da ta Saixia kuma da ta Shao(wato an kiranta kabilar Cao a da)

>>[Muhimman Birane]

Muhimman Birane a lardin Taiwan

Birnin Taibei

Birnin Taibei, wanda ke arewacin tsibirin Taiwan, ya fi sauran biranen Taiwan girma, yana da fadin murabba'in kilomita wajen 272. Yawan mutanen da ke da zama a birnin Taibei ya kai miliyan 2 da dubu dari 7, inda ya kai kashi 1 cikin kashi 8 na duk yawan mutanen Taiwan.

Birnin Taibei cibiyar cinikayya da masana'antu ce ta lardin Taiwan. An kafa hedkwatocin kamfanoni da masana'antu da bankuna da kantuna wadanda suka fi girma a Taiwan a birnin Taibei. Unguwar masana'antu da ta kasuwanci da ke kunshe da birnin Taibei da karamin lardin Taibei da na Taoyuan kuma da birnin Jilong sun fi girma a duk lardin Taiwan. Birnin Taibei yana kan matsayin cibiyar wadannan unguwoyin.

Bugu da kari, birnin Taibei ya kasance cibiyar al'adu da ta ilmantarwa a lardin Taiwan. Jami'ar Taiwan da Jami'ar koyar da ilmin siyasa ta Taiwan da jami'ar horar da malamai ta Taiwan wadanda suka fi suna a Taiwan da sauran jami'o'i guda 21 tare da kafofi da kamfanonin buga litattafai da gidajen rediyo da cibiyar daukar hoto da dakin karatu da dakin ajiye kayayyakin tarihi wadanda suka fi girma dukkansu suna nan birnin Taibei.

Tsarin zirga-zirga da ake yi a birnin Taibei yana da sauki domin yana daya daga cikin cibiyoyin jirgin kasa da na motoci ne. A tashar ruwa ta Jilong da ta Danshui ne aka fitar da kayayyaki daga birnin Taibei. Filin jirgin sama na kasashen duniya da ke gurin Songshan shi ne mafi girma na 2 a lardin Taiwan.

(Hoton Taibei a dare)

Birnin Gaoxiong

Birnin Gaoxiong wanda ke da fadin murabba'in kilomita 150 kuma da mutane miliyan 1 da dubu dari 5,yana kudu maso yammacin tsibirin Taiwan. Birnin Gaoxiong yana da dogon tarihin raya cinikayya domin an fi raya shi da wurwuri, saboda haka, yanzu masana'antu da cinikayya suna ta samun bunkasuwa da sauri a birnin Gaoxiong.

Birnin Gaoxiong shi kuma muhimmin tushen masana'antu ne daban a lardin Taiwan. Masana'antar sarrafa man fetur da masana'antar sarrafa karfe da ta kera jiragen ruwa wadanda suke birnin Gaoxiong sun fi girma a lardin Taiwan. Ban da wadannan, masana'antu na kayayyakin lantarki da na kera injuna da na yin siminti da na yin sukari da dai sauransu kuwa suna da zamani sosai. Bugu da kari kuwa, Birnin Gaoxiong, tushen kama kifi ne na lardin Taiwan. Masana'antar sarrafa kayan teku da ake yi a teku mai zurfi ta rinjaya a lardin Taiwan.

A birnin Gaoxiong, tsarin zirga-zirga na teku da na kasa har da na sama dukkansu suna da sauki. Tashar teku ta Gaoxiong inda jirgin ruwa mai daukan kaya ton dubu 380 ta shahara a duk duniya. Yawan kayayyakin da aka fitar ko shigar daga tashar teku ta Gaoxiong suna matsayi na 4, wato bayan tashar teku ta Hong Kong da ta Singapore da ta Rotterdam ta kasar Holland. A filin jirgin sama na Gaoxiong, ana da hanyoyin jirgin sama na tabbataccen lokaci da na rikon kwarya masu yawan gaske wadanda suke zuwa daga birnin Gaoxiong zuwa sauran birane na wurare daban-dabam.

Birnin Gaoxiong shi ma wani birni ne mai kyaun gain. A duk shekara, babu lokacin sanyi sai lokacin zafi kamar biranen kasar Najeriya da ke bakin tekun Atlantic.

Birane 5 da ke karkashin mulkin gwamnatin Taiwan kai tsaye

Birnin Taizhong

Birnin Taizhong yana yammacin tsibirin Taiwan, ya fi girma a matsayi na 3 a lardin Taiwan. Yanzu ya riga ya zama cibiyar koyarwa da ta al'adu da ta tattalin arzikin da ta zirga-zirga a yankin tsakiyar Taiwan. Yawan jami'o'in da ke birnin Taizhong ya fi yawa wato a bayan birnin Taibei. Birnin Taizhong shi kuwa cibiyar addinin Budda ne. A kowace shekara ana yin babban taron yada ilmin addinin Budda a Gidan Budda na Baojusi. Bugu da kari, domin a kan kiyaye tsabta a birnin Taizhong, ana kiran birnin Taizhong birni mafi tsabta.

Birnin Tainan

Birnin Tainan yana bakin teku kuma yana kudu maso yammacin tsibin Taiwan. Wannan birnin ya fi girma a matsayi na 4 a lardin Taiwan kuma ya fi sauran biranen Taiwan tsufa. Kafin birnin Taibei ya zama babban birni na lardin Taiwan, birnin Tainan shi ne cibiyar siyasa da ta tattalin arziki da ta al'adu ta Taiwan. A birnin Tainan, akwai wuraren tarihi da na yawon shakatawa da yawa. Bugu da kari, masu bin addinai suna da yawa suna da zama a birnin Tainan inda ke da gidajen addinin Budda da majami'ai dari 2 ko fiye. Wadanda suke bin addinin Budda da na Dao sun fi yawa a birnin Tainan. Ban da wannan kuwa, masu bin addinin Kirista da masu bin addinin Kirista na Rum ma suna da yawa suna da zama a birnin Tainan.

