logo

HAUSA

Babi13: Likitancin Gargajiya

0001-01-01 08:00:00 CRI

[Likitancin gargajiya]

Likitancin gargajiya

Likitancin gargajiya na kasar Sin wani tsarin likitanci ne mai tsarin sanin ka na musamman da al'ummar kasar Sin ta tsara bayan da suka aikata cikin dogon lokaci kuma ta yi ta takaita fasahohi.

Likitancin gargajiya na kasar Sin yana hade da likitancin kabilar Han da na kabilar Mongolia da na Uygur. A cikin likitancin gargajiya, da ya ke kabilar Han ta fi yawan mutane, kuma tana da rubutu tun can fil azal kuma tana da dadadden tarihi, shi ya sa likitancin kabilar Han ya fi ba da tasiri a kasar Sin har ma a duniya. Bayan da aka shigo da likitancin Turawa, an fara kira likitancin kabilar Han likitancin kasar Sin don banbanta shi da na likitancin Turawa.

[likitancin kasar Sin]

Tarihin likitancin kasar Sin

A cikin likitancin gargajiyar kasar Sin, likitancin kabilar Han yana da dadadden tarihi, kuma yana da tsarin sanin ka da fasahohi da yawa.

Mafarin likitancin kasar Sin yana wuraren da rawayan kogin ke ratsawa, an kafa tsarin likitanci tun can fil azal. A yayin da a ke yalwata likitancin kasar Sin cikin dogon lokaci an yi ta yin kagowa a fannoni daban daban, shahararrun likitoci da yawa sun bullo, kuma an wallafa shahararrun littatafai da yawa.

A cikin rubutun da aka yi kan bayan kunkuru da kasusuwa kafin shekaru dubu 3 da suka shige, an riga an rubuta likitanci da ciwace ciwace fiye da 10. Tun a sarautar Zhou an fara bin hanyar duba lafiya ta likitancin kasar Sin wato dubawa da sinsina da tambaya da tabawa da dabarun jiyya na ba da maganin sha da akyufanchu da fida. A sarautar Qin da Han an wallafa littafi mai suna Huangdineijin wanda ya ke cikakken tsarin sanin ka na likitancin kasar Sin. Wannan shi ne littafi na farko da aka wallafa game da tsarin sanin ka na likitancin kasar Sin. A sarautar Han likitancin fi da ya kai wani sabon matsayi. Bisa abin da aka arubuta a cikin littafi mai suna Tarihin kasashe 3, an ce, shahararren likita mai suna Hua Tuo ya fara yin amfani da maganin kashe zafi don yin fi da iri iri.

Daga sarautar Wei da Jin wato daga shekara ta 220 zuwa shekara ta 589 har zuwa sarautar Sui da Tang wato daga shekara ta 581 zuwa shekara ta 960 an samu babbar nasara a wajen duba lafiyar jiki ta hanyar taba jijiyar hannu. A cikin shahararren littafi mai suna Ilmin jijiya da shahararren likita Wang Shuhe na sarautar Jin ya wallafa ya takaiata shaidoji 24 na jijiya. Wannan littafi ya yi babban tasiri ga likitancin kasar Sin, kuma ya yadu har zuwa kasashen waje..

A sarautar Song wato daga shekara ta 960 zuwa shekara ta 1279, a yayin da a ke ba da ilmin likitanci an yi manyan gyare gyare ga likitancin sa alluira maras ruwa. Wang Weiyi ya wallafa littafi game da inda a ke sa allura, daga bisani ya tsara fasali kuma ya gina mutum mutumin tagula guda biyu don shaida inda za a sa allura maras ruwa ga dalibai. Wannan aikin da ya yi ya yi babban tasiri ga likitancin sa allura maras ruwa na nan gaba.

A sarautar Ming wato daga shekara ta 1368 zuwa shekara ta 1644, tarin likitoci sun rarraba ciwace ciwace iri iri.

Daga sarautar Ming an fara shigo da likitancin kasashen yammacin duniya zuwa kasar Sin, a wancan lokaci tarin likitoci suna da nufin harhada likitancin kasar Sin da na kasashen yammacin duniya, wato ke nan sun zama madugun aikin harhada likitancin kasar Sin da na kasashen yammacin duniya na zamanin nan. (Dogonyaro)

Tsarin sanin ka na tushe na likitancin kasar Sin

Tsarin sanin ka na tushe na likitancin kasar Sin shi ne tsarin sanin ka na dokokin canjawar aikace aikacen rai na jikin mutum da ciwace ciwace. Yana hade da sauye sauyen lafiyar jiki da sanadin ciwace ciwace da hanyar duba lafiya da maganin ciwace ciwace da kara lafiyar jiki.

