logo

HAUSA

Babi15: Adabin gargajiya

2020-10-30 10:13:53 CRI

>>[Rubutattun wakoki]

Sanannen marubuci Su Shi

Su Shi wanda aka haife shi a shekarar 1037 AD, kuma ya rasu a shekarar 1101 AD, dan gundummar Meishan ne ta lardin Sichuan, wani sanannen marubuci ne lokacin da kasar Sin take daular Song. An kuma kira shi Su Dongpo. Baban Su Shi shi ma wani marubuci ne wanda ya yi suna sosai a nan kasar Sin. Sakamakon haka, babansa ya ba shi tasiri sosai. Lokacin da yake yarantaka, yaro Su Shi ya sa babbar niyya. Bayan ya girma, ya zama wani dan siyasa. Su Shi ya mai da hankali sosai wajen yin gyare-gyare da kuma yin kokari kwarai wajen tafiyar da harkokin siyasa. Lokacin da yake kan mukaman gwamnatocin wurin, ko ya zama muhimmin minista a fadar sarkin daular Song na kasar Sin, Su Shi ya kan nuna kokari wajen yin gyare-gyare domin fama da al'amubazzaranci.

Amma domin Su Shi mutum ne mai gaba gadi kuma mai saukin kai, ya kan yi suka kan wasu kurakurai na daular Song kai tsaye. Sabili da haka, a cikin famar da aka yi a tsakanin jami'an daular, ya kan zama mutum mai zaman kashe wando. Bayan ya kai shekaru 43 da haihuwa, ya sha wahalolin siyasa kwarai. Sarkin daular Song ya kore shi daga mukaminsa kuma ya kai shi wuraren da ke fama da talauci sosai har sau da yawa. Amma lokacin da yake fama da abokan gabansa na siyasa, Su Shi ya hada da tunanin addinin Ru da na Buddha kuma da na Dao. Tunanin Buddha da na Dao sun taimake shi wajen duba matsalolin da ke kasancewa a zaman al'ummar kuma yadda zai kubutar da shi daga wahaloli da kansa. A sa'i daya, tunanin addinin Ru ya taimake shi kan yadda zai tsaya tsayin daka kan buri mai kyau da yake nema. Sabo da haka, ba ma kawai Su Shi ya iya kare halinsa da buri mai kyau da yake nema ba, har ma ya ci wahaloli masu tsanani da aka kai masa.

Domin Su Shi mutum ne kai tsaye mai karfin zuciya, kuma ba shi boye kome. Marubuta bayan Su Shi sun yaba wa irin wannan halinsa sosai. Ana kuma kiran irin wannan hali na Su Shi "misalin koyo na Dongpo" da sauran marubuta suka koya a cikin shekaru 800 bayan rasuwarsa.

Ba ma kawai Su Shi ya iya rubuta wakoki ba, har ma ya iya rubuta sauran bayanan nuna rayuwa iri iri kamar zube da yawa. Su Shi yana daya daga cikin marubuta 8 wadanda suka yi zamani a daular Tang da daular Song kuma suka fi suna a nan kasar Sin har yanzu. Daga cikinsu, Su Shi ya fi sauran marubuta 7 gwaninta wajen rubuta wakoki da zube. Kodayake Su Shi ya fi sauran marubuta shan wahaloli da yawa, amma daga baya, marubuta na kasar Sin su kan koyi fasaharsa ta rubuta wakoki da zube bi da bi.

Rubuce-rubucen zube mafi kyau zube ne da ya rubuta lokacin da yake yawon shakatawa. (Sanusi Chen)

"Sarkin Rubutaccen Wakoki" Du Fu da rubutaccen wakokinsa

A cikin tarihin adabin kasar Sin, a kan cewa "Li Du" suna wakiltar babban sakamakon da aka samu a fanning rubutaccen wakoki a daular Tang (618----907). Li, wato Li Bai, wani al'ajabin waka, Du, wato Du Fu, sarkin rubutaccen wakoki ne na kasar Sin. Yanzu dukkansu sun fi suna a duk duniya.

An haifi Du Fu ne a shekarar 712. Tun daga lokacin da yake yarantaka, Du Fu yana da hankali sosai kuma ya yi kokari wajen karatu. Domin kakansa Du Shenyan shi ma wani shahararren marubucin rubutaccen wakoki ne a daular Tang, Du Fu yana da damar koyon abubuwa da yawa ciki har da fasahar rubuta rubutaccen wakoki. Lokacin da yake da shekaru 7 da haihuwa, Du Fu ya fara rubuta rubutaccen wakoki. Bayan ya girma, ba ma kawai ya iya rubuta rubutaccen wakoki ba, har ma ya iya yin zane-zane da kide-kide da yin wasan takobi a kan doki. Hausawa su kan fadi cewa, "Yawan shekaru ba shi ne wayo ba". Bayan ya kai shekaru 19 da haihuwa, saurayi Du Fu ya fara shan iska a ko'ina na duk kasar Sin don nishadin zamansa. A waccan lokaci, daular Tang tana cikin halin bunkasuwa sosai. Saurayi Du Fu ya yi yawon shakatawa a duwatsu da kogunan da suka fi suna sosai a nan kasar Sin, kuma ya sami ilmi da yawa. Sakamakon haka ne, ya rubuta wata rubutacciyar wakar da ta fi suna a cikin tarihin kasar Sin, wato "Lakacin da kake kolin dutse, sai ka ga kome ya kankana."

Kamar yadda sauran mawaki da marubuta suke so, Du Fu ma ya fi son zama wani jami'in daular Tang. Sabo da haka, ya kan rubuta wasu rubuce-rubucen zube da rubutaccen wakoki don manyan jami'ai ko ya shiga jarrabawa. Amma abin bakin ciki shi ne bai sami nasara ba. Daga baya, lokacin da yake da zama a birnin Chang'an, babban birnin daular Tang, baba Du Fu wanda ke fama da talauci ya ga masu hannu da shuni suna nishadin zamansu kwarai, amma matalauta ba su iya samun isashen abinci da tufafi, sun mutu a kan titi. Sabili da haka ne, Du Fu ya rubuta wakar "Masu hannu da shuni suna batad da nama da giya, amma matalauta sun mutu a kan titi domin sanyi." Domin Du Fu bai iya cimma burinsa ba lokacin da yake mukamin gwamnati, kuma ya kan yi fama da talauci kwarai. Du Fu ya ga masu hannu da shuni suna cin hanci da rashawa, amma farar hula suna fama da talauci kwarai. A hankali a hankali ne Du Fu ya zama wani marubucin rubutaccen wakoki da ke jin tausayin kasa da farar hula.

A shekarar 755, Du Fu, mai shekaru 43 da haihuwa, ya zama wani jami'in daular Tang. Amma bayan wucewar wata daya kawai, an haddasa wani yaki a daular. Tun daga wannan lokaci, an yi ta yin yaki a daular Tang. A cikin wannan lokaci, Du Fu ya yi gudun hijira ya sha wahala kwarai, ya fi sanin halin da ake ciki kwarai. A cikin wannan lokaci, ya rubuta sanannun rubutaccen wakoki da yawa ciki har da "Jami'in Shigao" da "Jami'in Tongguan" da "Jami'in Xin'an" da "Ban kwana da amarya" da dai sauransu, inda ya bayyana tunaninsa na jin tausayin farar hula da fushi ga yake-yake.

A shekarar 759, Du Fu ya bata rai kwata kwata ga siyasa ya yi murabus daga mukaminsa. A wannan lokaci, ana fama da bala'in fari, Du Fu wanda ya yi fama da talauci bai iya yin zama a birnin Chang'an ba, ya gudu zuwa birnin Chengdu da ke kudu maso yammacin kasar Sin da iyalansa. Ya danganta da taimakon da abokansa suka samar masa ne, ya yi zama a birnin Chengdu. Lokacin da yake fama da talauci a birnin Chengdu, ya rubuta "Wakar Iskar fasalin kaka ta bata gidan jinka", inda ya bayyana yadda shi da iyalansa suke fama da talauci, kuma ya yi fata dukkan matalauta za su iya samun sabbin gidajen da suke nema don kawar da zafin talaucinsu.

A shekarar 770, Du Fu, mai shekaru 59 da haihuwa, wanda ya yi fama da talauci da ciwace-ciwace ya mutu a kan hanyar gudun hijira. Wakokin da Du Fu ya rubuta kuma muke samu yanzu sun kai fiye da 1400. Wadannan rubutaccen wakoki sun bayyana tarihin yake-yaken da aka yi a daular Tang, da zaman al'ummar daular Tang da aka shafe shekaru fiye da 20. Du Fu ya rubuta rubutaccen wakoki da tsare-tsaren rubuce-rubuce iri iri, kuma ya kan koyi kyawawan fasahohin rubuta rubutaccen wakoki na sauran mutane. Bugu da kari kuma, ya kan bayyana tunaninsa ko ya yi sharhi lokacin da yake rubuta abubuwan da ya gani ko ya ji. Tsare-tsaren rubuta rubutaccen wakokin da Du Fu ya bi sun ba da tasiri sosai ga mutanen bayansa. (Sanusi Chen)

"Marubucin wakoki mai Al'ajabi" Li Bai da rubutattun wakokinsa

Li Bai(701—762) wani mashahurin marubucin rubutaccen wakoki ne a daular Tang ta kasar Sin. Shi mutum ne mai girman kai kuma mai zaman kansa kwarai. Ban da wannan, shi mutum ne mai karfin zuciya kuma maras fargaba.

Asalin Li Bai yana wurin da ke cikin lardin Gansu na yanzu, amma har yanzu ba a san ainihin kakaninsa da kuma a ina ne aka haife shi ba. Daga rubutaccen wakokin da ya rubuta, an sani cewa, ya yi zama a cikin wani gida mai arziki kuma mai ladabi. A yayin da yake yarantaka, ya karanta latattafai iri iri da yawa. Ba ma kawai ya karanta litattafai da yawa ba, har ma ya iya wasan takobi sosai. Bayan da ya kai shekaru 20 da haihuwa, ya fara yawon shakatawa a wurare daban-dabam na kasar Sin domin kara sanin duniya. A sakamakon haka, yana da ilmi iri iri kuma yana da hankali sosai. Sabo da haka, Li Bai ya ci nasara sosai wajen rubuta rubutattun wakoki. Kodayake a lokacin can, fasahohin wallafa littafi da na sadarwa sun ja da baya ainun, amma domin marubuta su kan yi mu'ammala ko su yaba wa juna abubuwan da suka rubuta, saurayi Li Bai ya shahara sosai a daular Tang.

