logo

HAUSA

Babi16: Tatsuniyoyin Jama'a

2020-10-30 10:13:35 CRI

Babi16:Tatsuniyoyin Jama'a

>>[Tatsuniyoyi]

Labarin Sui Ren wanda ya samu wuta ta hanyar murza itace

Cikin tatsuniyoyin da ake bayarwa a tsakanin al'ummar kasar Sin, a kan yi bayani kan jarumai masu ilimi da janhali wadanda ke kokarin nemawa jama'a jin dadin zamansu. Sui Ren, shi ne daya daga cikinsu.

A shekarar aru aru, 'yan Adam suna cikin duhun kai, ba su san wuta ba, kuma ba su san yadda ake amfani da ita ba. Da dare, ya yi duhu kirin a ko ina, naman daji suna ta ihu. Mutane sun cunkusa a gu daya, suna jin sanyi suna tsoro. Sabo da rashin wuta, su kan ci danyen abinci. Wannan ya sa su kan kamu da cututtuka, kuma ransu a gajere ne yake.

Ganin 'yan Adam suke zama a cikin wahala, Fu Xi, wani babban mala'ika yana jin tausayinsu, yana so ya wayar da 'yan Adam da kansu game da wuta. Shi ya sa ya yi dabo, ya sa aka yi ruwa da tsawa a cikin daji. Tare da tsawa, akwai walkiya, kuma ta sa wani itace ya kama wuta. Da mutane suka ga tsawa da walkiya da kuma wuta, suna tsoro sosai har suna gudu a ko ina. Nan ba da dadewa ba, an daina ruwa, mutane sun taru a gaban itacen, suna kallon wuta cikin tsoro. Daga baya wani saurayi ya gano cewa, ba a iya jin ihun da naman daji su kan yi ba. Yana tsamanin cewa, ' Ko naman daji suna tsoron wannan abu mai haske ( ba ya san sunan wuta ba a lokacin) ? ' Ya matso kusa domin yin bincike kan wuta, sai ya ji dumi. Tare da farin ciki, ya yi kira ga 'yan uwansa cewa, ' Ku zo, abun na da dumi, kada ku ji tsoro.' Sa'an nan, wasu mutane sun tarad da gawawwakin dabbobin da wuta ta kona su su mutu na da kamshi. Sun dandana naman dabbobin, sai su ga yana da dadinci. Shi ya sa, sun fara sanin darajar wuta, sun tsinci itace sun kona shi a kan wuta, har itacen ya kamu da wuta, sai su ajiye iccen a cikin gida. Ko wace rana akwai wani mutum wanda ya mai da hankalinsa a kan iccen, domin kada wuta ta mutu. Ana nan cikin haka, sai wata rana, mutumin mai tsaron wuta ya shiga barci, wuta ta kone itacen, ta mutu. Mutane sun sake faduwa a cikin duhu da sanyi, suna bakin ciki kwarai.

Babban mala'ika mai suna Fu Xi ta ga abin da ya auku, sai ya shiga cikin mafarkin saurayin wanda ya fara sanin amfanin wuta tun da farko, ya gaya masa cewa, ' Ya kasance da wata kasa mai suna Suiming a can yamma, kuma a kasar za a iya samun irin wuta, dai dai kamar iri na itace.' Da saurayin ya farka, ya tuna da maganar Fu Xi, sai ya tsai da niyyar neman samun irin wuta a kasar Suiming.

Saurayin ya hawa manyan duwatsu, ya ketare babban kogi da kungurmin daji. Bayan shan wahaloli da yawa, ya isa kasar Suiming. Amma a wurin nan babu rana, ana duhu a ko ina. Ko haske ma babu, balle ma wuta. Saurayin yana bakin ciki kwarai, sai ya dogara kan wani itace mai suna Sui, ya huta. To, yana cikin halin nan ne, sai ba zato ba tsamani ya ga walka. Ya yi tsalle ya tashi, ya nemi a ko ina domin neman samun inda ake walka, sai ya tarar da wasu tsuntsye da ke kan itacen. Lokacin da suka yi koto a kan icce, za a ga walkar haske. Da saurayin ya ga haka, sai ya tsinci wasu kararen iyace, karama da babba. Ya murza karamar kara a kan babban kara, sai karar ta fitar da hayaki, ta kamu da wuta. Saurarin nan ya ji murna sosai, ya zuba ruwa a kasa ya sha domin murna.

Da saurayin ya koma gidansa, ya koyar wa ko wane mutum yadda za a samu wuta, daga baya 'yan Adam sun bar sanyi da duhu. Domin jin kaunar wannan saurayi, an nada shi a kan mukamin shugaba, kuma an fara kiransa Sui Ren, wato mutum da ya samu wuta.

Labarin tsoffin sarakunan kasar Sin

Cikin dogon tarihin kasar Sin, da sarki ya tsufa ya rasu, dansa zai gaji mukaminsa, kullum kamar haka yake har tsawon shekaru dubu. Amma bisa tatsuniyar kasar Sin, an ce, farkon sarakuna 3 na kasar Sin, wato Yao, Shun, Yu. Su uku ba dangi ba, balle ma iyali. A lokacin can, duk wanda ke da kirki da ilimi, za a ba shi gadon mukamin sarki.

Yao sarki na farko ne na kasar Sin. Da ya tsufa, yana so ya nemi wani da zai gaje shi, shi ya sa ya kira taro, ya yi tattaunawa da shugabannin kabilu na wurare dabam daban.

Da Yao ya gaya wa mutane nufinsa, wani mutum mai suna Fang Qi ya ce, " Danka Dan Zhu mutum ne mai wayin kai, ya dace da gadon mukaminka. " Yao ya ce, " A'a, dana ba shi da kirki, ya kan yi cacar baki da mutum ". Mutum daban ya ce, " Gong Gong mai kula da aikin ruwa yana da kwarewa." Yao ya ce, "Gong Gong yana da bakin ganga, ban amince da da shi ba." Tattaunawar da suka yi ba ta samu sakamako ba, Yao ci gaba da neman mutum da zai gaje shi.

Watanni suka wuce, Yao ya kirawo shugabannin kabilu domin su sake yin tattaunawa. Wasu daga cikinsu sun gabatar da wani saurayi mai suna Shun. Yao ya ce, " Na san sunan mutumin, kuma na ji an ce yana da kirki. Sai ku kara yi mana bayani kan saurayin nan." An yi bayani cewa, baban Shun, wanda ake kiransa Gu Sou ( wato tsohon makaho) mutum ne maras hankali. Mamansa ta rasu , uwar rana tasa ba ta yi masa abin kirki ba. Kanensa da uwar rana ta haifa ake kiransa Xiang, shi mutum ne mai girman kai, amma babanda na kaunar Xiang kwarai. Duk da cewa yana zama a cikin iyali maras kyau, amma ya kan yi abin kirki ga babansa da uwar rana tasa, da kanensa. Shi ya sa, ana ganin cewa shi mutum ne mai kirki.

Da Yao ya ji labarin Shun, yana so ya yi masa bincike. Shi ya sa ya aurad da shi da 'yansa biyu, Er Huang da NU Ying. Ban da wannan kuma, ya kafa masa rumbu, ya ba shi shanu da awaki da yawa. Da uwar rana tasa da kanensa sun samu labari, suna kishinsa kwarai. Shi ya sa sun yi makarkashiya tare da Gu Sou, suna neman kashe Shun, yadda za su samu arzikinsa.

Wata rana, Gu Sou ya bukaci Shun da ya je gyara rumbu. Da Shun ya hawa kolin rumbun da tsani, Gu Sou ya kunna wuta kan rumbun, yana neman kone shi har ya mutu. Da Shun ya ga wuta, sai ya fara neman tsani, amma an riga an cire shi. Ana cikin halin nan ne, sai ga shi Allah yana jin kai mutum mai kirki, Shun yana tare da manyan huluna 2. Ya yi amfani da huluna kamar fikafikai, ya daka tsalle, ya sauka, ko kadan bai ji rauni ba.

