logo

HAUSA

Babi19: Wasan Kwaikwayo

2020-10-30 10:07:47 CRI

Babi19:Wasan Kwaikwayo

>>[Wasan Kwaikwayo na Beijing]

Fuskar wasan kwaikwayo na Beijing

Wasan kwaikwayo na Beijing wato Beijing Opera na kasar Sin a kan kira cewa , shi ne wasan kwaikwayo na wake-wake na gabas . Dalilin da ya sa ya sami wannan suna shi ne saboda ya tasttara abubuwa masu kyau na wasannin kwaikwayo daban daban, kuma an haifar da shi a nan birnin Beijing.

'Yan wasa

A cikin wasan Beijing Opera na kasar Sin akwai manyan 'yan wasa guda 4 . Su ne mai gida da uwar gida ko yarinya da 'dan fuska mai furani (flowery face) da kuma 'dan kama mai ban dariya.

Tsoho Matasa Thohuwa

Qing Yi Wu Jing Wen Chou

Mai gida yana nufin wani namiji wanda yake da shekaru 30 zuwa 50. A galibin lokaci ya zama babban mutum ko sarki ko janar ko minista .

Uwar gida tana nufin wata mace wadda take da shekaru 30 zuwa 50 . A galibin lokaci ta zama matar babban jami'i. Yarinya akwai iri biyu . Ta farko yarinya tana dauke da makamai kuma ta iya wasan sanda ko wuka . Ta biyu budurwa ce . A galibin lokaci ta zama yarinyar gida ko mai yin aikin hidima ga matar babban jami'i.

'Dan fuska mai furani yana nufin mutum wanda aka shafa launuka daban daban a kan fuskarsa. A galibin lokaci ya zama namiji mai kirki ko wanda yake da halin musamman.

'Dan kama mai ban dariya yana rayuwa a cikin rukuni maras karfi . Galibinsu suna da wayo ko abin da suka yi mai ban dariya ne. (Ado)

Wasan kwaikwayo na Beijing

Wasan kwaikwayo na Beijing wato Beijing Opera na kasar Sin a kan kira cewa , shi ne wasan kwaikwayo na wake-wake na gabas . Dalilin da ya sa ya sami wannan suna shi ne saboda ya tasttara abubuwa masu kyau na wasannin kwaikwayo daban daban, kuma an haifar da shi a nan birnin Beijing.

Wasan kwaikwayon Beijing yana da tarihin shekaru fiye da 200 . Mafarinsa shi ne tsohon wasan kwaikwayo na Anhui dake kudancin kasar Sin . A shekarar 1790 , kungiyar wasan kwaikwayon Anhui ta farko ta shiga Beijing dong halartar nune-nunen ranar haihuwar Sarki . Bayan haka kungiyoyin wasan kwaikwayon Anhui sun zo nune-nune a Beijing bi da bi . A karshen karni na 19 zuwa farkon karni na 20 , bayan da aka yi tattara abubuwa masu kyau cikin shekaru masu yawa , sai aka haifar da wasan operar Beijing.

Wasan operar Beijing yana da shirye-shirye masu yawa. Kwararrun mutanen wasan suna da yawa . Kungiyoyin nune-nunen wasan kuma suna da yawa

Yawan 'yan kallon wasan operar Beijing da tasirin da ya kawo ya kai matsayi na farko a nan kasar Sin a cikin dukannin wasannin kwaikwayo .

Mei Lanfang shi ne daya daga cikin 'yan fasahar wasan operar Beijing wadanda suka fi suna a duniya . An haife shi a shekarar 1894. Lokacin da ya cika shekaru 8 da haihuwa, ya fara koyon rera wasan operar Beijing .A shekarar 1905 wato yayin da yake da shekaru 11 da haihuwa , sai ya hau dakali don nuna fasaharsa . A cikin rayuwarsa mai tsawon shekaru fiye da 50 , Mr. Mei ya haifar da halin musamman na fasaharsa . Shi namiji ne , amma a cikin shekaru 50 da suka wuce , kullum ya yi wasan da kayan Uwar gida ko yarinya.

('Yan wasa masu suna: Mei Lanfang, Chen Yanqiu, Gou Huisheng, Shang Xiaoyun)

A shekarar 1919 Mei Lanfang ya jagoranci kungiyar wasan operar Beijing zuwa kasar Japan . Wannan karo na farko ne da aka nuna fasahar wasan operar Beijing a kasar waje . A shekarar 1930 , Mr. Mei ya jagoranci kungiyar zuwa kasar Amurka don nune-nune da ziyarce-ziyarce , kuma ya sami babbar nasara . A shekarar 1934 , bisa gayyatar da aka yi masa , ya kai ziyara a Turai kuma ya sami yabo da maraba daga rukunin wasan kwaikwayo na kasashen Turai. (Ado)

>>[Wasan Kwaikwayo na Larduna]

Wasan kwaikwayon Huangmei

Wasan kwaikwayon Huangmei sunansa na da shi ne muryar Huangmei ko wasan kwaikwayon cire ganyn ti . Shi ne wani karamin wasan kwaikwayo na jama'a a shiyyar dake iyakar tsakanin larduna 3 wato Anhui da Hubei da Jianxi . Daya daga cikinsu ya kaura zuwa shiyyar Anqing wadda cibiyarta ita ce Gundumar Huaining ta Lardin Anhui . Sa'an nan kuma ya hade da fasahar jama'a ta wannan wuri , kuma ya haifar da halin musamman na kanta. Wannan mafari ne na wasan kwaikwayon Huangmei .