Birnin Jilong

Birnin Jilong, wani birni ne da ke bakin teku da duwatsu da yawa ke kewayansa, yana arewacin tsibirin Taiwan kuma yana fuskatar tekun Gabas. An fi raya wurin da birnin Jilong yake a tsibirin Taiwan. Ta haka ne, tsarin zirga-zirga a birnin Jilong yana da sauki sosai. An kuma raya masana'antun kera jiragen ruwa da masana'antun guba da na haka kwal kuma da na sarrafa kayan teku kwarai a nan birnin Jilong. Wannan birni yana kuma daya daga cikin muhimman wuraren cikinsu. Yawan kifaye da aka kama a birnin Jilong ya kai kashi 1 cikin kashi 5 na duk yawan kifaye da aka kama a duk lardin Taiwan. A birnin Jilong, domin ana nan ana ruwa har kwanaki fiye da 200 a duk shekara, ana kiran birnin Jilong "Tashar Ruwa".

Birnin Xinzhu

Birnin Xinzhu, wato wani muhimmin birnin kimiyya da al'adu wanda ke bakin tekun yammacin tsibirin Taiwan, yana cikin karamin lardin Xinzhu. Jami'ar Tsinghua da Jami'ar koyar da ilmin zirga-zirga da wurin raya masana'antun kimiyya na Xinzhu wadanda suka shahara kwarai a Taiwan dukkansu suna birnin Xinzhu.

Birnin Jiayi

Wannan birni yana cikin karamin lardin Jiayi. Dam na Zengwen wanda ya fi girma a tsibirin Taiwan yana birnin Jiayi.

>>[Tarihin Taiwan]

Tarihin Taiwan

Tarihin Raya Taiwan

Taiwan wani yanki ne da ba za a iya raba shi daga kasar Sin ba. Ilmin labarin kasa ya nuna mana cewa, a shekaru aru aru da suka wuce, Taiwan da babban yankin kasar Sin suna hade da juna. Amma a baya domin an yi girgizar kasa, yankin da ya hada da Taiwan da babban yankin kasar Sin ya fada ya zama wani mashigin teku, Taiwan kuwa ya zama wani tsibiri. Kayayyakin tarihi masu yawan gaske ciki har da naurorin duwatsu da tukwanen baki da masu launi da aka haka su bi da bi sun bayyana cewa, ainihin al'adun Taiwan da na babban yankin kasar Sin da suka kasance kafin a fara rubuta tarihi duk daya ne.

Litattafan tarihi sun gaya mana cewa, a shekarar 230 AD, sarki Sun Quan na kasar Wu ya taba aikawa da janar Wei Wen da Zhu Ge da su jagoranci sojojin ruwa wajen dubu 10 da su ketare mashigin tekun Taiwan su isa tsibirin Taiwan. Wannan ne karo na farko da mazaunan babban yankin kasar Sin suka yi amfani da ilmin zamani wajen raya Taiwan. Ya zuwa karshen karni na 6 da farkon karni na 7, wato lokacin da kasar Sin take daular Sui, har sau 3 sarki Yang ya tura wakilansa zuwa tsibirin Taiwan domin yin rangadin aiki da gai da mazaunan tsibirin Taiwan. Daga baya, a cikin shekaru 600, wato tun daga daular Tang zuwa daular Song, mazaunan babban yankin kasar Sin, musamman mazaunan Quanzhou da na Zhangzhou na lardin Fujian wadanda suke da zama a bakin teku, bi da bi ne suka gudu daga yake-yake da aka yi a babban yankin kasar Sin suka shiga tsibirin Penghu na Taiwan ko suka yi kaura zuwa Taiwan kai tsaye. A Taiwan sun yi noma sun fara raya Taiwan. A shekarar 1335, lokacin da kasar Sin take daular Yuan, an kafa hukumar bincike da take kulawa da harkokin farar hula na Penghu da na Taiwan. Wannan ne karo na farko kasar Sin ta fara kafa hukumar mulki a Taiwan.

Tun lokacin da kasar Sin ta shiga daular Ming, mazaunan babban yankin kasar Sin da na tsibirin Taiwan su kan kai wa juna ziyara. Malam Zhen He, wani sarkin teku na daular Ming na kasar Sin ya taba dan tsayawa a tsibirin Taiwan a kan hanyar da ta kai ziyara a kasashen kudu maso gabashin Asiya. Malam Zhen He ya kai wa mazaunan Taiwan kayayyakin fasahohi da kayan noma da yawa. A shekarar 1628, an yi fari sosai a lardin Fujian, farar hula ba su iya samun abinci ba. Wani mutum mai suna Zhen Zhilong ya tara mutane masu fama da fari sun je Taiwan. A Taiwan sun bude sabbin gonaki da yawa. Tun daga wannan lokaci ne aka fara raya Taiwan sosai.

Zhen Chenggong ya komar da Taiwan a kasar Sin

Bayan tsakiyar karni na 16, tsibirin Taiwan da ke da wadatattun arziki ya zama wurin da kasashen yamma na mulkin mallaka suke son sata. Bi da bi ne kasashen Spain da Portugal suka kai wa tsibirin Taiwan farmaki kuma suka shiga tsibirin Taiwan da karfin tuwo. A Taiwan sun sace arzikinsa ko sun yada addinansu har sun tura sojojinsu sun mamaye Taiwan. A shekarar 1642, mutanen kasar Holland sun kwace wani wurin na arewacin tsibirin Taiwan daga hannun mutanen Spain. Tun daga wannan lokaci, Taiwan ya zama wurin da ke karkashin mulkin kasar Holland.

