logo

HAUSA

Babi24: Shahararrun Mawaka

2020-10-30 10:07:16 CRI

Babi24:Shahararrun Mawaka

[Masu rubutu wakoki da kide kide]

Liu Wenjin

Liu Wenjin shi ne wani shahararren mai tsara kade-kade na kasar Sin, wanda ya sauke karatunsa daga jami'ar kade-kade ta kasar Sin a shekarar 1961.Ya taba zama shugaban kungiyar kade-kade na gargajiya ta kasar Sin da babban sufeto na fasaha, da shugaban gidan wasan opera da raye-raye na kasar Sin, yanzu shi ne fasaha darekta na gidan nan. Kuma shi ne dan majalisar makada ta kasar Sin da mataimakin shugaban kwamitin tsara kade-kade da zaunannen dan majalisar kiyaye ikon tsara kade-kade ta kasar Sin, mataimakin shugaban kungiyar philharmonic orchestra ta gargajiya ta kasar Sin ; sai a shekarar 2001 aka gayyace shi don ya zama shehun malamin jami'ar kade-kaden gargajiya na cikin babbar jami'ar kasa ta Korea ta Kudu.

Yayin da Liu Wenjin ke cikin samartaka wato lokacin da ya ke dalibta cikin makaranta, ya sami lakabi " dalibi nagari" da jami'ar kade-kade ta kasar Sin ta ba shi. Kade-kadensa na farko da ya tsara yayin da yake cikin jami'ar su ne : " kade-kaden bayyana al'amuran arewacin lardin Henan" da " kade-kaden kagawa na kwarin Sanmen" wadnada aka yaba cewa, su ne kade-kaden 'yan uwa da suka shahara wajen hada kayan kidan gargajiya Ehu da piano gu daya. A shekarar 1993, an zabi "kade-kaden bayyana alk'amuran arewacin lardin Henan" da ya zama nagarin kidan gargajiya na Sinawa cikin karni na 20"; A shekarar 1999, an zabi " kade-kaden kagawa na kwatin Sanmen" cikin littafin

musamman domin tunawa da ranar cika shekaru 50 na ranar bikin kasa, mai suna " nagartattu na fasahar stagecraft da fasahar sinima da TV na sabuwar kasar Sin ". A watan Mayu na shekarar 1982 , karo na farko an nuna concerto na Ehu mai suna " abubuwan da aka yi tunani a kai na babbar ganuwa " a gun biki mai suna Yanayin bazarar Shanghai, an ci nasara, wanda kuma ya sami mindar farko a gun zama na 3 na kade-kaden duk kasa, har cikin shekara da shekaru, bisa salo daban daban an sha nuna

kade-kaden " abubuwan da aka yi tunani na babbar ganuwa " a larduna da binane da yawa, ciki har da Hongkong da Macao da Taiwan na duk kasa, da kasashe sama da goma na Turai da Amurka da Asia, duk ya sami maraba sosai.

Cikin shekaru da sama da 40 da suka gabat, Liu Wenjin ya tsara ko yin gyara tarin kade-kaden gargajiya, wakoki har da kade-kade sama da daruruka na sauran iri. Ban da haka kuma, akwai kade-kade na raye-raye da wasan wake-wake da sinima da wasan kwaikwayo na TV. Liu Wenjin ya kuma shiga aikin tsara kade-kade na " wakar juyin juya hali ta kasar Sin" wato manyan wasannin kade-kade da raye-raye da wakoki。

A da'irar kade-kaden gargajiya, an yaba Liu Wenjin cewa mai tsara kidan da ke da halin wakilta na bayan Liu Tienhau", a watan Satumba na shekarar 1989, kungiyar Orchestra ta Sin ta Hongkong

ta shirya taron nuna kade-kade mai lakabi " daga Liu Tienhua zuwa Liu Wenjin "

Wata kungiyar binciken kade-kaden kasar Sin na Arewacin Amurka mai suna " Chese Music "ta nuna cewa, Liu Wenjin shi ne daya daga cikin masu tsara kade-kade wadanda babban yankin kasar Sin ke fin jin karfin girgiza nasa, kungiyar ta sha buga bayanai da shrhi don nazarin kade-kaden gargajiya da ya tsara.

Bisa gayyatar da aka yi masa har sau da yawa Liu Wenjin ya je kasashe gomai na Turai da naAmurka da na Asia, da Hongkong da Madau da Taiwan na kasar Sin. Banda haka, Sau da yawa ya zama madugun kungiyar kade-kaden Sin da kade-kaden kabilar Sin da kungiyar kade-kaden gargajiya ta Hongkong da kasar Singapore da na Taiwan domin taron nuna kade-kade musamman na kade-kaden shi kansa. Shi da masu tsara kade-kade na kasar Japan da na Korea ta Kudu sun kafa kungiyar kade-kaden Asaia tare.

Ma'aikatar al'adu ta shigad da sunan Liu Wenjin cikin 'yan fasaha masu ba da sakamakon fiffiko, shi kuma ya karbi takardar shaida girmamamwa da majalisar gudanarwa ta bayar masa da alawas musanman da gwamnatin kasa ta ba da.

Gao Weijie

Gao Weijie wani shahararen makadi ne na kasar Sin wanda ya sauke karatu daga jami'ar koyon kade-kade da wake-wake ta Sichun a shkarar 1960. Ya zama shugaban sashen tsara kade-kade na jami'ar koyon kade –kade da wake-wake ta Sichun, da shugaban sashen tsara kade-kade na jami'ar koyon kade-kade da wake-wake ta kasa da mai edita na mujjala mai suna " kade-kaden jama'a ".

A shekarar 1983, Gao Weijie ya kafa wata kungiyar kade-kade ta farko cikin kasar Sin mai suna " kungiyar nazarin akin tsara kade-kade ta masu shirya kade-kade" wadda shi ne shugaban kungiyar. Yanzu Gao Weijie shahe malami ne na jami'ar koyon kade-kade da wake-wake ta kasar Sin, mai shugabancin bincike da aka gayyatar shi musanman cikin cibiyar binciken salon ilimi na kade-kade ta jami'ar koyon kade-kade da wake-wake ta kasar Sin, bakon shehu malami na jami'ar Yan Bian, da bakon shehu malami na jami'ar koyon kade-kade da wake-wake ta babbar jami'ar kasar Amurka, mai edita na mujjala mai suna " kade-kade na Sin" da " Salon ilimi na kade-kade na kasar Sin".

Shi bisa matsayinsa na mai tsara kade-kade, an nuna kade-kadansa cikin gida da waje, da daba'asu , har ya sami kindoji cikin gida da waje. Muhamman kade-kaden da ya tsara suna hade da: symphony na

bayyana "abubuwan da suka faru a da cikin makiyaya", da kade-kade na orchestra ta gargajiya " dina ta cikin fadar daular Shu": da kade-kade na piano " dare na yanayin kaka": da kayan kada mai suna Ehu guda biyu da orchestra " alama game da farin doki" da kade-kaden gargajiya na cikin daki " saurara muryar sarewa a wani dare na yanayin bazara a cikin birnin Lou" da kida na sarewa iri biyu "cika mafarki" da kade-kaden gargajiya na cikin daki " Shao I" da "shao II" , kidan violin da piano " hanya " da kade-kade na wasan rawa " filaye" da kade-kade na raye-raye da waka " da sauransu.

Shi bisa mastsayinsa na kalamin koyarwa, Gao Weijie ya yi horar tarin kwararru na fanin kade-kade cikin aikinsa na koyarwa har shekaru dama da 40, wasu dalibansa sun sami mindoji cikin gasar masu tsara kade-kade na gida da na waje, wasu masu fiffiko sun zama masu tsara kade-kade da wasu ke sanin sunayensu ko 'yan hasashe na kade-kade ko malaman koyarwa. Bisa gayyatar da aka yi masa, Gao Weijir ya je jihohi ko kasashe kamar : kasar New Zealand da kasar Korea ta Kudu da kasar Faransa da kasar Britania da kasar Amurka da kasar Netherlands da kasar Mexico da Taiwan inda ya halarci taron nazarin hasashe da bikin kade-kade da yin lacca ko ya zama juji cikin gasa kan kade-kade ko wakokin da aka nuna, bisa gayyatar da aka yi masa, ya taba zama juji kan masu samun mindoji kan kade-kaden da aka tsara na karo na 4 da 6 da 8.

ya sami alawas na musanman da majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta ba

da. An shigad da sunansa cikin wani "kamus shahararrun kade-kade

da makada na gamayyar kasa da kasa" na Cambridge na Britania.

Fu Lin

Fu Lin mai tsara wakoki ne wanda ya rubuta kalamomi na wakar kuma ya tsara kidan waka. An haife shi ne a ran 17 ga watan Janairu na shekarar 1946 cikin birnin Fujin na lardin Helongjiang na arewa kaso gabas na kasar Sin, a shekarar 1968 ya sauke karatu daga sashen kade-kade na jami'ar wasan fasaha na rundunar soja, ya taba zama makadi , da mataimakin shugaba da darektan fasaha na kungiyar wake-wake da raye-raye na ofishin siyasa na rundunar sojan ruwa, a sa'an nan kuma ya dauki nauyin aikin dan kungiyar makada ta kasar Sin da mataimakin darekta na kwamitin samun bunkasuwa na kungiyar kade-kade, da mataimakin shugaban kungiyar light music ta kasar Sin.

A cikin shekaru sama da 40, Fulin ya yi aikin fasaha ya tsara wakoki masu dinbim yawa wadanda ke samun sha'awar tarin jama'a, kamarsu

" rana ta fi ja, shugaba Mao shi ne aka fi nuna kauna" da " Sumba daga Mama" da " karamin kakaki" da "Ni karama ce" da " soyayya ta tsohon lambu" da "mu hadu a lokacin Drgan" da " duk kauna ce" da "snow na garina" da "budurwa ta Loulan" da " ana zuwa sama taki kan taki" da "wakar jama'a ta tsibiri" da "samaniya mai launin shudi ruwan teku ma mai launin shudi ne" da "halin zuciya na gari" da sauran wakoki sama da dubu. Amma ya ce bai ji wata waka ta sa ya gamsu ba, ya yi sahihi da nuna cewa, wakar da jama'a ke gamsuwa da son saurara wadda ita ce na gamsar da ita. Amma, wasu wakokin da na ji gamsuwa amma ba su

karbuwa ba, a kan wannan, ya yi murmushi tare da cewa, na saba da haka. Cikin 'yan shekarun da suka shige na tsara wakoki har dubai, akan yi haka, muddin mu zabi akin fasaha, to wajibi ne a saba da haka.

Fu Lin ya wallafa wakoki wajen dari da ke cikin sinima ko wasan kwaikwiyo, kamar "tashin ambaliyar ruwa da batsewarta" da " soyayya daga yara" da "tsaunin Kunlun" da "Zhu De" da " Liu Shaoqi" da "sauyawar yanayin Wuxu " da " a matakan uba da dansa" da "Liu Hulan ". A cikin gasar mawaki samari da gidan TV na kasar Sin ya shirya, Fu Lin ya zama juji, da juji cikin gasar kade-kade na MTV, bayan haka bisa sunan ma'aikatar al'adu, Fu Lin ya je kasashen waje don zama juji cikin gasar kade-kade na gamayyar kasa da kasa, Ya kuma shirya wata mujjala mai suna " babban bangare na matsanancin son wakoki" wadda ya zama babban edita . Yanzu wallafa sabbin wakoki ko kade-kade sun zama wani kashi da ke cikin aikinsa, ya fi mai da hankalinsa don nazarin hasashe na kade-kade da horad da wasu samari cikin bangaren kade-kade.

A shekarar 1986 cikin birnin Harbin da ke arewa masu gabas na kasar Sin, Fu Lin ya yi wani taron nuna kade-kade nasa, haka kuma a shekarar 1987 a birnin Xi An kuma ya yi wani irin taron daban. A shekarar 2001, shiri mai suna " fad of music and draw " na gidan CCTV ya shirya wani taron kade-kade musamman domin nuna kade-kade na Fu Lin.

Wang Luobin

Wang Luobin ( daga shekarar 1913 zuwa 1996), shahararen mai yada wakokin jama'a na yammacin kasa, wanda aka ba shi lakabi sarkin wakokin zamani na kasar Sin. An haifi Wang Luobin a watan Janairu na shekarar 1913 a birnin Beijing. A shekarar 1919 ya shiga cikin makarantar firamare, lokacin nan lokacin harkar sabon al'adu ne, saboda haka Wang Luobin ya koyi wasu wakokin makaranta, kuma ya soma saurarar wasu kade-kade da wakoki na kasashen yamma da na kasar Japan. A shekarar 1924 Wang Luobin ya shiga cikin wata makarantar midil da wata majami'a ta kafa cikin gundumar Tongzhou da ke kusa da birnin Beijing, cikin kungiyar mawaka na majami'a ya soma sanin daidaito tsakanin kida da waka na kasashen yamma, har ma ya soma sanin kidan gambara. A shekarar 1931 Wang Luobin ya shiga cikin sashen wasannin fasaha na makarantar malaman koyarwa ta Beijing bayan ya shiga jarabawa ya ci, Madam Hrowath,yar Rasha ta zama malama wajen koyar da shi kan rera wakoki da piano, tun bayan nan dai, Wang Luobin aka soma ba shi ilimin da ya kamata kan kade-kade.

Sai a shekarar 1937, Wang Luobin ya shiga kungiyar yin hidima ta filayen yaki na arewa maso yamma wadda shaharariyar mawallafa Ding Ling ke shugabanta, tare da kungiyar, Wang Luobin ya je filayen yaki. A cikin zaman yaki na lokacin can, Wang Luobin ya tsara wakoki kamar "Wakar wanke tufaffi" da " 'yan uwan kauyuka su je filayen yaki" da "wakar

tashar ruwa Fengling". A yanayin bazara na shekarar 1938, bisa umurnin da shugabanninsu suka yi wa kungiyar yin hidima ta filayen yaki, an tura mawallafa Xiao Jun da mai wallafa wakoki Sai Ke da mai tsara kade-kade Wang Luobin da Zhu Nanxing don su je jihar Xingjiang wajen yin ayyuka. A nahiyar yamma, Wang Luobin ya saurari tarin wakokin jama'a, Karin wakoki na faranta rai kuma mai dadin ji, sun sa Wang Luobin ya zama bugagge saboda wakokin jama'a masu dadin ji. Wani direba na kabilar U'gur ya rera masa wata wakar jama'a ta Turfan mai suna "Gari Daban", sai nan da nan karin waka ya shiga zuciyarsa, ya rubuta kidan wakar, kuma ya gayyaci wani da ya fassara kalamomin da ke cikin wakar, ya yi gyara ga wakar, kuma ta nada sunan wakar " wakar direban kura", wakar da ya yi gyara, karinta na cike da ban dariya, ta haka wakar ta kara dadin ji. Wannan dai ya zama sauye-sauye cikin zamansa na tsara wakoki, kuma wanda shi ne wakar kananan kabilu na farko da Wang Luobin ya tattara da yin gyara a kai.

Bayan haka, inda Wang Luobin ya sa kafa, sai ya yi amfani da duk dama don tattara wakokin jama'a, bayan ya sanya kokari shekara da shekaru, ya tattara da yin gyara ko ya rubuta tarin wakokin jama'ar na kabilu daban daban wadanda ke da dadin ji har da darajar yin bincike, kamar wakar kabilar U'gur "A bude zanin rufen ka ta amarya", " Kidan rawa Kasger" da "kidan rawa na zamartaka", "Alamuhan" , "Rabin wata ta fito" wato

wata wakar soyayya da " Yilala", "Wakar galabaita" ta kabilar Kazak da "Ina jiranka ya zuwa gobe" da "Wani mai tunasheka na kwanta cikin <>" da "Mayila" da "Hayakin girki na lokacin yamma" da " Dutar da Maliya" da " Magariba" na wakokin jama'a na kabilar Kazak. Wadannan kara ya yi kama da ruwa ke malala, sai har zuwa yanzu ana rera wakokin nan.

Bisa harsashin tattara wakokin jama'a, Wang Luobin ya kuma yi gyara ga tarin wakokin jama'a, kamar waka mai suna "A wuri mai nisa" da akererawa shekara da shekaru, wadda ta zama wata shaharariyar waka, bayan Wang Luobin ya yi gyara bisa wata wakar jama'ar Kazak mai suna " Goshi fari fat". Wakar " A wuri mai nisa" ta karabu cikin lardin Gansu da na Qinghai, bayan haka ba da dadewa ba, wakar ta karbu a cikin wuraren duk kasa, har cikin shekaru gomai, ta sami maraba sosai daga wajen tarin jama'a.

Lei Zhenbang

Lei Zhenbang ( daga shekarar 1916—shekarar 1997 ), wani shahararren mai tsara wake-wake da kade-kade na sinima na kasar Sin wanda kuma shi ne mai tsara kade-kade na matsayin kasa, ya taba zama darektan kungiyar masu tsara kade-kade ta kasar Sin da darektan kungiyar sinima ta kasar Sin da mataimakin shugaban kungiyar sinima da kade-kade ta kasar Sin, da dan majalisa ta 6 ta ba da shawara kan harkokin siyasa ta duk kasar Sin. An haifi Lei Zhenbang a watan Mayu na shekarar 1916 a birnin Beijing, shi dan kabilar Man ne. Gidansa yana cikin zaman wadata, shi ya sa lokacin da yake karami, ya san wasan opera. Da ya ke shekaru 7 ko 8 ya iya rera wasu guntayen wakokin opera, har ya iya goge da wani kayan kida mai suna E Hu wajen nuna wasan opera da wakoki.

Sai a watan Janairu na shekarar 1931, Lai Zhenbang ya je kasar Japan don yin dalibta. A Tokyo ya shiga kos na share fage da ke karkashin babbar makarantar kade-kade ta Japan. Bayan shigowarsa bai kai rabin shekara ba, Lei Zhenbang ya kammala duk karatunsa cikin kos na share fage, sai shugaban babbar makarantar ya nuna yarda da ya yi tsalle zuwa aji na baya, sai a shekara ta gaba, ya zama dalibin mai neman digiri na farko cikin sashen koyon ilimin tsara kade-kade.

A shekarar 1943 Lei Zhenbang ya komo kasar mahaifa, bi da bi ne ya

zama malamin koyar da kade-kade cikin makarantar midil ta mata ta birnin Beiping da makarantar midil ta mata mai suna Huizhong.

Bayan samun nasarar yakin kin harin Japan, a lokacinsa na bayan aiki ya kafa wata kungiyar sumphony orchestra ba ta sana'a ba wadda ke hade da mutane sama da 50.

Lei Zhanbang ya gyara wani kidan tsohon zamanin Sin mai suna "waka mai ban tausayi" don ya zama kidan orchestra domin kungiyar symphony orchestra ta nuna wanda ya zama kida na farkon da aka nuna a fili da Lei Zhenbang ya tsara.

A watan Yuni na shekarar 1949, Lei Zhenbang ya shiga kungiyar kade-kaden sinima ta kasar Sin wadda a ciki sana'arsa tsara kade-kade, daga lokacin, ya soma aiki domin sinima.

A watan Afrilu na shekarar 1955 an shigad da Lei Zhenbang cikin ma'aikatar Changchun ta sinima studio inda ya dauki aikin tsara kade-kade, daga lokacin nan aikinsa na tsara kade-kade ya shiga wani sabon mataki. Cikin shekaru sama da 30, ya wallafa wakoki sama da dari domin sinima. Ya tsaya kan shiga cikin zaman jama'a da koyi daga wajen 'yan fasaha na jama'a, ya tsara tarin wakoki ko kade- kade masu dadin ji kuma ke cike da halayen musamman na wuri-wuri da na kabilu wadanda kuma ke bayyana zaman rayuwar jama'a, wadannan suka zama halin fasahar nasa ta musamman. Kamar kide-kiden da ya tsara domin sinima mai suna "furanni guda 5" da " bako ya bakunci duwatsun kankara" da " budurwa ta kabilar Jingpo" da " wakar soyayya ta Lusheng", wadanda ke da halin musanman na kade-kade.

A shekarar 1960, cikin mindar Bai Hua na zagaye na biyu, kidan da ya tsara domin sinima mai suna " budurwa ta 3 mai suna Lui" ya sami mindar kida mafi kyau. Bayan haka kade-kaden da ya tsara domin sinima mai suna "bako ya bakunci duwatsun kankara" da " JI Hongchan" da " samari ma'aikata", bi da bi ne suka sami mindar kida mafi kyau na mindar " kananan furanni dari" na zagaye na daya da na biyu da ma'aikatar Changchun sinima studio ta shirya a shekara ta 1964 da shekara ta 1980.

Cikin 'yan shekarun baya, kade-kaden da Lei Zhenbang ya tsara domin sinima suna hada da: "Dong Chunrui" da " furen Malan ya nufa" da " wakar soyayya ta kayan kidan Lusheng" da "kyakyawan furanni da wata" da " furanni 5 " da " Jin Yuji" da " Daji da Babanta" da " 'yan mata ta 3 mai suna Lui " da " sake samun rayuwa" da " bako ya bakunci duwatsun kankara" da " budurwa ta kabilar Jingpo" da " yaki da ambaliyar ruwa" da " mutm mai jan hali" da " mai laifin lekan asiri" da "Ji Hongchan" da "samari ma'aikata" da " wakar soyayya a kwari", da wasan kwaikwayon TV na jere mai suna " zuri'a 4 ke zaman tare". Galiban kade-kaden da ya tsara sun karabu sosai da sosai cikin duk kasa baki daya.

Zhang Li

Mai tsara wakoki Zhang Li asalinsa birnin Dalian, an haifi shi a ran 17 ga watan Oktoba na shekarar 1932. a shekarar 1945 ya shiga cikin makarantar midil na farko na birnin Dalian, sai a shekarar 1948 ya shiga cikin sashen wasan kwaikwayo na jami'ar LuYi na arewa maso gabas don yin nazari kan adabi, sai a shekarar 1950 ya sauke karatu, ya yi aikin wallafe-wallafe cikin jam'iar, a shekarar 1955 ya je sashen adabi na jami'ar malakan koyarwa ta Beiing inda ya zama malami, a shekarar 1957 an canza aikinsa a ofishin tsara kade-kade cikin gidan wasannin opera da na raye-raye na lardin Jilin, kuma a shekarar 1970 an shigad da shi cikin ofishin tsara kide-kide na kungiyar kayan kidan gargajiya na Orchestra ta Sin, ya zama mai wallafe-wallafe na matsayi na kasa.

A cikin sekaru sama da 50 da Zhang Li ya kama aikin wallafe-wallafe, ya tsara wakoki masu dadin ji da faranta ran mutane, kamarsu "inuwar shige" da "lokacin shan wahala da jin farin ciki" da "iska mai karfi daga Asia" da " ni da kasa mahaifata" da " Mutanen da aka rabu da su cikin dogon lokaci " da duwatsu da koguna ke sauyawa" wadanda suka sami maraba daga wajn jama'a, kuma wadannan wakoki sun karabu sosai cikin tarin jama'a.

Zhang Li mai tsara wakoki, masu aikin tsara wakoki da kadekade suna kiransa da cewa, mai cike da imani, amma ya kware ne bayan ya yi balagagge, domin kafin ya kware ya sha wahalhalu da dama. A shekaru 60 na karni na 20, wasu shahararrun masu tsara wakoki sun taba musunta wakokin da Zhang Li ya wallafa, amma shi ba ma kawai bai rasa karfin zuciya ba, maimakon haka, ya nuna karfin hali ya yi nazain tsara wakoki kwarai. Daga baya tarin jama'a sun nuna kauna ga wakokinsa, ya sami nasara. Wakokin da ya tsara nada halin musamman, ke bayyana sabon hali na zaman rayuwa, kamar a sa an game kome na sabuwa ce.

Yanzu Zhang Li ke da shekaru sama da 70 na haihuwa, amma ana shan aiki, kodayake ya yi ciwon aya sosai, amma ya tsaya kan tsara wakoki da shiga cikin taron kara wa juna ilimi, da ba da jagora ga masu tsara wakoki ba na sana'a ba, yana nan yana ba da taimakonsa domin sha'anin wasanin fasaha na kasar Sin.

Tian Han

Tian Han shi ya zama uban wasan kwaikwayo na kasar Sin, kuma mai yin gyara kan wasan opera a gaba, wanda mutane suke kiransa da cewa, Guan Hanqing na zamanin yanzu. Ya wallafa wasan kwaikwayo da wasan opera, har da sinima, wakoki da wakoki na cikin sinama. Saboda haka, Tian Han ya zama shahararren mai wallafa wasannin kwaikwayo, shi kuma ya yi suna a matsayi mai rubuta wakoki.

Tian Han dan birnin Changsha na lardin Hunan na kasar Sin, a ran 12 ga watan Mais na shekarar 1898, an haifi shi cikin wani gidan manoma. Tun bayan wata harkar dalibai ta ran 4 ga watan Mayu, ya shiga ckin wani tashe na sabuwar al'ada wanda ke nuna adawa ga masu nuna isa da mulkin gargajiya. A shekaru 20 na zamanin can ya kara wata kungiya mai suna "Nanguo She" ta ba da munimmin taimako cikin tarihin al'adu na zamani cikin kasar Sin. A lokacin can, wasan kwaikwayo sama da goma da Tien Han ya wallafa sun bude wani sabon shafi na wasan kwaikwayo na kasar Sin cikin zamanin da. Alal misali wasan kwaikwayo mai suna " wani dare a gidan sayar da Kofi" da daren da aka kama damisa" da "mutuwar wata shaharariyar mace".A shekarar 1932, bayan Tian Han ya shiga cikin jam'iyyar kwaminis ta Sin, sai ya soma tashe na biyu cikin ayyukansa na wallafa wasannin kwaikwayo, ya zama daya daga cikin mawallafi na wasan kwaikwayo da sinima masu ci gaba, kamarsu " mata uku 'yan gaye" da "hasken halin uwa" da " 'yan uwa jarumi", ban da wassannin kwaikwayo, ya kuma wallafa wasu rubuce-rubucen sinima. Wani wasan opera mai suna " Guguwar kogin Yantse" da ke bayyana zaman rayuwa da fama da ma'aikatan tshar jiragen ruwa na Shanghai, wadda ta zama daya daga cikin wasannin opera da ke bayyana tunanin juya-juyin hali na tun da wuri cikin kasar Sin. Tian Han ya kuma wallafa wakoki da yawa domin wasan kwaikwayo ko sinima wadanda suka tada karfin zuciyar mutane kuma suka ba da tasiri ga zamantakewar al'umma, kamar " March of the Volunteers" da "wakar sauke karatu". Daga ciki, Mr. Nie Er matsarin kidan wakoki ya tsara kida domin waka mai suna " March of the Volunteers", haka ya sa wakar ta tada kaimin jama'a dubbai. Har wakar ta karbu a kudu da arewa na kogin Yantse na kasar Sin, daga lokacin yakin kin harin Japan zuwa yakin yantar da duk kasa, wakar ta himmatad da 'yan uwa na kabilar Sin don su sanya matukarfama domin kasar mahaifa. Bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, an tsaida cewa, wakar mai suna " March of the Volunteers" ta zama taken mulkin kasar Sin.

Bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, Tian Han ya sha aikin shugabanci, amma ya kuma yi wallafe-wallafe sosai. Ya wallafa wasan kwaikwayo mai suna "Guan Hanqing" wadda a ciki ya bayyana yabonsa ga mutum na tsohon zamanin da saboda ya yi bajinta domin rashin adalci da aka yi wa wata mace mai suna Dou E . Bai yi tsammani ba, ya wallafa waniwasan kwaikwayo mai suna " Xie Yaohuan" domin yin kira saboda hukunci maras adalci da aka yanke mata, sai "tarkace mutane 4" ya yi

Masa zalunci har ya mutu, haka ya zama wani hukunci maras adalci fiye da kima wanda azabar da ya sha ta fi mutum na tsohon zamanin da Guan Hanqing. A shekarar 1968, saboda azaba har ba iyaka da aka yi masa, ya yi rashin lafiya, daga baya babu wanda ya san inda yake. Bai taba yin sallama da iyalinsa ba, bai rubuta kowace wasiya ba, har ba a san ina gawarsa take ba. Sai a ran 20 ga watan Afrilu na shekarar 1979, a gun bikin binne tokarsa, wani abokinsa mai suna Lin Muohan ya sa wani littafin wasan kwaikwayo da Tian Han ya wallafa mai suna Guan Hanqing, da wani garmaho na waka mai suna "March of the Volunteers", wani tabaro da wani alkalami cikin akwatin tokar. Ta haka an yi gyara ga hukunci maras adalci da aka yi wa Tian Han har lokaci na tsawon shekaru 10.

A duk rayuwarsa, Tian Han ya wallafa abubuwa masu dinbin yawa, bisa hasashen da aka yi ba sosai ba, ya wallafa wasannin kwaikwayo sama da 60, da wasannin opera fiye da 20, sinimomin guda 10 ko fiye, wakokin da aka same su wajen dari 9 da 'yan doriya, ban da wadannan, da akwai kalamomin wakoki da adabi da kagaggen labari da sauran littafin ya fassara. A cikin wani littfin da aka daba'a, mai suna "bayanai na Tian Han" ba a tattara duk bayaninsa ba, amma an kebe zuwa littafi guda 16. Babu wanda zai iya halakar da sakamakonsa kan bangaren wasan kwaikwayo da wakoki na kasar Sin, an rubuta sunansa a kan littafi na tarihin wasan kwaikwayo da wakoki na zamani na kusa-kusa na kasar Sin har abada.

Xu Peidong

An haifi Xu Peidong ran 1 ga watan Janairu na shekarar 1954 a birnin Dalian. A shekarar 1970 ya shiga jarabawa, sai aka shigad da shi cikin kungiyar wake-wake da raye-raye ta yankin soja na FuZhou, inda ya zauna kan kujerar girmmawa na mai goge violoncello, madugun makadi da tsara kide-kide. Ya ci jarabawar shiga sashen tsara kade-kade na jami'ar koyon ilmin kade-kade ta Sin a shekarar 1976. A shekarar 1985 an canza aikinsa zuwa gidan wasan opera na Sin don ya zama mai tsara kade-kade kuma madugu. Ya zama mai tsara kade-kade na matsayi na farko na kasa, kuma mataimakin shugaban kungiyar light music ta kasar Sin. A shekarar 1992 da 1996 an zabe shi da ya zama " masu tsara wakoki 10 na duk kasa", kuma ya sami mindar " sakamakon tsara kade-kade na shekaru 20 na dandamalin wakoki na kasar Sin" da "mindar sakamakon dandamalin wakoki masu yaduwa ta kasar Sin" .

Xu Peidong ya tsara wakoki masu dinbim yawa, ciki akwai wasan opera kamar "motsin rai na Janar" da wasan raye-raye mai suna " fure na wani dabino na Sin" da sinima mai suna " samari ??? " da wasan kwaikwayo na TV mai suna " shinge, mata da kore" mai babi 3, "kanakan kasashe na daular Zhou ta gabas" da " daular sarki Yongzheng". Da wakoki da yawa, kamarsu " ina kaunar garinmu" da " wata ya cika a ran 16 ba rab 15 ba" da "inuwar shige" da wakar soyayya mai suna " lokacin shan

wahala da jin farin ciki" da " iska mai karfi daga Asia" da "ba za yi rayuwa kamar haka ba" da " kaddara ba kura ta rijiya ba" da " kidan gari da soyayyar gari " da " budurwa mai son yaji" da " kishin kasata Sin" da "kasar Sin ke samun fata har abada " da " wanda ke samun goyon baya daga jama'a yana kan karagar mulki".

Qiao Yu

Qiao Yu wani shahararren mai tsara kalamomin wakoki na kasar Sin.

An haife shi a shekarar 1927, asalinsa birnin Jining na lardin Shangdong ne. Tsohon sunansa Qing Bao. Shi wani shahararren mai tsara kalamomin wakoki ne, wanda aka ba shi taken "sarkin kalamomin wakoki"

A shekarar 1946, ya shiga cikin kwalejin wasannin fasaha ta jami'ar Beifang. Yayin da yake cikin jami'ar ya tsara kalamomi cikin wasanin kwaikwayo guda 3 .

Bayan kafuwar sabuwar kasar Sin a shekarar 1949, ya kama aikin tsara kalamomi cikin wasan kwaikwayo na jami'ar koyon wasanin kwaikwayo ta kasar Sin, da kungiyar masu wasan kwaikwayo ta kasar Sin,da ofishin tsara kalamomin wasan kwaikwayo na ma'aikatar adabi.

Bayan shekarar 1977 Qiao Yu ya taba hawa kujerar mataimakin shuaban gidan wasan opera da wake-wake na kasar Sin, da shugaban gidan, da darekta na 4 na kungiyarmasu wasan kwaikwayo ta kasar Sin da shugaban kungiyar adabin kade-kade ta kasar Sin, dan kwamitin gudanarwa na cibiyar musanye-musanyen al'adu tare da gamayyar kasa da kasa. Da mamban majalisa ta 8 ta ba da shawara kan harkokin siyasa na duk kasar Sin.

Wallafe-wallafen Qiao Yu sun yi daidai da lokuta na zamani, a shekaru 50

na karnin da ya shige, ya wallafa wasannin, kamarsu " budurwa ta uku Liu" da " yara masu shiga juyin-juya hali" da wakoki "kasata mahaifa" da wakar furen peony" da " kowa ke yaba kyakkyawan lardin Shanxi" da " wakar yara da ke tuka kwale-kwale" wadanda suka zama wakokin da kowa da kowa na duk kasa ya sani. A shekaru 80, wato na bayan da kasar Sin ta tafiyar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, Qiao Yu ya wallafa wasu wakokin da ke bayyana halayen zuciyar jama'ar kasar Sin da ke cikin sabon lokaci, kamar su "furen rose da ke cikin zuciya" da "ba za a manta daren yau ba" da " tunawa" da "labarum dodani" da "mala'ika ta tsaunin Wu" da "kyakkyawan lokaci na fadowar rana" da " nuna kaunar kabilar Sin" da "wakar yaba kasar mahaifa", saboda haka wallafe-wallafensa sun karbu sosai, wadanda suka zama shahararrun wakokin da mutane kan rera.

Wakokin da Qiao Yu ya wallafa da ke da ma'anar wakilci su ne: "kasata mahaifa" da "Kowa na yaba kyakkyawan lardin Shanxi" da " wakar yara da ke tuka kwale-kwale" da " furen rose da ke cikin zuciya" da "ba za a manta daren yau ba" da nua kaunar kabilar Sin".

Nie Er

Nie Er, an haifio shi a ran 14 ga watan Fabrairu na shekarar 1912, a birnin Kunming na lardin Yunnan na kasar Sin. A shekarar 1918 aka shigad da shi cikin makarantar firamare wadda ke karkashin makarantar horon malamai, cikin makarantar firamare Nie Er ya yi fiffiko kan karatu kuma ya nuna kaunarsa wajen kade-kade, a lokaci na bayan darusa, yakan koyi daga wajen 'yan makada na gargajiya kan busa sarewa, da sauran kayayyakin kade-kade na kabilun kasar Sin, saboda haka ne ya san kade-kade na gargajiya. A shekarar 1925 ya shiga wani hadadden makaantar midil na farko na lardin Yun Nan bayan ya shiga jarabawa. Tun lokacin Nie Er ya fara samun tasiri daga wajen litattafai masu ci gaba da waka mai suna "The International" wakar juyin-juya hali . A shekarar 1927 ya shiga jarabawa kuma ya samu nasarar shiga cikin makaranta ta farko ta horon malamai ta lardin Yun Nan, tare da abokan kade-kade suka kafa wani rukunin kade-kade mai suna "Jiu Jiu", yakan halarci harkokin nuna kade-kade da wasan kwaikwayo a cikin makarantar ko waje da ita, kuma daga lokacin ya soma koyon "Violin" da "Piano".

A watan Nuwanba na shekarar 1930, Nie Er ya shiga cikin " babbar kungiyar yin adawa da masu nuna isa". A watan Maris na shekarar 1932, ya zama

mai gogen violin da ke cikin rukunin wasan opera mai suna Ming Yue, kuma ya koyi buga piano da nazarin ilmin daidaito tsakanin kade da waka da dabarun tsara kide-kide. A watan Afrilu na shekarar 1932 ya sami damar sanin Malam Tien Han mawallafi wansan kwaikwayo da wakoki wanda ke da tunanin ci gaba, daga nan dai Nie Er ya kulla cudanya tare da da'irar fasaha na masu tunanin ci gaba. Saboda ya kulla zumunci da yin hadin kai tare da Malam Tien Han, wadanda ke ba da babban tasiri ga sakamakon fasahar Nie Er. Sai a watan Augusta na shekarar nan, Nie Er ya je birnin Beiping wato tsohon birnin Beijing, inda ya himmantu ya shiga cikin harkokin nuna wasannin fasaha na rukunin wasan opera da na makada wadanda ke da tunanin ci gaba , kuma ya koyi fasahar goge violin daga wajen malamin kasar waje mai suna Tonov. Sai a watan Nuwanba na shekarar, ya sake komawa birnin Shanghai.

Bayan Nie Er ya koma birnin Shanghai ba da dadewa ba, ya shiga kamfanin sinima mai suna Lianhau inda ya sami aikin yi. Ya nuna matukar himma da zuciya daya ya shiga ayyuka na kade-kade da wasan kwaikwayo da sinima wadanda ke bayyana tunanin ci gaba, ya himmantu kan wallafe-wallafe da yin sharhohi. A kolacin kuma ya shiga kungiyar kade-kade mai suna " reshen yin abota da Tarayyar Soviet ", ya yi jagorar kafa " kungiyar binciken kade-kade masu sabon salo na

kasar Sin", bayan haka ya shiga cikin kungiyar kade-kade na masu

wallafe-wallafe na tunanin ci gaba na Sin.

A shekarar 1933, Nie Er a karo na farko ya nuna kwararrensa wajen tsara wakoki, wakar da ya tsara kamar "wakar mahaka " da " wakar sayar da jaridu" duk sun jawo hankulan masu sauraro. A watan Afrilu na shekarar 1934, Nie Er ya shiga kamfanin faifan kide-kide mai suna Baidai, shi da Malam Ren Guang sun shugabancin sashen kade-kade tare, sun shirya dauka wasu wakoki masu ci gaba cikin faifan. Shekarar nan ta zama shekararsa ta kade-kade, ya wallafa wakoka masu shahara da yawa kamar "wakar babbar hanya" , "wakar daukar karatu" " Sabbin mata" "wakar ma'aikatan tashar jiragen ruwa", "wakar ci gaba" , da kide-kide na al'adar kabilu, kamar "kade-kade da raye-rayen macijin zinariya", dukansu ya tsara cikin shekarar nan. A shekara mai zuwa wato 1935, ya tsara wasu wakoki masu dadin ji, da wata waka mai suna "March of the Volunteers" wadda ta zama wakar taken kasa bayan kafuwar sabuwar kasar Sin.

A ran 18 ga watan Afrilu na shekarar 1935, Nie Er ya je kasar Japan, inda ya bincike kade-kade da wasan kwaikwayo, da sinima, ya kuma bayyana wa da'irar fasaha ta kasar Japan sabon ci gaban da aka samu kan kade-kade na kasar Sin, ya kuma kara karfi wajen nazari harshen waje da

ilmin kide-kide. Sai a ran 17 na watan Yuli, ya rasu yayin da ya ke iyo a kasar Japan, a lokacin yana da shekaru 23 da haihuwa.

Nie Er ya yi shekaru biyu yana dukufa kan tsara kade-kade, amma ya tsara wakoki ko kide-kide da jimlarsu ta kai 20 , domin sinima guda 8 da wasan kwaikwayo 3 har da wasan dandamali, da wasu wakoki 15 da kide-kiden 4 da ya yi gyara bisa kade-kaden da ke yaduwa cikin jama'a, da kida biyu na firitsi guda biyu , wato adadin ayyuka ya kai 41.

Liu Tianhua

Liu Tianhua shi ne mashahurin mai tsara kide-kide , mai ba da ilmin wake-wake da kide-kide kuma babban malamin kide-kide da wake-wake na gargajiyar kasar Sin.

An haife shi a shekarar 1895 a wani gidan masu fasaha na gundumar Jiangyin da ke lardin Jiangsu na kasar Sin. Liu Tianhua da wansa da kannensa su ne shahararrun 'yanuwa uku a tarihin al'adun kasar Sin. Wansa mai suna Liu Bannong ya shiga harkar yin al'adu na sabon salo a shekarun da yake da kurciya, sa'anan kuma ya zama shahararren mawallafi, marubutan wakoki kuma masanin harshen sinanci na kasar Sin. Bisa tasirin irin gidan nan ne, Mr Liu Tianhua ya soma koyon ilmin busa kayayyakin kidan da ake cewa "Brasswind" na kasashen yamma a lokacin da yake karatu a makarantar sakandare. A shekarar 1912, ya shiga wata kungiyar kide-kide ta sana'ar musamman ta birnin Shanghai, daga nan ne ya soma koyon hasashen wake-wake da kide-kide da ilmin kada "Piano" da "Violin" da ilmin "Brasswind". A shekarar 1914 ya koma garinsa, ya shiga makarantar sakandare don koyar da ilmin wake-wake da kide-kide.

A shekarar 1915, Liu Tianhua ya yi bakin ciki da rasuwar mahaifinsa, sai ya kasance cikin bakin ciki sosai, amma bisa halin nan da yake ciki, ya wallafa wani kida mai suna 'Bing Zhong Yin" wato ana rera wakoki a lokacin kamuwa da ciwo ta hanyar yin amfani da kayan kidan da ake kira "Erhu", wannan ne karo na farko da ya tsara kidan don bayyana fushi da ya yi ga rashin adalci da aka samu a zamantakewar al'umma, kuma daga nan ne ya soma kama hanyar wallafa kide-kide da wake-wake.

Don koyon wake-wake da kide-kide na gargajiyar kasar Sin, Mr Liu Tianhua ya ziyarci jama'a masu fasaha a ko'ina, ya koyi yadda ake kada kayayyakin kida kamar su "Erhu" da "Pipa" da "Gu Qin" wato kayan kidan da aka yi da tsirkiyoyi guda 7 da sauransu daga wajen shahararun jama'a masu wake-wake da kide-kide, Mr Liu Tianhua ya yi niyyar sabunta wake-wake da kide-kide na gargajiyar kasar Sin, musamman ne ya mai da hankali ga sabunta kayan kidan "Erhu" wanda ke da matsayi a gun jama'a da kuma raya shi, daga wajen neman danyun kayayyaki da kera shi da kuma dabarar kada shi, ya sabunta su daga dukkan fannoni, sa'anan ya daga karfinsa na bayyanuwa, kuma ya tsara wasu kide-kide domin wannan, saboda haka ana shigar da "Erhu" cikin darasin kolejojin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide da kuma kada shi a dakalin nuna wasanni shi kadai.

A cikin shekaru 10 da suka wuce, wato daga shekarar 1922 zuwa 1933, Liu Tianhua ya zama Farfeser na jami'ar Beijing don koyar da ilmin kada kayayyakin kida kamar su 'Erhu" da "Pipa" da "Violin". Yawancin wake-wake da kide-kide da ya tsara a wannan lokaci ne. Ya tsara su daga cikin wake-wake da kide-kiden da ya tsara, ban da bayyanuwar halin da ya kasance cikin bakin ciki, yawancinsu suna bayyana yadda yake kaunar hallittu da kuma yadda yake tunawa da abubuwan da suka faru a garinsa, duk wadannan sun bayyana abubuwa masu kyau a cikin halin nutsuwa. A wani fanni, Mr Liu Tianhua ya ci gadon dabarar tsara kide-kide na gargajiyar kasar Sin, a wani fanni daban kuma, ya koyi dabarun tsara kide-kide na kasashen yamma ta yadda kide-kiden da ya tsara suke da wata sabuwar siga. Ya samar da wata sabuwar hanya ga bunkasuwar wake-wake da kide-kide na gargajiyar kasar Sin, saboda haka wake-wake da kide-kiden da ya tsara na da halayen musamman.

Liu Tianhua ya soma aikin ba da ilmin wake-wake da kide-kide a lokacin da ya cika shekaru 17 da haihuwa, bi da bi ne ya yi aikin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide a makarantar firamare da makarantar sakandare, shi ya sa ya tattara fasahohin koyarwa da yawa. Wajen aikin koyarwa, ya koyi fasahohi da darasi da tsofaffi suka samu, ya kuma koyi dabarar koyar da ilmin kayayyakin kidan kasashen yamma daga wajen mutanen kasashen yamma, ya yi aikin koyarwa ta hanyar haduwar "Etude" wato kide-kiden da aka yi gwajin kada su da sauran kide-kide a hankali hankali, saboda haka ya kafa tushen tsarin aikin koyar da wake-wake da kide-kide na gargajiyar kasar Sin.

A watan Mayu na shekarar 1932 , ya kamu da ciwo, kuma a ran 8 ga watan Yuni ya mutu, yawan shekarunsa na haihuwa ya kai 38 .

Wake-wake da kide-kiden da Mr Liu Tianhua ya tsara sun hada da "Bing Zhong Yin", wato rera wakoki a lokacin kamuwa da ciwo, da wata wakar da ake cewa "Bei Ge" wato waka mai nuna bakin ciki da wakar da ake cewa "Ku Men Zhi Ou" wato rera wakoki don bayyana bakin ciki da wata daban da ake cewa "Guang Ming Xing" wato tafiya zuwa makoma mai kyau da "Liang Xiao" wato dare mai kyau da " Kong Shan Niao Yu" wato kukan tsuntsaye a tsaunukan da ke kasancewa cikin halin nutsuwa da sauran wake-wake da kide-kide guda hudu ta hanyar yin amfani da kayan kidan da ake cewa "erhu" tare da kide-kiden "PiPa" guda uku ciki har da kidan da ke da lakabi "Ge Wu Yin", wato jagorancin da ake yi ga wake-wake da raye-raye.(Halima)

[Madugan makada]

Yan Lingkun

Yan Lingkun, shi ne mataimakin kungiyar makadi ta Sin, darektan kungiyar madugi na 'yan amshi kuma madugu na kungiyar kade-kade ta kasar Sin. An haife shi ne a shekarar 1923 a birnin Wuhan. Tun a shekarar 1938 ,wato cikin yunkurin rera wakoki na ceton kasa da kin harar Japan, ya soma madugunsa. Sai a shekarar 1940, sau na farko ya zama madugu na kungiyar wasan fasaha ta yara don nuna babbar wakar amshi ta Rawayen kogi. A shekarar 1942 ya ci jarabawa ya shiga sashen mazarin hasashen tsara kade-kade na jami'ar kade-kade ta kasa, wacce a ciki ya zama dalibi na shehu malami Jiang Dinxian, kuma ya koyi dabarar madugu daga wajen Malam Wu Bochao. Bayan da ya sauke karatu a shekarar 1947, ya je jami'ar kade-kaden kabilar Sin ta Hongkong, inda ya dukufa kan hasashen tsara kade-kade da koyarwa kan aikin maduganci.

Bayan kafuwar sabuwar kasar Sin a shekarar 1949, Yan Liangkun malamine cikin jami'ar kade-kade ta kasar Sin kuma madugu ne na 'yan amshi cikin kungiyar aiki ta samari ta jami'ar, a shekarar 1952 ya zama madugu 'yan amshi cikin kungiyar wake-wake da raye-raye ta kasa. A shekarar 1954 ya sami damar zuwa tsohuwar Tarayyar Soviet don kara ilimi, shi dalibi ne na samun digiri na biyu cikin sashen madugi na jami'ar kade-kade ta Tchaikovsky, inda muhimmin dai ya nazari hanyar madugi na philharmonic da na 'yan amshi, Anosov da Sokolov su ne malamansa.

Bayan ya dawo gida a shekarar 1958, ya zama madugu na kungiyar 'yan amshi ta kasa. A shekarar 1959 domin mika kyauta saboda ranar bikin kasa, ya zama madugu wajen nuna "Beethoven Symphony N0.9". A shekarar 1961 ya yi madugun taro na karo na farko na kade-kaden wakoki 'yan amshi . A shekarar 1964 yayin da aka nuna wakokin tarihi da kade-kade da raye-raye mai suna "Gabas ta yi ja ", shi ne madugu na farko na rera wakoki na mutane dubu. An shirya bikin duniya na farko na wakoki na 'yan amshi a shekarar 1979, ya yi jagoar kungiyar wakokin 'yan amshi ta kasa zuwa kasar Philippines don halarci bikin. A shekarar 1982 shi madugu ne na kungiyar wakokin 'yan amshi ta cikin kungiyar kade-kade ta kasa , don nuna wasan wakokin yammacin turai a gun taron kade-kade na'yan amshi.

A shekarar 1983, kwamitin tunawa da Kodaly na kasar Hungary ya ba Yang Liankun takardar shaida da mindar tunawa, duk domin yaba shi saboda taimakonsa da ya yi yayin da ya gabatar da wallafe-wallafeda hanyar koyarwa na Kodaly. A shekarar 1985 ya shugabanci kungiyar 'yan amshi ta kasa zuwa Hongkong don halarci " bikin kade-kade na Rawayen kogi", kuma bisa gayyatar da aka sake yi masa, ya je Hongkong don shiga "bikin fasaha na Asia", inda shi madugu ne ga kungiyar 'yan amshi ta Hongkong wajen nuna wasan fasaha. A gun "bikin 'yan amshi na Beijing " na biyu da aka shirya a shekarar 1986, ya zama zaunannen kwamiti da darektan kungiyar shugabanci. A sekarar nan, an kafa kungiyar madugi 'yan

amshi", an zabe shi da ya zama shugaban kungiyar. Ya zama madugu

na kungiyar 'yan mashi ta kasa, wadda kungiyar ta sami na farko cikin minda

na matsayi na daya na gasar nuna wasan fasaha ta sana'a da ke cikin bikin

'yan amshi cikin " bikin 'yan amshi na Beijing" na zagaya na biyu.

Yan Liankun ya shugabanci kungiyoyi ko bisa gayyatar da aka yi masa, ya je

Amurka ta arewa da Kudu maso gabashin Asia da Taiwan da Hongkong , shi

Madugu ne cikin wasan fasaha, kuma yakan yi lacca kan ilimi a wurare daban

daban. Yan Liankun shi ne daya daga cikin masu aza harsashi na sha'anin

'yan amshi na sana'a cikin kasarmu, ya yi madugu sosai wanda ya zama wani

fiffikon madugu na 'yan amshi cikin kasar Sin.

Piao Dongsheng

Mr. Piao Dongsheng, an haifi shi ne a shekarar 1934 a birin Shengyang na lardin Liaoning na kasar Sin, tun shekarar 1949 ya soma aikinsa na adabi da wasannin fasaha, daga baya ya sami damar shiga kwalejin wasannin fasaha na Lu Xun na arewa maso gabas don yin karatu. Piao Dongsheng ya taba zama madugu, mai matsayi farko na kasa, na kungiyar wake-wake da raye-raye na kasa, da daraktan babban kamfanin daba'ar daukan sauti da hoto na kasar Sin. Shi ne shsugabsan kungiyar nazarin kidar orchestra ta kasar Sin na yanzu,da mataimakin shugaban kungiyar kula da harkokin vediyo da abubuwan da ake iya saurara ta kasar Sin,mataimakin daraktan kwamitin tantance mukami a fanning fasaha na ma'aikatar al'adu, dan kwamitin tantance manyan mukamai a fanning fasaha na ma'aikatar al'adu, dan kwamitin kararrun ba da jagoranci kan matsayin fasaha na jama'a,manyan kungiyar nazarin ikon dabi'a na kasar Sin.