Yin da Yang da ma wani ra'ayi ne na fulosufiya. Bayan da aka bincike sabani, sai a mai da gefuna biyu na sabani su zama Yin da Yang. Kuma a yi amfani da karuwa da bacewar Yin da Yang don bayyana sauye sauyen abubuwa na duk duniya. A cikin likitancin kasar Sin ma an yi amfani da Yin da Yang don bayyana cudanyar da ke tsakanin jikin mutum da halitta, wato idan Yin da Yang ba su yi balas ba za a yi rashin lafiya.

Tsarin sanin ka na tafiyar iska shi ne tsarin sanin ka na bincike tasirin da yanayi ke yi wa lafiyar jiki. Wato a cikin yanayi daban daban na ko wace shekara akwai iska da sanyi da zafi da damshi da bushewa da wuta. Bisa wannan tsarin sanin ka duk sauye sauyen yanayi suna da tasiri da lafiyar jiki da faruwar ciwace ciwace a lokaci daban daban. (Dogonyaro)

Hanyar duba lafiya ta likitancin kasar Sin

Likita ya yi amfani da hanyar dubawa da saurara da sinsina da tabawa da yin hira da marasa lafiya don gane dalilin da ya sa su yi rashin lafiya, sa'an nan ya yi musu jiyya. Hanyar duba lafiya ta likitancin kasar Sin tana hade dubawa da saurara da tambaya da tabawa. Likita ya kan yi amfani da hanyoyin nan 4 gaba daya don tabbatar da ciwon masas lafiya.

Dubawa

Bisa likitancin kasar Sin mutum ba ya da lafiya, to, za a ga alama daga fuska da jikin mutumin nan, sabo da haka in mutum ya je wajen likita, da farko likita zai duba fuskar mutunin nan da launin jiki, sa'an nan zai gane inda ba ya da lafiya.

Sinsina

Likitan kasar Sin kuma ya kan saurara abin da ya ji da sinsina abin da ya ji daga wajen marasa lafiya, daga nan ne zai gane inda ba ya da lafiya.

Likita ya kan saurara murya da numfashi da kaki na maras lafiya don gane inda ba ya da lafiya.

Likita kuma ya kan sinsina warin jikin maras lafiya, daga nan ne ya gane inda ba ya da lafiya.

Tambaya

Likita ya kan tambayi maras lafiya yadda ciwo ya same shi da yaya ya ke ji yanzu don tabbatar da ciwon da ya same shi. Wani sa'I likita ya kan yi tambaya kan muhalli aikin sa da zamansa da cimakarsa da harkokinsa na yau da kullum don gane sanadin ciwonsa.

Tabawa

Likitocin kasar Sin su kan taba jijiyar da ke cikin hannun mutum don gane rashin lafiyar mutumin nan. Bugawar jijiya ta masu lafiya da maras lafiya ba daya ba ne, sabo da haka daga bugawar jijiya ce likitoci za su gane inda ba ya da lafiya. (Dogonyaro)

[Magungunan gargajiya na kasar Sin]

Magungunan gargajiya na kasar Sin

Magungunan gargajiya na kasar Sin magunguna ne a likitocin kasar Sin ke amfani da su don magani da warkar da ciwace ciwace. Magungunan kasar Sin musamman su ne halitattun abubuwa da kayyakinsu, ciki har da ciyayi da itatuwa da ma'adinai da wasu kayayyakin sarrafe sarrafe. Kasar Sin tana da tarihi mai shekaru dubbai na yin amfani da magungunan gargajiya, amma an fara yin amfani da kalmar magugunan gargajiya na kasar Sin ne bayan da aka shigo da magungunan sha na kasashen yammacin duniya don banbanta irin wadannan magungunan sha biyu.

Takaitaccen tarihin maganin kasar Sin

A cikin tarihin kasar Sin akwai wani tatsuniya cewa, Shen Nong ya dandana ciyayi iri dari, ya sha dafi har sau 70 a kwana daya. Wannan tatsuniya ya shaida yadda jama'ar kasar Sin suka gane magunguna a yayin da su ke fama da ciwace ciwace.

Tun a zamanin sarautar Xia da San da Zhou wato daga karni na 22 zuwa shekara ta 256 kafin haifuwar Annabi Isa, mutanen kasar Sin sun fara hada giyar magani da ruwan magani. Littafi mai suna Shijin shi ne littafi na farko da aka rubuta magungunan sha. A cikin shahararren littafi mai suna Neijing an gabatar da cewa, sai masu shan sanyi su sha maganin zafi, masu shan zafi kuma su sha maganin sanyi. Wannan ya zama tushen tsarin sanin ka na likitancin kasar Sin.

A cikin wannan littafi an rubuta magunguna 365, kuma an yi zane zanen magunguna don kyautata fasalin likitancin kasar Sin.