Lokacin da masu mulkin mallaka na Holland suke Taiwan, sun kwace arzikin Taiwan sosai. Jama'ar Taiwan ma sun yi ta yin gwagwarmaya sosai da Holland. A shekarar 1662, a karkashin taimakon jama'ar Taiwan, malam Zheng Chenggong ya shugabanci sojojinsa ya kau da mutanen Holland daga Taiwan kwata-kwata kuma ya komar da Taiwan a kasar Sin. Amma ba da dadewa ba ne Zheng Chenggong ya kamu da ciwo ya mutu, sai dansa da jikansa suka mulki Taiwan har shekaru 22. Lokacin da Zheng Chenggong da dansa da jikansa suke mulkin Taiwan, sun karfafa guiwar mutanen Taiwan da su yi sukari da kishiri kuma su kafa masana'atu domin raya cinikayya. Bugu da kari, sun sa kaimi wajen bude makarantu da kyautatuwar hanyar sha'anin noma da mutanen kabilar Gao Shan suke bi. Matakan da suka dauka sun ba da amfani sosai wajen raya tattalin arziki da al'adun Taiwan kwarai da gaske. A cikin tarihin Taiwan, wannan wani muhimmin lokaci ne da Taiwan ya samu bunkasuwa. A kan tarihi, an kira wannan lokaci cewar "Lokacin Zheng na daular Ming".

An shigar da Taiwan a cikin taswirar kasar Sin a farkon daular Qing

A shekarar 1683, sojojin gwamnatin daular Qing sun kai farmaki kan Taiwan, Zheng Keshuang da masu goyon bayansa sun yarda da a komar da Taiwan a cikin daular Qing. Ta hakan gwamnatin daular Qing ta kafa unguwa 1 wato unguwar Taiwan wadda take karkashin mulkin lardin Fujian, kuma take kunshe da kananan larduna 3. Sabo da haka, An sake sa Taiwan a karkashin gwamnatin tsakiya ta kasar Sin. Taiwan da babban yanki sun hada kan juna kwarai wajen harkokin siyasa da tattalin arziki da al'adu da dai makamatansu, ta kuma zama wani sashe na duk kasar Sin da ba za a iya raba shi sam sam ba.

A shekarar 1885, gwamnatin daular Qing ta kasar Sin ta canja matsayin Taiwan sai ta zama wani lardin kasar Sin. Mr. Liu Mingchuan shi ne gwamnan farko na lardin Taiwan. Mr. Liu Mingchuan ya kirayi mutane masu yawan gasket na lardin Fujian da na lardin Guangdong da su kaura zuwa Taiwan domin raya Taiwan kwarai. Ban da wannan, Mr. Liu Mingchuan ya kafa babbar hukumar raya Taiwan da babbar hukumar telegraph da babbar hukumar shimfida hanyoyin jirgin kasa da hukumar kera makamai da hukumar cinikayya da dai sauransu. Bugu da kari, Mr. Liu Mingchuan shi ma ya mai da hankali sosai wajen raya al'amuran soja a Taiwan. Bayan Mr Liu Mingchuan ya hau kan mukamin gwamnan lardin Taiwan, an shimfida layin lantarki da kafa gidajen waya da shimfida hanyoyin jirgin kasa da kera jiragen ruwa na kaya kuma da raya masana'antu da cinikayya har an kafa makarantun boko domin raya sha'anin koyarwa da yada al'adu a Taiwan.

Lokacin da Taiwan ke cikin hannun kasar Japan

A karshen karni na 19 da ya wuce, kasar Japan ta tafiyar da manufar yin gyare-gyare kwarai ta kuma kama kan hanyar raya tsarin jari hujja. A shekarar 1894, kasar Japan ta haddasa yaki a tsakaninta da kasar Sin. A shekarar 1895, gwamnatin daular Qing ta kasar Sin wadda ta fadi a cikin wannan yaki ta ci zubar da mutunci ta sa hannu a kan Yarjejeniyar Maguan. Bisa wannan yarjejeniya, kasar Japan ta sami ikon mulki kan tsibirin Taiwan da tsibiran Penghu. Ta hakan Taiwan ta shiga lokacin mulkin mallaka har shekaru 50 a Taiwan.

Bayan kasar Japan ta mamaye Taiwan, ta kafa gidan gwamna a Taibei, wato hukumar koli da ke mulkin Taiwan. Kasar Japan ta kuma kafa kananan gwamnatoci da yawa a duk fadin Taiwan. Ta hakan kasar Japan ta aiwatar da tsarin 'yan sanda da ta yi mulkin mallaka kuma da ta koyar wa jama'ar Taiwan da ilmin yadda za su iya zaman jama'ar sarkin Japana a Taiwan. A sa'I daya, kasar Japan ta raya sha'anin noma da kafa masana'antun sarrafa kayayyakin gona a Taiwan domin biyan bukatar bunkasuwar tattalin arzikin kasar Japan. Sabo da haka, masana'antun sarrafa kayayyaki da sha'anin sufuri da na zirga-zirga sun samu ci gaba a hankali a hankali a Taiwan. Lokacin da ake yin yakin duniya na 2, kasar Japan ta kai hari ga yankunan da ke kudu maso gabashin Asiya, sai ta kara raya masana'antu iri daban-dabam wadanda suka shafi harkokin soja.

An komar da Taiwan a nan kasar Sin da lokacin baraka

Bisa asalin tarihi na Taiwan, lokacin da ake yin yakin duniya na 2, sau da yawa ne aka amince da cewa Taiwan wani yanki ne na kasar Sin da ba za a iya kebe shi daga kasar Sin ba a cikin wasu yarjejeniyoyin kasa da kasa. A ran 1 ga watan Disamba, a cikin Sanarwar Alkahira da kasashen Sin da Amurka da Ingila suka kai ga daddalewa tare, an tsai da kudurin cewa: "Yankunan da kasar Japan ta sata daga kasar Sin, alal misali, Manzhou wato yankin arewa maso gabashin kasar Sin da Taiwan da tsibiran Penghu da dai sauran, dole ne a komar da su a cikin kasar Sin." A ran 26 ga watan Yuli na shekarar 1945, a cikin Sanarwar Potsdam da kasashen Sin da Amurka da Ingila da Soviet Unions suka kai ga daddalewa, an jadadda cewa "Tilas ne za a aiwatar da dukkan abubuwa na Sanarwar Alkahira".

