logo

HAUSA

Babi07: Gine-ginen kasar Sin

0001-01-01 08:00:00 CRI

>>[Takeitaccen Bayani]

Galiban tsare-tsaren gine-ginen kasar Sin

Gine-ginen kasar Sin da ke da sigar musamman sun sama wani babban kashi da ke cikin wayewar kai na al'ummar kasar Sin, gine-ginen kasar Sin da gine-ginen yammacin kasashen Turai da gine-gine na Musulmi, su ne suka zama babban tsare-tsare guda uku na duniya.

Gine-ginen kasar Sin sun zama daya dayan tsarin gine-gine wanda ginin tumba ya zama muhimman sigarsa, gine-ginen kasar Sin sun bayyana ra'ayoyin al'ummar Sin sosai, wato ka'idar da'a da ma'aunin masu faranta rai da manufar darajanta abubuwa da ra'ayin kiyaye halittu masu rai. Saboda al'adun gargajiya na kasar Sin, wasu halayen musamman na gine-ginen kasar Sin suna hade da: an bayyana ikon sarki da ke da girma fiye da kome da banbamcin mataki daban dabam, an mai da hankali kan kyaun gani na gine-gine, gine-gine na rukuni-rukuni suna girmamawa halittu masu rai.

Tun cikin lokacin tarihi, kasar Sin ta ke kula da yin musanye-musanye tare da gammayar kasashe kan sigar musanman ta fasaha da gwanintar gine-gine, wadannan sun taba kai babban tasiri ga gine-ginen kasashe da dama, kamar na kasar Japan da kasar Korea ta Arewa da kasar Vietnam da kasar Mongoliya. A yau kuma, yayin da gine-ginen kasar Sin ke kare samun sigogin gargajiya, kuma yana nan yana tsamo halayen fasaha na yammacin kasashe don hada abubuwan nagari daga wajensu, wajen sami ci gaba na ba fashi.

>>[Gine-ginen Kasar Sin]

Gine-ginen fadar sarakuna

Giner-ginen fadar sarakuna su ne kasaitattun gine-gine da sarakuna na zamanin da suka gina domin karfafa mulkinsu da bayyana kwajini na sarakuna, kuma ke biyan bukatunsu na zaman rayuwa da na tunaninsu. A kan yi ado sosai kan wadannan gine-gine masu girma kuma masu ban mamaki ne.

Tun daga zamanin daular Qing na tsohon zamanin da na kasar Sin, fadar sarakuna ta kasu kashi biyu, daya shi ne inda sarakuna da 'yan iyalansa ke zama, dayan kuwa shi ne ofishin da sarakuna ke yin aikinsu. a kyamaren fada an sa daben rufen daki mai suna LuiLi masu ruwan zinariya, an zana hotuna masu kyaun gani, Fada mai suna Tai He na cikin fadar sarakunan gargajiya na kasar Sin ita ce fadar da ke alamanta gine-ginen fadan kasar Sin.

Domin bayyana ikon sarakuna masu girma cikin duniya, da ikon sarakuna ya zama cibiyar duniya wato nuna banbamcin mataki, yayin da aka soma gina wadannan gine-gine, da farko an sheta wani layi, fadar da aka gina kan layi nan nada da girma da 'kayatarwa, amma a bangare biyu na layin nan, wato a gefuna biyu, gine-ginen ba masu girma sosai ba idan an kwatanta su da na fadar gine-ginen da ke layin. Ban da haka , fadar gine-gine ta kasu kashi biyu, wato gabanta ofishin kula da harkokin kasa, bayanta masauki ne inda sarakuna da matarsu da kwarakwarai ke zaune.

Fadar sarakuna mai suna Gu Gong da ke nan birnin Beijing

Fadar sarakuna mai suna Gu Gong nada wani suna dabam wato Zijencheng wadda ke wakiltar fadar gine-ginen kasar Sin, nan ne fadar sarakunan daular Ming da daular Qing , an kasance da sarakuna 24 sun taba zauna a ciki. Fadar ke da fadin muraba'in mita dubu 720 nan daular Ming da daular Qing , an kasance da sarakuna 24 da suka taba zama a ciki. Fadar na da fadin muraba'in mita dubu 720 tare da dakuna sama da dubu 9, Bango mai ruwan ja mai tsawo ne ke kewaye da fadar, tsawon bangon ya kai mita dubu 3 da dari 4 ko fiye, a wajajen bangon, karamin kogi ne ke kewayen bango.

Fadar ta kasu kashi biyu, kashi na gaba, wurin da sarakuna ke yin kasaitattun bukukuwa da bayar da umurni, manyan gine-gine suna hada da fadar Taihe da fadar Zhonghe da fadar Baohe. An gina wadannan fada kan wani wuri mai tsawon mita 8 wanda aka yi da wani irin farin tutse kuma mai daraja , daga ndesa in an hange su sai ka ce kamar fada mai benaye da aka kafa cikin samaniya, kashi na baya na fadar ya zama wurin da sarakuna ke daidaita harkokin kasa da kwarakwarai ke zaune, muhimman gine-gine sun hada da fadar Qianqing da fadar Kunning da lanbun shan iska na sarakuna, wadanda ke bayyana halayen zaman rayuwa, har gine-ginen na hade da lanbun shan iska da dakunan karatu da sauransu.

Saboda sauye-sauyen daulolin tarihi na tsohon zamanin da na kasar Sin, fadar gine-gine na zamanin da na kasar Sin da suka kasance a yanzu ba su da yawa, yanzu ban da fadar sarakuna mai suna Gugong da ke nan birnin Beijing. An kasance da fada mai suna Gugong da ke birnin Shengyang , kuma cikin birnin Sian, an kasance da fada guda biyu na daular Han da na daular Tang kawai.

Gine-ginen wuraren ibada

Wuraren ibada sun zama daya daga cikin gine-ginen addinin Buddah na kasar wadanda sanadiyarsu ita ce gine-ginen wuraren ibada na kasar India, tun daga daular Wei ta arewa aka fara samun yalwa sosai cikin kasar Sin. Wadannan gine-ginen sun dauki bunkasuwar al'adu na tsarin zamantakewar gargajiya da samun bunkasuwar addinai da dushewarsu, saboda haka wadannan gine-ginen suna da matukar daraja a tarihi da fasaha.

Sinawa na can da sun bayyana ra'ayoyinsu kan yadda abubuwa kishiyoyin juna ke zama tare kan tsarin gine-gine, kuma suna girmama wani halin 'da'a wanda ke hade da fasalin abubuwa masu tashi daya. Saboda haka wuraren ibada na kasar Sin suna kan filaye, an shata wani layi daga kudu zuwa arewa, fasalin gine-ginen da aka gina a bangarori biyu na layin nan iri daya ne. Daga wannan waje, cikin kasar Sin an kasance da wuraren ibada masu tsarin gine-gine na lambun shan iska wadanda su ma suna da yawan gaske. Wadannan fasalin fasaha sun kawo wa wuraren ibada na kasar Sin wani hali na ladabi kuma mai halin hallitu masu rai.

