logo

HAUSA

Babi17: Masu suna a tarihi

2020-10-30 10:07:57 CRI

Babi17:Masu suna a tarihi

[Sarkuna a Tarihi]

Qinshihuang sarkin kasa na farko da ya kafa dayantacciyar daula a kasar Sin.

"Qinshihuang" abin da ake nufi cikin Sinanci shi ne sarki da ya kafa daular Qin a kasar Sin, sunansa kuma shi ne Yingzheng. Ya zuwa karshen zamanin yakekeniya a kasar Sin wato tsakanin shekarar 403 zuwa ta 221 kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S.(B.C.), kasar Qin wadda ta fi sauran kananan kasashe kasaita, kuma ta sami karfin hadiye sauran kananan kasashi 6 da ke a gabashin kasar. Tun Qin Yingzhen ke karami, sai ya hau kan kujerar mulkin kasar, amma waziri Lu Buwei ke kula da harkokin mulki a madadinsa. Ya zuwa shekarar 238 kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S.(B.C.),ya kula da harkokin mulki da kansa, ya tube Lu Bewei daga mukaminsa na waziri, ya nada Wei Liao da Li Si da kuma sauran mutane. Tun daga shekarar 236 zuwa ta 221 kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S. (B.C.), ya hadiye kananan kasashe 6 kamar Han da Wei da Chu da Yan da Zhao da kuma Qi, wato ke nan ya kawo karshen zamanin yakekeniya a kasar Sin, ya kafa daular Qin, wato dayantacciyar daula mai yawan kabilu ta farko wadda ke rike da gwamnatin tsakiya mai wuka da nama a cikin tarihin kasar Sin.

A shekarar 221 kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S. (B.C.), Yingzheng ya dauki kansa bisa matsayin sarki na farko. Ya yi watsi da tsarin mulkin kananan kasashe masu zaman kansu a duk kasar Sin, maimakon haka ya gudanar da tsarin gundumomi da ke a karkashin mulkin sarkin kasar Sin kai tsaye, ya tsamo wasu dokokin kananan kasashe 6, ya kafa dokoki bai daya bisa tushen dokoki na tsohuwar kasar Qin, kuma ya bayar da su a fili. Ya yi kaurar da sarkuna da sauran manyan masu mulki da masu hannu da shuni zuwa Guanzhong da Bashu don hana su jawo baraka da sake hau kan mulki. Haka zalika ya bayar da umurni a fili don hana fararen hula su ajiye makamai, ya wargaza makamai da aka karba daga hannun fararen hula.

Game da harkokin tattalin arziki, Yingzheng ya aiwatar da manufar ba da muhimmanci ga aikin gona da ta dagule harkokin kasuwanci, ya ba da taimako wajen yalwata tsarin mallakar filaye masu zaman kansu. Ya bayar da umurni a shekarar 216 kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S. (B.C.) cewa, idan masu mallakar gonaki da manoma masu zaman kansu sun gabatar wa hukumomi fadin filaye da suke mallaka, kuma sun ba su haraji, to, hukumomi za su amince da ikonsu kan filayensu, su kare su. Ta haka dai ne aka kafa tsarin mallkar filaye irin na masu zaman kansu. Ya dauki ma'auni da wani mutum mai suna Shang Yang ya tsara a zamanin yakekeniya wato tsakanin shekarar 403 zuwa ta 221 kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S. (B.C.) bisa matsayin ma'auni bai daya a duk kasa. Ya kuma kafa tsarin kudi bai daya a duk kasa. Ya shimfida hanyoyi da suka hada da birnin Xianyang da wuraren Ye Qi da Wu Chu, da hanyoyi da suka hada birnin Xianyang da Yunyang da Jiuyuan, da hanyoyi a wuraren kudu maso yammancin kasar Sin, ya haka korama da ke tsakanin kogin Xiangjiang da na Lijiang don yalwata harkokin zirga-zirga da aka yi a kasa da ruwan koguna.

A fannin al'adu da na tunani, ya bayar da tsarin rubutu bai daya a duk kasar. Ya kuma kara aiwatar da dokar yanke hukuci mai tsanani. A shekarar 212 kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S.(B.C.), ya bayar da umurnin kone littattafai iri daban daban, ya rufe makarantu masu zaman kansu. Haka nan kuma ya kashe masanan ilmin Confucious da masu neman maganin mutuwa wadanda yawansu ya wuce arabamiya a sanadiyyar gudu da Hou Sheng da Lu Sheng suka yi yayin da suke nemo wa Qinshihuang maganin mutuwa. Wannan shi ne sanannen al'amari mai da ya auku a cikin tarihi dangane da kone littattafai da karkashe masanan ilmin Confucious.

Bayan da Qinshihunag ya hau kujerar mulki, ya aika da janar Meng Tian don ya ja ragamar sojoji wajen kai hare hare a kan kabila mai suna "Xiongnu", ya gina sabuwar ganuwa da ta hada da ganuwar da aka riga aka gina a arewancin kasashe uku kamar Qin da Zhao da Yan, don ta zama babbar ganawa da ta tashi daga Lintao a yamma zuwa Liaodong a yamma. An sami taimako daga wajen babbar ganuwa don tsaron kai daga wajen 'yan kabilar Xiongnu masu dadin hannun kibau wadanda suka kware wajen hawan dawaki. Ta haka an kara karfafa mulkin daular Qin, kuma an tabbatar da zaman karko a wurare da ke kan bakin iyakar kasa. Bayan da aka cinye yankin Baiyue, an kafa gundumar Guilin da Xiangjun da Nanhai da sauransu. Ya zuwa karshen zamanin daular Qin, yawan gundumomin nan da aka kafa tun can farko ya karu ya zarce 40.

Bayan da Qinshihunag ya dinke kananan kasashe 6 gu daya, ya gina kyakkyawar fada mai suna Afanggong da kabarin Lishan mai kayatarwa, ya yi babban rangadi daya bayan daya har sau biyar, a duk inda ya sa kafa ya nemi da a sassaka duwatsu, ya nemi ganin mala'ika. Ya aika da malam Xufu, mai neman maganin mutuwa ya ja ragamar yara maza da mata dubbai zuwa tsirirori da ke gabashin teku don neman maganin mutuwa. Ta haka dai ne ya yi almubazarancin makudan kudade da mutane masu yawa, ya jawo wa jama'a tulin wahalhalu. Qinshihunag ya rasu ne bayan da ya yi fama da ciwo a watan Yuli na shekarar 210 kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S.(B.C.) (Halilu)

Liu Bang

Liu Bang sarkin kasar Sin ne da ya kafa daular Xi Han (tsakanin shekarar 206 zuwa ta 220 kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S.(B.C.) Haka kuma yana daya daga cikin sarakunan kasar da suka fito daga iyalan farar hula a cikin tarihin kasar Sin.

An haifi Liu Bang ne a iyalin manomi. A lokacin samartakarsa, ya taba zama wani karamin jami'in daular Qin. Shi mutum ne mai karamci da sanin aiki. A shekarar 209, kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S.(B.C.) Liu Bang ya shriya mutane a kauyensa don ba da taimako ga bore da Chen Sheng da Wu Guang, jagoran rundunar sojoji manoma suka tayar. Daga baya dai, Liu Bang ya ja ramagar sojoji masu dimbin yawa da suka tinkari birnin Xianyang, hedkwatar kasar Qin, sun hambarar da mulkin daular Qin. Bayan da Liu Bang ya soke dokoki masu tsanani na daular Qin a hedkwatar kasar, ya tsaida ka'idoji tare da dattijai na Guanzhong cewa, a kashe duk wanda ya yi wa saura kisan gilla, a yanke hukunci a kan duk wadanda suka raunana saura ko yin satar abubuwa. Sabo da haka ya sami karbuwa sosai daga wajen jama'arsa.

Daga nan dai Liu Bang ya shafe shekaru 4 yana yake da ake kira Chuhan a tsakaninsa da Xiang Yu wanda shi ma ya ja ramagar sojojji masu dimbin yawa wajen yin adawa da daular Qin. A shekarar 202 kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S.(B.C.), sojojin Liu Bang wadanda yawansu ya kai dubu 300 sun yi kofar rago ga Xiang Yu kwarai, da ganin haka, sai Xiang Yu ya kashe kansa, wato ke nan Liu Bang ya ci nasara, kuma ya kafa daularsa a Shandong a shekarar 202, kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S.(B.C.), sunan kasarsa shi ne Han.

Liu Bang ya kware sosai wajen daukar mutane aiki. Ya sha tsira ransa daga hadarurruka da ya gamu a lokaci mai muhimmanci. SaukarLiu Bang a Hanzhong ke da wuya, sai wasu daga cikin rundunar sojojinsa sun yi ta gudu daga aikin soja, wani karamin hafsa mai suna Han Xin shi ma ya gudu. Bayan da Xiao He ya sami labarin gudansa, sai ya sanar da Liu Bang, sa'an nan kuma ya tada korensa. Da ya kama shi, sai ya gabatar da shi ga Liu Bang. A wancan lokaci, ko da yake Han Xin wani karamin hafsa ne da ba a san shi sosai ba, amma duk da haka Liu Bang ya amince da shawarar da Xiao He ya gabatar masa, ya nada Han Xin don ya zama babban janar. Daga bisani, ashe, Han Xin ya yi aikin bajinta wajen ba da babban taimako ga Liu Bang don mayar da mulkin kasa cikin hannu.

Babban hadari da ya auku yayin da Liu Bang ke kokarin kwatar mulkin kasa shi ne walima da ake kira Hongmenyan cikin Sinanci. A wancan lokaci, sojojin Xiang Yu sun fi na Liu Bang karfi, yana so ya kashe Liu Bang ta yadda zai hau kan kujerar mulkin kasa, da Liu Bang ya sami wannan labari, amma shi da mashawarcinsa Zhang Liang sun je wurin Xiang Yu, sun halarci walimar Hongmenyan da aka shirya don neman yin tuba a gabansa. Fan Zeng, mashawarcin Xiang Yu ya taba gabatar wa Xiang Yu shawara a kan yin amfani da damar da suka samu a gun walimar don kashe Liu Bang. A lokacin walimar, bisa sanaddiyar surutun baki na wai don taya wa juna murnar walima, Xiang Zhuang, babban janar na Xiang Yu ya yi wasan takobi yana neman damar kashe Liu Bang. Da ganin irin wannan hali mai hadari da suke ciki, sai Zhang Liang ya kirawo Fan Kuai, dan gadin Liu Bang cikin hanzari don ya kare Liu Bang. Jin kadan da aka yi haka, sai cewar da Liu Bang ya yi, wai zai yi bayan gida, da ya tashi daga wajen walimar, sai ya bi hanyar baya, ya koma gida duk a karkashin garkuwar dan gadinsa Fan Kuai. Bayan haka Zhang Liang ya koma cikin tantin da aka shirya walimar, ya bai wa Xiang Yu kyauta, ya yi ban kwana da shi, kuma ya ce, Liu Bang ya riga ya tashi. Wannan shahararren labari ne mai suna Hongmenyan da ya auku a cikin tarihin kasar Sin. Bayan da Liu Bang ya tsira, sai ya yi kokari sosai ya kafa wata rundunar sojojinsa mai kasaita, daga baya dai ya cinye Xiang Yu, ya kafa daular Xihan.

Bayan da Liu Bang ya hau kan kujerar mulkin kasa, ya dauki matakai da yawa wajen farfafo da aikin samar da kayayyaki da yalwata shi. Da ganin yawan mutanensa ya ragu sosai sabo da yake-yake da ya yi ta yi har cikin shekaru da yawa da suka wuce, sai ya nuna afuwa ga masu laifuffuka na duk kasar, ya saki bayi, ya komar da sojojinsa gida. Haka nan kuma ya rage ayyuka masu nauyi da aka yi wa jama'a, ya ci gaba da aiwatar da tsarin ba da kyautar gonaki da na gidaje ga sojoji da suka yi aikin bajinta daidai kamar yadda aka yi a zamanin daular Qin.

Bayan da aka hambarar da daular Qin, 'yan karamar kabila mai suna Xiongnu da ke zaune a arewacin kasar Sin ya sami damar tinkarar kudancin kasar. A farkon zamanin daular Han, 'yan kabilar Xiongnu sun yi ta kai hare-hare a kan wurare da ke kan bakin iyakar kasar Han. A shekarar 200 kafin bayyanuwar Annabi isa A.S.(B.C.), Liu Bang ya ja ragamar sojojinsa ya yi yaki da 'yan kabilar Xiongnu. A lokacin yakin, sojoji mahaya dawakai sama da dubu 300 sun yi wa Liu Bang kawanya har cikin wani mako a wani wuri mai suna Baideng wanda yanzu yake a arewa maso gabashin birnin Datong na lardin Shanxi na kasar Sin. Bayan da Liu Bang ya tsira daga hadarin nan, ya ga tilashi ne ya aiwatar da manufar zaman jituwa tare da 'yan kabilar Xiongnu, ya bude iyakar kasa da ke tsakanin kasar Han da ta Xiongnu don sassauta huldar da ke tsakanin bangarorin nan biyu.

A lokacin da Liu Bang yake saurayi, ya kan yi abubuwa yadda ya ga dama, ya nuna reni ga mabiyan Confucious. Bayan da ya zama sarkin kasar, yana ganin cewa ya hau kan kujerar mulkin kasa ne ta hanyar hawan dawaki wato yake-yake, sabili da haka 'wakoki' da 'littattafai' gaba daya ba su da amfani gare shi. Amma da bafadansa Lu Jia ya bayyana masa cewa, kai mai martaba ka hau kan kujerar mulki ne ta hanyar hawan dawaki, ko za ka iya gudanar da harkokin mulkinka ta hanyar hawan dawaki ? Da jin haka sai kansa ya waye, ya ba da umurni ga Lu Jia da ya rubuta littafi a kan yadda aka hambarar da daular Qin don tsamo darussa daga wannan lamari. Bayan shekara 12 da ya kafa daularsa, wato yayin da Liu Bang yake murkushe tashin hankali da 'yan tawaye na Yingbu suka tayar, ya sha kabiya da aka yi masa, bayan haka ya rasa ransa bayan da ya yi fama da ciwo mai tsanani. (Halilu)

Da Yu

Yau shekaru 4000 ke nan da suka wuce, Da Yu ya ba da babban taimako wajen kawar da bala'in ambaliyar ruwa daga wuraren da ke gabobin Kogin Yangtze, sabili da haka ya sami kwarjini sosai daga wajen jama'a, har wa yau ya maye gurbin Shun, jagoran kabilar Huaxia ya zama sarkin kasa. Labarin Da Yu kan kawar da ambaliyar ruwa yana ta barbazuwa daga zuriya zuwa zuriya.

Bisa labarin da aka samu daga mutanen zamanin da, an ce, a lokacin da sarki Yao ke kan kujerar mulkin kasa, ambaliyar ruwa ta salwantar da amfanin gona da gidaje, fararen hula suna ga tilas ne su yi kaura zuwa wuraren da ke tuddai. Da ganin haka, Yao ya kira taro don yin tattaunawa ga batun kawar da ambaliyar ruwa, jagoran kabilu daban daban gaba daya suka gabatar da Gun, baban Da Yu don ya kawar da ambaliyar ruwa.

Ko da yake Gun ya shafe shekaru 9 yana yin ayyukan tsare ruwa don neman kawar da ambaliyar ruwa, amma ina, maimakon haka bala'in cikon ruwa ya kara tsanani. Dalilin da ya sa haka shi ne domin hanyar da yake bi wajen tsare ruwa ba daidai ba ce.

Da ganin haka, sarki Shun wanda ya ci gadon sarautar Yao ya kashe Gun, sa'an nan kuma ya nemi dansa Yu da ya kawar da ambaliyar ruwa.

Yu ya canja hanyar da babansa ya taba bi wajen neman kawar da ambaliyar ruwa, ya haka maduganan ruwa, ya yashi koguna ta yadda za a jawo ambaliyar ruwa da ta malala cikin teku. Ya yi aiki tare da jama'a, ya shiga gaban kowa, ya haka kasa da kuma yin jigilarta, ya yi aiki ya gaji kwarai. Ya kago kayayyakin auna da hanyoyin safiyo da yawa yayin da yake tsare ambaliyar ruwa.

Bisa kokarin da ya yi ta yi har cikin shekaru 13 da suka wuce, daga karshe dai an sami nasara wajen jawo ambaliyar ruwa da ta malala cikin teku, bayan haka manoma sun sake iya yin aikin noma a gonakinsu.

Bayan da Yu ya yi aure ba da dadewa ba, sai ya kan yi kai da komowa a tsakanin wurare da yawa don yin aikin tsare ruwa, ko da ya ke ya sha bi ta kofar gidansa, amma duk da haka bai shiga ciki ba. Wata rana, jin kadan bayan da matarsa madam Tu Shanshi ta haifi dansu mai suna Qi ke da wuya, sai Yu da ke wucewa ta wajen gidansa, ko da ya ji kukar dansa ma, tare da karfin zuciya ya ki shiga cikin gidansa.

Zuriyarsa sun kira Yu da sunan Dayu cikin girmamawa don nuna yabo ga aikin bajinta da ya yi wajen kawar da ambaliyar ruwa.