A sarautar Ming wato daga shekara ta 1368 zuwa shekara ta 1644, Li Shizhen, masanin ilmin magungunan sha ya yi shekaru 27 ya wallafa babban littafi mai suna Tsarin magungunan sha, a cikin littafin nan an rubuta magunguna iri dubu daya da dari 8 da 92, har ya zama littafin da ya fi girma a kan tarihin magungunan kasar Sin.

Bayan da aka kafa Jumhuriyar mutanen kasar Sin a shekara ta 1949, an yi bincike bincike sosai a wajen ilmin shuke shuke da dubawa da sarrafe sarrafe da amfanin magungunan sha don tabbatar da gaskiyar magunguna iri daban daban. A shekara ta 1977 an buga Babban kamus na magungunan sha na kasar Sin, a cikin wannan littafi an rubuta magungunan sha har iri dubu 5 da 767. A sa'I daya kuma an buga littatafai iri iri na magungunan sha na kasar Sin, kuma an kafa ofisoshi da yawa na bincike da hada magungunan sha a kasar Sin.

Albarkatan magungunan kasar Sin

Kasar Sin tana da fadi kwarai, surar kasa ma iri iri ne, yanayi ma daban daban ne, sabo da haka ana iya samun ciyayi da itatuwa iri daban daban don su zama magungunan sha. A halin yanzu kasar Sin ta yi amfani da magunguna iri dubu 8, magungunan da a kan yi amfani da su sun kai guda 600. wato ya kai matsayin koli na duniya, kuma ana fitar da magungunan kasar Sin zuwa kasashe da jihohi 80, sun yi kwarjini a kasashen duniya.

Amfanin magungunan kasar Sin

Kasar Sin tana da dadadden tarihi a wajen yin amfani da magungunan kasar Sin, sun yi amfani kwarai da gaske a wajen kara lafiyar al'ummar kasar Sin. Tsarin sanin ka da aikatawa na magungunan kasar Sin sun shaida haliyar musamman na al'adun kasar Sin. Yawancin magungunan kasar Sin an samu ne daga halitattun abubuwa. Sabo da hak ba dafi da yawa.

An hada magungunan kasar Sin ne duk bisa tsarin sanin ka na likitancin kasar Sin, kuma bisa amfanin da za su yi a jikin mutum.

Yalwatuwar magungunan kasar Sin

Manufar bincike magungunan kasar Sin a nan gaba ita ce a gaji hanyoyin gargajiya na hada magungunan sha na kasar Sin, kuma a zaba da kyautata irin shuke shuken da za a yi magani da su, musamman za a yi bincike kan irin magungunan da a ke butakarsu da yawa, ban da haka kuma za a karfafa aikin bincike sabbin albarkatan magungunan kasar Sin. (Dogonyaro)

[Acupuncture]

Acupuncture

Acupuncture wata hanyar jiyya ce ta likitancin kasar Sin, wato likita ya sa wani rin allura ba tare da magani ba. Da farko acupuncture wata dabara ce ta jiyya, daga bisani ya zama wani muhimmin kashi na likitancin kasar Sin.

Acupuncture yana da dadadden tarihi. Tun can zamanin da an taba yin amfani da allurar dutse. An yi amfani da irin wannan allurar dutse ne a sabon zamanin dutse wato shekara ta dubu 8 zuwa dubu 4 kafin haifuwar Annabi Isa. Masanan ilmin tarihin kasar Sin sun taba iske irin allurar dutse. Ya zuwa zamanin Chunqiu wato shekara ta 770 zuwa shekara ta 476 kafin haifuwar Annabi Isa, likitoci na musamman sun bullo.

A zamanin Zhanguo da sarautar Han, an samu ci gaba a wajen narke karfe, sabo da haka an fara yin amfani da allurar tagula a maimakon allurar dutse, sabo da haka an fara habaka wuraren da aka yi amfani da da allura, kuma an kara samu ci gaba da sauri a wajen yin amfani da allura. A zamanin kasashe uku, an samu likitocin musamman na acupuncture. Littafi mai suna Fasahohin acupuncture da Huang Fumie ya wallafa ya zama littafi mai cikekken tsari na likitancin acupuncture. A zamanin Jin wato daga shekara ta 256 zuwa shekara ta 589, an yi wallafe wallafen littatafan acupuncture da yawa. Fasahar acupuncture kuma ta yadu zuwa Korrea da Japan.

A sarautar Sui da Tang, acupuncture ya zama wata sana'ar musamman. Daga bisani an yi ta samun ci gaba a wajen ilmin acupuncture. A karni na 16, an gabatar da acupuncture zuwa Turai. Amma a sarautar Qing an fi sa muhimmanci a wajen ba da maganin sha, sabo da haka an hana ci gaban ilmin acupuncture.

