logo

HAUSA

Babi21: Fasahar jama'a

2020-10-30 10:07:41 CRI

>>[Wasanni]

Wasan Piying na kasar Sin

Wasan Piying daya ne daga cikin fasahohin jama`a na kasar Sin,ya hada da wasan Piying na Longdong na lardin Gansu dake arewa maso yammacin kasar Sin da wasan Piying na Shaanxi na lardin Shaanxi na kasar Sin da wasan Piying na shanxi na lardin Shanxi na kasar Sin.Dalilin da ya sa a kiransa da sunan wasan Piying shi ne domin an yi kayayyakin da ake amfani da su yayin da ake yin wasan da fatar sa,saboda ma`anar `pi` a cikin Sinanci ita ce fata.

Wasan Piying na Longdong yana yaduwa a gundumar Pingliang da ta Qingyang da sauran gundumomi na lardin Gansu,yawancinsu suna kusa da lardin shaanxi da jihar Ninxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai.

A daular Ming da daular Qing ta tsohuwar kasar Sin wato tun daga karni na 14 har zuwa karni na 19,wasan Piying na Longdong ya yi yadu sosai,siffar kayayyakin wasan Piying tana da kyan gani kwarai da gaske.An yi amfani da fatar sa mai launin baki domin yin kayayyakin wasan Piying,irin wannan fata tana da taushi,da sauki an yi amfani da ita.

Da farko dai,a gyara fatarsa kamar yadda kake so,sa`an nan kuma a zana hoto a kanta,daga baya sai a saka hoton da wuka,daga baya a sa launuka iri daban daban a kanta,a karshe dai a busar da ita.Idan fatar ta bushe,to,kayan wasan Piying ya yi.

Kayayyakin wasan Piying suna da yawan gaske,alal misali mutane,musamman fuska da hula,suna da tsarin musamman,kuma launukan da aka zana kan kayayyakin sun yi sauki,alal misali launin ja da na rawaya da baki da kore.

To,yanzu kayayyakin wasan an shirya su,sai a fara yin wasa da su.Yayin da ake yin wasan Piying,sai a motsa jikin kayan wasan da yatsar hannu,a sa`i daya kuma,ana rera waka da babbar murya,wasan nan yana da ban shawa`a kwarai da gaske kuma yana cike da halaye masu farin jini.

Tatsuniyoyin da wasan Piying na Longdong ke nuna sun yi yawan gaske,alal misali tatsuniyar tarihi da sauransu.Dukkansu sun jawo hankulan masu kallo sosai.

Wasan Piying na Shaanxi

Wasan Piying na Shaanxi shi ma haka ne,ya yi kama da na wasan Piying na Longdong,amma yana da tsarin musammansa,wato wasan Piying na Shaanxi ya fi mai da hankali kan yin magana a maimakon rera waka yayin da ake yin wasa.

Wasan Piying na Shanxi

Wasan Piying na Shanxi kuwa,shi ma ya yi kama da wasan Piying na Shaanxi.Banbanci kadan tsakaninsu shi ne launin da aka sa kan kayan wasan Piying na Shanxi ya fi haske.

Ban da wannan kuma,kayayyakin wasan Piying na Shanxi sun fi so su nuna fatan alheri kamarsu `Ranka ya dade` da `haihuwar yara da yawa` da `samun kudi da yawa` da sauransu.

Duk da haka,ana iya cewar,faral hula na kasar Sin sun fi so su kallon wasan Piying na gargajiyar kasar Sin,dalilin da ya sa haka shi ne domin suna da ban sha`awa.(Jamila Zhou)

Kayayyakin wasan da ake yi da yumbu (1)

A kasar Sin,mutanen wurare da yawa suna yin kayayyakin wasa da yumbu,wanda a cikin lardin Henan da na Hebei sun fi yin suna.

A lardin Henan dake tsakiyar kasar Sin,akwai wani irin kayan wasa da ake kiransa da suna `karen yumbu`,launinsa baki ne.Amma karen yumbu ba kayan wasan kare da ake yi da yumbu ba ne,shi birin yumbu ne.Birin yumbu yana da ire-ire daban daban wato siffarsu da sunansu sun bambanta,ma`anarsu ita ma ta bambanta,amma dukkansu suna da ban sha`awa,yara suna son su yi wasa da su.

Saboda al`adun tarihin wuraren kasar Sin sun yi zurfi,shi ya sa kayayyawan wasa iri daban daban da ake yi da yumbu suna da ma`anar al`adu mai zurfi,wato su ba kayayyakin wasa kawai ba ne.

Kayayyakin wasan da ake yi da yumbu (2)

A shiyyar Huaiyang ta lardin Henan na kasar Sin,yawancin kayayyakin wasan yumbu suna da kawuna biyu,an yi su da hannu bisa matakai biyar.Da farko dai,an zuba ruwa kadan cikin yumbu,sa`an nan kuma an matsa yumbun da karfi,daga baya an yi kayan wasa mai siffar dabba da hannu da yumbun,bayan wannan,sai an sa launuka a kansa,a karshe an zana hoto a kansa.

Kayayyakin wasan da ake yi da yumbu (3)

A gundumar Jun ta lardin Henan na kasar Sin,kayayyakin wasan yumbu sun yadu sosai.Kowace shekara,yayin da ake taya murnar ranar bikin sallar wasan fitilu a ran 15 ga watan farko da bikin sallar fatalwoyi a ran 15 ga watan Yuli na kalandar gargajiyar kasar Sin,a kullum an sayar da kayayyakin wasan yumbu da yawan gaske,musamman `yan mata na kauyuka wadanda ba su haifi yara ba sun fi so su saye su.

An yi yawancin kayayyakin wasan yumbu na gundumar Jun da hannu,kuma an saka hoto a kansu da tsinke,bayan sun bushe,an zana launuka a kansu.Ire-irensu sun yi yawan gaske kuma suna da ban sha`awa.

Kayayyakin wasan da ake yi da yumbu (4)

Wanda a ciki dokin yumbu ya fi yin suna,suna hade da babban doki ja da babban doki baki da dokin kawuna biyu da karamin doki da dai sauransu.

Kayayyakin wasan da ake yi da yumbu (5)

Ban da wannan kuma,a kan tarihin kasar Sin,garin Baigou na gundumar Xincheng ta lardin Hebei dake arewacin kasar Sin ya yi suna sosai domin kayayyakin wasa na jama`a,ire-iren kayayyakin wasan yumbu na garin suna da yawa,wanda ke hade da mutumin yumbu.

Mutumin yumbu wanda ke daukar doguwar wuka a cikin hannunsa shi daya daga cikin shahararun kayayyakin wasan yumbu na garin Baigou,tsayinsa ya kai wajen sentimita 60,mutanen kasar Sin su kan sa su a kan tebur domin yin kwaskwarima a cikin daki.

Kayayyakin wasan da ake yi da yumbu (6)

Kazalika,a kauyen Luluba na garin Baigou na gundumar Xincheng ta lardin Hebei na kasar Sin,kajin yumbu ya fi yin suna,siffarsa tana da karfi,ya zama daya daga cikin abubuwa masu ba da misali na kayayyakin wasan yumbu a shiyyar arewacin kasar Sin.

Kajin yumbu ya hada da iri uku,manya da matsakaita da kuma kanana,tsayin babban kajin yumbu ya kai sentimita 25,tsayin karamin ya kai wajen sentimita 6.Fasahar yin babban kajin yumbu da babban mutumin yumbu ta fi wuya.