Haka zalika da ganin irin wannan aikin bajinta da Yu ya yi, sai jama'a suka zabe shi don ya zama jagoran kawancen kabilunsu bayan Shun.

Babban taimako da Dayu ya yi shi ne kawar da ambaliyar ruwa. Ko da yake a wancan zamani kabilu ba su hada kansu gu daya ba, amma da idon basira ya tsai da ka'idar tsare ruwa bai daya a duk kasa. Bisa labarin da aka samu daga bakin mutanen zamanin da, an ce, ya ba mataimakinsa Bo Yi da ya rubuta wani shahararren littafi da ake Shanhaijing cikin Sinanci, inda a karo na farko ne aka rubuta wasu abubuwa game da duwatsu da koguna da al'muran mutane da tsuntsaye a kasar Sin.

Bayan da Yu ya kammala aikinsa na kawar da ambaliyar ruwa, jama'a sun fara jin dadin zama da yin aikin yi ba tare da damuwa ba. Haka nan kuma bayan da ya zama jagaro, ya ci gaba da yin aiki wurjanjan, ya kokarta wajen gudanar da harkokin mulki, sabo da haka an shiga cikin wani sabon lokaci a karkashin mulkinsa.

Yayin da ake yin yakekeniya a tsakanin kabilu, an mayar da fursunonin yaki da aka kama don su zama bayi, wadannan bayi sun yi aiki domin sarkuna da sauran manyan masu mulki. Ta haka an fara samun ajujuwa biyu wato ajin bayi da ajin masarautan bayi a hankali a hankali.

Daga baya dai, sarkuna da sauran manyan masu mulki na kabilar Xia ta Yu sun nuna goyon bayansu ga danya Qi don ya ci gadon sarautar Yu. Ta haka an kawo karshen tsarin zabe da kawancen kabilu suka gudana a wancan zamni, sa'an nan kuma an fara gudanar da tsarin cin gadon sarauta.

Daular Xia wato daular tsarin bayi na farko ta bullo a cikin tarihin kasar Sin. (Halilu)

Yao da Shun

Yau sama da shekaru 4,000 da suka wuce, yayin da ake samun kabilar Xia ta zamanin da a kasar Sin a hankali a hankali, sai wasu mazajen duniya kamar su Yao da Shun da kuma Yu suka fito daga al'ummar kasar Sin daya bayan daya.

A cikin littafi mai suna "Shangshu" da wani littafi dabam mai suna "Shiji", an kira Yao da sunan "Fang Xun" ne. Haka nan kuma bisa labarin da aka samu daga bakin mutanen zamanin da, an ce, zuriyarsa suna kiransa da lakabinsa "Taotang", sunan iyalinsa kuwa shi ne Qi Shi, sabo da haka ainihin sunansa shi ne "Tang Yao".

An ce, Yao jikan Huang Di, kakanin-kakanin kabilar Hua Xia ne, shi mutum ne mai hazikanci, ya sami girmamawa sosai daga wajen jama'a. Yayin da shekarunsa suka kai 16 da haihuwa, sai aka zabe shi don ya zama jagoran kabila. Bisa abubuwa da aka rubuta a cikin littafin Shiji, an ce, Yao ya mayar da birnin Pingyang don ya zama hedkwatar kasarsa. Yanzu, an riga an canja sunan birnin Pingyang don ya zama birnin Linfe na lardin Shanxi da ke a arewancin kasar Sin. Ya zuwa yanzu dai, ya kasance da haikalin Yao da aka gina a zamanin dauar Jin ( tsakanin shekarar 265 zuwa ta 420) da kabarin Yao da aka gina a zaman daular Tang a birnin Linfen na yanzu.

Bayan da Yao ya hau kan kujerar mulki, ya nada mutune nagartattu masu hikima na kabilarsa don su zama manyan mutane, ta yadda a farkon farko, za a iya hadin kan 'yan kabilarsa sosai, haka nan kuma bisa sakamakon da ya samu daga binciken ci gaba da jami'ansa suka samu wajen gudanar da harkokin mulki, ya ba da kyauta ga wadanda suka sami sakamako mai kyau, sa'an kuma ya yanke hukunci a kan wadanda suka aikata laifuffuka. Ta haka an gudanar da harkokin mulki yadda ya kamata. Haka zalika Yao ya mai da hankalinsa sosai ga daidaita huldar da ke tsakanin rukunonin kabilu daban daban, ya yi wa fararen hulda tarbiyya da su yi zaman jituwa, ya tabbatar da kwanciyar hankali a duk kasarsa, ya gudanar da harkokin siyasa a fili kuma da kyau sosai, don haka an yi zaman alheri cikin kwanciyar hankali a duk kasar.

Bisa labarin da aka samu daga mutanen zamanin da, an ce, a zamanin Yao, a karo ne na farko da aka tsara kalanda. Bisa kalandar, jama'a leburori za su iya yin aikin samar da kayayyaki cikin lokaci-lokaci, ba za su jinkirtar da lokacin aikin gona ba. Mutanen zamanin da sun dauki zamanin sarki Yao bisa matsayin zamani da aka fi samun ci gaba da sauri wajen bunkasa aikin gona da al'adu.

An ce, zamanin Yao lokacin aukuwar ambaliyar ruwa ne. Ambaliyar ruwa ya yi tsanani sosai ya malala zuwa tuddai, ya jawo wa jama'a tulin wahalhalu, jama'a sun rasa jin dadin zamansu. A cikin irin wannan hali ne, Yao ya mai da hankali gosai ga bala'in nan. Ya saurari ra'ayoyi daga wajen kananan sarkunansa (leud), ya tambaye su cewa wa zai iya kawar da bala'in ambaliyar ruwa, kananan sarkunansa sun gabatar masa da Gun. Bayan haka sai Yao ya ba da umurni ga Gun don ya yi aikin tsare ruwa ta yadda za a kawar da bala'in nan.

Ban da wadannan abubuwa da muka ambata a baya, an ce, a cikin littafi na Zhu Zi, an rubuta cewa, sarki Yao ya kware a fannin ilmi da wasan karate, ya taba aika da sojojinsa wajen danne rukunonin kabilu da ke a kudancin kasar, kuma ya shiga cikin yaki da kansa. Haka zalika Yao ya aika da Yi Jiang don ya kashe wadancan namun daji, ya harbi rana guda 9 (an ce, ya kasance da rana 10 a sararin samaniya a wancan zamani ). An ce, jama'a sun nuna godiya ainun ga Yao saboda matakan nan da ya dauka wajen kawar da bali'in domin jama'a, sabo da haka an nuna masa goyon baya don ya zama sarkin kasa.

Bayan da Yao ya shafe shekaru 70 yana kan kujerar mulki. Sai ya gano cewa, wajibi ne, ya zabi magajinsa. Ya nemi kananan sarkunansa da su gabatar masa da wanda zai iya cin gadonsa. Kananan Sarkunan sun gabatar masa da Shun cewa, Shun da nagari ne, ya daidaita huldar tsakanin 'yan iyalinsa da kyau sosai, kuma ya iya shawo kan 'yan iyalinsa ta yadda za su daina yin danyen aiki su yi aiki mai kyau. Da jin haka, Yao ya dau niyyar gwada shi.

Ya bai wa Shun damar auren 'ya'yansa mata biyu, wato E Huang da Nu Ying don ya gane halinsa, ya san ko ya iya kula da harkokin iyalinsa da kyau ko a'a. Shun da matansa biyu E Huang da Nu Ying sun yi zamansu a bakin kogin Wei, sun yi abubuwansu tare da ladabi.

Yao ya ba Shun aikin koyar da jama'arsa kyawawan abubuwa biyar wadanda suka hada da nuna adalci irin na mahaifi, da tausayi irin na mahaifa, da aminci iri na 'yanuwa da zama 'ya'ya nagartattu, duk jami'ai da fararen hula sun ji farin ciki da bin umurninsa. Haka nan kuma Yao ya ba Shun aikin kula da harkokin jami'ai daban daban, ya gudanar da harkokin mulki. Dadin dadawa Yao ya bar Shun da ya karbi kananan sarkuna da suka zo hedkwatar kasa daga wurare daban daban don ganawa da Yao. Daga bisani dai, Ya bar Shun da ya shiga cikin kurmin daji da ke kan duwatsu shi kadai don ya jarraba halitta.

Bisa binciken da ya yi ta yi har cikin shekaru uku da suka wuce, Yao ya yanke shawara a kan bar Shun da ya ci gadonsa.

Shun ya yi kokarin bunkasa aikin samar da kayayyaki, ya haka magudanan ruwa da rijiyoyi, ya daura abuta da mutanen bangarori daban daban. A zamanin Shun, an sami babban ci gaba wajen kyautata aikin gona da na masana'antu. Yayin da yake gudanar da harkokin mulkinsa, ya kan raba fara daya da jama'arsa. Fararen hula sun sami nama da kifaye sun ci, sun sami sutura da suke bukata, kuma ba su yi ayyuka masu nauyi da mahukunta suka rarraba musu ba, haka zalika sukar da suka yi wa harkokin mulki ba laifi ba ne. A lokacin da Shun ke gudanar da harkokin mulki, jama'a suna da ladabi sosai, suna nuna masa biyayya a ko ina cikin kasar, sabili da haka cewar da aka yi ana gudanar da harkokin siyasa a fili kuma da kyau, an sami wadatuwa, lalle zamaninsa wani zamani ne mai haske a fannin siyasa da aikin samar da kayayyaki da kuma fasaha. Daga karshe Shun ya bar Yu da ya ci gadon sarautarsa sabo da aikin bajinta da ya yi wajen kawar da ambaliyar ruwa.

Shun ya rasu ne yayin da yake da shekaru 110 da haihuwa bayan da ya yi fama da ciwo. Yanzu, ana iya ganin kabarin Shun da ke a kan dutsen Ju Ni mai nisan kilomita 30 a kudancin gundumar Ningyuan na lardin Hunan na kasar Sin. Ana yabon Yao da Shun daga zuriya zuwa zuriya cewa su mutane ne nagartattu masu karimci kuma masu son mutane masu hikima. (Halilu)

Shen Nongshi

Yau sama da shekaru 5,000 da suka wuce, Shen Nongshi jagoran kabilar Jaing ne, ko da yake shi sarki ne, amma duk da haka ya dade yana aikin noma a gonaki daidai kamar yadda 'yan kabilarsa ke yi. Ta hanyar aikin noma, ya kago wani irin kayan aikin noma a kasar Sin, ya ba da babbam taimako wajen bunkasa aikin noma kwarai, sabili da haka ana kiran shi da sunan Shen Nongshi ne domin nuna masa girmamawa domin taimako da ya bayar ga aikin noma.

Zamanin Shen Nongshi farkon lokaci ne ga zamanin da maza ke mallakar kungiyoyin hadin kan jama'a. A wancan lokaci, ba ya kasance da cin zalunci da azaba ba, mutane suna zaman jituwa da juna kwarai. Bisa abubuwa da aka rubuta a cikin littafi mai suna "Shiji", an ce, a lokacin da Shen Nongshi ke kan kujerar mulki, maza su yi aikin noma a gonaki, mata kuwa su yi sakar zane a gida, an gudanar da harkokin mulki ba tare da bukatar gidan yari da hukunci da ake yankewa ba, haka nan kuma sarkin kasa ba ya bukatar sojoji da 'yan sanda.

Ban da wadannan kuma Shen Nongshi masanin ilmin likitanci na kasar Sin ne tun can shekaru aru-aru. An ce, da ya ga wahalhalu da jama'a ke sha bayan da suka kamu da cututtuka, sai ya bayyana damuwarsa kwarai. Da ya ga shinkafa da alkama da gero da makamatansu na gina lafiyar jiki, sai dabara ya fado a cikin zuciyarsa, wato mai yiwuwa ne a yi amfani da ganyaye ko saiwoyin tsire-tsire wajen hada magunguna don warkar da masu cututtuka. An kara da cewa, Shen Nongshi ya taba sa kafa a duwatsu daban daban ya cire ganyaye ko saiwoyi iri-iri na tsire-tsire. Ya taba dandana ganyaye da saiwoyin tsire-tsire iri daban daban don gano ainihin halayensu, amma ya kan ci ganyaye da saiwoyin tsimai masu guba ba tare da sani ba, abin da ya fi tsanani shi ne a wata rana ya taba shan wadanan tsire-tsiren guba fiye da sau 70. An ci gaba da cewa, ya taba shirya wani littafi da ake kira "Shennong Baicao", inda aka rubuta sunayen magunguna iri daban daban wadanda ake iya amfani da su wajen warkar da cututtuka.

Bugu da kari Shen Nongshi masanin ilmin yanayin sararin samaniya da na kalanda ne. Sa'an nan kuma ya taba kago wani irin kayan kida kamar " molo" don shere mutane da suke hutu bayan tashinsu daga aiki. Da an buga wannan kayan kida, sai murya kukar tsuntsaye ta tashi. Haka nan dansa shi ma ya fitar da wani irin kayan kida da ake kira "Zhong" cikin Sinanci, ya kuma tsara wake-wake da yawa, yanzu ma ana iya samun irin wadannan kayayyakin kida da suka kago.

Shen Nongshi ya shafe shekaru 140 yana kan kujerar mulki, Hunag Di ne ya maye gurbin kujerar mulkinsa. Bayan rasuwar Shen Nongshi, an binne shi a birnin Changsha na lardi Hunan, ya zuwa yanzu dai kabarinsa yana nan lami lafiya, amma ana kiran kabarinsa da suna kabarin Yan Di. (Halilu)

Fu Yishi, sarki na farko a kasar Sin

Bisa abubuwa da aka rubuta a cikin littafin zamanin da da aka wallafa a kasar Sin, an ce, Fu Yishi sarki na farko ne, ya yi zaman rayuwarsa yau kimanin shekaru 5,000 da suka wuce.

An ce, haihuwar Fu Yishi abu mai ban mamaki ne. Mahaifiyarsa wta budurwa ce mai suna "Hua Xushi". Wata wata mai kyau, yayin da take wasa a bakin fadama, ta ga wani sawu mai fadi wanda ya ba ta mamaki kwarai, sai ta taka da sawu da kafafunta biyu, bayan haka ta ci wake ta haifi Fu Yishi.

Fu Yishi yana da wata Kanwar da ake kira Nu Wa cikin Sinanci. Bisa abubuwa da aka rubuta a cikin littafin zamanin da, an ce, labarun haihuwarsu biyu masu ban mamaki ne kwarai, dukan kawunansu na bil-adam ne, amma jikunansu na "dodo" ne wato Dragon da ake kira cikin Turanci. Wannan ya ba da shaida cewa, a hakika dai, mai yiwuwa ne, Fu Yishi wani jagoran kabila ne da aka kago bisa alamar kabilarsa ta "dodo".

Zamanin Fu Yishi zamani ne da aka ci gaba wajen yin aikin kawo albarka, kirkire-kirkire masu yawa sun danganci Fu Yishi. Bisa abu da aka rubuta a cikin littafin zamanin da, an ce, ya kago alamu masu ban mamaki iri daban daban bisa yanayin sararin samaniya da sawunin tsuntsaye da na namun daji. Duk wadannan alamu suna taimakawa juna, suna kunshe da sunayen abubuwa iri daban daban da ake samu a duniya da sararin samaniya, sabo da haka an yi amfani da wadannan alamu wajen rubuta abubuwa da suka faru a cikin zaman rayuwarsu, daga nan ne aka kawo karshen tunawa da abubuwa ta hanyar nannade igiya.

Da ya ga an kawo karshen amfanin igiya, sai ya yi amfani da igiya wajen sassaka taro don kamun kifaye, kuma ya koyar da mutane hanyar da za su bi wajen kamun kifaye da yin farauta. Haka nan Fu Yishi ya kago wani irin kayan kida da ake kira "Se" a cikin Sinanci don murnar samun girbi mai armashi da bikin daurar aure da makamatansu. Ya tsara wata kida mai suna "Jia Bian", don kara jin dadin zaman rayuwar jama'a. Ban da wadannan kuma Fu Yishi ya koyar wa jama'a yadda ake hura wuta ta hanyar huda katako, a ci abinci bayan da aka dafa su, ta haka sun kubutar da kansu daga zaman jahilci da suke yi irin na cin namun daji ba tare da dafawa ba.

A wancan zamanin, Fu Yishi ya yi fadi-tashi ne musamman a Huai Yang na lardin Henan da Ji Ning da Qu Fu na lardin Shandong na kasar Sin, sabo da haka ya zuwa yanzudai, ya kasance da kabarin Fu Yi a Ji Ning. A ran 3 ga watan Marisa bisa na kalandar manoma ta gargajiyar kasar Sin ta ko wace shekara, manoma da suka fito daga wurare daban daban su kan shirya biki iri na zamanin da a Ji Ning don nuna alhini ga wannan kaka-kakkani mai wayin kai na al'ummar kasar Sin. (Halilu)

[Masu Ilmomi da na Siyasa a Tarihi]

Han Feizi

Han Feizi, babban masanin ilmin dokoki

Han Feizi shahararren masanin ilmin filosofiya da na dokoki, kuma mawallafi ne a zamanin yakekeniya na kasar Sin wato tsakanin shekarar 475 zuwa ta 221 kafin bayyanuwar Annabi Isa. Hasashensa game da gudanar da mulkin kasa ta hanyar shari'a ya zama hasashe ne ga kafa dayantacciyar gwamnati mai mulkin shifta na farko a kasar Sin.