Sai Gu Sou da Xiang sun bukaci Shun da ya je haka rijiya. Da Shun ya dinga hakawa ya shiga cikin rami, sai Gu Sou da Xiang sun jefa duwatsu cikin rami, domin neman binne shi a ciki. Amma, Shun yana da hikima, da ya shiga cikin rami sai ya haka wata hanya a kan bangon rami, ya fita ta wannan hanya, ya koma gida.

Xiang bai sani cewa Shun ya riga ya tsira ba, ya koma gida cikin murna, ya ce wa Gu Sou, "Tabban ne wana ya mutu, gaskiya ne ina da dabara. Yanzu bari mu raba arzikinsa." Sai ya nufi dakin Shun, da ya shiga, sai ya tarar da Shun ke buga molo a kan gado. Xiang ya ji mamaki da kunya, ya ce, " Kai, ina begenka."

Shun kuma ya nuna kamar ba abin da ya faru, ya ce, " Ka zo, ina shan aiki, kuma ina bukatar taimakonka." Bayan faruwar wannan batu, Shun ya ci gaba da yin abin kirki ga iyalinsa, Gu Sou da Xiang su ma su ji tsoronsa, ba su sake yunkurin kashe shi ba.

Bayan yin bincike da yawa, Yao yana ganin cewa Shun mutum ne mai kirki da kwarewa na gaskiya. Sai ya ba shi mukaminsa, wato ya nada masa zuwa mukamin sarki. Shi kansa kuwa, ya yi murabus.

Da Shun ya zauna kan karagar mulki, ya ci gaba da zamansa cikin himma da kwazo, ya kan yi aiki tare da farar hula. Jama'a suna kaunarsa sosai. Da Yao ya rasu, Shun yana so ya mika mukaminsa ga Dan Zhu, dan Yao, amma jama'arsa ba su yarda ba. Da Shun ya tsufa, ya zabi Yu wanda ke da kirki da kwarewa da ya zama mai gado, kamar yadda Yao ya yi.

Ana da imani cewa, a lokacin mulkin Yao, Shun, da Yu, an kasa samun rikici da arangama a duk kasar Sin, sarki yana zama cikin jin dadi da tsimin kudi kamar farar hula suke.

Labarin duwatsun aljanu biyar

Bayan da babbar mala'ika Nu Wa ta kera mutane, suna zamansu lami lafiya. Ana cikin halin nan ne, sai wata rana, ba zato ba tsamani, sama ya yi karo da kasa. Sama ya tsage, yayin da kasa ma ta rushe. Wuta ta fito daga cikin kasa ta kone kungurmin daji, ruwa ya sauka daga can sama ya kwashe manyan duwatsu. Fatalwoyi da namun daji su ma suka fita, suna adabar mutane a ko ina. 'Yan Adam suna cikin halin kaka nika yi.

Da Nu Wa ta ji ihun mutane na neman taimako, ta tashi tsaye, ta kashe fatalwoyi da namun jeji, ta dakatar da ruwa. Daga baya ta fara yin wa sama faci.

Nu Wa ta tara makamashi a wurare dabam daban, ta jigilar da su a karkashin inda sama ya tsage, kuma ta tila su har sun zama tarin da tsayinsa ya kai can sararin samaniya. Daga baya ta fara neman duwatsu masu launin shudi kamar sama. Sabo da babu irin wannan duwatsu da yawa a kasa, ta tara sauran duwatsu masu launin fari da rawaye da ja da baki. Daga baya ta ajiye wadannan duwatsu a kan kolin makamashi. Ta yi amfani da wuta da ta fito daga cikin kasa, ta kunna makamashi. Wuta ta tashi kwatsam, ta haskaka duk duniya. Duwatsun da ke kan tarin makamashi sun fara narkewa, suna malalowa a inda sama ya tsage kamar ruwa. Kafin makamashi sun kone, an gama aikin yin wa sama faci.

Ko da yake Nu Wa ta yi faci ga sama, amma ta kasa mayar da shi kamar a da yake. Sama ya karkata zuwa arewa maso yamma, ta yadda rana da wata su ma sun gusa zuwa can arewa maso yamma, yayin da kasa ma ta rushe a kudu maso gabas ta zama wani rami, shi ya sa ruwan da ke cikin koguna shi ma ya fara malalowa zuwa can, ya taru a cikin ramin, ya zama teku.

A can gabas na tekun Bohai, ya kasance da wani babban rami, wanda ake kira, "Guixu". Ruwan kogi da ruwan teku dukansu na kwarara zuwa cikin ramin. Duk da haka, ruwan da ke cikin ramin ba ya karuwa, kullum yana nan kamar yadda yake. Shi ya sa, bai taba haddasa ambaliya a duniya ba.

Cikin babban ramin Guixu ya kasance da duwatsun aljanu biyar. Ko wane daga cikinsu tsayinsa ya kai kilomita dubu 15, tazarar da ke tsakaninsu ta kai kilomita dubu 35. A kan wadannan duwatsu an gina manyan gine-gine na zinariya, inda aljanu da yawa ke zaune a ciki.

Dabbobin da ke kan duwatun dukansu nasu launin fari ne. Itatuwan da ke kan tsaunukan su kan ba da 'ya'ya mai dadin ci, wadanda idan mutum ya samu, ya ci, zai samu dogon rai, har ba zai mutu ba. Aljanun da ke zaune a kan duwatsun su kan sa fararen tufafin, kuma suna da fikafikai a bayansu. Su kan yi shawagi a sararin sama, suna kaiwa da dawowa a tsakanin duwatsun, domin kai wa dangogi ziyara. Suna jin dadin zamansu.

Amma, akwai wani dan batun da ke addabarsu. A hakika kuma, wadannan duwatsu suna yawo kan ruwa, ba su da tushe. Shi ya sa, idan an gamu da iska mai karfi, za su yi tafiya a cikin ruwa. Wannan ya kan kawo wa aljanun matsala da wahala. Sabo da haka, sun je neman taimako a wajen sarkinsu. Sarkin aljanu shi ma yana tsoron kada duwatsun su dinga yawo har su kai bangon duniya, ta yadda aljanun za su zama 'yan kaka gida. Shi ya sa ya bukaci aljani mai kula da teku da ya aike da manyan kififiyu 15 don su goya wadannan duwatsu biyar. Duwatsun sun samu tushe, aljanu suna murna kwarai.

Amma, wata rana, wani kato dan kasar Longbo ya je Guixu domin kamun kifi. Ya kama manyan kififiyu 6 da kugiyarsa, ya kwashe su zuwa gida. Wannan ya sa tsaununuka 2 suka nutse a cikin ruwa. Aljanun da ke kan duwatsun 2 dukansu sun tsira da rayukansu. Sun yi kaiwa da dawowa domin kaura daga wannan gida zuwa waccan, sun gaji sosai.

Da sarkin aljani ya samu labarin, ya ji fushi sosai. Ya canja mutanen kasar Longbo, wadanda a da katti ne, zuwa masu kananan jukuna, domin maganin sake ta da rikici. Sauran duwatsu 3 kuma suna can kan bayan kififiyu, ba wani abin da ya same su. Har yanzu suna cikin tekun da ke gabas da kasar Sin.