Kusan kowanen mutumin kasar Sin yana kaunarsu saboda suna da kyan gani kuma suna da ban sha`awa.

Kayan wasan da ake wasa da sanda

A zamanin da,a kasar Sin,mutane su kan kira kayan wasan da ake wasa da sanda da sunan `mutum mutumin da ake wasa da sanda`,yayin da ake wasa da irin wannan kayan wasa,dole ne a yi amfani da sanda,ido da baki na kayan suna iya motsi idan sanda ta motsa.Irin wannan kayan wasa ya kumshi iri uku wato manya da matsakaita da kuma kanana,dukkansu suna da tsarin musamman nasu.Yayin da ake kera wannan kayan wasa,masu kera sun fi mai da hankali kan fuska wato ido da hanci da baki,kansa yana da ban sha`awa.

Kayan wasan da ake wasa da sanda ya yi ta yaduwa sosai a shiyoyyi da yawa a kasar Sin,halayensu sun sha banban,sunayensu su ma sun sha banban.A arewa maso yammacin kasar Sin,mutane su kan kira shi da sunan `wasan sanda`,a lardin Sichuan dake yamma maso kudancin kasar Sin,mutane su kan kiransa da sunan `wasan kan katako`,a lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin,mutane su kan kiransa da sunan `wasan hannu`.Yayin da ake wasa da irin wannan kayan wasa,`yan wasa su kan rera waka,`yan kallo sun ji dadi kwarai da gaske.(Jamila zhou)

Kayan wasa da aka dinka na lardin Shaanxi

A lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin,jama`a suna son kayan wasa da aka dinka sosai,irin wannan kayan wasa yana da dogon tarihi,kuma yana da siffofi daban daban kamarsu yaro mai kiba da tsuntsaye da kifi da kwado da kan alade da fure da `ya`yan itatuwa da damisa da sauransu.Matan kauyuka suna so su nuna fatan alhari ta hanyar dinka irin wannan kayan wasa.

Kuma yana da siffofi daban daban kamarsu yaro mai kiba da tsuntsaye da kifi da kwado da kan alade da fure da `ya`yan itatuwa da damisa da sauransu.Matan kauyuka suna so su nuna fatan alhari ta hanyar dinka irin wannan kayan wasa.

Kayan wasa na 'sarkin biri da Bajie'

A cikin fasahar jama`a ta kasar Sin,`yan fasaha sun fi so su zana hoton sarkin biri da Bajie wato wani alade mai farin jini,daga hotunan da aka zana,ana iya gane cewa,sarkin biri yana da wayo,amma aladen Bajie yana da kirki

Kwaryar kwaro

Kwaryar tsiro kayan wasa ne da aka yi domin kiwon kwaro,idan kwaryar ta girma,sai a cire ta,bayan kwanaki kadan,sai a saka hotuna masu kyan gani a kanta,alal misali,tatsuniya da hoton dabbobi da fure da kifi da sauransu.A lokacin sanyi,an sa tsiro a cikin kwaryar da aka saka,kwaro ya rera waka a ciki,ana jin dadi.

Gunki ya buga ganga

A kasar Sin,`yan fasaha sun yi kayan wasa iri daban daban ta hanyar iri daban daban da katako,irin wannan kaya yana iya yin motsi kuma yana da murya.Alal misali `Bangchui wato irin wani kayan wasa dake yin kama da sanda` da `gunki ya buga ganga` da `damisar fata` da sauransu.

Kayan wasa da ake kiransa da suna `mutum mai dasa hatsi`,wannan kayan wasa yana hade da kashi uku wato hula da kai da kuma jiki,an hada su ne da layin karfe,idan an ja layin nan,kayan mutum zai yi motsi kamar yadda kake so,yana da ban sha`awa kwarai da gaske.

Mutum mutumin da ake yi da katako

A kauyen Fannian na gundumar Yancheng ta lardin shandong dake gabashin kasar Sin,kayan wasa da aka yi da katako ya fi yin suna a duk fadin kasar Sin,irin wannan kayan wasa yana da siffofi da yawa.

Wanda a ciki mutum mutumin da aka yi da katako ya fi jawo hankalin mutane,siffar irin wannan kayan wasa ta yi kama da wata karamar sanda,ba hannu ba kafa,kansa yana iya yin motsi,an fid da abin dake cikin cikinsa,shi ya sa cikinsa ba kome,ana iya zuba rairayi a ciki,idan an yi juyayi,murya tana da dadin ji.A kan fuskar jikin wannan kaya,`yan fasaha su kan zana hotuna da launuka iri daban daban,wannan kayan wasa yana da kyan gani sosai.

Shirwa

Shirwa tana daya daga cikin kayayyakin wasa na jama`ar kasar Sin,ana iya yin wasa da ita kuma ana iya motsa jiki da ita.Idan shirwa ta tashi sama,ma`anar wannan ita ce masifa ta gudu tare da ita,shi ya sa shirwa ta yi yaduwa a wurare daban daban na kasar Sin,musamman a birnin Weifang na lardin Shandong da birnin Beijing da birnin Tianjing da birnin Nantong na lardin Jiangsu da sauransu.

Shirwa ta Weifang na lardin Shandong tana da dogon tarihi,siffarta tana da kyan gani,fasahar yin shirwa tana da kyau sosai.

Tarihin yin shirwa na birnin Beijing ya kai shekaru fiye da dari uku,wadda ta fi ita ce shirwar swallow,siffarta ta yi kama da swallow,ma`anarta ita ce fatan alheri.

Wasan Nuo na gargajiyar kasar Sin

Wasan Nuo na kasar Sin yana da dogon tarihi,tun can can da,yayin da ake tunawa da kakanin kakaninmu,`yan wasan fasaha su kan yi wasan Nuo.Ya zuwa daular Shang,wato daga shekara ta 1600 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam zuwa shekara ta 1046 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam,an fara taka rawar Nuo don kore dodanni,bunkasuwar wasan Nuo ta kawo tasiri ga wasannin wuri na kasar Sin.

An fara yin wasan Nuo ne bisa tushen rawar Nuo,yayin da `yan wasan fasaha suke yi wasan Nuo,dole ne su sa kayan fuskar katako a kan fuskarsu,sun rera waka kuma sun taka rawa kamar su kansu dodanni ko gumaka.

Yanzu dai,a shiyyar dake arewa maso gabashin lardin Guizhou na kasar Sin,mutane su kan yi wasa Nuo.A gundumar Dejiang,a kalla dai akwai dandalin wasan Nuo fiye da sittin,yawan `yan wasan fasahar wasan Nuo ya kai fiye da dari daya.

Kayayyakin fuskar katako da aka yi domin wasan Nuo suna banbanci,wato suna hade da dodanni da gumaka da farar hula da kan shanu da fuskar doki da dai sauransu.

Wasan da ake yi a kan kasa na kasar Sin

Wasan da ake yi a kan kasa na kasar Sin ya yadu sosai a wurare da yawa na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin,musamman na shiyyar Anshun.Yayin da ake murnar bikin sallar bazara ko kafin bikin sallar wasan fitilu wato kafin ran 15 ga watan Janairu na kalandar gargajiyar kasar Sin,a kauyuka,ko ina ana iya ganin `yan fasaha manoma suna yin wasa a kan kasa.Makasudin yin wasan kasa shi ne domin gujewa haramtattun abubuwa da bala`o`i da kuma nishadi.