Lokacin da kasar Sin take dauloli iri iri, mutane su kan yi karatu kuma su shiga jarrabawa domin neman izinin zama jami'an dauloli. Saurayi Li Bai shi ma yana fata zai zama wani jami'in daular Tang. Sabo da haka, ya je birnin Chang'an, babban birnin daular Tang. Domin rubutattun wakokin da ya rubuta sun shahara sosai, kuma an yaba masa ga sarkin daular Tang, a shekarar 742, Li Bai ya sami izinin shiga fadar daular Tang ya zama wani shehun malami. Ya ji dadin zamansa a fadar sosai.

Amma domin Li Bai mutum ne mai girman kai, kuma ya fusata ga halin cin hanci da ake ciki a lokacin can. Li Bai yana fata sarki zai nada shi kuma zai ba shi damar yin amfani da gwanintarsa kan harkokin siyasa. Amma a ganin sarkin daular Tang, Li Bai wani marubucin wakoki ne da ke aiki a fadarsa kawai. Ban da wannan, sauran masu hannu da shuni da ke cikin fadar su kan zarge shi. Sabili da haka, sarkin bai amince da shi ba. Li Bai ya bata rai sosai ya bar birnin Chang'an ya sake shiga yawon shakatawa.

Li Bai ya kan yi yawon shakatawa har kullum lokacin da yake nan duniya. A cikin wadannan lokuta, ya rubuta wakoki da yawa da suke shafar wurare masu kayatarwa . Kamar misali, ya ce, "Ana shan wahalar bin hanyar zuwa lardin Shu, kamar yadda ake bin hanyar zuwa gidan gaskiya", "Aboki mai martaba ba ka ga ruwan kogin Rawaya ta zo ne daga sararin sama, kuma yana nufin teku amma ba zai dawo ba?" da dai sauransu. Wadannan rubutattun wakoki suna yaduwa kuma sun shahara sosai a nan kasar Sin.

Ya zuwa yanzu, rubutattun wakokin da Li Bai ya rubuta kuma ana karanta su har yanzu sun kai fiye da dari 9 tare da rubuce-rubucen zube fiye da 60. Domin Li Bai yana gwanance sosai wajen rubuta wakoki, bayan ya rasu, an kira shi "Marubucin wakoki mai Al'ajabi". (Sanusi Chen)

Rubutattun wakokin daular Tang da suka shahara a cikin tarihin kasar Sin

Daular Tang wata muhimmiyar daula ce a cikin tarihin kasar Sin. A wannan daular Tang, tattalin arzikinta na samun bunkasuwa kwarai, halin zaman al'umma yana da karko, haka nan kuma al'adu da fasahohin zane-zane da rubuce-rubuce ma sun samu bunkasuwa sosai, musamman an fi rubuta kyawawan rubutattun wakoki da yawa a wannan daula. A daular Tang, rubuta rubutattun wakoki ya riga ya zama muhimmin abu ga zaman rayuwar al'adu. Lokacin da fadar daular take shirya jarrabawa domin neman sabbin jami'ai, gwamma rubutattun wakoki da bayanin sharhi. A cikin littafin da aka fi sani da suna "Zababbun Rubutattun Wakokin daular Tang" akwai rubutattun wakoki kusan dubu 50 da marubuta fiye da 2300 suka rubuta.

Yanzu an raba matakai 4 game da bunkasuwar rubutattun wakokin daular Tang, wato lokacin farko na daular Tang da lokacin bunkasuwar daular Tang da matsakaicin lokaci na daular Tang da kuma karshen lokaci na daular Tang.

A farkon lokacin daular Tang, wato tun daga shekarar 618 zuwa shekarar 712, marubuta 4, wato Wang Bo da Yang Jiong da Lu Zhaolin da Lu Binwang da aka fi sani da suna "Gwanaye 4" sun gama aikin sauti da tsarin rubuta wakoki. A sakamakon haka, sun kafa hanyar rubuta wakokin kasar Sin. Sabo da haka, rubutattun wakokin daular Tang suna da halin musamman nasu. A karkashin wadannan marubuta 4 wadanda suka fi sani a lokacin can, ba ma kawai ana rubuta da rera rubutattun wakoki a fadar daular ba, har ma jama'a farar hula ma suna koyon fasahar rubuta da rera wakoki. Rubutattun wakokin suna kuma da karfi sosai ba kamar yadda rubutattun wakokin da aka rubuta a da lokacin hali maras kyau suke ba. Marubuci Chen Zi'ang wanda ya fi gwaninta a farkon lokacin daular Tang ya bayar da ra'ayinsa cewa, ya kamata a komar da kyawawan al'adun bayyana halin zamantakewa da jama'a ke ciki lokacin da ake rubuta wakoki. Rubutattun wakokin da ya rubuta suna da karfi kuma bai kawatar da su sosai ba. Chen Zi'ang ya bude hanyar kara raya rubutattun wakokin daular Tang.

Tun daga shekarar 712 zuwa shekarar 762, daular Tang ta shiga lokacin samun bunkasuwa kwarai. Sabili da haka, an rubuta wakoki mafi dimbin yawa a wannan lokaci, sannan kuma sakamakon fifiko da aka samu wajen rubutattun wakoki ya fi samun ci gaba kwarai. Rubutattun wakokin da aka rubuta a wannan lokaci sun kunshi abubuwa da yawa, kuma an rubuta su ne ta hanyoyi daban-dabam. Wasu marubuta sun yaba halitta, wasu kuma sun yi fatan zuwa yankin iyakar kasa, wasu kuma sun yaba jarumtaka, amma wasu sun yi ajiyar zuciya domin bacin ransu ga zaman al'umma. Yawancin marubuta sun iya rubuta wakoki cikin 'yanci kuma sun kafa muhalli na bunkasuwar daular Tang da ya girgiza daulolin bayan daular Tang.

A lokacin bunkasuwar daular Tang, marubuta wakoki wadanda suka fi shahara sun kunshi Li Bai da Du Fu da Wang Wei da Meng Haoran da Gao She da kuma Cen Cen. Cen Cen ya fi iya rubuta wakokin da ke shafar abubuwa game da yankin iyakar kasa. Gao Shi ya kan bayyana wahalolin da matalauta suke sha a cikin rubutattun wakokin da ya rubuta. Amma har yanzu ana ganin cewa, wadanda suke wakiltar sakamakon da aka samu wajen rubutattun wakoki a lokacin bunkasuwar daular Tang su ne "Marubucin wakoki mai Al'ajabi" Li Bai da "Sarkin rubutattun wakoki" Du Fu. Rubutattun wakokin da suka rubuta sun yi tasiri sosai ga sauran marubuta a bayansu.

A matsakaicin lokacin daular Tang, wato tun daga shekarar 762 zuwa shekarar 827, Bai Juyi da Yuan Zhen da Li He sun fi shahara. Bai Juyi ya kware kan rubuta wakoki na zambo. A cikin wakokin da ya rubuta ya kan yi wa masu hannu da shuni ba'a, kuma ya ki a kan yi yaki. Ban da wannan Bai Juyi ya yi kokari sosai kan yadda zai iya rubuta wakokin ban sha'awa masu saukin karantawa ga farar hula. Sabo da haka, an fi son karanta wakokin da Bai Juyi ya rubuta.

Li He, wani marubucin wakoki ne kuma mai fama da talauci wanda bai dade ba a duniya. Ya mutu lokacin da ya kai shekaru 20 da wani abu kawai da haihuwa. Li He ya kan bayyana tunaninsa sosai lokacin da yake rubuta wakoki. Ban da wannan, ya kan sa sabon tunaninsa da sabuwar hanyar bayyana tunaninsa, musamman tunanin bacin rai a cikin wakokin da ya rubuta. Bugu da kari kuma, Li He ya fi son amfani da kayatattun kalmomi a cikin wakokinsa domin ya fi son abubuwa masu kyaun gani.

Tun daga shekarar 827 zuwa shekarar 859, an shiga karshen lokacin daular Tang. A wannan lokaci, Li Shangyin da Du Mu sun fi shahara. Du Mu ya iya hada tunani mai sauki da tunani mai tsanani a cikin waka daya. Sabo da haka, ya kan bayyana zuciyarsa game da harkokin siyasa a cikin wakokinsa. Amma Li Shangyin ya kware kan tsarin wakoki. Ya kan yi amfani da wasu kayatattun kalmomi a cikin wakokinsa masu duhu-duhu, inda suka bayyana wahalolin da ya taba sha lokacin da yake mukamin jami'in daular. Sannan kuma, Li Shangyin ya kan bayyana bakin cikinsa a cikin wakokinsa. Mashahurin wakar da aka fi sani da suna "Babu Lakabi" da Li Shangyin ya rubuta, wannan wata wakar nuna soyayya ce ko wakar bayyana harkokin siyasa? Har yanzu ana yin muhawara game da wannan a nan kasar Sin. (Sanusi Chen)

Tao Yuanming da rubutattun wakokinsa

Tao Yuanming, wani marubucin wakoki ne na daular Dongjun na karni na 4, wani sunansa daban shi ne Tao Qian. Shi ne ya fara rubuta wakokin da ke bayyana yanayin kauyuka da ayyukan noma. Lokacin da yake nan duniya, Tao Yuanming bai lura da arziki ba ya kuma girmama yanayin halitta sosai. Shi mutum ne mai girman kai kuma mai gaba gadi. Har yanzu, marubutan dauloli daban-dabam ciki har da na yanzu na kasar Sin sun nuna yabo kuma suna girmama irin wannan hali nasa.

Tao Kai, kakani-kakanin Tao Yuanming, yana daya daga cikin manyan hafsoshin daular Dongjun wadanda suka kafa daular. Kakansa da mahaifinsa dukkansu jami'ai ne na daular. Lokacin da yake da shekaru 8 da haihuwa, abin tausayi ya faru, babansa ya rasu. Sabo da haka, gidansa ya fara shiga cikin halin talauci. Lokacin da yake karami, Tao Yuanming ya taba sa niyyar zama wani jami'in daular sabo da yana son bayar da gudummawarsa kan harkokin siyasa.

Amma daular Dongjun daula ce ta rashin kwanciyar hankali. Iyalan daular su kan yi fama da juna, kuma ba a iya tafiyar da al'amuran daular kamar yadda ya kamata ba. Lokacin da yake da shekaru 29 da haihuwa, Tao Yuanming ya taba zama wani jami'in daular, amma ba da dadewa ba, bai iya yin hakuri da duhu da al'amubazaranci na daular ba, ya yi murabus daga mukaminsa ya koma gida. Daga baya, ko da yake ya taba sake hawa kan wasu kananan mukaman daular domin zamantakewarsa ta tilasta masa ya yi haka, amma daga karshe dai ya yi murabus daga mukaman bi da bi ya kuma koma gida.