Tsari na galiban wuraren ibada na tsohon zamanin da ya zama haka, a tsakiyar wurin wato hanyar tsakiya da ke dab da wata kofar wurin ibada, cikin kofar hannun hagu hasumiyar kararrawa ce, hasumiyar ganguna ta tsaya a hannun dama, in an shiga kofar, wani babban haure ke dab da kofar, nan ne fada mai suna Tienwang wato sarkin da ke sama, cikin fadar sarkin sama, an kasance da mutum-mutumi na sarkunan daimun guda hudu, bayan fadar sarkin sama, an kafa babban dakin tunawa da mazajen jiya, da gini mai benaye na ajiye litattafan addini, gidan Buddah da dakunan cin abincin Buddah suna hagu da dama na hanyar tsakiya. Babban dakin tunawa da mazajen jiya ya zama wani muhimman gini cikin wuraren ibada kuma gini mafi girma, mazajen jiya yana nufin Sakyamuni wanda ya kirkiro addinin Buddah.

Ibada mai suna Baima da ke Luoyang

Tun daular Han aka soma aikin gina wurin ibada a birnin Luoyang na lardin Henan wanda ya zama wurin ibada da hukumar tsohunwar kasar Sin ta kafa mafi dadewa. Wurin ibada mai kusurwa hudu ne, muraba'in fadin ya kai wajen mita dubu 40. Kafuwar wurin ibada mai suna Baima ta sa kaimi ga kara bunaksuwar addinin Buddah cikin kasar Sin da Asia ta gabas da shiyyar Kudu maso gabas ta Asia. Sabili da haka, ya zuwa yau dai wurin ibada mai suna Baima ya zama wani tsarkakken wuri ne da masu bin addinin Buddah na kasa da kasa ke yin ibada.

Ibada mai suna Xuankong da ke tsaunukan Heng

Wani wurin ibada da ya kamata a gabatar da shi shi ne wurin ibada mai suna Xuankong da ke tsaunukan Heng na cikin lardin Shanxi, wanda aka kafa shi domin yana sama, saman wurin ibadan hayin duwatsau ne, wurin yana kwarin tsuni ne mai zurfi kwarai, saboda haka sigar wurin ibadan na da tsarin musamman, wanda ya zama wani ginin da ba safai akan ga irinsa ba.

Fada mai suna Budala

Addinin Lama wani reshen addinin Buddah ne na kasar Sin, wani tsarin musanman na gine-ginen wurin ibada shi ne, dakin ibada na da fadi, dakunan ajiye litattafan addini na da tsawo, wurinm ibada da aka gina galibi dai suna dogara ne bisa tsaunuka. Fadar Budala da ke birnin Lhasa na jihar Tibet ta zama misali cikin gine-ginen wuraren ibada na addinin Lama. Cikin dauloli da yawa an yi ta kara gine-gimnen fadar Budala wanda aka soma gina shi tun lokacin daular Tang, daga baya fadar ta zama wani rukunin gine-gine mai girma. Duk fadar Budala tana dogara ne bisa tsaunuka, duk fadinta tana da muraba'in mita dubu 20 ko fiye, ciki an kasance da haure sama da 20, a fadar da ke tsakiya, wato mihimmiyar fada , an girmama da ajiye mutum-mutumin tagulla da tsayinsa ya yi daidai da jikin Sakyamuni lokacin da ke da shekaru 12 da haihuwa wanda kuma an sa ruwan zinariya kan jikin. Gine-ginen fadar Budala na da sigar musamman na gine-ginen daular Tang sosai, wanda kuma ya tsamo sigar musamman na fasahar gine-gine na kasar Nepal da na India.

(Hoton fada mai suna Budala)

Daga wannan waje kuma, wuraren ibada guda 8 da ke birnin Chengde da fada mai suna Yonghe da ke nan birnin Beijing , su ma sun zama shahararrun gine-ginen addini Lama.

Gine-ginen lambuna

Gine-ginen lambuna na kasar Sin suna da dadadden tarihi, wadanda kuma sun shahara cikin trarihin lambunan gamayyar kasa da kasa. A daular Zhou na tsohon zamanin da wato kafin shekaru 3000 ko fiye, cikin kasar Sin an gina lambunan fadar sarakuna wadanda su ne lambuna mafi dadewa cikin kasar Sin. Lambunan birane na kasar Sin suna nan iri-iri, wadanda kuma suka dauki wani muhimman matsayi cikin tsarin lambuna uku na gamayyar kasa da kasa.

Gine-ginen lambuna na kasar Sin sun hada da manyan lambunan sarakuna da kananan lambuna masu zaman kansu, wadannan gine-ginen sun hada da abubuwa masu kyaun gani da mutane suka yi da hannunsu da na hallitu gu daya, daga cikin tsaunuka da ruwaye da furanni da ciyayi da bishiyoyi da farfajiyar gidaje da gadoji wadanda aka tsara sun dace kuma sun kara kayatar da lambunan.

Sigogin gine-ginen kasar Sin sun bayyana halin sarrafa duniya na tunanin Confucius, daga ciki an mai da muhimmanci kan abubuwan hakika da nuna alhaki sosai na tsarin zamantakewa da mai da hankali kan darajar ka'idar da'a da ma'anar siyasa, da tunanin darikar Taoist na kasar Sin wanda ke bayyana ra'ayin kankan da kai wato rashin son moriya da yin suna da tallafar kansa, har da mai da hankali kan tunani da halaye na masu mallakar lambuna. Lambu mai suna summer palace, wani shahararen lambun sarakuna ne, haikali mai suna Guchangdao na tsaunin Qingchen da ke lardin Sicuan da lambuna na wasu masana suna alamanta sifofi uku da muka ambata a baya.

Bambancin da ke tsakanin lambuna na Sin da na kasashen yamma shi ne: cikin lambuna na kasashen yamma akan bayyana ka'idar ilmin lissafi da mai da muhimmanci kan gine-gine; lambuna na kasar Sin sun mai da muhimmanci kan halin halittu na wurin da jin dadin kallo na maziyarta.

Lambun na Suchou

Lambuna na tsohon zamanin da da ke birnin Suzhou wadanda tun shekarar 1997 aka shigar da su cikin "sunayen wuraren tarihi na duniya", sun bayyana sigar musamman ta fasahar gine-ginen lambunan kasar Sin. Tarihin lambunan Suzhou ya kai shekaru sama da dubu biyu, yanzu an kasance da sama da goma. Yawancin lambunan Suzhou ba su da fadi sosai, cikin wurare marasa fadi, ana kayatar da tsaunuka da aka daddasa bishiyoyi da gine-gine masu benaye da randuna da kananan gadoji inda ke bayyana halin sha'awa irin na son ganin tsauni da ruwa da furanni da tsuntsaye kuma ke da tunanin wakoki na daular Tang da na daular Song, haka ya sa an bayyana sakamakon fasaha daga karamar fada. Cikin gine-ginen lambuna da suka yi suna kwarai cikin gamayyar kasa da kasa akwai Canglang Ting da Shizi ling da lambun Zhuozheng da lambun Liu.