Cikin zaman rayuwarsa na aikin kadekade na shekaru sama da 50, galibai dai Piao Dongsheng yana aikin madugu na kungiyar pilhamonic orchestra ta gargajiya. A gun bikin bude bikin fasaha ta farko ta kasar Sin, ya zama madugun kade-kade mai suna " manyan kade-kade na Sin" wanda kusan mutane dubu suka nuna; bisa gayyatar da aka yi masa, ya taba je Taiwan don ya zama bakon malamin madugu cikin kungiyar kade-kade na gargajiya ta birnin Taibei, da kungiyar kade-kade na gargajiya kwalejin nazari fasaha,da kungiyar kade-kade na gargajiya ta birnin Gaoxiong; ban da haka kuma, ya zama bakon malamin madugu bisa gayyatar kungiyar kade-kade ta gargajiya ta Hongkong da kungiyar kade-kade na gargajiya ta Singapore; Ya taba zama bakon malamin madugu da aka gayyatar musanman cikin kungiyar kade-kade na gargajiya ta kasa, da kungiyar kade-kade na gargajiya ta gidan wasan opera da raye-raye ma lasatr Sin, da kungiyar kade-kade ta gargajiya ta birnin Chengdu, ya zama madugun kungiyar wake-wake da raye-raye ta kasa cikin ziyarar da aka yi cikin kasashe da jihohi sama da goma. Ya taba zama madugu cikin sinima da wasan kwikwayon TV da faifan musamman da yawa.

A lokacin da ya dukufa kan aikin madugu, ya kuma nuna matukar tsanaki kan yin nazari aikin tsara kade-kaden gargajiya da hasashen kade-kade. Bi da bi ne ya tsara salon wakar symphonic ta kabila mai suna "labarin mala'ika ta furen Mudan" da kade-kaden orchestra na gargajiya " wakokin jama'ar lardin Jiangsu", da kadi da wake-wake na kayan kida mai suna Suona mai suna "Murnar nasara", da kade-kade solo na wani kayan kida mai suna Ehu " kan makiyayya", rera waja 'yan amshi da kungiyar orchestra, mai suna"wakar yaba kabilar Sin" da kade-kade na wake-wake da kade-kaden kayayyakin gargajiya kusan dari. Har a kasa Singapore da Taiwan da birnin Beijing, ya shiya "taron nuna kade-kade na kansa". Cikin 'yan shekarun baya, a gun mujjaloli na "kade-kaden jama'a" da "mujjalar mako-mako ta kade-kade" ta bayar da sharhi da bayanan bincike. An buga littafin musanman nasa mai suna "dabarar madugun kungiya makadi" da "hanya mai sauki na aikin madugu" da litafi na tattara bayyanai mai suna " halin zuciya ba zai kare ba ga kade-kaden gari"。

A shekarar 1993 ma'aikatar al'adu ta kasar Sin ta yaba masa da ya zama masana na fanning wasannin fasaha wanda ya ba da sakamakon fiffiko, wanda kuma ya sami alawas musamman da majalisar gudanarwa ta bayar masa.

Hu Bingxu

Hu Bingxu shi daya ne daga cikin nagartattun madugan makada na kasar Sin, a shekarar 1955 cikin jarabawar da aka yi , ya ci ya shiga cikin ajin yara na jami'ar koyon ilmin wake-wake da kade-kade, a shekarar 1958, ya zama dalibi na sashen makada na jami'ar. Saboda ya samu sakamako mai fiffiko , sai a shekarar 1959, aka zabe shi don shigad da shi cikin ajin kwararru na koyon amfani da kayan kade-kade mai suna Oboe na kasar Czech , a shekarar 1963 ya sauke karatu daga ajin tare da sakamako mai fiffiko, bayan haka ya shiga cikin symphony orchestra ta kungiyar kade-kade a kasar Sin ya zama mai sarafa kayan kida Oboe.

Hu Bingxu ya dauki nauyin aikin madugu da fasahar darekta cikin kungiyoyin wasannin fasaha masu matsayin kasar Sin guda 7 , kamarsu kungiyar kidan Orchestra ta Sin da gidan wasan Beijing opera na Shangai, da gidan wasan Beijing opera na Beijing, da gidan wasan wake-wake na Sin da kungiyar Dongfang ta wake-wake da raye-raye da kungiyar Sin ta wasan ballet, da kungiyar kade-kaden gargajiya ta kasar Sin.

Ya kuma shiga aikin tsara kade-kade na symphony mai suna " Sha Jia bang" da wasan Beijing opera "Zhe Qu Weihushang" da "DujuanShang" da ayyukan shirya nuna wasannin fasaha. Hada kade-kade na symphony da kayan kade-kade na kabila gu daya, ya zama wani babban

kagowa da bunkasuwa a kan tarihi na fasahar opera na kasar Sin.

Saboda sakamakon fiffiko na fasahar madugu da Hu Binbxu ya samu, sai ma'aikatar al'adu ta kasar Sin ta ba shi lambar madugun nagari, kuma sau da yawa ya dauki nauyin maduganci cikin wasannin fasaha kasaitattu, kamar kasaitaccen wasannin fasahar nishadi na bikin rufe wasannin motsa jiki na 11 na Asia. A shekarar 1995, babban kamfanin phonograph na Sin ya ba wa Hu Bingxu lambar musamman na madugu na faifan zinariya.

Ya yi aikin maduganci sosai . Kamfanin Philips a karo na farko ya yi phonograph guda 3 a babban yankin kasar Sin, guda biyu daga ciki, Hu bingxu ya zama madugunsu. Ya kuma yi aikin maduganci kan wasu sinima da suka shahara cikin kasar Sin, kamar "bikin kafa sabuwar Sin".

Hu Bingxu ya kware wajen hada kai da makadi, ya yi iyakacin karfinsa don kai abubuwan da kayayyakin kade-kide na Sin suka nuna zuwa wani sabon matsayi. Ya sa horon kungiyar kade-kade na gargajiya da fasahar nuna kade-kade da kayayyakin kida tare sun kai wani sabon mataki,

A shekarar 1999, Hu bingxu ya yi jagorar kungiyar kade-kade ta gargajiya ta kungiyar kade-kade ta kasar Sin zuwa birane 18 na kasar Amurka don nuna

wasannin fasaha, kuma sun hada kai da Ma Youyou mai Violoncello na duniya, cikin babban zauren Camegie sun nuna wasan "mafarki na yanayin bazara", sun sami nasara da ba a taba ganin irinta ba.

A lokaci na daga shekarar 1997 zuwa 2000, bisa gayyatar da aka yi masa ya je kasar Singapore don daukar nauyin babban sufeto na farko da madugu na matsayi na farko cikin kungiyar kade-kaden Sin ta kasar Singapore, cikin wa'adin aikinsa ya yi jagorancin kungiyar zuwa Beijing, da Shanghai da Xiamen da Taiwan don nuna wasannin fasaha, inda suka sami nasara sosai.

Chen Xieyang

Chen Xieyang, a shekarar 1953 ya shiga cikin makarantar midil ta jami'ar kade-kade, da farko ya koyi piano, daga baya ya shiga ajin koyon tsara kade-kade; sai a shekarar 1960 ya shiga sashen koyon aikin maduganci don samun digiri na farko, ya zama dalibi na shehun malami Huang Xiaotong; a shekarar 1965 bayan ya sauke karatu da sakamako mai kyau, ya zama madugu na kullum cikin Phiharmonic Orchestra na kungiyar ballet ta Shanghai. Tun bayan shekaru 70 na karnin da ya shige, tare da kungiyar ballet sun je kasar Korea ta Arewa da kasar Japan da kasar Canada da kasar Faransa don nuna wasannin fasaha.

A shekarar 1981, bisa gayyatar da aka yi masa, chen Xieyang ya je kasar Amurka don yin bincike, inda ya kara ilmin maduganci daga wajen shehun malami Otto Muller na Yale University, ban da haka bi da bi ne ya hada kai da kungiyar nuna kade-kade na zamani ta New York da Brooklyn Symphony Orchestra, da Symphony Orchestra na Honolulu don nuna wasannin fasaha, kuma ya gabatar da kade-kade na masu shirya kade-kade na kasar Sin.

A shekarar 1982, bisa gayyatar da aka yi masa, a gun bikin kade-kade na Asbon na Amurka, ya zama madugun kungiyar kade-kade ta bikin kade-kade, inda ya sami nasara sosai, bayan haka, ya zama madugun

na wasannin Symphony Orchestra na Plihilline da Hongkong Phiharmonic Orchestra. Bayan haka bisa gayaytar kamfanin faifai na kasar Faransa mai suna " the voice of music", ya zama madugun kungiyar kade-kade ta kasar Sin ta birnin Beijing wajen daukar muryar Beethoven Symphony N0.1 da N0 4 don yin fiafai, ban da haka ya kuma yi aikin shugabanci cikin manyan wasannin raye-raye da wakoki mai suna " wakar juyin juya halin kasar Sin".

Tun bayan shekarar 1985, bi da bi ne Chen Xieyang ya je kasar Rasha da kasar Japan da kasar Scotland da kasar Italiya da kasar Switzeland da Hong Kong da kasar Korea ta Arewa da kasar Korea ta Kudu da Macau da kasar Amurka da kasar Thailand da kasar Singapore da kasar Australia da kasar Jamus, inda ya zama madugun kungiyar kade-kade ko shahararrun kungiyoyin kade-kade na wurin cikin taron nuna wasannin kade-kade, duk ya sami maraba sosai. Chen Xieyang ya zama madugun kungiyar kade-kade ta kasar Sin da Symphony Orchestra ta Shanghai wajen daukar muryar kade-kaden Symphony da dama na Sin da na kasashen waje don yin faifai, ciki har da ya zama nadugun Symphony Orchestra ta shanghai waen dauka muryar Beethoven Symphony duka-duka da kade-kade na Symphony na mai tsara kade-kade na kasar Sin Ding Shande .

A shekarar 1987, ya sami mindar madugu nagari cikin bikin kade-kade mai suna "yanayin bazara na Shanghai", Chen Xieyang ya shugabanci waka da kade-kade na Violin mai suna " Liang Zhu" ya sami mindar zinariya ta faifai da kamfanin faifai na kasar Sin ya bayar a shekarar 1989. Har an shigad da sunansa cikin " Sunayen shahararun mutanen duniya" wanda cibiyar tarihin gamayyar kasa da kasa ta Cambridge ta Britania ta shirya.

Yanzu Chen Xieyang shi ne madugu na matsayin kasa, yana kan kujerar maduganci na farko kuma babban sufeto na Symphony Orchestra ta shanghai, da mataimakin shugaban kungiyar makada ta Shanghai da daraktan kungiyar makada ta kasar Sin da shugaban kungiyar masoyan symphony ta Shanghai.

Zheng Xiaoying

Shehun malama Zheng Xiaoying ta zama mace maduga ta farko cikin kasar Sin , ta taba zama madugar farko cikin gidan wasan opera na Sin da darektar sashen maduganci na jami'ar kade-kade ta Sin da babban sufeto na fasaha na kungiyar makadi mai suna "Ai Yue Nv". Yanzu an gayyace ta da ta zama babbar sufeto ta fasaha da madugar farko cikin " Xia Men Philharnonic Orchestra" wadda ita ce Symphony Orchestra ta sana'a ta farko da gwamnati ta ba da gudumuwa ga ita. Zheng Xiaying ta zama manajan darakta ta kungiyar makada ta kasar Sin. A shekarar 1981, ta sami lambar matsayi ta farko na kungiyar wasannin fasaha da ke karkashin ma'aikatar al'adu, a shekarar 1985, ta sami mindar yabo na al'adu da fasaha na kasar Faransa, a shekarar 1997 ta sami lambar ba da gudumuwa ta duk kasa mai suna "sanya kokari gwargwadon iyawa ta tsoffi. Wata cibiyar tarihin gamayyar kasa da kasa ta Cambridge ta Britania da sauran littafin shahararrun mutanen duniya da yawa sun shigad da tarihinta a ciki.

A shekarar 1947, Zheng Xiaoying ta shiga jarabawa da aka yi, ta ci ta shiga cikin jami'ar Union Medisan hospital ta Beijing, sai cikin jami'ar mata mai suna Jinling , ta shiga cikin sashen ilimin halittu da na kade-kade. A karshen shekarar 1948, ta je shiyyar samun yanci, ta taba aiki cikin kungiyar wasannin fasaha, a shekarar 1952 ta shiga cikin jami'ar kade-kade ta Sin don ta yi nazarin ilmin tsara kade-kade. Daga shekarar 1955 ta soma koyon ilimin maduganci na rera wakar 'yan amshi, a shekarar 1960 ta je tsohuwar Tarayyar Soviet don yin dalibta, ta shiga cikin kwalejin kasa na kade-kade na Thcaikovsky na Moscow, don kara ilimi kan wasan opera da maduganci na rera wakar 'yan amshi. A shekarar 1962 cikin gidan kade-kade na kasa da ke Moscow, Zheng Xiaoying ta zama maduga a wasan opera Tosco na kasar Italiya, ta sami nasara. An amince cewa Zheng Xiaoying ita ce daya daga cikin madugai nagari da ke cikin kasar Sin.

Tun bayan shekarar 1978, Zheng Xiaoying ta zama maduga cikin manyan wasannin fasaha da aka nuna, kamarsu wasan opera " Ubangiji mai kare furanni" da "amarya na 100" da "The Fallen woman" da "Carmen" da "Las Bodas De Figaro" da "Madama Butterfly" da Il Barbiere DI SIVIGLIA" da sauransu; Bayan haka ta taba hada kai tare da Symphony Otrchestra sama da 10 na kungiyar kade-kade ta kasar Sin , kungiyar symphony orchestra ta Shanghai, kungiyar radiyo symphony orchestra ta kasar Sin, gidan wasan wake-wake na Sin don shirya nuna kida da wake-wake, Zheng Xiaoying ta zama maduga cikin wasu wasan opera kamar " Amarya na dari" da "wakar makiyayya" da "Carmen" da "A'iguli" da wakoki na 'yan amshi masu nagartattu na cikin wasan opera na kasashen Turai, da Violin na kade-kade mai suna "Liang Zhu" da Malam Lv Siqing, wanda shi ya sami matsayi na farko cikin gasar Pagnini na 34, ya nuna, da sauran wasan opera na Orchestra na kasar Sin, an dauke su duka-duka domin yin faifai ko kaset, har an sayar da su cikin kasar Sin da gamayyar kasa da kasa.

Zheng Xiaoying ita kuma daya ce daga cikin shehunan malamai madugai wadda ke da azurtaciyar fasaha cikin kasar Sin. Cikin 'yan shekarun baya, wasu dalibanta sun sha samun sahon gaba cikin gasar madugun da aka shirya cikin gamayar kasa da kasa kamar a Amurka da Faransa da Italiya da Austria da Czech da Protugal, ko sun shiga sahon nagartattun madugai na gamayyar kasa da kasa da na gida. Daga wannan waje, ita mai son aikace-aikacen jin dadin jama'a ne na fannin kade-kade. Ta dauko matakai da yawa don bayyana wa jama'a ilmin kade-kade har kusan sau dubu, adadin masu sauraronta ya kai wajen dubu 200. tun bayan shekarar 1980, Zheng Xiaoying ta taba zuwa kasar Japan da Amurka da Italiya da Finland da Jamus da Faransa da Netherlands da Belgium da Ireland da Thailand don shirya nuna kade-kadan symphony ,ko halartar bikin al'adu na gamayyar kasa da kasa , wani lokaci ta zama maduga ga wasan opera ko yin lacca. Ta zama maduga ta farko wadda kuma ya zuwa yanzu akan gayyace ta da ta je kasashen ketare don shirya shahararrun wasannin opera na duniya. Cikin karo 6 ta je "Finland da Switzerland, inda ta yi maduganci don nuna "Madama Butterfly" da "Carmen" da "La Boheme" bisa gayyatar da aka yi mata cikin wasan opera sama da 60, duk ta samu yabo sosai.

Li Delun

Li Delun, mashawarci na wasar Orchestra ta kasar Sin kuma mataimakin shugaban kungiyar makada ta kasar Sin, tsohon darekta na kungiyar kade-kade ta Sin, dauwamammen madugu. A shekarar 1917 ne aka haifi shi a birnin Beijing, yayin da yake yaro, ya soma koyon piano da Vinlin, yayin da ya ke dalibta cikin jami'ar Furen , shi da malamai da dalibai sun taba kafa kungiyar philharmonic Orchestra na dalibai, ya kuma shiga yin kade-kade. A shekarar 1940 ya ci nasarar jarabawar shigad da shi cikin kwalejin kade-kade da wake-wake ta kasa, ya yi koyi daga wajen I. Shevizov da R. Duckson don koyon violomcello, ya yi dalibta daga wajen W. Frankel kan hasashe na kade-kade da wake-wake.

A shekarar 1942 a birnin Shanghai Li Delun tare da dalibai sun kafa the Youth Orchestra ya kuma halarci nuna kade-kade. A shekarar 1943 bayan ya sauke karatu daga kwalejin kade-kade da wake-wake, ya je birnin Yan An , inda ya zama madugun wakokin Philharmonic Orchestra of China kuma malamin koyarwa. Sai a shekarar 1949 ya dauki nauyin aikin madugancin makadi na gidan wasan opera na kasa Sin.

A shekarar 1953, bisa matsayi na dalibi mai neman samun digiri na biyu na shehun malami N. Anosov shahararren madugu, Li Delun ya je tsohuwar Tarayyar Soviet, ya shiga sashen horad da maduganci na jami'ar koyon kade-kade da wake-wake ta Moscow, ya zuwa yanayin kaka na shekarar 1957 ya dawo kasar Sin, sai ya zama madugu cikin kungiyar makada ta kasar Sin.

Li Delun ya zama madugu makadi a birnin Beijing , ya kuma shugabanci kungiyar symphony orchestra ta kungiyar kade-kade ta kasar Sin sun je sauran kasashe don nuna wasanni, kamar kasar Japan da kasar Korea ta Arewa da Hongkong da macau, ya kuma shigabancikungiyar makada na cikin daki sun je birane sama da 20 na kasar Spain. Ya zama madugu bako, bi da bi ne ya zama madugun kungiyar kade-kade sama da 20 na Leningrad da na Moscow na tsohuwar Tarayyar Soviet, ya kuma tafi kasar Finland da Czeck da Cuba inda ya zama madugun kungiyar kade-kade. Tun bayan shekarar 1959, sau da yawa ne ya zama madugu na babbar kungiyar kade-kade masu yawan daruruka , a shekarar 1987 a binin Beijing a gun wani kasaitacen taron kade-kade mai suna yanayin bazara na kade-kade, ya shugabanci wata hadadiyar kungiyar kade-kade mai mutane 800 wadda ta zama mafi kasaita.

Bayan shekarar 1985, Li Delun ya taba zuwa kasar Luxembourg, da kasar Spain da kasar Jamus da kasar Portugal da kasar Canada da kasar Amurka don nuna wasanni, a shekarar 1995 ya taba zuwa Taiwan don halartar taron nuna fitattun kade-kaden Sinawa na karni na 20.

A yayin da aka nuna kade-kade gomai na mawallafa a kasar Sin kamar su He Luding da Ma Sizong da Luo Zhongrong da Wu Zhuqing da Chen Peixun, shi Li Delun ya zama madugu, har a kasashen ketare an nuna kade-kaden kasar Sin sama da 20 kamarsu " babbar wakar yan amshi na rawayen kogi" da "wakar duwatsu da dazuzuka", ban da haka an kuma gama kai wajen nuna wasannin wake –wake da kade-kade tare da shahararrun makada na duniya kamarsu Ositrakh da Menuhin da Stem da Ma Youyou da Nikolayeva da Stackman, da wasu makada na kasar Sin kamarsu Fu Cong da Liu Shikun da Shen Xiang da Guo Shuzhen da Hu Kun da Lv Siqing da Xue Wei.

A shekarar 1985 a birnin Paris Li Delun ya taba zama mai tantance fasaha a gun gasar duniya ta goge Violin na Menuhin , kuma a shekarar 1986 ya zama mai tantance a cikin gasar duniya ta Tchaikovasky ta gogen violoncello da aka shirya a birnin Moscow.

Cikin 'yan shekarun baya, Li Delun ya dukufa kan samun bunkasuwa da ya da ilmin symphonic , ckin birane sama da 20 kamarsu Beijing, da Tientsin da Guang Zhou ya horad da kungiyar makadi da yawa, da sa kaimi kan kafa kungiyoyin makadi ta birnin Beijing da ta lardin Shangdong da ta jihar Mongoliya ta gida da ayyukan gina babban dakin nuna kade-kade na Beijing da na Guangzhou. Bayan haka ya je jami'a da ma'aikatu da hukumomin gwamnati na wurare daban daban na duk kasa don shirya taron kara ilimi kan symphonic.

A shekarar 1980 Li Delun ya sami mindar madugu ta girmamawa wadda ma'aikatar al'adu ta bayar, a shekarar 1986, ya sami lambar tunawa ta Liszt da ma'aikatar al'adu ta gwamnatin kasar Hungary ta bayar. Sai a ran 19 ga watan Oktoba na shekarar 2001 Li Delun ya mutu saboda ciwo, duk yana da shekaru 84.

Chen Zuohuang

Chen Zuohuang, an haifi shi a birnn Shanghai na kasar Sin, ashekarar 1956 ya sauke karatu daga sashen piano na makaranta ta jami'ar koyon kade-kade da wake-wake ta Sin. A shekarar 1981 ya sauke karatu daga sashen koyon madugun makada na jami'ar koyon kade-kade da wake-wake ta Sin. A yanayin zafi na shekarar nan, bisa gayyatar da shahararren madugun makada Mr. Seiji Ozawa ya yi masa, Chen Zuohuang ya je shaharariyyar cibiyar kade-kade ta Tanglewood da kwalejin koyon kade-kade na jami'ar Michigan na Amurka inda ya yi karatu. Sai a shekarar 1982 Chen Zuohuang ya sami digiri na biyu a fannin kade-kade. A shekarar 1985 ya sami digiri na uku na mai fasahar kade-kade na madugun makada wanda ya zama matsayi na farkon da jami'ar Muchigan ta bayar, sai Chen Zuohuang ya zama mutum na farko da ya sami digiri na uku na fasahar kade-kade cikin sabuwar kasar Sin.

Daga shekarar 1985 zuwa 1987, Chen Zuohuang ya dauki nauyin mataimakin professor na madugun makada cikin kwalejin koyon fasaha mukamin ta jami'ar Kansas ta Amurka, a gun lokacin, ya sami lambar falafasa da aka daukaka masa.

A shekarar 1987, Chen Zuohuang ya zama madugun makada na kungiyar kade-kade ta Sin, kuma ya yi jagorancin kungiyar don nuna wasannin fasaha mai ma'anar tarihi a New York da Washington da Chicago da San Francisco da Los Angeles da sauran birane 19. taron nuna kade-kaden da kungiyar kade-kade ta nuna ya sami kasaitaciyar nasara, kuma ya jawo abun mamaki, har ya sami yabo daga wajen 'yan kallo da manazarta kade-kade na Amurka.

Daga shekarar 1990 zuwa 2000, the Witchita Symphony Orchestra ta Amurka ta ba Chen Zuohuang aikin babban sufeto na kade-kade da madugun makada. Daga shekarar 1992 zuwa 1996, Chen Zuohuang ya kuma dauki nauyin aikin babban sufeto na kade-kade da madugun makada na the Rhode Island philharmonic Orchstra na Amurka. A gun lokacin, sau da yawa ne ya sami mindar fasaha ta gwamnan jihar Kansas da Rhode Island da umurnin ba da minda , ya sami yabo da girmamamwa daga wajen makadi na kungiyar kade-kade da masu sauraro.

Cikin 'yan shekaru, bisa gayyatar da aka yi masa, Chen Zuohuang ya je kasashe da jihohi sama da 20 don ya zama madugu na kungiyar kade-kade, ciki har da the Zurich tonhalle Orchestra da Vancouver Symphony Orchestra da Mexico National Symphony Orchestra da Tanglewood Music Festival Orchestra na Amurka da Hamburg Youth

Orchestra na Jamus da the Russia Phiharmonic Orchestra da Slovzk

Radio Symphony Orchestra daHaifa Symphony Orchestra na Isra'ila da the Hong Kong Phiharmonic Orchestra da the Pusan Phiharmonic Orchestra na Korea ta Kudu da the Taipei Symphony Orchestra da sauran kasashe ko jihohi sama da 20. Fasahar madugu na Chen Zuohuang ya sami yabo daga wajen 'an kallo da masu ba da sharhin kade-kade, da suka labarta cewa shi " wani makadi da ke nuna kwarewa", kuma " kwarare a gaban kowace irin kungiyar kade-kade" har da fasahar jagoranci na jawo hankula sosai".

A shekarar 1996 Chen Zuohuang ya yi ban kwana da wasu ayyukansa na kasashen waje, ya komo kasar Sin, bayan dawowarsa ya soma aikin shirya kafa Symphony Orchestra na kasar Sin duk bisa harsashi na kungiyar kade-kade ta Sin, ya zama babban sufeton fasaha na farko cikin Symphony Orchestra na Sin. A cikin Symphony Orchestra na Sin ana tafiyar da tsarin nuna wasannin fasaha na lokutan wake-wake da kade-kade kamar yadda Symphony Orchestra na sana'a na gamayyar kasa da kasa suke tafiyarwa, cikin shekarun an gayyaci kyawawan makada wajen dari na duniya da su zo nan don gama kai wajen nuna orthestra masu dinbim yawa na Sin da na gamayyar kasa da kasa , hakan ya ba da karfi wajen yunkurad da sha'anin kide-kiden Orthestra na kasar Sin gaba. Chen Zuohuang ya shugabanci symphony don nuna wasannin fasaha cikin kasashe uku na Turai ta yamma da kasar Japan da kasar Mexico, inda suka sami yabo daga wajen masauraro da manazarta kade-kade gaba daya.