Bayan ya koma gida, babu sauran hanyar neman kudi da zai iya zaba, sai ya yi noma. Tun da haka, ya shiga halin fama da talauci a kai a kai, amma bai iya renon iyalansa ba. A sakamakon haka dai, lokacin da yake da shekaru 41 da haihuwa, ya sake samun wani mukami daga daular, ya zama shugaban gundummar Pengze. Amma bayan kwanaki fiye da 80 kawai, ya sake yin murabus daga mukaminsa ya sake komawa gida. A sabili da haka, ya yi ban kwana da mukamin jami'in daular kwata kwata har abada ya yi noma kawai a wani kauye.

A kauyen, Tao Yuanming da iyalansa suna zama cikin halin fama da talauci. A lokacin da yake da shekaru 44 da haihuwa, wata gobara ta faru a gidansa. Tao Yuanming ya fi samun talauci. A sakamakon haka, ya rubuta wakar cewa "A lokacin zafi, sai yunwa nake ji cikin dogon lokaci. A lokacin sanyi, na kan shiga barci amma ba tare da mashimfidin gado mai kamar lifidi ba". Wannan waka ta bayyana halin da Tao Yuanming yake ciki a kauye. A cikin wakokin da ya rubuta, a karo na faro ne zamantakewar kauye da yanayin kauye sun zama muhimmai kuma kyawawan abubuwan da ake so. Ko da yake yana fama da talauci sosai a kauye, amma abubuwa game da kauye da ya rubuta a cikin wakokinsa dukkansu masu tsabta ne kuma masu kyaun gani.

Bayan Tao Yuanming ya tsufa, tsoho Tao Yuanming ya zama mutum mai ban tausayi. Har a wasu lokuta, ya yi bara ko ya yi bashin abinci. Amma ko da yake yana cikin mawuyacin hali sosai, duk da haka Tao Yuanming ya sake kin yarda da zama wani jami'in daular. Wani zuben da Tao Yuanming ya rubuta a lokacin da yake tsoho da aka fi sani da suna "Asalin furen Peach da rubutacciyar waka" ya bayyana wata zaman al'umma mai inganci. A cikin wannan zube, an ce, wata rana ba zato ba tsammani wani masunci ya shiga wani wuri mai suna "Asalin Furen Peach", wato Taohuayuan, inda ya ga akwai wasu mutane suna da zama a can. Kakanin-kakanin wadannan mutane sun isa wannan wuri ne domin gudu daga yake-yaken da aka yi. Bayan sun yi zama a can, ba su taba barin wannan wuri ba. Wadannan mutane ba su san sauran wuraren duniya ba sai wurin da suke da zama. Su zama mutane masu kai tsaye wadanda suke kokarin yin aiki kuma suke da zama a can cikin lumana amma ba tare da kowane irin damuwa ba. Kyawawan abubuwan da Tao Yuanming ya rubuta a cikin wannan zube sun bayyana cewa, jama'a masu shan wahalolin yake-yake a lokacin can sun yi fata za su iya yin zama a cikin zaman al'umma mai zaman lafiya.

Yanzu, za a iya ganin rubutattun wakoki fiye da dari 1 da zube guda 10 da 'yan kai kawai da Tao Yuanming ya rubuta. Amma a cikin tarihin ladabi na kasar Sin, Tao Yuanming yana da muhimmanci kwarai. A daular Dongjun, an fi mai da hankali kan hanyoyin rubuta wakoki da zube. Lokacin da ake rubuta wata waka ko wani zube, an kuma fi mai da hankali kan yin amfani da wasu kawatattun bakakku a ciki. Amma Tao Yuanming bai rubuta wakoki da zube kamar haka ba. Ya rubuta wakoki da zube masu dimbin yawa inda ya yaba wa yanayin kauyuka da ayyukan noma. Tao Yuanming kamar yadda sauran marubutan da suke nan duniya kafin shi suka yi, ba ya son yin amfani da kawatattun bakakku a cikin wakoki da rubutun zubensa. Yanzu za a iya karanta da gane wakoki da zuben da Tao Yuanming cikin sauki. (Sanusi Chen)

Qu Yuan da Rubutattun Wakokinsa

Qu Yuan wani sanannen mawaki ne da jama'ar kasar Sin suka fi kaunarsa da girmama shi a cikin shekaru fiye da dubu 2. Ya yi zama a lokacin Zhan Guo a nan kasar Sin, wato wajen shekarar 475 kafin haihuwar Annabin Isa zuwa shekarar 221 kafin haihuwar Annabin Isa. Ma'anar Zhan Guo ita ce, kananan kasashe da yawa a nan kasar Sin sun yi zaman tare, amma su kan yi yaki a tsakaninsu. A cikin wadannan kananan kasashe, kasar Qing da kasar Chu kasashe 2 ne da suka fi su karfi. Sauran kananan kasashe fiye da 10 sun dogara da wadannan manyan kasashe 2.

Qu Yuan wani dattijo ne na kasar Chu. Yana da wani muhimmin mukami a gwamnatin kasar Chu. Qu Yuan yana da ilmi kwarai kuma ya kware kan harkokin diplomasiyya. A farkon lokacin yin aiki a gwamnatin Chu, sarkin kasar Chu ya amince da shi sosai. A waccan lokaci, sarkuna da masu hannu da shuni na kasashe daban-dabam dukkansu sun yi kokarin neman wasu kwararru da 'yan kasa nagari da su zama masu ba da shawara a gare su. Sabo da haka, a lokacin Zhan Guo, kwararru da sanannun mutane wadanda suke da ilmi da yawa su kan kai wa sauran kasashe ziyara sun yi fatan bauta wa wani dan siyaya ko manyan jami'an gwamnatocin kasashe daban-dabam domin cimma burinsu na samun wasu sakamako wajen harkokin siyasa. Amma Qu Yuan bai yi haka ba, ya yi kishin kasar Chu kwarai, kuma ya yi fatan zai iya taimaka wa sarkin kasar Chu da ilminsa. Qu Yuan ya yi fatan kasar Chu za ta kara samun karfi, kuma za ta kara samun ci gaba wajen harkokin siyasa. Sabo da haka, har ya mutu, Qu Yuan bai taba barin mahaifa kasar Chu ba. Amma abin bakin ciki shi ne, domin Qu Yuan ya kan yin cacar baki sosai da rukunin masu hannu da shuni kan harkokin gida da na waje, wasu masu hannu da shuni sun wulakanta shi. Sarkin kasar Chu ma ya fara yin ko oho da shi. Bayan Qu Yuan ya yi murabus daga mukaminsa a gwamnatin kasar Chu, a hankali a hankali ne kasar Chu ta zama kasa maras karfi, kuma maras cigaba. A shekarar 278 kafin haihuwar Annabi Isa A.S, sojojin kasar Qing sun kai farmaki kan kasar Chu kuma sun mamaye birnin Cheng, babban birnin kasar Chu. Kasar Qing ta ci kasar Chu, Qu Yuan ya yi bakin jini kuma ya ji kunya kwarai da gaske. Wata rana ya yi kuka har ya daka tsalle a cikin kogin Mi Luo daga nan ya riga mu gidan gaskiya.

Ko da yake Qu Yuan ya mutu, amma kayayyakin da ya bari suna nan har abada. Domin shi mawaka mai zama kansa na farko ne a tarihin kasar Sin, marubutacciyar wakar da aka fi sani da suna "Li Sao" da ya rubuta ta zama wakar bayyana tunaninsa na siyasa wadda ta fi doguwa a tarihin adabin kasar Sin. A cikin wakar "Li Sao", mawaka ya yi amfani da tatsuniyoyin tarihi masu dimbin yawa. Qu Yuan ya yi fata sarkin kasar Chu zai yi koyi da nagartattun sarkuna Yao da Shen da Yu, kuma zai nada wasu 'yan kasa nagari da su hau kan muhimman mukamai. Ban da wannan, Qu Yuan ya yi fata sarkin kasar Chu zai iya daidaita harkoki cikin adalci da da'a, kuma zai iya hada kan sauran kasashe domin dagiya da kasar Qing. Wakar "Li Sao" ta zarce hanyar rubuta wakokin da aka tsara a cikin wakokin "Shi Jing". Qu Yuan ya kirkiro hanyoyi da yawa kan yadda za a iya bayyana tunani a cikin wakoki. Sabo da haka, an ce, Qu Yuan ya bude wani sabon shafi wajen rubuta wakoki a dauloli na da.

Ban da wakar "Li Sao", wakar "Mu Tambayi Allah" wata waka ce mai ban mamaki. A cikin wakar, Qu Yuan ya yi amfani da jimlolin tambaya ya gabatar wa Allah tambayoyi 172 wadanda suka shafi ilmin sararin sama da ilmin kasa da adabi kuma da ilmin tunani da dai sauran fannoni. Wannan waka ta bayyana cewa, Qu Yuan yana da jaruntaka wajen neman gaskiya. Bugu da kari kuma, a cikin "Wakoki 9" da ya rubuta bisa wakokin addu'a, ya kirkiro abubuwan al'ajabi da yawa, har ya rubuta soyayyar da ke kasancewa a tsakanin bil Adam da abubuwan al'ajabi.

A cikin wakokin da Qu Yuan ya rububa, za a iya ganin tunanin ban mamaki da yawa. Kamar misali, yak an sa halin dan Adam a kan furanni. Ya kuma kirkiro al'ajabin mata da yawa domin bayyana soyayyarsa. Sabo da haka, lokacin da ake karanta wakokin da Qu Yuan ya rubuta, ba ma kawai ana jin dadin kawatattun bakakun da kalmomin da ya rubuta ba, har ma ana sanin tunaninsa na kishin kasar. Sakamakon haka ne, a cikin shekaru fiye da dubu 1, Qu Yuan wani mawaka ne da aka fi kaunarsa a nan kasar Sin. (Sanusi Chen)

"Littafin Wakoki" littafin farko na gama kan wakoki a kasar Sin

A karni na 7 kafin haihuwar Annabi Isa (A.S), "Littafin Wakoki", wato littafin farko na gama kan wakoki a nan kasar Sin ya bullo. Wannan "Littafin Wakoki" ya hada da wakoki masu ma'anar tarihi da wakokin zambo gatse da wakokin soyayya da na soja da na fatan alheri da wakokin fasalin shekara kuma da wakokin kwadago da dai sauransu. Ko da yake mutane da yawa ne suka hada da wadannan wakoki, amma wannan littafi ya bayyanu shekaru daruruwa kafin "Wakoki masu ma'anar tarihi na Homer", wato sannanun wakokin da na kasar Girka.