(Hoton lambun na Suchou )

Lambu mai suna Yuanmingyuan

Lambu mai suna Yuanmingyuan, wani shahararren lambun sarakuna ne na kasar Sin wanda ke da lakabi lambun da ke cikin lambuna dubbai da ke nan birnin Beijing, ya takaita sigar fasahar lambuna da suka sha bamban sosai, kuma ya tsamo sigar gine-gine na wasu kasashen yamma, gine-ginen da ke cikin lambun kamar Allah ne ya yi don nuna sha'awa kwarai. Lambu mai suna Yuanmingyuan, ba ma kawai ya zama wani fittacen fadar sarakuna na kasar Sin a cikin lokacin can da ba, har ma lambun ya yi shahara cikin kasashen Turai, wanda kuma, ya yi tasirinsa ga lambunan halittu na kasashen Turai a karni na 18. Amma a shekarar 1860 sojoji mahara na Britania da na Faransa sun kone lambu mai suna Yuanmingyuan wanda ya zama mafi kasaita da kayatarwa.

Gine-ginen kaburbura

Gine-ginen kaburbura su ne wani muhimmin kashin da ke cikin tsarin gine-ginen tsohon zamanin da na kasar Sin, saboda Sinawa na zamanin da suna da wani tunani wato bayan mutum ya mutu, amma ruhunsa bai mutu ba. Saboda haka galibi dai ana mai da muhimmanci kan bikin jana'iza , sai ta kowane fanni , ana nuna komai tsanake a wajen gina kabari. Cikin tsarin ci gaban tarihi, tsarin gine-ginen kaburbura na kasar Sin ya sami bunkasuwa kwarai, daga nan dai cikin tsohon zamanin da an gano kasaitattun kaburbura na sarakuna da na kwarakwarai wadanda ba safai akan ga irinsu cikin duniya duka ba: Har cikin sauyue-sauyen tarihi, gine-ginen kabari sannu a hankali sun gauraya fasahohi gu daya kamar zane-zane da rubuce-rubuce da sassake-sassake, daga baya sun bayyana sakamakon fasahohi dabam daban.

Gine-ginen kaburbura sun zama daya daga cikin rukunonin gine-gine mafi kasaita da ke cikin tsohon gine-ginen kasar Sin. An yi wadannan gine-ginen kabarbura galibi dai bisa halin halittu na wuri-wuri, wato wasu suna dogara bisa tsaunuka, wasu an gina su kan filin karkara. Yawancin tsarin kaburbura na kasar Sin nada bango a bangarori hudu, kuma an yi kofa a duk bangarorin hudu, kuma an yi kusurwoyi guda hudu. A gaban kaburbura an shimfida hanyoyi, cikin farfajiyar kaburbura an dasa itacen cypress pine, kuma nuhallin karburburan sun kasance tsit.

Kabarin sarki Qingshihuang 

Wani kabari na sarki Qinshhuang ya zama wani kabari mafi shahara cikin kasar Sin wanda aka gina kafin shekaru dubu biyu da suka shige a arewancin gindin tsauni Lishang na birnin Sian da ke lardin Shaanxi . Mutum-mutumin mayaka da dawakai na Qinshhuang wadanda aka yaba su da cewar abubuwa ne masu ban mamaki na 8 cikin duniya , sun zama rundunar sojoji masu gadi ga kabarin nan. Wadannan mutum-mutumin mayaka da dawakai na Qingshhuang na da fasahar kira mai inganci kuma sun kasance cike da karfin zuciya, wanda aka shigad da su cikin " sunayen wuraren tarihi na duniya " tun shekarar 1987. Kwamiti kula da kayayyakin tarihi na duniya ya taba cewa, shahararun mutum-mutumin mayaka da ke kewayen kabarin Qingshhuang, har da dawakan yaki da kekunan yaki da makamai suna da sifofi dabam daban, wadanda suka zama fitattun abubuwa na hakika kuma ke kiyaye darajarsu ta tarihi.

(Hoton mayaka da dawakai na kabarin sarki Qingshihuang)

A wuraren da ke kusad da birnin Xian na lardin Shaanxi an gano kaburburan sarakunan kasar Sin da yawan gaske, banda kabari na Qingshhung kuma, akwai kaburburan sarakuna 11 na daular Han ta yamma, da kaburburan sarakuna 18 na daular Tang. Cikin kabari mai suna Mao na sarkin Liu Che na daular Han ta tsakiya ya zama tsarin kabari mafi girma cikin kaburburan sarakunan daular Han ta yamma, kuma an binne abubuwa masu daraja masu dinbim yawa: kabari mai suna Zhao shi ne kabarin sarkin Taizong na daular Tang, sunansa Li Shming , kabarin nan na da fadi kwarai, cikin kabarin nan akwai kaburbura guda 17 domin su kasance tamkar masu rakiya, inda aka binne jarumai da dangin sarki , ko a kasa ko a cikin kabarin, an kasance da kayayyakan tarihi masu daraja, ciki mafi shahara shi ne sukuwar dawakai 6 da aka saka a daular Tang.

Kaburbura na sarakunan daular Ming da Qing

Galiban kaburbura na sarakunan daular Ming suna gundumar Changping na birnin Beijing wato kaburbura 13, inda akwai kaburbura na sarakuna 13 na bayan daular Ming da ta mai da Beijing da ya zama fadarta, wadanda ke da fadin muraba'in kilomita 40. Kaburbura 13 na daular Ming ya zama gine-ginen kaburbura cikin kasa da ake da su yanzu kuma sun kasance cikakku , ciki mafi girma shi ne kabari mai suna Chang na sarkin Chengzhu na daular Ming, sunansa Zhudi da kabari mai suna Ding na sarkin Shengzong na daular Ming sunansa Zhu Yijun. Bayan da aka hako, an gane cewa, cikin kabari mai suna Ding, tsarin duwatsu masu sifar baka da aka tokare su cikin fadar duwatsu nada karfi sosai, kuma an gina wuraren ban ruwa kewaye da fadar duwatsu, haka ya sa babu ruwan da zai iya kkwanciya cikin fadar duwatsun, duwatsu masu sifar baka ba su rushe ba, wadannan abubuwa sun bayyana fasaha mai inganci ta gina gine-ginen kabubura a karkashin kasa na Sinawa na tsohon zamanin da.

Kabari mai suna Dong na daular Qing wanda ya zama gine-ginen fadar kaburbura mafi girma da ke kasancewa har zuwa yanzu kuma wanda ke da cikakkun tsarin gine-ginen fadar sakurana, yana da fadin muraba'in kilomita 78, a ciki ne aka binne sarakuna 5 na daular Qing da sarauniyoyi 15 da kwarakwarai sama da dari. Muhimman gine-ginen kabarbura da ke cikin kabari mai suna Dong na daular Qing suna da kayatarwa sosai suna da kira mai kyau.