`Yan wasan fasaha na wasan kasa su kan sa abu su rufe fuska yayin da suke rera wakoki,abun rufe fuska na wasan kasa ya hada da ire-ire har biyar.A kan hular dan wasan fasaha namiji,mutane su kan sa abu mai siffar dragon.A kan hular yar wasan fasaha mace,su kan sa abu mai siffar babban tsuntsu da furanni.(Jamila)

>>[Abin Ado]

Hoton sabuwar shekara da aka saka kan katako na kasar Sin

Hoton jama`a da aka zana don taya murnar sabuwar shekara yana da dogon tarihi,wato tun daga daular Han,mutanen kasar Sin suka fara zana hoto,sa`an nan kuma an sa hoton a kan kofa,dalilin da ya sa haka shi ne don gujewa haramtaccen abu.

Ya zuwa daular Song wato daga shekara ta 960 zuwa shekara ta 1279,saboda an fara yin amfani da fasahar buga hoto kan takarda bisa katakon da aka saka,shi ya sa ana iya buga hotunan taya murnar sabuwar shekara da yawan gaske,kuma an sayar da su a kantuna,daga nan wato tun daga daular Song,fasahar buga hoton sabuwar shekara ta sami bunkasuwa cikin sauri.

Ko a fannin abubuwan dake cikin hotunan da aka buga,ko a fannin hanyar nuna ma`ana,hoton sabuwar shekara na jama`ar kasar Sin yana da tsarin musammansa.

Ya zuwa karshen daular Ming wadda ta fara ne daga shekara ta 1368 kuma ta kammala a shekara ta 1644,har zuwa daular Qing wadda ta fara ne daga shekara ta 1368 kuma ta kammala a shekara ta 1911,fasahar buga hoton taya murnar sabuwar shekara ta kai matsayin koli,jama`ar kasar Sin suna kaunarsa kwarai da gaske.Wadanda suka fi yin suna a kasar Sin suna hade da `Hoton shanu a lokacin bazara` da `Muna da isashen abinci a kowace shekara` da `An sami girbi` da sauransu.A sa`i daya kuma,an kafa cibiyoyi da dama don buga hotunan taya murnar sabuwar shekara a kasar Sin,alal misali,cibiyar Yangliuqing ta birnin Tianjing da cibiyar Taohuawu ta birnin Suzhou na lardin Jiangsu da cibiyar Yangjiabu ta gundumar Wei ta lardin Shandong.Ya zuwa karshen daular Qing,saboda an shigo da sabuwar fasahar buga hoto daga kasashen yamma,shi ya sa hoton sabuwar shekara na wurare daban daban na kasar Sin bai sami ci gaba kamar yadda ya kamata ba.(Jamila zhou)

Takardar sifofin abubuwa da aka yanka da almakashi ta kasar Sin

A wurare daban daban na kasar Sin,yayin da ake taya murnar bikin sallar bazara,mutane su kan yanke takardar sifofin abubuwa daban daban,sa`an nan kuma an lika takardun da aka yanka kan marufin taga ko kofa ko a gaban tebur,ta yadda za a nuna fatan alheri ga sallar bazara.

Takardar abin kwaikwayar da aka yanka da almakashi ita ce daya daga cikin fasahohin jama`a wadanda suka fi yaduwa a kasar Sin.Ba a san asalinta ba,amma tun daga shekaru fiye da dubu daya da suka shige,sai mutanen kasar Sin suka fara yanke takardar sifofin abubuwa domin yin kwaskwarima.Bisa abubuwan da aka rubata a cikin littafin tarihi,an ce,`yan mata na daular Tang sun taba sa takardar da aka yanka a kansu domin yin kwalliya.Ya zuwa daular Song,mutane sun taba sa takardar da aka yanka a kan abubuwan kyauta domin yin kwaskwarima,wasu mutane sun lika takardun a kan tagogi da kofofi,wasu sun lika a kan bango da madubi da sauransu,wasu mutane sun mayar da aikin yanke takarda a matsayin sana`a.

An yanke takardar kwaikwayan sifofi daban daban da almakasai da hannu,takarda daya,almakasai guda daya sun isa,da sauki ake fara aikin nan.Amma,ga mutane na sana`a,aikin nan yana da wahala.

Ana iya yanke takarda domin kwaikwayon abubuwa da yawan gaske,alal misali,fure da tsuntsu da kifi da kananan dabbobi da mutane dake cikin tatsuniyoyin gargajiyar kasar Sin da sauransu.Ana iya yanke takarda kamar yadda ake so.

A da,a kauyukan kasar Sin,yayin da ake hutawa,`yan mata su kan yi taruruka kuma sun yanke takarda tare,suna jin dadi.Yanzu bisa bunkasuwar zaman al`umma,mutane wadanda suke koyon fasahar yanke takarda sun ragu bisa babban mataki,amma wasu sun mayar da aikin yanke takarda a matsayin sana`arsu.A halin da ake ciki yanzu,a kasar Sin,akwai kamfanin fasaha na yanke takarda,kuma akwai kungiyar fasaha ta yanke takarda,mutane masu kaunar fasahar yanke takarda su kan shirya nune-nune kuma su kan yi tattaunawa da kuma cudanya kan fasahar yanke takardarsu.

Kawo yanzu,aikin yanke takarda ya riga ya zama daya daga cikin fasahohin jama`ar kasar Sin,ko ina ana iya ganinsu,alal misali,littafi da jarida da mujalla da telebijin da film da dai sauransu.(Jamila zhou)

Hoton sabuwar shekara na lardin Shanxi na kasar Sin

An raba hoton taya murnar sabuwar shekara na Shanxi iri biyu wato na arewa da na kudu.

Cibiyar hoton sabuwar shekara ta arewacin lardin shanxi ta kumshi gundumar Datong da gundumar Ying,wanda a ciki,hotunan sabuwar shekara da aka lika a kan tagogi sun fi shahara.Abubuwan da hotunan suke nunawa suna da yawa,musamman suna kunshe da tatsuniya da dabbobi da furanni da `ya`yan itatuwa da kayayyakin lambu da sauransu.

Hoton taya murnar sabuwar shekara na kudancin lardin Shanxi ya mai da hankali kan hoton dake shafar addinin Buddah,yayin da aka zana su,`yan fasaha su kan yi amfani da launin ja da rawaya da kore da baki.

Jama`ar kasar Sin su kan lika hoton sabuwar shekara kamar yadda suke so.(Jamila zhou)

Kayan wasan yumbu mai siffar damisa

A birnin Fongxiang na lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin,akwai wani irin kayan wasan da ake yi da yumbu,siffarsa ta yi kama da damisa,irin wannan kayan wasa yana da ban sha`awa kwarai da gaske.Tsayinsa daga sentimita 6 zuwa 100,launinsa yana da haske.

Da farko dai,a yi amfani da wata takarda mai kauri wadda siffarta ta yi kama da damisa,a sa yumbu a kanta,bayan yumbu ya bushe,sai a zana hoton fuskar damisa a kansa,kewayayyun idanu da manyan kunnuwa da babban baki da sauransu.Daga baya,a hada kayan wasa na kananan tsuntsaye da furanni da ciyayi a kan fuskar damisa da karfe siriri,ana iya motsa su da hannu.