"Littafin Wakoki" littafin farko ne da aka hada da wakoki masu dimbin yawa, inda aka hada da rubutattun wakoki 305 da suka shafi shekaru wajen dari 5, wato daga farkon shekara na daular Xi Zhou wadda ta yi zama a nan duniya a karni na 11 kafin haihuwar Annabi Isa zuwa lokacin Chun Qiu, wato a karni na 7 kafin haihuwar Annabi Isa (A.S). An raba "Littafin Wakoki" har kashi 3, wato kashi na Feng da kashi na Ya kuma da kashi na Song. Kashi na Feng ya hada da wakoki 160 da jama'ar kananan kasashe 15 kan rera. Kashin Ya ya hada da wakoki 105 da a kan rera a karkarar babban birnin daular Zhou. "Song" ya hada da wakoki 40 na yin sadaka wadanda ake rerawa domin yabon gagarumar gudummuwa na kakanin-kanini da kuma dodanni.

Yawancin wakokin na "Littafin Wakoki" wakoki ne da ake kiransu da suna Wakoki masu kalma 4, wato a cikin kowane layi na waka, an rubuta kalmomi 4 kawai. Bugu da kari kuma, sauran wakoki ne masu kalma 2 zuwa masu kalma 8. A cikin wakokin, a kan sa kalma daya a cikin layi daya har sau 2. Ban da wannan kuma, an rubuta wadannan wakoki ta hanyoyi iri iri. Sabo da haka, ana jin dadin karanta wannan "Littafin Wakoki" sosai. A cikin wannan littafi, wakoki na kashin Feng sun fi kashi na Ya da kashi na Song muhimmanci. Wakoki na kashin Feng wakoki ne da jama'a kan rera. Ba a taba kawatar da su sosai ba, inda aka bayyana zaman al'ummar farar hula, kamar misali soyayyar da ke tsakanin maza da 'yan mata. Bugu da kari kuma, an bayyana tsarin bauta da yake-yake da dai sauransu a cikin wakokin kashi na Feng.

Marubuta wadannan wakoki suna da yawa wadanda suka hada da 'yan kwadago da sojoji da wasu kwararru da jami'ai da dattijai. Wasu marubuta har yanzu ba a iya tabbatar da asalinsu ba.

A da, an fi son rera wakoki na "Littafin Wakoki" domin bukukuwan taya murna ko zaman nishadin ko bayyana ra'ayoyin marubuta game da maganganun zaman al'umma da siyasa. Amma daga baya, "Littafin Wakoki" ya zama wani littafin koyarwa na dattijai. Ya zama daya daga cikin muhimman litattafan da dole ne dattijai suka yi koyi da su. Bayan an yi koyi da wadannan wakoki, za a iya kawatar da maganar da za a yi. Musamman lokacin da ake mu'amala da sauran mutane, a kan tsamo abubuwa na "Littafin Wakoki" domin bayyana abubuwan da ake son fada ba kai tsaye ba. A cikin "Maganar Confuzi", shehun malami Confuzi ya ce: "Idan ba a yi koyi da Littafin Wakoki ba, ba za a iya yin magana ba". Sabo da haka, "Littafin Wakoki" yana da muhimmin matsayi a nan kasar Sin.

A takaice dai, "Littafin Wakoki" ya zama littafin da ya alamantar da cewa adabin kasar Sin ya fara samun bunkasuwa kafin sauran kasashen duniya. Abubuwan "Littafin Wakoki" sun shafi bangarori daban-dabam na zaman al'ummar kasar Sin a shekaru aru aru da suka wuce, kamar misali, ya shafi kwadago da soyayya da yake-yake da bauta da matsin lambar da aka yi wa jama'a da al'adun kabilu iri iri da aure da liyafa da yanayin sama da na kasa da dabobbi da shuke-shuke iri iri. Kalmomin "Littafin Wakoki" sun zama muhimman kayayyaki lokacin da ake nazari kan harshen Sinanci da ya kasance a karni na 11 zuwa karni na 6 kafin haihuwar Annabi Isa (A.S). (Sanusi Chen)

>>[Wasan kwaikwayo]

Shehun malami Li Yu wanda ya kware kan ilmin wasan kwaikwayo

A cikin tarihin adabin kasar Sin da ya shafi shekaru dubbai da suka wuce, akwai sanannun marubutan wakoki da na wasannin kwaikwayo da na tatsuniyoyi da yawa. Amma har yanzu an kasa gane wani mutum kadai wanda ba ma kawai ya iya rubuta wasannin kwaikwayo da ba da jagora ga nune-nunensu ba, har ma ya kware kan ilmim wasan kwaikwayo da ba da jagoran nune-nunensu kuma da rubuta tatsuniyoyi iri iri. Mr. Li Yu, sanannen masani ne da ya kware kan ilmin wasan kwaikwayo, yana daya daga cikin irin wadannan masana.

A shekarar 1610, wato lokacin da kasar Sin take karkashin daular Ming ce aka haifi Li Yu. Lokacin da yake da shekaru 30 da haihuwa, daular Qing, daular karshe ta mulkin kama karya na kasar Sin ta canja daular Ming da karfin tuwo. Sabo da haka an tashi da hankali sosai a kasar Sin har tsawon shekaru goma-gomai. Li Yu ya yi zama a cikin irin wannan zaman al'ummar tashin hankali har ya mutu a shekarar 1680.

Lokacin da yake karami, ya sami ilmin gargajiya na tunanin Ru, wato a da a nan kasar Sin, yawancin kwararru kan ilmi daban-dabam su kan yi fatan za su iya shiga jarrabawar zaben jami'a da dauloli suka shirya. Amma domin Li Yu ya yi zama a cikin wata zaman al'ummar tashin hankali, ko da yake ya taba halartar wasu jarrabawa, amma bai taba cinsu ba. A sabili da haka, Li Yu bai sake neman izinin zama wani jami'i ba. Ya bude wani kantin sayar da litattafai a gidansa. Ya sayar da litattafai da abubuwan da ya rubuta domin neman wasu kudin sayen kayan masarufi. A sa'i daya, ya dukufa da kansa kan rubuta wasannin kwaikwayo.

Muhimman sakamakon da Li Yu ya samu sun hada da wasannin kwaikwayo da tunanin rubuta su. Wasannin kwaikwayo da Li Yu ya rubuta kuma za a iya samunsu yanzu sun kai 10 ciki har da Kifin Bimu da Huang Qiu Feng da Yu Saotou da Lian Xiangban da dai sauransu. Tunanin da Li Yu ya bayyana a cikin wadannan wasannin kwaikwayo shi ne soyayya. Wasannin kwaikwayo da Li Yu ya rubuta sun jawo hankulan mutane sosai domin harsuan da Li Yu ya rubuta suna da ban sha'awa. Sakamakon haka, wasannin kwaikwayo da Li Yu ya rubuta sun fi dacewa da a yi nune-nunensu a dandalin wasan kwaikwayo. An yi maraba da wasannin kwaikwayo da Li Yu ya rubuta sosai. Ban da wannan kuma, an yada wasannin kwakwayo har a kasashen kudu masu gabashin Asiya ciki har da kasar Japan wadanda suka yi cudanya da kasar Sin sosai. Har zuwa yanzu, ana nune-nunen wasannin kwaikwayo da Li Yu ya rubuta a nan kasar Sin.

Ba ma kawai Li Yu ya rubuta wasannin kwaikwayo da yawa ba, har ma ya ba da jagora kan nune-nune har ya zama dan wasannin kwaikwayon da ya rubuta. A da, yan wasan kwaikwayo ba su da matsayi a cikin zaman al'umma. Kwararru kan ilmi na gargajiya ma sun yi fatali da irin wannan aiki. Amma domin Li Yu yana kaunar rubuta da nune-nunen wasan kwaikwayo, ya kan jagoranci kungiyar wasan kwaikwayo zuwa larduna gomai na kasar Sin domin nune-nunen wasannin kwaikwayo da ya rubuta har tsawon shekaru fiye da 20.

A cikin wadannan shekaru fiye da 20, Li Yu ya sami fasahohi da yawa wajen rubuta wasannin kwaikwayo da zaben 'yan wasa da ba da jagora har da nune-nunen wasan kwaikwayo. Li Yu ya mai da hankali sosai kan wadannan abubuwa, ya kuma rubuta tunaninsa game da wannan aiki a cikin wani littafin da aka fi sani da suna "Tunanina na wasan kwaikwayo". A hankali a hankali ne ya rubuta wani cikakken tunanin rubutu da ba da jagora da nune-nunen wasan kwaikwayo. Bullowar wannan tunani ta alamantar da cewa tunanin wasan kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin ya fito yadda aka yi fata. Wannan tunanin wasan kwaikwayo ya yi kyakyawan tasiri sosai ga bunkasuwar wasan kwaikwayo da adabin kasar Sin.

Ba ma kawai Li Yu ya sami sakamako da yawa wajen rubuta wasannin kwaikwayo da tunanin wasan kwaikwayo ba, har ma ya fi suna sosai wajen rubuta tatsuniyoyi a cikin tarihin adabin kasar Sin. A cikin tatsuniyoyin da ya rubuta, Li Yu ya kan bayyana wasu ra'ayoyin da ba su dace da muhimman ra'ayoyin zaman al'ummar da yake ciki ba. Kamar misali, a da, a kan ce, idan wata mace ba ta da ilmi, to, sai ta kasance mai biyayya da kirki. A kan yi fatan mata su kasance jahilai. Amma a cikin tatsuniyoyin Li Yu, ya kan siffanta wasu mata wadanda suke da ilmi kuma suke da biyayya da kirki. Ya kuma sa kaimi ga mata da su yi koyi da fasahohi iri iri. Sabo da haka, a cikin tatsuniyoyin Li Yu, akwai tunanin zaman daidai wa daida a tsakanin maza da mata.