A ran 15 ga watan Augusta na shekarar 1945, kasar Japan ta shelanta cewa ta karbi duk sharudan Sanarwar Potsdam kuma ta ba da kanta ba tare da ko kowane sharadi ba. A ran 25 ga watan Oktoba na wannan shekara, gwamnatin kasar Sin ta yi bikin karbar ba da kai da Japan ta yi a birnin Taibei. Amma sa'annan kuma, gwamnatin kasar Sin ta waccan lokaci wadda ke karkashin jagorancin jam'iyyar Guomingdang ta dauki manufofin kuskure ta yi mulki a Taiwan ta hanyar soja. Ban da wannan jami'an da ke mulkin Taiwan sun ci hanci da rashawa sosai. Wannan ya sa gwamnatin jam'iyyar Guomingdang da jama'ar Taiwan cikin halin adawa da juna kwarai. A ran 28 ga watan Fabrairu na shekarar 1947, jama'ar Taiwan sun yi bore domin fama da gwamnatin jam'iyyar Guomingdang. Gwamnatin Guomingdang ta aika da sojojinta da yawa a Taiwan domin burga jama'ar Taiwan, inda aka yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dubu 30. A tarihi, ana kiran wannan "Matsalar Ran 28 ga watan Fabrairu".

A ran 1 ga watan Oktoba na shekarar 1949, a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, jama'ar kasar Sin sun kau da gwamnatin Guomingdang daga nan babban yankin kasar Sin kuma an kafa sabuwar kasar Sin. Kafin sabuwar gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta kafu, Jiang Jieshi, wato shugaban jam'iyyar Guomingdang da wasu mabiyansa da wasu sojojinsa sun gudu sun je Taiwan. Daga baya, a karkashin taimakawar kasar Amurka, Jiang Jieshi da gwamnatin jam'iyyar Guomingdang sun yi mulki a Taiwan har yanzu. Wannan ya sake sa Taiwan da babban yankin kasar Sin suna cikin halin baraka.

>>[Tarihin Maganar Taiwan]

Tarihin Maganar Taiwan

Bayan da aka sa ayar yakin duniya na 2, bisa dokoki da yarjejeniyoyin kasa da kasa, a hakika dai an riga an dawo da Taiwan a nan kasar Sin. Dalilin da ya sa maganar Taiwan ta bullo shi ne yakin basasa da aka yi a tsakanin sojojin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da na jam'iyyar Guomingdang bayan yakin duniya na 2. Amma dalilin da ya fi muhimmanci shi ne kasashen waje sun tsoma baki a cikin harkokin gida na kasar Sin.

Maganar Taiwan da yakin basasa da jam'iyyar Guomingdang ta haddasa

Lokacin da ake yin yaki da mahara na Japan, jam'iyyar Guomingdang da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin sun hada karfi domin yaki da harin da kasar Japan ta kai wa kasar Sin. Bayan da aka kori sojojin Japan daga nan kasar Sin, a karkashin taimakawar kasar Amurka ne, gwamnatin jam'iyyar Guomingdang wadda ke karkashin jagorancin Jiang Jieshi ta haddasa yakin basasa a nan kasar Sin. Babu sauran hanyar da za ta iya zaba sai jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta shugabanci jama'ar kasar Sin da su yi yaki da sojojin jam'iyyar Guomingdang har shekaru 3. A shekarar 1949 an kau da gwamnatin Jamhuriyar Sin wadda ke karkashin jagorancin jam'iyyar Guomingdang kwata kwata. A ran 1 ga watan Oktoba na shekarar 1949, Jamhuriyar Jama'ar Sin ta kafu da kuma ta zama gwamnatin da aka kafa ta bisa doka kadai a nan kasar Sin. Bayan an kau da gwamnatin Jam'iyyar Guomingdang, yawancin jami'ai da sojojin jam'iyyar babu inda za su iya gudu a nan kasar Sin sai tsibirin Taiwan da ke kudu maso gabashin kasar Sin. A karkashin goyon bayan gwamnatin Amurka, gabobi biyu da ke tsakanin mashigin tekun Taiwan har yanzu suna cikin halin baraka.

Maganar Taiwan da nauyin gwamnatin Amurka

Bayan da aka gama yakin duniya na 2, a cikin halin adawa da juna a tsakanin rukunoni biyu na Gabas da Yamma a nan duniya, bisa tushen tsarinta na aikin soja na dogon lokaci da kuma kiyayen moriyarta, kasar Amurka ta taba kebe kudi da samar da makamai da mutanenta ga hukumar jam'iyyar Guomingdang domin nuna mata goyon baya a cikin yakin basasa na kasar Sin da kuma yunkurin kawar da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a nan kasar Sin kwata kwata. Amma daga karshe, gwamnatin Amurka ba ta cimma burinta da ta tsara ba sam sam.

Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, gwamnatin kasar Amurka ta dauki manufofin ware da burga sabuwar kasar Sin. Bayan faruwar yakin Korea, da karfin tuwo ne kasar Amurka ta sa hannu a kan dangantakar da ke tsakanin gobobi biyu a tsakanin mashigin tekun Taiwan na kasar Sin, wato harkokin gida na kasar Sin. A shekarar 1950, rukuni na 7 na jirgin soja na kasar Amurka ya shiga mashigin tekun Taiwan, rukunin 13 na jirgin sama na kasar Amurka ya kuma fara zama a Taiwan. A watan Disamba na shekarar 1954, kasar Amurka da hukumar Taiwan sun kai ga daddale Yarjejeniyar Tsaron Taiwan Tare, inda aka sa lardin Taiwan na kasar Sin a karkashin kiyayewar Amurka. Domin gwamnatocin kasar Amurka sun kara bin manufar kuskure ta sa hannu a cikin harkokin gida na kasar Sin, wannan ya sa dangantakar da ke tsakanin gabobi biyu a tsakanin mashigin tekun Taiwan ta tsananta sosai, maganar Taiwan ma ta zama matsala mafi muhimmanci da ke kasancewa a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, kuma kasashen biyu su kan yin gwagwarmaya a kan wannan magana.

Amma halin da ake ciki a nan duniya yana ta samun sauye-sauye, kasar Sin ta samu bunkasuwa sosai bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, kasar Amurka ta fara canja manufarta game da kasar Sin. Dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka ta fara samun ci gaba. A watan Oktoba na shekarar 1971, a gun babban taron majalisar dinkin duniya an zartas da kuduri mai lamba 2758, inda aka maido da dukkan ikon Jamhuriyar Jama'ar Sin a MDD, kuma aka kori wakilin hukumar Taiwan daga MDD. A watan Fabrairu na shekarar 1972, shugaban kasar Amurka Mr. Richard Nixon ya kawo wa kasar Sin ziyara, bangarorin kasar Sin da kasar Amurka sun bayar da wata hadaddiyyar sanarwa a birnin Shanghai na kasar Sin. Wannan Hadaddiyar Sanarwar Shanghai ta jadadda cewa, "bangaren Amurka ya bayyana cewa, kasar Amurka ta gane cewa, Sinawan da ke da zama a yankunan da ke tsakanin mashigin tekun Taiwan dukkansu sun tsaya tsayin daka kan matsayin Sin daya tak a nan duniya, Taiwan wani yankin kasar Sin ne. Gwamnatin kasar Amurka ba ta ba da ra'ayi daban game da wannan matsayi ba."

A watan Disamba na shekarar 1978, gwamnatin kasar Amurka ta karbi ka'idodjin 3 na kafa dangantakar diplomasiyya a tsakaninta da Sin, kuma suka bayar da sanarwa tare, watau Amurka ta yanka dangantakar diplomasiyya da ke tsakaninta da hukumar Taiwan ta soke Yarjejeniyar Tsaron Taiwan Tare da kuma ta janye sojojinta daga Taiwan. Ta hakan kasashen Sin da Amurka sun kafa dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu a ran 1 ga watan Janairu na shekarar 1979. Hadaddiyar Sanarwar Kafa Dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Amurka ta bayyana cewa: "Kasar Amurka ta amince da cewa, gwamnatin Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin ita ce gwamnati kadai wadda take wakiltar kasar Sin. Bisa wannan tushe, jama'ar kasar Amurka za ta yi cudanya da jama'ar Taiwan a fanonnin al'adu da ciniki da kuma sauran dangantakar da ba ta gwamnati ba". Ban da wannan, "Gwamnatin kasar Amurka ta amince da matsayin Sin daya tak da kuma Taiwan wani yankin kasar Sin ne."

Amma abin bakin ciki shi ne sai watanni 3 kawai bayan kafuwar irin wannan dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, an zartas da "Doka game da dangantakar da ke tsakanin kasar Amurka da Taiwan" a zauren majalisun dokokin kasar Amurka, shugaban kasar Amurka ma ya sa hannu a kan wannan doka sai wannan doka ta fara aiki. Wannan doka wadda aka kafa ta bisa hanyoyin kafa dokokin gida na kasar Amurka, tana kunshe da babi da yawa da suke karya ka'idar Hadaddiyar Sanarwar kafa dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Amurka da ka'idojin dokokin kasa da kasa. Bisa wannan doka, gwamnatin kasar Amurka ta ci gaba da sayar wa Taiwan da makamai da kuma sa hannu a cikin harkokin gida na kasar Sin har da ta hana dinkuwar Taiwan da babban yankin kasar Sin.

Domin daidaita maganar sayar wa Taiwan da makamai da kasar Amurka ta yi, gwamnatocin kasar Sin da kasar Amurka sun yi shawarwari kuma sun kai ga daddale wata yarjejeniya a ran 17 ga watan Augusta na shekarar 1982. Wannan Hadaddiyar Sanarwa ta 3 ce da ta shafi dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, ana kiran ta Sanarwar ran 17 ga watan Augusta. A cikin wannan sanarwa, gwamnatin kasar Amurka ta bayyana cewa, ba za ta bi wata manufar sayar wa Taiwan da makamai a cikin dogon lokaci mai zuwa ba. Inganci da yawan makaman da za ta sayar wa Taiwan ma ba za ta wuce na makaman da ta sayar wa Taiwan a cikin 'yan shekarun da suka wuce bayan da kafuwar dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka ba, kuma za ta rage yawan makaman da za ta sayar wa Taiwan a hankali a hankali. Daga karshe za a warware wannan matsala bayan wasu lokuta. Amma a hakika dai, a cikin dogon lokacin da ya wuce, ba ma kawai gwamnatin kasar Amurka ba ta bi wannan Sanarwar ran 17 ga watan Augusta ba, har ma ta kan karya wannan sanarwa, har a watan Satumba na shekarar 1992, gwamnatin kasar Amurka ta tsai da kudurin cewa za ta sayar wa Taiwan da jiragen yaki na F-16 guda 150. Wannan kudurin da gwamnatin kasar Amurka ta yi ta sa sabon mahani kan hanyar raya dangantakar da ke tsakaninta da kasar Sin da daidaita maganar Taiwan.

Sabo da haka, dalilin da ya sa har yanzu ba a daidaita maganar Taiwan ba shi ne gwamnatin kasar Amurka tana sa bakin cikin wannan magana.