Han Feizi yana daya daga cikin dangin sarkin kasar Han na karshen zamanin yakekeniya. Ya yi i'ina,ko da yake bai sarrafa harshe a baka ba, amma littattafai da ya wallafa sun yi yawa.

A zamanin Han Feizi, karfin kasar Han sai kara raguwa yake yi a kwana a tashi. Cikin nuna kishin kasa, ya sha gabatar da takardu zuwa ga sarkin kasarsa, inda ya gabatar da shawarwarinsa na yin gyare-gyare. Bisa ra'ayinsa kamata ya yi, masu mulki su mayar da aikin raya kasa mai wadata da na kafa askarawa mai karfi bisa matsayin babban aikinsu ne. Amma sarkin kasarsa bai amince da shawarwarinsa ba. Sabo da haka, bisa sakamako da darasi da aka samu daga tarihi wajen gunadar da harkokin mulkin kasa da halin da ake ciki a wancan lokaci, ya wallafa littattafan siyasa da dama wadandan yawan kalmominsu ya wuce dubu 100. Ko da yake wadannan littattafai ba su jawo hankulan mutanen kasar Han ba, amma sun bazu a kasar Qin mai kasaita a wancan zamani. Qin Shihuang, sarkin kasar Qin ya yi sha'awar littattafansa ainun. Bayan da Qin Shihuang ya tura sojojinsa don tasam ma kasar Han, sai sarkin kasar Han ya aika da Han Feizi zuwa kasar Qin don neman sulhuntawa. Da ya sauka a kasar Qin, sai Qin Shihuang ya yi shirin ciyar da shi gaba. A wancan lokaci, wazirin kasar Qin Li Si dan ajin Han Feizi ne. Ya sani sosai Han Feizi ya fi shi ilmi nesa ba kusa ba, ya nuna kishi ya shafa masa kashin kaji a gaban Qin Shihuang. Da Qin Shihuang ya amince da makarkashiyarsa, sai ya jefa Han Feizi cikin gidan kurkuku, kuma ya kashe shi da guba.

Babban aiki mai suna "Han Feizi" littafi ne da Han Feizi ya wallafa a farkon zamanin daular Qin dangane da gudanar da harkokin mulkin kasa ta hanyar dokoki. Wannan littafi yana hade da bayanoni 55 wadanda yawan kalmominsu ya wuce dubu 100 a yanzu. A wancan zamani, bangaren tunani na kasar Sin wadanda mabiyan Confucious da na Mo Zi ke wakilta, ya nuna girmamawa ga cewar da aka yi "doka ta fi sarki " da "mayar da zamanin da", sun gabatar da ra'ayoyinsu na yin abubuwa da ke dacewa da halin da ake ciki. Han Feizi ya yi suka kan ra'ayi iri na " son mutane" da aka gabatar cikin hasashen Confucious, ya gabatar da manufofinsa guda hudu game da gudanar da harkokin mulkin kasa ta hanyar dokoki, da ba da babbar kyauta, da yanke hukunci mai tsanani, da ba da muhimmanci ga aikin gona da na yaki. Ya kuma gabatar da ra'ayinsa cewa, sarkin kasa ya sami ikonsa ne daga wajen Allah, tun bayan zaman daular Qin, hasashen Han Feizi ya jawo babban tasirinsa ga kafa mulkin shifta na gajigajiya na lokatai daban daban a kasar Sin.

A cikin bayanoninsa, Han Feizi ya kan tabbatar da ra'ayoyinsa ta hanyar kawo misalai. Alal misali, a cikin wani bayani da ya wallafa a karkashin lakabi haka "Wang Zheng", ya gabatar da ka'idoji 47 dangane da hambarar da mulkin kasa ta hanyar bincike-binciken abubuwa da suka faru.

Haka nan kuma a cikin bayanoninsa, Han Feizi ya yi rubuce-rubuce cikin jan hali, rubuce-rubucensa suna ba mutane mamaki, sabili da haka ana sha'awar bayanoninsa kuma ana jin dadin karanta su. Han Feizi ya kuma kware wajen tsamo dimbin tatsuniyoyi da zurfaffen ilmin tarihi don bayyana ra'ayoyin gaskiya. Ya zuwa yanzu dai, ana ci gaba da yin amfani da wadannan tatsuniyoyi da yawa da ya bayyana a nan kasar Sin. (Halilu)

Zhuang Zi

Zhuang Zi shahararren mutum ne da ke wakiltar darikar Dao a zamanin yakekeniya a kasar Sin wato tsakanin shekarar 403 zuwa ta 221 kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S. (B.C.) bayan Lao Zi.

Zhuang Zi , sunan iyalinsa shi ne Zhou. Kuma shi dan kasar Song ne a karni na 4 kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S.(B.C.), ya taba zama karamin jami'in karamar hukumar wuri-wuri na kasar Song. An ce, tun lokacin da yake karami, Zhuang Zi yaro ne mai hazikanci kuma ya yi kokarin karatu, ya taba yin ziyarce-ziyarce a kasashe daban daban da ke kudancin kasarsa, ya yi nazari kan tsofaffin dabi'o'i, a duk rayuwarsa shi mutum ne mai gaskiya, mai kuma son aikata gaskiya da son halitta, ya nuna raini ga sarkuna da sauran manyan masu mulki. Sarkin kasar Chu ya taba ba shi babbar kyauta don neme shi da ya zama wazirinsa, amma Zhuang Zi ya ki amincewa. Kuma daga nan ne bai taba sake zaman jami'i ba a duk sauran lokacin rayuwarsa, ya saka takalma da karan shimkafa, ya sayar da su don zaman rayuwarsa. Bisa labari da aka samu daga tatsuniya, an ce, ya taba wallafa littattafai wadanda yawan babbakunsu ya wuce dubu 100.

Littafi mai suna "Zhuang Zi" da ke kasancewa a yanzu yana kunshe da bayanoni 33.

Zhuang Zi ya gaji tunanin Lao Zi da na Dao, kuma ya yadada shi a fannin filosofiya, ya kafa tsarin filosofiyarsa mai cin gashin kai, sa'an nan kuma ya gwada halinsa na musamman a fannin karatu da wallafe-wallafe. A ganinsa, "Dao" wani hakikanin abu ne, ya dauki "Dao" bisa matsayinsa na asalin halitta, halitta kuma ta gagara. A fannin siyasa, ya gabatar da ra'ayinsa cewa, a gudanar da harkokin mulki yadda ya kamata, a yi zaman rayuwa daidai da halin da ake ciki kuma yadda ya kamata. Ya dauki abubuwa da ake kira halin kirki da kamilanci da dattaku da gaskiya da rashin gaskiya da ake yi duk sarka ce da aka yi wa dan adam, ya yi suka ga halin kirki da kamilanci da dattaku da harkokin mulki da ake gudanarwa bisa dokoki, kuma ya yi suka mai zafi ga tsofaffin dabi'o'i da dokoki da ikoki da ke kasancewa a zamantakewar al'umma, ya gabatar da ra'ayinsa mai zurfi cewa, " mutane masu hankali ba su mutuwa, manyan 'yan fashi ba su karewa", "a kashe kananan barayi, amma masu satar mulkin kasashe su kan zama sarakuna". Game da hanyar da ake bi wajen zaman rayuwa, ya girmama halitta, ya gabatar da ra'ayinsa cewa, "halitta da ni suna zamansu tare, duk abubuwa da ni daya ne", kuma a ganinsa, babban burin zaman rayuwar dan adam shi ne a yi zama cikin kwanciyar hankali da sakin jiki, a more 'yanci sosai a fannin tunani, amma ba a fannin kayayyaki ba. Duk wadannan tunani da ra'ayoyinsa sun kawo tasiri mai zurfi ga zuriyar baya, kuma suna da matukar muhimmanci ga tarihin tunanin bil-adam.

Littafi mai suna "Zhuang Zi" ya taba jawo babban tasiri a zamanin Wei Jin na tsakanin karni 3 zuwa na 5. Littafin nan da sauran littattafai biyu da ake kira "Zhou Yi" da " Lao Zi" wadanda ake kira su littattafan ilmi masu zurfi (profound or abstruse)guda uku, suna kan matsayi mai muhimmanci ga tarihin adabin kasar Sin. A zamanin daular Tang na tsakanin shekarar 618 zuwa ta 907, an mayar da littafin "Zhuang Zi" don ya zama daya daga cikin littattafai masu daraja na darikar "Dao".

Ba ma kawai Zhuang Zi ya kawo wa zuriyar baya tasirinsa a fannin filosofiya da na tunaninsa kawai ba, hatta ma ya yi a fannin adabi. Ya bayyana ra'ayoyinsa kan harkokin siyasa da filosofiyarsa da kuma tunaninsa ta hanyar ban sha'awa, ya kan bayyana su ne ta hanyar tatsuniyoyi da ba da misalai masu ban sha'awa da sarrafa harshe sosai, sabili da haka an yi sha'awarsu ainun. (Halilu)

Mencius

Mencius kwararre mai girma ne a fannin tunani a zamanin yakekeniyar kasar Sin wato tun dga karni na 5 har zuwa karni na 3 kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S.(B.C.), kuma yana daya daga cikin manyan wakilan Tunanin Confucius wanda shi ne babban hasashe a kasar Sin.

'Ke' sunan iyalin Mencius ne. An haifi Mencius ne a kasar Zou, wato garin Zou da ke a lardin Shangdong na kasar Sin a yau, kuma ya yi zaman rayuwarsa a karni na 4 kafin bayyanuwar Annabi Isa (B.C.). An ce, Mencius zuriyar Men Sunshi, babban mai mulkin kasar Lu ne. A lokacin rayuwarsa, an yi takara tsakanin makarantun tunani daban daban (a hundred schools of thought contend), Mencius ya ci gadon tunanin Confucius wanda shi ne ya tsara hasashen Confucius, kuma ya yadada shi, ya gabatar da cikakken tsarin tunani wanda ya haifar da tasiri sosai ga zuriyar baya, sabili da haka an dauke shi bisa matsayinsa na mutum mai tsarki na biyu bayan Confucius kawai.

Mencius ya gaji tunanin Confucius game da kula da harkokin mulki ta hanya ta nagari, ya yadada shi, ya mayar da shi don ya zama hasashen kula da harkokin mulki ta hanyar nuna kauna, wannan kwayar tunanninsa a fannin siyasa. Ya yi amfani da ka'idar nuna kauna cikin dogon lokaci wajen sassauta sabane-sabane da ake yi a tsakanin rukunoni daban daban, don kare moriyar dogon lokaci ta rukunin masu mulkin gargajiya.

A wani bangare, Mencius ya bambanta matsayin rukunonin masu mulki daga matsayin rukunoni da ke karkashin mulki. A ganinsa, masu aiki da kwakwalwa na yin mulki, masu aikin dantse na karkashin mulki, sa'an nan ya kwaikwayi tsarin zamanin Zhou ya tsara tsarin matakai daban daban na daga sarkin kasa har zuwa farar hula. A bangare daya kuma ya dauki hulda a tsakanin masu mulki da wadanda ke karkashin mulki bisa matsayin hulda a tsakanin iyaye da 'ya'ya, ya gabatar da ra'ayinsa cewa, ya kamata, masu mulki su kula da wahalhalu da jama'a ke sha kamar yadda iyaye ke yi wa 'ya'ya, haka nan kuma ya kamata, jama'a su bauta wa masu mulki kamar yadda 'ya'ya ke yi wa iyaye.

Daga sakamakon da aka samu a zamanin yakekeniya, Mencius ya gano dokar game da tabbatar da zaman lafiyar kasashe daban daban da rayuwarsu da kuma mutuwarsu. Ya kuma gabatar da ra'ayinsa irin na dimokuradiya cewa, " jama'a na da daraja, masu mulki ke biye da su ". A ganinsa, batun kulawa da jama'a yana da matukar muhimmanci ga tabbatar da zaman lafiyar kasa da rayuwarta da kuma mutuwarta. Mencius ya kan mai da hankalinsa sosai ga goyon baya da jama'a ke nunawa, ya sha bayyana cewa, irin wannan goyon baya bakin zare ne ga batun tsaida wadanda ke kan samun mulkin kasa ko za a tumbuke su daga karagar mulki ta hanyar gwada misalai da yawa da suka taba faruwa a tarihi.

Mencius ya hada da'a da siyasa a gu daya, ya jaddada cewa, zama mutum mai da'a abu ne mai muhimmanci ga gudanar da harkokin siyasa da kyau. Ya ce, kasa ta fi muhimmanci a duniya, iyali ya fi muhimmanci a kasa, haka kuma mutum ya fi muhimmanci a iyali.

Ka'idoji 4 na Mencius game da da'a su ne kauna (benevolence), da adalci, da ladabi, da kuma basira. A ganin mencius, daga cikinsu, kauna da adalci sun fi muhimmanci. Idan duk jama'a sun iya daidaita hulda da ke tsakanin mutum da mutum cikin nuna kauna da adalci, to, za a iya tabbatar da mulkin gargajiya lami lafiya.

Ko da yake tunanin Mencius ya haifar da tasiri mai zurfi ga zamanin dauloli daban daban na kasar Sin a fannin siyasa da tunani da al'adu da da'ar gargajiya, amma duk da haka masu mulki ba su nuna goyon bayansu ga hasashensa a wancan zamani ba.

Bisa matsayinsa na masani, Mencius ya taba lallashin masu mulki don neman yadada hasashensa game da gudanar da harkokin mulki ta hanyar nuna kauna. Ya taba sa kafarsa a kasar Liang (wato Wei) da ta Qi da Song da Teng da Lu wadanda ke kokarin neman zaman kasashe masu kasaita a fannin tattalin arziki da aikin soja a wancan zamani, kuma suke neman dinkuwar kasashe ta hanyar nuna karfin tuwo. A ganinsu, hasashen Mencius game da gudanar da harkokin mulki ta hanyar nuna kauna lalatacen abu ne, sabo da haka ba a sami damar aiwatar da wannan hasashensa ba. Amma a lokacin da yake wadannan kasashe, Mencius ya nuna halinsa sosai, ya nuna raini ga sarkuna da manyan masu mulki, ya yi fatan za a iya kwantar da tashin hankali, a kubutar da jama'a daga wahalhalu, a duk lokacin da yake yin ma'amala da sarkunan kasashen nan, ya kan nuna halinsa na aikata gaskiya da nuna jaruntaka.

Daga bisani, ya yi murabus daga mukaminsa, ya yi aikin koyarwa, ya wallafa littafi mai suna "Mencius" cikin hadin guiwa da dalibansa wanda ke hade da bayanoni 7. A cikin littafin nan, an rubuta jawaban Mencius, da muhawarar da aka yi a tsakaninsa da wakilan mabiyan sauran hasashe. Littafin nan ya bayyana yadda Mencius, babban malamin ilmin Confucius ya gaji hasashen Confucius da yadada shi bayan Confucius. Littafin nan na da dadin karatu. Ko da yake yau da shekaru dubbai ke nan da suka wuce, amma daga littafin nan za a iya gano halin Mencius na aikata gaskiya, kuma a ce, lallai Mencius babban malamin tunanin falsafa ne. Sabo da haka a cikin shekaru dubai da suka wuce, ana ta sha'awar karanta wannan littafi, ana nuna masa girmamawa, kuma an dauke shi bisa matsayin littafin gargajiya.(Halilu)

Confucius da hasashensa

Idan an tabo magana a kan al'adun gargajiyar kasar Sin, to, wani mutum da ya cancanci ambata shi ne Confucius. A shekarun 1970, yayin da wani masanin Amurka yake jera sunayen shahararrun mutane 100 wadanda suka haifar da tasiri mai zurfi ga tarihin dan adam, ya kai Confucius ga matsayi na 5, bayan Jesus da Sakyamuni da sauransu. A ganin Sinawa, watakila, tasiri da Confucius ya yi musu zai kai matsayi na farko. Duk Sinawa gaba daya suna samun tasiri daga wajen hasashen Confucius a wasu fannoni.

Confucius shi ne ya tsara hasashen Confucius. A cikin sama da shekaru 2000 da suka wuce, ba ma kawai tunanin Confucius ya haifar da tasiri ga kasar Sin a fannin siyasa da al'adu da sauransu ba, hatta ma ya haifar da tasiri ga duk Sinawa wajen yin aikace-aikace da wasa kwakwalwa. Har ila yau wasu masanan kasashen waje sun dauki tunanin Confucius bisa matsayin tunanin addinin kasar Sin. A hakika dai, tunanin Confucius yana daya daga cikin hasashe da yawa na tsohon zamanin kasar Sin kawai, kuma shi wani irin tunanin filosofiya ne, amma ba wani irin addini ba ne. A zamanin gargajiya da aka shafe sama da shekaru 2000 ana yinsa a kasar Sin, an dauki tunanin Confucius bisa matsayin tunanin halal, sabili da haka an dade ana nuna girmamawa gare shi. Ba ma kawai tunanin Confucius ya haifar da tasirinsa mai zurfi ga bayyanuwar al'adun kasar Sin ba, hatta ma ga wasu kasashen Asiya. Ya zuwa yanzu dai, da ya ke Sinawa na zaune a ko ina cikin duniya, sai an ce, tasirin tunanin Confucius ya riga ya ratsa Sin da Asiya da kuma sauran wuraren duniya.