Bugu da kari kuma,, Li Yu ya bayyana ilminsa a fannoni daban-dabam ciki har da rubuta wakoki da tunanin yin sharhi kan tarihi da dai sauransu. Littafin da ya rubuta kuma ya fi muhimmanci shi ne "Tunanina na wasan kwaikwayo", inda ke hade da tunanin wasan kwaikwayo da ilmin dafa abinci da ilmin gine-gine da ilmin yin nishadin zama da na shuke-shuke. Har yanzu ana da sha'awar karanta wannan littafi. (Sanusi Chen)

Guan Hanqing, sanannen marubuci na wasan kwaikwayo na kasar Sin

Guan Hanqing na daular Yuan ta kasar Sin, wani marubuci na wasan kwaikwayo ne, kuma yana daya daga cikin marubuta wadanda suka fi suna a kan tarihin littafi da na wasan kwaikwayo na kasar Sin. Wasan kwaikwayo mai ban tausayi da aka fi sani da suna "Haushin Dou'e" da Guan Hanqing ya rubuta, ya yi suna sosai kuma a kan nune-nunen wannan wasan kwaikwayo a cikin shekaru fiye da 700 da suka wuce. Ban da wannan, an kuma juya wannan wasan kwaikwayo na "Haushin Dou'e" cikin harsunan waje da yawa. Yanzu wannan wasan kwaikwayo ya shahara sosai a duk fadin duniya.

Guan Hanqing ya yi zamani a karni na 13, wato a daular Yuan da kasar Sin take. Shi mutum ne mai karfin gwiwa kuma mai cike da imani da ilmi sosai. Guan Hanqing ya kware kan rera da rubuta wakoki da yin raye-raye da dai sauran fasahohi iri iri. Guan Hanqing ya dade yana zaune a babban birnin daular Yuan, kuma ya yi aiki a asibitin sarauta. Amma ba shi da sha'awar fasahar likitanci, yana da sha'awar rubuta wasannin kwaikwayo sosai. Lokacin da yake nan duniya, wani irin wasan kwaikwayo mai suna "Wasan Kwaikwayo na Za" ya yadu sosai a daular Yuan. Abubuwa irin wannan wasan kwaikwayo ba ma kawai sun raya tatsuniyoyin jama'a ba, har ma sun bayyana halin da jama'a suke ciki sosai. Ko jami'ai masu hannu da shuni ko masu arziki ko jama'ar farar hula dukkansu suna da sha'awar kallon irin wannan wasan kwaikwayo na Za. Amma Guan Hanqing ya rubuta wasannin kwaikwayo na Za ne ba don jami'ai masu hannu da shuni da masu arziki ba, amma sai don bayyana wahalolin da jama'a farar hula suke sha.

Guan Hanqing ya fahimci wahalolin da jama'a farar hula suke sha, ya kuma san maganganun da suke yi. A sa'i daya, yana da ilimi kwarai. Sabo da haka, ya iya sa wahalolin da jama'a farar hula suka sha a cikin wasan kwaikwayon da ya rubuta. A lokacin can, ba a girmama masu nune-nunen wasan kwaikwayo, amma Guan Hanqing ya kan tuntube su, har ya shugabanci ko ya zama wani dan wasan kwaikwayo a cikin wasannin kwaikwayo da ya rubuta. A cikin wata wakar da ya rubuta, lokacin da yake bayyana halinsa na karfin zuciya kuma mai gaba gadi, Guan Hanqing ya ce: "Kamar wani wake irin na tagulla da ba a iya gasa shi, ba a iya burge shi." Sabili da haka ne wasannin kwaikwayo da Guan Hanqing ya rubuta ba ma kawai sun bayyana halin zaman al'umma da ake ciki ba, har ma sun bayyana kwazon juyin juya halin musamman na farar hula. A cikin wasannin kwaikwayo da Guan Hanqing ya rubuta, jama'a farar hula suna kuka suna fama da wahalolin da suke sha. Amma a sa'i daya, suna bayyana halin jama'ar farar hula mai karfin zuciya da gaba gadi. Sanannen wasan kwaikwayo mai ban tausayi da aka fi sani da suna "Haushin Dou'e" wasan kwaikwayo ne da ke wakiltar tunaninsa.

Wannan wasan kwaikwayo mai ban tausayi na "Haushin Dou'e" ya bayyana wahaloli masu tsanani da wata yarinya mai suna Dou'e ta sha. A cikin shekaru daruruwa da suka wuce, a kan yaba wannan wasan kwaikwayo na "Haushin Dou'e", wato yana daya daga cikin wasannin kwaikwayo masu ban tausayi 10 na kasar Sin.

Lokacin da yake nan duniya, Guan Hanqing, shugaba ne na kungiyar wasan kwaikwayo. Duk wasannin kwaikwayo da ya rubuta ya kai 67, amma yanzu sai wasannin kwaikwayo 18 da ya rubuta suke nan duniya.

Guan Hanqing yana da muhimmin matsayi a tarihin wasannin kwaikwayo na kasar Sin, an kira shi "Kakan kaka na wasan kwaikwayo na Za na daular Yuan". Bugu da kari kuma, Guan Hanqing ya samu girmamawa sosai a tarihin fasahohin zane-zane da rubuce-rubuce na duniya, ana kiran shi "Shakespeare na Gabas" .

>>[Tatsuniyoyi]

Pu Songling da Tatsuniyoyinsa na Dila

A farkon karni na 18, wani sanannenn lattafi mai kunshe da tatsuniyoyin Dila ya bullo a nan kasar Sin. Pu Songling, wanda ya rubuta irin wadannan tatsuniyoyin al'ajabi ya rububa tatsuniyoyi masu dimbin yawa game da dila mai wayo.

Pu Songling(1640----1715), wani sannanen marubuci ne a daular Qing ta kasar Sin. Shi kuma wani malami ne wanda aka haife shi a wani gidan dan kasuwa. Lokacin da yake nan duniya, Pu Songling ya rubuta alamara da tatsuniyoyi da yawa. Littafin Gajerun Tatsuniyoyin Dila da ya rubuta ya fi sauran tatsuniyoyinsa dadin karatu.

An hada da tatsuniyoyi 431 a cikin wannan Littafin Gajerun Tatsuniyoyin Dila. Daga cikinsu, tatsuniya mafi gajeta tana da kalmomi metan ko dari 3 kawai, amma tatsuniya mafi tsawo tana da kalmomi dubbai. A cikin wannan littafi, lokacin da Pu Songling yake rubuta tatsuniyoyi game da dila, ya kai kara ga ladabi da tsarin jarrabawa na daular mulkin kama karya, ya kuma bayyana tunaninsa na 'yantattar da halin kowane mutum. Amma masu karatu sun fi son karanta wasu tatsuniyoyin dila da suke shafar soyayya. A cikin galibin tatsuniyoyin soyayya, a kan bayyana wani saurayi da wata dila sun yi kaunar juna. Wannan ya bayyana fatansu na fashewar ladabin zaman al'ummar mulkin kama karya.

Dilar da ke cikin wannan littafin tatsuniyoyin dila na Pu Songling ta bullo ne ta siffar wata yarinya mai kyaun gani. Wata tatsuniyar da aka fi sani da suna "Yarinya Cui" ta fi dadin karatu. A cikin wannan tatsuniya, Pu Songling ya rubuta bayani kan wata yarinya mai kyau mai suna yarinya Cui wadda take da kirki da hankali. Amma a karshen wannan tatsuniya ne marubuci ya nuna cewa, yarinya Cui wata dila ce. Domin mamarta ta taba neman gudun hijira a gida na Wang Taichang, ta canja siffarta ta zama wata yarinya ta samar wa iyalan Wang Taichang taimako.

A cikin tatsuniyar dila daban, wato "Auren 'Yar Dila", Pu Songling ya bayyana halin jin dadin auren 'yarsu yadda iyalan 'yar dila suke yi. Iyalan dila suna da kirki kuma suna da ladabi sosai. Sun shirya liyafa don mutane wadanda suka shiga zaman al'ummar dila ba zato ba tsammani. Wannan tatsuniya ta sa masu karatu da su manta da wahalolin da suke sha a cikin zaman al'ummarsu.

Ban da dila mai kyaun gani, a cikin Littafin Tatsuniyoyin Dila, akwai mummunar dila wadda ke da kirki. A cikin tatsuniya mai suna "Mummunar Dila", an ce, wata mummunar dila ta ga wani dalibi ba shi da arziki. Sabo da haka, wannan dila ta taimake shi da iyalansa. Amma bayan wannan dalibi ya sami kyakyawan tufafi da babban gida, ya gayyaci wani maye da ya kori wannan mummunar dila. Mummunar dilar tana fushi sosai domin wannan dalibi ya yi tubulci. Ba ma kawai ta komar da dukkan abubuwan da ta bai wa wannan dalibi ba, har ma ta sa al'ajabi da ya hore masa. Marubuci ya yi amfani da wannan tatsuniya don sukar wasu munanan halin dan Adam.

Sannan kuma, a cikin littafin mai suna "Tatsuniyoyin Dila", akwai dila mai kyaun gani amma maras tausayi. A cikin wata tatsuniyar da aka fi sani da suna "Fatan Zane-zane", an bayyana wata dila wadda ta sa wata fata a kan jikinta sai ta zama wata yarinya mai kyaun gani. Amma ta kasance a nan duniya ne domin shan jinin mutane. Ko shakka babu, a karshen tatsuniyar, an kashe wannan dila maras tausayi.

A takaice dai, a cikin Tatsuniyoyin Dila da Pu Songling ya rubuta, ya siffanta 'yan mata iri iri ta siffar diloli wadanda suke da kyakyawan halin da ba a iya ganinsu a kan jikin dan Adam ba.

Lattafin Tatsuniyoyin Dila wani sanannen littafi ne a kan tarihin adabin kasar Sin. A cikin shekaru fiye da 200 da suka wuce, an riga an juya shi zuwa harsuna fiye da ashirin, kuma ana buga shi a wurare da yawa a duk duniya. Ban da wannan, an kuma shirya wasu tatsuniyoyin wannan littafi da su zaman wasan kwaikwayo da za a iya ganinsu a talibijin ko a cinema. Ana jin sha'awar karanta wannan littafi sosai. (Sanusi Chen)

Tatsuniyoyin wani biri mai wayo da ake kira Sun Wukong

"Tatsuniyoyin wani biri mai wayo da ake kira Sun Wukong" tatsuniya ce da ta fi samun nasara a cikin adabin tarihin kasar Sin. A karni na 7, wato lokacin da kasar Sin take cikin daular Tang, wani dan Buddha mai martaba mai suna Xuan Zang da aka fi sani da suna dan Buddha na daular Tang, a takaice ana kiran shi Tang Sen (a cikin harshen Sinanci, ma'anar Sen ita ce dan Buddha), ya je kasar Indiya domin neman ilmin gasikya na addinin Buddha. Marubucin "Tatsuniyoyin wani biri mai wayo da ake kira Sun Wukong" ya danganta wannan labari ne ya rubuta abubuwa kan mutane 4, wato Tang Sen da almajiransa 3 a cikin wadannan tatsuniyoyi, inda suka kawar da wahaloli masu dimbin yawa suka ci nasarar neman ilmin gaskiya na addinin Buddha. Ban da wannan, marubuci ya kuma ci nasarar kirkiro wani biri mai wayo kuma maras fargaba da aka fi sani da suna Sun Wukong wanda ya kan yi yaki da mugayen mutane har kullum. A boye ne marubucin ya bayyana fatansa ga zaman al'ummar da yake ciki a cikin wannan littafin "Tatsuniyoyin wani biri mai wayo da ake kira Sun Wukong".