Labarin Pan Gu wanda ya halicci sama da kasa

An ce a can can can da, babu sama, balle ma kasa. A lokacin duniya ta kasance kamar wani kwan kaza. Kuma a cikin kwan nan akwai duhu dulum, ko tafin hannu ma ba a iya gani. An kasa ganin gabas da kudu da yamma da kuma arewa. A cikin kwan, akwai wani jarumi mai girma, wato Pan Gu, wanda wai ya halicci sama da kasa. Bayan shekaru dubu 18, Pan Gu ya farka daga barci. Ya bude ido, sai ya ga duhu dulum. Ya ji zafi kwarai, har ba ya iya shakar iska. Yana so ya tashi, amma bawon kwai ya kulle shi a ciki, ko mika hannu ma bai iya yi ba. Ya yi fushi sosai, sai ya dauki wani gatari, ya sare bawon kwai da karfi. Sai ya ji tsawa, bawon kwai ya tsage, abu maras nauyi da ke cikin kwai ya tashi ya zama sama, yayin da abu mai nauyi da ke cikin kwai ya nitse ya zama kasa.

Bayan da ya kafa sama da kasa, Pan Gu ya yi murna sosai. Amma yana tsoron kada sama da kasa su sake hadewa tare. Sai ya dauki sama da hannu, ya taka kasa a karkashin kafa, ya fara dabon kara tsayin kansa. Ko wace rana tsayinsa ya kara mita goma, sai tazarar da ke tsakanin sama da kasa ita ma ta kara mita goma. Yana nan cikin wannan hali, sai bayan shekaru dubu 18, Pan Gu ya zama wani katon da tsayinsa ya kai kilomita 4500. Sai bayan shekaru dubbai, sama da kasa sun zama cikin halin karko, ba za su sake hadewa ba, sa'an nan Pan Gu ya kwantar da hankalinsa. Amma ya riga ya ji gajiya sosai, ba ya da karfi ya mike tsaye, jikinsa ya fadi kwatsam.

Lokacin da Pan Gu ya mutu, jikinsa ya canja. Idon hagu ya zama rana, yayin da idonsa na dama ya zama wata. Numfashinsa ya haifar da iska da gajimare. Muryarsa ta zama tsawa. Gashin kansa da gemunsa sun zama taurarin da ke can sama. Kansa da hannayensa da kafafuwansa sun zama manyan duwatsu. Jininsa ya zama koguna da tekuna. Namansa ya zama noma. Fatansa da gashin jikinsa sun zama itattuwa. Kasusuwansa sun zama albarkatun kasa. Guminsa ya zama ruwa. Shi ya sa aka fara samun duniyarmu.

Labarin Nu Wa wadda ta halicci 'yan Adam

Wa ya hallici Bil Adama. Bisa tatsuniyar kasar Sin, an ce, wata gunkiya mai suna Nu Wa, wadda ke da jikin mace da wutsiyar maciji, ta hallici 'yan Adam.

An ce, bayan da babban jarumi Pan Gu ya hallici sama da kasa, Nu Wa tana yawo a tsakanin sama da kasa. A lokacin, a kan kasa ya riga ya kasance da duwatsu da koguna da ciyayi da itatuwa. Tsuntsaye da naman daji da kwari da kifaye su ma suna zama a kan doron kasa. Amma, duk da haka, duk duniya ta kasance cikin hali mai gundura, domin babu 'yan Adam. Wata rana, lokacin da Nu Wa ke yawo a kan makekiyar kasa, ta kasance cikin kadaici. Tana so ta kara wa duniya wasu abubuwa masu ban sha'awa.

Nu Wa tana son itatuwa da ciyayi da kuma furanni, amma ta fi kaunar tsuntsaye da naman daji da kwari da kifaye wadanda suka fi ban sha'awa. Amma bayan da ta yi bincike kan wadannan halittu, tana ganin cewa, wadannan namun daji ba su da hikima kamar yadda take so ba. Tana so ta hallici halittu da suka fi hikima da nagarta.

Wata rana, Nu Wa tana yawo a gaban Rawayar Kogi, sai ta ga inuwarta da ke cikin ruwa, nan da nan ta ji murna domin ta sami wata dabara mai kyau. Tana so ta yi amfani da yumbun da ke cikin kogi, ta hallici mutum a bisa kamanta. Sai ta kwaba yumbu ta fara kera mutum-mutumi. Wannan mutum-mutumi ya yi kama da kanta, amma ba shi da wutsiyar maciji. A madadin haka, ta kera masa kafafuwa. Bayan da ta gama aiki, ta hura iska ga mutum-mutumin, sai ya samu rai. Ya zama wata halitta wadda ke da hikima sosai, kuma yana iya tafiya, har ma da magana. Nu Wa ta nada masa suna 'Mutum'. Sai ta ci gaba da kera sauran mutane. Wasu daga cikinsu, ta hura musu iskar namiji a cikin jikunansu, don haka sai suka zama maza. Wasu kuma suka samu iskar mace, suka zama mata. Wadanna mutane, maza da mata, sun kewaya mamarsu, Nu Wa, suna rawar jiki, suna ihu, sun kawo abubuwa masu ban sha'awa ga duniya.

Nu Wa tana so ta kera mutane da yawa, har su yadu a ko ina a duk duniya. Amma ta ji gajiyar kwaba yumbu, kuma wannan dabara ba ta da sauri. Sai ta fara neman wata sabuwar hanya. Ta dauki wata igiya, ta tsoma ta a cikin ruwan kogi. Bayan da igiyar ta shiga cikin tabon kogi, sai ta jawo igiyar, ta yarfa, kasa ta bazu a ko ina. Da kasa ta sauka a kan kasa, sai ta zama mutum. Ta wannan hanya, Nu Wa ta kera mutane da yawa, har suka bazu a ko ina a duk duniya.

Sai Nu Wa ta fara tunani kan yadda za a sa wadannan mutane su ci gaba da kasancewa a cikin duniya. Ka sani ko wane mutum na da ajalinsa, da wani ya mutum, sai a kera wani, wannan zai haddasa rashin jin dadi. Shi ya sa, Nu Wa ta mayar da namiji daya da mace daya su zama miji da mata, ta yadda za su haifi yara, wadanda za su gaje su. Ta haka, Mutane suka ci gaba da kasancewa a kan duniya, zuriya bayan zuriya, kuma suna ta karuwa.

Labarin soyayya na Niu Lang da Zhi Nu

Niu Lang wani saurayi ne mai farin ciki, ba shi da kome sai wani bijimi da garma guda. Ko wace rana ya yi aikin noma a cikin gona, da ya koma gida sai ya dafa abinci da kuma wanke tufafi da kansa. Amma wata rana, abin ban mamaki ya faru.

A ran nan da Niu Lang ya shiga kofar gida, sai ya ga an riga an tsabtace dakinsa, kuma an wanke dukan tufafinsa. Har ma akwai abincin da aka dafa a kan teburi. Amma, ba wanda ke cikin gida. Niu Lang ya ji mamaki kwarai, bai san dalilin da ya sa haka ba.

Bayan haka, kwanaki da yawa sun wuce, kuma ko wace rana da Niu Lang ya koma gida, sai ya ga tsabtatacen daki da abincin da aka dafa masa. Niu Lang yana so ya yi bincike kan abin da ya faru. Sai wata rana, da sassafe ya bar gida kamar yadda kullum ya kan yi a ko wace rana. Amma bai nufi gona ba. A madadin haka, ya boye a gaban gidansa, yana leken abin da zai faru.

Ba da dadewa ba, sai ya ga wata budurwa mai kyaun gani. Ta shiga gidansa kai tsaye, ta fara aikin gida. Ganin haka, Niu Lang ya fito daga wurin da ya buya, ya tambaye ta cewa, 'An gaishe ki budurwa mai kyaun gani, me ya sa kike taimako ni wajen aikin gida ?' Budurwar ta razana, kuma ta ji kunya. Ta yi magana da karamar murya, ta ce, 'Sunana Zhi Nu. Na ga kana zama cikin kadaici da shan wahala, shi ya sa na zo taimake ka.' Niu Lang ya ji murna kwarai da gaske, sai ya ce, ' Sai ki aure ni, bari mu yi aiki tare da zama tare, mu debe wa juna kewa.' Zhi Nu ta yarda. Daga baya, Niu Lang da Zhi Nu sun yi aure sun zama miji da mata. Ko wace rana, Niu Lang ya je aiki a cikin gona, Zhi Nu sai ta yi aikin saka a cikin gida. Bayan shekaru, sun haifi yara 2, namiji daya, mace daya. Suna jin dadin zamansu.