Gine-ginen gidajen jama'a

Gine-ginen kwana da ke wurare daban dabam na kasar Sin wadanda kuma ake kiransu gine-ginen gidajen jama'a. Gine-ginen kwana su ne wasu ire-iren gine-gine da suka bullo tun da wuri kuma masu yawa da ke cikin wuraren. Amma saboda an kasance da banbamci na muhallin halittu masu rai da na sauran abubuwa, sai gine-ginen jama'a na wurare daban dabam sun sha banbam ainun.

A shiyyar da kabilar Han ke zaune na cikin kasar Sin, gine-ginen jama'a na gargajiya su ne gine-ginen da ke cikin kusurwa 4 wanda bangarori biyu na tsakar gida daidai wa daida ne. Irin wadannan gine-ginen jama'a na da farfajiya guda biyu wato na gaba da na baya, dakunan da ke kallon kudu muhimman dakuna ne ake nuna musu girmamawa , inda duk iyalai sun yi biki ko karbar gaggan baki, baranda ke hada da dakuna na kusurwa hudu. Gine-ginen da ke cikin kusurwa hudu na birnin Beijing sun bayyana tunanin addinai da tsarin iyalai na zamanin da na tsohuwar kasar Sin, amma farfajiya nada girma, an dasa bishiyoyi da ciyayi, wadda kuma ta zama wuri na waje da dakuna. A arewanci da kudu maso gabas na kasar Sin an kasance da irin gine-gine da ke cikin kusurwa hudu masu fadi.

(Hoton gine-ginen masu kusurwa hudu na birnin Beijing)

Daki na tsakiya da ke cikin manyan dakuna da dakuna masu benaye na Hakkas mai suna Tu na Sinanci

.

Gine-ginen gidajen jama'a na kudancin kasar Sin ana yinsu ne kusa-kusa kuma gidaje masu benaye sun fi yawa, gine-ginen dakunan jama'a da ke da tsarin musamman wata karamar farfajiya ce mai kusurwa hudu da ke tsakiyar gidajen wanda ake iya ganin daga wajensa, mai kusurwa hudu, sun kasance da yawa sosai cikin lardunan kudancin kasar Sin.

A kudancin lardin Fujian da arewacin lardin Guangtong da na lardin Guangxi, wasu mutane da ake kira Hakkas sukan zaunacikin manyan gine-ginen gidaje, kewayayyu ko masu kusurwa hudu, tsakiyarsu wani babban daki ne wanda gidaje masu benaye 4 ko 5 ke kewaye da shi, irin gine-ginen na da wani tsarin musamman wato na yin tsaro, wanda dakuna masu benaye na mutanen Hakkas da ke gundumar Yongding ta lardin Fujian sun hada da sifofi da yawa kamar na kusurwa hudu da kewayayyu da kusurwa guda 8 da masu sifar kwai, masu yawan sama da dubu 8, wadannan gine-gine masu girma ne kuma masu kyaun gani, suna bayyana halin kimiyya da saukin zama , kana da halin musamman , har sun zama wata duniyar gine-ginen jama'a mai ban mamaki.

Gine-ginen gidajen kwana na kananan kabilu

Gine-ginen da ke cikin shiyyar da kananan kabilun kasar Sin ke zaune suna da sanfurori da yawa, alal misali, dakuknan kwana na kabilar Uygur da ke jihar Xingjiang na arewa maso yamma na kasar Sin, marufin daki mai shafe da tanti, banguna na kasa ne, masu benaye 1 zuwa 3, farfajiya na kewaye da gine-ginen; gine-ginen gidajen jama'ar Tibet da aka gina a kasa, an yi amfani da guntun dutse don gina bangayen dakan, a ciki na tsarin tumba ne; Gidajen kwana na kabilar Mongoliya su ne wani irin tanti mai kubba kuma ke da saukin kaura; kananan kabilun da ke zaune a kudu maso yamma na kasar Sin sukan gina wasu irin gidaje masu benaye da ke dogara bisa gindin duwatsu kuma ke fuskantar ruwa, a bene na kasa babu daki, mutane ke zaune a bene na sama, ciki kabilar Dai da ke lardin Yunan sun zauna cikin gidajen gora masu benaye da ke da tsarin musamman. A shiyyar kudu maso yamma na kasar Sin, mutane na kabilar Miao da na Tujia ke zaune cikin gine-ginen katako wadanda ginshikai ke tokare da su , gine-ginen gidaje da ke da benaye 2 ko 3, a bene na sama ba tsawo inda akan ajiye amfanin gona kawai, a bene na kasa kuwa akan ajiye abubuwa ko gidan renon dabbobin gida.

Kogon mazauni na arewacin kasar Sin da gine-ginen gidajen jama'a da ke tsohon birni

A shiyyar tsakiyar wurin da Rawayen kogi ke malala na arewancin kasar Sin an kasance da kogunan mazauna da yawa sosai, a shiyyar da ke rawayen kasa na lardin Shaanxi da lardin Gansu da lardin Henan da lardin Shanxi, mazauna sun haka kogun cikin bangayen kananan tudai , kuma akan hada kogo da yawa, a ciki kuwa an mammanna tubalai don kara karfin kogo. Irin kogon mazaunan na iya hana gobara da hana jin motsi, cikin yanayin sanyi na da dumi , a yanayin zafi kuwa ana jin sanyi, kana an yi tsimin filaye da kawo tsimin tattalin arziki da gini filaye, wadanda ke hade da halittu da zaman rayuwa tare kuma ke dacewa da halayen wurin.

Daga wadannan waje kuma, cikin kasar Sin akwai wasu tsoffin birane da har yanzu suke kasancewa , cikin wadannan tsoffin birane an kasance da gine-ginen gidajen jama'a na zamanin da. Ciki tun shekarar 1998 aka shigad da sunayen tsohon birnin Pingyao na lardin Shaxi da tsohon birnin Lijiang na lardin Yunan cikin sunayen muhimman wuraren al'adun gargajiya na duniya.

Tsohon birni mai suna Pingyao shi ne wani garin gunduma na daular Ming da Qing da ke kasancewa yanzu, wanda ya zama wani misali na garin gunduma na zamanin da na kabilar Han da ke shiyyar tsakiyar kasar Sin. Ya zuwa yanzu, bangayen birnin da tituna da gine-ginen gidajen jama'a da kantuna da gine-ginen haikali da dakunan ibada suna kasancewa. kana tsarin gien-gine da sigarsa ba su canza ba. Saboda haka birnin Pingyao ya zama wani abu na musamman don binciken bunkasuwar tarihi kan siyasa da tattalin arziki da al'adu da gine-gine da fasaha.

Tsohon birnin Lijiang wanda aka soma ginawa tun lokacin daular Song ta kudu na zamanin da na kasar Sin, birnin ya zama birni daya tak da ya hada gine-ginen gargajiya na kabilar Naxi da halin musamman na gine-gine na sauran kabilu. Tsarin ladabi na gine-ginen biranen shiyyar tsakiyar Sin bai yi tasiri ga gine-ginen tsohon birnin Lijiang, tituna da ke cikin birnin Lijiang masu yawa, kuma birnin ba shi da bango. Wani randar ruwa mai suna Helongtan ta zama sanadiyar ruwan tsohon birnin, ruwan randar ya kasu gulabe da ke kewayen da gidajen jama'a, saboda haka cikin birnin ko-ina ana iya ganin ruwa ke malala cikin gulabe, bishiyoyi ke kama a bakin gulabe.