Confucius an haife shi ne a shekarar 551 kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S.(B.C.), kuma ya mutu ne a shekarar 479 kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S.(B.C.), ya bar Yaristud, shahararren masanin kasar tsohuwar Greece shekaru 100 da 'yan doriya. Yayin da Confucius yake da shekaru 3 da haihuwa, sai babansa ya rasa ransa, bayan haka mahaifiyarsa ta dauke shi zuwa lardin Shandong da ke gabashin kasar Sin ta yau sun yi zamansu. Sunan Confucius Kong Qiu ne, "Confucius" sunan girmamawa ne da ake kiran shi. A zamanin da, sunan ko wane mutum na kasar Sin ya hada da sunan iyalinsa da "Zi", "Zi" kuwa kalma ce da ake kira don nuna girmamawa.

A duk rayuwarsa, ko kusa, Confucius bai taba rike mukamin babban jami'i ba. Amma yana da ilmi mai zurfi. A zamanin da, sai manyan masu mulki ne kawai ke da ikon samun ilmi a kasar Sin. Amma Confucius ya saba wa irin wannan ikon musamman na masu manyan mulki ta hanyarsa. Ya dauki almajirai a makarantarsa, ya koyar da su, duk almajiransa wadanda kome matsayinsu sun iya samun damar shiga makarantarsa, sai ya ba da abubuwa kalilan a bakin kudin makaranta. Confucius ya yi wa almajiransa farfaganda kan ra'ayoyin siyasarsa da tunanin da'arsa. An ce, yawan almajirai da suka taba yin karatu a makarantarsa ya wuce 3,000, daga cikinsu akwai manyan masana da dama daidai da Confucius. Wadannan manyan masana sun gaji tunanin Confucius, kuma sun yadada shi a wurare daban daban.

Me ya sa tunanin Confucius ya yi ta tsayawa kan matsayi mafi muhimmanci a zamanin gargajiyar kasar Sin? Da kyar, za a iya amsa wannan tambaya a saukake. A takaice dai, an amsa tambayar cewa, tunaninsa game da matakan jama'a da kyautata harkokin siyasa sun dace da moriyar rukunin masu mulki, kuma sun ba da taimako ga tabbatar da zaman karko da raya zamatakewar al'umma a wancan zamani. Confucius ya ba da matukar muhimmanci ga ka'idojin da'a da dokoki, a ganinsa, idan wani karamin mutum ya saba wa burin babban mutum ko da ya saba wa burin baba, to, sun yi babban laifi ke nan. Bisa hasashensa, kamata ya yi, sarkin kasa ya gudanar da harkokin mulkinsa da kyau, fararen hula kuwa su nuna biyayya sosai ga sarkinsu. Ko wane mutum na kan matsayinsa daban daban, alal misali, wani da namiji, shi uba ne, sa'an nan kuma shi farar hula ne ga sarki, amma wajibi ne, ya tsaya kan matsayinsa da ke dacewa da wurare daban daban. Ta haka dai za a iya tabbatar da zaman lafiya a kasa, jama'a kuwa za su yi zaman rayuwarsu cikin kwanciyar hankali.

Bayan da hasashen Confucius ya bulla, bai zama tunani mai matukar muhimmanci nan da nan ba. Ya zuwa karni na biyu kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S.(B.C.), kasar Sin ta riga ta zama wata babbar kasa mai kasaita da dinkuwa da ke karkashin mulkin gwamnatin tsakiya. Masu mulki sun gano cewa, hasashen Confucius ya dace da halin da ake ciki a wancan zamanin gargajiya wajen kare zaman karko, sabo da haka sun mayar da hasashensa don ya zama tunanin halal ga kasarsu.

A cikin wani kundi maras kauri mai suna "The Analects of Confucius", an rubuta tunanin Confucius da maganganu da kuma aikace-aikacensa. An kaddamar da wanna kundi ne musamman domin bayyana nassin Confucius da hirar da ya yi tare da almajiransa. A zamanin da, mutanen Sin sun dauki wannan kundi bisa matsayin littafi mai tsarki daidai da littafin "The Bible" da Kiristoci ke nuna masa girmamawa. Idan wani farar hula ne, to, kamata ya yi, ya yi zaman rayuwarsa bisa ka'idojin tunanin wannan kundi, kana idan wani mutum ne mai son zaman jami'i, to, wajibi ne, ya yi nazari sosai a kan wannan kundi. A zamanin da, wani karin magana da ake fada a kasar Sin cewa, a yi amfani da rabin kundin "The Analects of Confucius" wajen gudanar da harkokin mulkin kasa, abin da ake nufi shi ne, idan wani ya nakalci rabin hasashen wannan kundi, to, zai iya kula da harkokin mulkin kasa da kyau.

Amma a hakika dai, kundin nan ba wani liffafi ba ne mai cike da wa'azi. Banban da haka kundin nan wani littafi ne mai kunshe da abubuwa masu inganci, da kalmomi masu ban sha'awa da kuma hasken hikima da basira sosai. Ra'ayoyin Confucius da aka bayyana a cikin wannan kundi ya dangaci karatu da kide-kide da wake-wake da yin yawon shakatawa a kararkar birane da daura abuta da kuma sauran fannoni. Bisa wani labari da aka rubuta a cikin kundin nan, an ce, akwai wani almajari mai suna Zi Gong ya yi tambaya a kan batun gudanar da harkokin mulkin kasa cewa, daga cikin askarawa da abinci da jama'a, wane ne za a soke shi idan ya zama wajibi? Confucius bai yi wata wata ba wajen amsa cewa, askarwa.

Hasashen Confucius yana hade da azurtattun abubuwa, ya zuwa yanzu dai ma da yawa daga cikinsu suna da daraja kwarai. Nassi da yawa daga cikin wannan kundin Confucius sun riga sun zama karin magana da Sinawa su kan yi amfani da su a yau. Alal misali daidai da yadda ya bayyana cewa, ko shakka babu daga cikin mutane uku, akwai wani wanda shi ne malamina. Abin da ake nufi da wannan karin magana shi ne, kowa na da abu mai rinjaye, sabo da haka ya kama a yi koyi da juna. (Halilu)

Lao Dan mai fito da tunanin Dao

Lao Dan sunansa Li Er ne. Li sunan iyalinsa ne, kana Er sunansa ne, amma a kan kira shi da sunan Lao Zi, ranar da aka haife shi da kuma lokacin mutuwarsa duk ba a san su ba. An ce, shi dan kasar 'Chu' ne, ya yi zaman rayuwarsa a zamanin Bazara da Kaka wato tsakanin shekarar 770 zuwa ta 476 kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S.(B. C.). Lao Dan mutum ne dogo, da manyan idanu da kunnuwa masu tsayi da kuma lebe mai kauri. Lao Dan ya taba zama jami'i mai kula da littattafai da aka ajiye a zamanin daular Zhou. Sabo da haka Lao Dan mutum ne mai zurfin ilmi, kuma ya yi suna sosai a wancan zamani. A lokacin da Confucius yake samarintaka, ya taba kai ziyara mai girmamawa ga Lao Dan, ya koyi labadi iri na zamanin daular Zhou daga wajen Lao Dan. Da Lao Dan ya ga tabarbarewar daular Zhou, sai ya tashi daga birnin Luo Yang, hedkwatar kasar. Da ya yada zango a wani wuri mai suna Hanguguan, ya rubuta littattafai biyu da ake kira "Darikar Dao", bayan haka ya tashi daga garin kan shanu, daga nan dai ba a san inda yake ba. An ce, Lao Dan ya rasu ne yayin da yake da shekaru 60, har wa yau an ce ya rasu ne yake da shekaru sama da 200. Amma an hakake cewa, ya yi tsawon rai. Dalilin da ya haka shi ne domin shi mutum nagari ne ba tare kwadayin mukamai da kaddarori ba.

Littafin "Darikar Dao" wanda kuma ake kira da suna "Lao Zi" yana da babbaku da yawansu ya wuce 5,000, kuma yana kunshe da abubuwan ilmi masu arziki kwarai. Wannan littafi wani tsohon littafi ne mai muhimmanci ga al'adun zamanin da a kasar Sin. Lao Dan kwararre ne a fannin tunanin "Materialism", a karo na farko ne ya kai filosoliya zuwa matakin koli a kasar Sin, abin da ake nufin "Dao" shi ne hanya, ana kai ko ina a wurare daban daban kan hanya, a wancan zamani kuma an dauki "Dao" bisa matsayin ka'idoji. Lao Dan ya mai da hankali ga sauye-sauyen halitta da hulda tsakanin mutum da mutum, ya sabunta ma'anar "Dao". A ganin Lao Dan, "Dao" hakikanin abu ne, kuma shi ne babban asalin haifar da duk hakikanan abubuwa.

Ra'ayoyi irin na "son mallakar duniya" da aka bayyana a cikin "Littafin Darikar Dao" wani kashi ne mai inganci ga tunanin filosofiyar Lao Zi. Ya bayyana cewa, an kasance da abubuwada ba su rabuwa da juna, banban da haka abubuwa suna dogara da juna kuma suna daganta da juna.

Lao Dan ya bayyana ka'idojin sauye-sauyen al'amura a cikin littafinsa na "Darikar Dao". Yana ganin cewa, alheri da bala'i su iya canjawa a tsakaninsu. Akwai abu mai alheri a cikin bala'i, sa'an nan kuma akwai tohon bala'i a cikin abu mai alheri. Haka zalika ya fara gano cewa, sauye-sauyen abubuwa zai jawo canjawar halinsa. Ya ce, iri karami ya iya zama bishiya mai girma, kasa a tarwatse zai zama tudu. Ya kuma ce, kada a durkusa a gaban wahala, idan an yi ta yin kokari, to, tabbas ne, za a iya kawar da wahalhalu a cim ma buri mai girma.

Lao Dan ya yi nukura da yaki. Ya ce, bayan barkewar yaki, ko shakka babu za a gamu da bala'i. Haka nan kuma ya ki rukunin masu mulki da su yi wasoson kayayyaki daga wajen fararen hula ba ji ba gani.

Lao Dan ya taba bayyana zaman rayuwar jama'a mai dadi da yake so a cikin zuciyarsa, wata kasa karama ce, mutanenta ba kadan ne, ko da yake kasar na da makamai, amma ba a bukatarsu ba, sa'an nan kuma kasar tana da amalanke da kwale-wale, amma ba a dauke su. Jama'a su sami abinci mai dadin ci, su sanya tufafi masu kyaun gani, su ji dadin kwana a gidajensu, kasashe makwabtanta suna iya ganin haka, amma jama'arsu ba su kai wa juna ziyara ba. A kasar an yi zaman rayuwa a saukake, ba su bukatar rubutu, wato ke nan a sake shiga cikin zamanin tunawa da abubuwa ta hanyar nannade igiya. Ko da yake burinsa na masu ra'ayin rikon rikau ne, amma ya bayyana cewa, Lao Dan ya yi kyamar yake-yake da aka yi ta yi a zamanin Bazara da Kaka (the spring and Autumn period) wato tsakanin shekarar 770 zuwa ta 476 kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S. (B. C.), haka nan kuma burinsa burin manoma ne da ke kishin zaman rayuwa cikin kwanciyar hankali.

Tunanin filosofiya na Lao Dan yana kan matsayi mai matukar muhimmanci ga tarin filosofiyyar kasar Sin. Tunaninsa game da siyasa ya haifar da tasiri ga kwararru masu ci gaba a fannin tunani da kwararru masu zaton iska a fannin gyare-gyaren zamantakewar al'umma. (Halilu)

[Masu Bincike a Tarigi]

Zu Chongzhi da ∏

Gano ∏ wata matsala ce mai matukar muhimmanci da wahala yayin da ake yin nazarin ilmin lissafi. A zamanin da, masanan lissafi da yawa sun yi kokari wajen yin lissafi don gano ∏ a kasar Sin, sakamakon da Zu Chongzhi ya samu a karni na 5 babban ci gaba ne da aka samu wajen gano ∏. Zu Chongzhi masanin ilmin lissafi da na taurari mai girma ne na kasar Sin a zamanin da. An haife shi ne a birnin Jiankang (wato birnin Nanjing na lardin Jiangsu a yau) a shekarar 429, kakanninsa su ma sun kware wajen nazarin ilmin taurari da na kalanda. Sabo da haka tun yake karami, ya fara taba ilmin lissafi da na taurari. Yayin da shakarunsa suka kai 35 a shekarar 464, ya fara yin lissafin ∏.

Daga aikace-aikacen da aka yi a kasar Sin a zamanin da, an gano cewa, tsawon gefen da'ira ya fi diameter sau uku da 'yan doriya, amma 'yan doriyar nan nawa ne, aka yi gardama a kai. Kafin lokacin Zu Chongzhi, Liu Hui, sakamakon lissafi da kwararren kasar Sin a fannin ilmin lissafi ya samu dangane da ∏ ita ce 3.1415. Bisa sakamakon da tsoffafinsa suka samu, Zu Chongzhi ya yi ta yin kokari sosai wajen yin lissafi, sakamakon ∏ da ya gano shi ne tsakanin 3,1415926 zuwa 3.1415927. Amma yanzu ba a iya gano hanyar da Zu Chongzhi ya bi wajen samun wannan sakamakon ∏ ba.

Bayan sama da shekaru 1,000 da suka wuce, masanan ilmin lissafi na kasashen waje su ma sun sami sakamakon ∏ daidai da na Zhu Chongzhi. Sabo da haka wasu masanan ilmin lissafi na kasashen waje sun gabatar da shawara a kan kira ∏ da sunan ∏din Zhu don tunawa da fifitaccen taimako da Zhu Chongzhi ya bayar. Bayan da wannan, Zhu Chongzhi da dansa suka yi kokari tare, sun gano ka'ida mai kyau da ake bi wajen lissafin girma ko yawan abin da ke cikin wani abu.Turawa na kiran irin wannan ka'ida da sunan "Cavalieri", amma Cavalieri, masanin ilmin lissafi na kasar Italiya shi ma ya gano irin wannan ka'ida ne bayan fiye da shekaru 1000 da Zhu Chongzhi da dansa suka gano. Yanzu, bangaren 'yan ilmin lissafi su ma suna kira wannan ka'ida da sunan ka'idar Zhu don tunawa da babban taimako da Zhu da dansa suka bayar wajen gano ka'idar nan.

Sakamako da Zhu Chongxhi ya samu a fannin ilmin lissafi yana daya daga cikin nasarori da kasar Sin ta samu wajen nasarin ilmin lissafi a zamanin. Alal misali, a kimanin karni na 2 kafin bayyanuwar Annabi Isa A.S.(B.C.), an riga an bayyana ka'idar The Pythagorean thorem a cikin wani littafi mai suna "ka'idar lissafi na Zhou Bi "da aka wallafa dangane da ilmin lissafi a kasar Sin tun wancan zamanin da. Haka nan kuma a cikin wani littafi daban mai muhimmanci da ake kira "lissafin Jiu Zhang da aka wallafa a karni na 1 dangane da ilmin lissafi, an gabatar da ka'idoji game da adadi da ke kasa da sifiri wato negative number da hada adadi da ke sama da sifiri da na sama da sifiri wato positive number da nagative number; a karni na 13, haka nan kuma a karni na 13, an riga an gano wasu hanyoyin da ake yin lissafi mai wuya a nan kasar Sin, wadanda kuma ya zuwa karni 16 Turawa suka gano. (Halilu)

Masanin ilmin magani Li Shizhen

Likitancin kasar Sin yana da dadadden tarihi, kuma akwai shahararrun masanan ilmin magani da yawa a cikin tarihin kasar Sin. A karni na 16 wato sarautar Ming, shahararren masanin ilmin magani LI Shizhen ya wallafa wani littafi mai suna Tsarin magungunan gargajiya wanda ya zama littafin misali a kan tarihin magungunan kasar Sin.

Li Shizhen an haife shi ne a Qizhou na lardin Hubei na kasar Sin. Qizhou wani wuri ne da ke fitar da magungunan gargajiya, mahaifin Li Shi zhen likita ne, tun lokacin da ya ke yaro ne ya yi sha'awar halitta kwarai, ya kan bi mahaifinsa zuwa cikin tuddai don cire magungunan, bayan sun koma gida sai su sarrafa su da su zama magani. Amma a wancan zamani ba a girmama likita, sabo da haka mahaifinsa yana son ya yi karatu don ya zama jami'in gwmnati.

A shekara ta 1531, wato lokacin da Li Shizhen ya ke da shekaru 14 da haifuwa, ya samu nasara a wajen jarrabawar zama Xiucai, amma daga baya ba a ciyar da shi gaba ba. Daga bisani sai ya fara koyon likitanci daga wajen mahaifinsa, ya yi kokarin koyon likitanci kuma ya warkar da matalauta marasa lafiya. Ya kan kai ziyara ga masunta da mafarauta har da manoma da masu tattara magunguna don tattara dabarun warkar da ciwace ciwace, ban da haka kuma ya yi bincike da nazari a tsanaki har ya gane halayen magunguna sosai.