Suna nan cikin halin, sai wata rana, ana iska kuma ana hadari a can sama. Aljanu biyu sun sauka daga sama, sun zo gidan Niu Lang. Sun sanar da shi cewa, Zhi Nu jika ce ta sarkin aljanu. Shekarun da suka wuce ta bar gida ba tare da izini ba, daga baya sarkin aljanu na ta kokarin nemanta. Daga baya, aljanun 2 sun kama Zhi Nu, sun kai ta sama.

Niu Lang ya rungume yaransa, yana bakin ciki kwarai. Ya lashi takobin cewa zai nemi matarsa, da kuma dawo da ita gida. Amma, yaya mutum zai iya hawa can sama ?

Ganin Niu Lang na bakin ciki kwarai, har yana neman kashe kansa, tsohon bijiminsa ya yi magana cewa, 'Mai gida, sai ka kashe ni, ka shiga cikin fatata, za ka iya yin shawagi.' Niu Lang ba ya so ya kashe bijiminsa, amma bijimin ya yi ya yi har Niu Lang ya yarda. Domin Niu Lang shi ma ya sani, ba ya da sauran hanyar da zai bi domin ceton Zhi Nu. Shi ya sa tare da hawaye a cikin idanunsa, ya kashe tsohon bijimin.

Niu Lang ya shiga cikin fatan bijimin, ya dauki yaransa biyu, ya tashi zuwa can sama. Amma ba a yarda ya shiga cikin fadar sarkin aljanu ba. Sarkin aljanu ya ki yarda da shi da ya sadu da Zhi Nu.

Niu Lang da yaransa suna ta rokon sarkin aljanu, suka gurfana a gaban sarkin aljanu, suka yi kuka, har a karshe dai sarkin ya yarda da su sadu a cikin dan lokaci. Da Zhi Nu ta fito daga cikin gidan yari, ta ga mijinta da yaranta, ta ji murna kwarai da gaske, tana ta kuka, har ta kasa magana. Amma, lokaci ya wuce cikin sauri, an kama Zhi Nu, za a sake mai da ita cikin gidan yari. Niu Lang ya bi ta yana gudu, sauran kadan zai kama hannunta. Amma matan sarkin ta cire fin da ke cikin gashin kansa, ta shata layi a tsakanin Niu Lang da Zhi Nu. Sai layin nan ya zama babban kogi. Niu Lang da Zhi Nu, daya ya tsaya a gefe nan, daya ma a gefe can, suna hangen juna, amma ba za su sadu da juna ba. Daga baya, shekara da shekaru, Niu Lang da Zhi Nu ba su iya gamuwa da juna ba, ban da ran 7 ga watan Yuli a bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. A ran nan, tsuntsaye da yawa sun zo, sun kafa gada a kan kogin da fikafikansu domin Niu Lang da Zhi Nu da yaransu sun sadu da juna.

Labarin Kua Fu wanda ya bi wa rana da gudu

A can can can da, ya kasance da wani babban dutse a arewacin kasar Sin. A cikin dajin dutsen, ya kasance da wasu katti masu karfi. Shugaban kattin na da macizai biyu masu launin zinariya wadanda suka rataya a kan kunnuwansa, kuma ya kan rike macizai 2 a cikin hannayensa. Sunansa Kua Fu. Shi ya sa ake kiran wadannan mutanen kabilar Kua Fu. Mutanen kabilar Kua Fu na da jan hali da kirki, da kuma himma da kwazo. Suna jin dadin zamansu.

Wata shekara, an yi zafi kwarai. Hasken rana ya sauka kan kasa, ya kone koguna, ya gasa itatuwa har sun mutu. An yi zafi har an kasa yin hakuri da shi, mutane da yawa da ke cikin kabilar Kwa Fu zun mutu. Shugabansu Kua Fu yana bakin ciki, ya kalli rana, ya ce, ' Muguwar rana tana so ta kashe mu. Zan bi ta in kama ita, domin in tilasta mata da ta bi umurnin mutum.' Da mutane suka ji maganarsa, sun lallashe shi da cewa, 'Kada ka biye wa rana. Tana da nisa gare mu, za ka ji gajiya har ka mutu !' Wasu kuma sun ce, 'Rana na da zafi ainun, za ta kone ka idan ka matsa kusa da ita.' Amma Kua Fu ya riga ya dauri niyya, ya ce, 'Domin jin dadin zamanmu, kome wahala zan je.'

Kua Fu ya yi sallama da iyalinsa da jama'arsa, ya nufi inda rana ta tashi, ya fara gudu. Rana tana motsi cikin sauri a can sama, Kua Fu yana ta gudu a kasa. Ya hau manyan duwatsu da yawa, kuma ya ketare manyan koguna da yawa. Da ya gaji, ya kada yashin da ke cikin takalmansa a kasa, sai ya zama babban tsauni.

Kua Fa na ci gaba da bin rana da gudu, ganin yana ta kara matso kusa da rana, ya kara daukan niyyar kama ta. A karshe dai, ya samu rana a inda ta sauka. Ganin wani babban kwallon wuta a gabansa, hasken rana ya sauka a kan jikinsa, Kwa Fu ya ji murna kwarai, ya mika hannu, yana so ya kama rana. Amma, rana na da zafi kwarai da gaske, ta sa Kua Fu ya ji gajiya kuma ya ji kishirwa. Shi ya sa ya je gaban Rawayen Kogi, ya shanye ruwan kogi duka. Daga baya ya shanye ruwan Kogin Wei, amma har wannan ma bai ishe shi ba. Sai ya nufi arewa, inda ke da makeken tabki. Amma kafin ya isa babban tabkin, sai ya fadi ya mutu sabo da kishirwa.

Lokacin da Kua Fu ke bakin mutuwa, yana bakin ciki kwarai, kuma yana begen iyalinsa da jama'arsa. Ya jefar da sandar da ke cikin hannunsa a kasa, sai ya zama itatuwa wadanda su kan ba da 'ya'ya masu zaki, domin mutanen da ke kaiwa da dawowa su ci, su kau da gajiya da kishirwa.

Labarin Kua Fu wai wanda ya bi rana da gudu, ya bayyna mana yadda kakan kakanin Sinawa ke kokarin neman yaki da fari. Ko da yake Kua Fu ya rasu, amma ruhunsa ba zai mutu ba.

Labarin game da babban yakin da aka yi a tsakanin Huang Di da Chi You

Shekaru dubai da suka wuce, ya kasance da kabilu da yawa wadanda ke zama a kwarin Rawayen Kogi da kuma a gaban kogin Yangtse. Huang Di shi ne daya daga cikin sarakunan kabilun da ke kwarin Rawayen Kogi, kuma shi ne wanda ya fi shahara a cikinsu. Shugaban kabila dabam wanda ya yi suna shi ne Yan Di. Su Huang Di da Yan Di, 'yan uwa ne. Ban da su biyu kuma, ya kasance da wani shugaba mai karfi wanda ake kira Chi You a wurin da ke kusa da kogin Yangtse, shi shugaba ne na kabilar Jiu Li.

Chi You yana da 'yan uwa 81, ko wane daga cikinsu ya iya fada sosai, kuma su kwarare ne wajen kera wuka da kibiya da baka da ko wane irin makamai. Chi You ya kan jagoranci 'yan uwansa, don kai hari ga sauran kabilu.