Peng Xiuwen

Peng Xiuwen madugun makada kuma mai shirya kade-kade na kasar Sin, ( 1931-1996), asalinsa na birnin Wuhan na lardin Hupei, shi ne babban malamin kade-kaden gargajiya da ya yi suna cikin kasar Sin, babban madugun kungiyar makadan kabilu ta watsa labaru ta Sin, daya daga cikin wadanda suka kafa the Broadcasting Philharmonic Orchestra of China.

Peng Xiuwen, tun da ya ke karami ya soma koyon amfani da kayayyakin kide-kide na kabilun Sin kamar su Er Hu da Pi Pa wato kayayyakin gargajiya na goge. A shekarar 1949 ya sauke karatu daga makarantar kasuwanci, a shekarar 1950 ya soma aiki a gidan rediyon jama'a na birnin Chong Qing na lardin Sichuan.

A shekarar 1952, an shigad da Peng Xiuwen cikin the Broadcasting Traditional Instruments Orchestra of china, a shekara na gaba ya zama madugun kungiyar makada kuma mai shirya kade-kade. Saboda tare da sauran 'yan kungiyar sun sanya kokari tare, sun yi aikin farko wajen kafa the New Philharmonic Orchestra of China.

A shekarar 1957 a gun gasa ta 6 ta fasahar bikin murna na samarin gamayyar kasa da kasa da aka shirya a Moscow, Peng Xiuwen ya zama madugun makada , traditonal instruments Orchestra ta nuna kade-kade

da Peng Xiuwen ya yi gyara , kungiyar ta sami mindar zinariya. Wadannan kade-kade sun zama kwararrun kade-kade na Traditonal Instruments Orchestra of China.

A shekarar 1981, bisa gayyatar da the Hong Kong Philharmonic Orchsetra ta yi masa, an ba Peng Xiuwen lakabin madugu mai ziyara. A shekarar nan kuma. Ya zama mai fasahar sarrafa Traditional Instruments Orchestra of the Broadcasting Art Troupe of China. Sai a shekara mai zuwa, ya yi jagorar Philharmonic Orchestra zuwa Hong Kong inda suka nuna wasannin fasaha.

A shekarar 1983, Peng Xiuwen ya zama shugaban Taditional Instruments Orchesra of the Broadcasting Art Troupe of China.

" Shigad da halin mutum cikin kade-kade, kade-kade na bayyana halin mutum" ya zama daya daga cikin halayen musamman na kula da fasaha na Peng Xiuwen . Ya yi aikin madugun makadi wanda a ciki ya kuma nuna sha'awarsa kan aikin a tsanake. Saboda aikinsa na madugu, Traditional Instruments Orchestra of the Broadcasting Art Troupe of China ta kai wani babban matsayi kan samun daidaito tsakanin kayayyakin kide-kide da digirgire da gwaninta, wadda ta zama mafi nagartattu cikin kasar Sin.

Peng Xiuwen ya ba da babban taimako domin sha'anin kade-kade na kabilun Sin, kade-kadan da ya gyara ko ya tsara sun kai dari 4 ko 5. Ban da haka kuma ya yi jarabawa don nuna shahararrun kade-kade na kasashen ketare da kayayyakin kade-kade na gargajiya na kasar Sin, alal misali "kyakkyawan kogin Soro" da "kide-kiden rawar Horo" da "wakar sare itatuwa", ya yi gyara kan wasu kade-kade na shahararrun makada da su zama kade-kade na kayan kidan gargajiya , kamar "Ruins of Athens" na Beethoven da "nune-nunen hotuna" na Mussorgsky, har da kade-kade na kusa-kusa "cloud" na Debussy da "Flamingo" na Stravinsky . Hakan ya yadada kidan orchesta na gargajiyawajen nuna fasaharta.

Bayan shekaru 80 na karnin da ya shige, Peng Xiuwen ya tsara wasu muhimman kade-kade na gargajiya, wadanda suka azurta kade-kaden gargajiya na kasar Sin.

A ran 28 ga watan Disamba na shekarar 1996, Peng Xiuwen ya rasu saboda ciwo a birnin Beijing.

[Masu wakoki]

Tang Can

Tang Can, wata shahararriyyar mawakiya, ta birnin Zhu Zhou na lardin Hunan na kasar Sin, wadda ta taba nazari kan wakar baka cikin jami'ar koyon kade-kade da wake-wake ta Wuhan, bayan ta sauke karatu ta ci jarabawa wajen shiga kungiyar wake--wake da raye-raye ta kasar Sin, inda ta zama mawakiya mai salon wakar mutum daya.

A cikin dabi'ar rera waka ta kabilar da ke cikin mawaka na sana'a na samun mindoji na TV da aka shirya a karo na 7 domin mawaka samarin duk kasa, Tang Can ta sami mindar kyakkyawar mawakiya , kuma a gun zama na 5 na gasar samun mindoji na kade-kade da wake-wake na TV, Tang Can ta sami mindar azurfa bisa wakar " a cika kyakkyawan mafarki", da mindar tagulla na wakar " budurwa 'yar su" da mindar kyau ta wakar " an kasance da wani lokaci".

A yanayin zafi na shekarar 1998, an yi bala'in ambaliyar ruwa wanda ba a taba ganin irinsa ba cikin wasu shiyoyyin kasar Sin, Tang Can, banda ta halarci taron nuna wasannin fasaha mai suna " mu jama'a dubu dubai muna da zuciya daya" da CCTV ta shirya domin ba da taikamon bala'in, ta kuma halarci nuna wasannin fasaha da lardin Hunan da lardin Hupei da lardin Jiangxi suka shirya, ta je wuraren kawar da bala'in don ba da taimakon kudade da kayayyaki, har ma ta dauki MTV mai

suna " Yabon jarumai" daga aljihunta wadda ke sa mutane suka jiku, inda ta bayyana halin nuna girmamawa ga jarumai masu kawar da bala'in ambaliyar ruwa daga jama'ar duk kasa , ta wakokin da ta rera. Bayan an yi ta watsa shirin MTV din nan har sau da yawa cikin tashar CCTV, sai aka haifar da kyakkyawan tasiri cikin zamantakewar al'umma, daga baya CCTV ta shigad da MTV cikin shirn kade-kade na musamman na aikin kawar da bala'in ambaliyar ruwa.

A lokacin da Tang Can ta himmantu wajen shiga harkoki daban daban na kungiyar wake-wake da raye-raye ta Sin, kuma sau da yawa ta halarci aikace-aikacen jin dadin jama'a da bangarori daban daban na zamantakewar al'umma suka shirya da wasu kasaitattun taron nuna wassannin fasaha, ta sha shiga cikin kungiyar "zuciya hada zuciya" ta CCTV, don nuna wasannin fasaha a Huai An da Kunming da Lasa da sauran wurare na tsoffin wuraren sansanoni na lokacin juyin juya hali da na inda kananan kabilu ke da yawa da wurare masu nisa da wuraren da ke fama da talauci don nuna jejeto, har ta halarci nuna wasannin fasaha domin "harkar ba da taimako ga yara da su samu ilmi na tilas" da aka shirya a gidan wasannin motsa jiki na Beijing da gidan wasannin motsa jiki na ma'aikata, Tang Can ta ba da taimakon kudi da kayayyaki na karo

karo domin taimakawa yara da su rasa damar samun ilmi da su sake sami ilmi.

A gun taron nuna wasannin fasaha da CCTV ta shirya domin murnar rana ta farko ta shekarar 1999, Tang Can da wani shahararen mawaki Huo Fong sun hada kai don rera wata waka mai cike da fara'a na samari namiji da mace sun yi tambaya da ba da amsa cikin waka mai suna "Make a good beginning", kuma an yi MTV na wakar nan, wakar ta shiga salo cikin sunayen wakokin kasar Sin , har an mai da wakar da ta zama wata muhimiyar waka cikin gidan TV da yawa na duk kasa don nuna ta. A gun shagalin marabtar sabon karni da sabon shekaru dubu da aka shirya a dandamalin karni na shekarar 2000 da shagalin murnar sallar bazara na shekarar 2000, Tang Can ta sake rera wakar, ta sami yabo sosai daga bangarori daban daban na zamantakewar al'umma.

Domin murnar ranar cika shekaru 50 da kafuwar kasar mahaifa, Tang Can ta rera wata waka mai suna " A albarkata kasar mahaifa" na wani shahararen mawallafi kidan waka Mong Qingyun . Kuma an dauki wakar cikin MTV, Chang Yimou shahararen darekta na sinima ya shiga aikin tsara da shirya MTV wanda ya zama karo na farko da Chang Yimou ya sa hannu cikin shirya MTV, shi ya yaba Tang Can bisa iyawarta da

halin nagari ta sosai. Daga baya a gidajen TV na birane da lardunan duk kasa , an nuna MTV na " A albarkata kasar mahaifa" , an mayar da martani sosai. A gun shagalin nuna wasannin fasaha da gidan talebijin na CCTV na kasar Sin ya shirya domin murnar ranar cika shekaru 50 da

kafuwar kasar mahaifa, Tang Can tare da wani shahararren mawaki Wu Yangze sun rera wakar. Ban da haka kuma, Tang Can ta rera wakar a gun shagulgulan da gidajen TV na lardin Hunan da lardin Hupei da lardin Zejing da birnin Shanghai da jihar Kwanxi da lardin Shangdong da lardin Jiangxi suka shirya dom,in murnar ranar cika shekaru 50 da kafuwar kasar mahaifa.

A cikin gasar rera wakoki domin ranar cika shekaru 50 da kafuwar sabuwar kasar Sin, wakar " A albarkacin kasar mahaifa " ta sami minda mai kyau, wadda gaba daya aka nuna cewa, wata kyakkyawar waka ce, wadda kuma wakar ta sami mindar zinariya cikin MTV na TV na kasar Sin.

A shekarar 2000, Tang Can ta rera MTV mai suna " zaman alheri fiddin jiddin" da saurayi mawallafi na kidan wakar Fuke ya yi, an watsa shi a cikin shirin CCTV mai suna " waka daya kowane mako", ya sami yabo. A cikin wakokin gargajiya na tsamo dabarar rera waka ta yau da kullum cikin wakokin jama'a, ta hakan ya zama wani sabon salo na bayyana halinh zamani cikin wakokin jama'a, da'irar wake-wake da kade-kade ta

yaba cewa, haka ya zama kyakkyawar waka ta sabon salo da sabon bincike har da sabon sakamako. Ita Tang Can ta zama "kan gaba a sabuwar wakar jama'a" kafofin yada labarai sun yaba cewa. Bayan haka Tang Can ta kuma gabatar da wani sabon MTV mai suna " Kyakkyawan yankin gargajiya" wanda ya yi kunnen doki da MTV " Zaman alheri fiddin jiddin " kuma ke da sabon salon wakar jama'a.

A shekarar 2001, Tang Can ta sami " mindar ham na zinariy

" wato mindar kyawawan mawaka goma , mindar fasaha ta watsa labaru ta kasar Sin wadda karo na farko babbar hukumar watsa labaru da TV da sinima ta kasar Sin ta shirya na mawaka da masu sauraro na duk kasa ke kauna.

Yan Weiwen

Mr Yan Weiwen mawaki ne da ke rera wakoki tare da dagaggen sauti na kungiyar wake-wake da raye-raye ta sashen siyasa na rundunar sojoji ta kasar Sin kuma mamban kungiyar masu wake-wake da kide-kide na kasar Sin, sa'anan kuma shi dan wasa ne da ke bisa matsayin farko na kasar Sin, ya sami alawas na musamman daga wejen majalisar gudanarwa ta kasar Sin.

Mr Yan Weiwen ya bi sawun shehun malami Jin Tielin, ya koyi fasahohin rera wakoki masu kyau daga sauran mawaka da yawa, yana da makogwaro mai murya mai dadin ji sosai, ya kware sosai wajen rera wakoki, ya kuma zama nagartaccen mawaki a cikin da'irar wake-wake da kide-kide ta kasar Sin, ya sami karbuwa da kauna sosai daga wajen masu sauraronsa da 'yan kallonsa. Wakokin da ya rera, kamar su "Xiao Bai Yang" da "E Mei Jiu Jia" da "Shuo Ju Xin Li Hua" da "Yi Er San Si Ge" da "Xiang Jia De Shi Hou" da "Zai Jian Ba, Lao Bing" da "Jun Ren Ben Se" da "Dong Fang De Tai Yang, Dong Fang De Yue Liang" da "Zu Guo Wan Sui" da "Jun Qi Xia De Wo Men" da sauran wakoki suna yaduwa a tsakanin sojoji da jama'a.

Mr Yan Weiwen ya dauki muryar fayafaye goma da shi kadai ya rera bi da bi, kuma ya dauki muryar wakoki kamar su "Mo Dai Huang Di" wato sarkin karshe da "Hai Deng Chuan Qi" wato tarihin wani mai bin addinin Buhta mai suna Hai Deng da "Yang Nai Wu Yu Xiao Bai Cai" da "Dong Zhou Lie Guo" da "Hong Yi Fa Shi" da "Hong Shi Zi Fang Dui" da " Guo Lanying" da "Tai Ping Tian Guo" da sauransu domin simima da shirye-shiryen TV fiye da goma.

A madadin kasar Sin ne ya taba kai ziyara a kasar Amurka da Japan da Canada da Faransa da Jamus da Italiya da sauran kasashe da jihohi fiye da 20, ya sami yabo da marhabi daga wajen masu sauraronsa da 'yan kallonsa na gida da waje .

Mr Yan Weiwen ya sami lambobin yabo sau da yawa a gun gasannin da aka shirya a duk rundunar sojoji da kuma duk kasar Sin. Daga cikinsu, da akwai lambawan da ya samu a shekarar 1988 wajen rera wakokin gargajiyar kasar Sin a tsakanin samari mawaka ta hanyar shirye-shiryen TV na gasa ta uku, a shekarar 1989, ya sami lambawan a gun wasannin da aka nuna a tsakanin mawakan duk rundunar sojoji ta kasar Sin, kuma a shekarar 1990, an yi masa kirari da cewa, mawaki ne da ke cikin nagartattun mawaka goma na rera wakoki domin sinima da TV da aka zabe su a karo na biyu , a shekarar 1992, ya sami lambar faifan zinariya ta kasar Sin, a shekarar 1993 da shekarar 1995 ya sami lambawan daga cikin mawakan da 'yan kallo na duk kasar Sin suka yi musu kauna sosai da sosai. A shekarar 1995, ya sami lambar zinariya a gun gasar da aka yi domin shirye-shiryen TV. A shekarar 2001, ya yi hadin guiwa da mawaki Tong Tiexin da Lu Jihong wajen rera waka mai suna " Kasar Sin ke dosawa gaba" , ya sami lambar zinariya.(Halima)

Yang Hongji

Yang Hongji wani shahararren mawaki mai karin sauti mikakiyya na kasar Sin, shi dan kungiyar makada ta kasar Sin, kuma dan kungiyar mawallafan wasan kwaikwayo na kasar Sin.

An haifi Yang Hongji a watan janairu na shekarar 1942 a birnin Dalian na lardin Liao Ning na kasar Sin. Tun yana karami, yana son rera waka, a shekarar 1959, wato yayin da yake karatu a aji biyu na babbar makaranta , ya ci jarabawa ya shiga cikin kungiyar wake-wake da raye-raye ta Dalian, sai a shekarar 1962 ya ci jarabawa ya shiga kungiyar wasan opera ta babbar ma'aikatar siyasa ta Beijing ya zuwa yanzu . Ya yi dalibta daga wajen Malam Li Mongxiong kan wakar baka, kuma ya taba koyon wakar baka a wajen Malam Yang Huatang cikin wani lokaci, har yakan sami jagoraranci daga wajen shehun malami Shen Xiang.

Yang Hongji ya gane sosai cewa, in ba a taba nazarin hasashe taki kan taki cikin jami'ar koyon kade-kade da wake wake ba, da kyar zai zama wani mawaki mai kwarewa wajen rera wakoki ko-wadanne iri, saboda haka yayin da ya ke saurayi, shi da kansa ya yi nazarin duk hasashe na kade-kade da wake-wake wadanda dalibi da ke neman samun digiri na farko ya koya tilas, cikin har da piano da ilmin daidaito tsakanin kide da waka,da horon da aka yi don diadiata lafazin waka,da harshen Italiya. Wadannan nazarce-nazarce sun ba da amfani na kudura kome cikin nasarar da ya samu.

A shekarar 1979,madugun makada mai suna Seiji Ozawa na kasar Japan ya zo kasar Sin don hada kai da kungiyar kade-kade ta Sin wajen nuna Beethoven Symphony N0.9. daga cikin mawaka sama da gomai,an zabi Yang Hongji shi kadai, cikin nuna wake-wake, ya sami yabo daga wajen Seiji Ozawa. A shekarar 1984, shehu malami Shen Xian ya gabatar da shi, Yang Hongji ya hada kai da kungiyar St. ta kade-kade da madugun makada Mo Yongxi, asalinsa Amurka , Yang Hongji maza mai karin sauti na mikakke sun nuna "Seasons", wani tsohon kade-kade da Haydn ya tsara cikin turanci na tsahon zamanin da. Bayan haka Yang Hongji ya dauki babban nauyi na maza salon waka na mutum daya mai Karin sauti mikakke , ya hada kai tare da kungiyar kade-kade ta Sin, wajen nuna Requiem na cikin Verdi, da Creation na Haydn da Mass na Mozart, da Missa Solemnis na Beethoven . Yayin da kuniyar wasan opera ta babbar ma'aikatar siyasa ta Beijing da kungiyar kade-kade ta Sin sun hada kai sun nuna wasan opare Carmen sa Madama Butterfly da Tosca da wasan Opera ta tsohuwar Tarayyar Soviet " A lokacin asuba kome ya yi shiru ", Yang Hongji ya dauki nauyin manyan mutanen da ya takarawa cikin wasan. Ban da wannan, cikin wasu wasannin opera sama da gomai na kasar Sin kamar " idon ruwa digo daya" da "diyar jam'iyya " Yang Hongji ya zama babban mutum da ya takarawa cikin

wasan kwaikwayo。Musamman a shekarar 1998, cikin wasan opera Qu Yuan da marigayi makadi na jama'a Shi Guangnan ya wallafa, Yang Hongji ya nuna Malam Qu Yuan, har ya sami babbar nasara.

Yang Hongji ya sami manyan mindoji na wasan opera Meihua ta duk kasa da Wenhua ta majalisar gudanarwa. Yang Hongji yakan halarci kasaitattun shagalin nuna wasannin fasaha na tashoshin T.V. na duk kasa da sauran manyan shagulgula da ma'aikatar al'adu da babbar ma'aikatar siyasa suka shirya, ya kuma rera babbar wakar da ke ckin sinima da wasan kwaikwayo na T.V., kamar wasan kwaikwayo na T.V. mai suna "The Romance of the Three Kingdoms " da wakar da ke cikin fina-finan T.V. mai suna "yin sallama da Moscow", duk sun ba mutane alaman da

lu Jihong

Mr Lu Jihong shi ne mawaki da ke rera wakoki tare da daggagen sauti, kuma shi ne dan wasa da ke bisa matsayin farko na kasar Sin, yana daya daga cikin mawakan da ke da karfi sosai a cikin da'irar rera wakoki ta kasar Sin a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, ya sami alawus na musamman daga wajen majalisar gudanarwa ta kasar Sin.

A shekarar 1982, Mr Lu Jihong ya kammala karatu a sashen koyar da ilmin rera wakoki na kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na birnin Xi'an na kaasr Sin. Ya taba bin sawun shehiyar malama mai suna Tao Liling, kuma ya sami digiri na farko, bayan da ya kammala karatunsa , sai ya je aikin koyarwa a sashen koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na kolejin musamman na horar da malaman koyarwa na birnin Lanzhou na kasar Sin, a shekarar 1985 ya shiga kungiyar wake-wake da raye–raye ta lardin Gansu na kasar Sin, a shekarar 1989, ta shiga kungiyar raye-raye da wake-wake ta sashen siyasa na rundunar sojojin ruwa ta kasar Sin , ya zama 'dan wasan rera wakoki shi kadai a cikin wasannin da aka shirya, ya bi sawun shehun malami Jin Tielin.

Mr Lu Jihong ya taba samun lambawan har sau uku a gun gasar rera wakoki da aka shirya a lardin Gansu. Ya kuma sami lambar azurfa a gun gasar cin kofin Jinlong ta rera wakoki a tsakanin mawakan duk kasar Sin. A shekarar 1992, ya zama na biyu a gun gasar cin kofin manyan nahiyoyi biyar, wato kofin "Wu Zhou" ta biyar da gidan rediyo mai hoto na tsakiya na kasar Sin wato CCTV ya shirya a tsakanin samari mawaka na duk kasar Sin. A wannan shekara kuma, ya sami lambawan a gun gasa ta 6 ta nuna wasannin fasaha da aka shirya a cikin rundunar sojoji ta kasar Sin, sa'anan kuma ya sami lambawan a gun gasar rera wakokin gargajiyar kasar Sin wadda ma'aikatar al'adu ta kasar Sin ta shirya. A shekarar 1995, a gun gasar rera sabbin wakoki ta hanyar gidan rediyo , shi ma ya sami lambar zinariya daga wajen gwamnati.

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, ban da lambaboin yabo da ya samu, Mr Lu Jihong ya kuma dauki muryar wakoki domin sinimar da ake kira "Yan Jia Jiang" wato jaruman da suke cikin gidan iyalin Yan da "San Guo Yang Yi" wato tatsuniya mai suna kasashe uku, kamar dauloli uku da ake cewa "The Romance of The Three Kingdoms" cikin Turanci da "Tang Ming Huang" wato sarkin daular Tang na tsohuwar kasar Sin da ke da lakabi "Minghuang" da "Yang Gui Fei" wato wata matar sarki mai suna Yang Rui Huan da "Han Wu Di" wato wani sarkin tsuhuwar kasar Sin da ke da lakabin nan da dai sauransu. Wakokin da ya rera kamar su, "Zai Jian Le, Da Bie Shan" wato yi ban kwana da tsaunin Da Bie da "Hui Sichuan" wato komawa lardin Sichuan da "Ma Ma De Ge Yao" wato wakokin da mahaifiya ta rera da sauransu sun riga sun yadu a duk fadin kasar Sin. Wakokin da ya rera sun burge mutane sosai da sosai tare da halayen musamman da ya bayyana ta hanyar yin amfani da dabarar rera wakokin gargajiyar kasar Sin, a lokacin da ya nuna wasanni, yana cikin himma da kwazo tare da kuzari sosai da sosai. Ya taba zama babban dan wasa a cikin wasan kwaikwayo mai suna "Hong Shan Hu" , ya ci nasara. Ba sau daya ba ba sau biyu ba ya shiga manyan shagulgulan dare na nuna wasannin fasaha da CCTV da gidajen rediyo mai hoto na wuri wuri na kasar Sin suka shirya.

A gun babbar gasa ta TV ta nuna wasannin rera wakoki na MTV na shekarar 2001 na duk kasar Sin, waka mai suna " Kasar Sin ke dosawa gaba" da shi da Mr Tong Tiexin da Mr Yan Weiwen suka rera cikin hadin guiwa ta sami lambar zinariya. A shekarar 2003, ya kuma sami lambar faifan zinariya ta karo na biyu na shekarar 2003 na kasar Sin.

A madaddin kasar Sin da rundunar sojoji ne, Mr Lu Jihong ya kan kai ziyara a kasar Jamus da Rasha da Philipings da Thialand da Amurka da sauran kasashe, ya sami karbuwa da marhabi daga wajen 'Yan kallo na gida da na waje. (Halima)

Liao Changyung

Liao Changyung daya daga cikin kalilan din shahararrun mawaka na kasar Sin wanda yana nan yana kokari kan dandamalin opera ta gamayyar kasa da kasa.

Liao Changyung ya taba dalibta daga wajen Chou Xiaoyang, shahararriyar mai koyar da ilmin wakar baka da Luo Wei mawaki na Karin sauti mai hawa , a shekarar 1995 ya sami digiri na biyu daga jami'ar koyon kade-kade da wake-wake ta Shanghai.

Cikin 'yan shekaru, Liao Changyung ya yi ta samun manyan mindoji na duniya kan wakar baka, alal misali cikin shekara guda wato daga shekarar 1996 zuwa 1997, Liao Changyung ya zo na matsayin farko cikin 41 French International Toulouse Singing Competition da Placido Domingo Opera Competition the World, da Queem Songja International Music Competition, wadannan suka sa da'irar kide-kide da wake-wake ta duniya ta yi mamaki kwarai. Musamman samun mindar matsayin farko cikin Placido Domingo Opera Competition the World, Liao Changyung ya zama mawaki na Asia da ya sami mindar nan cikin gasar nan. Babban malami Placido Domingo ya yaba Liao Changyung sosai cewa: shi ne maza na Karin sauti mai mikakici mafi dadi wanda na taba saurara, ya kware wajen rera waka kuma fasaharsa wadda ba wanda zai kai shi, ya sami mindar nan, amma wadda a da mawaka na Turai ko

na Amurka ne kawai ke samun mindar nan ne.

Cikin 'yan shekaru, Liao Changyung ya sa kafarsa a wurare da yawa na gamayyar kasa da kasa, alal misali ya je kasar Amurka da Faransa da Japan da Australia da Britania da Sweden da Norway da Jamus da Rasha, inda ya gama kai da manyan 'yan fasaha da kungiyar kide-kide wajen nuna wasannin fasaha. Bisa matsayinsa na mawaki na kasar Sin wanda shi ne na farko da hau dandamali na shahararen gidan opera na Washington , Liao Changyung ya hada kai da Donmingo wajen nuna wasan opera Trobatore na cikin Verdi wadda aka nuna cikin yanayin nuna wasan opera na 2000 na cibiyar kennedy , ya sami cikakkiyar nasara, har 'yan kallo sun yi sha'awa kwarai. Har jaridar "Washington Times" ta kebe wani shafi domin bayar da labari na musamman kan nuna wasan opera cikin gama kai tsakanin babban malami Donmingo da Liao Changyung, an nuna cewa: a wurin da mashahuran mawaka na duniya ke cunkushe, wani mai shahara shi ne Liao Changyung da ya zo daga kasar Sin. Ya kware wajen rera opera Verdi kamar shi asalinsa na al'adar mawaka ne na nuna opera Verdi, sabili da haka ya bayyana halin Verdi ; har salon sautinsa da ingancin sauti masu dadin ji wanda ke nuna karfi, halin da ya bayyana cikin waka da gwanintar fasaharsa da ya nuna, duk sun sa cibiyar kenney ta ba da sha'awa sau da yawa. Mun hakake cewa, dan fasaha da ya kware zai zama wani nadiri cikin da'irar

kade-kade da wake-wake na duniya.