Tun bayan da aka kafa Jumhuriyar mutanen kasar Sin a shekara ta 1949, an samu babban ci gaba a wajen acupuncture. Yanzu an kafa sassan acupuncture a asibitoci dubu biyu na likitancin kasar Sin, an yi bincike da nazari sosai kan ilmin acupuncture don gane amfaninsa a wajendaidaitawa da kashe zafi da kara karfin garkuwar jikin mutum, kuma an samu ci gaba da yawa a wajen gwaje gwajen kimiya. (Dogonyaro)

[Matsa]

Matsa

Matsa wata irin muhimmiyar dabara ce a cikin likitancin kasar Sin, wato a danna a kan wani wuri na jiki don warkar da ciwo ko kara lafiyar jiki.

An yi matsa ne duk bisa tsarin sanin ka na likitancin kasar Sin, wato an yi matsa ne ba tare da yin amfani da maganin sha ba, amma tana da amfani kwarai a wajen warkar da ciwace ciwace, sabo da haka ita ce wata saurakkiyar hanya a wajen warkar da ciwo. Ana yin amfani da dabarar nan a wurare da yawa musamman a wajen warkar da ciwon kashi da amosani da raunin da aka samu.

Idan ana son yin matsa dole ne a bi wasu fasahohin musamman, wato sai a danna da karfin daidai cikin dogon lokaci. Kuma ba da hannu kawai a ke matsa ba, kuma ana iya yin amfani da kafa, har ma da wasu kayayyaki. Wani sa'I kuma a kan yi amfani da magani don shafa wurin da za a matsa, har ma a kan shafa mai iri iri a wurin da za a yi matsa.

Matsa kuma ta kasu iri biyu wato na yi wa saura da yi matsa shi kansa. A kan yi matsa don gyara kashi, mutum kuma ya iya yi wa kansa matsa don kara lafiyar jiki misali a yi matsa a ido da hannaye da kafafuwa da ciki da kwantar da hankalin mutane. (Dogonyaro)

[Likitancin kabilu ]

Likitancin kabilu

Likitancin gargajiya na kasar Sin ba likitancin kabilar Han kawai ba, kuma yana hade da likitancin kananan kabilun kasar Sin. A yayin da kananan kabilu ke samun ci gaba sun samu likitancin kananan kabilu sabo da wurare daban daban da su ke zama da al'adu, musamman su ne likitanci na kabilar Zang, da na Mongolia da na Uygur da na Korea da na Zhuang da na Dai da na Yi da na Miao da na Lagu da na Elunchun.

Tarihi da al'adu na kananan kabilu daban daban ne, shi ya sa likitanci na kabilu ma daban daban ne, wasu kananan kabilu suna da hanyoyi iri iri na jiyya, kuma suna da tsarin sanin ka na musamman na magungunan sha, wasu kabilu kuma suna da littatafansu na likitanci wadanda suka bazu a cikin jama'a, yanzu ana shirya su, wasu kabilu kuma ba su da rubutu, suna koya wa jikokinsu ne daga baki kawai.

Wasu kananan kabilu sun yi koyi da likitancin kabilar Han, kuma sun tsamo likitanci na sauran kasdashe. Misali likitancin kabilar Zang ya tsamo likitancin kabilar Han kuma ya tsamo likitancin tsohuwar India. Likitancin kabilar Mongolia ya tsamo likitancin Han, kuma ya tsamo likitancin Rasha. (Dogonyaro)

Ilmin likitancin Tibet

Ilmin likitancin Tibet wani kashi ne na ilmin cuce-cuce na gargajiyar kasar Sin. An gano shi ne daga ayyukan ba da magani da 'yan kananan kabilu wadanda 'yan kabilar Tibet ke ginshikinsu suka dade suna yi. Ana amfani da shi musamman a wuraren da 'yan kabilar Tibet da yawa ke zaune kamar jihar Tibet da lardin Qinghai da lardin Sichuan da LARDIN Gansu da sauran wurare na kasar Sin, haka nan kuma ana amfani da ilmin likitancin Tibet sosai a kasar Indiya da ta Nepel da sauran kasashe da ke kudancin nahiyar Asiya.

Ilmin likitancin Tibet an same shi ne a tudun Qinghai-Tibet, kuma ya dace da halin musamman da ake ciki a wadannan wurare dangane da kabilu da zaman rayuwar jama'a da kuma halitta. Tudun Qinghai-Tibet wurare ne masu sanyi kwarai, kuma da wuyar zuwa, sabili da haka ilmin likitancin Tibet ya dade yana nan ba tare da sauye-sauye ba. Alal misali, ire-iren dabbobi da tsire-tsire da ake iya samu kalilan ne a tudun Qinghai-Tibet, don haka a kan hada magungunan Tibet da dabbobi da tsire-tsire masu jurewa sanyi wadanda suka girma ba tare da shan iska mai kyau sosai ba.