Wata rana, sojojin Chi You sun kai hari ga Yan Di. Yan Di ya yi yaki kin harin, amma ya fadi. Ganin ba abin da zai yi, Yan Di ya gudu zuwa Zhuo Lu, wurin da ke karkashin mulkin Ya Di, domin neman taimako. Da ma Yan Di yana so ya kawar da wannan mugun shugaba. Shi ya sa, ya tara sojojin kabilu da yawa tare a Zhuo Lu, domin yaki da sojojin Chi You. Wannan yaki ana kiransa Yakin Zhuo Lu.

Da aka fara yakin, Chi You ya sami nasarori da yawa, tun da yake yana da makamai masu kyau, da sojoji masu jarumtaka. Daga baya, Huang Di ya yi amfani da dodo da naman daji a wajen yaki. Ko da yake sojojin Chi You na da jar zuciya sosai, amma sun kasa fama da naman daji. Don haka, sojojin Chi You sun tarwatse sun gudu.

Huang Di da sojojinsa suna bin Chi You, amma kwatsam ya zama duhun dulum, hazo ya mamaye ko ina, iska na bugawa sosai, kuma ga walkiya da tsawa, ba da dadewa ba ruwa ya sauka. Yanayi ya sa sojojin Huang Di suka kasa ci gaba da bin Chi You. A hakika ma, Chi You ya samu taimako daga wajen aljani mai kula da iska da ruwa. Shi ya sa, Huang Di shi ma ya nemi taimako daga wajen aljanin fari. Nan da nan iska da ruwa sun tsaya, Huang Di ya ci gaba da bin Chi You.

Ganin haka, Chi You ya yi dabo ya fid da hazo, domin neman hana sojojin Huang Di. Sai Hauan Di ya kera wata mota mai nuna kudu, ta yadda za a ba da ja gora ga sojojinsa domin su fita daga cikin hazo.

Bayan kazamin fada sosai, Huang Di ya kashe 'yan uwan Yan Di 81 daya bayan daya, a karshe dai ya kama Chi You. Ya kashe shi, kuma ya binne kansa da jikinsa a wurare dabam, domin tsoron an farfado da shi.

Bayan da ya kashe Chi You, sannu a hankali, Huang Di ya zama shugaban dukan kabilun kasar Sin.

Sinawa suna ganin cewa, Huang Di da Yan Di su ne kakaki-kakakinsu. Shi ya sa har yanxu a lardin Sha'an Xi ya kasance da kabarin Huang Di. Ko wace shekara a lokacin bazara, Sinawa su kan taru a can, domin nuna masa ta'aziyya.

Labarin Hou Yi wanda ya harbi rana

A lokacin da can, ya kasance da rana 10 a can sama. Zafin rana ya shanye koguna, ya kone kayayyakin gona, mutane da yawa sun suma sabo da zafi. Wasu namun daji kuma sun kasa daure zafi, sun fito daga cikin daji, sun kawo barna ga 'yan Adam.

Ganin haka, sarkin aljanu ya aika da Hou Yi zuwa duniya domin ya ba da taimako ga 'yan Adam. Shi ya sa, Hou Yi ya dauki kwari da bakarsa, ya sauka daga sama zuwa kasa, tare da matansa, Chang E.

Hou Yi ya lallashi rana 'yan uwa goma, ya ba su shawarar cewa, su yi aikinsu daya bayan daya, ko wace rana daya ta fito. Amma, wadannan rana suna da girman kai da taurin kai, ba su ji maganar Hou Yi ba, hatta ma sun kara matsawa kusa ga kasa da gangan, sun kone kasa har sun ta da wuta. Ganin yadda rana goma ke yin abin da suka ga dama ga mutane ya sa Hou Yi ya yi fushi sosai. Shi ya sa, ya dauki kibiya, ya ja baka, ya harbi rana. Kibiyoyinsa sun samu rana tara, sun fadi, sun mutu. Rana ta karshe ta ji tsoro sosai, ta roki Hou Yi da ya yi mata hakuri, shi ya sa Hou Yi bar ita da rai.

Hou Yi ya ceci dan Adam, amma ya sa sarkin aljanu ya yi fushi sosai, domin wadannan rana da Hou Yi ya kashe, 'ya'yansa ne. Shi ya sa ya saukar da Hou Yi daga mukaminsa na aljani, ya hana shi komawa sama. Tun da yake ba a yarda ya koma sama ba, Hou Yi ya yanke shawarar zama a cikin mutane, ya ci gaba da ba su taimako. Amma matarsa Chang E ba ta ji dadin zama a kasa ba, ta kan yi wa Hou Yi koke-koke.

Hou Yi shi ma ya tsargu, domin yana ganin cewa, laifinsa ne ya sa matarsa ta kasa komawa gida. Ya ji an ce, akwai wata aljana mai suna Xi Wang Mu wadda ke zaune a kan kolin dutsen Kun Lun. Tana da wani magani, da mutum ya sha maganin, zai iya tashi zuwa sama. Shi ya sa ya yi ta tafiya, ya sha wahaloli da yawa, ya hau dutsen Kun Lun, ya nemi maganin daga wajen Xi Wang Mu. A karshe dai ya samu, amma maganin ya ishe mutum daya kawai. Hou Yi ba ya so ya bar matarsa ya tashi zuwa sama shi kadai, kuma bai yarda matarsa ta bar shi a kasa ba. Shi ya sa da ya dawo gida, ya boye maganinsa.

Amma Chang E ya gano asirin Hou Yi. Ko da yake tana son mijinta, amma ta kasa hakura da kwadayinta. Shi ya sa a ran 15 ga watan Augusta, yayin da wata ya fi girma, kuma Hou Yi ba shi gida, Chang E ta sha maganin. Sai ta ga jikinta ya zama maras nauyi, ta fara tashi zuwa sama. A karshe dai ta sauka a kan duniyar wata, ta zauna a cikin fadar Guang Han. Da Hou Yi ya dawo, ganin matansa ta tashi zuwa sama ita kadai, ya yi bakin ciki sosai. Ko da yake zai iya harbin wata, amma ba ya so ya lahanta matarsa, sai ya yi ban kwana da ita.

Hou Yi ya zama shi kadai ke nan, ya ci gaba da farauta, da ba da taimako ga mutane, da koyar wa mutane fasahar harbi. Feng Meng, daya daga cikin dalibansa ne, shi ma ya zama gwani a wajen harbi. Amma yana ganin cewa, idan Hou Yi ya cigaba da kasancewa a duniya, shi Feng Meng ba zai zama wanda ya fi gwaninta a wajen harbi ba. Shi ya sa, wata rana, lokacin da Hou Yi ya bugu, ya harbi shi daga baya, ya kashe shi.

Chang E tana ci gaba da zamanta a kan duniyar wata, inda babu mutum, ban da wani tsoho wanda ke yanke itace, da wani zomo wanda ke daka saiwa da bawon itace domin hada magani. Tana ta zama a cikin kadaici da rashin jin dadi, ta yi da na sani. Kuma ko wace shekara a ran 15 ga watan Augusta, ta kan tuna da zamanta cikin jin dadi yayin da take tare da mijinta.

Labarin Chang E wadda ta tashi zuwa duniyar wata

Ran 15 ga watan Augusta a bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin ranar wata ce. Ranar wata da sallahr Bazara, da sallahr Duan Wu, su ne manyan sallahr gargajiya guda 3 na kasar Sin. Yanzu bari mu karanta wani labari game da ranar Wata mai taken "Labarin Chang E wadda ta tashi zuwa duniyar wata".

A lokacin da can, ya kasance da rana 10 a can sama. Zafin rana ya shanye koguna, ya kone kayayyakin gona, mutane da yawa sun suma sabo da zafi. Wasu namun daji kuma sun kasa daure zafi, sun fito daga cikin daji, sun kawo barna ga 'yan Adam.