>>[Ka'idar da gwamnatin kasar Sin take bi wajen daidaita matsalar Taiwan]

Ka'idar da gwamnatin kasar Sin take bi

wajen daidaita matsalar Taiwan

Ka'idar da gwamnatin kasar Sin take bi wajen daidaita matsalar Taiwan

Ka'idar da gwamnatin kasar Sin take bi wajen daidaita matsalar Taiwan ita ce: "Dinkuwar duk kasa cikin lumana" da kuma "Kasa daya amma tare da tsari biyu"

A shekaru 50 na karnin da ya wuce, gwamnatin kasar Sin ta taba tsara shirin daidaita matsalar Taiwan cikin lumana. A ran 1 ga watan Janairu na shekarar 1979, zaunannun kwamitin majalisar dokokin jama'a ta kasar Sin ya bayar da "Sanarwa ga 'Yan Uwanmu na Taiwan" inda aka yi kira da a yi shawarwari kan yadda za a kawo karshen aikin soja na adawa da juna da ake ciki a tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan. Gwamnatin kasar Sin ta kuma bayyana cewa, lokacin da ake dinke duk kasar Sin baki daya, tilas ne a girmama halin da ake ciki yanzu a Taiwan kuma a dauki ka'idoji da manufofin da ke daidai halin da ake ciki a Taiwan."

A ran 30 ga watan Satumba na shekarar 1981, shugaban majalisar dokokin jama'ar kasar Sin Mr. Ye Jianying ya yi jawabi, inda ya kara da bayyana ka'idar da gwamnatin kasar Sin take bi wajen daidaita matsalar Taiwan. Mr. Ye ya ce: "Bayan an dinke duk kasar Sin gaba daya, Taiwan zai iya zama yankin musamman mai cin gashin kanta sosai."

A shekarar 1982, lokacin da yake ba da sharhi kan jawabin da Mr. Ye Jianying ya yi, Mr. Deng Xiaoping ya nuna cewa, a hakika dai, ma'anar "Kasa daya amma tare da tsari biyu" it ace, a karkashin tushen tabbatar da dinkuwar duk kasa gaba daya, za a iya tafiyar da tsarin gurguzu a babban yanki, amma za a iya ci gaba da tafiyar da tsarin ra'ayin jarin-hujja a Taiwan.

A ran 12 ga watan Oktoba na shekarar 1992, babban sakatare Jiang Zeming na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya nuna cewa: "Za mu ci gaba da neman dinkuwar mahaifa bisa ka'idojin 'Dinkuwar duk kasa cikin lumana' da 'Kasa daya amma tare da tsari biyu'"

Ma'anar "Dinkuwar duk kasa gaba daya cikin lumana" da "Kasa daya amma tare da tsari biyu"

Ma'anar "dinkuwar duk kasa gaba daya cikin lumana" da "kasa daya amma tare da tsari biyu" da gwamnatin kasar Sin take bi wajen daidaita matsalar Taiwan ta kunshi abubuwan da za a ambata a baya.

1, Sin daya tak. Akwai Sin daya tak a nan duk duniya, Taiwan wani yanki ne da ba za a iya raba shi daga kasar Sin ba. A kafa gwamnatin tsakiya a birnin Beijing. Wannan tushen da ake ciki lokacin da ake daidaita matsalar Taiwan cikin lumana.

2, Tsari biyu za su yi zaman tare. Wato a karkashin tushen tabbatar da dinkuwar duk kasa gaba daya, za a tafiyar da tsarin gurguzu a babban yanki, amma za a ci gaba da tafiyar da tsarin ra'ayin jari-hujja a Taiwan.

3, Mulkin kanta sosai a Taiwan. Bayan an dinke duk kasar Sin gaba daya, Taiwan za ta zama yankin musamman, matsayinta ba kamar yadda sauran lardunan kasar Sin suke ba, tana da ikon mulkin kanta sosai.

4, yin shawarwari cikin lumana bisa halin da ake ciki yanzu a tsakanin gobobi biyu na mashigin tekun Taiwan, gwamnatin kasar Sin tana fatan kafin a dinke duk kasar Sin gaba daya, bisa ka'idar girmama wa juna da neman moriyar juna, gabobi biyu da ke tsakanin mashigin tekun Taiwan za su ingiza hadin kan tattalin arziki da yin musaye-musaye a tsakaninsu a cikin hali mai yakini. Ban da wannan, za a iya yin musayar wasiku da yin ciniki da yin zirga-zirga a tsakanin gabobi biyu kai tsaye domin kafa sharudan dinkuwar duk kasar Sin gaba daya cikin lumana.

Ra'ayoyi 8 kan yadda za a iya ingiza dinkuwar duk kasar Sin gaba daya

A ran 30 ga watan Janairu na shekarar 1995, a gun shagalin murnar gargajiyar ranar sabuwar shekara ta kasar Sin da ofishi mai kula da harkokin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da na majalisar gudanarwa ta gwamnatin kasar Sin ya shirya, shugaban kasar Sin Mr. Jiang Zeming ya yi jawabi, inda ya bayar da "Ra'ayoyi 8 kan yadda za a iya ingiza dinkuwar mahaifa gaba daya". Wadannan ra'ayoyi 8 su ne, daga farko a tsaya tsayin daka kan ka'idar Sin daya tak. Na biyu, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ba ta ki yarda ba da jama'ar Taiwan su raya dangantakar tattalin arziki da ta al'adu a tsakaninsu da jama'ar sauran kasashen waje ba, amma ta ki yarda da hukumar Taiwan ta yi harkoki na wai kara "wurin kasancewa a duniya". Na uku, yin shawarwari kan maganar dinkuwar kasar Sin gaba daya cikin lumana a tsakanin gobobi biyu. Na hudu, A yi kokari kan yadda za a cimma burin dinkuwar duk kasar Sin gaba daya cikin lumana da kuma Sinawa ba su yi yaki da juna ba. Na biyar, a kara yin musaya da hadin guiwa kwarai a fannonin tattalin arziki a tsakanin gobobi 2. Na shida, 'yan uwa na gobobi biyu su raya kyawawan al'adun kasar Sin tare. Na bakwai, a girmama wa hanyar zamantakewar jama'ar Taiwan da fatansu na zama masu mulkin Taiwan. Na takwas, mu yi maraba da shugabannin hukumar Taiwan da su kawo wa babban yanki ziyara a matsayin halin daidaici, mu ma muna son kai wa Taiwan ziyara bisa gayyatar da hukumar Taiwan ta yi mana domin yin shawarwari tare kan harkokin kasa, ko a farko a yi musayar ra'ayoyi kan wasu matsalolin da ke kasancewa a gabanmu.