Marubucin wannan tatsuniya shi ne Wu Cheng'en, mutumi ne na garin Huai'an na lardin Jiangsu da ke gabashin kasar Sin. Wu Cheng'en mutum ne mai wayo kuma ya fi son koyon abubuwan da yake so. Ban da wannan, ya iya yin zane-zane da rubuta wakoki iri iri da wasan farar dara da bakar dara wato Weiqi na kasar Sin. Sannan kuma ya fi son ajiye zane-zanen da sannanun masu yin zane-zane suka kirkira. A sabili da haka ne, yaro Wu Cheng'en ya shahara sosai a garinsa domin gwanintarsa ta adabi, an kuma yaba masa kwarai. Amma Wu Cheng'en bai iya cimma burinsa na cin jarrabawar neman izinin zama jami'in fadar daular Tang ba kamar yadda yake fata. Sabo da haka, halin zaman rayuwarsa da yake ciki bai yi kyau ba, kuma ya kan yi fama da talauci sosai. Wu Cheng'en ya kara sanin zaman al'ummar tsarin mulkin kama karya, kuma ya kara fusata ga halin cin hanci da ake ciki a tsakanin jami'an daular tsarin mulkin kama karya. A cikin wata rubutacciyar wakar da ya rubuta ya bayyana ra'ayinsa cewa, dalilin da ya sa munanan abubuwa suka bullo a cikin zaman al'umma shi ne ba a nada mutane masu kirki da su zama jami'ai ba, kuma munanan mutane ne ke mulkin jama'a. Wu Cheng'en ya fi son yin sauye-sauye ga irin wannan zaman al'umma maras kyau, amma bai samu dama ko kadan ba. Babu sauran hanyar bayyana fatarsa da fushinsa da zai iya zaba, sai ya rubuta su a cikin "Tatsuniyoyin wani biri mai wayo da ake kira Sun Wukong". Kodayake Wu Cheng'en ya rubuta tatsuniya bayan ya tsufa, amma lokacin da yake yarantaka ne ya kan kai ziyara a wasu gidajen addinin Buddha tare da babansa. Da isowarsu a wani gidan addinin Buddha, babansa ya fada masa wasu tatsuniyoyi masu jawo hankalinsa. Ban da wannan, Wu Cheng'en ya fi son saurarar tatsuniyoyin ban sha'awa. Bayan ya kai shekaru 30 da haihuwa, ya riga ya san tatsuniyoyin ban sha'awa da yawa kuma ya fara tsara shirin rubuta tatsuniya da kansa. Lokacin da ya kai shekaru wajen 50 da haihuwa, ya rubuta farkon babobi 10 na "Tatsuniyoyin wani biri mai wayo da ake kira Sun Wukong". Amma daga baya ya jinkirtar da rubuta wannan tatsuniya har wasu shekaru sai ya yi murabus daga mukamin fadar daular Tang ya koma garinsa ya sake rubuta tatsuniyoyin kuma ya gama su.

Kowace tatsuniya ta "Tatsuniyoyin wani biri mai wayo da ake kira Sun Wukong" tatsuniya ce mai zaman kanta, amma an kuma iya hade su tare. A cikin wadannan tatsuniyoyi, Wu Cheng'en ya kirkiro al'jannu da dodanni da yawa wadanda suke wakiltar adalci da mugunta. A cikin duk tatsuniyoyin gaba daya, marubuci ya kirkiro wata duniya mai kunshe da kome da kome kamar yadda ake nan duniyar bil Adam, inda aka ga fadar sararin sama tana cikin halin ban girma, amma sarkin sararin sama mai martaba yana can kamar wani wawa bai iya bambanta mai kirki da maras kirki ba. A cikin fadar dodanni (the Hades), jami'an dodanni sun kiyaye juna kuma sun ci hanci kwarai. Marasa laifi ba su iya samun wurin daukaka karansu. Sabo da haka, a cikin wadannan tatsuniyoyi, babu bambanci a tsakanin fadar dodanni da fadar daular bil Adam. A cikin tatsuniyoyin, dodanni suna kashe mutane, suna cin mutane, suna cin hanci kuma suna neman mata har suna burge jama'ar da ke karkashin mulkinsu kamar yadda wasu jami'ai da masu hannu da shunni na daular bil Adam ke yi. Bugu da kari kuma, Wu Cheng'en ya kirkiro wani biri mai wayo da ake kiran shi Sun Wukong wanda yake kin jinin laifufuka kuma yake da karfin dabo sosai. A karkashin sandar zinariya ta Sun Wukong, Duk dodo wadanda suka fi mugunta sun sami bacin rai ko sun mutu ko an iya cafke su. A hakika dai, wannan ya bayyana fatan Wu Cheng'en na kawar da duk mugu daga zaman al'umma.

Littafin "Tatsuniyoyin wani biri mai wayo da ake kira Sun Wukong" da Wu Cheng'en ya rubuta ya yi tasiri sosai ga mutane bayan Wu Cheng'en. A cikin shekaru daruruwa da suka wuce, "Tatsuniyoyin wani biri mai wayo da ake kira Sun Wukong" sun zama tatsuniyoyin da yara suka fi kauna. An kuma sake shirya shi da ya zama fim da wasan kwaikwayo. (Sanusi Chen)

"Labarun kasashe 3" na kasar Sin

A nan kasar Sin sananniyar tatsuniyar gargajiya da aka fi sani da sunanta "Labarun kasashe 3", kowa ciki har da mata da yara sun san wannan littafi. A cikin karnukan da suka wuce, yake-yake da mutane kuma da yadda mutane masu wayo suke fama da juna da aka rubuta a cikin wannan littafi sun jawo hankulan kowane Basine. Ban da wannan kuma, a cikin shekaru masu dimbin yawa, masana da kwararru sun yi nazari kan wannan littafi.

Marubucin wannan littafi shi ne Luo Guanzhong ya yi zama a nan duniya a karni na 14. An haife shi a cikin wani gidan 'yan boko. Tun daga lokacin da yake karami, ya fi son karanta litattafai ciki har da wasu litattafan tarihi da tatsuniyoyi iri iri. Ilmin da ya samu daga cikin wadannan litattafai ya zama tushe mai kyau a gare shi lokacin da yake rubuta litattafansa bayan ya girma. Lokacin da Luo Guanzhong yake zama lokaci ne da ke hade da ra'ayoyin bambanci na kabilu daban-dabam da na bangarori daban-dabam. Dattijan kabilar Mongolia sun kafa daular Yuan inda suka sarrafa jama'ar kabilar Han da karfin tuwo. A sabili da haka, jama'ar kabilar Han, kabila mafi girma ce a nan kasar Sin, sun tashi sun fara yin fama da daular Yuan. A yawancin wuraren daular Yuan, dakarun sa kai sun bullo sun yi yaki da dakarun daular Yuan. Amma ba ma kawai dakarun sa kai sun yi yaki da dakarun daular Yuan ba, har ma sun hade da juna domin yunkurin mallake mulkin duk kasar Sin bayan an kau da daular Yuan. Saurayi Luo Guanzhong ma ya shiga cikin wata rundunar dakarun sa kai ya zama wani hafsa. Saurayi Luo Guanzhong yana da dogon buri sosai ya yi fata zai iya zama sarki kuma zai iya mulkin kasar Sin. Amma daga baya, dakarun sa kai da ke karkashin jagorancin Zhu Yuanzhang sun ci nasara sun kau da daular Yuan, kuma sun kafa daular Ming, inda Zhu Yuanzhang ya zama sarkin daular Ming. A sakamakon haka dai, Luo Guanzhong ya bar dogon burinsa ya koma gida ya fara rubuta tatsuniyoyi.

A cikin "Labarun kasashe 3", Luo Guanzhong ya bayyana wasu labarun tarihi da suka faru a cikin shekaru kusan dari 1 watau tun daga shekarar 184 zuwa shekarar 280. Luo Guanzhong ya nemi labarun tarihi da na ban sha'awa da tatsuniyoyn jama'a da dai makamatansu game da kasashe 3. Ya kuma hada da ra'ayin kashin kansa na siyasa da zamansa lokacin da yake cikin dakarun sa kai na manoma a cikin wannan littafi mai suna "Labarun kasashe 3", inda ya bayyana tarihin yadda kasashe 3, wadanda suka hada da kasar Wei da kasar Shu kuma da kasar Wu suka yi fama da juna a fannonin siyasa da soja.

A fannoni daban-dabam ne littafin "Labarun kasashe 3" ya bayyana fasahohin zane-zane. A cikin littafin, lokacin da yake rubuta labarun yake-yake da gwagwarmayar siyasa da aka yi wadanda suka jawo hankulan mutane sosai, marubuci Luo Guanzhong ya kirkiro matane masu dimbin yawa wadanda suke da halayen musamman nasu. A cikin littafin nan, marubuci ya kirkiro mutane fiye da dari 4. Daga cikinsu, marubuci ya mai da hankali sosai kan mutane fiye da gomai. Kamar misali, Cao Cao, sarkin kasar Wei mutum ne mai wayo kuma mai ha'inci wanda ya kware kan yin amfani da iko. Wani sanannen mutum mai wayo da Luo Guanzhong ya kirkiro a cikin littafin shi ne Zhu Geliang, mai ba da shawara kan aikin soja ga sarkin kasar Shu da janar Zhang Fei na kasar Shu, mutum ne mai kai tsaye kuma mai gaba gadi amma a wasu lokuta ya mai da hankali sosai kan wasu kananan abubuwa. Sanannen janar daban da Luo Guangzhong ya kirkiro a cikin littafin shi ne Zhou Yu na kasar Wu. Zhou Yu, mutum ne mai wayo amma kuma mai halin kifin rijiya. Dukkansu mutane ne da masu karanta wannan littafi suke kauna sosai.

Wannan Littafin "Labarun kasashe 3" da Luo Guanzhong ya rubuta ba ma kawai yana da daraja a fannin adabi ba, har ma ya bayyana abubuwa game da zaman al'ummar kama mulki ta kasar Sin ta da. Luo Guanzhong ya kuma rubuta fannoni daban-dabam na zaman al'umma din. Yanzu a nan kasar Sin kwararru da masana masu dimbin yawa suna nazari kan wannan sanannen littafi na "Labarun kasashe 3" daga fannonin tarihi da ilmin neman samun kwararru da ilmin soja da dai makamatansu.