(Hoto na tsohon birnin Lijiang )

>>[Gine-ginen tsohon zamanin da]

Halayen gine-gine na tsohon zamanin da

Gine-ginen tumba na kabilar Han sun zama muhimman gine-ginen tsohon zamanin da na kasar Sin , ciki har da gine-gine masu kyau na kananan kabilu. Wadannan gine-ginen tsohon zamanin da suka sami bunkasuwa cikin halin al'adun gargajiya na kasar Sin, a karni na 2 ,kafin haihuwar Annabi Isa Alaihissalam zuwa tsakiyar karni na 19, bayan bayyanuwar Annabi Isa, alaihissalam sun zama wani tsari wanda kofa a rufe suke kuma ke da ma'auni masu faranta rai da darajanta abubuwa da matsayin fasaha, wadanda ke da ma'ana mai zurfi na Bil Adam. Fasahar gine-ginen tsohon zamanin da na kasar Sin ya zama wani tsarin fasaha na musamman wanda aka jinkirta cikin dogon lokaci na tarihi a duniya, kuma ke kasancewa a wurare masu fadi sosai, har tsarin na da sigarsa ta zahiri, kana tsarin ya yi tasiri na kai tsaye ga gine-ginen tsohon zamanin da na kasar Japan da na kasar Korea ta Arewa da na kasar Vietnam, bayan karni na 17 na bayan bayyanuwar Annabi Isa Alaihissalam, tsarin gine-gine na tsohon zamanin da na kasar Sin ya yi tasiri ga gine-gine na kasashen Turai.

Kasar Sin wata makekiyar kasa ce da ke da kabilu da yawa, mutane na tsohon zamanin da na kasar Sin sun kago gine-gine na tsohon zamani da ke da tsarin gine-gine iri daban dabam da sigogin fasaha da suka sha banbam , duk bisa sharudan halittu masu rai da na labarin kasa. A wurin da Rawayan kogi ke malala a arewancin kasar Sin, mutane na tsohon zamani sun yi dakin tumba da kasa mai launin rawaya don gina gidaje wadanda ke iya jure sanyi mai tsanani da babbar iska da kankara mai taushi wato snow, amma cikin kudancin kasar Sin, kayayyakin gine-gine har sun hada da gora da wani irn tsire-tsire da ke a bakin ruwa, sifarsa kamar ciyayi, a cikin wasu yanki saboda maganin danshi da a sa iska ta rinka kadawa, sai aka yi gine-ginen katako wadanda ginshikai ke tokere da su.

Cikin tarihin bunkasa gine-ginen tsohon zamanin da na kasar Sin an yi yunkuri sau 3, su ne a lokacin daular Qin da ta Han da lokacin daular Sui da ta Tang, da lokaci na daular Ming da ta Qing. Cikin lokuta 3, aka gina tarin gine-gine masu wakiltar lokutan can kamar su fadar sarakuna da gine-ginen kaburbura da fadar birane da gine-ginen tsaro da ayyukan madatsar ruwa, duk wadannan gine-gine ko wajen sigarsu ko kayayyakinsu duk sun ba da tasiri sosai ga gine-gine na zamani masu zuwa.

Amma saboda dadewar lokaci da wutar yaki, wasu tsoffin gine-ginen masu daddaden tarihi sun bace a babban yankin kasar Sin, yanzu galiban tsohon gine-gine na kasar Sin da ke kasancewa na daular Tang ne wato na bayan karni na 7 bayan bayyanuwar Annabi Isa.

Gine-gine na daular Tang

Daular Tang wato daga shekara ta 618 zuwa 907 na bayan bayyanuwar Annabi Isa Alaihissalam, ta zama wani lokacin da tattalin arziki da la'adu na zamantakewar mulkin gargajiya ta kasar Sin suka sami bunkasuwa sosai, sigar gine-ginen daular Tang ita ce ke bayyana halin kasaita.

Cikakken tsarin gine-ginen kasar Sin ya dada samun kyautatuwa. A fadar daular Tang Changan wato birnin Xian na yanzu da gabashin fadar Luoyang, an gina fadar sarakuna da gandunan dabbobi da hukumomin gwamnati masu kasaitattu, kuma tsarin wadannan gine-gine masu dacewa ne. Fadar daular Tang Changan ya zama wani birni mai kasaita na duniyar lokacin, fadar Daming da ke cikin fadar sarki na birnin Changan tana da kasaita sosai, har fadin fadar ya kai ninki 3 na duk fadin muraba'in birnin Zijing Cheng, fadar sarkuna na daular Ming da ta Qing.

Gine-ginen tumba na daular Tang sun bayyana yin kayayyakin gine-gine da wasu abubuwa don yi wa gine-gine ado ta hanyar fasaha da tsarin gine-gine sun hadu gu daya, ciki kamar ginshikai da bim na daki sun hada karfi da kyaun gani gu daya. Babban daki mai suna Foguang da ke tsaunin Wutai na lardin Shanxi tana wakiltar gine-ginen daular Tang , kuma gine-ginen sun bayyana halayen musamman na baya.

Daga wadannan waje kuma, gine-gine na bulo na cikin daular Tang sun kara samun bunkasuwa, an gina galiban hasumiya ta addinin Buddah da bulo ne. wata hasumiya mai suna Dayan da hasumiya mai suna Xiaoyan da ke birnin Xian da hasumiya mai suna Qianxun da ke yankin Dali na lardin Yunnan, dukansu su ne hasumiya da aka gina da bulo na daular Tang da ke kasancewa yanzu cikin kasar Sin.

(Hoton hasumiya mai suna Dayan da ke birnin Xi'an)

Gine-ginen daular Song

Daular Song ( daga shekara 960-1279 na bayan bayyanuwar Anabi Isa ) Alaihissalam ta zama daular tsohon zamanin da da ta lalace a fannin siyasa da sha'anin soja, amma daular ta sami bunkasuwa kan tattalin arziki da sana'ar hannu da kasuwanci, a wajen kimiyya da fasaha, ta fi samun babban ci gaba. Wani sigar musamman kan gine-gine ita ce, gine-gine masu kayatarwa wadanda aka yi musu ado sosai.

A biranen daular Song, kantuna suna gefe biyu na titi wadanda suka zama tsarin tituna, kuma an sami sabon bunkasuwa wajen bangaran tsaro don hana tashin gobara, da tafiye-tafiye da jigila, da kantuna da gadoci. Afadar daular Song ta arewa mai suna "Bianliang" wato birnin Kaifong na lardin Henan na yanzu, an kasance da sura birnin kasuwanci. A lokacin can, gine-ginen kasar Sin sun kara fadi, don sa muhimman gine-gine su bayyana sosai, bayan haka, an yi kokari sosai kan adon gine-gine da launukansu, alal misali, a dakin Ibada na Jen da ke birnin Taiyuan na lardin Shanxi, a gaban babban fadar dakin akwai wata randar ruwa mai kusurwa hudu, an kafa gadar da aka yi da tumba a kan randar, a karkashin gada an kafa ginshikai na dutse, cikin Sinanci ana kiranta Yuzhao Feiliang, babban fadar daki da randar sun zama abun misali da ke cikin gine-ginen daular Song.