A tsakiyar karni na 19 wannan wasan ya shigo da muryar Qingyang . Ta haka an karfafa dadin wasan Operar Huangmei. Daga shekara zuwa shekara a hankali a hankali mutanen kasar Sin sun san shi kuma suna kaunarsa .

Shirin wani manomi ya yi aure da wata yarinya dake samaniya ya bayyana wani labari mai ban sha'awa . Manoma da kauyawa suna son irin wannan shiri kwarai da gaske wanda ya bayyana fatan alheri da jin dadinsu .

Sauran shirye-shirye masu kyau na wasan kwaikwayon

Huangmei Akwai mai kiwon shanu da yarinya mai sake-sake da kuma Mijin gimbiya 'yar daudu da kuma Miji da mata sun yi kallon fitilu wadanda suka yi suna a wuraren da ke kudancin kasar Sin . (Ado)

Wasan kwaikwayon Kun

A cikin dogon lokacin tarihi , wasan kwaikwayon Kun ya taba samun sunan babbar muryar Kunshan. A da sabo da aka yi wasan a kan dakalin da ake shirya a gindin Tudu , shi ya sa a kan kira shi cewa , wasan operar tudun Kunshan . Bayan da aka kafa Jamhuriyar jama'ar kasar Sin an fara yin amfani da Wasan kwaikwayon Kunshan . Wannan wasan yana yaduwa a kudancin lardin Jiangsu da birnin Shanghai . Wannan wasan daya ne daga cikin wasannin kwakwayo mafiya kasance da tasiri .

Wasan kwaikwayon Kunshan , an haifar da shi a karshen Daular Ming zuwa farkon Daular Chin . A farkon lokaci an mai da hankali kan rera opera da murya kawai , shi ya sa ya sami kaunar jama'a farar hula . Saboda haka ya sami yalwatuwa da saurin gaske .

Bayan da aka haifar da wasan kwaikwayon Kunshan , an sami rukunoni masu bambanci guda 2. Rukuni na farko shi ne muryar Xiangfu dake birnin Kunshan . Rukuni na biyu shi ne muryar birnin Shanghai. .

Lokacin da ake yi wasan kwaikwayon Kunshan a kan yi amfani da wasu kayayyakin kide-kide . A cikinsu akwai sorewa da goge tamkar molo da pipa da kakakin sona da sauransu . Wasan kwaikwayon Kunshan yana da halin musamman sosai na wurin kudancin kasar Sin , kuma ya bayana zaman yau da kullum na jama'a farar hula .

Bayan da operar Kun ya yi dogon lokaci har ya kai shekaru 230 . Daga Sarki Longqing na Daular Ming zuwa farkon shekarar Sarki Jiaqing na Daular Ching wato daga shekarar 1570 zuwa shekarar 1800 , fasahar wasan kwaikwayon Kun ta fi haske kuma ta fi shahara a kasar Sin .

Wasan kwaikwayon Kun yana da shirye-shirye masu faranta rai da yawa . Duk shirye-shiryen suna da talifi da adabi sosai . Kowane shirin da aka nuna ya hade da fayfai mai dadin ji . Wasan kwaikwayon Kun yana hade fasahar wake-wake da raye-raye da musanyar miyau da motse-motsen jiki . Ma iya cewa wannan wasan cikakkiyar fasaha ce mai jawo hankunan mutane .

Wasan kwaikwayon Kun ya wakilci wasannin kwaikwayon kasar Sin . Kuma ya kawo tasiri kai-tsaye ga Wasan operar Beijing da na Sichuan da na Hunan da na Shaoxing da na Huangmei . Wannan dalili ne da ya sa a kan kira wasan kwaikwayon Kun da kakan wasannin kwaikwayo dari . (Ado)

Wasan kwaikwayon Henan

A cikin dogon lokacin tarihi , wasan kwaikwayon Henan ya taba samun sunan babbar muryar Henan. A da sabo da aka yi wasan a kan dakalin da ake shirya a gindin Tudu , shi ya sa a kan kira shi cewa , wasan operar tudu . Bayan da aka kafa Jamhuriyar jama'ar kasar Sin an fara yin amfani da Wasan kwaikwayon Henan . Wannan wasan yana yaduwa a lardin Henan da Shandong da shanxi da Hubei da Jihar Ninxia da Xinjiang da Lardin Qinghai da sauran larduna da jihohi bakwai . Wannan wasan daya ne daga cikin wasannin kwakwayo mafiya kasance da tasiri .

