logo

HAUSA

Babi11: Xinjiang da Tibet

0001-01-01 08:00:00 CRI

■ Xinjiang

>>[Takaitaccen bayani na Xinjiang]

Me ka sani game da Xinjiang

Jihar xinjiang ta kabilar Ughur mai ikon tafiyar da harkokin kanta tana arewa maso yammancin kasar Sin kuma tana cikin cibiyar nahiyar Turai da ta Asiya.Fadin jihar ya kai muraba'in kilomita miliyan daya da dubu dari shida da sittin,jihar ce mafi girma daga cikin jihohi da larduna na kasar Sin.Ta yi iyaka da kasashe 8 a yammancinta da kuma arewacinta,daga gabas zuwa yamma su ne Mongoliya da Tarayyar Rasha da kuma Kazakistan da Kirghistan da Tajidkistan da Afghanistan da Pakistan da kuma Indiya,tsawon iyakar kasa tsakaninta da wadannan kasashe ya kai sama da kilomita dubu biyar da dari hudu,jihar ce dake da iyakar kasa mafi tsawo da kuma bakin mafita mafi yawa a cikin kasar Sin.

Ina Xinjiang

Jihar Xinjiang tana cibiyar Asiya.Daga arewacinta zuwa kudancinta da akwai tsaunukan Altay da Tianshan da kuma Kunlun,a tsakanin tsaunuka da akwai kwarin Junggar da na Tarim.Ana kiran kudancin tsaunin Tianshan kudancin jihar,arewancin tsaunin Tianshan arewacin jihar,ana kira kwarin Hami da Turfan gabashin jihar.Dukkan birane da garuruwa na jihar Xinjiang suna cikin dausayi,dausayi daya bayan daya da suke shimfidu a gefen kwarurruwa biyu tamkar lu'u lu'u a jihar nan.

Kogin Tarim dake cikin jihar Xinjiang kogi ne maras mafita ta teku mafi girma a kasar Sin,tafkin Bosteng,tafki ne mafi karancin gishi a cikin kasar Sin da kwarin Turfan wanda ya kasa leburin teku.

Jihar Xinjiang tana cikin yanayi busashe mai tsanani,yanayin ya sha bambam daga wuri zuwa wuri.Yankin Altay ya taba kasance yanki mafi sanyi a kasar Sin,yankin Turfan ya kasance yanki mafi zafi a kasar Sin cikin dogon lokaci.

Kashi biyu cikin kashi uku na hamadar kasasr Sin yana cikin jihar Xinjiang.Hamadar Takelamagan mai fadin kilomita dubu 330,hamada ce mafi girma a kasar Sin,kuma hamada ce ta biyu mai rairayi ga masu tafiya a duniya.Hamadar Gurbantonggute dake cikin kwarin Junggar wadda fadinta ya kai kilomita dubu 48,hamada ce mafi girma ta biyu a kasar Sin.Da akwai azurtattun albarkatun mai da gas da kuma ma'adinai a karkashin hamadar jihar Xinjiang.

A cikin jihar Xinjiang da akwai duwatsu da tsaunukan da dama da kankara ta kan rufe su shekara da shekaru sai ka ce randar ruwa da ta daskare.Mutanen jihar Xinjiang suna jerin gaba wajen mallakar albarkatan ruwa a kasar Sin.

(Hoton lokacin kaka na Kanas)

Tarihi

Xinjiang wani yanki ne na hadaddiyar kasa mai yawan kabilu na kasar Sin kafin shekaru dubu biyu da 'yan kai.A shekara ta sittin bayan bayyanuwar Annabi Isa(A.S),gidan sarauta na Han ya kafa wata gwamnati a bangaren Xiyu wadda ta mallaki yankin nan kai tsaye da ya hade da yankin tafkin Balkhash da na Pamir na yanzu.A cikin shekaru fiye da dubu na baya,bangaren Xinjiang yana karkashin mallakar gwamnatin tsakiya na kasar Sin,gwamnatin tsakiya ta kafa hukumomin kula da harkokin mulki na yankin Xinjiang.

Yau shekaru fiye da dari uku ke nan gidan sarauta na Qing,gwamnatin tsakiya ta nada wani Janar a garin Huiyuan na yankin Yili domin mallake bangaren Xinjiang baki daya.A shekara ta 1884,an kafa lardin Xinjiang,ta haka aka kara cudanya tsakaninsa da sauran larduna na cikin kasar Sin.

A watan Satumba na shekara ta 1949 aka yantad da Xinjiang ta hanyar lumana.A ran 1 ga watan Oktoba na wannan shekara,aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin,kamar yadda sauran larduna na kasar Sin suke,Xinjiang ta zam wata jiha ta kabilar Ughur mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin.

Sansanin Makamashi

Da akwai albarkatai masu yawan gaske a jihar Xinjiang,yawan kwal da gurbataccen man da aka gano da jihar Xinjiang ta tanada kowanensu ya dau kashi daya cikin kashi uku na irinsu a kasar Sin.Gas da aka tanada ya yi yawa.jihar Xinjiang ta kasance fili mafi girma na mai a bangaren arewa maso yammancin kasar Sin,kuma tana da makoma mai haske wajen yin safiyon mai a karkashin kasa mafi fadi.An yi kiyasi cewa filayen da ake tanadin mai da gas a jihar Xinjiang da fadinsu ya kai muraba'in kilomita dubu 740 dake da mai TON biliyan 20.8 da gas da yawansu ya kai cubic mita bliyan dubu goma,yawansu ya dauki kashi talatin cikin kashi dari na albarktan mai da gas da aka tanada a yankin kasar Sin. Kwararru na kasar Sin da kasashen waje sun dauki jihar nan jihar mai kawo alheri ga masana'antun man fetur na kasar Sin.A watan Oktoba na wannan shekara da muke ciki za a kammala aikin samar da gas daga yammacin kasa zuwa gabashin kasa,ta bututun gas da za a shimfida za a samar da gas daga jihar Xinjiang zuwa birnin Shanghai da kewayensa dake gabashin kasar Sin.

Jihar Xinjiang ta fi yawan albarkatun kwal a kasar Sin da ya kai Ton sama da biliyan dubu biyu,watau ya dauki kashi arba'in cikin kashi dari na kwal da kasar Sin tanada.Wurin gwajin samar da wutar lantarki da karfin iska a Dabanchen wuri ne mafi girma na samar da wutar lantarki da karfin iska a kasar Sin.

>>[Tattalin Arzikin Xinjiang]

Tattalin arzikin masana'antu

Tattalin arzikin masana'antu ya samu saurin cigaba a jihar Xinjiang a halin yanzu,an sami wani cikakken tsarin masana'antu ciki har da narke karfuna da kanannaden karfe da haka kwal da mai,da kera injuna da hada magagungunan kemical da yin kayayyakin gine gine da saka da sukari da takarda da jima da sigari.An kuma bunkasa harkokin fitar da kayayyakin dake da halayyar musamman ta jihar Xinjiang da sana'o'in da jihar Xinjiang ta fi samun cigaba cikin amfani da albarkatun da jihar nan ke da su.Jihar Xinjiang ta mallaki masana'antu iri iri har fiye da dubu sittin,da ire iren kayayyaki sama da dubu biyu da suka shafi fannonin man fetur da kwal da narke karafa da samar da wutar lantarki da saka da masana'antun kemical da kera injuna da yin kayayyakin gine gine da abinci.

Muhimman ayyukan masana'antun da ake yi a jihar Xinjiang su ne aikin samar da kayan ethylene a Dushanzi,da aikin samar da kayan polyester,da aikin hada takin zamani na biyu,da mataki na farko da na biyu na aikin gina masana'antar samar da wutar lantarki ta Manas da tashar ba da wutar lantarki da karfin ruwa dake bakin duwatsun Jingda,da mataki na hudu na aikin fadada masana'antar sama da wutar lantarki ta Hongyanchi,da wurin samar da wutar lantarki da karfin iska a Dabnchen wanda ya fi girma a cikin irinsu na kasar Sin.