Ba ma kawai Sinawa ne suke son karanta "Labarun kasashe 3" ba, har ma jama'ar sauran kasashen duniya suna son karanta wannan littafi. Yanzu an riga an juya shi zuwa harsunan waje da yawa, kuma za a iya samun wannan littafi a kasashe da yawa. An kira wannan littafi cewa, "Wani hakikanin nagartaccen littafi ne da jama'a fararen hula suke so". (Sanusi Chen)

Mafarki na Ginin Ja

A tsakanin lokuta na karni na 18 da ya gabata, kasar Sin ta samu bunkasuwa kwarai domin bullowar sarki Qian Long na daular Qing. Amma a wannan lokaci, an rubuta wata tatsuniya inda aka yi hangen nesa cewa, daular mulkin kama karya za ta shiga lokacinta na karshe. Wannan tatsuniya ita ce "Mafarki na Ginin Ja" da Cao Xueqin ya rubuta.

"Mafarki na Ginin Ja" nagartaciyyar tatsuniya ce daga cikin tatsuniyoyin da. Dalilin da ya sa Cao Xueqin ya iya rubuta irin wannan nagartaciyyar tatsuniya shi ne ba ma kawai shi mutum ne mai wayo kuma mai ilmi ba, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne ya taba zama a cikin wani gida mai arziki kuma mai hannu da shuni, amma daga baya gidansa ya lalace shi da iyalansa sun shiga mawuyacin hali. Kakan Cao Xueqin ya taba samun amincewa sosai daga wajen sarki Kangxi na daular Qing. Sabo da haka, yaro Cao Xueqin ya yi girma ne a cikin wani gida mai arziki kwarai. Amma daga baya, gidan Cao Xueqin ya sami sauye-sauye sosai, an kori kakansa daga mukaminsa. Yaro Cao Xueqin da iyalansa sun yi kaura daga birnin Beijing zuwa wani wurin da ke kudancin kasar Sin. Saurayi Cao Xueqin ya sha wahaloli sosai. Bayan ya tsufa, ya dawo nan birnin Beijing ya zauna a wani wurin da ke yammacin karkarar Beijing. A cikin mawuyacin hali, ya rubuta babi 80 na Mafarki na Ginin Ja. Amma bai gama dukkan tatsuniyar ba sai ya gamu da ciwo ya riga mu gidan gaskiya.

Suna daban na Mafarki na Ginin Ja shi ne "Tatsuniyar wani Dutse". Kafin Cao Xueqin ya gama farkon babi 80, abubuwan da ya rubuta sun riga sun fara yaduwa a tsakanin mutane da yawa. Bayan ya rasu, wani marubucin da aka fi sani da suna Gao E ya yi nazari kan tunanin Cao Xueqin ya ci gaba da rubuta sauran babi 40 ya gama dukkan Mafarki na Ginin Ja.

A cikin Mafarki na Ginin Ja, Cao Xueqin ya siffanta mutane masu dimbin yawa ciki har da iyalan sarki da masu hannu da shuni da dattijai da 'yan matan gidan da 'yan kasuwa da manoma da dai sauransu wadanda suke shafar kusan dukkan bangarori daban-dabam na al'ummar kasar Sin da zaman al'ummarsu.

Amma lokacin da yake siffanta duk al'ummar kasar Sin a cikin Mafarki na Ginin Ja, Cao Xueqin ya mai da hankali kan yadda ya siffanta gidaje 4 wadanda suka hada da gidan Jia da gidan Shi da gidan Wang da gidan Xue. Daga baya, ya sake mai da hankalinsa sosai kan yadda ya siffanta gidan Jia. Ban da wannan, Cao Xueqin ya sa mutane da yawa, musamman 'yan mata da yawa a cikin wata lambun shan iska mai suna Da Guanyuan inda suke zaune suna shan iska. Lokacin da yake siffanta wadannan 'yan mata, ya rubuta yadda suke yin musanye-musanye da sauran al'ummomin kasar Sin domin bayyana al'ummar duk kasar Sin, kuma yadda gidan Jia ya fara lalacewa a hankali a hankali.

Cao Xueqin ya ci nasarar siffanta mutane iri iri a cikin Mafarkin Ginin Ja, inda yawan mutanen da Cao Xueqin ya siffanta ya kai fiye da dari 7. Daga cikinsu, muhimman mutane sun kai fiye da dari 1. Bugu da kari kuma, Cao Xueqin ya kware sosai kan bayyana tunanin mata, musamman tunanin 'yan mata. Cao Xueqin ya ji tausayinsu, musamman ya fahimci soyayya da suke nema.

Mafarki na Ginin Ja yana da daraja kwarai, musamman harsuna da tsarinsa da mutanen da aka siffanta sun isa matsayin koli a cikin tarihin adabin kasar Sin. (Sanusi Chen)

>>[Waka mai ma'anar tarihi]

Waka mai ma'anar tarihi ta kabilar Tibet: Sarki Ge Saer

"Wakokin yaba wa sarki Ge Saer" waka mai ma'anar tarihi ce da ita kadai take nan duniya yanzu. Har yanzu, mawakan fararren hula fiye da dari 1 suna waka a jihar Tibet mai cin gashin kanta da jiha mai cin gashin kanta ta kabilar Mongolia da lardin Qinghai na kasar Sin, inda suke yaba wa babban sakamakon da jarumi sarki Ge Saer ya samu.

Wakokin yaba wa sarki Ge Saer sun fara bullowa ne tun shekaru dari 2 ko dari 3 kafin haihuwar Annabi Isa zuwa karni na 6 da ya gabata. A cikin shekaru kusan dubu 1, mawakan fararren hula sun rera wakoki kuma sun koyar da zuriyoyi bayansu da baka. Lokacin da suke waka, sun kuma kara sabbin abubuwa a cikin wakoki da sabbin kalmomi. Ya zuwa farkon karni na 20 da ya gabata, an kusan gama dukkan wakokin yaba wa sarki Ge Saer, kuma an yada su a yankunan kabilar Tibet sosai.

A cikin wakokin yaba wa sarki Ge Saer, an bayyana wata tatsuniya kamar haka: yau da shekaru aru aru da suka wuce, bala'u daga indallahi da hadarurruka sun kasance a ko'ina a yankunan kabilar Tibet. Dodanni iri iri ma su kan kashe dan Adam kuma su kan kawo wa dan Adam matsaloli iri iri. Babban dan Buddha Guanshiying wanda ke tauyin dan Adam ya roki shugaban 'yan Buddha Amitabha da ya aika da wani dan sarkin sararin sama da ya taimaki dan Adam kuma ya kubutar da su daga wahaloli. Sabo da haka, Amitabha ya tura Tuibagewa zuwa yankunan kabilar Tibet da ya zama sarkin 'yan kabilar Tibet, wato Ge Saer. Nauyin da aka dora wa sarki Ge Saer shi ne yin yaki da dodanni iri iri, da taimakawa wadanda ba su da karfi da kuma kawo wa jama'a alheri. Sabo da haka, a cikin bakin mawaka, sarki Ge Saer ya zama wani nagartaccen jarumi.

Bayan an haife shi sarki Ge Saer, an wulakanta shi sau da yawa, amma domin yana da karfi kuma Allah ke kare shi, dodanni ba su iya kashe shi ba, amma shi ne ya kashe dodanni. Bayan an haife shi, sarki Ge Saer ya fara yin yaki da dodanni domin jama'a. Lokacin da yake da shakeru 5 da haihuwa, Ge Saer da mahaifansa sun kaura zuwa bakin Rawayen kogi. A lokacin da yake da shekaru 12 da haihuwa, ya ci nasara a gun gasar dawaki, kuma ya sami sarautar sarki. Tun daga wannan lokaci ne, Gesaer ya fara bayyana karfinsa ya yi yaki da mugayen mutane da dodanni. Bayan ya ci dukkan nasarori, Ge Saer da mahaifarsa da matarsa sun koma gidan Gaskiya. An kuma gama "Wakokin yaba wa sarki Ge Saer".

Wakokin yaba wa sarki Ge Saer suna dogo sosai. Wadannan wakoki suna kunshe da babi fiye da 120 kuma suna cike da layuyuka fiye da miliyan 1 da bakaku miliyan 20. Sabo da haka, wannan waka mafi doguwa ce a nan duniya. Yawan layuyuka da bakaku na wakokin sarki Ge Saer ya fi jimlolin layuyuka da bakaku na sauran wakoki masu ma'anar tarihi guda 5 na kasashen Duniya, wato waka mai ma'anar tarihi ta Gilgamesh ta tsohuwar daular Babylon da Iliad da ODYSSEY na kasar Greece da Ramayana da Mahabharata na kasar Indiya da yawa.

Wakokin yaba wa sarki Ge Saer suna kunshe da wakokin jama'a da tatsuniyoyi iri iri, inda aka siffanta mutane iri iri. Ko jarumai ko mugayen sarkuna, ko maza ko mata, ko tsofaffi ko samari, aka siffanta su sosai. Kowane mutum yana da halin musamman nasa. Ban da wannan kuma, an kuma yi amfani da Karin Maganganu na kabilar Tibet masu dimbin yawa.

Wakokin yaba wa sarki Ge Saer wani kayan tarihi ne na al'adu mai daraja kwarai. Gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan yadda aka shirya kuma aka yi aikin juyawa har aka wallafa shi. A shekarar 2002, an shirya wani gaggarumin bikin tunawa da cikon shekaru dubu 1 da bullowar wakokin yaba wa sarki Ge Saer. Yanzu a jami'o'i fiye da 10 da wasu hukumomi, masana da yawa suna nazari kan wadannan wakoki. (Sanusi Chen)

Waka mai ma'anar tarihi ta kabilar Mongolia: Jangur

Lokacin da yake da shekaru 2 da haihuwa kawai ya zama maraya, amma a loakcion da yake da shekaru 3 da haihuwa ya fara shiga filayen yaki. A lokacin da ya cika shekaru 7, ya zama wani jarumin da ya shahara a duk fadin kasar Sin. Wadannan muhimman abubuwa ne na waka mai ma'anar tarihi ta kabilar Monglia mai suna Jangur

A wajen karni na 15 zuwa farkon rabin karni na 17 ne wakar Jangur ta fara bullowa a shiyyar Weilate ta kabilar Mongolia. Weilate, sunan wata tsohuwar kabila ce ta kabilar Mongolia. Ma'anar Weilate ita ce kabilar gandun daji da ke zama a zirin dutsen Altair da ke arewa maso yammacin kasar Sin.