Babban hasashen ilmin likitancin Tibet

An kafa tsarin hasashen ilmin likitancin Tibet ne a hankali a hankali bisa sana'o'i da zaman rayuwa da aikin ba da magani da aka yi a cikin dogon lokaci.

A cikin hasashen ilmin likitancin Tibet, an bayyana cewa, abubuwa da ke cikin jikin mutum sun hada da jini da kitse da nama da kashi da ruhu da fitsari da kashi da kuma gumi. Idan wani mutum yana cikin koshin lafiya, to, wadannan abubuwa na doraga da juna, na cudanya da juna, na taimakon juna cikin daidaituwa. Amma idan wani daga cikin abubuwan nan ya yi karfi ko ya ragu , to, ciwo zai kamu mutum, saboda haka wajibi ne, a sami daidaituwa a tsakanin wadannan abubuwa ta yadda za a warkar da mutumin nan daga ciwon.

Masu ilmin likitancin Tibet suna ganin cewa, dalilin da ya sa ake kamuwa da cuta, shi ne domin an sami rashin daidaituwa a tsakanin abubuwan nan. Saboda haka an warkar da mai kamu da cuta ta hanyar mayar da daidaituwa a tsakaninsu.

Dissect and Physiology (aikin jiki)

Da ganin yadda tsabi'un kabilu, a cikin hasashen ilmin likitancin Tibet, an bayyana abubuwa filla-filla a kan ilmin abubuwa da ke cikin jikin mutum da ilmin Physiology. Game da halittu na cikin jiki, ilmin likitancin Tibet shi ma yana ganin cewa, halittu na cikin jiki sun hada da zuciya da hanta da saifa da huhu da koda da tumbi da babban hanji da karamin hanji da mafitsara da matsarmama da sauransu. Tsohon ilmin likitancin Tibet ya gwada halittu na cikin jiki kamar abubuwa iri daban daban, alal misali zuciya ta tashi da sarki da ke zaune a kan kujera mai daraja, tana cibiyar kirjin jiki, fufu ya yi kama da minista da dan sarki, suna kewaye da sarki, hanta da saifa su ne kamar uwargidan sarki da kananan matansa da ke a gindinsa, amma suna dangantar juna sosai, koda kuma ya yi kama da ginshikin gida, idan an rasa shi, to, jiki ba zai zama kamar wani babban gida ba.

Daga wadannan, za a gano cewa, tsohon likitancin ilmin Tibet ya riga ya bayyana ra'ayin gaskiya a kan jikin mutum.

Abubuwan musamman na ilmin likitancin Tibet

Hanzarta amai

Hanzarta amai wata hanya ce da ake yi wajen yin amfani da magani don a yi amai. A kan iya bin hanyar nan wajen warkar da masu ciwon tumbi da cin abu mai dafi da samun tsutsosi cikin jiki da tari da dai sauransu. Amma kada a bi hanyar nan wajen warkar da tsofaffi da mata masu juna biyu da jarirai da majiyyata wadanda suka kamu da cututtuka, ko suka ci abinci mai dafi ma , ba za a bi irin wannan hanyar ba da magani ba.

Yin wanka da ruwan magunguna

Hanyar da ake bi wajen yin wanka da ruwan magunguna wata hanyar halitta ce. Magunguna da a kan yi amfani da su sun hada ruwa mai dumi iri-iri da aka samu daga idon ruwa.

Hanyar wanka da magunguna ta kasu gida biyu wato yin wanka da ruwan magunguna da manna kunshin magunguna a kan jiki. Masu cuta da ake warkar da su ta hanyar yin wanka da ruwan magunguna su ne wadanda zafi da ke cikin jikinsu ya yi yawa. Wata hanyar warkar da masu cuta daban ita ce a manna kunshin magunguna da aka dafa cikin ruwa a kan sassan jiki da aka sami ciwo. (Halilu)

Ilmin likitancin Mongoliya

Muhimman abubuwa dangane da likitancin Mongoliya

Ilmin likitancin Mongoliya ilmin likitancin gargajiya ne da 'yan kabilar Mongoliya suka samu a hankali a hankali, bayan da suka dade suna ba da maganunguna. Yana da dogon tarihi, kuma ya yi armashi kwarai. Ilmin likitancin Mongoliya sakamako mai kyau ne da 'yan kabilar Mongoliya suka samu dga wajen fama da cututtuka, haka nan kuma shi ilmin likitanci ne da ya dace da 'yan kabilar nan da wurare da suke zama. Ana iya yin amfani da ilmin likitancin Mongoliya wajen warkar da masu cututtuka da sauri da magunguna kadan kuma ba tare da biyan kudi mai yawa ba.