Aikin gona a Jihar Xinjiang

Jihar Xinjiang tana da isashen hasken rana da kuma filayen noma,mutanen jihar sun gano hanyoyin noma a cikin dausayi a wuraren dake da ruwa.Muhimmin amfanin gona shi ne shinkafa,amfanin gona na sayarwa su ne auduga da mabunkasa da ake kira " beet" a turance da kuma kayan da ake amfani da shi wajen yin giya(beer)Daga cikinsu noman auduga na da muhimmancin sosai a kasar Sin,kuma jiha ce da ta fi samu yawan auduga a kasar Sin,audugan da aka samun a jihar nan ta dau kashi sama da 95 cikin kashi dari na duk auduga mai kyau na kasar Sin,ingancinta ya yi daidai da audugan kasar Massar wadda ta fi shahara a duniya.

Xinjiang da ke da lakabi mai kyau watau wurin samar da kankana da 'ya'yan itatuwa,kuma jiha ce da ta samu ire-iren kankana da 'ya'yan itatuwa masu dadi sosai a kasar Sin.Da akwai inabi da kankanar Hami da pear da apricot da peach da ramegranate da cherry da fig da walnut da sauransu.Daga cikinsu inabi na Turfan da kankana na Hami na da sukari mai yawa a ciki.

A cikin shekarun baya,jihar Xinjiang ta kama hanyar zamani wajen bunkasa aikin gona,watau ta mai da noman tumatir da kayan beet da kuma karas da safflower da tattasai da inabi da auduga mai launi manyan sana'o'i cikin jihar.

(Manoman Uighur suna cire yayan itatuwa)

Kiwon dabobbi a jihar Xinjiang

Jihar Xinjiiang tana daya daga cikin jihohi masu muhimmanci wajen kiwo dabobbi a kasar Sin,da akwai dabobbin gida barkatai a cikinta.Tun fil azal ana kiwo tumaki da dawaki da shanu da awakai da jakuna da alfadari da rakuma da irin shanu da ake kira yak a turance.Jihar Xinjiang ta zo na biyu a kasar Sin kan nauyin naman tumaki da take da shi,yawan dabobbin gida dake cikin jihar ya zarce miliyan 40.

Fadin filayen ciyayi dake cikin jihar Xinjiang ya kai murabba'in kilomita dubu 570 wanda ya dau kashi 87 cikin kashi dari na filayen noma da dazuzzuka na jihar nan.Filayen ciyayi muhimmin wuri ne na kiwo dabobbi.kashi fiye da saba'in cikin kashi dari na dabobbin gida ana kiwonsu a filayen da samar da abubuwan da ake bukata.

Jihar Xinjiang sansani ne na renon sabbin dabobbin gida.Da akwai sabbin dabobbin gidan da ake renonsu ciki har da tumaki masu gashi mai kyau da sabbin shanu da dawaki da kuma aladai.Duk wadannan dabobbin gida suna da nasu halayen musamman kuma suna da daraja sosai wajen tattalin arziki.ba ma kawai muhimmiyar randar ajiye genes na dabobbin gida na jihar Xinjinag ba har ma ta kasar Sin baki daya.

Sana'o'in musamman

Da akwai sana'o'in musamman sama da goma a jihar Xinjiang,kamar su yin giya da abin sha da kayan madara,da kayan kemical da ake amfani da su a yau da kullum,da kayan kara kamshi,da gyara lu'u lu'u,da yin sukari da kayayyakin musamman da 'yan kananan kabilu ke bukata.Daga cikinsu muhimman kayayyakin da ake fitarwa su ne kayan tumatir da kayan giyar innabi,da abin sha na 'ya'yan itatuwa,da sukari da lu'u lu'u da sauran kayayyakin musamman.Ban da wannan kuma giyar madara da kuma yoghurt na dawaki da kuma abinci mai gina jiki wanda ya kunshe da abubuwan magani na Ughur sun fi samu karbuwa a kasuwanni.

>>[Kabilun Xinjiang]

Kabilar Uighur

Kabilar Uighur wata tsohuwar kabila ce dake zama a arewancin kasar Sin,a cikin harshen Uighur "uighur" yana nufin "hadin kai" ko "hadin gwiwa".Kabilar Uighur,muhimmiyar kabila ce jihar Xinjiang,yawan mutanenta ya kai sama da miliyan bakwai,suna shimfidu a duk jihar Xinjiang,yawancinsu suna zama a Kash da Hetian da Akesu da sauran wurare kudu da duwatsun Tianshan.Suna da nasu harshe da rubutu.

Tufaffin gargajiya na mutanen kabilar Uighur su ne hula mai zanen furanni ga maza da mata, tsofaffi da yara,Maza sun fi so babar riga,da rigar ciki mai zane,mata sun fi son doguwar riga da ake kira "dress" a turance da karamar riga mai launin baki da ake kira 'vest',da abin kune da munduwa da zobe da abin wuya,'yan mata suna son kitso,'yan birane suna sa kayan zamani.

Mutanen Uighur suna da da'a da ladabi.In wani ya gana da babansa ko amininsa,ya kan ajiye hannunsa na dama a gaban kirji,ya sunkunyar da kansa,sai ya yi gaisuwa.kuma suna son baki sosai.

Mutanen Uighur mutane ne masu sha'awar wake wake da raye raye.Mutane ne da suka shahara wajen yin wasannin raye raye masu kyaun gani da ban sha'awa tare da kida mai dadin ji,wannan ya shaida halayyar mutanen Uighur mai hazikanci.

Noma ita ce muhimmiyar sana'ar mutanen Uighur,kuma suna kiwon dabbobi,kuma suna da al'adar ciniki da yin kayayyakin hannu da na fasaha.Darduma da surfani da kayan siliki da butar tagulla da wuka da kayan kidan da suka yi suna da nasu tsarin musamman na kabilarsu.

(Kyawawan 'yan mata na Kabilar Uighur)

Kabilar Kazak

Da akwai mutanen Kizak kimanin miliyan daya da dubu metan a jihar Xinjiang,yawancinsu suna zama yankin kabilar Kazak mai ikon tafiyar da harkokin ta a bangaren Yili da ke arewancin jihar.Mutanen Kazak suna da nasu harshe da rubutu.

Yawancin mutanen Kazak makiyaya ne,kadan daga cikinsu suna zauna a wuri daya suna noma.Yawancin makiyaya suna kiwo dabobbinsu bisa yanayi suna kiwon dabobbinsu a wuraren da ke da ruwa da ciyayi.

Mutanen Hazak suna so baki sosai,su kan samar da abinci mafi dadi ga bakon da ya bakunci gidansu har ma da naman tumaki.In lokacin abinci ya yi,maigida ya ajiye naman kan tumaki cikin faranti a gaban bako,bako ya yanke wani kashi daga kan tumaki ya ci,sa'an nan ya yanke kunnen tumaki'ya ba 'ya'yan maigida,daga baya ya mayar da kan tumaki ga maigida.

Mutanen Kazak maza da mata sun gwanance a hawan dawaki.Maza samari sun gwamance a kokawa da kama akwiya.A kowace salla ko biki makiyaya su kan shirya wasan hawan dawaki ko yin gasa,a cikin wasa maza dake bisa kan dawaki na gaba cikin gudu,'yan mata na bi sawunsu,wasa ne da samari matasa suke so,kuma kyakkyawar dama ce gare su da samu masoyi ko masoyiya.