Wasan kwaikwayon Henan an haifar da shi a karshen Daular Ming zuwa farkon Daular Chin . A farkon lokaci an mai da hankali kan rera opera da murya kawai , shi ya sa ya sami kaunar jama'a farar hula . Saboda haka ya sami yalwatuwa da saurin gaske .

Bayan da aka haifar da wasan kwaikwayon Henan , an sami rukunoni masu bambanci guda 4. Rukuni na farko shi ne muryar Xiangfu dake birnin Kaifeng . Rukuni na biyu shi ne muryar Donglu dake birnin Shangqiu. Rukuni na uku shi ne muryar Xifu dake birnin Luoyang . Rukuni na hudu shi ne Muryar Shahe dake birnin Luohe .

Lokacin da ake yi wasan kwaikwayon Henan a kan yi amfani da wasu kayayyakin kide-kide . A cikinsu akwai sorewa da goge tamkar molo da pipa da kakakin sona da sauransu . Wasan kwaikwayon Henan yana da halin musamman sosai na wurin Henan , kuma ya bayana zaman yau da kullum na jama'a farar hula .

Kafin shekarar 1927 a cikin wasan kwaikwayon Henan babu 'yan wasa mata . Bayan da aka bullo da 'yan wasa mata , sai wasu kwararrun 'yan wasa sun yi suna a dakalin wasan . Kamar su Chang Xiangyu da Chen Suzhen da Ma Jinfeng da Yan Lipin da Cui Lantian sun kafa rukuni na kansu daban daban.

Yawan shirye-shiryen gargajiyar Henan opera ya kai fiye da dubu . Galibin shirye-shiryen sun zo daga kagaggun labaran tarihi. Wasu kuma sun bayana labarun aure da soyayya da kamilanci ko da'a . Bayan da aka kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin , an yi nune-nunen wasannin kwaikwayo na zamani da sababin

shirye-shirye wadanda suka bayana sababin labarun tarihi. Wannan ya sa aikin wasan kwaikwayon Henan ya sami sabon ci gaba .

Yau ko da ya ke wasan kwaikwayon Henan har ila yanzu ya sami kauna daga jama'a masu yawa , amma yalwatuwarsa ta kasance da wasu maganganu masu tsanani . (Ado)

>>[Labaran Wasan Kwaikwayo]

Marayan iyalin Zhao

Daga karni na 8 , kafin hijira wato B.C.zuwa karni na 5, B.C. lokacin ChunQiu na kasar Sin . A lokacin can akwai sarkuna da yawa . A cikinsu akwai wata kasar Jin . Kasar Jin tana da manyann ministoci guda biyu . Zhao Dun , wani ministan gwamnati ya nuna biyayya sosai ga daula . Tu Angu , ministan tsaron kasa ya yi sabani da Zhao Dun , da zuciya daya yana son kashe Mr. Zhao.

A cikin dogon lokacin da ya wuce , ya yi makarkashiya don lahanta Zhao Dun . Sarkin kasar Jin ya shiga cikin tarkonsa kuma yana ganin cewa Zhao Dun mugun minista ne . Sa'an nan kuma ya ba da umurni da a kashe 'yan iyalinsa da masu aikin hidima fiye da 300 . Amma ba a kashe Zhuang Ji , matar 'dan Zhao Dun ba , saboda ita ce gimbiya. An tsare ta a cikin Fadar sarki .

A lokacin , Zhuang Ji ta riga ta dauka ciki . Ba da dadewa ba sai ta haifi wani jariri a fadar sarki . An ba shi suna Marayan Iyalin Zhao . Bayan da Tu Angu ya sami labarin gimbiya ta haifi jariri , sai ya aike da 'yan gadi da su kare kofar Fadar Sarki , kuma yana son da maraya ya cika wata daya , sai a kashe shi don maganin zai rama Masa gayya nan gaba.

Cheng Ying wani aboki ne na Zhao Dun . Don ceton maraya Zhao , ya dauki akwatin magunguna kuma ya shiga cikin fadar don yi wa gimbiya jiyya . Sa'an nan kuma ya boye jariri cikin akwatin magani . Yana nufin kawo jariri daga fadar Sarki . Amma a bakin kofar fadar , Janar Han Jue mai gadin fadar ya gano jaririn . Amma Mr. Han shi ma ya nuna jin kai ga 'yan iyalin Zhao Dun.Sa'an nan kuma ya bar Cheng Ying ya tafi tare da jaririn , shi ma ya kisa kansa .

Bayan da Tu Angu ya sami labarin an yi ceton maraya , sai ya ba da umurni cewa, Idan a cikin kwanaki uku ba wanda ya gabato da marayan sai za a kashe dunannin yara wadanda ba su kai shekara daya da haihuwa ba.