Babban hasashen likitancin Mongoliya

Bisa ilmin likitancin Mongoliya, an bayyana abubuwa da ke faruwa dangane da Pathology da Physiology ta hanyoyi uku su "Heyi" da "Xila" da kuma "Badagen". Abin da ake nufi da "Heyi" shi ne aikin kula da tunani da harshe da aikace-aikace da halittun cikin jiki. Idan aikin nan bai tafiya yadda ya kamata ba, to, za a kamu da cutar tabin hankali da wuyar shiga barci da mantuwa da sauri da kuma makamantansu. Abin da ake nufi da "Xila" shi ne zafi mai yawa da ke cikin jiki (suffer from excessive internal heat). Idan irin wannan zafi ya yi yawan gaske, to, za a ji daci a harshe, a ji tsami a baka, kuma hankali ya tashi da sauran alamomi. Haka zalika abin da ake nufi da "Badagen" shi ne, wani irin ruwa mai kauri da ke cikin jiki, yana sanyayya jiki. Idan ruwan nan ba ya tafiya daidai ba, to, za a ji sanji, kuma yawan kashi ko fitsari ko kuma gumi da ake yi zai karu.

Halayen musamman na likitancin Mongoliya

Warkar da masu cututtuka ta hanyar zubar da jini

A yi amfani da allura wajen huda wani sashen kashin jikin mutum don zubar da jini mai kwayoyin cuta ta yadda za a warkar da masu cututtuka. Ana amfani da wannan ne wajen warkar da masu cutar Tibi, da furuncle da sore da med or gout.

Warkar da masu cututtuka ta hanyar yin amfani da tulu (jar or pot or tin) mai zafi.

A kan bi hanyar nan da ta zubar da jini tare. Da farko a manna tulu mai zafi a kan fatun sashen jikin mutum da aka yi ciwo a kai, bayan haka a yi amfani a allura wajen yin hoda a wannan sashen jiki ta yadda za a zubar da jini mai kwayoyin cuta ko rawayen ruwa, ta haka za a warkar da masu cututtuka da sauri kuma ba tare da jin zoki ko zafi ba.

Warkar da masu cututtuka ta hanyar shan madara mai tsami ta godiya

Hanyar nan hanyar gargajiya ce da 'yan kabilar Mongoliya ke bi wajen warkar da masu cututtuka. Ana bin wannan hanya don kara gina lafiyar jiki da warkar daga cututtuka musaman suma bayan jin rauni, da jan numfashi da kyar da jin zafi a kewayen zuciya da sauransu. Daga binciken da aka yi, an gano cewa, madarar godiya tana hada da sukari da furotin da kitse da Vitamin da ma'adinai da sauran abubuwa da yawa wadanda ake butaka don gina lafiyar jiki.

Hanyar yin dori ga ilmin likitancin Mongoliya

Hanyar yin dori ta Mongoliya hanya ce da kwararru na zuriyoyi a fannin ilmin dori suka samu don warkar da ciwon karayar kashi da gabobi da raunuka da aka ji a wasu sassan jiki masu taushi. Hanyar nan tana hada da

daidaita kashi ko gabobi da suka karya, da tausawa da yin wanka da ruwan magunguna da yin motsa jiki da sauransu. (Halilu)

Ilmin likitancin kabilar Uygur

Wasu muhimman abubuwa na ilmin likitancin kabilar Uygur

A zamanin da, wuraren da ke Xinjinag ya kasance a yankin da ke yammacin Yumenguan wato tsakiyar Asiya. A lokacin zamanin daular Han ta yamma wato tsakanin shekarar 206 kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S.(B.C.) zuwa shekarar 25, "Hanyar Siliki" ta kawo saukin zirga-zirga a tsakiyar Asiya, ta ba da taimako wajen bunkasa harkokin kasuwanci da ma'amalar al'adu, kuma likitocin kasashen yamma da na gabas sun taru a Xinjiang da ke a tsakiyar Asiya, sun sa kaimi sosai ga yalwata sha'anin aikin likita na kabilu da ke zaune a yankunan Xinjiang. Sabo da haka an kafa tsarin ilmin likitancin gargajiya wanda ke da salon musamman na kabilar Uygur ne bayan da aka zurfafa ilmin likitancin kabilar Uygur da koyon kyakkyawan al'adun ilmin likitanci da na hada magunguna na wurare da kabilu daban daban na yamma da gabas.

Maganganun gargajiyar kabilar Uygor

Daga binciken da aka yi, an gano cewa, yawan ire-iren magunguna da ake samu a duk jihar Xinjiang ta kabilar Uygor mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin ya wuce 600, daga cikinsu akwai yawan ire-iren magungunan yau da kullum ya kai kimanin 300, a kan hada magungunan nan ire-ire misalin 160 a jihar nan, wato ke nan ya dauki kashi 27 cikin dari bisa na duk yawan magunguna.