(Wasan hawan dawaki na Kabilar Kazak)

Kabilar Kirgis

Yawan mutanen Kirgis ya kai fiye da dubu 150,suna da nasu harshe da rubutu.

Yawancin mutanen Kirgis suna zaune ne a yankin Kirgis mai ikon tafiyar da hakokin kansu na Kezilesu kan tudun Pamir dake yammacin jihar Xinjiang,kuma makiyaya ne.A lokacin bazaar su kan yi kaura sun zama dab da koguna a karakara,a lokacin sanyi su kan shig kwarin duwatsu dake nufin rana.Gidaje da suke zaune a ciki nada taga a sama,kewayensu da akwai kayan lambu da kankana da kuma 'ya'yan itatuwa.Suna da abinci iri iri.daga cikinsu kayan madara sun fi yawa.

Tufafin gargajiya na mutanen Kirgis suna da kyaun gani.Maza suna son hular ulu na musamman,mata suna son riga mai aninin azurfa.'Yan mata na yin kitso da yawa,bayan aure,kitso biyu gare ta.

>>[Yawon Shakatawa a Xinjiang]

Tafkin Kanas

Tafkin Kanas yana cikin gundumar Burjin dake arewacin jihar da tazarar kilomita 150 daga hedkwatar gunduma,tafki ne da ke kan duwatsu cikin kungurmin daji na Altay.Cikin harshen Mongoliya,"Kanas" yana nufin tafkin dake cikin kwari.Tafkin Kanas ya kasance kan duwats masu tsayin mita 1374 daga leburin teku,mafi zurfi cikin tafkin ya kai mita 188.5,fadinsa ya kai muraba'in kilomita 45.73.

Kewayen tafkin Kanas duwatsu ne da kankara ke rufe su,ruwan tafki na walkiya a karkashin hasken rana,lallai wuri ne mai kyaun gani sosai. Shi ne wuri daya kawai a kasar Sin dake da irin wadannan dabbobi da itatuwa da ciyayi na kudancin Siberia,yawan ire iren itatuwa da ake da su ya kai dari takwas,dabbobi 39 da tsuntsaye 117 da dabobbi hdu masu rarrafe a ruwa da kasa,da kwari sama da dari uku.Da yawa daga cikinsu babu irinsu a sauran larduna da jihohin kasar Sin sai jihar Xinjiang.A bangaren nan akwai kungurmin daji da koguna da dama,kuma yana da kyaun gani sosai,wuri ne mai daraja wajen yawon shakatawa da kare muhalli da binciken kimiyya da tarihi da kuma al'adu.

Tsohuwar ganuwa ta Loulan

Tsohuwar ganuwar Loulan tana kuriyar arewa maso yammacin tafkin Luobu da ya bushe a kudancin jihar Xinjiang,ta taba zama muhimmin wuri ne a kan hanyar silki ta zuwa kasashen yamma daga kasar Sin.Ga shi a yau tana cikin hamada,wuri ne da mutane ba su faye zuwa ba kuma da hadari.

Bisa abin da aka tanada a cikin littafin tarihi,an ce a karni na biyu kafin bayyanuwar Annabi Isa(A.S),Loulan yana daya daga cikin wurare masu wadata a bangaren Xiyu.Abin mamaki shi ne bayan shekaru tsakanin dari biyar da dari shida kasar mulukiya ta Loulan wadda ta fi shahara ta bace ba zato.Ta yaya ganuwar Loulan ta bace?batu ne da ya jawo hankulan masu binciken kayayyakin tarihi da masana kimiyya na gida da na kasashen waje cikin dogon lokaci.Loulan, wuri ne mai ban al'ajabi da masu binciken labaran kasa ke sha'awar zuwa.

Masu binciken kayayyakin tarihi sun gano cewa hamada ce ta cinye tsohuwar ganuwar Loulan saboda kogunan dake wurin sun karkata hanyoyinsu da iska mai dauke da rairyi ya kan kada da sauran dalilai da dama.An ce fadin ganuwar loulan ya kai muraba'in mita dubu 120,an gina ta ne da kwaba da kyauro da reshen itatuwa,Wata tsohuwar hanyar kogi ta ketare ganuwar nan daga arewa maso yamma zuwa kudu maso gabas.Har yanzu ana iya ganin wuraren hasumiyar addinin Buddha da gine gine kewayenta,da tsohon gari da wuraren ba da alamun yaki da rumbuna hatsi da tsofaffin kaburbura.A cikin wani tsohon kabari a Loulan an gano "wata busashiyar gawar kyakkyawar mata ta Loulan" mai tsawon shekaru 3800.A cikin tsohuwar ganuwa har wa yau dai ana iya ganin guntayen tukwane da tabarmar ulu da tsofaffin kerarru kudade da makamai da silk da sauran kayayyakin tarihi da yawa.

Kogunan mutum-mutumin Buddha

A gefunan hanyar silki da ta shimfidu a jihar Xinjiang da akwai mashahuran wuraren tarihi da dama ciki har da mashigi da tasamahara da kogunan dutse,da gidajen waya da wuraren ba da alamun tada yaki.

Kogon dake da mutum-mutumin Buddha sama da dubu a wurin Kezil da wurin Pazikelike kogunan dutse da suka shahara a duniya,mutum-mutumin da zane zanen jikin bango dake cikin koguna sun hada al'adun kasar Sin da na Indiya da na Farisa,kuma suna da sigar musamman na fasaha,,kuma sun shaida hanyoyin aikin da mazaunan kabilu dabam dabam suke bi da zamansu a wancan zamani.

"Pazikelike" harshe ne na Uighur,yana nufin gangarar duwatsu.Kogon nan yana arewa maso gabashin birnin Turfan.An haka kogon nan ne daga karni na shida zuwa karni na sha hudu bayan bayyanuwar Innabi Isa,a jikin kogon akwai zane zane masu kyaun gani sosai wajen rubutu ko launi,mutane a zane tamkar a raye suke,cigaba ne na zanen gidan sarauta na Tang dake cikin kogon Mogao.Dayake zanen dake jikin Kogon ya sha lahani mai tsanani,fadin zanen da ya rage ya kai muraba'in mita sama da 1200.Sanin kowa ne kogon nan wata taska ce ta adana kayayyakin fasaha mafi muhimmanci wajen fasahohin addinin Huihu,kuma abubuwa masu daraja ne na binciken tarihi da al'adu da fasahohi na bangaren Xiyu.

Turfan

A tsakiyar jihar Xinjiang da akwai wani wurin da ake kira wuri mai zafi,a nan Turfan ta ke inda ake noman iri iri masu inganci.A karkashin kasa na wannan wurin musamman da akwai ruwa mai yawan gaske,shi ya sa a kan noma kankana da 'ya'yan itatuwa kamar innabi da gunaguni.'Ya'yan itatuwan da aka samu a wannan wuri sun kushi da sinadarin sukari mai yawa bisa sanadin rashin ruwan sama,masu yawon shakatawa da yawa suna so su yi yawon shakatawa a wannan wuri domin suna so su ci 'ya'yan itatuwan wurin.

Turfan kasa ce ta innabi.Garin yana cikin itatuwan innabi haka kuma mutane.ko mutanen wuri ko baki dukkansu su kan yi magana kan innabi cikin fara'a.Bisa abin da aka rubuta a cikin tarihi,an ce yau sama da shekaru dubu biyu ke nan aka fara noman innabi a wannan wuri.

A Turfan ko ina za ka tarar da tsofaffin lambunan innabi,a gefunan hanyoyi manya da kanana,a gidaje gaba da baya,itatuwan innabi da aka dasa kamar rumfuna sun shimfidu.A nan Turfan a kan samu busashen innabi ta hanayr musamman,watau an gina dakuna da tubali,a jikin bangon daki akwai kofofi da tagogi masu yawan gaske domin wucewar iska.innabi ya bushe cikin iska mai zafi,shi ya sa innabin wurin nada dadin ci sosai,mutane suna sha'awarsa.