(Hoton randar ruwa mai suna Yuzhao Feiliang)

A cikin daular Song, matsayin gine-gine na bulo da dutse ya yi ta daguwa, a lokacin, muhimman gine-ginen bulo da dutse su ne hasumiyar Buddah da na gadoji. Hasumiya mai suna Lingyin na birnin Hangzhou na lardin Zhejiang, hasumiya mai suna Fan na birnin Kaifeng da ke lardin Henan da gada mai suna Yongtong na gudumar Zhao da ke lardin Hepei, dukansu sun zama abin misali da ke cikin gine-ginen bulo da dutse na daular Song.

A daular Song, zamantakewar tattalin arziki ta kasar Sin ta sami bunkasuwa kan wani fanni, an soma kafa ganduna masu bayyana halin zuciya. Ganduna na tsohon zamann kasar Sin sun mai da kyawawan halittu da na Dan Adam gu daya, ana bayyana halin fasaha bisa gine-gine da tsauni da kogona, tsauni da kwari da furanni da bishiyoyi wadanda duk na Dam Adamne. Gine-ginen daular Song da ke da halin wakilci sun hada da rumfa mai suna Cang Lang na Malam Su Shunqin da lambu mai suna Dule na Malam Simaguang.

A daular Song an buga wani littafi mai suna hanyoyin sayarwa, ciki musamman an yi su don kyautata littafi na fasahar " giggina dakuna " da ke amfanawa litattafin musamman kan gine-gine" wanda ke bayyana kasar Sin tana kan wani sabon matsayi kan fasahar ayyuka da aikin kula da masu gina dakuna.

Gine-ginen daular Yuan

Kasar Sin ta shekarar 1206 –1368 na bayan bayyanuwar Annabi Isa, Alaihissalam, wato cikin daular Yuan, wata kasar mulkin soja ce wadda masu mulki na Mongoliya suka kafa kuma makekiyar kasa, amma a lokacin, kasar Sin ba ta sami saurin ci gaba kan tattalin arziki da al'adu ba, wajen gine-gine kuwa, ba ta sami bunkasuwa ba, akashin haka tana cikin halin rashin ci gaba, yawancin gine-gine masu sauki ne kuma ba kyau ko kadan.

Babban birni Dadu na daular Yuan wanda ke nahiyar arewa ta birnin Beijing, birni mai girma ne kuma an waiwayi tsarinas, birnin sarakuna na daular Ming da na Qing wato birnin Beijing, an kafa tsarinsa a lokacin can. Wani dutse mai suna Wuansui da randar Taiye na daular Yuan wanda ke kasancewa yanzu, wato tsibirin Qiong na lambun shan iska na Beihai dake birnin Beijing, wanda ke bayyana kasaitaccen hali na daular Yuan.

Gine-ginen addinai yana da yawa kuma manya ne, dalilin da ya sa haka, shi ne masu mulki na daular Yuan sun amince da addini, musamman addinin Buddah irin na Tibet. Hasumiyar Bai na dakin ibada mai suna Miaoyin da ke nan birnin Beijing wata hasumiyar Lama ce wadda wani mai sana'a , dan kasar Nepal ya tsara kuma ya gina.

(Hoton Hasumiyar Bai na dakin ibada mai suna Miaoyin da ke birnin Beijing )

Gine-ginen daular Ming

Daga daular Ming ( 1368-1644, na bayan bayyanuwar Anabi isa Alaihissalam), kasar Sin ta shiga karshen lokaci na zamantakewa ta mulkin gargajiya. Sigar gine-gine na lokacin nan, galibi dai sun sami asali daga daular Song, wato babu sauye-sauye sosai, amma tsarin gine-gine mai girma ne kuma na bayyana hali mai kyau.

Tsarin birni da gine-ginen fada na lokacin nan, har suna amfanawa mutane na bayan daular nan: alal misali, wadannan tsari da gine-gine na daular Ming, sun yi tasiri ga hedkwatar Beijing da tsohon birnin Nanking, wani tsohon birni da ke kasancewa yanzu a kasar Sin, an kafa fadar sarakunan daular Qing duk bisa harsashi na daular Ming , kuma bayan da aka yi ta kyautata ta. Hedkwatar kasa wato Beijing na lokacin can, an kyautata shi ne bisa harsashi na da, wato an kasance da kashi 3, a birnin waje da na ciki da birnin sarki.

A daular Ming, an yi ta yin kokariwajen gina wani kasaitaccen tsarin tsaro wato babbar ganuwa, wasu muhimman kashi daga cikin babbar ganuwa, bangaye da wurin da ke waje da kofar ganuwa da garuruwa ko tsoffin sansanoni, duk an gina da tubali, saboda haka gine-ginen sun kai matsayin koli. Babbar ganuwa ta daular Ming ta soma ne a nahiyar gabas daga bakin kogin Yalu, ya zuwa nahiyar yamma na wurin ketare duwatsu, birnin Jiayu da ke lardin Gansu, wadda tsawonta ya kai kilomita 5660. Shahararrun wurin ketare duwatsu mai suna Shanghai da na birnin Jiayu, sun zama fitattun gine-gine da ke da sigar musamman cikin fasahar gine-ginen kasar Sin : Babbar ganuwa ta Badalin na Beijing da ta Simatai, suna da fasaha mai ma'ana.

(Hoton Babbar Ganuwa)

Cikin lokacin can, yin ado da zana hotuna masu launuka ga gine-ginen ?? sun zama kamar wani tsari: a wajen kayayyakin yin ado an kasance da tubali da dutse da dabe mai suna Luili da tumba mai tauri, kuma an yi amfani da tubali wajen gina bangayen gidajen jama'a.

Cikin daular Ming, tsarin gine-gine na kungiya-kungiya na kasar Sin ya sami kyautatuwa. Kabarin Mingxiao da ke birnin Nanking da kabari Shisan na birnin Beijing sun zama masu abubuwa masu amfani na kwarewa wajen yin amfani da labarin kasa da muhalli don shinfida halin ladabi da na zama shiru.

Ya kamata wani abu da aka bayyana shi ne, dabarar kimanta makoma ta yadu sosai cikin daular Ming, wadda ta zama al'ada ta zamanin da ke cikin tarihin gine-ginen kasar Sin , har ta yi tasiri ya zuwa zamanin yanzu. Daga wannan waje kuma, kayayyakin daki na sigar Ming sun shahara cikin kasa da kasa.

Gine-gine na daular Qing

Daular Qing ( daga shekarar 1616 – 1911 na bayan bayyanuwar Annabi Isa Alaihissalam) ta zama wata daular gargajiya ta karshe cikin kasar Sin, gine-gine na lokacin nan, sun fi mai da muhimmanci kan kyaun kwarai da kayatarwa, duk saboda galibansu sun gaji al'adun daular Ming.