A farkon shekarar 1998, bisa gayyatar da Domingo ya yi masa, a Tokyo an yi shagalin kade-kade na sabuwar shekara, a shekarar nan kuma, shi da Jose Carrcras sun gama kai wajen yin shagalin kade-kade da wake-wake musamman domin sabon gidan opera na Shanghai. Bayan haka ba da dadewa ba, a zauren kide-kide da wake-wake na Carnegie da ke birnin New York, Liao changyung ya nuna wasan opera mai suna Maria Stuarda, inda ya sake cin nasarar 'yan kallo na New York wadanda sukan 挑剔. Jaridar "New York Times" ta nuna yabo sosai cewa, Liao Changyung ya zama maza Karin sauri mai mikakici mafi dadi wanda muka saurara har cikin 'yan shekaru na kusa-kusa.

Liao Changyung ya zama wani dalibin babban malami Domingo wanda malamin ya nuna masa sha'awa sosai, kuma bisa gayyatar da babban malami ya yi masa, Liao changyung ya nuna wasanni har cikin wurare daban daban na duniya. Alal misali, a shekarar 2001, ya sake gama kai da Placido Domingo, sun nuna wasan opera "Story of Hofman" na Offenbach a cibiyar Kenney . A shekarar 2002, Domingo ya gayyaci Liao Changyung da su rera wakoki a gun kasaitaccen bikin murnar ranar cika shekaru 10 na yin gasar wasan opera Domingo cikin duniya wanda aka shirya a birnin Paris na kasar Faransa, a shekarar nan kuma, zauren

kade-kade da wake-wake na Carnegie ya gayyaci Lian Changyung da ya yi taron wake-wake shi kadai.

Yanzu Liao Changyung wani shehun malami ne cikin jami'ar koyon kade-kade da wake-wake ta shanghai, shi ne kuma shugaban sashen wakar baka.

Guo Lanying

Guo Lanying wata shaharariyar zabiya ce mai rera wakoki tare da dagaggen sauti. An haife ta a watan Disamba na shekarar 1930 a wani gidan iyali mai fama da talauci sosai a gundumar Pingyao ta lardin Shansi na kasar Sin. A lokacin da ta kai shekaru 6 da haihuwa, ta soma koyon rera wani irin wakar da ake kira "Bangzi" na Zhonglu na lardin Shanxi na kasar Sin, ya zuwa shekaru 7 da haihuwarta, ta soma nuna wasanni a dakalin gidan nuna wasanni na haikalin da ake kira "Kaihua" na birnin Taiyuan na lardin Shanxi. A lokacin da ta cika shekaru 11 da haihuwa, sai ta tafi birnin Taiyuan tare da wata kungiyar nuna wasannin kwaikwayo, bi da bi ne ta nuna wasannin kwaikwayo na gargajiyar kasar Sin fiye da 100, kamar su "Li San Niang Tiao Shui" wato ma'anar wakar ta bayyana yadda wata tsohuwa ta dauki ruwa da "Er Du Mei" da dai sauransu. Wadanda take nunawa a cikin wasanni da kuma wakokin da ta rera duk suna da kyau sosai, daga nan ta soma kwarewa wajen nuna wasanni.

A yanayin kaka na shekarar 1946, ta bar kungiyar nuna wasannin kwaikwayo daga birnin Zhangjiakou, ta shiga cikin kungiyar nuna wasannin fasaha ta hadadiyyar jami'ar arewacin kasar Sin, ta soma aikin nuna sabbin wasannin kwaikwayo.

A shekarar 1947, Guo Lanying ta shiga karatu da nuna wasanni a sashen koyar da ilmin wasannin kwaikwayo na hahadiyyar jami'ar arewacin kasar Sin. A watan Augusta na shekarar 1948, ta kaura zuwa kungiyar farko ta nuna wasannin fasaha ta jami'ar. Ta taba nuna wasannin kwaikwayo da suke hada da " Wang Da Niang Gan Ji" wato ma'anar wasan nan ta bayyana yadda tsohuwa mai suna Wang ta tafi kasuwa da wata waka daban da ake kira " Fu Qi Shi Zi", ma'anar sunan wakar ita ce, wani namiji da matarsa suna karatu, da "Xiong Mei Kai Huang", ma'anar sunan wakar ita ce, wa da kanwarsa suna kyautata sauruka da dai sauran wasannin kwaikwayo, saboda haka ta sami maraba daga wajen jama'ar farar hula. A watan Afril na shekarar 1949, ta tafi kasar Hungary tare da kungiyar samari ta kasar Sin don shiga shagali na biyu na murnar samun zaman lafiya da zumunci a tsakanin samarin duniya, inda ta rera wakar da ke da lakabi haka: " wakar nuna 'yancin kan mata", kuma ta sami lambar yabo.

Bayan kafuwar sabuwar kasar Sin a shekarar 1949, bi da bi ne Guo Lanying ta zama babbar yar wasa a tiyatar nuna wake-wake da raye-raye da ke karkashin kolejin koyar da ilmin wasannin kwaikwayo na tsakiya na kasar Sin da tiyatar yin gwajin wake-wake da wasannin kwaikwayo ta kasar Sin da tiyatar nuna wasannin kwaikwayo ta hanyar wake-wake da raye-raye ta kasar Sin, kuma ta zama mambar kwamitin duk kasa na hudu na hadadiyyar kungiyar mawallafa na kasar Sin da 'yar majalisar wake-wake da kide-kide ta kasar Sin ta biyu da ta uku. Ta zama babbar 'yar wasa a cikin sabbin wasannin kwaikwayo na zamani kamar su: "Yarinya mai farin gashin kai" da yarenmu ake cewa "Bai Mo Nu" da wata jarumar da ake kira "Liu Hu Lan" da "Aladun yanayin bazara" wato da yarenmu ake kira "Chun Lei" da "Hong Xia" da "Xiao Er He ya yi Aure" wato da yarenmu ake cewa "Xiao Er He jie Hun" da "Dou E Yuan" wato rashin adalci da aka yi wa wata mace da dai sauransu, ta kago samfurori iri iri na 'yan wasannin fasaha a jere da suke burge mutane sosai kamar su "Xi Er" da "Xiao Qin" da "Liu Hu Lan" da sauransu. Saboda haka ta sami maraba sosai daga wajen dimbin jama'a, ta zama daya daga cikin 'yan wasa da suke iya wakiltar sabbin wasannin kwaikwayo na kasar Sin. Bisa matsayin manzon musamman na nuna wasannin fasaha na kasar Sin ne ta taba kai ziyara a tsohuwar Tarayyar Soviet da Romaniya da Poland da tsohuwar kasar Czechoslovakia da Yogoslaviya da Italiya da Japan da sauran kasashe 13, ta ba da gudumuwa ga ma'amalar al'adu a tsakanin kasar Sin da kasashen waje.

A shekarar 1982, zabiya Guo Lanying ta yi ban kwana da dakalin nuna wasanni, ta je aikin koyarwa a kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na kasar Sin. A shekarar 1986, ta kafa makarantar koyar da ilmin wasannin fasaha ta Guo Lanying a lardin Guangdong, ta dau mukamin shugabar makarantar . A shekarar 1989, ta sami lambar yabo ta faifan zinariya da aka samar a karon farko.

Zabiya Guo Lanying tana da makogwaro mai muryar dadin ji sosai, kuma ta bayyana kalmomin wakoki sosai, sa'anan kuma ta kware sosai wajen bayyana halayen musamman na wakokin gargajiyar kasar Sin . Dayake ta taba samun horo mai tsanani wajen bayyana wasannin kwaikwayo tun daga lokacin da take karama, shi ya sa ta kware sosai wajen nuna wasannin fasaha, ta kai babban matsayin rera wakoki da nuna fasahar wasanni , ta ba da gudumuwa ga kafa da kuma raya tsarin nuna sabbin wasannin rera wakoki da nuna wasannin fasaha a kasar Sin. Wakokin da ke iya wakiltar ta su ne, "Fu Nu Zi You Ge" wato "wakar murnar 'yancin mata" da "Wata tsohuwa mai suna Wang tana neman zaman lafiya" da " Bayyana godiya bayan da aka sami 'yanci" da "Nan Ni Wan" da " Xiu Jin Bian" da wata waka mai suna "Kasar mahaifiyata" da ke cikin sinima mai suna "Shang Gan Lin", da wata wakar da ke da lakabi haka " Magudanar ruwa layi layi da tsaunuka layi layi" wato da yarenmu ake cewa, " Yi Dao Dao Shui Lai Yi Dao Dao Shan", ta rera wakar nan ne a cikin wata sinima mai suna "Liu Hulan" da dai sauransu.(Halima)

Zhang Ye

Zhang Ye , garinsu a lardin Hunan, zabiya ce da ke da karfi sosai wajen rera wakokin gargajiyar kasar Sin. A shekarar 1991, Zabiya Zhang Ye ta kammala karatu a sashen koyar da ilmin rera wakoki na kolejin wake-wake da kide-kide na kasar Sin, ta bi sawun mashahurin shehun malami Jin Tielin mai koyar da ilmin wake-wake da kide-kide a kasar Sin, a shekarar 1995, ta sami digiri na biyu wajen koyon ilmin rera wakoki, yanzu ta zama malamar koyarwa ta sashen koyar da ilmin rera wakoki na kolejin koyar da wake-wake da kide-kide na kasar Sin.

A shekarar 1988, a lokacin da zabiya Zhang Ye ta hau dakalin rera wakoki ba da dadewa ba, ta sami zama ta uku a gun gasar cin babbar lambar yabo ta shirye-shiryen TV a tsakanin samari mawaka na duk kasar Sin da sakamako mai kyau na samun lambar zinariya a gun gasar da ke tsakanin nagartattun mawaka na duk kasar Sin bisa gayyatar da aka yi musu. A shekarar 1990, a gun gasar cin kofin "Hui Tong" don sake waiwayon wakoki masu kyau kuma masu dadin ji sosai da aka rera daga shekarar 1980 zuwa shekarar 1990 a gidan rediyo mai hoto na birnin Beijing wato BTV, ta sami babbar lamba da ke da lakabi haka: "Zabiya da na fi kaunarta". A shekarar 1992, ta kuma samu lambatu a gun gasar cin kofin halittu wato lambar da ke da lakabi "mawakan da 'yan kallo suke kaunarsu" wadda gidan rediyo na tsakiya na jama'ar Sin ya shirya. A shekarar 1995, a shagalin dare na murnar bikin yanayin bazara na gargajiyar kasar Sin da CCTV ya shirya , ta rera wata wakar da ke da lakabi haka: "Kome ya yi daidai yadda ya kamata" wato "Wan Shi Ru Yi" cikin Sinanci. A wannan shekara kuma, ta sami lambar yabo da ake cewa " Faifan zinariya" . Ta kuma sami lambar azurfa wajen gasar rera waka mai suna " Duo Qing De Dong Jiang Shui" domin shirye-shiryen MTV na karo na hudu da aka shirya. Sa'anan kuma ta sami lambar zinariya a gun gasa ta biyar ta cin kofin "Kang Jia" domin shirye-shiryen MTV, wakar da ta rera a gun gasar ita ce "Shiga cikin sabon zamani" wato "Zou Jin Xin Shi Dai" cikin Sinanci.

A lokacin da ta ke karatu da kuma nuna wasannin rera wakoki, zabiya Zhang Ye ita ma ta zama babbar 'yar wasa da ake kira "Jiu Niang" a cikin sinimar TV da ake kira "Tang Bohu da Shen Jiuniang", sa'anan kuma ta dauki muryar wakoki domin wasan kwaikwayo mai suna " Hong Hu Chi Wei Dui" wato jan rundunar soja a wani tafkin Honghu, ta zama 'yar wasa mai suna "Han Ying" , ta kuma shiga nuna wasan kwaikwayo mai suna "Xiao Er He Jie Hun" wato wani saurayi mai suna Xiao Erhe ya yi aure , a cikin wasan, ta zama 'yar wasa mai suna "Xiao Qin". Ban da wadannan kuma , ta taba daukar muryar wakoki domin sinima da wasannin kwaikwayo na shirye-shiryen TV da yawa. Ta taba kai ziyara a kasar Ingila da Faransa da Switzerland da Jamus da Sweden da Belgium da Luxembourg da Japan da kasashe daban daban na kudu maso gabashin Asiya da Hongkong da Macao, ta sami karbuwa da kauna sosai daga wajen 'Yan kallo da masu sauraro na gida da na waje sosai da sosai.

Zabiya Zhang Ye ita ma ta kware wajen rera wakokin kabilu daban daban na kasar Sin da ke da halayen musamman iri daban daban, ta rera wakoki bisa abubuwan da ake son a bayyana ba tare da abin da bai dace da wakokin ba, muryarta na da dadin ji sosai tare da tashi da sauyaya rai . wani mai ba da sharhi kan wakarta ya bayyana cewa, muryar wakar da ta rera tana tamkar yadda tsabtaccen ruwa ya ke malala daga tsaunukan da kankara mai taushi ke rufawa, na da daji da gamshi da tsabta sosai da sosai.(Halima)

Wu Bixia

Zabiya Wu Bixia ita ce mai rera wakoki tare da dagaggen sauti na irin salon da ake kira "Coloratura" a kasar Sin. An haife ta a birnin Changde na kasar Sin. A lokacin da ta kai shekaru 12 da haihuwa, ta soma nuna wasannin rera wakoki a dakalin wasanni. A lokacin da take karatu a kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na kasar Sin don neman digiri na farko da na biyu, kuma ta hanyar horon da aka yi mata wajen kara ilmin rera wakoki da kuma yin koyo da bincike kan wakoki da yawa daga sauran mutane tare da hazikanci da bajinta da ta yi , a sa'I daya ne ta sami bambancin hanyoyi guda biyu wajen rera wakokin gargajiyar kasar Sin da na kasashen waje, kuma ta kware sosai wajen rera irin wadannan wakoki.

A shekarar 1993, zabiya Wu Bixia ta taba samun lambar yabo ta azurfa a gasar rera wakoki da hadadiyyar kungiyar masu wake-wake ta kasar Sin da ma'aikatar al'adu ta kasar Sin suka shirya cikin hadin guiwa. Sa'anan kuma a shekarar 1993 , ita kanta ta dauki murya a cikin faifanta na farko da ke da lakabi "Yarinya ta kasar Sin" domin kamfanin sinima da wakoki na tekun Pasific. Sa'anan kuma, ta sami lambawan wajen rera wakar gargajiyar kasar Sin a gasar rera wakoki ta duk kasa a shekarar 1996 da kuma zama lambawan wajen gasar rera wakoki ta farko da kasar Sin ta shirya a tsakanin kasa da kasa har da lambawan a gasa ta karo ta 8 da aka shirya don rera wakoki a tsakanin kasa da kasa da aka shirya a Bicbao na kasar Spain da lambatu wajen gasar rera wakoki a tsakanin kasa da kasa da aka shirya a Moniuszko na kasar Poland. A gun gasar rera wakoki a tsakanin kasa da kasa kan Tchaikovsky, wato wanda ake kira gasar da cewa wai "Olimpic" ne wajen rukunin wake-wake da kide-kide na kasashen duniya, zabiya Wu Bixia ta sami lambatu wajen rera wakoki, muryarta da fuskarta da ke da murmushi tamkar yadda mala'ika ake yi sun sake tabbatar da matsayin mawakan kasar Sin a duniya.

Tun daga shekarar 2000 har zuwa yanzu, Zabiya Wu Bixia ita kanta ta shirya wasannin rera wakoki ita kadai sau da yawa a birnin Beijing da lardin Hunan na kasar Sin da kasar Singapoure da sauran wurare , kuma ta fitar da fayafayen da ita kanta ta dauki murya a ciki da yawa , sa'anan kuma ta yi hadin guiwa da mashahuran masu tsara kide-kide da masu ba da jagoranci ga kungiyar makada da masu kada kayayyakin kida da kuma kungiyoyi fiye da goma na yin sana'ar musamman ta wake-wake da kide-kide na gida da na waje don nuna wasannin rera wakoki, kamar a watan Mayu na shekarar 2001, bisa gayyatar da kwamitin shirya wasannin rera wakoki na tsakanin kasa da kasa da gidan rediyo mai hoto na kasar Spain suka yi mata ne, ta shiga shagalin nuna wake-wake da kide-kide na Gala Lirica da aka shirya a Madrid. A watan Disamba na shekarar 2001, bisa gayyatar da kwamitin kula da harkokin rera wakoki na kasashen duniya da dakunan nuna wasannin kwaikwayo da ake kira " Arriaga" suka yi mata ne, ta yi nasarar zama babbar yar wasa da ke cikin wasan kwaikwayo mai lakabi "Rigoletto" , a shekarar 2002, bisa gayyatar da cibiyar nuna wasannin fasaha ta Binhai ta kasar Singapoure ta yi mata ne, ta zama 'yar wasa da ke bayyana wata gambiya a cikin wani wasan kwaikwayo, sa'anan kuma ta nuna wasannin zamani da yawa, duk ta sami babbar nasara.

Nasarar da ta samu wajen nuna wasanni ta jawo hankulan kafofin watsa labaru na gida da na waje da yawa, Gidan Rediyo mai hoto na tsakiya na kasar Sin wato CCTV na kasar Sin ya shirya shirye-shiryen musamman da suka shafe ta sau da yawa, jaridun kasar Spain sun bayar da bayani cewa, muryarta tamkar wata muryar da ta sauko daga sararin samaniya, kafofin watsa labaru na kasar Rasha sun bayyana cewa, ita ce mala'ikar rera wakoki da ta zo daga gabashin duniya. Jaridar "Ren Min Ri Bao ta kasar Sin da wata jaridar kasar Singapoure da wata mujallar mako mako kan takara ta kasar Faransa da sauran kafofin watsa labaru su ma sun bayar da bayanan musamman dangane da zabiya Wu Bixia.(Halima)

Cheng Zhi

Cheng Zhi shi ne mashahurin mawaki na kasar Sin da ke rera wakoki tare da daggagen sauti, kuma mamban hadadiyyar kungiyar masu wake-wake da kide-kide ta kasar Sin, sa'anan kuma shi ne dan wasa da ke bisa matsayin farko a kungiyar wake-wake da raye raye ta sashen siyasa na rundunar sojan suncin jama'ar kasar Sin. An haife shi a shekarar 1946. A shekarar 1962, ya shiga rundunar sojan suncin jama'ar kasar Sin, a shekarar 1965, ya shiga cikin kungiyar wake-wake da raye-raye ta rundunar sojan suncin jama'ar kasar Sin, a shekarar 1983 ya kammala karatu a sashen koyar da ilmin wasannin kwaikwayoi na kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na tsakiya na kasar Sin, ya bi sawun shehun malamim koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na kasar Sin Mr Shen Xiang .

Mr Cheng Zhi ya kware sosai wajen rera wakoki tare da daggagen sauti da tashi da sanyaya rai , kuma kalmomin da ke cikin wakokin da ya rera suna bayyanu sosai da sosai, kai , yana da makokwaro mai muryar dadin ji sosai, sa'anan kuma ya kware sosai wajen rera wakoki ta hanyar yin amfani da dabarar "bel canto" ta gargajiya ta kasar Italiya ,ya iya sarrafa muryarsa, ba ma kawai ya iya rera karin wakokin da ake kira " Operatic solo" na kasashen yamma ba, hatta ma ya kware wajen rera wakokin gargajiyar kasar Sin ta hanyar dabarar kimiyya da fasaha , ya taba zama babban dan wasa a cikin wasan kwaikwayon da mashahurin mai tsara wake-wake da kide-kide na kasar Sin Mr Shi Guangnan ya wallafa da ke da lakabi haka "Shang Shi".(Mr Shi Guangnan ya riga ya rasu.) Ba sau daya ba ba sau biyu ba Mr Cheng ya zama mawakin da ke rera wakoki shi kadai a cikin wasanni har ma ya zama babban mawaki wajen rera wakoki cikin yin hadin guiwa da sauran mawaka, ya sami karbuwa da yabo sosai da sosai daga wajen kwararru da masu sauraronsa da 'yan kallonsa.

Wata zabiya Bevery.Bechi wadda take daya daga cikin shahararrun zabiyoyi goma da ke rera wakoki tare da daggagen sauti na duniya kuma shumagabar dakin wasannin kwaikwayo ta birnin New York na kasar Amurka ta yaba masa cewa, shi ne mawakin da ke rera wakoki tare da daggagen sauti da ba a kan samu ba. Wani mashahurin malamin koyar da ilmin rera wakoki kuma mawakin kasar Italiya da ke rera wakoki tare da matsakaicin sauti Mr Gino .Bechi ya yaba masa cewa, shi ne mawakin da ke rera wakoki tare da daggagen sauti kuma ba safai a kan samu kamarsa ba, wakokin da ya rera wakoki ne na Bel Canto na kasar Italiya na gaskiya. Wata jaridar kasar Amurka ta bayar da bayani a cikin kundinta don nuna masa yabo sosai da sosai da cewa, a cikin 'yan shekaru da yawa, da wuya ake samun damar saurarar irin wannan daggagen sautin a cikin wakokin da mawaki ya rera, makokwaronsa na da muryar dajin ji sosai tare da sabon salo da sauran halayen musamman, wannan kalubale ne da ya zo daga bangaren Gabas wajen da'irar rera wakoki ta duniya.

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, sau da yawa ne Mr Cheng Zhi ya kai ziyara a wurare daban daban na duniya bisa matsayin dan wasannin fasaha na kasar Sin, kuma bi da bi ne ya shirya wasannin rera wakoki shi kadai a birnin Beijing da Shanghai da Kwangzhou da Shenzhen da Hongkong da sauran wurare, ya yi suna sosai a da'irar rera wakoki na zamanin yau bisa kwarewarsa da makokwaronsa mai dadin ji sosai.

Song Zuying

Song Zuying tana daya daga cikin ,yan mata masu rera wakoki da ke da karfi sosai a zamanin yau na kasar Sin.

An haifi zabiya Song Zuying a ran 27 ga watan Yuni na shekarar 1966 a wani kauyen kabilar Miao da ke da iyalai guda uku kawai a gundumar Guzhang ta lardin Hunan na kasar Sin. A watan Yuli na shekarar 1981, Song Zuying ta kammala karatu a makarantar sakandare. A wannan shekarar, wata kungiyar wasan kwaikwayo ta gundunar Guzhang ta dauki 'yan wasa, a wancan lokaci, mahaifin Son Zuying ya rasu ba da dadewa ba, amma ta hakurin da bakin ciki na rasuwar mahaifnta, ta je wurin yin jarrabawa. Bayan wata guda, kungiyar wasannin kwaikwayo ta gudumar ta dauke ta. Sa'anan kuma, Song Zuying ta canja wurin aiki ta tafi kungiyar wake-wake da raye-waye ta kabilar Tujia da ta Yao. A lokacin da bai kai shekara daya ba ne, zabiya Song Zuying ta ci jarrabawar shiga cikin sashen koyar da ilmin wake-wake da raye-raye na kolejin kananan kabilu na tsakiya na kasar Sin, a shekarar 1987, ta kammala karatu a kolejin. A watan Oktoba na shekarar 1988, kungiyar wake-wake da kide-kide ta kasar Sin ta shirya gasar cin kofin Jinlong a tsakanin masu rera wakoki ta duk kasa bisa gayyatar da aka yi musu a birnin Changsha na kasar Sin, Song Zuying ta sami lambar yabo ta zinariya wajen rera wakar da ke da lakabi haka "A Ge Mo Zou", ma'anar wakar ita ce, "wana, kada ka bar ni" wadda ke da halayen musamman na kabilar Miao, mashahurin mai ba da ilmin wake-wake na kasar Sin Mr Jin Tielin wanda daukar nauyin yin alkalanci a inda ake yin gasar, ya dauke ta don ta zama dalibarsa. Sa'anan kuma, a wani shagalin dare da gidan rediyo mai hoto na tsakiya na kasar Sin wato CCTV ya shriya don murnar ranar bikin gargajiyar kasar Sin, wato bikin yanayin bazata, Son Zuying ta yi suna sosai saboda wakar mai suna "Xiao Bei Lou" wato (Wani karamin kwando da aka dauke goya wa a bayan ) da ta rera. A shekarar 1991, ta shiga cikin kungiyar wake-wake da raye-raye ta sashen siyasa na rundunar sojojin ruwa ta suncin jama'ar kasar Sin, yanzu ta zama 'yar wasa da ke bisa matsayin farko na kasar Sin, kuma tana samun alawas na musamman daga wajen majalisar gudanarwa ta kasar Sin.

Son Zuying tana da makogwaro mai dadin murya kuma mai dadin ji. Tana nacewa ga bin wake-wake da kide-kiden gargajiyar kasar Sin, sa'anan kuma ta mayar da dabarar rera wakokin "bel canto" wajen rera wakoki ta hanyar kimiyya da fasaha, lokacin da ta rera wakoki, tana fahimtar wakokin da ta rera bisa daidaici , kuma tana hade da murya da abubuwan da ta ji a zuciya, saboda haka ta kafa halayen musamman nata na kanta wajen rera wakoki.