Gwamnatin birnin Turfan ta shimfida wani titin musamman domin shere masu yawon shakatawa a gefunan titin akwai hanyoyin dake tsakanin dakuna,wurin nishadi da dakunan nuna kayayyakin tarihi,dukkansu suna da alaka da innabi.Ga shi a yau da isowar baki a Turfan,suna iya shiga lambunan innabi,suna iya more wuri mai kyaun gani da ni'ima,kuma suna iya dibar innabi su ci yadda suka ga dama.

Kash

Kash cikakken sunansa "Kashgel",yana da kyakkyawar lakabi "lu'ulu'u a kan hanyar silki",shahararen birni ne na tarihi da al'adu a kasar Sin.

Kash wani tsohon dausayi ne dake yammancin Talimu tamkar wurin kudancin kasar Sin,kuma wani muhimmin sansani ne na noman auduga na sayarwa a kasar Sin.

Kash wuri ne na yawon shakatawa,yana da kyakkyawan gani sosai da jawo hankulan mutane.Masu yawon shakatawa na kasashe dabam dabam za su iya yin yawo a cikin hamada ko duwatsu da ke rufe da kankara da manyan duwatsu.Kash yana da dadadden tarihi,da wuraren tarihi na al'adu kamar su masallancin Aitigal wanda ya fi shahara,da kabarin Apakehejia(matar sarki),da kabarin mohammed Kashgari,da tsohon wurin tarihi na gidan sarauta na Yelqianghan,duk wadannan abubuwan sun shaida al'adun Uighur da fasahohinsu wajen gine gine.

Kash na tattare da al'adun tarihi da dabi'un kanana kabilu da wurare masu ban sha'awa,wuri ne mai ba da misali da wakilci sosai a jihar Xinjiang gaba daya yana jawo hankulan masu yawon shakatawa na gida da na waje,shi ya sa a kan ce"In ba ka isa Kash ba kada a ce ka shiga jihar Xinjiang."

Hetian

Hetian akan kira ta "Yutian" a zamanin can da na tarihi,kuma wata tsohuwar kasa ce mai wayewar kai da ta shahara a bangaren Xiyu.tana cikin cibiya ta tsakanin Asiya da Turai,muhimmin wuri ne a hanyar silki ta kudu.Mutanen kabilu da dama suna zama a wurin nan daga zuriya zuwa zuriya,al'adu na kasashen gabas da na yamma sun hadu a nan,a kan ganin manzanni da 'yan kasuwa na kasashe dabam dabam a hanyar.

Hetian ya dab da hamadar Takelamagan a arewa da duwatsun Kunlung a kudu.A nan da akwai hamada dake da duwats masu kankara na ban al'ajabi,da karkarar ciyayi dake da tafki mai ban mamaki,da filayen noma dake da giza gizon itatuwa.Hetian ya fi shahara wajen samun duwatsu masu daraja da ake kira "jade"a turance da silki da darduma da kilisai da kankana da 'ya'yan itatuwa,shi ya sa a kan kira shi "garin duwatsu masu daraja",da "grin silki" da 'garin 'ya'yan itatuwa".

>>[Addinai na Xinjiang]

Hada-hadr addinai

A cikin tarihi,addinin Buddha da addinin Jing da addinin Moni da kuma addinin musulunci sun taba bazuwa a Xinjiang wadda ta kasance wuri daya kawai a duniya na cudanyan manyan addinai guda hudu.

A karni na farko na bayyanuwar Innabi Isa,addinin Buddha ya shiga cibiyar kasar Sin ta hanyar siliki ta Xinjiang.addinin Jing wani rukuni ne na addinin Krista,ya shiga Xinjiang a karni na shida bayan bayyanuwar Annabi Isa(A.S).Masu binciken kayayyakin tarihi sun kuma gano cewa a zamanin can da na tarihi a Xinjiang ba ma kawai addinin Jing ya fi bazuwa har ma wata cibiya ce ta addinin nan.Daga baya addinin musulunci ya shigo,addinin Jing ya ja da baya daga Xinjiang.A shekara ta 694 bayan bayyanuwar Innabi Isa,addinin Moni ya shiga kasar sin.

Tun farkon karni na 19,an gano takardu da yawa na addinin Moni a kogon kayan tarihi na Mogao a Dunhuang da Turan a Xinjiang,wannan ba ya da shaida cewa addinin Moni ya taba bazuwa a wurare dabam daban na arewa maso yammancin kasar Sin kuma yana da tasiri mai zurfi.A tsakiyar karni na goma,addinin musulunci ya shigo Kash ta hanyar silki,kuma ya bazu a Xinjiang gaba daya tsakanin karni na 16 da na 17.Ga shi a yau mutanen kabilu na Uighur da Kazak da Hui da Uzibik da Kirgis da Tajik da Tatar dukkansu suna bin addinin musulunci.

Mabiyan addinai a Xinjiang

Xinjiang jiha ce dake da addinai da yawa a halin yanzu.Musulunci na da babban tasiri a zaman yau da kullum na mutanen Xinjiang.Da akwai masallatan musulunci da sauran wuraren addinai ciki har da dakin ibada na addinin Lama da dakin addinin Kirista sama da dubu 23 da ke biyan bukatun mabiyan addinai a jihar Xijiang.

■ Tibet

>>[Me Ka Sani Game da Tibet]

Me ka sani game da Tibet

Jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta tana daya daga cikin jihohi biyar masu ikon tafiyar da harkokin kansu a kasar Sin inda mutanen kabilar Tibet sun fi yawa,tana kudu maso yammacin kasar Sin haka ma a tudun Qinghai-Tibet plateau,ta yi iyaka da Myama da Indiya da Bhutan da Sikkin da Nepal daga kudu zuwa yamma,tsawon iyakar kasa tsakaninta da wadannan kasashe ya kai kilomita kimanin dubu hudu,fadin jihar ya kasance muraba'in kilomita miliyan daya da dubu metan da ashirin,ta dau kashi sha biyu da digo takwas cikin kashi dari na daukacin fadin yankunan kasar Sin.

Jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta tana kan tudun Qinghai-Tibet plateau da matsakaicin tsayinsa ya kai mita dubu hudu daga leburin teku shi ya sa a kan ce tana kololuwar duniya.Yawan mutanen jihar Tibet ya kai miliyan biyu da dubu dari shida,daga cikinsu mutanen kabilar Tibet sun kai miliyan biyu da rabi wadanda suka dauki kashi 96 cikin kashi dari na mutanen jihar,jihar Tibet,jiha ce mafi karancin mutane a kasar Sin,a fadin kasa na kwatankwancin muraba'in kilomita daya mutanen da ke zaune a ciki bai kai biyu ba.

Labarin kasa

Tudun Qinghai-Tibet Plateau yana da nasa halayen musamman na halita,yana kan matsayi mai muhimmanci daga cikin tuddai da duwatsu na duniya baki daya,a kan ce ita ce "kuriyar duniya ta uku."

Muhimmin dalilin da ya sa aka dauki tudun Qinghai-Tibet plateau "kuriyar duniya ta uku" shi ne yana kan tudu mai tsayi sosai daga leburin teku kuma yana da yanayi mai tsananin sanyi.Matsakaicin tsayin tudun ya kai sama da mita dubu hudu,a kewayensa ma da manyan duwatsu ko ma a kansa akwai duwatsu masu tsayi.A cibiyar tudu mai tsayin mita dubu hudu da dari biyar,zafin yanayi ya yi kasa da sifiri na centigrade,ko ma a lokacin mafi zafi,zafin yanayi ya yi kasa da digiri goma na centigrade.