A shekara ta 1551 Li Shizhen ya zama wani shahararren likita. Wata rana dan sarkin Chu ya yi rashin lafiya, sai Li Shizhen ya ba shi magana, kuma ya warke nan da nan. Da sarkin Chu ya ga haka ya yi farin ciki kwarai. Sai ya nada shi da ya zama likitan fada.

A wancan lokaci sarki ya so ya samu maganin da zai sa ya yi tsawon rai, har ba zai mutu ba, sauran likitocin fada ma haka su ke yi don neman maganin tsawon rai. Da Li Shizhen ya ga haka, sai ya yi bakin ciki, kuma ya yi murabus daga mukaminsa, ya koma gida don ci gaba da aikinsa na wallafa littafi.

A yayin da ya ke aikinsa na likitanci ya ga wasu littatafan likitanci ba su da gaskiya. Har an rubuta wasu abubuwan wauta a cikinsu. Da Li Shizhen ya ga haka, sai ya ji lallai ya kamata ya wallafa wani sabon littafin magungunan gargajiya. A shekara ta 1522 wato lokacin da Li Shizhen ya ke da shekaru 35 da haifuwa ne ya fara wallafa littafi mai suna Tsarin magungunan gargajiya.

Domin wallafa wani sabon littafin magunguna, Li Shizhen ya karanta litattafai da likitoci fiye da 800 suka wallafa, kuma ya tattara abubuwa game da magunguna, kuma ya gyara littafin da ya wallafa har sau uku. Bayan da ya yi shekaru 30 ya wallafa littafi, a shekara ta 1578 ya kammala aikinsa na wallafa babban littafi mai suna Tsarin magungunan gargajiya.

Littafi mai suna tsarin magungunan gargajiya yana da kalmomi mkiliyan da dubu 900 wanda ya bayyana magunguna har iri dubu daya da dari 8 da 92, ya rubuta dabaru dubu 11 na hada magunguna, kuma ya zana zane zane har fiye da dubu don siffanta magungunan gargajiya.

Li Shizhen ya sadaukar da ransa don takaita fasahohin da jama'ar kasar Sin suka dandana a wajen yin amfani da magunguna, har ya wallaka littafi mai suna Tsarin magungunan gargajiya. Sabo da haka ya zama babban masanin ilmin magani. Daga bisani an yi ta buga littafin nan a kasasr Japan. Kuma an fassara littafin nan zuwa Turanci da Faransanci da Jamusanci da sauran harsuna. Daga karni na 17, littafi mai suna Tsarin magungunan gargajiya ya yadu a wuraren duniya, ya zama muhimmin littafin da masu bincike magani ke karantawa. (Dogonyaro)

Shahararren masanin ilmin sararin sama Zhang Heng

Zhang Heng an haife shi ne a gundumar Nanyang ta lardin Henan a tsakiyar kasar Sin. Tun lokacin da ya ke yaro ne ya yi kokari a wajen karatu, kuma ya gwanance a wajen wallafe wallafe. A lokacin da ya ke da shekaru 17 da haifuwa ne ya bar garinsu ya je Changan, wato birnin da ya zama hedkwatar kasa na sarauta da dama a kan tarihin kasar Sin. A nan Zhang Heng ya yi bincike da nazarin abubuwan tarihi, ya bincike al'adun jama'a da tattalin arzikin zaman tarayya. Daga bisani gwamnati na wancan zamani ta nada shi ya zama jami'I na Luoyang, daga baya kuma ya kama sauran mukamai.

Zhang Heng ya yi sha'awar ilmin halitta kwarai da gaske, amma ba ya sha'awar suna da riba, ya yi murabus har sau biyu. Ya yi shekaru 3 yana bincike firosufiya da lissafi da ilmin sararin sama, ya samu ilmi da yawa, kuma ya fara wallafa littafi.

A zamanin sarautar Han wato kafin shekaru dubu 2, akwai hasashe da dama game da samaniya. A ganin Zhang Hen, duniya ta yi kama da kwai, kasar da mu ke zaune ta yi kama da rawayan kwai, samaniya ta fi kasa girma. Wannan ra'ayinsa yana da ci gaba kwarai a wancan zamani. A ganinsa tun can farko duniya a harhade ta ke, amma daga baya, abubuwa maras nauyi sun yi sama sun zama samaniya, abubuwa masu nauyi sun nutsa har sun zama kasa. A ganinsa nisan da ke tsakanin taurari ne ya kudura saurin tafiyar taurari.

Zhang Heng bai bincike hasashe kawai ba, kuma ya sa muhimmanci a wajen yin aikatawa. Shi kansa ne ya bincike da kera kayayyaki da yawa na auna sararin sama da kasa. Misali ya kago wata na'urar auna girgizar kasa. A shekara ta 138, wannan na'urar auna girgizar kasa ta yi nasarar auna girgizar kasa da aka yi a lardin Shanxi.

Zhang Heng kuma ya bincike ilmin sararin sama da yawa. Misali ya ce, a tsakiyar kasar Sin ana iya gani taurari misali dubu 2 da 500. A ganin zhang Heng, ko da ya ke da safe da yamma, in an duba rana, ta yi girma, amma da tsakar rana ta yi karama, amma hasali ma daya ne, domin da sassafe da magariba, duniya ta yi dan duhu. Amma da tsakar rana, da haske da yawa, shi ya sa an yi tsammani rana ta yi karama. Misali in an duba wuta da dare, ta kan yi girma, amma da rana ta kan yi karama. Irin wannan ra'ayin Zhang Heng yana da gaskiya.

Zhang Heng kuma ya bincike ilmin sararin sama da yawa. Misali ya ce, a tsakiyar kasar Sin ana iya gani taurari misali dubu 2 da 500. A ganin zhang Heng, ko da ya ke da safe da yamma, in an duba rana, ta yi girma, amma da tsakar rana ta yi karama, amma hasali ma daya ne, domin da sassafe da magariba, duniya ta yi dan duhu. Amma da tsakar rana, da haske da yawa, shi ya sa an yi tsammani rana ta yi karama. Misali in an duba wuta da dare, ta kan yi girma, amma da rana ta kan yi karama. Irin wannan ra'ayin Zhang Heng yana da gaskiya.

Zhang Heng ba masanin ilmin sararin sama kawai ba, kuma shahararren mawallafi ne na zamanin Donghan, kuma ya gwanance a wajen zane. Shi ne daya daga cikin shahararrun masu zane 6 na wancan zamani. Bisa lissafin da aka yi an ce, Zhang Heng ya wallafa littatafai har 32 don nuna ra'ayinsa game da 'yan Adam da karatu. A cikin littatafan da ya wallafa kuma ya siffanta al'amura na wancan zamani wadanda su ke da daraja kwarai a wajen bincike tarihi na wancan zamani. (Dogonyaro)

[Saura]

Kwararren likita Hua Tuo

Idan wani mutum ya yi rashin lafiya, to, zai yi fatan likita ya zo ya warkar da shi. A kasar Sin, idan wani mutum yana fama da rashin lafiya har dogon lokaci, to, za a ce, idan Hua Tuo yana nan, to, zai warkar da shi nan da nan. Hua Tuo wani likita ne na kasar Sin kafin shekaru fiye da dubu 2, da ya ke ya gwanance a wajen likitanci, jama'a suna girmama shi kwarai da gaske.

Hua Tuo mutumi ne na lardin Anhui a gabashin kasar Sin, amma ba a san lokacin da aka haife shi ba, abin da muka sani shi ne mahukunta sun kashe shi kafin shekara ta 208. Bisa labarin da aka samu an ce, Hua Tuo yana da lafiya kalau, ko a lokacin da ya ke da shekaru 100 da haifuwa ma yana da kuruciya. Bisa abin da aka rubuta a cikin tarihi an ce, Hua Tuo wani likitan jama'a ne wanda ba ya sha'awar suna da riba, ya ki shawarar da aka ba shi da ya zama jami'in gwamnati. Daga bisani, Cao Cao, babban mahukunci na wancan zamani yana da ciwon kai, kuma ya kira shi, ya ga tilas ne ya je wajensa kuma ya warkar da ciwonsa nan da nan. Cao Cao ya tilasta masa da ya zama likita na kansa. Daga baya Hua Tuo ya ce zai koma garinsu domin matarsa ba ta da lafiya. Bayan da ya koma garinsu ya ki sake zuwa wajen Cao Cao. Sabo da haka Cao Cao ya jefa shi cikin kurkuku, kuma ya kashe shi.

Hua Tuo ya yi zurfi a wajen likitanci, kuma ya iya warkar da kusan ko wane irin ciwo, musamman ya gwanance a wajen fi da. Hua Tuo shi ne daya daga cikin likitocin da suka kago allurar kashe zafi, likitoci na kafin Hua Tuo ba su taba yin amfani da irin wannan allurar kashe zafi ba.

Hua Tuo ya gwanance a wajen yin fi da. Wata rana ya yi wa wata yarinya fi da. A kan gwiwar wannan yarinya akwai wani kurji, ba ta jin zafi, amma ta ji kaikayi, ta yi fama da wannan kurji har shekaru 8, ba wanda ya iya warkar da ita. Sai ta roki Hua Tuo ya warkar da ciwon nan. Bayan da Hua Tuo ya yi fi da, sai ya fitar da wani abu mai kama da maciji, kuma ya sa magani a cikin kurjin nan, bayan kwanaki 7 sai ta warke. Wannan yarinya da iyalinsa sun yi masa godiya kwarai da gaske. Wata rana wani tsoho maras lafiya ya roke shi da ya warkar da ciwonsa. Bayan da Hua Tuo ya duba lafiyarsa ya ce, wannan ciwo ba magani zai warkar da shi ba, wato dole ne a yi fi da, amma ko na yi masa fi da ma, zai rayu shekaru 10 kawai. Daga baya ya yi masa fi da, amma bayan shekaru 10 wannan tsoho ya mutu.

Hua Tuo kuma ya gwanance a wajen duba ciwon da mutane suka kamu da shi. Kuma ya san ko za a iya warkar da ciwon nan. Wata rana ya ga wadansu mutane suna shan giya, bayan da ya duba lafiyar wani mutum mai suna Yan Xin, sai ya gaya masa cewa, sai ka daina shan giya kuma ka koma gida. A kan hanyar koma gida wannan mutum ya fadi ya mutu.

Tabbatar da ciwon da mutum ya kamu da shi yana da amfani kwarai da gaske. A lokacin da Hua Tuo ke warkar da maras lafiya, ya kan ba da magani gwagwadon ciwon da ya same shi, sabo da haka ya samu maraba sosai daga wajen marasa lafiya. Wata rana mutane biyu masu ciwon kai sun zo wajensa don roke shi da ya ba su magani. Bayan da Hua Tuo ya duba lafiyarsu, sai ya ba su maganin da ya sha banban da juna. Sauran mutane ba su gane dalili ba, sai Hua Tuo ya ce, ko da ya ke dukkansu sun yi ciwon kai, amma dalilin da ya sa su yi ciwon kai ba daya ba ne, sabo da haka maganin da na ba su ma ba daya ba ne. bayan da suka sha maganin duk sun warke. Hua Tuo kuma ya sa muhimmanci a wajen motsa jiki. A ganinsa wasannin motsa jiki suna da amfani kwarai a wajen kara lafiyar jiki. Shi kuma ya kago wasannin kwakwayon dabobi 5 wato damisa da gada da bear da biri da tsuntsu don kara lafiyar jiki da maganin ciwo. Hua Tuo yana da dalibai da yawa, guda uku na cikinsu sun fi shahara. Bayan rasuwar Hua Tuo an gina dakin ibada na Hua Tuo don shaida tunawar da jama'a ke yi masa. (Dogonyaro)

Tawayen Chen Sheng da Wu Guang

Chen Sheng da Wu Guang shahararrun shugabanni ne na tawayen manoma. Tawayen da suka shugabanta ya barke ne a karshen sarautar Qin wato shekara ta 300 kafin haifuwar Annabi Isa. Wannan shi ne babban tawaye na farko da aka yi a kan tarihin kasar Sin.

A shekara ta 210 kafin haifuwar Annabi Isa, sarki Qinshihuang ya mutu, dansa Hu Hai ya gaji sarauta, ya zama sarki Qin na biyu.

Sarki Qin na biyu ba ya da imani. A karkashin mulkinsa jama'a sun sha bakar wahala, tarin 'yan kwadago suna fama a bakin mutuwa.

A shekara ta 209 kafin haifuwar Annabi Isa Sarki Qin na biyu ya umurci manoma 900 na bakin kogin Huai su yi gadi a Yuyang.

An nada Chen Sheng da Wu Guang da su zama shugabanninsu. A lokacin da suka isa Daze, ruwan sama ya hana tafiyarsu. Bisa dokar sarautar Qin idan ba su iya isa wurin da aka tsai da a daidai lokaci ba, to, za a yanke musu hukuncin kisa gaba daya.

Hafsoshi biyu da suka tura keyarsu ba su da imani, sai Chen Sheng da Wu Guang sun kashe su, kuma sun gaya wa mutane cewa, ga shi yanzu ana ruwan sama kamar bakin kwarya, ba za mu isa wurin gadi a daidai lokaci ba, sabo da haka za a yanke mana hukuncin kisa. Ko ba a kashe mu ma yawancinmu za mu mutu a wurin gadi. Dukkanmu maza ne, ya kamaata mu nuna jaruntaka mu yi tawaye! Da mutane sun ji haka, duk sun yarda kuma sun zabi Chen Sheng da Wu Guang da su zama shugabanninsu, kuma sun gabatar da kira cewa, sai mu kai farki ga sarki maras imani. Sun kafa wata kungiyar sojoji 'yan tawaye. Wannan shi ne babban tawaye na farko da manoma suka yi a kan tarihin kasar Sin.

Domin habaka tasirinsu, sai sun kunna wuta a wurin da su ke zaune kuma sun yi kirari, jama'a sun yi tsammani Alla ne ya aiko su don su ka da mulkin sarautar Qin. Sabo da haka da sauri suka mamaye gundomomi, manoma matalauta da yawa sun shiga rundunarsu. Bayan da 'yan tawaye suka mamaye gundumar Chen, sai sun kafa mulkin Zhangchu, Chen Sheng ya zama sarki. Wannan shi ne mulkin juyin juya hali na farko na manoma a kan tarihin kasar Sin.

'Yan tawaye sun ci gaba da dosa wa gaba, sun kai wa Qin farmaki daga hanyoyi 3, a wannan lokaci sojoji 'yan tawaye sun kai dubu daruruka, kuma suna da kekunan yaki dubu daya.

Wata rundunar sojoji 'yan tawaye da ke karkashin shugabancin Zhou Wen ta isa wurin da ke kusa da Xianyan wato hedkwatar kasar nan. Da sarkin Qin na biyu ya ga haka sai ya firgita. Sai ya aika da sojoji da yawa don yin yaki da 'yan tawaye. Daga baya 'yan tawaye sun yi hasara, sai sun janye jiki zuwa Chaoyan don jiran gudummuwar da za a kawo.

Wata rundunar sojoji manoma daban da ke karkashin shugabancin Wu Chen ta mamaye birnin Handan, bisa zugawar wasu tsofaffin fadawa ne ya nada kansa da ya zama sarkin Zhao. Chen Sheng ya yi hakuri, kuma ya umurce shi da ya kai gudummuwa ga Zhou Wen, amma sun ki. Sauran mutanen tsofaffin sarakuna ma sun nada kansu da su zama sarakuna. Sabo da haka sojoji 'yan tawaye da ke karkashin shugabancin Chen Sheng da Wu Guang sun kife cikin mawuyacin hali. Zhou Wen ya shugabanci sojoji 'yan tawaye don yin yaki har watanni 3, bayan da ya yi hasara har sau da yawa ya kashe kansa. Daga bisani an kashe Wu Guang da ke yi wa Ronyang kawanya. A watan Disamba na shekara ta 209 kafin haifuwar Anabin Isa, zhang Han ya shugabanci sojojin Qin don auka wa gundumar Chen. Chen Sheng shi kansa ne ya shugabanci sojoji 'yan tawaye don yin dagiya, daga baya ya yi hasara. Matukin keken yaki ne ya kashe shi.

Lu Chen da sauran mabiyan Chen Sheng sun ci gaba da yin yaki. Daga baya sun hada kansu da sojoji 'yan tawaye da ke karkashin shugabancin Xian Yu da Liu Bang don ci gaba da yin yaki da sojojin Qin. A shekara ta 206 kafin haifuwar Anabin Isa, sojoji 'yan tawaye manoma sun ka da mulkin sarautar Qin. (Dogon Yaro)

Wang Zhaojun

A cikin tarihin kasar Sin, mulkin tsakiyar kabilar Han a tsakiyar kasar Sin ya kan yi sabani da mulkin wuri wuri na kananan kabilu da ke a kewaye. Sabo da haka a kan ta da yaki don daidaita sabani, amma wani sa'I an yi amfani da hanyar auren diyar sarki don daidaita sabanin da ke tsakaninsu, ta yadda za su yi sulhu. Tafiyar Zhaojun zuwa Mongolia ita ce daya daga cikin labarun nan.