A kan fuskar damisa,`yan fasaha kan zana hotuna iri daban daban,ma`anarsu ita ce fatan alheri,alal misali,`haihuwar yara da yawa` da `samun kudi da yawa` da `gujewa haramtattun abubuwa` da sauransu.Kayan wasan yumbu mai siffar damisa yana nuna mana fatan alherin da ake bukata.(Jamila zhou)

Kayan wasa mai siffar damisa da aka yi da zane

Kayan wasa mai siffar damisa da aka yi da zane ya yadu sosai a tsakanin jama`ar kasar Sin.A cikin zuciyar mutanen kasar Sin,damisa na iya gujewa haramtaccen abu kuma yana iya kare dukiya.A bikin sallar Duanwu wato a ran 5 ga watan Mayu na kalandar gargajiyar kasar Sin,al`ummar kasar Sin su kan yi kayan wasa mai siffar damisa da zane,wasu kuma su kan zana fuskar damisa a kan fuskar yara da ruwan `xionghuang` wato wani irin maganin gargajiyar kasar Sin,ma`anarsu ita ce lafiyar jiki da karfi da kuma jarumtaka.Akwai damisan zane iri daban daban,alal misali,damisan zane mai kai daya da damisan zane mai kai biyu da damisan zane mai kai hudu da damisan zane mai matashin kai da dai sauransu.

Kayayyakin da ake yin amfani da su wajen yin damisan zane suna da yawa,kuma fasahohi sun sha banban,wanda a ciki zane da siliki sun fi yawa.Da farko dai,a yanke zane bisa siffar damisa,sa`an nan kuma a dinka su,daga baya,a sa zane a ciki.A kan fuskar zanen,a zana fuskar damisa,wato babban kai da babban ido da babban baki da doguwar wutsiya.Kan damisa yana da ban sha`awa kamar yaro.

Ban da sallar Duanwu,a bikin sallar bazara da bikin sallar wasan fitilu da sauran bukukuwan gargajiyar kasar Sin,mutanen kasar Sin su kan yi damisan zane domin nuna fatan alheri.(Jamila zhou)

>>[Tuffafi]

Gyalen mata mai siffar gajimare

Daga daular Sui ta kasar Sin wadda ta fara daga shekara ta 581 kuma ta gama a shekara ta 618,an fara mai da gyalen mata mai siffar gajimare a matsayin wata irin tufa,`yan mata su kan kewaya gyale mai siffar gajimare a kan wuya.Ya zuwa daular Qing ta kasar Sin wadda ta fara daga shekara ta 1644 kuma ta gama a shekara ta 1911,kusan dukkan `yan mata su kan yi amfani da gyale a cikin zaman rayuwarsu na yau da kullum.Daga baya,`yan mata suna son daura gyale a lokacin bikin salla da bikin aure.

Mutane su kan yi amfani da zane takwas domin dinka gyale,siffar zane ta yi kama da gajimare,a kan kowane zane,masu dinka gyale su kan dinka furanni da tsuntsaye da ciyayi,ban da wannan kuma,su kan dinka sifofin dake shafar tatsauniya a kansu.Idan ana so a dinka wani gyale mai kyan gani kwarai da gaske,to,ana bukatar dogon lokaci,kuma ana bukatar fasaha mai nagarta.(Jamila zhou)

Takalman da aka dinka furanni a kansu na kabilar Yi ta kasar Sin

Kabilar Yi daya ce daga cikin kananan kabilu 55 na kasar Sin,tana kudu maso yammacin kasar Sin,tufafi da takalmanta suna da tsarin musamman na shiyya-shiyya,ana iya ganin abubuwa da yawan gaske daga tufafi da takalmansu,alal misali,tunanin gargajiya na mutanen kabilar Yi da al`adar kabilar da sauransu.Mutanen kabilar Yi su kan dinka furanni iri daban daban a kan tufafi da takalma.

Takalman da aka dinka furanni a kansu na kabilar Yi sun fi yin suna a kasar Sin,irin wannan takalmi ya yi kama da karamin jirgin ruwa,`yan mata na kabilar Yi su kan dinka furanni masu launin ja da rawaya da shudi a kan zane mai launin fari.Amarya ta kabilar Yi ta kan sa takalman da aka dinka furanni a kansu a gun bikin daura aure,ma`anar wannan ita ce amarya za ta ji dadin zaman rayuwarta har abada.(Jamila Zhou)

Karamar jaka dake cike da abu mai kamshi

Karamar jaka da aka dinka wadda ke cike da abu mai kamshi daya ce daga cikin kayayyakin fasaha na jama`ar kasar Sin,ana iya ajiye kananan kayayyaki a ciki,kuma ana iya yin amfani da ita wajen kwaskwarima.Ba ma kawai tana da sifofi daban daban ba,har ma tana da ma`anar al`adun jama`a.A bikin sallar Duanwu wato a ran 5 ga watan Mayu na kalandar gargajiyar kasar Sin,karamar jaka dake cike da abu mai kamshi tana iya gujewa haramtattun abubuwa,yawancin abubuwan dake cikin karamar jaka su ne magungunan gargajiyar kasar Sin mai kamshi kamarsu

`Aiye` da sauransu,suna iya kashe kwayoyi,wato jakar za ta ba da gudumuwa ga lafiyar jikinmu.Karamar jaka dake cike da abu mai kamshi tana nuna mana fatan alheri,launinta yana da haske,siffarta tana da ban sha`awa.(Jamila zhou)

Fasahar dinki ta Linfen na lardin Shanxi na kasar Sin

A kauyukan Linfen na lardin Shanxi dake arewacin kasar Sin,mutane su kan dinka furanni da dabbobi a kan tufafi da takalma da huluna,alal misali,su kan dinka furanni a kan tufafi da gyalen mata da hular yara da takalma da falmaran da sauransu,ban da wannan kuma su kan dinka furanni a kan zanen gado da zanen taga da zanen matashin kai da zanen jakar kudi da zanen tebur da sauransu.Ma`anar yawancin abubuwan da aka dinka ta kan nuna fatan alheri,alal misali,`haihuwar yara da yawa` da `ranka ya dade` da `samun kudi da yawa` da dai sauransu.(Jamila zhou)

Tufafin kabilar Yao ta kasar Sin

Mutanen kabilar Yao suna yin zaman rayuwa a kudancin kasar Sin,ire-iren tufafin kabilar Yao sun kai fiye da 60,kuma sun sha banban a bayyane.Tufafin `yan mata na Panyao na Tianlin dake jihar Guangxi mai cin gashin kai ta kasar Sin suna da tsarin musamman irin nasu,wato sun sha banban da na sauran kananan kabilun kasar Sin.

`Yan mata na Panyao su kan dinka sifofi da yawa da launi da yawa a kan tufafinsu,fasahar dinki tana da wahala,amma tufafin da suka dinka suna da kyan gani kwarai da gaske,kuma sun nuna mana cewa,`yan mata na Panyao suna da kirki kuma fasahar dinkinsu tana da kyau sosai.(Jamila Zhou)

Fasahar dinka ta kabilar Miao ta kasar Sin

Mutanen kabilar Miao da yawa suna zama a lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin,tufafinsu na da sifofi daban daban kuma suna da tsarin musamman.A cikin zaman rayuwarsu na yau da kullum,su kan sa tufafi na yau da kullum,amma yayin da suke taya murnar bukukuwa ko a gun bikin daura aure,mutanen kabilar Miao su kan sa tufafi na musamman wato tufafin da aka dinka musamman domin bukukuwa,fasahar dinka irin wadannan tufafi tana da wahaka,mutanen kabilar Miao su kan dinka `dragon` da tsuntsu da kifi da ganga da furanni a kan tufafinsu.Sifofin da suke dinka suna da kyan gani kwarai da gaske.