Cheng Ying da Gongsun , wani aboki daban na Zhao Dun sun yi shawarwari . suna ganin cewa, muddin wani mutum ya yi kama da 'dan gudun hijira kuma tare da wani jariri, sai ya iya ceton marayan Zhao da sauran jarirai na duk kasar . Mr. Cheng daidai yana da jariri , sai ya mika shi ga Gongsun . Sa'an nan kuma ya yi kulle-kellen

makarkashiya ya tafi wurin Tu Angu kuma ya gaya masa cewa, Gongsun ya boye marayan Zhao . Ba da dadewa ba Tu Angu ya kama Gongsun da jaririn kuma ya kashe su . Bayan shekaru 15 , marayan Zhao ya yi girma , sai Cheng Ying ya gaya masa labarin gaskiya. A karshe dai marayan Zhao ya san asalinsa kwata kwata kuma ya kashe mugun mutum Tu Angu da karurukansa . (Ado)

Suo Linlang

A zamanin da , a wani wuri mai sunan Dengzhou akwai wani 'dan kasuwa mai arziki . Sunansa shi ne Xue . yana da wata diya mai sunan Xue Xiangling . 'Yan iyali suna kaunar wannan yarinya kwarai da gaske . Bayan da Xiangling ta yi girma har zuwa lokacin aure , sai iyayenta sun saye mata kayayyakin aure masu yawa . Babarta ta dinke mata wani aljihu mai suna Suolin da hannunta . Wannan aljihun yana da kyaun gani kwarai da gaske . Ana iya sa lu'u lu'ai iri daban daban a cikin aljihun . Bisa tatsuniyar da aka yi , an ce , in wata budurwar da ta yi aure ta rike da aljihun Suolin , to , za ta haifi wani jariri mai basira kuma mai kyaun gani .

A ranar aure , Xianglin tana zaune a cikin kujerar aure mai kyau . Ana bushe-bushe da kide-kide . A kan hanyar zuwa gidan mijinta , ba zato ba tsamani an yi ruwa . Sai sun je marufin Chunqiu don gudun ruwa . Da su shiga cikin marufin ba da dadewa ba , kujerar rure daban ita ma ta shiga cikin marufin . Wannan kujerar karama ce kuma tsohuwa ce . Amariyar dake zaune a kujerar tana kuka ba tare da tsayawa ba . Lokacin da Xianglin ta ji muryar kuka , sai ta yi mamaki . Sa'an nan kuma ta aike da mabiyanta zuwa wurin karamar kujerar don tambayar me ya faru. Wannan amaryar sunanta shi ne Zhao Shouzhen , iyayenta matalauta ne , kuma babbarta ta mutu tun tuni . A gidanta akwai babanta tsoho ne kawai . Saboda haka gidanta bai ba ta kyautar aure ba . Zhao Shouzhen tana tsaron za a yi mata dariya don talaucinta kuma tana damuwar babanta shi kadai a gida , ba wanda zai kula da shi ba . Shi ya sa ta yi kuka .

Da Xianglin ta ji haka , sai ta nuna jin kai gare ta . Daga yarantakarta ta yi girma a gida mai arziki . Ko yaushe ba ta san matalauciya tamkar Zhao Shouzhen . Xianglin ta yi tunanin yadda za ta ba da taimako ga Zhao Shouzhen . Nan da nan ta taras aljihun Suolin da ta ajiye a cikin kujerar , sai ta ba Zhao Shouzhen kyauta , kuma ba ta gaya mata sunanta ba . A wannan lokaci ruwa ya gyara , sai kujeru biyu sun yi ban kwana da juna su ci gaba da tafiya .

Bayan shekaru 6 , a wurin Dengzhou an yi ambaliya . Xianglin ta wargaje da mijinta da 'danta . Ita kadai ta sha wahaloli da yawa kuma ta zuwa wurin Laizhou . A nan Xianglin ta kula da wani yaro mai sunan Tianlin wanda yake da shekaru 5 da haihuwa . Yaron nan yana kaunar Xianglin sosai . Ko wace rana tana neman Xianglin da ta raka shi wasan kwallo a lebun shan iska .

Wata rana Tianlin ya jefa kwallo cikin wani gini , Sai Xianglin ta shiga cikin ginin don samun kwallo . Ba zato ba tsamani ta ga wani aljihu mai kyaun gani da ake rataye a tsakiya . Wannan aljihun shi ne daidai a lokacin aurenta ta ba Zhao Shouzhen kyauta . Lokacin da Xianglin ta ga aljihun Suolin , sai ta tuna da mijinta da 'danta kuma ta yi kuka . Tianlin da sauri ya gaya wa babarsa wannan hali. Babar Tianli ita ce Zhao Shouzhen . Ta auri Mr. Lu . Saboda ta sami aljihun Suolin , shi ya sa gidanta ya yi arziki sannu a hankali . Ko yaushe Zhao Shouzhen take tuna da mutumiya mai ba da taimako gare ta , shi ya sa ta gina wani gini a lambun shan iska , kuma ta rataye aljihun a tsakayar ginin don yin nuni da cewar har abada ba za ta manta ba . Da ta ji maganar Tianlin cewa , Xiangli ta yi kuka , sai ta tambayi yaushe ne ta yi aure da kuma me ya faru a wancan ranar aure . Xianglin ta fadi gaskiya duka . Ta haka Zhao Shouzhen ta san wadda ta taimake ta , kuma ta yi farin ciki kwarai da gaske . Sa'an nan kuma ta ba da taimako ga Xianglin a wajen neman miji da 'danta . Ba da dadewa ba Mijin Xianglin da 'dansa su ma sun isa Laizhou . Da suka ji labarin Xianglin tana gidan Mr. Lu , sai su je gidan Lu . 'Yan iyali duka sun taru a karshe . Kuma Xianglin da Zhao Shouzhen sun zama aminai mafi kyau . ( Ado )