Jarumi Jangur da aka siffanta a cikin wakar ya zama maraya a shekaru 2 da haihuwa kawai bayan Manggusi, wani abokin gaba ne mai ban tsoro kuma mugu ya kai hari kan gidan Jangur, ya kuma kashe iyayensa. Sabo da haka, lokacin da ya kai shekaru 3 da haihuwa kawai, jariri Jangur ya hau kan dokinsa mai suna Arenzai ya shiga filayen yaki yana neman ramuwa domin iyayensa. Da ya kai shekaru 7 da haihuwa, Jangur ya ci nasara kwarai ya zama wani sanannen jarumi a cikin kabilar Mongolia. Sabili da haka, jama'ar da ke zama a shiyyar Baomuba sun zabe shi da ya zama sarkinsu da aka fi sani da suna Khan. Amma babban abokin gabansa Mangusi ba ya son ba da kansa, ya kan nemi damar kai wa shiyyar Baomuba hari. Babu sauran hanyar da zai iya zaba, sai ya shugabanci janar janar masu jarumtaka guda 35 da sojoji dubu 8 domin yin yaki da Mangusi kuma sun ci nasara sun tabbatar da zaman lafiya a shiyyar Baomuba. A sakamakon haka, Jangur ya yi suna a kasashe 44. Bayan ya sha wahalolin da yake-yake suka haddasa masa, da gwanintarsa ne Jangur ya kafa wata kasa mai inganci. Jama'ar da ke zama a wannan kasar Baomuba suna nan duniya har abada kamar kullum shekaru 25 ne da haihuwa. An yi zama a kasarsa inda ke cike da murya kamar suke cikin lokacin bazara a duk shekara. A kasarsa babu lokacin kankara, a duk shekara ana jin kamshin lokacin bazara. A kasarsa babu lokacin zafi sai kamshin fasalin kaka ake ji.

A cikin wannan waka mai ma'anar tarihi, an rubuta cewa "Babu lokacin sanyi da na kankara, a duk shekara ana jin kamshin lokacin bazara. Kuma babu zafi babu mutuwa, kowa saurayi ne. Ban da wadannan, a kasar Baomuba, babu talauci sai arziki, babu marayu da zawarawa sai bunkasuwa da cigaba, babu yaki da rikici sai alheri da lafiya. Namun daji sun cika duwatsu, shanu da tumaki da dawaki da rakuma suna yawo a kan filayen ciyaye. Iska maras karfi tana shafa fuskarmu, ruwan sama kadan ke jika gonaki."

A matsayin doguwar waka mai ma'anar tarihi inda aka kirkiro jarumai da yawa, a cikin wakar Jangur, an sami babban cigaba wajen kirkiro mutane iri iri. Kamar misali, lokacin da ake rubutabayani kan sarki Jangur, har sau da yawa ne aka rubuta wahalolin da ya sha lokacin da yake yarantaka da tarihinsa na yin yake-yake. Jangur da aka kirkiro ya zama wani jarumi mai hankali kuma mai jarumtaka kwarai ya sami goyon baya sosai daga wajen jama'arsa kuma ya yi gwagwarmaya kwarai domin neman 'yancin kan Baomuba. Lokacin da ake siffanta babban jarumi Hongguer, a cikin wannan waka, ya kasance cike da jikuwa ne aka fadi cewa, jarumi Hongguer yana da "Abubuwa 99 masu isa yabo na kabilar Mongolia" wadanda suka bayyana dukkan abubuwa masu isa yabo na jarumai na filayen ciyaye. Hongguer jarumi ne mai biyaya ga jama'a kuma ya ki abokan gaba kwarai.

Lokacin da ake siffanta abubuwa masu ban sha'awa na filayen ciyaye, a cikin wakar Jangur, da harshen kabilar Mongolia ne aka siffanta abubuwa masu ban sha'awa na dutsen Altair da zamantakewar tsohuwar kabilar Weilate da sauran abubuwa masu ban sha'awa na kabilar Mongolia. Ban da wannan, an kuma rubuta wakokin Jangur da harsunan jama'ar kabilar Weilate da wakokin fatan alheri da irin na nuna yabo da tatsuniyoyi iri iri. Kamar misali, lokacin da ake siffanta labari kan yadda Jangur take neman aure, da sau da yawa ne an rubuta cewa, janar Jangur ya ki amincewa da 'yan mata 49 wadanda suka je wurinsa domin neman aure. Daga karshe dai, ya yi aure da gimbiya Agaishabudela wadda take da shekaru 16 da haihuwa kawai.

Wakar Jangur ta zama daya daga cikin matsayin koli da kabilar Mongolia ta kai wajen raya adabin gargajiya, ta kuma ba da gudummawa sosai ga adabin zuriyoyi masu zuwa. Yanzu wannan waka mai ma'anar tarihi daya ce daga cikin ayyukan al'adu da gwamnatin kasar Sin ta fi mai da hankali kan kiyaye su. (Sanusi Chen)

"Manas"

Bambancin da ke kasancewa a tsakanin rubutacciyar waka mai ma'anar tarihi ta "Manas" ta kabilar Kirgiz ta kasar Sin da rubutacciyar waka mai ma'anar tarihi ta "Labarun sarki Gesar" na kabilar Tibet da rubutacciyar waka mai ma'anar tarihi ta "Jiang Ge'er" na kabilar Mongolia ta kasar Sin shi ne a cikin wakar Manas, tauraro ba guda daya kawai ba, har ma suna kunshe da iyalan zuriyoyi 8.

"Manas" waka ce mai ma'anar tarihi ta kabilar Kirgiz ta kasar Sin inda ake yaba wa jarumai. Kabilar Kirgiz wadda ke zama a jihar Xinjiang mai cin gashin kanta a arewa maso yammacin kasar Sin tana daya daga cikin tsofaffin kananan kabilu wadanda suke da dogon tarihi a nan kasar Sin. Tun daga karni na 9 zuwa karni na 10 an fara kirkiro wakokin Manas. Daga baya a hankali a hankali ne mawaka masu wayo na kabilar Kirgiz sun yi ta rera kuma kara yawansu daya bayan daya inda suka bayyana basirar kabilar Kirgiz. A sakamakon haka, yanzu dai littafin wakar Manas ya riga ya zama wani sanannen littafin da ke bayyana halin musamman na kabilar Kirgiz kwarai. An ce, marubuta na wakokin Manas sun rubuta da rera wakokin ne ba domin suna da hankali ba, amma domin Allah ne ya ba su wayo. Bayan mawaka wadanda suka rera wakokin Manas sun farka, ba zato ba tsammani ne sun sami karfin rera wakoki har layuka fiye da miliyan 1. Har yanzu ba wanda ya amince da wannan sai 'yan kabilar Kirgiz.

Na ji an ce, Manas wai wani sanannen jarumi ne kuma shugaba na kabilar Kirgiz wanda yake nuna karfi da jarumtaka da hankali na kabilar. A cikin wakokin Manas an bayyana labaru yadda jarumi Manas da iyalansa na zuriyoyi 8 suka shugabanci jama'ar kabilar Kirgiz da suka yi gwagwarmayar da sauran kabilu wadanda suka kai hari ga yankin kabilar Kirgiz domin neman 'yancin kai. An raba wadannan wakokin Manas har babi 8 kuma an sa sunan Manas kan wadannan wakokin. Kowane babi inda aka bayyana labaru game da jaruman zuriya 1 yana zaman kansa, amma an kuma hada da su tare. Wakokin Manas suna da layuka fiye da dubu 210 da bakakku fiye da miliyan 20.

Halayen musamman na wakokin Manas sun hada da mutanen da aka kirkiro kuma da halin da wadannan mutane ke ciki. A cikin wakokin Manas, ban da malam Manas da jikokinsa, akwai sauran mutane fiye da dari 1 wadanda suke da halayen musamman nasu. Wadannan mutane sun hada da dattijai masu nuna basira da aminan Manas wadandan suke nuna wa Manas goyon baya kuma da abokan gaba na Manas ciki har da sarki Karmark da dodanni da yawa. A cikin wakokin Manas an rubuta filayen yake-yake gomai, ba ma kawai an rubuta makamai iri iri ba, har ma an bayyana ire-iren launin dawakin jarumai fiye da 30.

Jama'a masu dimbin yawa sun rubuta kuma sun rera wakokin Manas. Sabo da haka, marubuta da mawaka wadanda suka kirkiro wakokin Manas da rera su sun kai fiye da dubu 10. A jihar Xinjiang mai cin gashin kanta, ana kiran wadannan mutane Manaski. A cikin shekaru fiye da dubu 1, kafin Yusuf Mamayi ya bullo, ba wanda ya iya rera dukkan wakokin Manas, balle a rubuta cikakkun wakokin Manas.

Baba Jusuf Mamayi, mai shekaru 86 da haihuwa yanzu ya shahara kuma an kira shi "mawaki Homer wanda har yanzu yake nan duniya". Baba Jusuf Mamayi ya ba da kai ga aikin nema da rera wakokin Manas bayan ya yi girma har yanzu. A shekarar 1940, lokacin da yake hutu, malam Mamayi ya rera wakokin Manas a dare na kwanaki 7. Sabili da haka ya yi suna sosai. Tun daga shekarar 1984 zuwa shekarar 1995, bi da bi ne baba Jusuf Mamayi ya rera dukkan wakokin Manas na babi 18 da aka buga su a cikin litattafai 8. A cikin wakokin tarihi 3 na kasar Sin, Manas ta zama waka daya da mutum daya kadai ya rera.

Yanzu an riga an wallafa wakokin Manas da aka juya su zuwa harshen Sinanci. Ban da wannan, an kuma juya wasu muhimman babi zuwa harsunan Turai da Faransa da Jamus da Japan. A ran 17 ga watan Fabrairu na shekarar nan, an mika wa baba Jusuf lambar nuna yabon ba da gudummawa.

A matsayin masanin adabin jama'ar kabilar Kirgiz, wakokin Manas sun shahara sosai a cikin jama'ar kabilar Kirgiz. Jama'ar kabilar Kirgiz suna ganin cewa, jarumi Manas bai mutu ba har yanzu. A sa'i daya, domin wakokin Manas sun samu girmamawa a cikin tarihin adabin kasar Sin da na kasashen duniya, M.D.D ta taba sa shekarar 1995 da ta zama "shekerar kasa da kasa ta wakokin Manas". (Sanusi Chen)