A cikin daular Qing, an kiyaye hedkwatar birnin Beijing irin na daular Ming, cikin birnin an kasance da kofofi masu girma guda 20, kofar Zhengyang ita ce kofar da ke nuna kasaitaccen hali da ke cikin birnin. Saboda an yi amfani da fadar sarakuna na daular Ming, sarakuna na daular Qing sun giggina gandunan sarakuna masu kasaita, ciki har da gandu Yuanming Yuan mai kayatarwa da babban gandun Yihe Yuan mai kyaun gani. Cikin lokacin kuwa, N an soma yin amfani da gilashi a gine-ginen kasar Sin haka kuma akwai gine-ginen jama'a masu sanforori daban daban.

Gine-ginen addinin Buddah na Tibet da ke da halin musamman sun bunkasa sosai. Gine-ginen haikali na addinin Buddah iri-ri ne, wadanda suka da tsarin musamman na gine-ginen al'adu na dakin ibada da haikali na da, an kago sanfurori da yawa kan gine-ginen, alal misali haikalin Yonghe da ke birnin Beijing da wasu dakunan ibada da aka gina a birnin Chengde na lardin Hepei , duk sunawakiltar addinin Buddah irin na Tibet.

A karshen lokacin daular Qing, cikin kasar Sin an kuma kasance da sabbin gine-gine da ke hade da tsarin gine-gine na Sin da na Turai.

(Hoton haikalin Yonghe da ke birnin Beijing)

>>[Gine-ginen zamani]

Galiban tsare-tsaren gine-gine na zamani na kasar Sin

Gine-ginen zamani na kasar Sin ana nufin gine-ginen kasar Sin tun bayan tsakiyar karni 19.

Tun daga shekarar 1840, lokacin tashin yakin wiwi, ya zuwa shekarar 1949 wato lokacin kafuwar sabuwar kasar Sin, gine-ginen kasar Sin suna da wani halin musamman wato sun hada gine-gine na Sin da na Turai kuma suna bayyana halaye da yawa. Amma cikin lokacin, tsohon tsarin gine-gine na gargajiya na kasar Sin su ma sun sami fiffiko saboda yawansu, wasu gine-ginen kasuwanci kamar gidajan nuna wasannin fasaha da gidajen abinci da hotel da babban kantin sayar da hajjoji, wadanda suka karya tsarin gine-gine irin na gargajiya, sun kara fadin gine-ginen . Cikin birnin Shanghai da birnin Tiantsin inda ke da shiyyar haya ga mutanen waje, an gina ofishohin kananan jakadanci na kasashen waje da kamfanonin ciniki da bankuna da hotel-hotel da kulob-kulob irin na waje.

Bayan shekarar 1949 na kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, gine-ginen kasar Sin sun shiga wani sabon lokacin tarihi. Cikin lokacin, gine-ginen zamani na kasar Sin sun karya kuntata na kusa-kusa kan matsayin zamanintarwa da adadinsu da tsare-tsarensu da fannoninsu har da shiyyar da aka gina gine-ginen zamani, an bayyana wani hali sabo fil. Tun bayan shekaru 80

na karnin da ya shige, taki kan taki, gine-ginen kasar Sin sun soma bude kofa ga kasa da kasa da shigad da na kassahen waje, tun daga lokacin, gine-ginen zamani na kasar Sin sun sami bunkasawa kan bangarori da yawa.

Gine-ginen zamani da ke da halin musamman na kasar Sin

Hotel na birnin Shanghai

An kafa Peace Hotel na birnin Shanghai a shekarar 1929, da sunan hotel Huamao,wanda ya zama gini iri na Gothic na tunanin jami'ar Chicago, tsawon ginin nan ya kai mita 77 da ke da benaye 12. An gina bangayen waje na hotel din ne da wani irin dutse mai suna Huagan, akwai ginin hasumiya irin na dala da babbar kofa mai juyawa; babban zaure mai fadi da baranda, a daben kasa an shinfida marmara irin na kasar Italiya da kafa ginshikai na marmara; tsoffin kayayyakan fitilu, dakunan kwana na musamman masu sigar kasashe 9 wadanda ba a taba irinsu ba. duk gine-gine masu kayatarwa ne kuma na bayyana tsoffin halayae, sabili da haka ginin na da wani lamba "gini na farko na gabasmai nisa".

Kabarin Zhongshan na birnin Nanking

Kabarin Zhongshan na birnin Nanking shi ne kabari na Mista Sun Yat-sen na tawayen yada dimokuradiyya na kasar Sin wanda ke tsaunin Zhong da ke karkarar birnin Nanking, duk kabarin ya dogara kan tsaunuka da su mike sama-sama, kabarin mai girma ne. In an hange duk shiyyar kabarin sai a ce sigarsa kamar wani babbar kararrawa ce, ganiyar kararrawa ita ce wani fili mai sifar rabin wata. Sigar gine-ginen kabarin Zhongshan ta hada da sigar kasar Sin da ta kasashen Turai, manyan gine-gine da ke cikin kabarin da tsaunin Zhong mai girma sun hadu gu daya, ciki ke da filayen ciyawa da mataki mai fadi da ya mike sama. Sabili da haka an yaba kabarin da cewa "kabari ne na farko cikin tarihin gine-gine na yanayin kusa na kasar Sin".

(Hoton Kabarin Zhongshan)

Babban dakin taruwar jama'a

Babban dakin taruwar jama'a yana nahiyar yamma ta filin Tian Anmen na nan birnin Beijing, inda shugabannin kasar Sin da jama'a ke yin harkokin siyasa da na diplomasiya, wanda kuma ya zama dya daga cikin muhimman gine-gine masu alama na kasar Sin. A shekarar 1959 ne aka gina babban taruwar jama'a wanda ke da fadin muraba'in mita dubu 170 , babban dakin taruwa mai kayatarwa ne, a kyamaren babban daki an sa dabe mai suna Luili na launin rawaye da kore, da manyan gishinkai har da gine-ginen da ke kewayen da babban dakin, kamar an zana wani hoto mai kayatarwa na duk filin Tian Anmen. Cikin babban dakin taruwa, akwai babban zaure da dakunan taro sama da dari, kowanensu yana da nasa halin musamman, a kan sigar gine-gine, ba ma kawai an bayyana tunanin gargajiya wajen sigar gine-ginen kasar Sin ba, har ma an tsamo abubuwa masu fiffiko na gine-ginen kasashen waje cikin babban dakin taruwar jama'a, duk babban dakin nada kyaun gani kuma na da halayen musamman.