A karni na daya kafin haifuwar Annabi Isa sarautar Han ne ke mulki a kasar Sin. A cikin kabilar Xiongnu sabani ya tashi don neman kwace mulki, kuma an yi baraka, sarakuna 5 sun yi yakekeniyar juna, daga baya guda biyu sun yi saura. Wadannan sarakuna biyu duk suna jin tsoron abokinsa na gaba ya hada kan sarautar Han na tsakiya. A lokacin nan daya daga cikinsu mai suna Huhanxie shi kansa ne ya zo Changan wato hedkwatar sarautar Han don nuna biyaya ga sarkin Han. Sarkin Han ya nuna masa maraba da hannu bibbiyu, kuma ya ba shi abinci da yawa a yayin da zai bar birnin Changan, kuma ya aika da sojojin doki don raka shi zuwa wurinsa. Bisa goyon baya na sarautar Han ne Huhanxie ya sake hada Xiongnu gaba daya.

Domin sada zumunta da sarautar Han daga zuri'a zuwa zuri'a, a shekara ta 33 kafin haifuwar Annabi Isa Huhanxie ya sake zuwa Changan, wannan shi ne karo na uku da ya zo birnin nan. Kuma ya gabatar da rokonsa na neman aure wata diyar sarki. Sarkin Han ya yarda da rokon Huhanxie, amma ba ya son diyarsa ta je Xiongnu. Sabo da haka sai sarki ya gaya wa bayin fadarsa cewa, idan wata yarinyar da ke cikin fada tana son aure sarkin Xiongnu, to, sarki zai dauke ta a kama da diyarsa.

'Yan mata da ke cikin fada duk 'yan mata masu kyau ne da aka zaba daga duk kasa. In an zabe su kuma a kai su cikin fada ba za su damar fita daga cikin fada ba, amma da suka ji labari cewa, za a kai su zuwa Xingnu, to, sai su yi shuru, ba sa son zuwa.

Bisa dokar da aka kafa a wancan zamani, 'yan mata na fada ba su da iznin zuwa gaban sarki, dole ne mai zane ya zana surar 'yan mata, sa'an nan a kai zanensu zuwa gaban sarki don sarki ya zaba. Wani mai zane yana da sunan Mao Yanshou ba ya da kirki, ya kan nemi kudi daga wajen 'yan mata na fada don ya kara kyaun surarsu. Yarinya mai suna Wang Qian wato Wang Zhaojun tana da kyau kwarai da gaske, kuma tana da ilmi mai zurfi, kuma ta iya kade kade, lallai tana da kirki da adalci, ba ta son ba wa Mao Yanshou kudi wato yi masa rashawa, sabo da haka Mao Yanshou ya ki jininta, sai ya bata surar zanen da ya yi, bayan da aka kai zanenta zuwa wajen sarki, sai sarki ya yi tsammani, wannan yarinya ba ta da kyau, ya rufe ta a cikin fada kawai, ita ma ba ta da damar gana da sarki.

Da Wang Zhaojun ta ji labarin yin aurataya da sarkin Xiongnu, sai ta ce ta yarda da zama matan sarkin Xiongnu. Sarkin Han ya yi farin ciki kwarai da jin haka. Ya tsai da cewa za a shirya bikin aure na Huhanxie da Wan Zhaojun a birnin Changan, hedkwatar kasa.

Sarki Huhanxie ma ya yi farin ciki kwarai da samun yarinya mai kyau kamar haka, sai shi da Wang Zhaojun sun je gaban sarkin Han don nuna godiya. Da sarkin Han ya ga Wang Zhaojun sai ya yi mamaki da irin kyaunta, kuma ya yi nadama. Amma a lokacin nan ba dama a gyara, tilas ne ya bar sarkin Xiongnu ya tafi da Wang Zhaojun. Bisa yadda ake yi wa diyar sarki ne, sarki ya ba Wang Zhaojun kayayyaki da yawana aure.

Saye da kayayyaki masu kyau Wang Zhaojun ta hau farin doki, a rakiyar jami'an sarautar Han da Xiongnu ne ta bar Changan, ta yi doguwar tafiya har zuwa Xiongnu. Da farko ko kadan ba ta saba da irin zama na makiyaya ba, amma ta yi kokarin kau da wahaloli. Daga bisani ta saba da zamansu, kuma ta yi jituwa da mutanen Xiongnu sosai.

Wang Zhaojun ta yi duk zaman rayuwarta a Xiongnu, kuma ta mika al'adun kabilar Han ga al'ummar Xiongnu. 'Yayanta ma sun gaji niyyarta don ci gaba da yalwata dangantakar aminci a tsakanin kabilar Han da kabilar Xiongnu. Har yanzu ma akwai kabarin Zhaojun a karkarar birnin Huhouhaot na jihar Mongolia ta gida ta kasar Sin, jama'ar Xiongnu ta zamanin da sun gina wannan kabari ne don tunawa da wannan manzon sada zumunta ta al'umma. A cikin shekaru fiye da dubu da suka shige an yada wannan labari mai kyau daga zuri'a zuwa zuri'a a cikin tarihin kasar Sin. Kuma a kan yi wasannin kwaikwayo iri iri don bayyana wannan labari. (Dogon Yaro)

Yanzi

A cikin shahararren littafin tarihi mai suna Labarun tarihi na zamanin da na kasar Sin, Shi Maqian, mai wallafa littalin nan ya rubuta wani dan diflomasiya mai wayo, wato Yanzi na kasar Qi a karni na 6 kafin haifuwa Anabi Isa. A kasar Sin akwai labarun Yanzi da yawa, yanzu sai mu kawo muku wasu labarunsa a yayin da ya zama manzon kasar Qi zuwa kasar Chu.

Wata rana an nada Yanzi ya zama manzo zuwa kasar Chu. Da ya ke sarkin kasar Chu ya san Yanzi gajere ne, sai ya so ya yi wasa da shi. Sai sarki ya ba da umurnin gina wata karamar kofa a gefen babbar kofa don Yanzi ya shiga cikin birni ta wannan karamar kofa.

Da Yanzi ya ga haka sai ya kekasa kasa ya ki. Ya ce, " sai a kasar karnuka ne za a bi kofar kare, ni manzon kasar Qi ne, ba zan bi kofar kare ba."

Da jami'in kula da Yanzi ya ji haka, sai ya bar Yanzi ya shiga ta babbar kofa. Bayan da Yanzi ya shiga cikin birni, sai ya kai ziyarar ban girma ga sarkin kasar Chu. Da gangan ne sarkin kasar Chu ya tambaya cewa, "dalilin da ya sa aka aiko ka zuwa kasar Chu domin ba sauran mutane, ko ba haka ba?"

Yanzi ya amsa cewa, "akwai mutane masu dimbin yawa a kasar Qi, a cikin hedkwatar kasa kawai akwai tituna fiye da 100, in mutane sun daga hannu za a rufe rana, in mutane sun goge gumi, za a yi kamar ana ruwan sama. Mutane suna zaune a cunkushe, yaya ba mutane a kasar Qi?"

Sarkin Chu ya ci gaba da tambaya cewa, "da ya ke an yi haka, domme an aike ka zuwa nan?"

Sai Yanzi ya amsa cewa, "a kasarmu wato kasar Qi, muna da ka'ida a wajen aika manzani, mu kan aika manzani masu wayo zuwa kasashe masu girma da wayin kai; mu kan aika manzo wawa zuwa kasashen da ba abun a zo a gani ba. Ni ne manzo wawa a cikin manzanin kasar Qi, sabo da haka an aiko ni zuwa nan kasar Chu." Wannan maganar da Yanzi ya yi ya sa sarki da mutanensa na kasar Chu sun kidime.

Bayan haka, wata rana an sake nada Yanzi da ya zama manzo zuwa kasar Chu. Da sarkin kasar Chu ya ji labari cewa, Yanzi zai sake zuwa, sai ya tambayi wazirinsa cewa: " Yanzi na kasar Qi yana da hikima kuma ya kware a wajen muhawara. Yanzu zai sake zuwa kasarmu. Ni ina son cin mutuncinsa, ko kuna da dabara mai kyau?

Wani jami'I ya ba da shawara cewa, " a lolacin da Yanzi ya zo wajenmu, sai mu daure wani mutum don su wuce a gaban sarki, sai yallabai ka tambaya cewa, wanene ku daure shi? Sai sojoji su amsa cewa, mutumin kasar Qi ne. sai yallabai ka sake tambaya cewa, domme a daure shi? Sai sojoji su amsa cewa, domin ya yi sata. Da sarkin kasar Chu ya ji haka, ya ce, lallai wannan dabara mai kyau ne, sai a shirya.

Bayan da Yanzi ya wo kasar Chu, sai sarkin kasar Chu ya shirya masa walima. A lokacin da su ke shan giya ne, sojoji biyu sun daure wani mutum don wuce gabansu. Sai sarkin Chu ya tambaya cewa, wane mutum ne ku daure shi? Domme ku daure shi?

Sai sojoji sun amsa cewa, " Mutumin kasar Qi ne, domin ya yi sata."

Sai sarkin kasar Chu ya dubi Yanzi, kuma ya ce, " da ma mutanen kasar Qi duk baratu be?"

Da Yanzi ya ji haka, sai ya tashi ya ce, na ji an ce, akwai wani irin itace, lokacin da aka dasa shi a kasar Qi ya kan ba da 'ya'ya masu dadin ci, amma in an dasa shi a kasar Chu, ko da ya ke reshe da ganye duk daya ne, amma 'ya'yansu ko kadan ba dadin ci. Dalilin da ya sa haka ruwa da kasa ba daya bane. Yanzu ga wannan mutum, lokacin da ya ke a kasar Qi bai taba yin sata ba, amma bayan da ya zo kasar Chu sai ya yi sata, ko ruwa da kasa na kasar Chu suna iya sa mutane su zama barayi?"

Da sarkin Chu ya ji haka, ya yi na'am cewa, " da ma ina son yi maka ba'a, amma ka yi mana dariya, lallai ka cancanci yabo.

Har wa yau kuma akwai labarai da yawa game da Yanzi a yayin da ya zama manzo kasar Qi zuwa kasar Chu. A lokacin da a ke hira ne ya murkushe makarkashiyar wasu mutanen da ke neman cin mutuncin kasar Qi. Yanzi ya ya yi suna ya zama wani shahararren dan diflomasiya. (Dogon Yaro)

Su Wu

A kasar sin akwai wani labarin da kusan kowa ya sani, wato Su Wu ya kiwo awaki. Wannan labari ya bayyana yadda Su Wu ya yi biris da daular tasku a cikin sharadi mai wuya, kuma yana rike da mutuncin al'umma mai daukaka.

Su Wu wani mutum ne na sarautar Han a karni na daya kafin haifuwar Anabi isa. A wancan zamani sarautar Han da mulkin kananan kabilu su kan yi gardama kuma su kan yi sulhu. A shekara ta 100 kafin haifuwar Anabi Isa, sabon sarkin muliin Xionnu ya hau kan karagar mulki, domin nuna zumunci sarkin sarautar Han ya aika da Su Wu da sauran mutane fiye da 100, sun yi tafiya da kayayyaki da yawa don ya zama manzo a kasar Xionnu. Amma a daidai lokacin da Su Wu zai gama aiki na manzo ne, mahukuntan Xionnu sun yi rikici, har riakicin nan ya shafi Su Wu, kuma an tsare shi, kuma an neme shi da ya ci amanar sarautar Han don nuna biyaya ga sarkin Shanyu.

Da farko sarkin Shanyu ya aika da mutane don shawo kan Suwu, kuma ya yi alkawarin ba shi babban mukami da sarari da yawa, amma Su Wu ya kekasa kasa ya ki. Da Shanyu ya ga lalashi ba ya yi, sai ya fara yin amfani da bulala. A wancan lokaci hunturu ya fadi, ana sanyi sosai, kuma ga kankara na zuba. Sai Shanyu ya jefa shi a cikin wani rami mafas rufi. Kuma an daina ba shi ruwa da abinci, ya yi tsammani da haka za a canja imaninsa. Da haka dai Su Wu ya sha bakar azaba. Da ya ji kishi sai ya ci kankara, da ya ji yunwa sai ya ci tufar fata. Bayan kwanakin da suka shige, Shanyu ya ga Su Wu bai sunkuyar da kai ba, sai ya sake shi.

Da ya ke Shanyu ya ga dukkan dabarunsa ba su yi amfani ba, sai ya nuna masa ban girma domin ya yi tsammani lallai Su Wu namiji ne, sabo da haka bai kashe shi ba, amma ba ya son komar da shi gida. Sai ya tsai da kudurin kai shi zuwa tabkin Begal don ya kiwo awaki. Kafin ya tashi sai ya gana da Su Wu, kuma ya ce, tun da ba ka ba da kai ba, to, dole ne ka je ka kiwo awaki. A lokacin da rago zai haifi 'ya'ya ne zain bar ka koma gida.

Bayan da aka kai shi zuwa wannan wurin da ba mutane wato a bakin tabki. Shi kansa ko kusa ba zai gudu ba. Abubuwan da ke raka shi su ne wani sandan manzo da awaki. Kullum Su Wu yana rike da wannan sandan manzo, a ganinsa ko ba dade ko ba jima zai koma gida rike da wannan sandan manzo. Da haka bayan shekara da shekaru, adon da ke kan wannan sandan manzo ya bace, Su Wu ma ya yi furfura.

A bakin tabkin Begal Su Wu ya kiwo awaki har shekaru 19. a cikin shekaru 19 da suka shige, sarkin Shanyu da ya ba da umurnin tsare Su Wu ya mutu, sansa ya hau kan karagar mulki. A wannan lokaci sarkin sarautar Han da ya nada Su Wu ya zama manzo ma ya mutu, dansa ya hau kan karagar mulki. A wannan lokaci sabon sarkin Shanyu ya aiwatar da manufar yin abuta da sarautar Han, sabo da haka sarkin sarautar Han ya aika mutane nan da nan don karbar Su Wu zuwa kasar mahaifa.

A lokacin da Su Wu ya dawo hedkwata sarautar Han ya samu maraba sosai, ko ma'aikatan gwamnati, ko farar hula duk sun nuna wa wannan jarumin al'umma ban girma. Shekaru dubu 2 ke nan, amma irin wannan hali mai daukaka na Su Wu ya zama misalin koyo ga Sinawa, ya zama muhimmin abu na cikin al'adun al'ummar kasar Sin. (Dogonyaro)

Guan Zhong da Bao Shuya

Guan Zhong da Bao Shuya 'yan siyasa ne na kasar Sin a lokacin Chunqiu wato karni na 7 kafin haifuwar Anabi Isa, su abokan juna ne. Guan Zhong yana da talauci, amma Bao Shuya yana da arziki, amma suna da fahintar juna da amincewa juna. Guan zhong da Bao Shuya sun taba gama kai don yin kasuwanci, Guan Zhong ya fitar da jari kadan, amma ya samu riba da yawa. Amma Bao Zhuya bai yi bakin ciki ba domin ya san yana da nauyin ciyar da iyalinsa, banban da haka ya tambayi Guan Zhong cewa, ko kudin nan ya ishe ka? Guan Zhong ya taba ba da shawarwari har sau da yawa ga Bao Shuya don daidaita al'amuransa, amma ya yi hasara. Ko da ya ke an yi hasara, amma Bao Shuya bai yi fushi ba, kuma ya ce, dalilin da ya sa aka yi hasara ba sabo da shawararka ba ta yi kyau ba, amma sabo da lokaci bai yi ba, kada ka damu. Guan Zhong ya taba zama jami'ai har sau uku, amma duk an tube shi daga kan mukaminsa, amma a ganin Bao Shuya ba sabo da Guan Zhong ba ya da hikima ba, amma sabo da ba wanda ya san hikimarsa ne. Guan Zhong ya taba shiga soja, amma ya gudu daga fagen yaki, amma Bao Shuya bai yi masa ba'a ba, ya ce, ya gudu ne sabo da yana son ciyar da mahaifiyarsa wadda ta tsufa.

Daga bisani Guan Zhong da Bao Shuya duk sun shiga siyasa. A wancan lokaci rikici ya tashi a kasar Qi, domin gudun masifa 'ya'yan sarki duk sun gudu zuwa sauran kasashe don jiran dama. Guan Zhong ya bi yarima Jiu wanda ke zama a kasar Lu, amma Bao Shuya ya bi yarima Xiao Bai da ke a kasar Lv. Ba a jima ba sai an yi artabu a kasar Qi, kuma an kashe sarkin kasar Qi. Da aka ji labarin nan sai yarima Jiu da yarima Xiao Bai sun tashi zuwa kasar Qi don neman hau karagar mulki, kuma sun gamu a kan hanya, da Guan Zhong ya ga haka sai ya harba kibiya ga yarima Xiao Bai domin yana son yarima Jiu ya zama sarki, amma bai kashe shi ba. Daga bisani Xiao Bai ya zama sarki wato Qihuangong.