Yang Silang ya koma gida don yin gaisuwa da uwarsa

Daga karni na 10 zuwa karni na 12 , a arewa maso gabashin kasar Sin akwai wata Daular karamar kabila mai sunan Liao wadda ta yi kunnen doki da Daular Song dake tsakaiyar kasar Sin . Karo mai yawa daular Liao ta kai hari ga Daular Song . Daulolin Biyu su kan yi yaki shekara shekara .

A lokacin Daular Song akwai wani iyalin janar Yang . Yang Linggong , babansu da Madam She babarsu da 'ya'ya takwas sun kware a wajen yin yaki . Kuma sau tari sun kafa nasarori ga Daular .

Wata rana , daular Liao ta gayyaci Sarkin Daular Song zuwa daular Liao don yin shawarwari . Amma daular Son ba ta san bangaren gaba ko tana da gaskiya ne? Don kiyaye Sarkin 'da na farko na iyalin Yang ya yi kama da sarkin Daular , sauran 'yan uwa guda 7 sun kiyaye wansu zuwa daular Liao don yin shawarwari . Amma duk da haka 'yan kungiyarsu sun sami farmakin da sojojin daular Liao suka kai musu .'Yan uwa 3 na iyalin Yang sun mutu . Kuma sojojin Daular Liao sun kama 'dan iyalin Yang na hudu wato Yang Silang . cikinsu akwai wata kasar Jin . Kasar Jin tana da manyann ministoci guda biyu . wani ministan gwamnati ya nuna biyayya sosai ga daula . ministan tsaron kasa ya yi sabani da zuciya daya yana son kashe Mr. Yang

A cikin dogon lokacin da ya wuce , ya yi makarkashiya don lahanta Yang Silang . Sarkin kasar ya shiga cikin tarkonsa kuma yana ganin cewa mugun minista ne . Sa'an nan kuma ya ba da umurni da a kashe 'yan iyalinsa da masu aikin hidima fiye da 300 . Amma ba a kashe matar 'dan Yang ba , saboda ita ce gimbiya. An tsare ta a cikin Fadar sarki .

A lokacin , Yang ya riga ya shiga cikin . Ba da dadewa ba sai ya rungume 'dansa don gani matar Sarki . A asirice , ta buga jaririn , sai jaririn ya yi kuka da karfi . Matar Tsohon sarki Xiao ta fi son wannan 'dan tattabe kunne . wani jariri a fadar sarki . An ba shi suna Marayan Iyalin Yang . Bayan da ya sami labarin , sai gimbiya ta ce , 'danta yana son wasan Takobi , sabo da Matar tsohon sarki take son 'dan tattaba kunnenta , shi ya sa ta bai wa masa da takobin umurni . Kuma ta gaya wa gimbiya cewa , kashe gari ta mayar mata .

Yang Silang ya tare da takobin umurni ya zuwa sansanin sojojin Daular Song , kuma ya gana da kanensa Yang Liulang . Sai su biyu sun rungume juna sun yi kuka . Daga baya Yang Silang ya yi gaisuwa da babarsa Madam She . Ba da dadewa ba gari ya waye , sai Yang Silang ya yi ban kwana da babarsa don zuwa sansanin sojojin Daular Liao . Da Yang Silang ya wuce ganuwar sojojin Liao , an gano cewa , shi ne mijin gimbia , sai nan da nan sun kai Yang Silang zuwa gaban Matar tsohon Sarki. Madam Xiao ba ta iya tunanin cewa , ita kanta ta karbi mijin gimbia janar ne na daular Song , kuma gimbiya ta taimake shi zuwa daular Son don yin gaisuwa da babarsu, sai ta yi matukar fushi , kuma nan da nan tana shirin kashe shi . Gimbiya TieJing tana rungume 'dansu zuwa gaban matar thohon sarki don ta gafara mijinta. Sabo da haka Matar tsohon sarki ta yafi Yang Silang , kuma ta yarda da cewa , nan gaba Yang Silang zai sake zuwa daular Song don yin gaisuwa da babarsa . (Ado)

Husmiyar Mudan

Tun shekara aru aru , Du Bao , shugaban Gundumar Nan An yana da wata diya mai sunan Du Liniang . Tana da kyaun gani sosai kuma tana da basira . Du Bao ya sami wani malamin koyarwa. Kowace rana ya koya wa Du Liniang babban littafin wake-wake na zamanin da na kasar Sin . . Chunxiang , mabiyar Du Liniang ita ma ta raka ta don yin karatu . Amma tana son wasa ainu . A lokacin karatu ta kan yi wasa a waje .