Kasancewar tudun Qinghai-Tibet plateau mai tsayin sma da mit dubu hudu tana da alaka da babban motsin duniya a can can zamanin da inda aka samu duwatsun Himalaya,duwatsu da yawa a kan tudun nan da tsayinsu ke tsakanin mita dubu shida da dubu takwas daga leburin teku,sabbin duwatsu ne a duniya,kuma mafarin manyan koguna da dama na Asiya.

Tarihi da halin da ake ciki na yanzu

Kafin bayyanuwar Innabi Isa,kakanin kakanin kabilar Tibet sun zaunu a tudun Qinghai-Tibet plateau suna da mu'amalla da mutanen kabilar Han dake zama cikin kasar Sin.Bayan da aka shafe shekara da shekaru,kananan kabilu barkatai sun hadu har sun zama kabilar Tibet a yanzu.

A farkon karni na bakwai bayan bayyanuwar Innabi Isa,halin baraka na tsawon shekaru fiye da dari uku a bangaren tsakiyar kasar Sin ya kare.A wannan lokaci jarumin kabilar Tibet Songzuanganbu ya kafa gidan sarauta na Tufan dake da hedkwata a Lasa.A lokacin da yake kan karagar mulki,Songzuanganbu ya tsamo fasahohin zamani na aikin kawo albarka da ilmin siyasa da al'adu daga gidan sarauta na Tang,ya kuma rike kyakkyawar dangantakar aminci da gidan sarauta na Tang wajen siyasa da tattalin arziki da kuma al'adu.

A tsakiyar karni na 13,yankin Tibet ya zama wani yanki na kasar Sin.Dayake an samu wasu dauloli daya bayan daya da canje canjen mulkin gwamnatin tsakiya,a duk lokaci Tibet yana karkashin mulkin gwamnatin tsakiya.

Bayan da aka kafa gidadn sarauta na Qing a shekara ta 1644,gwamnatin tsakiya tana tafiyar da harkokin mulki na kanta a jihar Tibet yadda ya kamata bisa tsare tsare da shari'a.A shekara ta 1727,gidan sarauta na Qing ya nada wani minista a jihar Tibet dake tafiyar da harkokin mulki a madadin gwamnatin tsakiya.

Bayan da Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin ta kafu a shekara ta 1949,gwamnatin jama'a ta tsakiya ta dauki matakin yantar da Tibet ta hanyar lumana bisa tarihinta da kuma halin da take ciki a wannan lokaci.Gwamnatin jama'a ta tsakiya ta biya bukatun mutanen jihar Tibet ta kawo sauyi bisa tafarkin dimokuradiya,ta soke tsarin bayi manoma na gargajiya,ta haka bayi manoma da sauran bayi miliyoyi sun sami 'yanci,ba a dauke su kmar kadarorin maigida na bayin manoma ba yadda suka yi a da da cinikinsu da mai da su bayin kyauta,ko musayarsu da biyan bashi da su,ba a tilasta musu da su yi aiki domin maigida na bayin manoma ba,daga nan sun iya yin abubuwa yadda suka ga dama,su ma sun zama masu gida a cikin sabuwar kasar Sin.Bayan da aka rika samun cigaba cikin kwanciyar hankali,an kafa jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta a watan Satumba na shekara ta 1965.

>>[Kabilu na Tibet]

Takaitaccen labari

Jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta,jiha ce da aka fi samun mazaunan kabilar Tibet a kasar Sin da suka dauki kashi 45 cikin kashi dari na dukkan mutanen kabilar Tibet a kasar Sin.Ban da kabilar Tibet,da akwai kabilu sama da goma dake zaune a jihar daga zuriya zuwa zuriya ciki har da Han da Hui da Menba da Luoba da Naxi da Nu da Dulong.kuma da yankunan da aka kebe musamman domin mutanen kabilun Menba da Luoba da Naxi.

Kabilar Tibet

Kabilar Tibet muhimmiyar kabila ce a jihar Tibet.Harshenta yana cikin sashen harsunan Tibet-Myanma na iyalin harsunan Han-Tibet.Aikin gona da kiwon dabobbi ne muhimman sana'o'in mutanen kabilar Tibet,mazaunan birane suna cikin sana'o'in aikin hannu da kere kere da kasuwanci.

Mutanen kabilar Tibet mabiyan addinin Buddah iri na Tibet,masu fara'a da gwanance ma newajen rera wakoki da raye raye.Wakokinsu nada dadin ji sosai.In an rera waka a kan yi raye raye.Mazan kabilar Tibet su kan sa babbar riga da taguwa a ciki,mata su kan sa babbar riga maras hannu da majanyi,matan aure su kan daura zane mai launi.Maza da mata dukkansu suna da kitso a kai,suna sha'awar kayan ado na kai.Tufaffinsu sun sha bambam bisa wurare.Abincinsu shi ne garin wake,su kan sha ti hade da nono tsala da na madara da giyar sha'ir,sun fi so naman shanu da na tumaki.A zamanin can da mutanen tudun Tibet plateau su kan binne gawawwaki cikin kasa,ga shi a yau ana bin hanyoyi dabam dabam na barin gawawwaki a waje da kone su ko sa su cikin ruwa.

Kabilar Menba

Kabilar Menba tsohuwar kabila ce a tudun Tibet plateau,yawancin mutanen kabilar suna zaune a yankin Menyu dake kudancin jihar Tibet mai ikon tafiyar da kanta,wasu suna zaune a warwatse a gundumomi na Meituo da Lingzhi da Cuona.Aikin gona muhimmiyar sana'arsu ne kuma suna kiwon dabobbi da kula da dazuzuka da farautar dabobbin daji da aikin hannu.Maza da mata na kabilar Menba su kan sa doguwar riga mai launin ja da karamar hula mai launin rawaya ko hular ulu mai launin baki;Mata su kan sa munduwa da 'yan kunne da sauran kayan ado,maza su kan daura wuka a kugu.Maza da mata dukkansu suna so su sha giya da taba da hanci.Abincinsu shi ne shimkafa da masara da sauransu.Yawancin mutanen kabilar Menba mabiyan addinin Buddha ne irin na Tibet,ana bin darikar bokaye a wasu wurare.Ana binne gawawwaki ta hanyoyi dabam dabam ciki har da sa su cikin ruwa da binne su a kasa ko a bar su a waje ko a kone su.

Kabilar Luoba

Mutanen kabilar Luoba suna zaune a yankin Luoyu a kudu maso gabashin jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta.Sana'arsu noma da sakar kayan gora.Maza su kan sa karamar kwat ta ciki da aka saka da ulun tumaki da hular da aka saka da fatar dabobbi ko rassan itatuwa.Mata su kan sa karamar riga dake da matsatsen hannu mai wuya da kuma daura zane matsatse da abin rufe cinyoyinsu.Abincinsu shi ne masara da shimkafa da sauransu.

>>[Tattalin Arziki]

Masana'antu

A da babu masana'antun zamani a jihar Tibet sai ayyukan hannu na gargajiya kamar su yin darduma da kilisai da tabarma da zane mai launi domin mata da dogayen takalma da kwanon katanko.Bayan da aka yantar da Tibet ta hanyar lumana a shekara ta 1951.musamman bayan da aka kawo sauyi bisa tafarkin dimakuradiya a shekara ta 1959,harkokin masana'antu sun bunkasu da sauri,an kafa masana'antu na samar da wutar lantarki da narke karafa da haka kwal da kera injuna da hada magungunan kemical da kayan gine gine da kula da dazuzuka da yin ashana da kayan leda da saka da abinci da jima da yin takarda,yawancinsu kanana masana'antu ne da suka kafu a birnin Lasa da Lingzhi da Rikezhe.