>>[Halin Cinikayya da Yin Musayar Tattalin Arziki Tsakanin Gobobi Biyu Na Mashigin tekun Taiwan]

Halin cinikayya da yin musayar tattalin arziki da ake yi ciki

a tsakanin gobobi 2 na mashigin tekun Taiwan

A cikin shekaru 30, wato tun daga shekarar 1949 zuwa shekarar 1978, domin rikice-rikicen soja su kan faru a mashigin tekun Taiwan, dangantakar da ke tsakanin babban yanki da Taiwan ma ta tsananta sosai, kusan ba a yi ciniki a tsakanin babban yanki da Taiwan ba, sai dai a shigar da wasu maganin gargajiya na kasar Sin a yankin Taiwan domin ba a iya samunsu a Taiwan ba. Dole ne daga farko a shigar da maganin gargajiya na kasar Sin ta Hongkong, daga baya, sai a shigar da su zuwa Taiwan, kuma yawansu ya yi kadan kwarai.

Bayan shekarar 1979, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai da yawa domin raya dangantakar tattalin arziki a tsakanin babban yanki da Taiwan na kasar Sin. Hukumar Taiwan ma babu hanyar da za ta iya zaba sai ta daidaita manufar yin ciniki da babban yanki, inda ta rage wasu kayadaddun manufofi a hankali a hankali. Ya zuwa karshen watan Satumba na shekara ta 2003, jimlar kudaden cinikayya da aka yi a tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan ta kai dolar Amurka biliyan 309 da miliyan 180, daga cikinsu, yawan kudaden ciniki da aka yi domin fitar da kayayyaki daga babban yanki zuwa Taiwan ya kai dolar Amurka biliyan 48 da miliyan 890, amma an shigar da kayayyakin Taiwan a nan babban yankin kasar Sin da suka kai dolar Amurka biliyan 260 da miliyan 290. Sabo da haka, riban da kamfanonin Taiwan suka samu ya kai dolar Amurka biliyan 211 da miliyan dari 4. Tun daga shekarar 1991, babban yanki ya zama wuri mafi girma da Taiwan take samun riba. A sa'i daya, Taiwan ma tana daya daga cikin wurare mafi muhimmanci da babban yanki na kasar Sin ya samu jarin waje.

Yanzu, ainihin halin musamman na cinikayya da ake ciki a tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan shi ne, daga farko, har yanzu ba a iya yin ciniki a tsakanin gabobi biyu kai tsaye ba, kuma sai 'yan kasuwa na Taiwan suna iya zuba jarinsu a nan babban yanki, inda suke kafa masana'antu da yin musayar kimiyya da fasaha da yin musayar sha'anin kudi da yin horarwa. Na biyu, dangantakar cinikayya da ke tsakanin gabobi biyu tana cikin halin da ba na kai tsaye ba da halin rashin daidaituwa da kuma sai mutanen Taiwan ne suke zuwan nan babban yanki kullum, amma mutanen babban yanki ba su iya samun izinin zuwa Taiwan kuma ba su iya zuba jari a Taiwan. Domin hukumar Taiwan ta kayyade, 'yan kasuwan Taiwan ma ba su iya zuba jari a babban yanki kai tsaye ba, sai dai su yi rijistar wani kamfani a wuri na 3 a farko, daga baya sai su zuba jari a nan babban yanki na kasar Sin a matsayin kamfanin da ya yi rajista a wuri na 3. Amma idan jarin da zai zuba a nan kasar Sin bai kai dolar Amurka miliyan 1 ba, zai iya zuba su a nan babban yanki a matsayin kamfanin Taiwan, amma ya shigar da jarinsa a nan babban yanki ta sauran wuri na 3. Ban da wannan, hukumar Taiwan ta ki yarda da a yi ciniki a tsakanin Taiwan da babban yanki kai tsaye, har yanzu, ana yin ciniki a tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan ba kai tsaye ba sai ya kai kayansa a wuri na 3 tukuna, daga baya zai iya kawo kayansa a nan babban yanki. Bugu da kari, har yanzu, hukumar Taiwan ta hana shigar da jarin babban yanki a Taiwan. Sabo da haka, cinikin da ake yi a tsakanin Taiwan da babban yanki ba ya cikin halin daidaici. Na uku, a 'yan shekarun nan, tattalin arzikin Taiwan da na baban yanki suna dogara kan juna da kuma fara shiga halin moriyar juna.

Musaye-musaye a fanonni 3 da Ake yi

a Tsakanin Gobobi Biyu Na Mashigin tekun Taiwan

A shekarar 1979, gwamnatin kasar Sin ta bayar da ra'ayinta na yin waya da yin ciniki da kuma yin zirga-zirga a tsakanin Taiwan da babban yanki na kasar Sin kai tsaye, wato ana kiransu "musaye-musaye a fanonni 3" a takaice. A cikin shekaru fiye da 20 da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta yi namijin kokari ba tare da kasala ba wajen ingiza wadannan al'amura.