A cikinsu,sifofi biyu sun fi yin suna,daya daga cikinsu shi ne `wani mutum ya hau kan bayan dragon`,wata daban ita ce `wani mutum ya hau kan bayan sa`,sifofin nan biyu sun nuna mana cewa,mutanen kabilar Miao suna da jarumtaka kuma suna da karfin zuciya.A cikin sifofin da mutanen kabilar Miao suke dinka,siffar dragon ta fi yawa,dalilin da ya sa haka shi ne domin mutanen kabilar Miao sun nuna biyayya ga dragon,amma ba su ji tsoronsa ba.(Jamila)

Zanen da aka rina da launin shudi na kasar Sin

A kudancin kasar Sin,zanen da aka rina da launin shudi ya taba yaduwa sosai,manoman wuraren kudancin kasar Sin sun saka zanen da hannu,daga baya,sun yi amfani da ciyawar `landian` wato wani irin abun rini mai launin shudi domin yin rini,launin da aka rina yana da haske kuma yana da kyan gani.Ana iya yin amfani da su a fannoni daban daban kamarsu zanen gado da zanen tufafi da zanen jaka da zanen rufe kofa da sauransu.

A cikin zaman rayuwar yau da kullum na `yan matan kauyukan kudancin kasar Sin,su kan daura tufafin zanen shudi,irin wadannan tufafi tufafin gargajiya ne nasu.

A halin da ake ciki yanzu,samari da abokanmu na kasashen waje da yawan gaske suna kaunar irin wannan zanen da aka rina da launin shudi kwarai da gaske,su kan dinka tufafi ko yin kwaskwarima a cikin gidajensu da irin wannan zane.(Jamila)

Zanen da ake daura a gaban ciki

A kasar Sin,akwai wani irin zanen da ake daurawa a gaban ciki ko a gaban kirji,irin wannan zane wani irin tufa ne da mutanen kasar Sin suke daurawa a ciki domin kare kirji da ciki,yana da siffa mai kusurwa hudu.

Mutane su kan manna ko dinka furanni a kan zane,sun fi son zanen da aka rina da launin shudi domin dinka irin wannan karamar tufa.sifofin da aka buga ko dinka a kan zanen suna hade da su:`haihuwar yara da yawa` da `samun isashen abinci da sutura a kowace shekara` da sauransu.Mutanen kasar Sin sun fi son dinka furanni a kan zanen,dalilin da ya sa haka shi ne domin gujewa haramtattun abubuwa.Launin yawancin zanen shi ne launin ja da kore da rawaya.(Jamila)

Makullin dogon rai da ake daurawa a wuya na kasar Sin

Tun tuni,yaran kabilar Han ta kasar Sin su kan daura irin wani makulli a wuyansu,dalilin da ya sa haka shi ne don nuna fatan alheri na `ranka ya dade`.Makullin yana hade da wani dutsen wuya da ake yi da azurfa da wani makullin azurfa,idan jariri ya kai cikon wata da haihuwa,iyalansa su kan daura makullin azurfa a kan wuyansa,dole ne jariri ya daura wannan makulli kafin aurensa.

A da,saboda matsayin likitanci ya yi kasa kasa kuma sharadin tattalin arziki ba shi da kyau,yara da yawan gaske sun mutu bayan haihuwa,shi ya sa iyalansu su kan nuna fatan alheri domin lafiyar yaransu.Mutane su kan saka hoton `ranka ya dade` a kan makullin azurfa.

Ban da wannan kuma,makullin azurfa irin wannan kayan kwaskwarima ne,hoton da aka saka a kan makullin azurfa yana da sifofi daban daban,dukkansu suna da ban sha`awa.(Jamila)

Tufafin kabilar Bai ta kasar Sin

A lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin,akwai kananan kabilu fiye da 20,dukkansu sun kware da fasahar saka da kuma dinki,suna iya rini ko saka ko dinki ko manna sifofi daban daban a kan zane,dukkan sifofin da suka samu suna da kyan gani kwarai da gaske.Fasahar saka da dinki ta lardin Yunnan na kasar Sin tana da dogon tarihi har ya kai wajen shekaru dubu 2 ko 3,ya zuwa yanzu,fasahar saka da dinki ta yadu sosai.

A Dali na lardin Yunnan,mutane sun fi son saka da dinka furanni a kan zane,alal misali,gyalen da aka daura a kai da gyalen da ake daura a kugu da gyalen dake kan hula da zanen takalma da dai sauransu.Wanda a ciki,tufafin budurwa na kabilar Bai sun fi kyan gani wato sun fi jawo hankulan mutane.(Jamila)

Kayan zane da aka saka a cikin takalmi

Bisa al`adun gargajiyar kasar Sin,jama`ar kasar su kan saka wasu hotuna a kan tufa ko hula ko takalmi don nuna fatan alheri.

Alal misali,kayan zane da aka saka a cikin takalmi,tsohuwa ta kan saka zane mai siffar kafa domin matar danta,wato bayan danta da matarsa sun daura aure,tsohuwa ta kan saka wasu hotuna kamarsu `ya`yan itatuwa a kan wani zane mai siffar kasa,daga baya ta bai wa matar danta wannan kyauta,tana fatan matar danta za ta haifi yara da yawa kuma cikin sauri.

Tufar da aka dinka da kananan zannuwa da yawa

A kasar Sin,tufar da aka dinga da kananan zannuwa da yawa domin yara su sa ita ce daya daga cikin tufafin gargajiya,ma`anarta ita ce iyayen yara suna fatan yaransu za su girma lami lafiya.

Idan ana so a dinka tufa da kananan zannuwa da yawa,sai dole ne ta tafi iyalai da yawa domin neman samun kananan zannuwa,sa`an nan kuma ana iya dinga wata tufa da kananan zannuwa waje dari daya,tufar da aka dinka da kananan zannuwa da yawa tana da launuka da yawa,shi ya sa tana da kyan gani kwarai da gaske.

Irin wannan tufa ta yi ta yaduwa sosai a lardin Shaanxi da lardin Shanxi da lardin Gansu da lardin Henan da lardin Hebei da lardin Shandong da sauransu,a wasu wurare na kudancin kasar Sin kuwa,ita ma ta yi yaduwa kamar yadda ta yi a wuraren dake arewacin kasar Sin.

Karamar jaka da aka dinka da zane

A zamanin da,mutanen kasar Sin su kan sa karamar jaka da aka dinka da zane don ajiye kananan kayayyaki,irin wannan jaka tana da sifofi iri daban daban,dukkansu suna da kyan gani sosai,mutane su kan daura irin wannan jaka a kugu.

Hotunan da aka saka a kan kananan jaka suna da yawan gaske,alal misali furanni da tsuntsaye da dabbobi da ciyayi da duwatsu da ruwa da kuma kalmomi masu nuna fatan alheri da sauransu,ana mayar da irin wannan jaka a matsayin kayan kwaskwarima ne.

Dalilin da ya sa ake daura karamar jaka da aka dinka da zane a kugu shi ne don nuna fatan alheri,ban da wannan kuma ana iya ajiye kananan kayayyaki a ciki.

>>[Mutum Mutum]

Gumakan dake cikin tatsuniyoyin kasar Sin (1)

A da,mutanen kasar Sin suna da al`adar haka kogin kewayen gari,makasudin wannan shi ne domin tsaron lafiyar mazaunan garin,ban da wannan kuma ana bukatar karewar ubangiji,daga nan ubangiji mai kare gari ya bullo.Bisa littafin tarihin da aka rubuta,an ce,ubangiji mai kare gari ya bullo daga ubangijin ruwa dake cikin kogin kewayen gari da aka haka,dakin ibada na ubangijin kare gari na farko na kasar Sin shi ne dakin ibada na ubangiji na Wuhu da aka gina a shekara ta 239 a gabashin kasar Sin.