A kan yi amfani da danyun abubuwa masu kamshi wajen hada magunguna irin na kabilar Uygor. Danyun abubuwan nan sun hada da Juda da Lilac da sauransu. Haka nan kuma abubuwa masu guba kwarai wadanda a kan yi amfani da su wajen hada magunguna sun hada da Vomiting Nut da "Datura" da sauransu. (Halilu)

Ilmin likitancin kabilar Korea

Wasu muhimman abubuwa na ilmin likitancin kabilar Korea

An kafa tsarin ilmin likitancin gargajiya na kabilar Korea ne ta hanyar koyon hasashen ilmin likitancin gargajiya na kabilar Han, kuma bisa tushen al'adun kabilar Korea da sakamako da 'yan kabilar Korea suka samu wajen rigakafin cututtuka da warkar da su. Tun can shekaru aru-aru, ya kasance da ma'amalar aminci da ake yi tsakanin 'yan kabilar Korea da ta Han, kuma sun yi musaye-musaye sosai a tsakaninsu a fannin al'adu da ke hada da ilmin likitanci. Yayin da suka yi koyi da ilmin likitanci na kabilar Han, likitoci 'yan kabilar Korea sun hada al'adun gargajiyar kabilarsu da ayyukan ba da magani gu daya. A cikin wani littafi mai suna "Dong Yi Shou Shi Bao Yuan " da marigayi Li Jima ya wallafa a karni na 19, an gabatar da hasashen ilmin likitanci na kabilar Korea, kuma daga nan ne aka kafa tsarin ilmin likitancin kabilar nan a hankali a hankali.

Asalin magungunan sha na kabilar Korea

Magungunan sha da 'yan kabilar Korea ke yin amfani da su sun kasu cikin gidaje iri biyu. Na farko shi ne magunguna na kabilar Han, na biyu kuwa shi ne magangunan manoma.

Da ya ke likitoci 'yan kabilar Korea suka yi koyi da ilmin likitancin kabilar Han a fannoni da yawa, likitocin nan sun mayar da magungunan Han bisa matsayin makamai da ake yin amfani da su wajen shawo kan cututtuka. Alal misali yawan ire-iren magunguna da likitoci 'yan kabilar Korea ke yin amfani da su dukansu magungunan kabilar Han ne. Haka zalika ire-iren magunguna 1297 da aka rubuta a cikin littafi mai suna "magungunan asiri na Dong Yi", da ire-iren magunguna sama da 1500 da aka rubuta a cikin littafin mai suna "jagorancin ilmin likitancin Han" da dai sauransu su ma kusan dukansu magungunan kabilar Han ne.

Magungunan manoma na kabilar Korea suna da dogon tarihi. Musamman ma bayan shekarr 1949, a kasar Sin an yi kokari sosai wajen farfado da magungunan kabilu daban daban. Abubuwa da aka sake yin amfani da su wajen haka magungunan sha na kabilar Korea sun hada da tsire-tsire da saiwoyinsu iri daban daban. Ban da wadannan magunguna kuma, akwai magunguna da farar hula ke mallaka, alal misa ana yin amfani da saiwoyin wani irin tsire wajen warkar da masu ciwo daga jin zogi a kugi da makamantansu. (Halilu)

Ilmin likitancin kabilar Zhuang

Wasu muhimman abubuwa na ilmin likitancin kabilar Zhuang

Kabilar Zhuang wata kabila ce da yawan mutanenta ya fi na duk sauran kananan kabilu na kasar Sin. Tun bayan zamanin daular Tang, an sami ilmin likitancin kabilar Zhuang a hankali a hankali wanda ba ma kawai yake da salon musamman na kabilar nan ba, hatta ma ya cudu da ilmin likatancin kabilar Han kwarai. A cikin wani littafi da aka kaddamar a zamanin daular Tang da ta Song wato tsakanin shekarar 618 zuwa ta 1279, an rubuta wasu magunguna masu suna "Lingnan" da ake sha don neman kawar da abubuwa masu guba daga jikin mutum. Irin wadannan magunguna da aka rubuta a cikin littattafan likitoci sun alamanta cewa, ilmin likitancin kananan kabilu da ke zaune a kudancin kasar Sin ciki har da na kabilar Zhuang ya tsaya kan matsayinsa mai muhimmanci ga ilmin likitancin gargajiya na kasar Sin. A zamanin daular Ming da ta Qing wato tsakanin shekarar 1368 zuwa ta 1911, tsowon lokaci ne da aka fi samu ci gaba wajen yalwata ilmin likitancin kabilar Zhuang. Ban da aka rubuta abubuwa kan ilmin likitancin kabilar Zhuang a cikin littafi mai suna "Compendium of Materia Medica" da Li Shizhen ya wallafa da kuma littattafan tarihin wurare daban daban na jihar Guangxi, kuma an kafa makarantaun koyon aikin likitanci na wuri-wuri, kwararru da yawa a fannin ilmin likitancin kabilar Zhuang sun ballo.