Ganin haka, sarkin aljanu ya aika da Hou Yi zuwa duniya domin ya ba da taimako ga 'yan Adam. Shi ya sa, Hou Yi ya dauki kwari da bakarsa, ya sauka daga sama zuwa kasa, tare da matansa, Chang E.

Hou Yi ya lallashi rana 'yan uwa goma, ya ba su shawarar cewa, su yi aikinsu daya bayan daya, ko wace rana daya ta fito. Amma, wadannan rana suna da girman kai da taurin kai, ba su ji maganar Hou Yi ba, hatta ma sun kara matsawa kusa ga kasa da gangan, sun kone kasa har sun ta da wuta. Ganin yadda rana goma ke yin abin da suka ga dama ga mutane ya sa Hou Yi ya yi fushi sosai. Shi ya sa, ya dauki kibiya, ya ja baka, ya harbi rana. Kibiyoyinsa sun samu rana tara, sun fadi, sun mutu. Rana ta karshe ta ji tsoro sosai, ta roki Hou Yi da ya yi mata hakuri, shi ya sa Hou Yi bar ta da rai.

Hou Yi ya ceci dan Adam, amma ya sa sarkin aljanu ya yi fushi sosai, domin wadannan rana da Hou Yi ya kashe, 'ya'yansa ne. Shi ya sa ya saukar da Hou Yi daga mukaminsa na aljani, ya hana shi komawa sama. Tun da yake ba a yarda ya koma sama ba, Hou Yi ya yanke shawarar zama a cikin mutane, ya ci gaba da ba su taimako. Amma matarsa Chang E ba ta ji dadin zama a kasa ba, ta kan yi wa Hou Yi koke-koke.

Hou Yi shi ma ya tsargu, domin yana ganin cewa, laifinsa ne ya sa matarsa ta kasa komawa gida. Ya ji an ce, akwai wata aljana mai suna Xi Wang Mu wadda ke zaune a kan kolin dutsen Kun Lun. Tana da wani magani, da mutum ya sha maganin, zai iya tashi zuwa sama. Shi ya sa ya yi ta tafiya, ya sha wahaloli da yawa, ya hau dutsen Kun Lun, ya nemi maganin daga wajen Xi Wang Mu. A karshe dai ya samu, amma maganin ya ishe mutum daya kawai. Hou Yi ba ya so ya bar matarsa ya tashi zuwa sama shi kadai, kuma bai yarda matarsa ta bar shi a kasa ba. Shi ya sa da ya dawo gida, ya boye maganinsa.

Amma Chang E ya gano asirin Hou Yi. Ko da yake tana son mijinta, amma ta kasa hakura da kwadayinta. Shi ya sa a ran 15 ga watan Augusta, yayin da wata ya fi girma, kuma Hou Yi ba shi gida, Chang E ta sha maganin. Sai ta ga jikinta ya zama maras nauyi, ta fara tashi zuwa sama. A karshe dai ta sauka a kan duniyar wata, ta zauna a cikin fadar Guang Han. Da Hou Yi ya dawo, ganin matansa ta tashi zuwa sama ita kadai, ya yi bakin ciki sosai. Ko da yake zai iya harbin wata, amma ba ya so ya lahanta matarsa, sai ya yi ban kwana da ita.

Hou Yi ya zama shi kadai ke nan, ya ci gaba da farauta, da ba da taimako ga mutane, da koyar wa mutane fasahar harbi. Feng Meng, daya daga cikin dalibansa ne, shi ma ya zama gwani a wajen harbi. Amma yana ganin cewa, idan Hou Yi ya cigaba da kasancewa a duniya, shi Feng Meng ba zai zama wanda ya fi gwaninta a wajen harbi ba. Shi ya sa, wata rana, lokacin da Hou Yi ya bugu, ya harbi shi daga baya, ya kashe shi.

Chang E tana ci gaba da zamanta a kan duniyar wata, inda babu mutum, ban da wani tsoho wanda ke yanke itace, da wani zomo wanda ke daka saiwa da bawon itace domin hada magani. Tana ta zama a cikin kadaici da rashin jin dadi, ta yi da na sani. Kuma ko wace shekara a ran 15 ga watan Augusta, ta kan tuna da zamanta cikin jin dadi yayin da take tare da mijinta.

>>[Almara]

An yi wani hoton macijin da aka kara masa kafa

A tsohon zamani na da, wata kasa mai suna Chu, a cikin wannan kasa akwai wani mai babban mukami kuma mai kudi da yawa, wata rana bayan da aka yi aikace aikacen addu'a, sai ya mika kyautar wata kwalba mai giya ga 'yan bazaki dake yi masa hidima.

Bayan da wadannan 'yan bazaki sun sami wannan kwalba mai giya sai sun yi shawarwari cewa, wannan kwalbar giya guda daya kawai, wato yawan giyar nan bai ishe mu mutane da yawa haka ba, in wani daga cikinmu zai iya shan wannan kwalbar giya guda, kai shi ne zai iya jin dadin sha kwarai. Kowa ya nuna yarda ga wannan dabara,amma ba wani da yake so bar damar shan giyar nan, sai suna kallo ya juna kawai.

Daga baya, wani mutun ya ba da shawara cewa, yanzu kowanenmu zai zana wani hoton maciji a kan kasa, in wani ya kammala da farko, to shi ne zai iya shan wannan kwalbar giya. Sai kowa ya nuna yardarsa ga wannan dabara, nan da nan kowa ya fara yin zanen nan. Wani daga cikinsu ya yi zane da sauri, wato shi ya yi zane ba na cikin tsanaki ba. A lokacin da ya yi farin ciki da kammala wannan hoto da farko, sai ya dau kwalbar giya yana shirin shan wannan giya, ya ga sauran mutane suke yin zane sannu sannu, wato wadansu ba su kammala tukuna, sai ya yi tunani cewa, ku ne ku kasa daga ni sosai,sai ya ce, ni zan yi wannan maciji kafafuwa masu kyau. A wannan lokaci wani mutun daban shi ma ya kammala zanensa, sai ya ga hoton da wannnan mutun ya yi, Ashe me yasa hoton macijin da ka yi yana da kafafuwa haka? In haka ne wannan hoto ba na maciji ba ne. Sai ya kama wannan kwalbar giya, ya ce, ni zan sha giyar nan. Kai wannan mutun da ya kammala hoton maciji a farko bai samu giya ko kadan ba. Daga nan ne an fara barbaza wannan tatsuniya, wato in an kammala aiki shi ke nan, in an yi wa maciji kafafuwa wannan aikin banza ne.

Labarin Bian He wanda ya samu lu'u-lu'u

A lokacin da can, wani mutum na daular Chu, wanda ake kiransa Bian He ya samu wani lu'u-lu'un da ba a yi masa gyara ba. Ganin lu'u-lu'u na da kyau, ya je ya mika dutsen ga sarkin kasar Chu, Li Wang. Sarkin ya ba kwararru dutsen domin su duba, kwararren sun nuna cewa, wannan dutse ba shi da daraja. Sarkin na ganin cewa, karya ce Bian He ke yi. Shi ya sa ya yanke kafarsa ta hagu.

Bayan da sarki Li Wang ya mutu, Wu Wang ya gaje shi, ya zama sabon sarki. Bian He ya je mika dutsen ga Wu Wang. Wu Wang ya ba gwanaye dutsen, su ma sun nuna cewa, dutsen ba shi da daraja. Shi ya sa Wu Wang ya yanke kafar dama ta Bisan He, domin yana ganin cewa, shi mazambaci ne.

Bayan da Wu Wang ya mutu, Wen Wang ya zama sarkin kasar. Bian He ya dauki dutsen, ya tafi zuwa gindin dutsen Chu, ya yi kuka, ya yi kuka har kwanaki 3. Ruwan idonsa ya kare, har jini ya fito daga idanunsa. Da sarkin Wen Wang ya ji labarin, sai ya aika da mutum ya tambaye shi cewa, "mutanen wadanda suka rasa kafafuwansa sun yi yawa, me ya sa ka yi bakin ciki haka?"