Da Qiwangong ya zama sarki sai ya matsa wa kasar Lu lamba don ta kashe yarima Jiu, kuma an daure Guan Zhong. Qi huangong ya so ya nada Bao Shuya da ya zama firayim minista don ya tafiyar da harkokin kasa. Amma Bao Shuya ya ce bai cancanci ya zama firayim minista ba. Ya ce, a wajen tafiyar da harkokin kasa, Guan Zhong ya fi ni. Domin yana da kamilanci da kirki, yana da biyaya da amincewa, kuma ya iya tsara tsarin kasa mai kyau, kuma ya iya zama kwamandan sojoji, sabo da haka ni ban kai matsayinsa ba. Idan yallabai kana son tafiyar da harkokin kasa da kyau, dole ne ka nada Guan Zhong da ya zama firayim minista. Qihuangong ya nuna kin yardarsa. Ya ce, Guan Zhong ya taba harbe ni da kibiya don kashe ni. Amma yanzu ban kashe shi ba sabo da kamilancina, yaya zan nada shi da ya zama firayim minista? Sai bao Shuya ya ce, na ji an ce, sarkin kirki ba ya ki jinin wani. Balantana ma an ce, a wancan lokaci ya yi haka ne don nuna biyaya ga mai gidansa. Wannan al'amari ya shaida biyayarsa. In ka nada shi da ya zama firayim minista, shi ma zai nuna kama biyaya. Da ba ka nada Guan Zhong ba, da ba za ka kafa babbara daula ba. Tabbas ne ka nada shi. Daga baya Bao Shuya ya shawo kan Qihuangong, kuma ya karbi Guan Zhong daga kasar Qi.

Bayan da Guan Zhong ya koma kasar Qi ya zama firayim minista, don ta Bao Shuya ya zama mataimakinsa. Bisa kokarin da Guan Zhong da Bao Shuya suka yi tare a wajen tafiyar da harkokin kasa, kasar Qi ta zama kasar da ta fi karfi a cikin kasashen wancan zamani, Qihuangong ya zama shugaban sarakuna.

Bayan da Bao Shuya ya rasu, Guan Zhong ya yi ta kuka ya yi ta kuka a gaban kabarinsa. Da ya tuna da fahinta da goyon bayan da Bao Shuya ya nuna masa sai ya ce, a wancan lokaci yarimar Jiu da na ba shi taimako ya yi hasaram anna Bao Shuya bai yi minbi dariya ba, ya san nufina shi ne yin babban sha'ani. Iyayena ne sun haife ni, amma Bao Shuya ne ya fahince ni.

Irin zumunci mai danko da ke tsakanin Guan Zhong da Bao Shuya ya zama taken da Sinawa ke yi daga zuri'a zuwa zuri'a. A kasar Sin a kan yi amfani da zumuncin da ke tsakanin Guan Zhong da Bao Shuya don siffanata zumunci da amincewa da ke tsakanin abokai. (Dogonyaro)

Chuzhuangwang

Kasar Sin wata kasa ce da a ke iya hakuri, a ganin mutane, hakuri yana iya guji gardama don samu zaman jituwa. Wani karin maganar kasar Sin da a ke cewa, Chuzhuang ya cire igiyoyin hula ya gaya mana cewa, sai da hakuri ne za a daidaita al'amura yadda ya kamata.

A zamanin Chunqiu wato a karni na 7, akwai mahukunta da dama a kasar Sin. Sarki Chuzhuangwang na kasar Chu wani sarki ne mai idon basira, a karkashin mulkinsa ne kasar Chu ta girma daga karama, kuma ta yi karfi.

Wata rana sarkin Chuzhuangwang ya shirya walima domin jami'ansa, matansa da kishiyoyinsa ma sun zo wurin walima don a sha giya da kallo raye raye da wake wake. An yi walimar nan har zuwa dare ya yi, kowa ya yi farin ciki. A lokacin nan sai sarki ya ba da umurnin kunna kandal don ci gaba da walimar nan. Da sarki ya ga kowa ya yi farin ciki shi ma ya yi murna, sai ya umurci kishiyoyinsa biyu da su zuba wa jami'ansa giya.

Ba zato ba tsammani sai iska ta tashi har ta kashe wutar dukkan kandal, wato an yi duhu a walimar. A lokacin nan wata kishiyar sarki mai suna Xu ta ji wani mutum ya taba hannunta. Sai ta yi fushi kwarai, nan da nan ta cire igiyar hularsa, sa'an nan ta je wajen sarki, kuma ta gaya masa cewa, dazo nan wani jami'I ya yi mini iskanci, shi ya sa na cire igiyar hularsa, bayan an kunna wuta, sai ka duba, wanda ba ya da igiyar hula shi ne ya yi mini iskanci, sai ka yanke masa hukunci mai tsanani. Da sarki ya ji haka sai ya ce, kada a kunna wuta, a sha giya cikin duhu ma abin farin ciki ne, sai mu ci gaba da shan giya. Sa'an nan ya tambaya cewa, ko kun yi farin ciki yau, duk mutanensa sun ce, lallai mun yi farin ciki, muna wa sarki godiya. Sai sarki ya ce, da ya ke kun yi farin ciki, sai ku cire dukkan igiyar hularku. Sa'an nan a kunna wuta, da mutane sun ga ba wanda yana da igiyar hula, sai kowa ya yi dariya, sai a ci gaba da shan giya har gari ya waye, sa'an nan kowa ya koma gida.

Da kishiya Xu ta koma fada ta yi fushi kwarai da gaske, ta ce, da gangan ne sarki ya shagwaba wanda ya yi mata iskanci. Kuma ta ce, da ya ke ka yafe masa yau, nan gaba za su yi mugunta da yawa. Sarki ya ce, makasudina na shirya walima shi ne don faranta ran mutanena, in na yanke hukunci ga wani, to, walimar nan ba za ta yi kyau ba.

Daga bisani sarki Chu Zhuangwang ya kai farmaki ga kasar Zheng, wani janar mai suna Tang Jiao ya nuna jaruntaka kwarai da gaske, ya yi aikin bajinta da yawa har zuwa hedkwatar kasar Zheng, sarkin Chu Zhuangwang ma ya yi suna kwarai. Hasali ma janar Tang Jiao shi ne wanda ya taba hannun kishiya Xu. Dalilin da ya sa ya nuna jaruntaka a fagen yaki shi ne don nuna godiya ga sarki sabo da ya yafe shi.

A kan tarihin kasar Sin ana kira wannan walimar da sarki Chu Zhuangwang ya shirya ita ce walimar cire igiyar ruwa. Wannan al'amari ya gargadi mutane cewa, ya kamata a yi hakuri ga kowa da kowa. (Dogonyaro)

Yu Boya da Zhong Ziqi

A zamanin Chunqiu na kasar Sin an yi wani shahararren gwanin kade kade da goge goge, sunansa shi ne Yu Boya. Tun lokacin da ya ke yaro ne yana da wayo kwarai, kuma ya yi sha'awar kade kade sosai, ya roki Cheng Lian, shahararren mai kade kade da ya zama mallaminsa don koya masa ilmin kade kade.

Bayan da ya yi shekaru 3 yana koyon ilmin kade kade, sai Yu Boya ya kware kwarai. Amma ya kan yi bakin ciki domin yana son kai wani sabon matsayi. Da mallaminsa Cheng Lian ya ga haka, ya san abin da ya ke so, sai ya ce, na riga na koya maka dukkan ilmina na kade kade, kuma ka koya. Idan kana son kara ilminka, sai ka je wajen mallamina Fangzichun wanda ya gwanance kwarai a wajen kade kade. Yanzu yana zamansa a wani tsibiri na tekun gabas, bari in kai ka zuwa wajensa don yi koyo a wajensa, da Yu Boya ya ji haka, sai ya yi farin ciki, ya ce, da kyau!

Sun shirya isashen abinci, su dau kwale kwale zuwa tekun gabas. Wata rana kwale kwale ya isa tudun Penglai na tekun gabas. Sai Chen Lian ya gaya masa cewa, sai ka jira a kan tudun nan, ni zan je karbar mallamina, sa'an nan ya tafi cikin kwale kwale. Amma bayan kwana da kwanaki, mallaminsa bai dawo ba, Yu Boya ya yi bakin ciki kwarai da gaske. Da ya duba teku, sai ya ga rakumin ruwa na bugawa, da ya duba cikin dajin tsibirin nan, ya ji tsit, tsuntsaye kawai ke kuka, kamar suna bakin ciki. Da Yu Boya ya ga haka, sai ya kada molo, kade kaden da ya yi yana cike da bakin ciki. Daga nan ne Yu Boya ya kara kwarewa. Hasali ma mallaminsa Cheng Lian ya so ya yi koyo a cikin halitta.

A lokacin da Yu Boya ya ke zamansa a cikin wannan tsibiri, kullum yana tare da teku da daji, lallai ya gane ainihin halitta, kuma ya zama fifitaccen mai kade kaden molo, amma wadanda su ke iya gane kade kadensa kadan ne.

Wata rana Yu Boya ya dau kwale kwale don yin ziyarar yawon shakatawa a cikin kogi. Da kwale kwalensa ya isa gindin wani dutse, sai an yi ruwan sama, sai ya tsaya a gindin tudun nan. Da ya ga wurin nan mai ni'imma cikin ruwan sama sai ya fitar da molo, ya kada abin da ya gani. A lokacin da ya ke kade kade ne, ya ji layin molonsa yana jinjinawa, wannan ya shaida cewa, akwai wanda ke saurara kade kadensa. Da ya fito daga kwale kwalensa ya ga wani mai sare itatuwa Zhong Ziqi yana zaune a cikin daji don saurara kade kadensa.

Da Yu boya ya ga haka, sai ya gayyaci Zhong Ziqi da ya wo kwale kwalensa, ya ce, bari in yi maka kade kade, Zhong Ziqi ya ce, ina son saurara. Sai Yu Boya ya yi kida mai suna Tudu mai tsayi. Da Zhong Ziqi ya saurara ya jiku, ya ce, lallai tudu ne mai tsayi. Yu Boya kuma ya sake yin kidan Ruwan da ke tafiya. Da Zhong Ziqi ya saurara, sai ya ce, lallai ruwan babban kogi na malalawa. Da Yu Boya ya ji maganarsa ya jiku kwarai da gaske, ya gaya masa cewa, a cikin duniyar nan, sai kai ne ka gane muryar zuciyata, daga nan ne sun zama aminan juna.

Sun yi alkawari, bayan da Yu Boya ya gama ziyararsa zai kai ziyarar ban girma a gidansa. Bayan 'yan kwanaki, wato a lokacin da Yu Boya ya gama ziyararsa ya zo gidansa, amma a lokacin nan Zhong Ziqi ya rasu sabo da rashin lafiya. Da Yu Boya ya ji haka, ya yi bakin ciki kwarai da gaske, ya je gaban kabarinsa, ya yi masa kade kade na bakin ciki, sa'an nan ya tsaya ya fasa molonsa a gaban kabarin. Daga lokacin nan ne Yu Boya bai sake yin kade kade ba. (Dogonyaro)

Sun Wu

Sun Wu, shahararren gwanin soja ne na a karni na 6 kafin haifuwar Annabi Isa, littafi mai suna Dokokin soja na Sunzi shi ne littafin soja da ya fi shahara a zamanin da na kasar Sin, har ma ya shahara a duk duniya. Sojoji na gida da waje na zamanin da da zamanin yau duk suna girmama Sun Wu har suna kira shi kakan soja.

An haifi Sun Wu ne a shekara ta 551 kafin haifuwar Annabi Isa, wato zamani ne da a ke yakekeniya don kafa daularsa. Wun Wu dan kasar Qi ne, a lokacin da ya ke da shekaru 19 da haifuwa ne ya je kasar Wu a gabashin kasar Sin, ya karanta littatafan soja a tsanaki a hedkwata kasar Wu. Waziri Wu Zixu na kasar Wu ya gabatar da Sun Wu ga sarkin kasar Wu, Sun Wu ya gabatar da sarki babi 13 na dokokin soja. Bayan sarki ya karanta ya ce, yana da kyau, amma bai sani ba ko zai aiwatar da wadannan dokoki a cikin yaki, sai ya gaya wa Sun Wu cewa, bari mu yi amfani da matan fada don jarraba abin da ka rubuta a cikin littafi.

Wun Wu ya raba mata 180 na fadar sarki da su zama kungiyoyi 2, mata biyu da sarki ya fi sonsu sun zama shugabanni na kungiyoyin nan biyu don su ja ragamar mata da su yi gwaje gwaje.

Sun Wu ya tsaya kan dakalin ba da umurni don gaya wa mata yadda za a yi jarrabawa. Bayan haka, sai Sun Wu ya buga ganga don ba da umurni, amma wadannan matan sarki ba sa bin umurni, sun yi wasa da dariya kawai, sabo da haka kungiyoyin nan biyu sun yi rikici. Ko Sun Wu ya yi ta ba da umurni ma ba wadda ta bi. Da Sun Wu ya ga haka, sai ya ba da umurnin kashe shugabannin nan biyu na matan sarki. Da sarki ya ga Sun Wu zai kashe mata biyu da ya ke so sosai, sai hankalinsa ya tashi kuma ya hana, amma Sun Wu ya ki, bisa dokar soja ce ya kashe wadannan mata biyu, sa'an nan ya sake nada mata biyu da ke a gaba da su zama shugabanni don ci gaba da yin gwaje gwaje. Da Sun Wu ya sake ba da umurni, ba wadda ta yi wasa ko dariya, sun yi gaba da baya duk bisa umurnin Sun Wu. Da sarkin Wu ya ga dabarar Sun Wu ta yi amfani, sai ya daina fushi, kuma ya nada Sun Wu da ya zama janar.

Bisa horon da Sun Wu ya yi ne, sojojin kasar Wu sun kware sosai, a shekarun baya ya ba da taimako ga sarki har zuri'a biyu, kuma ya kan yako nasara a cikin yakekeniya da aka yi.

A shekara ta 482, sarkin kasar Wu ya zama shugaban sarakuna duk sabo da kokarin da Sun Wu ya yi a wajen yi wa sojoji horo.

Bayan da kasar Wu ta yi karfi kuma sarkin kasar Wu ya zama shugaban sarakuna, sai ya fara nuna girman kai, kuma ya fara jin gurma. Da Sun Wu ya ga haka, sai ya ja da baya ya yi zamansa a cikin tuddai. Kuma bisa fasahohin da ya dandana a cikin yakekeniyar da aka yi ya gyara babi 13 na dokokin soja don ya kara kyau.

Ko da ya ke littafi mai suna Dokokin soja na Sunzi yana da babi 13 masu kalmomi dubu 6 kawai, amma sun shaida cikakken tsarin tunanin yaki na Sun Wu, ana kira shi littafi na farko na dokokin soja na duniya, har yanzu ma ana yin amfani da tunaninsa a wajen soja da siya da tattalin arziki. (Dogonyaro)

Qi Jiguang

A tudun Yu na lardin Fujian na kasar Sin akwai wani dakin ibada na Qi Jiguang, masu ziyarar yawon shakatawa su kan zo wurin don nuna ban girma a gaban mutum mutumin jarumi Qi Jiguang mai kishin kasa da tunawa da aikin bajinta da ya yi a wajen yin dagiya da mahara Japanawa.

Qi Jiguang, shahararren janar na kishin kasa ne na sarautar Ming, mahaifinsa ma janar ne, tun lokacin da ya ke yaro ne ya yi sha'awar sha'anin soja sosai, kuma ya kudura niyyar zama wani kwararren soja. A wancan lokaci, gajerun 'yan fashi wato mahara Japanawa su kan kawo fashi, Qi Jiguang ya ki jinin muguntar da gajerun 'yan fashi suka barkata. A lokacin da ya ke da shekaru 16 da haifuwa ne ya rubuta wata waka cewa, abin da na ke so ba don samun mukami ba, amma don shimfida zaman lafiya a tekuna. A lokacin da ya ke da shekaru 17 ga haifuwa, ya gaji mukamin mahaifinsa, wato ya fara aikin soja. Da Qi Jiguang ya kama mukami ke da wuya sai ya gamu da dawainiyar kau da gajerun 'yan fashi.

Mutanen da a ke kira su gajerun 'yan fashi su ne sojojin da suka shiga yakin basasa na cikin gidan Japan har da wasu 'yan iska. A karni na 14, su kan tuka kwale kwale zuwa bakin teku na kasar Sin don yin fashi, su kan karkashe mutane da ta da gobara. A karshen karni na 15, gajerun 'yan fashi sun haukace, har sun shigo cikin kasar Sin don yin wasoso, sabo da haka gajerun 'yan fashi sun zama masifa ga jama'ar tekun kudu maso gabashin kasar Sin.

A shekara ta 1555, da ya ke Qi Jiguang ya kan samu nasara a wajen yin fada da gajerun 'yan fashi, sai sarki ya aike shi zuwa lardin Zhejiang, ya zama janar na Dinghai, inda cibiya ce ta gajerun 'yan fashi. Qi Jiguang ya kafa wata rundunar soja da ke kunshe da manoma da mahakan ma'adinai. Bisa halin da a ke ciki a kudancin kasar Sin wato akwai fadamu da yawa, sai ya samu wata dabarar yaki, wato yin fada da 'yan fashi gaba da gaba. A cikin yakin da za a yi, da farko su kan bude wuta kan makiya, sa'an nan sun harba kibau, idan makiya za su sake kawo hari, sai sun zabura su yi fada da makiya.