Sarki na farko na daular Ming wadda ta fara daga shekara ta 1368 kuma ta gama a shekara ta 1644 Zhu Yuanzhang ya taba nada ubangijin kare gari da ya zama wani babban jami`i.Ubangijin kare gari yana shugabancin dukkan fatalwoyi,shi ya sa akwai fatalwoyi da yawa dake kusa da shi.Mutanen kasar Sin su kan yi wani mutum mutumin ubangijin kare gari domin yin yawo a kan tituna,kowace shekara,mutane su kan daga mutum mutumin ubangijin kare gari domin yin yawo a kan tituna sau uku wato a lokacin bazara da lokacin kaka da lokacin sanyi,wannan gaggarumin biki ne da aka shirya tare da sauran ayyukan al`adun gargajiyar kasar Sin.

Gumakan dake cikin tatsuniyoyin kasar Sin (2)

A cikin addinin Buddah,akwai sarakuna hudu,amma a cikin addinin Taoism na kasar Sin,shi ma akwai kwamandoji hudu.

Wadannan kwamandoji hudu suna hade da:Ma Tianjun da Zhao Gongming da Guan Yu da Wen Qiong.Launin jikin Ma Tianjun fari ne,na Zhao Gongming baki ne,na Guan Yu ja ne,na Wen Qiong shudi ne.Dukkansu suna iya gujewa haramtattun abubuwa.Jama`ar kasar Sin suna nuna musu biyayya sosai.

Gumakan dake cikin tatsuniyoyin kasar Sin (3)

A kasar Sin,mutane sun fi nuna biyayya ga ubangijin sana`o`i,a cikin gidajen kwana da dakunan kera kayayyaki da kantuna,ko da yaushe mutane kan lika hotunan ubangijin sana`o`i a kan bango,wasu kuma sun nuna biyayya ga ubangijin sarakunan magani domin gujewa cututuka da bala`o`i.Sarakunan magani kakannin-kakannin sana`ar likitanci ne,suna hade da: malam Sun Ximiao da malam Bian Que da malam Hua Tuo da malam Pi Tong da malam Lu Dongbin da malam Baoshengdadi da malam Li Shizhen da sauransu,dukkansu shahararrun likitoci na zamanin da na kasar Sin.Ban da wannan kuma,an mayar Wei Cizang da Wei Gudao da Wei Shanjun da sauransu a matsayin sarakunan magani.

Gumakan dake cikin tatsuniyoyin kasar Sin (4)

A lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin,kananan kabilu da yawa suna zama a nan,ubangijin da suke nuna biyayya sun sha banban da na sauran wurare,musamman a shiyyar da mutanen kabilar Bai ke zama.

A Dali wato wurin da mutanen kabilar Bai ke zama,mutanen kabilar Bai sun fi nuna biyayya ga ubangijin wuta,suna mayar da ubangijin wuta a matsayin sarkinsu,hoton ubangijin wuta da aka zana ya yi kama da sarki,mutanen kabilar Bai su kan kiransa da sunan `babban sarkin dragon wuta`.

Gumakan dake cikin tatsuniyoyin kasar Sin (5)

A cikin al`adar kasar Sin,ubangijin kasa ya fi samun maraba daga wajen jama`a.Tun daga daular Ming wadda ta fara daga shekara ta 1368 kuma ta gama a shekara ta 1644,dakunan ibada na ubangijin kasa sun kara karuwa,mutane sun kuma kiran ubangijin kasa da sunaye da yawa.Fuskar ubangijin kasa fari ce,gemunsa baki ne,a kullum ya yi murmushi.

Gumakan dake cikin tatsuniyoyin kasar Sin (6)

A cikin addinin Buddah,akwai gumaka hudu,gunki Guanshiyin daya ne daga cikinsu.Bayan addinin Buddah ya shiga kasar Sin,gunki Guanshiyin ya fi samun biyayya daga wajen jama`ar kasar Sin.Ya zuwa daular Tang ta kasar Sin wadda ta fara daga shekara ta 618 kuma ta gama a shekara ta 907,saboda sunan sarkin daular Tang Li Shimin,shi ya sa an hana a kiran gunkin da sunan Guanshiyin,sai an kiransa da sunan Guanyin.

Bisa addinin Buddah,ba wadda ta haifi ubangiji ba kuma gunkin ba zai mutu ba,kuma ba a san su mace ko namiji ba ne,suna iya sauyawa sifofinsu bisa bukatun mutane.Tun daga daular Tang ta kasar Sin,ana mayar da gunki Guanshiyin a matsayin abin bauta `yar mata,ana ganin cewa,ubangijin Guanyin tana iya gujewa haramtattun abubuwa kuma tana iya taimakawa mutane su haifi yara da yawa,saboda haka `yan mata da yawan gaske na kasar Sin suna nuna biyayya sosai ga ta.(Jamila)

Mutum mutumin da aka yi da takarda na gundumar Cao ta kasar Sin

Mutum mutumin da aka yi da takarda na gundumar Cao ta lardin Shandong na kasar Sin ya fi shahara a kasar Sin.

(Hoton Mutum mutumin da aka yi da takarda)

Zhang Fei jarumi ne dake cikin shaharariyar tatsuniyar kasar Sin wato `labarai game da kasashe uku`.Da farko dai,a yi mutum mutumin da takarda da hannu,sa`an nan kuma a zana fuska da launi daban daban,a cikin hoton,fusktarsa ta yi fushe kwarai da gaske,ya dauki wata bindigar itace a hannunsa,siffarsa tana da ban sha`awa,ana iya gane cewa fasahar yinsa tana da wahala.

Lu Zhishen shi ma jarumi ne dake cikin shahararriyar tatsuniyar kasar Sin wadda ke da lakabin haka `labarai game da jarumai`,ya ceci abokinsa Lin Chong daga hannun miyagun mutane wato Dong Chao da Xue Ba a YanZhulin wato wani wuri inda ba wanda ya je.Lu Zhishen ya buge su da sanda har su fadi.daga baya,ya tafi da abokinsa Lin Chong.(Jamila)

Fasahar yin sifofin abubuwa da takarda ta kasar Sin

A kasar Sin,a gun bikin jana`iza,mutane suna son su sallame mutanen da suka mutu tare da wasu kayayyaki kamarsu kayayyakin amfanin yau da kullum,shi ya sa aka yanke sifofin wadannan kayayyaki da takarda,sa`an nan kuma an lika su,da karshe dai,an binne su tare da akwatin gawa,daga nan fasahar yin sifofin abubuwa da takarda ta bullo a kasar Sin.

Ire-iren sifofin abubuwan da aka yi da takarda sun hada da : jikin gunki da mutum mutumin takarda kamarsu yara da gine-gine da motoci da abin daukar abinci da abinci da sauransu.Fasahar nan tana da wahala.(Jamila)

Dokin takarda mai ajiye kudi

Dokin takarda hoto ne da aka manna daga katarkon da aka saka a kan takarda,mutane su kan kara zana wasu sifofi a kan takarda da launin ja da kore,wannan ya sa dokin takarda ya kara kyan gani.

A lardin Zhejiang da lardin Jiangsu dake kudu maso gabashin kasar Sin,`yan fasaha sun fi mai da hankali kan aikin zane,musamman sifofin dodanni,sun fi jawo hankalin mutane.