Kasuwancin zamani da yawon shakatawa da gidan waya da hidimar abinci da al'adu da nishadi da sadarwa sun samu saurin bunkasuwa da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin jihar Tibet.

A shekara ta 2003,jimlar kudin kayayyakin masana'antun da aka samar a jihar Tibet ta kai kudin Sin Renminbi Yuan miliyan dubu biyu da dari bakwai da saba'in,masana'antun sun dau kashi 15 cikin kashi dari na tattalin arzikin jihar Tibet.A nan gaba jihar Tibet za ta himmantu wajen bunkasa masana'antu,za ta daidaita tsare tsaren sana'o'inta kuma za ta dukufa ka in da na in wajen ayyukan ma'adinai da dazuzuka da kayan dabobbin gida,za ta kokkarta wajen sabunta fasahohin masana'antu ta yadda za a kara kudin samarwa na masana'antu a cikin kayayyakin samarwa na tattalin arzikin kasa.

Aikin Gona

A jihar Tibet kiwon dabobbi shi ne muhimmiyar sana'a,aikin gona kuma na da muhimmanci kuma yana da halayen musamman nasa a kan tuddai masu sanyi.Aikin gona ya sha bambam bisa wurare da tsayinsu.Ana noma shuke shuke a kwari mai ni'ima.Babu amfanin gona da yawa,sha'ir muhimmin kayan abinci,bayansa sai alkama da ganyaye masu ba da mai da wake da shinkafa da masara kadan.Daga cikinsu fadin filayen da aka shuka sha'ir ya fi girma ya shimfidu a yankunan masu tsayi tsakanin mita 2500-4500 daga leburin teku saboda sha'ir yana iya jurewa sanyi.

Kiwon dabobbi

Sana'ar kiwon dabobbi gishiki ne na tattalin arzikin noma na jihar Tibet,tana da dadadden tarihi da makoma mai haske.Fadin filayen ciyari a jihar ya kai kadada miliyan 82,daga cikinsu kadada miliyan 56 ana amfani da su,watau sun dau kashi daya cikin kashi biyar daga fadin filayen ciyayi na duk kasa baki daya.suna daya daga cikin manyan bangarori biyar na kiwo dabobbi a kasar Sin,sama da kashi casa'in cikin dari suna kan duwatsu da tuddai,ciyayin na da abin gina jikin dabobbi sosai.

Jimlar kudin da aka samu daga wajen kiwon dabobbi ta dau kashi sittin cikin kashi dari na yawan kudin da aka samu daga fanning aikin gona.Daga cikin dabobbin da ake kiwo a jihar da akwai shanu masu tsawon gashi da tumaki da akuya,shanu masu tsawon gashi sun fi yawa.Shanu masu tsawon gashi na iya jurewa sanyi da shakar iska maras oxgen da yawa,suna so su zauna a wurare masu damshi da sanyi,a kan ce shi ne "jirgi a kan tudu".Shanu masu tsawon gashi ya kan samar da madara da nama da yawa,ana iya amfani da shi wajen sufuri.Tumakin Tibet ma na iya jurewa sanyi da kishirwa a cikin zamansu kan tudu mai sanyi,kiwonsu nada fa'ida,shi ya sa tumakin da ake kiwo sun barbazu ko ina a jihar.

Dazuzuka

Fadin dazuzukan jihar Tibet ya kai wajen kadada sama da miliyan shida da dubu dari uku wanda ya dauki kashi biyar cikin kashi dari na fadin jihar nan,ya kuma kasa da matsakaicin matsayi na duk kasar Sin baki daya.Duk da haka yawan katakon da aka tanada a jihar ya kai cubic mita miliyan dubu daya da dari hudu,tana kan matsayi na biyu daga cikin jihohii da larduna na kasar Sin wajen tanadin katako,muhimmin sansani ne na samun katako a kasar Sin.Dazuzuka sun shimfidu a sashen tsakiya da na kasa na kogin Yaluzhanbu da kwarin yankin kudanci da gabashin jihar.Yawancin itatuwan dake cikin dazuzuwa su ne itatuwa masu jurewa sanyi,suna girma da saurin da ba a samunsa a sauran wuraren duniya ba.

Gwamnatin jihar Tibet ta dora muhimmanci kan muhalli,ta kebe yankuna 18 na kare muhalli a matsayin kasa da na jihohi,fadinsu ya dauki kashi 33.9 cikin kashi dari na fadin jihar,ta haka 'ya'yan halite dake kasance a kan tuddai da muhallin birane da garuruwa sun samu kariya yadda ya kamata.A halin yanzu muhallin jihar Tibet ya kasance kamar yadda ta ke a da,jiha ce mafi nagarta wajen kare muhalli a kasar Sin.

Ayyukan taimakon jihar Tibet

Tibet da ake kiranta "kololuwar duniya",tattalin arzikinta da zamantakewarta a baya suke cikin dogon lokaci bisa sanadin tarihi da halin da ta kasance.Ayyukan da gwamnatin tsakiya ta zuba jari da kuma larduna da birane tara na kasar Sin suka ba da taimakon yinsu sun kai 43,kudin da aka zuba ya kai kudin Sin Renminbi Yuan miliyan 480.A gun taro na uku da gwamnatin tsakiya ta kira kan ayyukan Tibet a shekara ta 1994,an tsai da kudurin yin ayyuka 62 domin ba da taimako ga jihar Tibet wadanda suka shafi aikin gona da kiwon dabobbi da dazuzzuka da makamashi da sufuri da gidan waya da sadarwa,kudin da aka zuba ya kai kudin Sin Renminbi Yuan miliya 4860.Yanzu an kammala ayyukan nan da fara amfani da su,har sun kawo babbar fa'ida ga tattalin arziki da kuma zamantakewar al'umma.

Ayyukan 62 na ba da taimako ga Tibet sun kara saurin bunkasa tattalin arzikin Tibet kuma sun canza dabi'un zama na mutanen tuddai na tsawon shekaru sama da dubu.Ga shi a yau a birnin Lasa,hedkwatar jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta,'yan birane za su iya kallon shirye-shirye da dama daga rediyo mai hoto ta taurarin dan Adam a sararin samaniya,A wuraren dake tsakanin koguna uku dake gabashin jihar Tibet,manoman wurin sun mai da su dausayi;a kudancin Tibet,manyan gine ginen koyarwa sun maye guraban tsofaffin kanana dakuna,yaran manoma sun shiga makaranta tare da fatan iyayensu,a dandalin dake gaban fadar Budala da aka gina da tubalin duwatsu,tutoci masu launi iri iri na karkadawa,mutane na kai da kawowa a duk shekara,ya zama wata tagar bayyana fuskatar tudu mai kankara ga sauran kasashen duniya.

>>[Yawon Shakatawa a Tibet]

Namucuo

"Cuo" yana nufin tafki cikin harshen Tibet.Da akwai tafki manya da kanana fiye da dubu daya da dari biyar a jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta,fadinsu ya kai muraba'in kilomita sama da metan da arba'in,sun dau kashi daya cikin kashi uku na fadin dukkan tafkin kasar Sin.Tafki kan tuddai masu tsayi ya fi fadi,kuma yana da ruwa mai zurfi da yawan gaske.

Tafki mafi girma a jihar nan shi ne Namucuo."Namucuo" yana nufin "tafki na sararin samaniya" ko "tafkin do "tafkin mala'ika",wuri mai tsarki da ya fi shahara a cikin addinin Buddha na Tibet.Yana tsakanin gundumar Dangxiong na birnin Lasa da gundumar Bange na yankin Naqu.A sashen kudu maso gabashin tafkin manyan duwatsu Tanggulashan da kankara ke rufe da su shekara da shekaru ke zaune,a arewancinsa tuddai masu tsayi sun shimfidu,filayen ciyayi ke kewayen tafki,tafki ya yi kama da wani madubi mai daraja da aka sa a cikin filin ciyayi da ke arewancin Tibet.Ga samarin sama mai shudi,ga tafki mai tsanwa,ga farin kankara,ga filayen ciyayi,ga tantin gashin shanu da tumaki,ga furani masu launi iri iri sun hadu sun zama wani kyakkyawan zane mai ban sha'awa.