Xiangshan hotel na Beijing

Xiangshan hotel na Beijing yana cikin lanbun shan iska na Xiangshan da ke yammacin karkarar birninBeijing, wanda aka kafa a shekarar 1982, ofishi mai zanen gine-gine na Mr. Bei Lumin, shahararenmai zanen gine-gine na kasar Amurka ne ya tsara gine-ginen hotel din. An tsamo halayen musamman na gine-ginen lambunan shan iska na kasar Sin. Yawancin gine-ginen fara ce, bangayen gine-gine irin na babbar fada. Farfajiyar tsarin gine-ginen Siangshan Hotel tana da halin gandun shan iska na kudancin kasar Sin , kuma ke da sarari mai fadi kamar lanbunan shan iska na arewacin kasar Sin, duk gine-ginen ke dace da fasalin gine-ginen lanbunan shan iska na gargajiya, kuma ke dacewa da bukatun yawon shakatawa na zamani. A shekarar 1984, Hotel Xiangshan ya sami lambar girmamawa ta kungiyar gine-gine ta kasar Amurka.

Sabon dakin ajiye litattafai na Jami'ar Qinghua

A shekarar 1991 an kafa sabon dakin ajiye litattafai na jami'ar

Qinghua, wanda ke hade da tsohon dakin ajiye litattafai da aka gina a shekarar 1931, suna dacewa da juna kuma ke bayyana nasu halin zamani, wadannan sabbin dakunan da na tsoho sun zama gine-gine mafi girma da ke cikin shiyyar cibiya ta farfajiyar jami'ar. Masu tsare gine-ginen sabon dakin ajiye litattafai na Jami'ar Qinghua sun ci nasara kan ta yaya za a sa sabon tsarin ya dace da na tsoho wanda ya zama kowane sabon gine-gine ke fuskanta. An shiga da gine-ginen cikin manyan gine-gine guda 10 na birnin Beijing na shekaru 90 na karnin da ya shige.

Babban ginin Jinmao na birnin Shanghai

Babban ginin Jinamao na shanghai wanda ke da tsawon mita sama da 420, ya zama "gini mai tsawo na farko cikin Sin", muhimman gine-gine na da benaye 88 wanda ya zama babban gini mafi tsawo cikin kasar Sin a yanzu, wanda kuma ya zama babban bene mafi tsawo na uku a duniya duka. Jimlar fadin gine-ginen Jinmao ta kai fadin muraba'in mita dubu 290, tsare-tsarensa da ginawarsa, sun bayyana fasalin gine-ginen kasar Sin fasahar kimiyya ta zamani sun hada sosai, saboda an ce gine-ginen ya nuna tsari mafi kyau na duniya da na kasar Sin kan tarihin gine-ginen kasar Sin , kuma ya zama fiffiko na fasahar gine-ginen zamani, kuma ya zama aikin gine-gine na matsayi na duniya wanda galiban Sinnawa ke daukar nauyin ginawa bisa wuyansu .

>>[Shahararrun masu zanen gine-gine]

Shahararrun masu zanen gine-gine na kasar Sin

Liang Sicheng

Mr. Liang Sicheng ( 1901-1972 ), ya dukufa kan aikin ba da ilimi na tsara zanen gine-gine har cikin dogon lokaci, sabili da haka ya ba da babban taimakonsa kan aikin.

A wajen fanning yin bincike, tun daga shekaru 30 na karni na 20, Mr. Liang Sicheng ya soma in bincike kan gine-ginen tsohon zamani na kasar Sin, ya rubuta bayanan musamman da takardun bayanai dangane da gine-ginen kasar Sin na tsohon zamani. Wadanda ke da babbar daraja kan ilimi.

Mr. Liang Sicheng ya kma gabatar da wasu muhimman shawarwarin tsarin fasalin birnin Beijing da tsara zanen gine-gine, ya kuma shiga aikin tsara fasalin birnin Beijing, da aikin tsara zanen tambarin kasa da na dogon dutse da aka kafa don tunawa da mazajen jiya, da babban dakin taruwa da limamin addinin Buddah Jianzhen da ke birnin Yanzhou, ya yi nazarin tsara gine-gine na sigar kabilar.

Mr. Liang Sicheng ya zama daya daga cikin masanan da suka yi binciken gine-ginen tsohon zamanin da da takaita takardun gine-gine ta hanyar kimiyya na kasar Sin tun da wuri. Sabili da hakja litattafansa na ilimi sun zama kayan gargajiya masu daraja na cikin dari'kar gine-ginen kasar Sin.

Wu Liangong

Mr. Wu Liangong wanda aka haife shi a shekarar 1933, ya taba zama mataimakin shugaban kungiyar gine-ginen duniya, da shugaban kungiyar WSE, ya zama daya daga cikin masu jagorancin gine-ginen kasar Sin da tsara fasalin birane. Ya gabatar da ra'ayi da shawara dangane da gine-ginen kasar Sin da ba da ilimin tsara fasalin birane, kana ya ba da babban taimako domin yin binciken kafa tsarin ba da ilimi kan gine-ginen da ke da sigar musamman na kasar Sin da tsara fasalin birane. Sabbin gine-ginen da ke cikin kusurwa 4 na wata farfajiya da aka gina a 'yar hanya mai suna Juer na nan birnin Beijing wadanda Mr. Wu Liangyong ya tsara fasalinsu, sun samu mindar mazauna ta kasa da kasa ta shekarar 1992 ta Majalisar Dinkin Duniya, da mindar zinariya ta tsara gine-gine nagari ta kungiyar gine-ginen Asia da mindar tsara fasalin gine-gine nagari ta kungiyar nazarin gine-ginen kasar Sin. Kiyaye muhallin gine-gine da nazarin bunkasuwarta cikin ajandar mai da shiyyar ci gaba da ta zama birni wanda ke zama muhimmin aiki na asusun kimiyya na halittun kasa da ya shugabanta , ya zama wani sakamakon binciken kimiyya da ke da matsayin gaba na duniya.

Zhang Kaiji

Zhang Kaiji shi ne mai tsara zanen gine-gine na zuri'a ta farko na cikin sabuwar kasar Sin, an haife shi a shekarar 1912 a birnin Shanghai, ya sauke karatu daga sashen nazarin gine-gine na jami'ar tsakiya ta Nanking a shekarar 1935, ya taba zama babban mai tsara zanen gine-gine na cikin hukumar tsara zanen gine-gine da yin bincike, mai ba da shawarar gine-gine na gwamnatin birnin Beijing,mataimakin babban direkta na hukumar gine-ginen kasar Sin, a shekarar 1990 ma'aikatar gine-gine ta ba shi lakabin "babban malamin tsara zanen gine-gine". Ya taba tsara dandalin duba farati na filin Tian Anmen, dakin ajiye kayayyakin juyin juya hali da dakin ajiye kayayyakin tarihi da masaukin bakin kasa mai suna Diao Yutai, da babban zauren kallon yanayin samaniya na Beijing.

Yang Tingbao

Mr. Yang Tingbao ( daga shekarar 1901 – 1982), a shekarar 1921 ya yi dalibta cikin kasar Amurka, ya shiga sashen ilmin gine-gine na jami'ar Pennsylvania , a shekarar 1924 ya sami minda ta matsayin farko na Emerson Priza Competition da minda ta matsayin farko na Municipal art Society Priza Competition ta Amurka.