A lokacin bazara , Chunxiang ta gaya wa Du Liniang cewa , gidanta yana da wani lambun shan iska a baya . Yanayi yana da ni'ima . Tun yarantakar Du Liniang , tana bin addinin gargajiya . Ko wace rana ban da koyon dinki sai ta yi karatu , kuma ba ta taba yin wa sa a waje ba .

Yanayin lambun shan iska yana da ni'ima kwarai da gaske . Itatuwa suna sa koriyar riga . Furani suna budewa . Yarinyar Du Li tana ganin irin wannan yanayi , sai ta yi tunanin cewa , ko wace rana take karanta litattafai kawai a gida , yadda samarantakarta kamar yanayin bazara ? Koda ya ke samarantakarta tana da kyaun , amma ba wanda yake jin dadi , ina amfanin samarantakarta ?

A cikin mafarkinta , ta sake koma lambun shan iska . Da ta shiga lambun , sai wani saurayi wanda yake dauke da litafi kuma ya yi hira da ita . Wancan saurayin yana kaunar kyaun gani da basirar Du Liniang . Du Liniang tana jin cewa , yana fahimtarta kwarai da gaske . Sai a zuciyarta taa fara kaunarsa . A cikin lambun shan iska , furani daban daban suna rawa don yin murnar soyayyar tsakanin Du Liniang da saurayin . gani shekaru fiye da dubu suna zaman rayuwa a tudun. Daya daga cikinsu farin maciji ne . Daya daban kuma bakin maciji ne . Saboda su biyu suna kaunar yanayin duniyar mutane , shi ya sa sun zama yarinyoyi biyu masu kyaun gani . Sunan yarinya ta farko shi ne . Lokacin da babar Du Liniang ta zo don ganin diyarta , sai ta warke da Du Liniang daga mafarki . Du Liniang tana son yanayin dake cikin mafarkinta , sai ta sake zuwa lambun shan iska don neman yanayin mafarkin . Amma duk da haka saurayin ba ta sake zuwa ba .

Daga baya , iyalin Du Liniang ya kaura . Bayan wasu lokaci , wani saurayi ya wuce wannan lambun shan iska , ba zato ba tsamani ya sami wani ciwo. Sai ya sami waniwurin dake kusa da lambun . Wannan saurayin sunansa shi ne Liu Mengmei . shi ne saurayin da Du Liniang ta taba gana da shi a cikin mafarkinta .

Da Liu Mengmai ya sami sauki , sai ya yi yawo a cikin lambun shan iska . Ba zato ba tsamani ya tsinci wani zanen da Du Liniang ta yi ita kanta . Yana jin cewa , wannan budurwa ita ce wadda ya taba ganinta a wani wuri .

Bayan da Du Liniang ta mutu , kurwarta tana cikin lambun shan iska . Da ta ga soyayyar Liu Mengmei kamar haka , wato yana kaunar kanta , sai kowace rana da dare ta zuwa dakin karatu na Liu Mengmei don gana da shi , sai a safe ta bar dakin . Liu Mengmei ya tambayi Duliniang cewa , yaya za su taru har abada? Du Liniang ta ce , sai ya bude kabarinta , za ta iya farfado . Da Liu Mengmei ya ji haka , sai ya yi farin ciki kwarai da gaske . Daga baya sai ya haka kabarin Du Liniang da fartanya . Da gaskiya ne Du Liniang ta farfado, kuma tana da kyaun gani kamar yadda ta yi a da . Kuma sun yi aure .

Du Liniang ta mutu don soyayya, kuma ta farfado don soyayya . Wanna labari ya burge mutane masu yawa . ( Ado )

Tarihin Farin Maciji

Tun shekara aru aru , a Tudun Emei akwai macizai biyu . Sun yi shekaru fiye da dubu suna zaman rayuwa a tudun. Daya daga cikinsu farin maciji ne . Daya daban kuma bakin maciji ne . Saboda su biyu suna kaunar yanayin duniyar mutane , shi ya sa sun zama yarinyoyi biyu masu kyaun gani . Sunan yarinya ta farko shi ne Bai Suzhen . Sunan yarinya daban shi ne Xiao Qing . Wata rana sun yi yawon shakatawa a Tafkin Xihu da ke birnin Hangzhou , shahararren wuri mai ni'ima .Yanayin Tafkin Xihu yana da ni'ima kwarai da gaske . Da su isa wurin kusa da Gadar Duanqiao , sai gari ya yi durum durum , kuma an fara yin ruwa . Su biyu sai sun zo karkashin wani itace , don gudun ruwa . A daidai wannan lokaci , wani saurayi yana zuwa kuma rike da wata laima . Sunansa shi Ne Xu Xian . Ya dawo daga kabarin ba da dadewa ba . Da ya ga yarinyoyi biyu suna tsaya a karkashin itace , sai ya yi aron laimarsa gare su , kuma ya ba da taimako gare su don kiran wani jirgin ruwa da kai su koma guda.