A cikin hoton taya murnar sabuwar shekara na jama`ar kasar Sin,dokin takarda na da ma`anar ajiye kudi,siffar mutumin da aka zana ta yi kama da ta dodon kudi,ya sa hular jami`i,kuma ya daura manyan tufafin jami`i mai launin ja,akwai kudi da yawa a kusa da shi.(Jamila)

Wasan da ake yi a kan kasa na kasar Sin

Wasan da ake yi a kan kasa na kasar Sin ya yadu sosai a wurare da yawa na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin,musamman na shiyyar Anshun.Yayin da ake murnar bikin sallar bazara ko kafin bikin sallar wasan fitilu wato kafin ran 15 ga watan Janairu na kalandar gargajiyar kasar Sin,a kauyuka,ko ina ana iya ganin `yan fasaha manoma suna yin wasa a kan kasa.Makasudin yin wasan kasa shi ne domin gujewa haramtattun abubuwa da bala`o`i da kuma nishadi.

(Hoto: Ana wasan)

`Yan wasan fasaha na wasan kasa su kan sa abu su rufe fuska yayin da suke rera wakoki,abun rufe fuska na wasan kasa ya hada da ire-ire har biyar.A kan hular dan wasan fasaha namiji,mutane su kan sa abu mai siffar dragon.A kan hular yar wasan fasaha mace,su kan sa abu mai siffar babban tsuntsu da furanni.(Jamila)

Rawar gumaka

Rawar gumaka daya ce daga cikin bikin addini mafiya gaggarumi da ake yi a dakin ibada na addinin Budha na Tibet.An yi yawancin kayayyakin fuska ne da katako,wasu kuwa aka yi su ne da zane.Dalilin da ya sa aka sa kayayyakin fuska yayin da suke taka rawa shi ne domin suna so su nuna mana sifoffin gumaka da donanni iri daban daban dake cikin haramtattun addinai biyu wato `Yixiba` da `Jideba`.

Kayayyakin fuska na Tibet suna hade da iri uku,wato kayayyakin fuska na rawar gumaka da kayayyakin fuska da aka sa a kan kai da kayayyakin fuska na wasan Tibet.Irin wannan kayan fuska yana da ban tsoro saboda ana so a yi amfani da kan mutum ko zuciyar mutum ko jikin mutum wajen yin kwaskwarima.Ban da wannan kuma,kayayyakin fuska su kan muna mana abubuwa game da addini,shi ya sa dole ne a yi amfani da su cikin dakin abada,in ba haka ba,to,da kyar ana iya gane ma`anarsu.

>>[Kayayyakin Gida]

Tangaram na kasar Sin (1)

A tarihin kasar Sin,shiyyar Zibo ta lardin Shandong dake gabashin kasar Sin ta fi suna da tangaram wato kayayyakin fadi ka mutu,ana iya kiransa da sunan `china`.Jama`a da yawan gaske suna yin tangaram da kansu..

Siffar kifi batu mafi samun maraba ce yayin da ake yin tangaram,a cikin yaren Han,ma`anar kifi wadatuwa ce.Farantin tangaram da aka zana siffar kifi a kansa yana da kyan gani kwarai da gaske,`yan fasaha su kan zana siffar kifi kan faranti da hannu.

Launin siffar kifin da aka zana ja ne,yana da kyan gani.

Tangaram na kasar Sin (2)

A zamanin da,mutanen kasar Sin su kan yi amfani da matashin kai da aka yi da tangaram a lokacin zafi.Ya zuwa daular Tang da daular Song na kasar Sin,matashin kai na tangaram suna da iri daban daban,launinsa shi ma yana iri daban daban,dukkansu suna da kyan gani.Alal misali,matashin kai na tangaram mai siffar kyanwa,irin wannan matashin kai yana da ban sha`awa,ana iya ganinsu a lardin Hebei da lardin shandong dake arewacin kasar Sin.

Tangaram na kasar Sin (3)

A lardin Anhui dake tsakiyar kasar Sin,tukwanen Jieshou ya fi yin suna,fasaharsa tana da wahala.An zana sifofin mutane biyu kan tukwane mai launin fari,irin wannan siffa ta yi kama da siffar da aka saka kan dutse.Siffar tukwanen tana da ban sha`awa kuma tana da kyan gani.

Tangaram na kasar Sin (4)

A daular Yuan ta kasar Sin wadda ta fara daga shekara ta 1206 kuma ta gama a shekara ta 1368,tangaram iri na Qinghua ya yadu sosai a duk fadin kasar Sin,ko ina akwai dakin yin tangaram na Qinghua a kasar Sin,na farar hula da na hukuma.

Dakunan yin tangaram na Qinghua na farar hula sun fi na hukuma yawa.kayayyakin da aka yi suna iri daban daban.Manyan jami`ai da masu kudi sun yi amfani da kayayyaki masu kyau,jama`a sun yi amfani da kayayyaki marasa kyau.

Sifofin da aka zana kan tangaram na Qinghua sun kasance da iri daban daban,alal misali,sifofin mutane da na dabbobi da tsuntsaye da furanni da `ya`yan itatuwa da kalmomi da sauransu.

Tangaram na kasar Sin (5)

Sha`anin tangaram da tukwane na lardin Shandong dake gabashin kasar Sin yana da dogon tarihi,musamman na shiyyar Zibo.Kayayyakin tukwane na farar hula suna da sifofi iri daban daban,ana iya yin amfani da su wajen daukar ruwa da abinci da sauransu.Alal misali,kodayeke fasahar yin tukwane mai daukar ruwa ba ta da wahala,kuma yana da araha,amma yana da amfanin hakika,kuma yana da kyan gani.

Tangaram na kasar Sin (6)

Tangaram mai daukan ruwan shayi na Qinghua ya nuna mana halin jama`a na kasar Sin sosai.Akwai hanci hudu a kansa,bakinsa yana da ban sha`awa,hoton dake kansa sifofin yara ne,yana da farin jiki.

Tangaram na kasar Sin (7)

`Yan fasaha su kan sa irin wani mai a kan fuskar tangaram,wannan ya sa kayan tangaram ya kara kauri.kuma ya kara kyan gani,ban da wannan kuma,da sauki ake wanke shi.

Tangaram na kasar Sin (8)

A tarihin kasar Sin,kayayyakin fadi ka mutu da yawan gaske sun zama kayayyakin fasaha wadanda suka yi suna a duk fadin duniya.Alal misali,tun daga daular Song da daular Yuan har zuwa daular Ming da daular Qing na kasar Sin,mutanen kasar Sin sun fi son su yi amfani tukwane na Yuhuchun da aka yi a birnin Cizhou na lardin Hebei wajen daukan giya.

Siffar irin wadannan tukwane na da kyan gani kwarai da gaske,kuma ya dace da daukan giya,ba kwaskwarima ko kadan a kansa.

Tangaram na kasar Sin (9)

A zamanin Shang ta kasar Sin wadda ta fara daga shekara ta 1600 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam kuma ta gama a shekara ta 1046 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam,mutane sun fi son kayayyakin tagulla a cikin zaman rayuwar yau da kullum.Wanda a ciki siffar dragon ta fi samun maraba.A daular Yuan da daular Ming da daular Qing ta kasar Sin,farantin tangaram da aka zana siffar dragon a kansa ya fi yawa.

Farantin tangaram da aka zana siffar dragon a kansa shi fari ne,a cikin farantin,an zana siffar dragon guda daya,a kusa da shi,an zana dragon guda biyu,a kusa da dragon nan uku,an zana furanni da yawa.(Jamila)

Gidajen kwanan da aka gina da kasa na kudancin kasar Sin

Gidajen kwanan da aka gina da kasa gidajen kwanan da aka gina bangayensu da kasa,mutanen kauyukan Kejia na lardin Fujian dake kudu maso yammacin kasar Sin sun fi son irin wannan gini,shi ya sa ana kiransa da sunan `ginin kasa na Kejia`.