Ko da yake ba a rubuta cikaken bayani a kan yadda aka yalwata ilmin likitancin kabilar Zhuang ba, amma an ci gadonsa ta hanyar koyarwa da malamai ke yi wa almajirai da kuma daga bakin jama'a da sauransu. Sabo da haka a cikin shekaru dubbai da suka wuce, an yi ta samun magungunan asiri masu dimbin yawa na kabilar Zhuang daga hannun jama'a, ta haka an ba da taimako ga yalwata ilmin likitancin gargajiyar kasar Sin.

Magungunan kabilar Zhuang

Magungunan kabilar Zhuang magungunan wata kabila ce mai tasowa, ya zuwa yanzu dai ba a kafa tsarinsa ba. A galibi dai, ana hadin magungunan kabilar da na farar hula a gu daya. Ya kasance da dabbobi da tsire-tsire masu armashi a wurare masu zafi kadan da 'yan kabilar Zhuang ke zaune. Da ya ke 'yan kabilar Zhuang na sha'awar cin maciji da bera da tsuntsaye da kuma sauran namun daji, shi ya sa ake yin amfani da dabbobi iri daban daban wajen hada magunguna.

Wani salon musamman na magungunan kabilar Zhuang shi ne, a iya yin amfani da su wajen kubutar da mutane wadanda maciji da tsotsaye da sauran irinsu suka cije su. Shahararren maganin cizon maciji da ake samu a jihar Guangxi babban taimako ne da aka samu daga wajen magungunan kabilar Zhuang. (Halilu)

Ilmin likitancin kabilar Hui

Ilmin likitancin kabilar Hui ilmi ne da aka samu cikin hadin guwar ilmin likitancin gargajiyar Sin da ilmin likitancin Musulmi-Larabawa. A zamanin daular Jin, an fi samu ci gaba sosai wajen raya ilmin likitancin kabilar Hui, an wallafa littafi mai suna "Magungunan Kabilar Hui" da sauran manyan littattafai game da ilmin likitanci wadanda ke da halayen musamman na kabilar Hui, wadanda kuma suka hada ilmin likitancin Larabawa da na gargajiyar kasar Sin gu daya. Daga sunayen magunguna da aka rubuta a cikin wannan littafin "Magungunan Kabilar Hui", akwai "Pill" da "Pharm" da "Plaster" da "decoction" da dai sauransu iri na gargajiyar kasar Sin, kuma da magunguna masu kamshi da giya da mai da ruwan sugari da sauransu irin na Larabawa.

A cikin dogon lokacin da aka yalwata ilmin likitancin kabilar Hui, an kafa wani cikakken tsarin ka'idojin musamman da farar hula ke bi dangane da warkar da masu cututtuka. Wata hanyar musamman da 'yan kabilar Hui ke bi wajen shan magani ita ce, a sha magani, a ci abinci tare don samun warkewaaga cututtuka. Dalilin da ya sa haka shi ne domin 'yan kabilar Hui sun kware wajen dafa abinci da kuma cin abinci mai dadi. Alal misali, an zuba man ridi a cikin magani don warkar da mutane daga cutar rashin kashi da ta hanji da ciwon ajali da aka samu a hanji da dai sauransu. (Halilu)

Ilmin likitancin kabilar Miao

Likitocin kabilar Maio suna ganin cewa, abubuwa shaida kamar dafi da rashin karfi da rauni da gajiya cikin dogon lokaci da kwayoyin cuta da tsutsotsi sun yi sanadinyyar kamuwa da cuta. Likitoci suna binciken masu cututtuka ta hanyar binciken jin bugun jiki da jin murya da yin tambayoyi da sauran irinsu.

Tsire-tsire da dabbobi manyan abubuwa ne da likitocin kabilar Maio ke yin amfani da su wajen hada magungunan sha, sa'an nan kuma suna yin amfani da ma'adinai kadan. Magungunan nan sun kasu cikin gidaje uku wadanda suka hada da magunguna masu zafi, da magunguna masu sanyi da kuma magunguna da ba su da zafi kuma ba su da sanyi. Ana amfani da magunguna masu zafi wajen warkar da wadanda suka kamu da cututtuka sabo da sanyi, sa'an nan kuma ana amfani da magunguna masu sanyi wajen warkar da wadanda suka kamu da cututtuka saboda zafi, haka zalika ana amfani da magunguna irin na baya wajen warkar da wadanda suke fama da rashin karfi. Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka yi, an ce, yawan iri-irien magungunan kabilar da a kan gani ya wuce 1,500 a yanzu, amma akwai 200 wadanda a kan yi amfani da su. (Halilu)