Bai Suzhen ta fara kaunar Xu Xian , sai ta sa Xu Xian za ta zo gidanta don daukar laima . A kashe gari Xu Xian ya zo gidan Bai Suzhen dake jan ginin a bangaren tafkin . Bai Suzhen ta gode wa XuXian saboda ya taimake ta . Da ta san iyayen Xu Xian sun mutu , kuma yanzu yana zaune a gidan kawarta , kuma yana aiki a wani kantin magani . Bai Suzhen ta roki Xu Xian , su yi aure . Ko shakka babu Xu Xian ya yi farin ciki kwarai da gaske . Sa'an nan kuma a karkashin jagorancin Xiao Qing sun yi bikin aure . Bayan da suka yi aure , sai su da kansu sun kafa wani kantin magani . Bai Suzhen ta kware a wajen jiyya . Ko wace rana tana ganin mutane masu fama da cututtuka . Mutane suna kaunarta sosai kuma suna kiranta da Madam Bai .

A birnin Zhenjiang akwai wani haikalin Jinshan . A cikin wannan haikalin akwai wani budda , sunansa shi ne Fa Hai . Da ya sami labarin cewa , Bai Suzhen wata dodon maciji ce wadda take da shekaru dubu . Yana tsamanin cewa , tabbas ne kowane dodon maciji zai lahanta mutane , sai ya fitar da dabaru ga Xu Xian , ya sa Xu Xian ya bar Bai Suzhen kuma ya zama budda .

Wata rana Fa Hai ya zo gidan Xu Xian kuma ya gaya wa Xu Xian cewa , matarsa ita ce wani dodon maciji . Xu Xian bai amince da wannan ba , sai Fa Hai ya koyar masa cewa , a ran 5 ga watan Mayu , ya sa Bai Suzhen shan giya , sai za ta fitar da masifarta ta da .

Ya zuwas ranar bikin Ran 5 ga watan Mayu , kowane iyali suna shan giya don maganin masifa . Amma maciji yana tsoron wannan giya . Bai Suzhen da Xiao Qing suna tunanin zuwa tudu don gudun bikin . Amma tana tsoron Xu Xian yana shakkarta.

Da aka ceci Xu Xian sai ya yi 'dan tsoro . Bai Su Zhen ta yi tunani da wata dabara, sai ta yi amfani da mayani mai launin fari don ya zama wani farin maciji kuma ta rataye a marufin daki , ta bar Xu Xian gani . A wannan lokaci , sai Xu Xian bai sake shakkar matarsa dodon maciji ce, kuma sun farfado da soyayya da juna . (Ado)

Hada kai bayan sun sha wahaloli

Lian Qi , matar Xu Dong , Sarkin Zhongshan ba ta haifi namiji ba . A lokacin da babu 'da sai babu soyayya daga mijinta . Don magance rashin soyayya , sai ta canza wani jariri da jaririyar da ta haifa . Kuma ta buga wani tambari a kafadar jaririyarta . Sa'an nan kuma ta ba sunan Xu Tianbao ga jaririn da ta musanya .

A bayan shekaru 18 , Chang Ming , 'dan babban jami'i ya kwace Bai Liying ,'yar wasan wake-wake kuma ya kashe babanta . Ba da dadewa ba Xu Tianbao ya ceci Liying , don maganin Chang Ming ya rama gayya , ya boye ta cikin gidan farar hula . Sannu a hankali , Tianbao da Liying sun yi soyayya kuma sun yi yarjejeniyar aure . Babar Tianbao ba ta son iyayen Liying saboda suna cikin talauci . Saboda haka ta je gidanta don yin zargi da kai bugu ga Liying . A lokacin da ta cire hannun rigar Liying , sai ta ga tambarin dake kafadarta . A daidai wannan lokaci , Sarki ya karbi Tianbao da ya ya zama mijin gambiya . Tianbao ba shi da dabara sai ya ci gaba da soyayyar Liying kuma ya yi nisa da gambiya . Gambiya ta yi matukar fushi , sai ta yi niyyar kashe Liying . Don ceton Liying , Tianbao ya kai naushi ga gambiya .