Fadar Budala

Fadar Budala tana kan tudu na arewa maso yamma na birnin Lasa,hedkwatar jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta,fada ce mafi girma tamkar tasamahara da ke kan tudu mai tsayi daga leburin teku na duniya.An fara gina fadar nan a karni na bakwai bayyan bayyanuwar Innabi Isa,tana da benaye 13,fadinta ya kai kadada 41,an gina ta da tubalan duwatsu,tana da dakuna sama da dubu.A cikin fadar nan da akwai hasumiya da dama inda aka ajiye gawawwakin dukkan shugabannin addinin Tibet Dalailama na tarihi da dakunan tunawa da su da kuma dakuna iri iri na karatun littattafan addini.Hasumiya mafi tsayi ita ce hasumiyar Dalailama ta biyar,tsayinta ya kai mita 14.85,an gina ta da zinariya mai nauyi kimanin kilo dubu shida,lu'ulu'u manya da kanana sama da dubu hudu,da kuma sauran kayayyaki masu daraja masu yawan gaske.Dalailama yana zama cikin fadar yana tafiyar da harkokinsa na yau da kullum kuma yana yin ayyukan addinin Buddha.Dakin da ya ke kwana yana kan kolin tudu,shi ya sa rana ta kan haskaka dakin duk lokaci,da haka ana kiran dakin haske.

A shekara ta 1961,gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta mai da fadar Budala muhimmin wurin tarihi na duk kasa da ya kamata a kare ta.Ta kuma kebe kudin musamman kowace shekara domin kula da fadar nan da gyara ta domin hana ta lalacewa.Tsakanin bazaar ta shekara ta 1989 da rani na shekara ta 1994,kudin da gwamnatin tsakiya ta zuba wajen kula da fadar da kuma gyara ta daga dukkan fannoni ya kai kudin Sin Renminbi Yuan miliyan 53,fadar da aka yi mata gyarar fuska ta kara ba da haske.

Dakin Ibada na Dazhao da Titin Bakuo

Dakin Ibada na Dazhao yana cibiyar birnin Lasa,an gina shi ne a shekara ta 647 bayan bayyanuwar Annabi Isa,sarkin Tibet Songzuanganbu ya gina dakin nan domin shigowar gimbiya Wencheng daga gidan sarauta ta Tang a Tibet da sauranta.A cikin harabar dakin ibada da akwai wani kyakkyawan ginin Buddha mai benaye hudu da aka shafa masa fentin zinariya da tagulla da dakunan karatu da sauran gine gine,dukkansu suna da halayyar gine gine na gidan sarauta na Tang da kuma haliyar musamma ta kasar Nepal da Indiya.A cikin dakin ibada akwai mutum mutumin tagulla ke zaune na Sakyamuni mai shekaru 12 da gimbiya Wencheng ta kawo daga Changan.A jikin bangunan dakuna an zana zane iri iri na Tibet dangane da yadda gimbiya Wencheng ta shiga Tibet da tatsuniyoyi da al'mara,tsawonsu ya kai kimanin mita dubu,duk zanen da aka zana a jikin banguna tamkar a raye suke.

Dab da dakin ibada na Dazhao akwai wani titin da ake kira Baojiao,a gefunan titin da akwai kantunan da 'yan kasuwa na wuri da na Nepal da na Indiya suka kafa daya bayan daya,suna sayar da kayayyakin hannu na fasaha masu ban sha'awa.Abun da ya fi jawo hankulan mutane a wannan titin shi ne mutanen dake sukunyar da kansu a kan titin.Da farko su hada hannayensu tare,su yi sujada,suna tafiya.Wannan wata hanya ce ta nuna girmamawarsu ga addinin Lama,wani reshen addinin Buddha, suna nuna biyayyansu ga Buddha.Daga cikinsu akwai mutanen da suka zo nan daga nesa,da kuma mazaunan birni.Da safe su kan kewaye dakin ibada su sunkuyar da kansu wajen rabin awa,sa'an nan su koma gida su canja tufafinsu da wanke hannayensu da sannan si karya kumallo,daga baya su tafi aiki.sunkuyar da kansu tamkar motsa jiki ne da mutane na sauran larduna da jihohi suka kan yi domin kara lafiyar jikinsu.Amma a nan aikin addini ne,yana da wata ma'ana dabam mai zurfi,kuma wata hanyar musamman ce ta zaman mazaunan birnin Lasa mai halayen musamman.

Dakin Ibada na Zhashilunbu

Dakin ibada na Zhashilunbu dakin ibada ne mafi girma a cikin wani reshen addinin Tibet,yana da tarihi na tsawon sama da shekaru dari biyar,wurin addini ne da Dalailama ya kan yi kuma cibiyar harkokin siyasa ce.

Harabar dakin ibada tana kan gangarar tudu,da akwai dakunan karatu sama da hamsin da sauran dakuna sama da metan.Daga cikinsu akwai wani daki mai tsawon mita 30 inda mutum mutumin tagulla na Maitreya mai tsawon mita 26.2 ke zaune,an kasa shi gida gida akwai gidan kai da gidan fuska da gidan kirji da gidan kugu da kuma gidan kafa.An yi wannan mutum mutumin tagulla ne da zinariya kilo 235 da tagula kilo dubu 115.A jikin mutum mutumin akwai lu'ulu'u da duwatsu masu daraja iri iri da yawansu ya zarce dubu daya da dari hudu.

>>[Aikin Ba da Ilmi]

Takaitaccen labari

Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta aikata manufar shiga makaranta a fayu a jihar Tibet.Gwamnati ce ta biya kudin makaranta daga ta firamare zuwa jami'a ga daliban Tibet.A jihar Tibet kawai ake tafiyar da wannan manufa.A zamanin da a jihar Tibet babu wata makaranta ta zamani balle ma jami'a.Ga shi a yau akwai jami'o'I guda hudu a jihar Tibet.

Domin ba da taimako ga jihar Tibet wajen bunkasa ilmi,gwamnatin tsakiya ta kafa makaranta ko ajujuwa domin daliban Tibet a sauran larduna da birane 21 a cikin kasa,ta horar da mutanen kimanin dubu goma da suka kammala karatunsu a jami'a ko makarantun middle na musamman tun daga shekara ta 1985.Gwamnatin tsakiya ta ba daliban Tibet kudin tufaffi da abinci da na kwana da kuma na makaranta.

Kawo karshen shekara ta 2003,da akwai makarantu iri iri sama da dubu daya da sha daya a jihar Tibet,wuraren koyarwa dubu biyu da ashirin,da 'yan makaranta dubu 453 da dari hudu,kashi 91.8 cikin kashi dari na yaran da suka isa shiga makaranta sun shiga makaranta,yawan jahilai ya ragu bai kai kashi talatin cikin dari ba.An gina makarantu sama da 180 na fatan alheri,makarantu ne da aka kafa domin taimakawa yara daga matalautan iyalai tun daga shekara ta 1992,'yan makaranta da suka samu taimako sun kai dubu 36. Ga hoton 'yan makarantar firamare masu farin ciki.