Bayan da Qi Jiguang ya yi musu horo, wannan rundunar soja da ke kushe da mutane dubu 4 sun kware, sun samu nasarori da yawa a cikin yakin da aka yi, jama'a sun kaunaci wannan rundunar soja kwarai da gaske, suna kira wannan rundunar soja rundunar Qi.

A shekara ta 1561, gajerun 'yan fashi dubbai sun dau jiragen ruwa fiye da 100 don kai babban hari ga jihar Taizhou ta lardin Zhejian. Da rundunar soja ta Qi Jiguang ta ji labarin, nan da nan sun tashi tsaye su yi fada da makiya har sau 9, duk sun ci karfin makiya. Daga nan gajerun 'yan fashi sun firgita. An ciyar da Qi Jiguang gaba sabo da ayyukan bajinta da ya yi, kuma ya je lardin Fujian don yin fada da gajerun 'yan fashi.

Bisa kokarin da Qi Jiguan da sauran sojoji suka yi, an yi ta samun nasara a wajen yin dagiya da gajerun 'yan fashi. An shimfida zaman lafiya a lardunan da ke bakin teku, kuma an bunkasa tattalin arziki. A cikin yakin kare harin gajerun 'yan fashi na Japan, Qi Jiguang ya yi aikin bajinta na tarihi, kuma ya samu yabo daga wajen jama'a na zuri'a zuwa zuri'a. (Dogonyaro)

Xuan Zang

Wani kagaggen labari mai lakabi haka "Ziyara Zuwa Yamma" littafi ne da kowa ya sani a kasar Sin. A cikin littafin nan, an gabatar da wata tatsuniya dangane da ziyara zuwa yamma da 'yan addinin buddah hudu suka yi don neman ilmin addinin Buddah. Bayan da wadannan 'yan addinin Buddah suka kawar da wahalhalu, sun ga bayan aljanu da shedanu iri daban daban, sun ci nasara daga bisani. Tang Sanzang, daya daga cikin taurari da aka bayyana a cikin wannan littafi, asalinsa shi ne dan addinin Buddah Xuanzang, shahararren manzon al'adu na kasar Sin a can zamanin da.

Xuanzang an haife shi ne a zamanin daular Tang wato a shekara ta 600. Tun lokacin da yake karami, shi haziki ne, kuma ya yi sha'awar addinin Buddah ainun wanda ya samu karbuwa sosai daga wajen jama'a a wancan zamani. Xuanzang ya fara karanta littafin addinin Buddah ne yayin da yake da shekaru 11 kawai. Haka kuma yayin da shekarunsa suka kai 13, sai aka mayar da shi don ya zama dan addinin Buddah a garin Luoyang na kasar Sin wanda shi ne wurin al'adu mai muhimmanci a wancan zamani. Bayan haka ya ziyarci wurare daban daban na duk kasar Sin don neman samun shahararrun malamai, kuma ya yi matukar kokari wajen nazarin hasashen addinin Buddah. Da shekarunsa ya kai 18, sai Xuanzang ya dan shahara a bangaren addinin Buddah.

Yayin da yake samartaka, Xuanzang ya yi kokari kwarai wajen nazarin filosofiyar addinin Buddah, har ma babu wani abu da yake sha'awa, sai filosofiyar nan. Da ya gano cewa, ba a fassara bayanonin addinin Buddah cikin Sinanci daidai sosai ba, sai ya dau niyyar zuwa kasar Indiya, mafarin addinin Buddah don neman kara samun ilmin addinin Buddah.

A shekarar 627, Xuanzang ya tashi daga birnin Changan, fadar gwamnatin daular Tang ta kasar Sin a wancan lokaci wanda shi ne birnin Xi'an a yanzu, ya fara yin doguwar tafiya zuwa kasar Indiya.

Akwai nisa kwarai a tsakanin Sin da Indiya, ba shakka, doguwar tafiya da ya yi da kafa daga tsakiyar kasar Sin zuwa Indiya ya sanya shi wahala kwarai saboda karancin ilmin labarin kasa da ake da shi, kuma harkokin zirga-zirga sun yi baya-baya ainun yau sama da shekaru 1,300 da suka wuce. A lokacin tafiyarsa, ya bi ta hamada da kungurmin daji da manyan duwatsu da kankara ta rufe su a arewa masu yammacin kasar Sin. Amma duk da haka, Xuanzang, cikakken dan addinin Buddah ya haye wahalhalu, ya isa arewacin kasar Indiya daga bisani a yanayin zafi na shekarar 629, daga nan ya je wurare da ke tsakiyar Indiya, inda ya yi ziyarar girmamawa a manyan wurare masu tsarki na addinin Buddah guda 6.

Xuanzang ya fara yin karatu a wani shahararren dakin ibada na kasar Indiya a shekarar 631. Ya shafe shekaru 5 yana kokari sosai wajen karatu, ya karanta kusan duk shahararrun littattafan addinin Buddah. Bayan haka ya sake shafe shekaru 6 yana neman ilmi a wurare daban daban na kasar Indiya, ya taba koyon ilmi daga wajen shahararrun masanan ilmin addinin Buddah sama da 10 daya bayan daya, sabo da haka ilminsa ya karu kwarai, har wa yau shi ma ya zama fifitaccen masanin ilmin addinin Buddah a wancan zamanin da. A gun wani taron muhawara na duk kasar Indiya da aka yi, Xuanzang ya zama jagoran wannan muhawara, ya amsa duk tambayoyi da 'yan addinin Buddah suka yi, daga nan ne ya shahara sosai a bangaren addinin Buddah na kasar Indiya.

Xuanzang ya tashi don komowa kasar Sin ne a yanayin bazara na shekarar 643. Ya koma gida ne tare da littattafai da mutum-mutumi na addinin Buddah da ya tattara a cikin shekaru da yawa da suka wuce. Sarki Tang Taizong na kasar Sin a wancan zamani ya aika da mutanensa don taryarsa. Xuanzang ya ki amincewa da bukatar da sarkin kasar ya yi masa don nada shi kan wani mukami, ya fara zamansa a dakin ibada mai suna Hongfu na birnin Changan. Bisa taimako da sarki Tang Taizong ya yi masa, Xuanzang ya dauki limaman limamai da masanan ilmi daga wurare daban daban don yin ayyukan fassara bayanonin addinin Buddah, bayan haka sun shafe shekaru 19 suna yin ayyukan nan.

Xuanzang ya yi iyakacin kokarinsa wajen fassara bayanonin addinin Buddah, yawan littattafan addinin Buddah da ya fasara ya kai 75 a cikin shekaru 19 da suka wuce, kundayensu kuma ya kai 1,335.

A lokacin da Xuanzang ke yin aikin fassara, kuma yana wa'azin addinin Buddah. Darikar Faxiangzong ta addinin Buddah Xuanzang ne ya kafa ta a cikin tarihin addinin buddah na kasar Sin. Bayan da almajirinsa na Japan ya koma gida, ya yi wa'azin darikar nan a kasar Japan . Haka nan kuma almajirinsa na kasar Korea shi ma ya yi wa'azin darikar nan a kasar Korea .

Ban da littattafan addinin Buddah, Xuanzang ya bayyana wa almajiransa mai suna Bian ji abubuwan da ya yi, ya ji ya gani a lokacin da ta yi ziyara a kasar Indiya don ya rubuta, sun shafe shekara 1 da 'yan doriya sun wallafa wani littafi mai suna "labaran ziyarar Tang zuwa Yamma ". A cikin littafin nan, an rubuta labarun ziyarce-ziyarcen da ya shafe shekaru 10 da 'yan watanni yana yi a sama da kasashe 100 daya bayan daya. Littafin nan ya bayyana abubuwa masu dimbin yawa dangane da canje-canjen tarihi da yankun kasa da asalin kabilu da albarkatun kasa da kayayyaki da yanayi da al'adu da kula siyasa da sauransu na kasashen nan daban daban. Ya zuwa yanzu dai , littafin ya zama ajiyayyun bayanonin tarihi da na labarun taswira na zamanin da da ake yin nasari a kai a kasar Afghanistan da Pakistan da Indiya da kuma duk tsakiyar Asia. Tun daga karni na 19, an riga an fassara littafin nan cikin Faransanci da Japanci da Jamusanci da kuma sauran harsunan waje. Masu binciken tsofaffin kayayyaki na zamanin yanzu sun yi bincike-bincike a kan tsofaffin wuraren al'adu na tsohuwar Indiya da tsakiyar Asiya bisa abubuwa da aka rubuta a cikin wannan littafi, kuma sun sami sakamako mai yalwa. An mayar da al'adun Xuanzang bisa matsayi mai muhimmanci a cikin tarihin al'adun Sin da na gabas. Ba ma kawai an dauke shi bisa matsayin fifitaccen mai fassara da mai hasashen ilmin addinin Buddah a kasashen duniya ba, har ma shi mashahurin mai yawace-yawace ne na kasar Sin a zamanin da. Ya taba yin tafiye-tafiye mai nisan kilomita 25,000, ya ziyarci kasashe 110 a cikin shekaru 17 da suka wuce, lallai wannan ba safai a kan iya ganin haka ba a tarihin duniya. Tun da farko, an riga an amince da littafin da aka wallafa kan ziyararsa kamar wani shahararren littafin duniya ne mai girma.

Labarun Xuanzang sun ba jama'a al'ajabi sosai a zamanin da, kuma ya jawo hankulan mashahuran masana na zamanin dauloli daban daban na kasar Sin. Tun daga zamanin daular Tang, mashahuran masana sun fara mayar da labaurnsa don suka zama tatsuniyoyi, an wallafa wani kagaggen littafi mai lakabi haka " labarun neman ilmin addinin Buddah da Xuanzang ya yi a zamanin babbar daular Tant" a zamanin daular Song, bayan haka an wallafa wani littafin tatsuniyoyi da ke a karkashin lakabi haka "Ziyarar Zuwa Yamma" a zamanin daular Ming. Yau sama da shekaru 1,000 ke nan, labarun Xuanzang kowa ya sani ne, kuma ana sha'awarsu ainun. (Halilu)

Jian Zhen

Jian Zhen, mutumin gundumar Jiangyang ta birnin Yangzhou na lardin Jiangsu da ke a gabashin kasar Sin, kuma an haife shi ne a wani iyalin 'yan buddah. A shekarar 708 yayin da Jian Zhen yake da shekaru 21 da haihuwa, an mayar da shi don ya zama limanin addinin Buddah. Daga wannan lokaci, ya yi ta yin wa'azi, ya gina gidajen ibada, ya yi mutum-mutumin addinin Buddah har cikin shekaru 40 da suka wuce, 'yan addinin Buddah wadanda ya taba mayar da su don su zama limamai sun wuce 40,000. Daga baya dai da yawa daga cikinsu sun zama shahararrun limaman limamai. Sabo da haka an dauke shi bisa matsayin babban malami da ke mayar da 'yan addinin Buddah don su zama limamin limamai a gabashin kasr Sin, ya sami girmamawa sosai daga wajen 'yan addinin Buddah, kuma ya zama daya daga cikin manyan ginshikan addinin Buddah.

Limaman kasar Japan biyu sun je birnin Yangzhou a shekarar 743, sun gayyaci Jian Zhen don ya yi wa'azi a kasarsu, Jian Zhen ya yi farin ciki da karbar gayyatar nan, kuma ya yi shirin zuwa kasar Japan. A inuwarsa, shi da almajiransa 21 sun je kasar Japan. Amma a karo na farko, ba su sami damar zuwa kasar Japan ba sabo da katsalandan da hukumar ta yi musu.

A karo na biyu, bayan da Jian Zhen ya sayi jiragen ruwan yaki da mutum-mutumin addinin Buddah da sauran kayayyakin addinin Buddah da magungunan sha da hatsi masu yawa, ya tashi daga babban yankin kasar Sin cikin jiragen ruwa tare da almajiransa da sauran mutane 85 cikin wani dan lokaci, sai kwaram guguwa ta tashi, ta lalata jiragensu, ta haka ya ga tilas su komo gida su yi wa jiragensu kwaskwarima. Bayan da suka gama kwaskwarima, ya sake tashi daga babban yankin cikin jiragen ruwa, amma da tashinsu ke da wuya, sai jiragensu suka ci karo da dutse da ke cikin teku, suka sake yin hasara.

Ko da yake Jian Zhen ya yi hasara har sau uku, amma duk da haka niyyarsa bai karya ba. Ya sake yin shirin tashi zuwa kasar Japan ne a shekarar 744, amma ya sake cin hasara saboda kiyewa da gwamnatin ta nuna masa. A lokacin da Jian Zhen ke da shekaru 61 da haihuwa a shekarar 748, ya sake tashi daga birnin Yangzhou zuwa kasar Japan a karo na hudu, amma daga bisani bai isa kasar Japan da yake kokarin zuwa ba, maimakon haka ya isa wuri da ke kudancin tsibirin Hainan a kudancin kasar Sin sabo da guguwa mai karfin gaske. Da ganin haka sai ya koma birnin Yangzhou. Bayan haka ya sake cin hasara a karo na biyar. Ya yi babbar hasara a wannan gami, wani limamin kasar Japan da wani almajirin Jian Zhen mai suna Xiang Yan sun mutu daya bayan daya, bayan da suka yi fama da ciwo, Jian Zhen shi ma ya zama makaho sabo da matsanancin aiki da ya yi.

Bayan shekaru 5, ko da yake makafo Jian Zhen ya taba cin hasara har sau biyar, amma ya sake daura niyyar zuwa kasar Japan cikin jirgin ruwa. Wannan makaho limanin limaman addinin Buddah ya sake tashi daga birnin yangzhou ne a ran 19 ga watan Oktoba na shekarar 753, ya sauka a kasar Japan a ran 20 ga watan Disamba na shekarar. Da saukarsa a kasar Japan, ya sami karbuwa sosai daga wajen limamai masu rike da mulki da kuma limamai 'yan hamayya. Nan take ba da dadewa ba, sai gwamnatin Japan ta bayar da umurni a kan bai wa Jian Zhen ikon mayar da 'yan addinin Buddah don su zama limamai, kuma ta gina dakin ibada wadda ke karkashin jagorancinsa. Gwamantin Japan ta nada Jian Zhen don ya zama babban limamin limamai ne a shekarar 756. Irin wannan nadi ba a taba ganin irinsa ba a da. Bisa kokari da suka yi cikin hadin guiwa, Jian Zhen da almajiransa su ne suka gina wani babban dakin ibada wanda yanzu ya shahara sosai a kasar Japan. Babban limamin limaman addinin Buddah Jian Zhen ya bakunci lahira ne a watan Mayu na shekarar 763 yana da shekaru 76, kuma an binne shi a kasar Japan.

Jian Zhen ya shafe shekaru 10 yana zama a kasar Japan, ya ba da babban taimakonsa ga bunkasuwar al'adun kasar Japan da musaye-musayen al'adu da aka yi a tsakanin Sin da Japan. A lokacin da Jian Zhen ke kokarin zuwa kasar Japan, an yi ta bunkasa harkokin al'adu sosai a kasar Sin. Sabo da haka Jian Zhen ya isa kasar Japan ne tare da kwararru a fannin aikin surfani da sassakar duwatsu masu daraja da kuma kayayyakin al'adu na kasar Sin masu dimbin yawa wadanda suka hada da zane-zane da abubuwan surfani da maduban tagulla da makamatansu. Irin wadannan sakamakon al'adun kasar Sin da Jian Zhen ya kai wa kasar Japan sun zama wani kashi ne ga al'adun Tianping na kasar Japan. Ginshikin irin wannan al'adun kasar Japan shi ne al'adun addinin Buddah. Jian Zhen ya ba wa kasar Japan babban taimakonsa ne ta fuskar addinin Buddah. Game da fasahar gina dakunan ibada, babban dakin ibadan da Jian Zhen ya gina bisa tsarin dakin ibada na kasar Sin ya zama misalin dakunan ibada da aka gina a kasar Japan.

Ban da wadannan kuma Jian Zhen ya kai wa kasar Japan ilmin likitancin kasar Sin. Ya taba ba da magani ga sarauniyar kasar Japan. Ko da yake shi makaho ne, amma ya kan ba da magunguna ga masu ciwo yadda ya kamata.

Jian Zhen ya shafe shekaru 10 yana ta yin kokari wajen kara dankon aminci da ke tsakanin jama'ar kasar Sin da ta Japan, lallai ya yi aikin bajinta da ba a iya goge shi ba wajen yin ma'amalar al'adu tsakanin Sin da Japan. Yayin da Marigayi Deng Xiaoping, mataimakin firayim ministan kasar Sin ya kai ziyara a babban dakin ibada da Jian Zhen ya gina a kasar Japan a shekarar 1973, ya amsa tambayar da dattijon wannan dakin ibada ya yi masa don neman komar da mutum mutumin Jian Zhen gida cikin wani gajeren lokaci. Mutum-mutumin Jian Zhen da aka nuna a birnin Yangzhou a ran 19 ga watan Afrilu na shekarar 1980 ya sami karbuwa sosai daga wajen mutane masu dimbin yawa.