Bian He ya ce, "Na yi bakin ciki ba wai domin an yanke kafafuwana ba. Lu'u-lu'u ya zama dutse maras daraja, mutum mai gaskiya ya zama mazambaci, wannan shi ne dalilin da ya sa na yi bakin ciki haka!" Shi ya sa Wen Wang ya sa aka sarrafa wannan dutse, sai ya gano cewa, gaskiya ne dutsen nan lu'u-lu'u ne mai daraja sosai. Sai ya nada masa sunan 'lu'u-lu'u na Bian He'.

Labarin Bian Que sarkin likita na kasar Sin

Wata rana, sarkin likita Bian Que ya je ganin sarkin daular Cai, Huan Gong. Bayan gaisuwa, Bian Que ya dubi fuskar sarki, ya ce, "Ranka ya dade, na ga kana da cutar fata, bari in yi maka jinya. In ba haka ba, cutar za ta shiga cikin jikinka." sarki bai amince da shi ba, ya ce, "Ba ni da ciwo." Sai ya yi ban kwana da Bian Que. Bayan da Bian Que ya fita, Sarki ya ce wa waziri, "Su likitoci kullum su kan yi wa mutum maras ciwo jinya, kamar su ne wadanda suka ba shi lafiya."

Kwanaki goma sun wuce, Bian Que ya sake shiga fada domin gai da sarki. Da ya gan shi, sai ya ce, "Ran ka ya dade, cutar da ma tana kan fatarka, amma yanzu ta riga ta shiga cikin namanka. Za ta kara tsanani, idan ba ka mai da hankali a kai ba!" Sarki ya yi fushi, ya kyale shi. Shi ya sa Bian Que ya sallame shi ya fita.

Bayan da kwanaki goma sun wuce, Bian Que ya sake shiga fada. Ya gai da sarki, ya ce, "Ran kan ya dade, cutar ta shiga cikin cikinka, na iya kara tsanancewa, ida ba ka dauki mataki ba." Amma sarki ya yi watsi da shi.

Kwanaki 10 dabam sun wuce, Bian Que ya sake shiga fada. Da ya hangi sarki, sai ya juya ya fita. Sarki ya yi mamaki, ya sa aka bi shi, aka tambaye shi dalilin da ya sa ya bar fada ba tare da yin magana da sarki ba.

Bian Que ya amsa da cewa, "Yin wanka da ruwan magani, cutar fata za ta warke. Allura za ta iya warkar da cutar da ke cikin nama. Da cutar ta shiga cikin mutum, shan magani zai iya shawo kanta. Amma, da cuta ta shiga cikin kashi, ba abin da za mu yi, sai ikon Allah. Yanzu, cuta ta riga ta shiga cikin kashin sarki, na kasa ba da taimako."

Kwanaki 5 sun wuce, sarki ya ji ciwon jiki a ko ina. Ya aika da mutane domin su je neman Bian Que, amma ya riga ya gudu. Ba da dadewa ba, sarkin ya mutu.

Labarin Zhou Ji wanda ke da kyayyawa

Zhou Ji, wazirin daular Qi ne, kuma yana da kyaun gani sosai. Wata rana da safe, da ya tashi, ya sa tufafi da hula, ya dubi kansa ta madubi. Sai ya tambayi uwargidansa cewa, "Ni da Xu Gong da ke zaune a arewacin birnin, wane ne ya fi kyaun gani?"

Uwargidansa ta ce, "kai ka fi shi kyau, Xu Gong bai kai ka ba."

Xu Gong mutum ne mai kyaun gani sosai, wanda ya yi suna a duk kasa. Zhou Ji bai amince da cewa shi ya fi Xu Gong kyaun gani ba. Shi ya sa ya tambayi amaryarsa cewa, 'A ganinki, ni da Xu Gong, wane ne ya fi kyaun gani ?' Amaryarsa ta ce, 'Xu Gong bai kai ka ba.'

Kashegari wani bako ya zo, Zhou Ji ya tambaye shi, 'Ni da Xu Gong, wa ya fi kyaun gani ?' Bakon ya amsa da cewa, 'Xu Gong bai kai ka ba.'

Sai wata rana, Xu Gong ya kai wa Zhou Ji ziyara. Zhou Ji ya tantance shi, yana ganin cewa, Xu Gong ya fi shi kyaun gani. Sai ya dubi madubi, sai ya ga gaskiya ne shi kansa bai kai Xu Gong kyaun gani ba.

Da dare, Zhou Ji ya kwanta a kan gado, ya yi tunani, sai ya gane cewa, Uwargidansa ta ce shi ya fi kyaun gani domin so ya hana ganin laifi, amaryarsa ta ce ya fi kyaun gani domin tana tsoronsa, yayin da bakon ya ce haka domin yana neman taimako daga wajensa. Dukansu sun ce ya fi kyau gani, amma a hakika, ba haka ba ne.

Labarin wani kwado da ke rijiya

A cikin wani rijiya maras zurfi, wani kwado yana jin dadin zamansa ko wace rana. Wata rana, ya gaya wa wata babbar kififiya wadda ta zo daga gabashin teku cewa, " ni ina jin dadin zamana! Idan ina son wasa a waje, sai in yi tsalle-tsalle a kan sanda da ke bakin rijiyar; idan ina son hutawa, sai in zauna a cikin hudojin katangar rijiyar; idan in taka tadi, tadin ya haye kafafuwa biyu nawa kawai. Idan na waiwaya, sai in ga kananan halittu kamar su kaguwa da kanannan kwadi, dukkansu ba su iya kwatanta kansu da ni. Ban da wannan kuma, ina zama ni kadai a wannan rijiya, idan ina son tsalle, sai in yi tsalle-tsalle; idan ina son hutawa, sai in huta sosai. Wannan ya fi kome dadi. Don me ba ki sauko cikin rijiyar nan kin yi ziyara ba?"

Da wannan kififiya ta ji haka, sai ta fara sauka, amma duk jikinta ya yi girma sosai, ga bakin rijiyar karami ne, sai ba za ta iya shiga cikin wannan rijiya ba, sai ta ja da baya, ta gaya wa wannan kwado abin da ta gani game da teku. Kififiyar ta ce, kilomita dubu ya yi nisa a ganinka, amma teku ya fi haka, kuma yana da zurfi sosai. A zamanin Xiayu, an yi ambaliya har shekaru 9 cikin shekaru 10, amma wannan bai iya kara adadin ruwan da ke cikin teku ba; a sarautar Shangtang, an yi fari har shekaru 7 cikin shekaru 8, amma ruwan teku bai ragu ba. Teku mai girma ne, ba zai canza da tafiyar lokaci ba, haka kuma ba zai canza ba tare da ruwan sama ba. To, wannan shi ne abin morewa da na ji yayin da nake zama a tekun."

Bayan da wannan kwado ya ji haka, sai ya ji mamaki kwarai da gaske kuma ya ji tsoro sosai, sabo da ya san cewa, shi kansa karamin abu ne.

Wannan almara ta gaya mutane cewa, bai kamata ba a ji murna sosai da sosai har wani ya manta da kansa domin karamin sani da ya samu ko karamin aikin da ya yi ba.

Labarin wata dila da damisa

Wata rana, wata damisa ta ji yunwa sosai, shi ya sa tana neman abinci a ko ina. Ta yi sa'a ta kama wata dila, amma yayin da take shirin cin dilar, sai dila ta ce mata, "kada ki cinye ni, sabo da ni Allah ya aiko ni da na zama sarkin dukkan namun daji. Idan kin cinye ni, sai ki saba wa nufin da Allah ya yi."