Wakokin da Son Zuying ta rera kamar su "Xiao Bei Lou" da "La mei Zi" da "Hao Ri Zi" da "Ai Wo Zhong Hua" da "Da di Fei Ge" da Dong Xi Nan Bei Zhong" da "Bing Ge ge" da "Zhang Da Hou Wo Jiu Cheng Le Ni"da dai sauransu suna yaduwa a tsakanin jama'ar Sin da rukunonin masu magana da harshen Sinanci da ke da zama a kasashen waje. Masu tsatsauran kishin wakokinta suna ko'ina na birane da kauyuka da tsaunuka masu rufe da kankara mai taushi da kauyukan da ke iyakar kasa da sauran wuraren da kabilu daban daban na kasar Sin suke.

A shekarar 2000, hadadiyyar kungiyar al'adu da fasaha ta kasar Sin ta rada mata suna da cewa "Tagari ta kowa wajen fasaha da halin mutumtaka. A wannan shekara kuma ta sami lambar yabo mafi kyau wajen rera wakokin gargajiyar kasar Sin na Sinawan da ke kasashen ketare. A shekarar 2002, ta shirya wasannin rera wakoki ita kanta a tiyatar da ake kira "Sydney Opera House", a shekarar 2003, ta shirya irin wasannin rera wakoki ita kadai a gidan da ake kira "Golden Concert Halla" na Viena , duka kuma ta sami nasara.(Halima)

Jiang Dawei

An haifi Jiang Dawei a shekarar 1947 a birnin Tianjing na kasar Sin. Shi ne mashahurin mawaki na kasar Sin. tun daga lokacin da yake karami, yana kaunar wake-wake da kide-kide da kuma zane-zane. A shekarar 1968, ya je kauyukan da ke karkarar birnin Huhehaote na kasar Sin don karbar horon da aka yi masa, a shekarar 1970, ya shiga kungiyar nuna wasannin fasaha ta 'yan sanda na kurmin kasar Sin.

A shekarar 1975, ya shiga cikin kungiyar nuna wasannin wake-wake da raye-rayen gargajiyar kasar Sin ta tsakiya ta birnin Beijing bisa matsayin dan wasa. A wannan lokaci, ya taba zama shugaban kungiyar da kuma shugaban kungiyar yin wasannin kide-kiden da ake kira "Light Music" ta kasar Sin.

Jiang Dawei shi ne mashahurin mawakin kasar Sin da ke rera wakoki tare da daggagen sauti , ya kware sosai wajen ilmin wake-wake da kide-kide. Wakokin da ya rera na da dadin ji sosai tare da sahihiyar zuciyarsa. Kuma wakokinsa sun sami karbuwa da kauna sosai daga wajen jama'ar kabilu daban daban na kasar Sin.

A cikin shekara da shekaru, yawan wakokin da ya rera da kuma muhimman wakokin da ya rera a cikin sinima da shirye-shiryen TV ya wuce dubu. Wakokin da ya rera kamar su "Zai Na Tao Hua Sheng Kai De Di Fang" wato "A wurin da furannin peach suka bude" da "Wakar Furen Peony" da "Hawan doki don kare kasar mahaifa" da "Ko a iya tambayar mafitar hanya?" da "Yanayin bazara na arewacin kasar Sin" da sauransu dukkansu sun yadu ko'ina a kasar Sin , kuma kamar a ce kowa ya taba saurarar wakokin da ya rera da kuma kowa ya taba rera wakokinsa.

Mr Jiang Dawei ba sau daya ba ba sau biyu ba ya kai ziyara a kasar Amurka da Canada da Japan da Jamus da Singapore da Tailand da sauran kasashe da jihohi don nuna wasannin rera wakoki, ya sami yabo sosai daga wajen masu sauraro da 'yan kallo.

Wakokin da ke iya wakiltarsa su ne wakar da ke da lakabi "A wurin da furannin peach ya bude" da "Wakar Furen Peony" da wakar "Ko a iya tambayi mafitar hanya?".(Halima)

Zhou Xiaoyan

An haifi malama Zhou Xiaoyan a shekarar 1918, ita ce zabiya mai rera waka tare da dagaggen sauti ta irin salon da ake kira "Coloratura" a kasar Sin kuma ita ce mai aikin ba da ilmin tarbiyya. Sa'anan kuma ita ce Shehiyar malamar kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na birnin Shanghai a duk tsawon rayuwarta a duniya.

An haifi malama Zhou Xiaoyan ne a wani iyalin masana'antu da kasuwanci na birnin Wuhan na lardin Hubei na kasar Sin. Mahaifinta mai suna Zhou Changguo shi ne mai aikin masana'antu da ke da tunani mai ci gaba sosai . Yana kaunar wake-wake da kide-kide sosai da sosai, dayake ta sami tasiri daga wajen mahaifinta , shi ya sa tun daga lokacin da take karama, ta nuna sha'awa sosai da sosai ga wake-wake da kide-kide.

A watan Satumba na shekarar 1935, ta ci jarrabawar shiga cikin makarantar musamman ta koyar da ilmin wake-wake da kide-kide ta Guo Li ta birnin Shanghai musamman domin koyon ilmin rera wakoki. A shekarar 1937 ne, an barke da yakin kin harin Japan a kasar Sin, don haka Malama Zhou Xiaoyan ya zama tilashi ne ta katse karatunta, ta koma garinsu.

A karshen shekarar 1938, Zhou Xiaoyan ta yi hakuri da wahaloli da yawa ta tafi birnin Paris na kasar Faransa, inda ta kara da wani mashahurin mai tsara kide-kide, bisa taimakonsa ne ta shiga kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kiden kasar Rasha na birnin Paris a watan Oktoba na shekarar 1945, bayan shekaru 7 da ta jure wahaloli da yawa, a karshe dai ta rera wakoki a dakalin nuna wasannin wake-wake da raye –raye na babbar tiyatar kasa ta birnin Paris. Kodayake wannan karo na farko ne, amma ta burge 'yan kallo na kasar Faransa bisa fasahohinta masu kyau sosai tare da makogwaro mai dadin murya. Sa'annan kuma malama Zhou Xiaoyan ta tafi kasar Czech bisa gayyatar da aka yi mata don halartar wasannin wake-wake da kide-kide na bayyana yanayin bazara na birnin Prague. Malama Zhou Xiaoyan ta sami babbar nasara, ana kiranta da cewar wai wata tsuntsa ce da ake kira "Nightingale" ta kasar Sin.

A watan Oktoba na shekarar 1947, Zhou Xiaoyan ta komo gida tare da niyyarta ta bauta wa kasar mahafa, a wancan lokaci, kasar Sin tana karkashin mulkin jam'iyyar Guomindang., jama'ar kasar Sin suna ci gaba da fama da mawuyacin zaman rayuwa, duk wadannan sun sa malama Zhou Xiaoyan ta yi bakin ciki sosai da sosai, ta tafi ko'ina a kasar Sin domin rera wakoki ga dalibai masu neman ci gaba.

A shekarar 1949, sabuwar kasar Sin ta kafu, malama Zhou Xioyan ta yi farin ciki da shiga cikin sabon zaman rayuwa, an dauke ta don ta zama malamar koyarwa ta sashen koyar da ilmin rera wakoki na kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na birnin Shanghai. Ta soma zaman rayuwar ba da ilmi ga dalibai.

A lokacin da aka yi babban tawayen al'adu a shekaru goma da suka wuce a kasar Sin, malama Zhou Xiaoyan ta kasance cikin hali mai duhu, a cikin wadannan shekaru goma da suka wuce, ba ta iya rera wakoki ba, kuma ba ta iya yin aikin koyarwa yadda ya kamata ba, amma tana nacewa ga sha'aninta na rera wakoki bisa sanadiyar kaunarta. Mashahurin mawaki mai suna Wei Song shi ne dalibinta da ta horar da shi a lokacin tawayen al'adu da aka yi a kasar Sin. Yanzu, kwararrun fannin rera wakoki na kasar Sin da na waje sun yi sharhi cewa, dan wasa Wei Song ya kai matsayin duniya wajen rera wakoki.

Bayan da aka kawo karshen tawayen al'adu a kasar Sin, Zhou Xiaoyan ta ci gaba da horar da dalibai. A shekarar 1984, a gun gasar rera wakoki a tsakanin kasa da kasa a birnin Viena, dalibanta guda hudu sun sami lambobin zinariya guda uku tare da wata azurfa daya. Sakamakon nan ya sa rukunonin kasa da kasa sun yi mamaki sosai.

Domin farfado da sha'anin nuna wasannin kwaikwayo na kasar Sin da kuma horar da 'yan wasa na wannan fannin da kuma kara ma'amala da hadin guiwa wajen nuna wasannin wake-wake da kide-kide da al'adu a tsakanin kasa da kasa, a watan Mayu na shekarar 1988, Zhou Xiaoyan ta kafa cibiyar wasannin kwaikwayo ta Zhou Xiaoyan a cikin kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na birnin Shanghai. A shekarar 1989, cibiyar ta soma shirya wasan kwaikwayo da ake cewa "Riboletto", kuma ta sami nasara wajen nuna wasan.

A cikin shekaru fiye da 50 da suka wuce, mawaka da shehiyar malama zhou Xiaoyan ta yi musu horo sun sami yabo domin kasa mahaifa a gasanin da aka yi a tsakanin kasa da kasa. Daga cikinsu da akwai daliban da suka riga suka nuna wasannin a babbar tiyatar da ake kira "Metropolitan Opera" ta kasar Amurka da kuma babbar tiyatar da ake kira "San Fransisco Opera", kuma sun zama manyan 'yan wasa. Zhou Xiaoyan ta horar da kwararru masu yawan gaske, wasu suna ba da ilmi a jami'o'I na kasar Sin, wasu suna rera wakoki a dakalin kasashen duniya, wasu ma sun zama lambawan a gasannin da aka shirya a gida da waje, kamar su Mr Liao Changyong da Mr Zhang Jianyi da Gao Manhua da dai sauransu.(Halima)

Hu Songhua

An haifi Hu Songhua a shekarar 1930 a wani gidan kabilar Man ta kasar Sin da ke birnin Beijing. Ya yi suna ne a lokacin da yake saurayi saboda wakokin da ya rera , kamar su "Sen Ji De Ma" da "Feng Shou Zhi Ge". Daga shekarar 1952, ya shiga nuna wasanni a cikin kungiyar wake-wake da raye-raye na gargajiyar kasar Sin ta tsakiya ta kasar Sin.

Tun tuni, wakokin kananan kabilu na kasar Sin sun jawo hankulan Mr Hu Songhua sosai.

A shekarar 1952, ana bukatar wani mawakin da zai rera wata wakar kabilar Mongoliya a cikin wasannin nuna wake-wake da raye-raye da ke da lakabi haka " Dong Fang Hong", dawainiyar nan an dora wa Mr Hu Songhua wanda ke fahimtar zaman rayuwar 'yan kabilar Mongoliya. Mr Hu Songhua ya waiwayi zaman rayuwar da ya yi a makiyayar da yake kauna sosai da sosai, ya yi amfani da dabarar musamman da 'yan kabilar Mongoliya suke yi wajen bayyana abubuwan da suka gani suka ji, ya rera wata waka mai suna "Zan Ge" wato wakar nuna yabo.Wakar nan ta jawo sha'awa sosai da karbuwa daga wajen masu sauraro da 'yan kallo dubu dubai, kuma har zuwa yanzu ana rera wakar nan, kuma ta zama wakar da ke iya wakiltar wakokin da Mr Hu Sonhua ya rera.

Sa'anan kuma, Mr Hu Songhua ya kuma zama babban dan wasa mai suna Ashar a cikin wasan kwaikwayo da ake kira "A Yi Gu Li", har ma ya taba daukar muryar wakoki tamkar yadda babban dan wasa mai suna A He ya rera a cikin sinimar "A shi Ma", sa'anan kuma ya dauki muryar wakokin da mashahurin mai tsara wakoki Shi Guang Nan ya tsara tamkar yadda babban dan wasa mai suna Da Ga ya rera a cikin sinimar "Shen Qi De Lu Bao Shi", kuma ya taba daukar muryar wakoki domin sinimar da ake kira "Lei Feng" da "Kasar Mahaifa, mahaifiyata" da sauran sinima fiye da 30.

A shekarar 1992, Mr Hu Songhua shi kansa ya shirya kungiyar masu daukar sinima don bayyana halayen musamman na nuna wasannin wake-wake da kide-kiden gargajiyar kasar Sin har kashi 12 , sinimar din nan na da lakabi haka " Chang Ge Wan Li Xing". Shi kansa ya dau nauyin babban direktan sinimar da babban mai sa ido kan aikin daukar sinima da babban mawaki da babban dan wasa, matarsa ita ce shaharariyar mai raye-raye kuma mai suna Zhang Man Ru ta zama babbar mai tsara shirin sinima da fasalin sinima. Sinimar ta bayyana fasaha mai kyau na kananan kabilun kasar Sin, saboda haka ta sami karbuwa sosai daga wajen dimbin 'yan kallo.

A cikin 'yan shekaru da yawa da suka wuce, Mr Hu Songhua ya taba tattara wakokin kananan kabilu fiye da 40 na kasar Sin, ya sami malaman koyarwa wajen koyon fasahohi, a kai a kai ne ya sami halayen musamman nasa na kansa na rera wakoki tare da daggagen sauti mai dadin ji sosai da sosai.

Wakokin da ya rera kuma ya iya wakiltarsa su ne wakar "Zan Ge" da wakar "Yi Duo Xian Hua Xian You Xian" da sauransu.

[Masu kide kide]

Wang Ciheng

Mr Wang Ciheng shi ne mashahurin mai busa sarewa na kasar Sin. Yana daya daga cikin mutanen da suke yunkurin aiki a dakalin wake-wake da kide-kiden gargajiyar kasar Sin. Yanzu ya zama mamban kungiyar masu wake-wake da kide-kide ta kasar Sin da mamban kungiyar masu kada kayayyakin da aka yi da tsirkiyoyi na gargajiyar kasar Sin da mamban kungiyar yin nazari kan kide-kiden da aka kada ta hanyar yin amfani da kayayyakin kidan da aka yi da tsirkiyoyi ta kasar Sin da mai busa sarewa shi kadai a cikin wasanni na kungiyar wake-wake da kide-kiden gargajiyar kasar Sin ta tsakiya ta kasar Sin.

An haifi Wang Ciheng a shekarar 1959 a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang na kasar Sin, tun daga lokacin da ya zama saurayi, ya soma bin sawun mashahurin mai busa sarewa Mr Zhao Songting don koyon busa sarewa, sa'anan kuma a sa'I daya ne ya ci jarrabawar shiga kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na tsakiya na kasar Sin da na birnin Shanghai. Bayan zaben da ya yi ,ya shiga kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na tsakiya na kasar Sin a shekarar 1980, ya bi sawun mashahurin mai busa sarewa Mr Zeng Yongqing. Ya kuma sami horo daga wajen mashahurin masanin tarihin wake-wake da kide-kide da mai aikin wake-wake da kide-kiden gargajiyar kasar Sin kuma mai ba da ilmin kayayyakin kidan gargajiyar kasar Sin , wato shehun malami Lan Yusong a fannoni da yawa. A shekarar 1984, ya kammala karatu a kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na tsakiya na kasar Sin. Sai ya shiga cikin kungiyar wake-wake da kide-kiden gargajiyar kasar Sin ta tsakiya ta kasar Sin don yin aikin busa sarewa shi kadai a cikin wasanni . a lokacin, ya kuma sami taimako daga wajen mashahurin mai busa sarewa na rukunin arewacin kasar Sin Mr Wang Tiechui da mashahurin mai busa sarewa na kudancin kasar Sin Mr Lu Chunling. Bisa kokarin da ya ke yi ba tare da kasala ba, ya kware sosai wajen daidaita karin wake-wake da kide-kide da muryoyinsu, shi ya sa ya bayyana halayen gargajiya na arewa da na kudu na kasar Sin gu daya sosai.

Wasannin kide-kiden da Mr Wang Ciheng ya busa ta hanyar yin amfani da sarewa na da dadin ji sosai da sosai tare da tashi da sauyaya ran mutane, yana kan halartar manyan aikace-aikacen nuna wasannin wake-wake da kide-kide da aikin busa sarewa shi kadai , kamar wasannin da ake shirya da ke da lakabi haka: "Muryar wadatar da kasar Sin" da "Muryar farfado da wake-wake da kide-kiden gargajiyar kasar Sin" da dai sauransu, kuma ya sami yabo daga wajen datijjan rukunin wake-wake da kide-kide na kasar Sin wato Mr Lu Ji da Mr Li Huanzhi da Mr Shi Lemong da dai sauransu. Sa'anna kuma ya yi hadin guiwa da masu tsara kide-kide sosai , ya tsara sabbin kide-kide da yawa, kuma karo na farko ne ya kago sabbin fasahohin busa sarewa, wato "Kaqiang" da "Gunzou", har ma ya yi yunkurin yin amfani da fasahar busa sarewa na rukunin arewacin kasar Sin wajen busa sarewa da tattausan murya .

Bisa fasaha mai kyau kuma mai zurfi da ya samu wajen busa sarewa, Mr Wang Ciheng ya sami lambobin yabo sau da yawa a gasannin wake-wke da kide-kiden da aka yi a cikin gida da waje. daga cikinsu, wani kidan sarewa da ya tsara a shekarar 1982 mai suna "San Yuan Chun" ya sami lambar yabo ta uku daga kolejin koyar da wake-wake da kide-kide na tsakiya na kasar Sin a fannin kide-kiden gargajiyar kasar Sin, da kuma wani kidan sarewa da shi kadai ya busa bisa gayyatar da aka yi masa ya sami lambawan a gun gasar nuna wasannin kide-kiden lardin Kwangdong na kasar Sin da aka shirya a karo na farko a shekarar 1987. A gun gasar farko da aka shirya a TV wajen nuna wasannin kada kayayyakin kidan gargajiyar kasar Sin a shekarar 1989 ya zama lambatu, a gun shagalin samari na karo na 13 da aka shirya a Korea ta Arewa a watan Yuli na shekarar 1989, ya sami lambar yabo mafi koli, wato lambar zinariya wajen busa sarewa shi kadai a cikin wasanni , a shekarar 1991, ya sami lambar yabo da ke da lakabi da cewa "nagari na 'yan wasan fasaha" daga wajen ma'aikatar al'adu ta kasar Sin.

A shekarar 1990, Wang Ciheng ya shirya wasannin busa sarewa shi kadai a dakin wake-wake da kide-kide na birnin Beijing, inda ya sami yabo sosai daga wajen rukunin wake-wake da kide-kiden garagajiyar kasar Sin. Musamman ne Mr Lu Ji ya yaba shi da cewa, Wang Ciheng shi ne wanda ke kwarewa sosai wajen busa sarewa a zamanin yau , bisa tushen yin gadon fasahar gargajiyar kasar Sin wajen busa sarewa, yana yunkurin samun mafita wajen kago sabbin abubuwa.

A madadin kasar Sin ne, sau da yawa ya tafi zuwa kasar Austria da Faransa da Jamus da Amurka da sauran kasashe da jihohi don nuna wasannin, kuma ya yi nasarar samun babban yabo .

Mr Wang Ciheng ya mai da hankali sosai ga kara ilminsa, ya yi koyi daga sauran mutane, bai nuna bambancin rukunoni ba, kullum yana yin tunanin bayyana halaye masa na kansa wajen busa sarewa.(Halima)

Sheng Zhongguo

Mutane masu kwar jini wajen rukunin wake-wake da kide-kide na duniya sun yaba wa wani mai kada kayan kidan da ake kira "Violin" na kasar Sin Mr Sheng Zhonguguo ,da cewa, " fiffitacen malamin bayyana fasahar wake-wake da kide-kide" da " Mai kada kayan kidan "Violin" da ke jawo hankulan mutane sosai da sosai".

Bisa matsayin kasar Sin na wanda ke kada "Violin" shi kadai a cikin wasanni na kungiyar kada kide-kiden "Symphony" ta kasar Sin , Mr Sheng Zhongguo yana daya daga cikin masu kada "Violin" na kasar Sin da suka sami yabo sosai daga kasashen duniya ga kasar Sin tun tuni .

An haifi Mr Sheng Zhongguo a wani iyalin wake-wake da kide-kide daga zuri'a zuwa zuri'a, mahaifinsa mai suna Sheng Xue shi ne wani mashahurin shehun malami wajen kada "Violin", mahaifiyarsa mai suna Zhu Bing ita ce mai aikin wake-wake. Sun haifi yara da yawansu ya kai 11 da kuma yi tallafensu sosai da sosai, daga cikinsu, goma ne suke aikin wake-wake da kide-kide, kuma tara ne suke aikin kada "Violin". Mr Sheng Zhongguo shi ne na farko daga cikinsu, an haife shi a shekarar 1941, a wancan shekarun da aka sami rikici da yawa, tamkar yadda dukkan jama'ar Sin suke, iyayensu sun yi fatan kasar Sin za ta kara ingantuwa da wadatuwa , da kuma kada ta sha wulakanci daga sauran kasashe, bisa sanadiyar nan ne iyayensa sun rada masa suna da cewa "Sheng Zhongguo".

Ya soma koyon kada "Violin" daga mahaifinsa a lokacin da ya cika shekaru 5 da haihuwa, bayan shekaru biyu, karo na farko ne ya soma hawa dakalin nuna wasanni, a lokacin ranar hauhuwarsa ta cika shekaru 9, Gidan Rediyo na birnin Wuhan ya dauki muryar kide-kiden da ya kada ta hanyar yin amfani da "Violin", sa'anan kuma gidan rediyo ya watsa shirye-shiryen nan, kai, nan da nan masu sauraronsa sun ji dadin kide-kiden da ya kada da kuma nuna sha'awarsu sosai, sun ce shi ne yaron da ya kware sosai waje kada kayan kidan da aka yi da tsirkiyyoyi ba kamar yadda mutumi yake yi ba, wai kamar yadda mala'ika yake yi ne. A shekarar 1954, ya ci jarrabawr shiga cikin makarantar sakandare da ke karkashin kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na tsakiya na kasar Sin bisa maki mai kyau da ya samu. A shekarar 1956, a gun wasannin da aka shirya domin tunawa da ranar cika shekaru 200 da haihuwar Mozart, a cikin wasannin kide-kiden "Concerto" da kungiyar "Orchestral" ta tsakiya ta kasar Sin wadda Mr Li Delun ke zama direktanta ta nuna, Mr Sheng Zhongguo ya yi nasarar kada kide-kiden "Concerto" na irin karin "A" na Mozart ta hanyar yin amfani da "Violin" . A wannan shekarar kuma, ya shiga makon wake-wake da kide-kide na duk kasar Sin, ya yi hadin guiwa da kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na tsakiya na kasar Sin don kada kide-kiden "Concerto" na irin karin "F" na Mr Ma Sicong ta hanyar yin amfani da "Violin", ya sami yabo sosai daga wajen rukunonin wake-wake da kide-kide, kuma an mai da hankali sosai gare shi.

A shekarar 1960, An zabi Sheng Zhongguo don ya tafi kara ilmi a kolejin da ake kira "Tchaikovsky Conservatory Of Music" na Moscow, ya bi sawun mashahurin babban malamin kada "Violin" na duniya mai suna Leonid Kogan. A kolejin, ya shiga gasar kada kide-kiden Tchaikovsky a tsakanin kasa da kasa ta hanyar yin amfani da "Violin" bisa matsayin Olimpic a fannin wake-wake da kide-kide, ya sami lambar yabo , ya zama daya daga cikin wadanda suka kada "Violin" kuma suka sami lambobin yabo tun tuni na sabuwar kasar Sin a gun gasannin wake-wake da kide-kide da aka shirya a kasa da kasa . A shekarar 1963, ya yi hadin guiwa da kungiyar "Symphony" ta birnin Shanghai don nuna wasannin kada kide-kiden "Concerto", wannan karo na farko ne da aka yi a tarihin kada "Violin" a kasar Sin.

A shekarar 1964, Mr Sheng Zhongguo ya kammala karatu ya komo gida, ya ci gaba da nuna wasanni a dakalin wake-wake da kide-kide na kasar Sin. Kodayake a cikin shekaru goma da kasar Sin ta yi tawayen al'adu, bai iya shirya wasannin wake-wake da kide-kide ba, amma bai taba dakatar da cim ma burinsa na kara fasahar wake-wake da kide-kide ba. Bayan shekarar 1976, ya yi kokari sosai da ba a taba gani ba don rage rashin da ya samu, a kowace shekara, yana nuna wasanni har fiye da sau 100 a wurare daban daban na duniya, saboda haka ya zama daya daga cikin wadanda ke kada "Violin" kuma ke samun karbuwa sosai da sosai a duniya.

A farkon shekaru 80 na karnin da ya shige, a kowace shekara, Mr Sheng Zhongguo yana kan yin tafiya zuwa kasashe daban daban na duniya don nuna wasanni a zagaye. A shekarar 1980, ya tafi birane 6 na kasar Australiya ya nuna wasanni har sau 12, wasannin sun burge duk kasar, shi ya sa wannan ya zama muhimmin abin tunawa a tarihin ma'amalar al'adu a tsakanin kasar Sin da kasar Australiya.

Daga shekarar 1987, a kowace shekara, Mr Sheng Zhongguo yana tafiya zuwa kasar Japan don nuna wasanni, kuma ya samar da kudadden da ya samu don su zama asusun warkar da ciwace-ciwace ga daliban kasashe daban daban na duniya da ke dalibta a kasashen waje ,gwamnatin Japan ta dora masa lakabi da cewa "jakadan al'adu". Saboda fiffitaciyar gudumuwar da ya samar wajen ma'amalar al'adu a tsakanin Kasar Sin da kasar Japan, shi ya sa a shekarar 1999, ya sami lambar yabo ta irin ministan harkokin waje daga wajen gwamnatin Japan.

Mr Sheng Zhongguo ya yi kwangiloli da yawa da kasashen waje wajen nuna wasanni, aikace-aikacen nuna wasanni da ya yi sun ba da babbar gudumuwa sosai ga gaggauta ma'amalar al'adun duniya. A sa'I daya kuma, ya kan tafi jami'o'I na kasar Sin don ba da lacca, ya sa kaimi ga raya sha'anin wake-wake da kide-kide na kasar Sin cikin himma da kwazo.