Ginin kasa na gargajiyar kasar Sin yana da ire ire daban daban.Wanda a ciki kewayayyen gini ya fi yawa,dalilin da ya sa haka shi ne domin mutanen Kejia sun gina irin wannan gini domin tsaron kansu,kuma sun gina gini da benaye uku,a cikinsa,ko shakka babu an haka rijiya,kuma akwai babbar kofa daya kawai,ana fita da kuma shiga daga nan.A bene na farko,an dafa abinci kuma an ci abinci,babu tagogi;a bene na biyu,an ajiye hatsi da kayayyakin yau da kullum,shi ma babu tagogi;bene na uku dakin kwana ne,akwai tagogi.

Fasahar gina bangunan ginin kasa tana da wahala,shi ya sa irin wannan gini yana da kyau wato yana da lafiya.Mutane da yawa suna zaman tare cikin ginin kasa suna jin dadinsu.(Jamila)

Kayan da aka sa kwanon wanke fuska na gargajiyar kasar Sin

Kayayyakin daki da aka yi da katako na kasar Sin suna nan iri-iri da yawa,kayan da aka yi da katako don sa kwanon fuska a kansa yana da kafaffu uku ko hudu ko biyar,ba ma kawai ana iya sa kwanon wanke fuska a kansa ba,har ma ana iya sa tawul da kayan ajiye sabulu da kuma madubi a kansa.

Kayan da aka sa kwanon wanke fuska a kansa shi ne daya daga cikin kayayyakin fasaha na gargajiyar kasar Sin,`yan fasaha su kan saka hotuna masu kyan gani a kan katako don nuna fatan alheri.

Akwatin ajiye tufafi na gargajiyar kasar Sin

A cikin kayayyakin daki na gargajiyar kasar Sin,akwatunan ajiye tufafi suna da sifofi daban daban,a cikin babban akwati,mutane su kan ajiye kananan akwatuna kamar aljihun tebur a ciki don ajiye kananan kayayyaki.

Kamar yadda jama`ar kasar Sin suka yi a da,su kan saka hotuna masu ma`ana masu kyau a kan katako na akwatin ajiye tufafi.

Kwandon ajiye kifi

A wuraren dake bakin koguna na kudancin kasar Sin,mutane su kan yi kwandon ajiye kifi da gora da hannu,siffarsa ta yi kama da kwalaba,masu kama kifi su kan daura kwandon ajiye kifi a kugunsu.A hakika dai,kwandon ajiye kifi shi ne kayan fasaha na gargajiyar kasar Sin.

Babban ginin iyalin Wang

A daular Ming da daular Qing wato daga shekara ta 1368 zuwa shekara ta 1911,`yan kasuwa masu dukiya na lardin Shanxi dake arewacin kasar Sin sun yi kwazo da himma don gina babban gini,daga nan aka gina manyan gine-gine da yawa a lardin Shanxi.

Gini wanda ya fi yin suna a kasar Sin shi ne babban ginin iyalin Wang na gundumar Lingshi dake tsakiyar lardin Shanxi.

Gaba daya fadin babban ginin iyalin Wang ya kai muraba`in mita dubu goma,aka gina shi ne a kan duwatsu,tsarin babban ginin nan yana da rikitarwa,mutane su zauna a cikin dakunan da suka dace wato dakunan da aka gina musamman dominsu,alal misali,maza da mata da yara sun yi zaman rayuwa a cikin dakuna daban daban.

Kyanwa da aka yi da yumbu

A kullum,jama`ar kasar Sin suna mai da hankali sosai kan aikin yin ado a kan gininsu,bayan daular Han wato bayan shekara ta 220,mutanen kasar Sin su kan sa kaya mai siffar kifi da aka yi a yumbu a kan gini,ma`anar wannan ita ce don kashe gobara.

Ban da wannan kuma jama`ar kasar Sin su kan sa kyanwa da aka yi da yumbu a kan gini,kyanwa da aka yi ta kan bude bakinta,kanta na da girma,jikinta kuma karami ne,ana fatan kyanwar nan za ta yi maganin aukuwar masifa.

Kaya mai siffar abinci da aka yi don dafa abinci

Tun daga daular Ming da daular Qing wato daga karni na 14 zuwa karni na 19,abincin gargajiyar kasar Sin da aka dafa da masara suna kara karuwa a kwana a tashi,kaya mai siffar abinci da aka yi don dafa abinci shi ma ya karu,musamman ma kaya mai siffar wainar wata ta sallar tsakiyar kaka.

Mutanen kasar Sin sun fi son ma`anar `fatan alheri` da ta `ranka ya dade`,shi ya sa su kan yi kaya irin wannan don daga waina.Musamman a shiyyar Jiaodong ta lardin Shandong dake gabashin kasar Sin,kusan kowane iyali yana da irin wannan kaya.

Babban ginin iyalin Qiao na lardin Shanxi na kasar Sin

Lardin shanxi na kasar Sin shi ne daya daga cikin mafarin al`adun gargajiyar kasar,wadanda suka fi yin suna suna hade da manyan gine-gine na gundumar Qi da ta Lingshi da ta Xiangfen.

Babban ginin iyalin Qiao yana kauyen iyalin Qiao na gundumar Qi dake tsakiyar lardin shanxi,an gina shi ne a daular Qing,daga baya an kara yin masa gyare-gyare,gaba daya.wannan babban gini yana kumshe da kananan gine-gine 19 da kananan dakuna fiye da daru uku,ya yi kama da wani lambun shan iska.

Kofar babban ginin nan tana da kyan gani kwarai da gaske,`yan fasaha sun saka hotuna da yawa a kanta.

Katangar Wu ta dakin ibadar Wen na gundumar Lingshi ta lardin Shanxi

A cikin gine-ginen gargajiyar kasar Sin,mutane su kan gina wata katanga tsakanin babbar kofa da dakuna.

Katangar Wu ta dakin ibadar Wen na kauyen Jingsheng na gundumar Lingshi ta lardin shanxi na kasar Sin ta yi shahara a duk fadin kasar Sin,aka saka dragon biyu a cibiyarta,tsayinta ya kai mitoci 7,fadinta ya kai fiye da mitoci 10.Dakin ibada na Wen na kauyen Jingsheng shi ne wata makaranta.

Kayan zana layi kan katako ta gargajiyar kasar Sin

A cikin sana`ar gargajiyar ta yin kayan katako ta kasar Sin,ma`aikata su kan yi amfani da kayan zana layi kan katako ta gargajiyar kasar Sin,wato ana yin amfani da layin baki wato a kan sa tawada a kan layi,daga baya kuma za a saka katako bisa layin nan da aka zana.

Irin wannan kaya yana da siffofi daban daban kamarsu siffar kifi da siffar dragon da siffar damisa da sauransu.

Gadon Luohan na kasar Sin

A kasar Sin,gado yana da dogon tarihi,jama`ar kasar Sin su kan yi gado da katako,amma wani lokaci su kan yi amfani da gora domin yin gado,alal misali gadon Luohan.

Tun daga daular Ming da daular Qing,mutanen kasar Sin sun fara gina katanga bisa gefuna uku na wani gado,gadon Luohan shi ma haka ne,an yi gadon Luohan da gora mai kyau,ana iya zama ko kwanciya a kansa,ana jin dadi kwarai da gaske saboda gadon Luohan yana da dogon tarihi.