Saboda haka gambiya ta je wurin Sarki kuma ta yi kuka . Da farko dai Sarki yana tsamanin cewa diyarsa da mijinta yara ne , ba laifi su yi fama da baki ko kuma su yi bugu da juna . Shi ya sa Sarkin bai yi bincike ba . Changming kullum yana yin gyama da Tianbao , sai ya gaya wa Sarkin cewa , saboda Tianbao yana da Liying sai ya kai bugu ga gambiya . Sarkin ya yi matukar fushi sai ya yi shirin kashe Liying . Babar Tianbao tana kaunar diyarta , sai ta gaya wa Sarkin cewa , Liying diyar Sarkin Zhongshan ta gaskiya . Ba wanda ya yi tsamanin Sarkin ya yi fushi kwarai da gaske , sai ya kore 'yan iyalin Xu Dong , kuma ya tsai da kudurin yanke hukuncin kisan kai ga Tianbao . Jami'I mai kula da aikin kisa kan Tianbao shi ne Chang Ming .

A tsakar rana , lokacin da jami'in yake kashe Tianbao da wuka , sai gambiya ta isa filin kisan kai kuma ta sanar da umurnin Sarkin cewa , ya yi wa Tianbao afuwa kuma ya ci gaba da zaman mijin gambiya . ( Ado )

Soyayya da hasuma na Janar

Jiu Baolian ya iya maganin cututuka 100 . Shi ne abu mai daraja na Zhou Hongde , likitan Sarki da ya riga ya ritaya . Wata rana an yi ambaliya mai tsanani Mr. Zhou ya ceci Liao Zhongping wanda yake fama da ciwo , kuma ya sa shi ya zama 'dansa . A daidai wannan lokaci , matar tsohon sarki ba ta da lafiya . Saboda magani ba shi da mafani , Mr. Zhou ya mai da 'dansa Zhaonian da 'dansa ba na gaskiya ba Zhongping su tafi hedkwatar kasar don ba wa matar tsohon sarki magani mai kyau . Amma duk da haka a kan hanyar Zhongping ya manta da alherin da babansa ya kawo masa kuma ya tura Zhaonian, 'dan Mr. Zhou na gaskiya daga tudu , kuma ya kwace magani mai kyau . Sa'an nan kuma ya zuwa hedkwatar kuma ya warke da matar tsohon sarki . Ba da dadewa ba Sarki ya nada shi ya zama jami'I mai kula da iyalai dubu 10 . Lokacin da ya koma gida , ya yi kariya cewa , Zhaonian ya fadi cikin ruwa kuma ya mutu . Don rufe bakin 'yan iyalin Mr. Zhao , ya kone gidan iyalin Zhou , kuma ya tilasta Wanqing , diyar Zhou ta zama matarsa . Amma Wanqing ta tsalle cikin kogi ta mutu don kiyaye kirkinta .

Manya da kanana , 'yan iyalin Zhou sun kubuta daga gobara . Zhou Hongde kuma yana damuwa cikin dogon lokaci har ya sami ciwo mai tsanani kuma ya ci basusuka masu yawa . Matar 'dansa Shuxian ba ta da dabara sai ta sake auri Xiong Yemeng , Janar wanda ya jibge a iyakar kasar . Da suka yi aure ba da dadewa ba , makiya sun kawo hari a iyakar kasa . Sarki ya ba Yemeng umurni zuwa iyakar kasar don yaki da makiyan . Yemeng ya mika 'dansa Xiong Heen wa matarsa Shuxian don raya shi .

A bayan shekaru 8 , Shuxian ta raya 'danta Zhou Xiaoping da 'dan mijinta Xiong Heen har su girma . A cikin jarrabawar duk kasar , su biyu sun ci nasara kuma sun zama jami'ai . A daidai wannan lokaci , Wanqing wadda aka cece ta daga ruwa ta kai kara a hedkwatar . Ba zato ba tsamani Zhou Xiaoping ya gana da innarsa Wanqing . A karshe dai su hada kansu sun kashe Zhongping kuma 'yan iyalin Zhou sun yi murna da sake haduwa . ( Ado )

Matar Sarki ta sha giya ta bugu

Wasan Matar sarki ta sha giya ta bugu yana da suna daban . Shi ne Rumfar furanni 100.

Sarkin Daular Tang Xuanzong ya yi yarjejeniya da matarsa Yang Guifei kuma ya ba ta umurni don shirya liyafa a Rumfar furanni 100 , Kuma ya yi alkawari zai zuwa Rumfar don duba furani da sha giya. Ya zuwa ranar kashegari , Yang Guifei ta zuwa rumfar tukuna , kuma ta shirya walima don jiran Sarki . Amma duk da haka ta yi dadewa tana jira , kujerar Sarkin Tang Xuanzong bai zo ba . Har lokaci da yawa ya wuce , an ba ta labari cewa , Sarki ya riga ya je fadar matarsa daban . Da Yang Guifei ta sami wannan labari , sai ta yi matukar fushi harzuwa mutuwarta . ta riga ta dauka ciki . Ba da dadewa ba sai ta haifi wani jariri a fadar sarki . An ba shi suna 'yar iska . Bayan ta yi wasa da Gao Lishi da Pei Lishi ta hanyoyi daban daban har ta gai ainu ta goma fadar Sarki . Ba dadewa ba ta mutu. ( Ado )