Yanzu, ya zama mamban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin da na kwamitin tsakiya na kawancen dimokuradiya na kasar Sin da dan majalisar kungiyar masu wake-wake da kide-kide na kasar Sin da dan majalisar asusun raya kide-kiden "Symphony" ta kasar Sin da mamban kwamitin nuna fasahar wasanni.

Tang Junqiao

Tang Junqiao budurwa ce mai busa sarewa ta kasar Sin, yanzu tana matsayin farko wajen busa sarewa a kungiyar wake-wake da kide-kiden gargajiyar kasar Sin ta birnin Shanghai.

Tang Junqiao ta bi sawun mahaifinta wajen koyon busa sarewa tun daga lokacin da take karami. A lokacin da ta shiga jerin samari, ba sau daya ba ba sau biyu ba ta sami babbar lambar yabo a gun gasar kada kayayyakin kida a tsakanin samari. A shekarar 1986 ta ci jarrabawar shiga cikin makarantar sakandare da ke karkashin kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na birnin Shanghai, bi da bi ne ta bi sawun mashahurin shehun malami Zhao Songting da Yu Sunfa don koyon busa sarewa. A lokacin da take makarantar, ta dauki muryar shahararriyar kidan da ake kira "Mei Hua San Nong" da "Mu Min Xin Ge" da "Yang Bian Cui Ma Yun Liang Mang" da sauran shahararrun kide-kide na CD da sauran kaset. A shekarar 1996, ta kammala karatu daga makarantar sakandare tare da samun makin karatu mai kyau sosai, kuma ta shiga karatu a kolejin koyar da ilmin kide-kiden gargajiyar kasar Sin na birnin Shanghai, ta kama matsayin farko wajen kada kayyayakin kida a kungiyar wake-wake da kide-kiden gargajiyar kasar Sin ta birnin Shanghai, saboda haka ta zama mace mai busa sarewa da ke matsayin farko a kungiyar wake-wake da kide-kide na gargajiyar kasar Sin .

Malama Tang Junqiao ta kware sosai wajen nuna wasannin busa sarewa, kide-kiden da ta busa ta hanyar yin amfani da sarewa na da dadin ji sosai, tana kan halartar manyan wasannin kada kide-kiden "Concerto" iri daban daban don busa sarewa ita kadai bisa matsayin baka da aka gayyace ta da wasannin da ake kira "Chamber Music" da yin shirye-shiryen gidan rediyo mai hoto. Duk wadannan sun hada da "wasannin wake-wake da kide-kide da aka nuna don ba da taimako a shekaru dubu na Hongkong" da "wasannin wake-wake da kide-kide don murnar sabuwar shekara ta 2000 a babban gidan nuna wasanni na birnin Shanghai" da "wasannin wake-wake da kide-kide don murnar sabuwar shekarar 1999" da "wasannin wake-wake da kide kide don murnar ranar cika shekaru 4 da kafa yankin musamman na Hongkong" da "wasannin wake-wake da kide-kide don murnar sabuwar shekarar 2001 na birnin shanghai" da dai sauransu.

Bisa gayyatar da aka yi mata ne, malama Tang Junqiao ta taba halartar daukar muryar kide-kiden da ita kadai ta busa ta hanyar yin amfani da sarewa da wani kayan kida daban da ake kira "Ba Wu" kuma Mr Tan Dun ya tsara su a cikin sinimar da Mr Li An, direktar sinimar "Wo Hu Cang Long" ya yi , kide-kiden nan sun sami lambobin zinariya a fannonin wake-wake da kide-kide 18 na sinimar duk duniya ciki har da lambar yabo na Oscar da lambar yabo ta Gelaime. Ya zuwa yanzu, Tang Junqiao ta jawo hankulan mutanen da ke cikin da'irar wake-wake da kide-kide ta kasa da kasa. Bisa gayyatar da aka yi mata ne ta tafi cibiyar yin wasannin fasaha ta Babiken na birnin London na kasar Britaniya don yin hadin guiwa da mashahurin mai kada wani kayan kidan da ake kira "Violoncello" kuma mai suna Ma Youyou wajen kada kidan "Concerto" da Mr Tan Dun ya tsara a cikin sinimar "Wo Hu Cang Long", inda ta sami babbar nasara, daga nan sai ta soma yawon zagaye a duk duniya don nuna wasannin busa kide-kiden da ke cikin sinimar "Wo Hu Cang Long" . Sa'anan kuma ta yi hadin guiwa da wasu shahararrun masu tsara kide-kide na kasar Sin , wato ta yi hadin guiwa da Mr Jia Daqun wajen busa kidan "Concerto" mai suna "Bian Chui Sui Xiang" ta hanyar yin amfani da sarewa; Kuma ta yi hadin guiwa da Mr He Xun Tian wajen fitar da fayafayen da aka yi ta hanyar busa kida mai suna "A Jie Gu" da wani daban da ake kira "Yang Jin Ma" da kuma kidan "Po Luo Mi Duo", saboda haka ta sami yabo sosai.

A bikin yanayin bazara na shekarar 2001, wato babban bikin gargajiyar kasar Sin ta shekarar 2001, tare da kungiyar wake-wake da kide-kide ta gargajiyar kasar Sin ta birnin Shanghai ne ta tafi "dakin zinariya" na Binin Viena don halartar wasannin nuna wake-wake da kide-kide don murnar sabuwar shekara, a cikin wasannin da aka yi, ta busa sarewa ita kadai, a watan Yuli na wannan shekarar , bisa gayyatar da aka yi mata ne ta shirya wasannin musamman na busa sarewa a Macao na kasar Sin.

Bisa matsayin mai nuna wake-wake da kide-kide, ta kan shiga cikin shahararrun wasannin nuna wake-wake da kide-kide na duniya da shagulgulan nuna wasannin fasahohi bisa gayyatar da aka yi mata, wato shagalin nuna wasannin fasaha na tsakanin kasa da kasa na birnin Osaka na kasar Japan da shagalin wake-wake da kide-kide na zamanin yau na kasar Faransa da shagalin wake-wake da kide-kide da ke da lakabi: "wuta kan Ruwa" na birnin London da shagalin wake-wake da kide-kide tsakanin kasa da kasa na birnin Beijing da shagalin nuna wasannin fasaha tsakanin kasa da kasa na birnin Shanghai da shagalin wake-wake da kide-kide tsakanin kasa da kasa a yanayin bazara na birnin shanghai da shagalin wake-wake da kide-kide na tsakanin kasa da kasa na Macao na kasar Sin . Kwarewar da ta nuna a cikin wasanni ta sami yabo sosai daga wajen kwararru da 'yan kallo. Sa'anan kuma ta taba busa kidan sarewa mai suna "Huan Le Ge" domin shugabannin kasashe 21 da suka halarci taron Apec bisa matsayinta na fiffitacciyar busa kidan gargajiyar kasar Sin , inda ta sami kyakkyawar maraba da yabo sosai daga wajen manyan baki na gida da na waje.

Malama Tang Junqiao ta kan yin hadin guiwa da mashahuran kungiyoyin wake-wake da kide-kide da yawa, ciki har da kungiyar "Symphony" ta London da kungiyar "Symphony" ta kasar faransa da kungiyar "Symphony" ta Hamburg da kungiyar "Orchestral" ta Hongkong da kungiyar ""Symphony" ta birnin Taibei na kasar Sin da kungiyar "Ai Yue" ta kasar Sin da kungiyar ""Symphony" ta birnin Shanghai da kungiyar "Symphony" ta gidan rediyo na birnin Shanghai da sai sauransu. Ta taba kai ziyara a kasar Amurka da Jamus da Japan da Britaniya da Austria da Belgum da Faransa da Italiya da Taiwan da Hongkong da Macao da sauran kasashe da jihohi, tana daya daga cikin fiffitattun samari masu busa sarewa na kasar Sin.(Halima)

Xue Wei

Xue Wei shi ne mai kada kayan kidan da ake kira "Violin" a cikin harshen Turanci. An haifi shi a shekarar 1963. Da farko ya soma koyon kada kayan kida a karkashin jagorancin malami Teng Maolong, sa'anan kuma ya bi sawun Mr Jin Zhongping da Chen Xinzhi da Tang Shuzhen da Zheng Shisheng da sauran mutane don koyon kada "Violin". Ya sami horo mai tsanani, saboda haka ya kafa tushe mai inganci wajen nuna wasannin wake-wake da kide-kide. Bi da bi ne ya sami lambar yabo a gun babbar gasar da aka shirya wajen kada "Violin" a kasar Sin a shekarar 1981 da gasar da aka yi wajen kada "Violin" ta Carl Flesch a kasashen duniya a shekarar 1982.

A shekarar 1983, ya ci jarrabawar shiga karatu a kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na kasar Sin, ya bi sawun wani shehun malami mai suna Lin Yaoji. Bayan shekaru biyu da suka wuce, ya tafi kasar Britaniya don ci gaba da kara ilminsa. A shekarar 1986, ya sami lambar azurfa a gun gasar kada kidan Tchaikovsky ta hanyar yin amfani da "Violin" wadda aka shirya a birnin Moscow na kasar Rasha. Bayan makonni biyu, ya koma wa birnin London don halartar gasar kada "Violin" ta kasashen duniya ta Carl Flesch, ya sami lambawan da sauran lambobin yabo, ciki har da lambar yabo ga kidan "Sonata" da ya kada da

lambar yabo ga kungiyar makada da lambar yabo daga wajen 'yan kallo. A wannan shekara kuma, ya sami lambar yabo ga makada na samarin kasar Britaniya.

Bayan da Mr Xue Wei ya sami lambobin yabo, sai nan da nan ya sami yabo mai kyau daga wajen bangarori daban daban. Wata shaharariyyar mujallar kasar Britaniya ta ce, shi ne daya daga cikin fiffitattun masu kada "Violin" na zamanin yau, wata jaridar London ita ma ta bayyana cewa, shi ne mai kwarjini wajen kada kayan kida, yana da fasahar da ba a iya kai wa ba tare da karfi da sauyawa sosai. Ya kan yin hadin guiwa da kungiyoyin makada daban daban na kasar Britaniya, ya nuna wasannin kada kide-kide a dakalin nuna wasannin wake-wake da raye-raye na kasashen Turai. Ya taba daukar muryar kide-kiden da ya kada da yawa don yin fayafaye ga kamfanin ASV da saruan kamfanoni. A lokacin da wani mai yin sharhi kan CD na zamanin da ya nuna yabo a kan muryar kidan "concerto" na Tchaikovsky da ya dauka domin fitar da fayafaye , ya bayyana cewa, ko a lokacin daukar murya don fitar da fayafaye ko kuma a gun wasannin nuna wake-wake da kide-kide, ban taba ganin irin kwarewar da ya nuna a gun wasannin kada kayan kida ba, ba zan manta da shi ba.

Daga shekarar 1989, an dauki Mr Xue Wei don ya zama shehun malami na kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na gidan sarkin kasar Britaniya.(Halima)

Zhao Songting

An haifi Zhao Songting a shekarar 1924 a wani wurin da akr kira Dongyang da ke lardin Zhejiang na kasar Sin. Tun daga lokacin da yake karami, yana kaunar wake-wake da kide-kide , lokacin da ya cika shekaru 9 da haihuwa, ya soma koyon ilmin busa sarewa, sa'anan kuma ba da dadewa ba ya soma koyo kuma ya iya kada kayyayakin kidan da aka yi da tsirkiyoyi kamar su "Erhu" da "Pipa" da "Sanxian" da Algaita wato "Suona" da sauran kayayyakin kida na gargajiyar kasar Sin. Lokacin da ya cika shekaru 16 da haihuwa, ya kammala karatu a makarantar sakandare, sa'anan ya shiga kos na rera kide-kiden "Kun" a zaune, daga bisani kuma ya shiga karatu a kolejin horar da malaman koyarwa, bayan da ya kammala karatunsa, ya zama malamin koyarwa a makarantar sakandare da kolejin horar da malaman koyarwa wajen ba da ilmin wake-wake da kide-kide. Lokacin da ya cika shekaru 22 da haihuwa, bisa niyyar mahaifinsa ne ya ga tilashin tilashi ne ya bar kaunarsa ga wake-wake da kide-kide, ya shiga cikin kolejin koyar da ilmin dokokin shari'a na birnin Shanghai don yin nazari kan dokokin shari'a.

A shekarar 1949, ba tare da shakka ba Mr Zhao Songting ya katse koyon dokokin shari'a, ya yi jarabawar shiga cikin kungiyar yin wake-wake da kide-kide, ba ma kawai ya iya kada wasu kayayyakin kida na kasashen yamma ba, hatta ma ya iya tsara kalmomin wakoki da kide-kide. A shekarar 1954, a lokacin da Mr Zhao Songting ya ke hutun domin shakatawa a arewa maso gabashin kasar Sin, ya kan tsaya a gaban ni'imtattun tsaunuka da koguna masu sifar kyaun gani sosai tamkar yadda wakoki da hotuna suke a kowace rana da kuma ya dudduba yadda mutane suke yin farin ciki da aiki da zaman rayuwa , saboda haka ya soma tsara kidan sarewa mai suna "Safiya", wato "Zao Chen" cikin sinanci, kidan nan ya siffanta yadda kasar mahaifa take kara samun bunkasuwa da wadatuwa . A shekarar 1956, Mr Zhao Songting ya shiga cikin kungiyar raye-raye da wake-wake irin gargajiyar kasar Sin ta lardin Zhejiang, a cikin makon wake-wake da kide-kiden da aka shirya a duk kasar Sin a karo na farko, ya busa kidan sarewa da ke da suna "Safiya", kuma ya sami babbar nasara.

A shekarar 1964, a gun karo na biyar na nuna wasannin wake-wake da kide-kide da aka shirya da ke da lakabi haka: "Yanayin bazara na birnin Shanghai", ya busa kide-kiden sarewa guda biyu da shi kansa ya tsara , kamar su "Wu Jiang Feng Guang" wato ma'anarsa ita ce "ni'imtaccen kogin Wujiang" da kida mai suna"Cai Cha Mang" wato kidan ta yi nufi da cewa, ana kokarin aikin cire ganyayen ti, ya sami maraba sosai daga wajen masu sauraronsa da kuma yabo daga wajen kwararru.

Sa'anan kuma, Mr Zhao Songting ya soma yin bincike kan sarewa ta hanyar kimiyya da fasaha. Bisa taimakon da kannensa , masanin ilmin phisics Mr Zhao Songling ya yi masa ne, ya yi bincike da gwaje gwaje cikin dogon lokaci , ya kammala kidayar sakamakon gwaje-gwaje da yawansu ya wuce dubu goma wajen zafi da ma'aunin murya da yawan saurin kadawa, a karshe dai ya gabatar da dabarar kera sarewa ta hanyar kimiyya.

Wajen aikin koyarwa, Mr Zhao Songting ya sami sakamako da yawa, dalibansa da yawa su ma sun sami suna sosai a gida da waje. Sa'anan kuma, Mr Zhao Songting ya yi bincike a fannoni biyu, na daya a kan wani kidan da ake kira "Firitsi", wato sarewa da aka iya kara tsawonsa, amma ba a kawo cikas ga saukin busawa ba; Na biyu a kan wani kayan kidan da ake kira "Shuang Guan Shuang Di", sunansa daban shi ne "Yan Di", lokacin da ake busa shi, hannayen mutum tamkar yadda wata tsuntsar " babba da jakka" take kada fukafukinta, na da kyaun gani sosai. An taba rubuta irin wannan sarewa a cikin ajiyayyun takardun tarihi da kuma gan ta a cikin hotunan da aka zana a kan banguna na zamanin da, amma ba a gano ta na hakika ba.

Sarewar kasar Sin ta kasu kashi biyu, wato na da irin na kudancin kasar Sin mai sifar silili kuma mai kyaun gani sosai da irin na arewacin kasar Sin da ke da halayen bayyana karfi da haske sosai, Don kara bayyana halin zamanin yau, Mr Zhao Songting ya karya iyakar da ke tsakanin kudu da arewa, ya yi amfani da nagartatun abubuwan rukunonin biyu, kuma bisa taimakon wasu fasahohin kera "Flute" na kasashen yamma ne , ya kafa rukunin Zhejiang da ke hade da halayen bayyana karfi da laushi, ya kuma yi amfani da dabarar busa "Algaita" a wajen busa sarewa, ta hakan ya wadatar da dabarun busa sarewa. Fasahar busa sarewa da Mr Zhao Songting ya samu tana da nasa tsari wajen busa kide-kide da tsara su da aikin koyarwa da daukar muryarsu.

Wajen ra'ayin bayyana abubuwa masu kyaun gani, Mr Zhao Songting yana tsayawa cewa, ya kamata a bi hanyar yin amfani da dabarun nuna wasannin wake-wake da kide-kide domin bauta wa abubuwan da wasannin suka bayyana, in dabarun sun kubutar da kansu daga wajen abubuwan da aka bayyana, to ba za a iya ce musu dabaru ba. Sarewa da aka kera da gora ita kanta tana kara samun bunkauwa, to dole ne a sabunta dabarun busa su , kome dabaru na gida ko na waje, na gabas ko na yamma, in za su iya ba da taimako ga abubuwan da ake bayyanawa, to ya kamata mu yi koyi da su.

Kodayake fasahar busa sarewa da Mr Zhao Songting ya samu daga wajen jama'a, kuma bai taba shiga karatu a kolejin koyon ilmin wake-wake da kide-kide ba, amma yana da ilmi mai zurfi sosai da sosai, saboda haka dalibansa da yawa sun kware sosai .

Mr Zhao Songting ya kan tafi ko'ina ba tare da gajiya ba don yada wake-wake da kide-kide na gargajiyar kasar Sin, kuma ya kasance mai aiki sosai a dandalin wake-wake da kide-kide na gargajiyr kasar Sin. Ya rasu a shekarar 2001 bisa sanadiyar fama da ciwo.(Halima)

Lu Rirong

An haifi Mr Lu Rirong a ran 1 ga watan Yuni na shekarar 1933 a gundumar Jun ta lardin Hubei na kasar Sin. Ya kama aikin nuna wasannin fasaha a shekarar 1945; A shekarar 1950, ya zama mai kada kayyayakin kida da ake kira "Erhu" da "Violin" a kungiyar nuna wasannin fasaha ta Hanzhong. Sa'anan kuma ya ci jarrabawar shiga cikin kolejin koyon ilmin wasannin fasaha na arewa maso yammacin kasar Sin don koyon kada "Erhu" wato irin kayan kidan da aka yi da tsirkiyoyi biyu, kuma ya yi karatu kan darasin tsara kide-kide da na ba da jagoranci ga kungiyar makada. A shekarar 1954, ya kammala karatunsa, kuma ya sami aikin koyarwa a kolejin, ya ba da lacca ga dalibai wajen kada "Erhu" da kuma ba da jagoranci ga kungiyar makada ta hanyar nuna wasannin kide-kiden gargajiyar kasar Sin. Ya taba rike mukamin direktan sashen koyarwa da shugaban sashe da mataimakin shugaba na Kolejin da sauran mukamai. Yanzu ya zama malami mai ba da jagorancin karatu ga daliban da ke neman digiri na biyu na kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na birnin Si'an, kuma mataimakin direktan kwamitin wake-wake da kide-kide na gargajiyar kasar Sin na hadadiyyar kungiyar masu wake-wake da kide-kide ta kasar Sin , mataimakin shugaban kungiyar nazarin kayayyakin kida irin da aka yi da tsirkiyoyi da irin da ake iya busawa na gargajiyar kasar Sin , shugaban kungiyar nazarin kayayyakin kida irin wadanda aka yi da tsirkiyoyi da irin wadanda ake iya busawa ta lardin Shan'xi ,kuma shi ne mashawarcin yin wasannin fasaha na kungiyar "Symphony" ta nuna wasannin kada kide-kiden gargajiyar kasar Sin ta tiyatar nuna wasannin raye-raye da wake-wake na birnin Shan'xi da sauransu.

A cikin zaman rayuwarsa wajen aikin koyarwa a fannin wasannin fasaha a cikin lokacin kusan rabin karnin da ya wuce, Mr Lu Rirong ya yi aikin koyarwa da nuna wasannin fasaha da wallafa kide-kide da ba da jagoranci ga kungiyar makada . Ya tsara kide-kiden da aka yi amfani da su don neman kwarewa a fannin kada "Erhu" da yawansu ya kai 150 ko fiye, da kide-kiden da aka iya kada su shi kadai har fiye da 20 ,da kide-kiden da ake kada da kayayyakin kida fiye da biyu ,da kide-kiden da aka iya kada su ta hanyar yin amfani da kayayyakin kida iri na tsirkiyoyi, da kide-kiden gargajiyar kasar Sin da aka kada ta hanyar yin amfani da kayayyakin kida irin na tsirkiyoyi da irin da ake iya busawa su fiye da 20, da kuma bayanan da ya rubuta da yawansu ya wuce goma , ya ba da babbar gudumuwa ga kafa rukunin Qin wajen kada "Erhu" da rukunin Yue na Chang'an.

Wajen aikin koyarwa, Mr Lu Rirong ya tsaya kan ra'ayin hada aikin koyarwa da nuna wasannin kada kide-kide da kago kide-kide da yin nazarin hasashe. Ya roki dalibai da su sami ci gaba daga dukkan fannoni, halayen musamman nasa su ne, tsara ka'idoji sosai da ba da lacca iri daban daban ga wadanda suke da bambancin matsayin kwarewa , koyon fasahohi masu kyau daga kowa da kowa,ba da misali ga dalibai bisa abubuwan da shi kansa ya yi , kuma ya koyar da dalibai bisa fasahar da aka samu daga wajen wasannin fasaha da halin nagari na kowa. A cikin shekaru gomai, ya tsara littattafan karatu a jere da tsarin koyarwa da ke da halayen musamman. Ya horar da wasu nagartattun kwararru wajen tsara hasashen kide-kiden gargajiyar kasar Sin da koyar da ilmin kada "Erhu" da nuna wasannin kada kide-kide da tsara kide-kiden gargajiyar kasar Sin da ba da jagoranci ga kungiyar makada da dai sauransu.

Wajen kada kide-kide, muryoyin kidan da ya kada nada dajin ji sosai tare da tabshi da sanyaya rai , ya kware bisa tushen wake-wake da kide-kide da al'adu na wurin Qin da na gargajiyar kasar Sin, ta hanyar ayyuka da bincike da ya yi ta yi, a kai a kai ne ya sami fasahar kada "Erhu" da ke da halayen musamman na wuri wuri. A shekarar 1960, a gun taron binciken littattafan karatu a kan ilmin "Erhu" da "Pipa" da aka shirya, bayan da Mr Lu Rirong ya kada kida mai karin Mihu da kida mai karin "Xin Tian You" da shi kansa ya kago da ke da halayen musamman na wurin Qin da ke arewa maso yammacin kasar Sin, sai tsofaffin masu kada kayan kida da aka yi da tsirkiyoyi wato "Erhu" da mahalartan taron sun daukaka masa cewa, sabon kago ne da ya yi ga halayen musamman na kada kayan kidan da ake kira "Erhu" da dabarar kadawa.

Wajen tsara kide-kide, ya tsara kide-kide bisa wadatattun fasahohin da aka samu na nuna wake-wake da kide-kide na gargajiyar kasar Sin, kuma kide-kiden nan suna da halayen musamman na rawayen kasar tsaunuka masu fadi, "Qinqiang" mai babban kari da "Wanwan Qiang" mai lankwasasshen kari da "Mihu" da ke da halin nuna haske da sauki da dai sauransu sun zama albarkatan da yake yin amfani da su ba tare da karewa ba wajen wallafa kide-kide. Saboda haka kide-kiden da ya wallafa suna bayyana al'adar jama'ar "Qin" da tunaninsu. Manyan kide-kiden da ya wallafa suna hade da kide-kiden da ake kira karin "Mihu" wanda aka kada shi ta hanyar yin amfani da kayan kidan da ake kira "Erhu" da "Qinqiang zhu ti sui xiang qu" da "Huan Le de Qinchuan" da "Cai Hua" da "Yao Lan Qu" wato kidan lalashin jinjiri da "Qu Jiang Yin" da dai saruansu.

Wajen ba da jagoranci ga kungiyar makada, ya yi daidaituwa yadda ya kamata wajen nuna wasannin kide-kide da wake-wake, kuma ya fahimci ma'anar kide-kiden da aka kada cikin salo mai zurfi sosai, wasu kide-kide kamar "Huan Du Xin Chun" da "Qinqiang Zhu ti Sui Xiang Qu" da " Yin Shi-Li Shan Yin" da "Chang'an She Huo" da sauran kide-kiden gargajiyar kasar Sin da aka kada ta hanyar yin amfani da kayayyakin kidan da aka yi da tsirkiyoyi wadanda kungiyar masu kada kide-kiden gargajiyar kasar Sin ta hanyar yin amfani da kayayyakin kidan tsirkiyoyi ta Xi'an ta gabatar da su ga duk kasar Sin. Mr Lu Rirong ne ya horar da kungiyar kuma ya ba da jagoranci ga makadan da ke cikin kungiyar cikin shekara da shekaru. Wasannin kide-kide da wake-wake da kungiyar ta yi sun sami karbuwa sosai daga wajen masu sauraro na gida da na kasashen waje.

Ya kuma tsara kide-kide da kuma kada su domin sinimar da ake kira "Huang Tu Di" da saruan sinima fiye da goma. A shekarar 1991, ya jagoranci kungiyar kide-kiden zamanin da ta Chang'an don yin ziyara a kasashen Turai, inda wani kaset na CD na musamman da aka yi bisa jagorancin kasar Faransa ya sami lambar zinariya na birnin Paris.