Halin da ake ciki wajen ayyukan raya musaye-musaye a fanonni 3 a tsakanin gobobi 2

Yin musayar wasiku: A wajen aikin musayar wasiku, kungiyar kula da dangantakar da ke tsakanin gobobi 2 na mashigin tekun Taiwan da asusun yin musaya a tsakanin gobobi 2 na mashigin tekun Taiwan sun kai ga daddale Yarjejeniyar binciken wasikun rajista da biyan diyyarsu a tsakanin Gobobi 2 na mashigin tekun Taiwan. Bisa wannan yarjejeniya, gidajen waya na gobobi biyu sun fara aikawa da wasikun rajista a tsakaninsu.

A wajen harkokin wayar tarho, a shekarar 1996, kamfanin wayar tarho na kasar Sin da takwaransa na lardin Taiwan kamfanin wayar tarho na Jamhuriyar Sin sun kafa dangantaka a tsakaninsu, yanzu za a iya buga waya a tsakanin lardin Taiwan da babban yanki na kasar Sin kai tsaye.

Zirga-zirgar da ke tsakanin gobobi 2 na mashigin tekun Taiwan. A wajen yin zirga-zirga kan teku, a watan Aflilu na shekarar 1997, jiragen ruwa na kaya sun fara yin zirga-zirgar gwaji a kan hanyoyin da ke tsakanin birnin Fujian da birnin Shamen na babban yankin kasar Sin da birnin Gaoxiong na Taiwan. A farkon shekara ta 2001, hukumar babban yankin kasar Sin ta ba da taimako sosai kan yadda jiragen ruwa za su iya yin zirga-zirga a kan teku a tsakanin tsibiran Jinmen da Ma da yankunan lardin Fujian da ke bakin teku. Jiragen ruwa na fasinjoji da na kaya na kamfanonin zirga-zirga na gabobi biyu sun fara aiki a wadannan hanyoyin teku.

A wajen zirga-zirga ta sama, a watan Disamba na shekarar 1995 da watan Augusta na shekarar 1996, bi da bi ne kamfanin Macau Airways da kamfanin Ganglong na Hongkong suka bude hanyoyin sama daga Taiwan zuwa Macau da kuma daga Taiwan zuwa Hongkong, sannan kuma mutanen Taiwan za su zo nan kasar Sin daga Macau ko daga Hongkong.

Yin ciniki da juna Tun daga shekarar 1979, hukumar babban yanki na kasar Sin ta bude kasuwa ga kayayyakin Taiwan. Hukumar babban yanki ta kuma rage da soke harajin kayayyakin Taiwan. A shekarar 1978, yawan kudin cinikayya da aka yi a tsakanin babban yanki da lardin Taiwan na kasar Sin ya kai dolar Amurka miliyan 46 kawai, amma a shekarar 2003, wannan adadi ya karu, wato ya kai fiye da dolar Amurka biliyan 58.3. Bisa kidayar da aka yi a shekarar 2002, babban yanki ya riga ya zama kasuwa mafi girma ga 'yan kasuwa na Taiwan. Taiwan ya kuma zama kasuwa mafi girma ta biyu ga babban yanki wajen shigo da kayayyaki.

A wajen zuba wa juna jari. Hukumomi da wurare daban-dabam na babban yanki na kasar Sin sun kara ta kyautata muhallin samun jari. Ya zuwa karshen shekarar 2003, jimlar masana'antun da hukumomin babban yanki ya amince da mutanen Taiwan suka zuba jari a babban yanki ta kai kusan dubu 60, inda kudin kwangila ya kai dolar Amurka biliyan 68, jimlar jarin da aka riga aka yi amfani da su ta kai dolar Amurka biliyan 36. Tun daga shekarar 1993, babban yanki ya riga ya zama wurin da 'yan kasuwa na Taiwan suka fi son zaba don zuba jari. A wajen yin musayar sha'anin kudi, yawan bankunan Taiwan da suka kafa ko suke neman izinin kafa ofisoshi a nan babban yanki ya riga ya kai guda 10, yawancinsu suna birnin Shanghai da birnin Beijing.

Amma har yanzu, yin musaye-musaye a fanonni 3 yana cikin halin da ba na kai tsaye ba, kuma ba a duk fanonni ba. Ban da wannan ana yin musaye-musaye a fanonni 3 sai daga Taiwan zuwa nan babban yanki kawai, amma kamfanonin babban yanki ba su samu izinin zuwa Taiwan ba.

A wajen harkokin gidan waya, ba a iya kai wasiku daga babban yanki zuwa Taiwan kai tsaye ba. Idan ana son kai wata wasika zuwa Taiwan, dole ne daga farko, a kai wannan wasika zuwa Hongkong, sannan kuma a kai wannan wasika daga Hongkong zuwa Taiwan. Ban da wannan, har yanzu, ba a iya kai kananan kunshin kaya da kudi daga babban yankin zuwa Taiwan ba.

A wajen yin zirga-zirga. Jiragen ruwa da jiragen sama na gobobi 2 ba su iya yin zirga-zirga a tsakanin babban yanki da Taiwan na kasar Sin kai tsaye Ba. Kowa yana son zuwa Taiwan ko zuwa nan babban yanki, dole ne daga farko ya je Hongkong ko Macau, sannan kuma ya zo nan babban yanki ko ya je Taiwan daga Hongkong ko Macau. Jiragen ruwa da jiragen sama na kaya ma dole ne daga farko su je wani wuri na 3 kamar misali Japan ko Hongkong, daga baya za su iya tafiya Taiwan ko zuwa nan babban yanki.

A wajen ciniki ma, babban yanki ya riga ya bude kasuwa ga 'yan kasuwa da kayayyaki na Taiwan kwata-kwata, amma 'yan kasuwa da kayayyaki na babban yanki ba su samu izinin zuwa Taiwan ba.