>>[Addinai na Tibet]

Addinin Buddha iri na Tibet da hankalin Lama

Addinin Buddha irin na Tibet ya fi yaduwa a jihar Tibet da ta Mongoliya ta gida da sauran jihohi da larduna,ana kiran shi "addinin Lama",addinin Buddha ne mai halayen musamman na Tibet da ya zo jihar Tibet daga Indiya da cikin gidan kasar Sin a zamanin can da,ya kuma hadu da sauran addinan gargajiya na jihar nan.

Bisa tasirin da addinin Buddha na kabilar Han na kasar Sin da na Indiya suka kawo,haikalin addinin Buddha irin na Tibet ya kan bi salon fadar kabilar Han,yana da girma sosai da kyakkyawan gani da kuma zane zane masu ban sha'awa a jikinsa.Alal misali,fadar Budala da haikalin Zhebang da haikalin Taershi na lardin Qinghai dukkansu gine gine ne masu kyaun gani na gargajiya.

A haikalin Buddha na Zangdi,an fi ba da fiffikko kan wani abu na addinin Buddha da ya gagara fahimtar mutum.Yawancin haikali sun fi girma da zurfi,a cikinsu akwai kyallaye da darduma masu launi iri iri da aka rataya,babu haske sosai,da ka shiga haikalin sao ka kasa gane abin da ya ke nufi.A kan shafa wa jikin haikalin launin ja,da kuma zana zirin fari kan jikin bango mai ja.A kan shafe dakin karatu da hasumiya da fentin fari,tagogi masu launin baki ne ke jikin bango mai launin fari,lalle wannan launin ya kawo wani abu da ya gagara fahimta.

(Ga hoton mabiyan addinin Lama suna muhawara.)

Dabi'un addini na mutanen Tibet

Mutanen Tibet suna da cikakken 'yancin bin addinai.Yawancin mutanen kalibar Tibet da na Menba da Luoba da Naxi,mabiyan addinin Buddha iri na Tibet,a sa'I daya kuma mutane da yawa suna bin addinin musulunci da Kirista.A halin yanzu da akwai wurare sama da 1700 na tafiyar da harkokin addinin Buddha iri na Tibet a jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta,da masu zaman zuhudu maza da mata dubu 46 da masallatai guda hudu,da mabiyan addinin musulunci sama da dubu uku,da church na Kirista daya da mabiyansa sama da 700.Ana iya tafiyar da harkokin addinai yadda ya kamata,ana biyan bukatun mabiyan addinai,'yancinsu na bin addinai ya samu girmamawa sosai.

Dabi'u da al'ada na mutanetn Tibet sun sami girmamawa da kariya,kamar yadda mutane na sauran kananan kabilu suke samu a kasar Sin mutanen Tibet suna da iko da 'yanci na gudanar da harkokinsu na zaman yau da kullum bisa dabi'u da al'adarsu.Yayin da suke kiyaye hanyoyinsu da salonsu na tufaffi da cin abinci da kuma gidajen zama,su ma sun tsamo sabbin dabi'u da al'ada na samun tufafi da abinci da kuma gidajen kwana,ko ma wajen bikin aure da na yin ta'azziya..An kuma tanadi da ci gadon bukukuwan addinai a jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta kamar su bikin sabuwar shekara bisa kalandar Tibet,da bikin Sagadawa,da bikin fatan samun 'ya'yan itatuwa da bikin Xuedun da sauran bukukuwan addinai a cikin haikali,a sa'I daya kuma an tsamo sabbin bukukuwa iri iri daga kasar Sin da na sauran kasashen duniya.

(Hoto:kyallaye masu launi iri iri dake dauke da kyakkyawan fatan alhere na 'yanuwa na Tibet.)

>>[Al'adun Tibet]

Tangka

Cikin harshen Tibet,tangka wani iri surfani ne ko wani irin zane ne da aka zana a jikin kyalle ko silk ko takardu,yana da halayen musamman na al'adun Tibet sosai.

Kyalle da aka zana zane a jikinsa kyalle ne na silk ya fi daraja.An ce yayin da gimbiya Wencheng ta shiga Tibet,ta kawo fasahohin saka da na sauransu,daga kyalle da aka yi zane ana iya ganin fasahohin aikin kawo albarka da ake amfani da su a wancan zamani.

Abu mai launi da aka yi amfani da shi wajen zane,an samo su ne daga ma'adinai da shuke shuke,an hada su da dankon dabbobi da man shanu ta hanyar kimiyya.Cikin busashen yanayi na Tibet,irin zane zane da aka zana sun shafe shekara da shekaru,launinsu bai dakushe ba ya yi kama yadda aka zana shi na da launin walkiya.

Abubuwan da aka zana cikin zane zane sun shafi dabi'un jama'a na wancan zamani a fannoni dabam dabam,yawancinsu na da alaka da addini.

Zane zane da aka yi da man shanu

Abubuwan zane zanen man shanu sun shafi fannoni da dama,ciki har da tatsuniyoyin Buddha da labarin Sakyamuni da labaran tarihi da wasannin kwaikwayo.sifoffin da aka yi da man shanu suna da yawa.Akwai rana da wata da tauraro,da furani da ciyayi da itatuwa,da tsuntsaye da kuma dabbobi,da gine gine da mabiyan addinin Buddha da malamai masu zurfin ilmi da wazirai da manyan mayaka.Hanyoyin da aka bi wajen yin zane sun fi dauke hankulan mutane,kuma suna kan matsayin koli na fasaha.

Bisa girman zane zane da amfaninsu,an kasa zane zanen man shanu gidaje biyu, babba domin 'yan kallo da karami da aka ajiye a karamin dakin ibada.Zane zanen da aka yi da man shanu wadanda aka ajiye a cikin dakunan ibada suna da kyaun gani sosai,launinsu na da haske,da akwai irinsu na launi dabam dabam da simfurori iri iri,suna da alamun bukukuwa.A kan jejjera zane zanen man shanu gomai ko daruruwa a waje domin shere jama'a.

Wasan Opera na Tibet

A cikin harshen Tibet,wasan opera na Tibet ana kiran shi "Ajilamu",yana nufin "mala'iku 'yan mata",a saukake ana iya kiran shi "Lamu".Fasahar wasan Opera na Tibet tana da dadadden tarihi,tana da rukunoni da yawa,hanyoyin nuna wasanni suna da halayen musamman na mutanen Tibet.Wasanni guda takwas ciki har da wasan " gimbiyar Wencheng" da "yarimar Nosang" sun zama wasanni na misali,kida da aka buga da kuma waka da aka rera cikin wasan nada dadin ji sosai,maska da tufaffi masu launi iri iri sun fi dauka hankulan mutane.Duk wadannan sun shaida tarihin al'adu mai tsawo na wasan opera na Tibet.

Wasan opera na Tibet,wasa ne da ake yi da wake wake da raye raye,wanda a ciki ya kan gaya wa mutane tatsuniyoyi.Tun karni na goma sha biyar,dan addinin Gaju Tangdongjiebu ya shirya wasan opera dake dauke da tatsuniyoyi bisa addinin Buddha,ya nuna wasan a wurare dabam dabam.Wannan mafarin wasan opera na Tibet.Ga shi a yau fuskarsa ya canza saboda gyare da kyautatawa da azurta da masu fasaha suka yi cikin shekara da shekaru.har ya zama wasa na zamani da ke da littafin wasa,da raye raye da murya daban daban da tufaffi da abubuwan rufe fuska da ake kira "mask"a turance da kungiyoyin kida da na mawaka.

Kungiyoyin wasan opera na Tibet suna da yawa.ko ina ka sa kafa a cikin Tibet kana iya tarar da wasan opera na Tibet da ake yi ko ma a filayen kauyuka,da aka kafa wani babban tanti ko tayar da babban bangon kyalle,sai an fara nuna wasan opera.mutanen da ke zaune a kewaye sun zo su yi kallon wasa,'yan kallo su kan cika filin nuna wasanni.