Manyan littattafai da ya bayar su ne, da da da da da da da < Mai da hankali ga tsara kide-kiden gargajiyar kasr Sin da ake kadawa a cikin dakuna da sa kaimi ga yaduwar kada su>

Tun daga shekaru 80 na karnin da ya gabata har zuwa yanzu, bisa gayyatar da aka yi masa ne, bi da bi ya kai ziyara a kasar Japan da Jamus da Faransa da Belgium da Holand da Switzerland da Spain da Malasiya da Singhapor da Hongkong da Taiwan da saruan kasashe da jihohi don yin ma'amalar al'adu da ba da lacca, duk domin yin farfagandar wake-wake da kide-kide da al'adu na gargajiyar kasar Sin, ya sami maraba sosai daga wajen rukunonin wake-wake da kide-kide na wurare daban daban saboda laccar da ya yi kan kidan rukunin "Qin" da aka kada ta hanyar yin amfani da "Erhu" da bayanin da ya yi kan rukunin kada kida na Chang'an. A shekarar 1992, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta yi masa kirari mai daukaka da cewa "kwararren da ke ba da babbar gudumuwa ga kasa".(Halima)

Liu Dehai

Mashahurin mai kada kayan kidan garaya, wato "pipa" da ake kira cikin sinanci Mr Liu Dehai, shi ne wakilin nagartattun masu kada kayayyakin kida na kasar Sin da ya yi tashe a karshen shekaru 50 na karnin da ya gabata. Mutane suna kiran shi da cewa, babban malamin kada kayan kidan da ake kira "pipa" da dukiyar kasa, ya yi suna sosai a gida da waje.

An haifi Liu Dehai a shekarar 1937 a birnin Shanghai, amma garinsa yana gundumar Cang ta lardin Hebei. A lokacin da yake makarantar sakandare, ya soma kaunar wake-wake da kide-kide na gargajiyar kasar Sin , kuma ya bayyana kwarewa sosai wajen wake-wake da kide-kide. A shekarar 1954, ya bi sawun mashahurin mai kada "pipa" kuma mai gadon rukunin "Pudong" Mr Lin Shicheng. A shekarar 1957, Mr Liu Dehai ya ci jarrabawar shiga kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na kasar Sin don mai da hankali ga koyon ilmin "pipa".

Mr Liu Dehai ya kware sosai wajen kada "pipa", muryoyin kide-kiden da ya kada sun fito ne da dajin ji sosai, mutanen da suka ji kide-kiden da ya kada sun burge sosai da sosai, sun sami alamar tunawa mafi kyau daga wajen wasannin kada kayayyakin kida da ya yi. Bisa tushen rike da fasahar kada garaya ta rukunin Pudong, Mr Liu Dehai ya kuma koyi fasahohin kada kayayyakin kida daga sauran rukunoni da yawa, sa'anan kuma ya soma koyon ilmin kada garaya daga wajen malami Cao Anhe na rukunin Chongming da malami Sun Yude na rukunin Wang na birnin Shanghai da malami Yang Dajun na rukunin Zhuying, ya koyi nagargattun fasahohi daga wajensu, ya hade fasaharsa ta kada pipa da da na sauran mutane wajen kada kide-kide , saboda haka ya raya fasahohin kada pipa sosai da sosai, kuma ya sami kwarewa mai zurfi wajen kada kide-kiden gargajiyar kasar Sin.

Bisa tushen dabarar kada kayayyakin kida na gargajiya, Mr Liu Dehai ya soma yin gyare-gyare da yawa don sabunta dabarar kada kide-kide da kyautata tsarin kide-kide. Wato wajen babban fannin sabunta dabarar kada kayan kida, ya 'yantar da babbar yatsar hannu ta hagu, ta hakan za a iya rage yawan canja inda ake kadawa, saboda haka a iya kara saurin kida tare da fitowar muryar kide-kide ba katsewa don kara karfin bayyana fasahar kada pipa. Sa'anan kuma ya yi gyare-gyare wajen kada kayan kidan , wato za a iya yin amfani da sauran yatsun hannu guda hudu wajen kada kayan kida kowacensu kadai ta yadda muryoyin kide-kiden da aka kada za su iya samun bambancin sauyi tare da dadin ji sosai.

Kide-kiden da Mr Liu Dehai ya kada na da yawan gaske, kamar su kide-kide na zamanin da, wato "Shi Mian Mai Fu" da ke bayyana halin jarumtaka da "Yang Chun Bai Xue" da ke bayyana halin annashuwa da ake ciki da kuma kide-kide na zamanin yau wato "Lang Ya Shan Wu Zhuang Shi" , wakar tana bayyana cewa, jarumai guda biyar a wani tsaunin da ake kira Langyashan, da kide-kiden kabilar Yi wajen raye-raye da wata kidan da ke da ma'ana kamar haka: a rera wata waka a kan tsauni domin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da sinanci ake cewa " Chang Zhi Shan Ge Gei Dang Ting" da dai sauransu. Lokacin da ake saurarar kide-kiden da ya kada da ke kunshe da kidan da ake kira " Lang Ya Shan Wu Zhuang Shi" da "Cao Yuan Xiao Jie Mei" (Ya da kanwarta a makiyayya) da "Shi Mian Mai Fu" da dai sauransu, sai a ji tamkar yadda ya bayyana labaran tarihi ga mutane, wato kamar ana ganam ma idonsu a inda labaran suka faru, mutane sun yi mamaki sosai a kan fasaharsa ta kida.

Don mayar a wake-wake da kide-kide su zama na yau da kullum, Liu Dehai ya gyara kide-kiden wakoki da yawa kamar wakar "Liu Yang He" wato "kogin Liu Yang" da "Yuan Fang De Peng You Qing Ni Liu Xia Lai" da ke da ma'anar da cewa, ana rokon aminan da suka zo daga wuri mai nisa su ci gaba da zamansu, da wakar "You Ji Dui Zhi Ge", wato wakar 'yan sari-ka-noke da "Ma Lan Hua Kai" da ke bayyana yadda fure mai suna Ma Lan ya bude da sauran kide-kiden wakoki don su zama kide-kiden da aka kada da pipa, wadannan kide-kiden da ya kada na da dadin ji sosai ga masu sauraronsu da ke fahimtar ilmin wakoki da kide-kide sosai da sauran masu sauraronsu. Sa'anan kuma ya yi gyare-gyare kan wasu kide-kiden gargajiyar kasar Sin na zamanin da da kyautata su sosai. wadannan kide-kide suna kunshe da "Ba Wang Xie Jia" wato sarki mai kama karya ya ajiye makamai da "Chen Sui" da "Xun Yang Yue Ye" wato "Daren kogin Xun Yang tare da wata" da dai sauransu.

Ban da wadannan kuma, Mr Liu Dehai shi kansa ya wallafi kide-kide da yawa dangane da zaman rayuwar mutane, kamar su "Tian E" da "Lao Tong" da wadanda ke shafar gonaki, kamar su "Gu Xiang Xing" da "Yi Zhi Chan" da sauransu tare da wadanda ke shafar addinai kamar su "Di Shui Guan Yin" da "Xi Qing Luo Han" da dai sauransu da ake iya kada su da pipa. Ya sami wadatattun sakamako wajen yin nazarin hanyoyin kada pipa da neman sabunta su da kuma neman sabon hanyar kago kide-kide.

Daga shekarar 1978 zuwa shekarar 1981, Mr Liu Dehai ya taba yin hadin guiwa da kungiyar da ake kira "Boston Symphony Orchestra" ta kasar Amurka da kungiyar taron makada ta Berlin ta yamma, wato kungiyar da ake kira "Symphony Orchestra ta Berlin ta yamma" da mashahurin mai da ba jagorancin makada Mr Seiji Ozawa , ya kuma yi wasannin kada kidan "Cao Yuan Xiao Jie Mei" wato "Ya da kanwarta a makiyayya" cikin sinanci da pipa a nan birnin Beijing da kasar Amurka da birnin Frankfurt, inda ya sami karbuwa sosai da sosai daga wajen masu sauraronsa na gida da na waje, kuma ya rubuta bayani mai inganci wajen hada da kide-kide na kasashen yamma da na kasar Sin gu daya.

Mr Liu Dehai ya sami fasahohin kide-kide masu zurfi sosai ta hanyar yin wasannin kada kayayyakin kida da samun horo mai tsanani da ba da lacca ga dalibai cikin dogon lokaci , ya fi sauran mutane kwarewa wajen kada kide-kide. Yanzu ya zama shehun malami na kolejin koyar da ilmin wake-wke da kide-kide na kasar Sin, mataimakin direkta na kwamitin nuna fasahohin wasanni da mamban din din din na kungiyar masu wake-wake da kide-kide ta kasar Sin da kuma mamban hadadiyyar kungiyar masu fasahohin wasanni ta kasar Sin. Ya taba kai ziyara da nuna wasannin kada pipa da ba da lacca a kasashe da jihohi har fiye da 30, ya yi gwaji tare da sakamako da ba da gudumuwa sosai wajen nuna fasahar kada pipa a cikin kungiyar makada , wato kungiyar da ake kira " symphony Orchstra", ya bude sabon shafi ga yin musanyar al'adu a kasa da kasa ta hanyar kada pipa.(Halima)

Liu Mingyuan

Liu Mingyuan yana daya daga cikin nagartatun masu kada kide-kiden gargajiyar kasar Sin a cikin rabin karni ko fiye, a wajen dandalin wake-wake da kide-kide na kasar Sin da na kasa da kasa, ya sami yabo sosai da ake cewa, "hannu mai kyau na kada kayayyakin kidan da aka yi da tsirkiyoyi na kasar Sin". Mr Liu Mingyuan ya kware wajen kada ire-iren kayyayakin kidan da aka yi da tsirkiyoyi da yawa kamar su "Banhu" da "Gaohu" da "Erhu" da "Zhonghu" da "Jinghu" da "Zhuihu" da dai sauransu, musamman ma ya kware wajen kada "Banhu" da "Zhonghu", wajen kwarewar kada kayyayakin kidan da aka yi da tsirkiyoyi, ba wanda ya wuce shi.

An haifi Mr Liu Mingyuan a shekarar 1931 a birnin Tianjing, lokacin da ya cika shekaru 6 da haihuwa, ya soma koyon kada kayyayakin kidan da aka yi da tsirkiyoyi, wato "Banhu" da "Zhonghu" daga mahaifinsa, lokacin da ya cika shekaru 7 , ya shiga cikin kungiyar wake-wake da kide-kide ta "Bailing" ta birnin Tianjing da rukunin wake-wake da kide-kide na kungiyar lardin Fujiang da Kwangdong, ya taba koyon kide-kiden da ake cewa "Sizhu" cikin sinanci, kamar a ce "siliki da gora" cikin harshen Hausa da kide-kiden lardin Kwangdong da wasan Opera da wasan kwaikwayo da wasan kwaikwayo irin na lardin Hebei da sauransu. Daga shekarar 1947 zuwa shekarar 1952, ya taba yin aikin kada kide-kide a kungiyoyin wake-wake da kide-kide da raye-raye na Shengli da Huanggong da Yong'an da Huizhong na birnin Tianjing da dai saraunsu. A shekarar 1957, ya shiga gasar kada kayayyakin kida na gargajiyar kasar Sin a gun shagalin samari na 6 na tsakanin kasa da kasa bisa matsayin samari mai fasaha na kasar Sin , ya sami lambar yabo na zinariya. A cikin aikatawar nuna wasannin kada kide-kiden gargajiyar kasar Sin cikin shekaru 30, ya kafa ingantaccen tushe ga nuna wasannin kada kide-kide, ya sami nasarar kwarewa sosai da kuma nuna wasannin kada kayan kidan da ake kira "Huqin" bisa matsayin da ba a taba kaiwa ba.

A cikin tsawon lokacin da Mr Liu Mingyuan ya kada kayan kidan da ake kira "Huqin", wato kayan kidan da aka yi da tsirkiyoyi guda biyu, dayake ya ba da taimako ga rukunonin nuna wasannin kide-kide da ke da halayen musamman na nuna wasannin kwaikwayo da na wurare daban daban , shi ya sa ya horar da shi kansa wajen kada bambancin muryoyin kide-kide da salonsu tare da kwarewa sosai. Ya kware sosai wajen kada kayan kidan da ake cewa "Huqin", sa'anan kuma ya kware wajen kada Piano, ya taba kai matsayin malamin kada kidan Jazz da Piano, a sa'I daya kuma ya taba samun malamin da ke koyar masa wakokin kabilar Mongoliya, ya iya rike halayen musamman na kide-kiden Mongoliya a daidai yadda ya kamata, A sa'I daya kuma, kide-kiden da Liu Mingyuan ya wallafa ko ya kada na da yawan gaske, wadannan kide-kiden da ya wallafa sun bayyana halayen gargajiyar kasar Sin da kwarjinin fasaha sosai da sosai .Daga cikinsu , kide-kiden da aka kada cikin hadin guiwa kamar su "Xi Yang Yang", wato "Yin farin ciki sosai da sosai" da "Xing Fu Nian" wato "Shekarar kawo zaman alheri" da kidan lardin Henan da ya kada ta hanyar yin amfani da "Erhu" , wato irin kayan kidan da aka yi da tsirkiyoyi guda biyu da kida mai suna "Kan makiyaya" da shi kansa ya kada ta hanyar yin amfani da "zhonghu" da kidan da ke da lakabi haka: "Dawowar Makiyayi" da sauransu wadanda suka fi jin dadin saurara.

Sa'anan kuma, Mr Liu Mingyuan ya ba da gudumuwa sosai wajen yin gyare-gyare kan tsarin kayayyakin kidan da aka yi da tsirkiyoyi da aikin koyarwa, ya bincike yi kuma ya kera "Banhu" da ke iya kada babban karin kida da karamin karin kida na sabon salo ta yadda tsofaffin kayayyakin kida da ke ba da taimakon kada kide-kide suka zama kayayyakin kida da ke iya kada kide-kide su kadai. Tun daga shekaru 50 har zuwa yanzu, Mr Liu Mingyuan yana kokarin sa kaimi ga aikin horar da kwararrun wake-wake da kide-kide, kuma daga shekarar 1982, ya zama shehun malami na sashen koyar da ilmin kada kide-kide ta hanyar yin amfani da kayayyakin kida da aka yi da tsirkiyoyi na kolejin koyar da wake-wake da kide-kide na kasar Sin, kwararrun wake-wake da kide-kide da ya horar da su sun yi yawan gaske. A watan Janairu na shekarar 1996, Mr Liu Mingyuan ya rasu. (Halima)

Fu Cong

Fu Cong an haife shi ne a ran 10 ga watan Maris na shekarar 1934 a wani gidan masu fasaha da ke cike da halin nuna fasaha da yin nazarin ilmi sosai a birnin Shanghai na kasar Sin, mahaifinsa mai suna Fu Lei shi ne wani mashahurin masani kuma kwararren hasashen fasahohi da mai fassara harsunan waje na kasar Sin. Lokacin da ya cika shekaru 3 zuwa 4 da haihuwa, wakoki da kide-kide sun soma jawo sha'awarsa sosai da sosai , kuma yana kaunar wakoki da kide-kide da ba a taba ganin yadda yake yi ba. A lokacin da ya cika shekaru 7 da rabi da haihuwa, ya soma koyon kada Piano, kuma ya bi sawun mai ba da jagorancin makada wato kondakta na mawaka ko makada kuma mashahurin mai kada Piano Mr Mario Paci. Mr Mario Paci shi ne dalibin Liszt. Fu Cong ya yi karatu daga wajen Mr Mario Paci har shekaru uku. A shekarar 1951, Fu Cong ya sami wata malamar koyarwa daga tsohuwar kasar Tarayyar Soviet, wato shaharariyar mai kada Piano mai suna Ada Bronstein.

A shekarar 1953, A kasar Romaniya, an yi shagalin samari na duniya. Bayan zaben da aka yi a cikin kasar Sin ne, Fu Cong ya shiga gasar kada Piano bisa matsayin 'dan wasa shi kadai kawai da ya zo daga kasar Sin don halartar gasar, ya sami lambar yabo ta uku. Lokacin da ya kada kidan Prelude na Scriabin ta hanyar yin amfani da Piano, ya burge 'yan takara na tsohuwar Tarayyar Soviet sosai har da hawaye.

A watan maris na shekarar 1955, a birnin Warsaw na kasar Poland, an yi gasar kada piano na karo na biyar a tsakanin kasa da kasa a kan kide-kiden Chiopin. 'Yan takara 74 da suka zo daga wurare daban daban sun taru gu daya a shagalin samarin duniya. Fu Cong shi kadai da ya zo daga kasar Sin don halartar gasar, kuma shi ne ba ya da dogon tarihi na kada Piano ba, bayan da aka yi gasar har sau uku, ya sami lambar yabo na uku da makinsa ya yi kusan daidai da na wadanda suka ci lambawan da lambaru, kuma ya sami lamba mai kyau wajen kada kidan Mazurka. Wannan karo na farko ne da wani mutumin gabas ya sami sakamako mai kyau wajen gasar da aka yi wajen kada kidan Chopin. Kodayake ya sami lambar yabo na uku ne, amma kwar jinin da ya nuna wajen kada Piano ya mayar da shi bisa matsayin daya daga cikin mutanen da suka jawo hankulan mutane sosai wajen gasar .

Bayan gasar, Fu Cong ya ci gaba da zama a Poland don koyon ilmin kada Piano, har zuwa shekarar 1958 ya kammala karatunsa kafin lokacin da aka kayyade. A duk tsawon lokacin, Fu Cong ya taba koma wa gida don yin hutu a tsakanin watan Augusta zuwa watan Oktoba na shekarar 1956, kuma ya shirya taron kada piano shi kadai a birnin Beijing. A birnin Shanghai, ya yi hadin guiwa da kungiyar masu kada kide-kide iri na Symphony don shirya taron Concerto na Mozart. A wartan Disamba na shekarar 1958, Fu Cong ya bar kasar Poland ya kaura zuwa birnin London na kasar Britaniya.

A cikin shekaru fiye da 20 da suka wuce na tsakanin shekaru 60 zuwa 70 na karnin da ya shige, Fu Cong ya yi wasannin kada kide-kide shi kadai har sau 2400, ciki har da hadin guiwar da ya yi da Menuhin da Barenboim da Chung Kyung –Wha da sauran mashahuran masu kada kide-kide na kasa da kasa da yawa, ya yi fayafayan kide-kide har da 50. Ya taba zama alkali na gasar kada kide-kiden Chopin ta kasa da kasa ta hanyar yin amfani da Piano da na gasar wasannin kada kide-kide a tsakanin kasa da kasa ta tsohuwar sarauniyar Elizabeth ta kasar Belguim da ta gasannin nuna wasannin wake-wake da kide-kide da aka shirya a kasar Norway da Italiya da Switzerland da Portugal da kasashe da jihohi na kudu maso gabashin Asiya. Kai ,ya sa kafa a ko'ina na kasashen Turai da na Nahiyar Amurka da na Gabas ta Tsakiya da na Kusu maso gabashin Asiya da Japan da na Ocenia da saraun wurare don nuna wasannin kada Piano, ya sami yabon da ke da lakabi haka: Babban malamin da ke da karfi sosai. Mujallar mako mako da ake kira " Time" ta taba darajanta shi da cewa , shi ne mashahurin mai wake-wake da kide-kide mafi girma na kasar Sin.

A shekarar 1976, A kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na kasar Sin , Fu Cong ya shirya wasannin nuna kide-kide. Daga nan kusan a kowace shekara yana komo wa birnin Beijing da Shanghai da Xi'an da Chengdu da Kunming da sauran wurare na kasar Sin don nuna wasannin kide-kide da ba da yin lacca da dai saruansu. Ya taba ba da laccar musamman a kan Chopin da Mozart da Debussy da sauransu, kuma ya taba nuna wasannin kide-kiden da wadannan masu mawallafan kide-kide suka tsara. Ya kuma yi hadin guiwa da kungiyar wake-wake da kide-kide ta kasar Sin, ya kada kidan Beethoven, wato concerto na Beethoven ; Ya kuma yi hadin guiwa da daliban kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na kasar Sin wajen kada Concerto na Mozart, kuma ya dau nauyin ba da jagorancin wasannin kada kide-kide. Sa'anan kuma ya ba da jagoranci ga horar da kungiyar masu nuna wake-wake da kide-kide a cikin daki ta makarantar sakandare da ke karkashin kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na kasar Sin. Wadatatun fasahohin da ya samu da halin hakuri da ya nuna wajen horar da dalibai sun sami girmamawa da yabo daga wajen dimbin dalibai da malaman koyarwa da masu kishin wake-wake da kide-kide.(Halima)

Song Fei

Song Fei wata mace ce da aka haife ta a shekarar 1969,kuma ta shahara wajen kada goge da sauran kayayakin kida da aka yi da tsirkiyoyi har iri 13, ana girmama ta da lakabin "saurauniyar kidan jama'a"

Song Fei ta soma samun ilmi daga wajen mahaifinta wanda shehun malami ne a kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na birnin Tianjing kuma mashahurin mai kada goge na kasar Sin. A shekarar 1981 ta yi karatu a wata makarantar sakandari da ke karkashin kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na Tianjing ; a shekarar 1987, bayan da ta ci jarrabawar da aka yi , ta shiga karatu a sashen koyon ilmin kayayyakin kida na kolejin koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na kasar Sin, ta mai da muhimmanci ga koyon ilmin kada goge da wani kayan kida da aka yi da tsirkiyoyi guda 7, a cikin sinanci ana kiran kayyayakin kidan da suna "Erhu" da "Guqin". Ta kammala karatu a shekarar 1991, sa'anan kuma ta zama mai kada goge a cikin kungiyar masu wake-wake da kide-kide ta gargajiyar kasar Sin . A shekarar 1998, ta shiga karatu don koyon ilmin kada goge da kayan kida da aka yi da tsirkiyoyi guda 7 don neman digiri na biyu a kos na koyar da ilmin wake-wake da kide-kide na gargajiyar kasar Sin da ma'aikatar al'adu ta kasar Sin ta shirya, a shekarar 2000, ta kammala karatunta a kos din.

Da lokacin da take karatu a makarantar sakandare, ta kan shiga gasannin da aka shirya don kada kayayyakin kidan gargajiyar kasar Sin iri iri a duk kasa, kuma ta kan samu lambobin yabo masu daraja sosai. Sa'anan kuma ba sau daya ba ba sau biyu ba ta sami lambobin yabo a cikin gasannin da aka shirya a gida ko a kasashen waje. A cikin shekaru da yawa, ta kan yi ziyara a wurare daban daban na duniya, musamman ma ta kada kayayyakin kide-kide a Carnegie Hall na kasar Amurka da Golden Concert Hall na Austria bisa matsayin wakiliyar masu wake-wake da kide-kide ta kasar Sin.

A shekaru 90 na karni na 20, tare da kungiyar mata masu wake-wake da kide-kide da ke da lakabin "Aiyue" ta Malama Zheng Xiaoying ne ta kan kada goge a manyan jami'o'I da kolejoji don yaddada ilmin kide-kide na gargajiya na kasar Sin. A sa'I daya kuma ta kai ziyara a kasashen Turai, ta kuma sami nasara sosai wajen nuna wasannin kada kayayyakin kida, a wani gami, ta kada kidan Korsakov mai suna "Flight of the Bumble Bee" ta hanyar yin amfani da goge, masu kallo na kasashen yamma sun yi farin ciki da mamaki sosai da sosai.

A shekarar 1996, 'yar wasa Song Fei da mata 9 masu kada kayayyakin kidan gargajiyar kasar Sin wadanda ke da kuzari sosai sun kafa wata karamar kungiyar masu kada kayayyakin kidan gargajiyar kasar Sin da ake kira "Hua Yun Ju Fang", wato ma'anar sunan ta bayyana cewa, furanni 9 ke nan da ke da halayen kasar Sin duk domin yaddada kide-kiden gargajiyar kasar Sin da yin nazari da gabatar da su. Su da kansu tare da kide-kiden da suka kada sun bayyana sabon karfin rayuwa na kide-kiden gargajiyar kasar Sin da kuma fadakar da mutane da su sake fahimtar kide-kiden gargajiyar kasar Sin.

A bikin yanayin bazara na shekarar 1998 da na 1999, sau biyu ne 'yar wasa Song Fei ta shiga cikin Golden Concert Halla tare da kungiyar masu kide-kiden gargajiyar kasar Sin , Kidan da Song Fei ta kada ta hanyar yin amfani da goge ya burge masu sauraro na kasashen waje sosai da sosai.

A shekarar 1999, A yayin da Song Fei ta shiga lokaci mafi kyau wajen nuna wasan kada goge, ba zato ba tsammani ta zabi sana'ar koyar da dalibai, ta bayyana cewa, ta yin haka ne bisa sanadiyar shan tasiri daga ubanta mai nuna misali ga malaman koyarwa, sa'anan kuma bisa burinta na wuce matsayin malaman koyarwarta. Song Fei ta bayyana cewa, tana son ta ci gaba da tsayawa kan matsayinta na koli wajen tunani da zuciya don gano karfin rayuwa na gargajiyar kasar Sin da ke da halin musmman na gargajiyar kasar Sin shi kadai tare da samari.

A shekarar 2002, Song Fei ta shirya taron nuna wasannin kada kayayyakin kida ita kadai a nan birnin Beijing, taron na da lakabi haka: "Kada kayayyakin kida iri 13". A gun taron nuna wasannin kada kayayyakin kida, Song Fei ta kada goge da garaya da kayan da aka yi da tsirkiyoyi 7 da sauransu har ire-ire 13 , wannan ya jawo hankulan rukunonin masu wake-wake da kide-kide na kasar Sin sosai, kuma ta sami babbar nasara a gun taron.

Kide-kiden da ke iya wakiltar wasannin da ta nuna sun hada da "Idannun ruwan da ke nuna hasken wata" wato da sinanci ake cewa, "Er Quan Ying Yue" da "kukan tsuntsaye a kwarin tsaunuka" wato da sinanci ake cewa "Kong Shan Niao Yu" da "Yin Tunani a Babbar Ganuwa" wato da sinanci ake cewa "Chang Cheng Sui Xiang" da sai sauransu.