Da damisar ta ji abin da dila ta fada, ba ta sani ba ko gaskiya ne ko ba gaskiya ba, amma tana jin yunwa sosai, ta rasa abin da za ta yi. Sai dila ta ce, "a ganinki maganar da na yi ba gaskiya ba ne, ko? To, bari in wuce gaba, ki bi ni, sa'an nan ki ga abin da sauran namun daji za su yi: za su watse, za su gudu."

Wannan damisa tana tsammani maganar na da ma'ana, sai ta bi dilar. Wayo Allah! Gaskiya ne, da namun daji suka ga dila da damisa, sai suka gudu ta ko ina. Damisar ba ta sani ba, ita ce naman dajin da suke jin tsoro, amma tana tsammani suna tsoron dila ne!

Wannan almara ta gaya mana cewa, bai kamata ba a ga fuskar wani abu kawai, a maimakon haka, ya kamata a ga abin da ke boye a karkashin fuskar, wato a yi bincike sosai a ga gaskiya. In ba haka ba, mutane kamar dila za su cuce mu cikin sauki.

Labarin wani tsohon mutum mai suna Shashasha

Da da da can, akwai wani tsohon mutum mai shekaru 90 da haihuwa, ana kiransa Shashasha. A gaban gidansa, ya kasance da manyan tuddai biyu, wani an ce masa dutsen Taihang, wani daban sunansa dutsen Wangwu, sabo da duwatsun nan biyu, mutanensa ba su iya sami saukin shigowa da fitowa.

Wata rana, Shashasha ya tattara dukkan iyalansa inda ya ce, "wadannan duwatsu biyu sun toshe hanyarmu, shi ya sa idan muna son fita waje, sai mun yi doguwar tafiya sosai. Ya fi kyau mu yi namijin kokari, mu kawar da duwatsun zuwa wani wuri daban. Mene ne ra'ayinku?"

Da 'ya'yansa da jikokinsa suka ji haka, sai suka ce, "abin da ka fada gaskiya ne, sai mu fara aikinmu tun daga gobe." Amma matan Shashasha tana tsammani cewa, aikin daukan duwatsu na da wuya sosai gare su, sai ta ce, "tun da mun riga mun yi zama a nan har shekaru da yawa, don me ba mu iya ci gaba da irin zaman nan? Ko mun iya daukar duwatsun a kwana a tashi, amma ina wurin da za mu ajiye kananan duwatsu da kasa da muka dauka?"

Maganar da matarsa ta yi ta haddasa tattaunawar da aka yi, to, gaskiya wannan babbar matsala ce. A karshe dai, sun sami ra'ayi daya tare da yanke shawarar ajiye wadannan duwatsu da kasa cikin teku.

A kashegari, Shashasha ya fara gudanar da aikinsa na daukar duwatsu tare da iyalansa. Wata makwabciyarsa wata mace wadda mijinta ya mutu, tana da wani 'dan mai shekaru bakwai ko takwas da haihuwa. Da suka ji labarin wannan Shashasha, sai suka je waje da murna sun ba da taimako. Ko da yake haka ne, amma iyalan Shasha suna da faretani da kwanduna, haka kuma duwatsun sun yi nisa da teku, idan wani ya je teku, sai ko wace rana ya iya tafiya sau daya ko biyu kawai. Sabo da haka ne, suna aiki har wata daya, amma duwatsun bai canza ba idan aka kwatanta su da na da.

Akwai wani tsohon mutum daban, ana kiransa mai wayo. A ganinsa abin da iyalan Shashasha suke yi abin dariya ne. Wata rana, ya gaya wa Shashasha cewa, "ka yi shekaru 90 kamar haka, har ba ka iya tafiya sosai ba, ba mai yiwuwa ba ne ka dauki duwatsu biyu zuwa teku."

Shashasha ya amsa cewa, "ko da yake sunanka shi ne Mai wayo, amma ba ka fi yara wayo ba. Da yake ba da dadewa ba zan mutu, amma ina da 'ya'ya ; idan 'ya'yana suka mutu, akwai jikoki ; kamar haka mutanenmu ba su kare ba. Amma kananan duwatsun da ke kan duwatsun nan biyu ba su iya karuwa ba, wato idan mun dauki kadan, sai sun ragu kadan. Muna nan muna yin aikin a kwana a tashi, don me ba mu iya daukar duwatsun har zuwa teku ?" Da mai wayo ya ji haka, sai ya rasa abin da zai fada.

Shashasha yana shugabantar iyalansa, suna yin namijin kokari a ko wace rana da dare wajen daukar duwatsun nan biyu ba tare da kulawar yanayi mai tsananin zafi da lokacin dari. A karshe dai aikin da suke gudanarwa ya burge Allah, sai Allah ya aiko mala'iku biyu zuwa duniyar mutum domin daukar duwatsun nan biyu zuwa wani wuri daban. Amma ana jin dadin labarin Shashasha har zuwa yanzu. Wannan labari ya gaya mana cewa, ko da yake akwai wani abu mai wuya a gabanka, amma idan kana da niyya, to, mai yiwuwa ne za ka ci nasara a karshe.(Danladi)

Labarin wani 'dan addinin Dao da ke dutsen Lao

A da da da can, akwai wani dutse mai suna dutsen Lao da ke dab da teku, cikin dutsen wani 'dan addinin Dao yana zamansa a kai, ana kiransa 'dan addinin Dao da ke dutsen Lao. An ce, wannan 'dan addinin Dao ya iya rufa ido wanda mutanen kullum ba su iya yi. A cikin garin da ke da nisa da dutsen Lao har kilomita dari, wani mutum mai suna Wang Qi ke zama a can. Tun daga yarantakarsa, Wang Qi yana sha'awar rufa ido sosai da sosai, yayin da ake gaya masa cewa wannan 'dan addinin Dao ya iya rufa ido sosai, sai ya rabu da iyalinsa, ya je dutsen Lao koyon rufa ido. Da isowar Wang Qi a dutsen ke da wuya, sai ya gana da wannan 'dan addinin Dao, sun yi hira, cikin hirarsu, Wang Qi yana ganin cewa, wannan 'dan addinin Dao ya iya rufa ido sosai, sabo da haka ne ya roke 'dan addinin Dao da ya zama dalibinsa. Bayan da 'dan addinin Dao ya dube shi, sai ya ce, "na ga kana jin dadin zamanka sosai a gida, ba za ka iya hadiye wahalolin koyon rufa ido ba." Sai Wang Qi ya sake rokonsa har sau da dama, sabo da haka ne 'dan addinin Dao ya yarda da ya zama dalibinsa.

Da dare ya yi, Wang Qi yana hangen hasken wata ta taga, yana tsammani zai iya koyon rufa ido nan da nan, sai ya ji murnar da bai iya fada ba. A alfijir na kashegari, Wang Qi yana gudu a gaban wannan 'dan addinin Dao, tsammanin yake wannan 'dan addinin Dao zai koyar masa rufa ido, amma a maimakon haka, wannan 'dan addinin Dao ya ba shi wani gatari, kuma ya sa Wang Qi da sauran dalibansa su je dutse domin yin kirare. Wang Qi bai ji dadi ba ko kadan a cikin zuciyarsa, amma babu abin da zai yi sai ya bi umurnin da malaminsa ya yi masa. A kan dutsen, cike yake da kananan duwatsu da kayoyi, har rana ba ta sauka ba, hannayensa da kafafunsa sun yi bororo mai jini.

Da wata daya ya wuce, hannayensa da kafafunsa sun yi kanta a tashi a hankali, ba zai iya hakurar wahalar yin kirare da ciyawa ba, sai yana son komawa gidansa. Dare ya yi, ko da Wang Qi da 'yan ajinsa suka koma wurin zama, sai ya ga wannan 'dan addinin Dao tare da baki biyu, suna shan giya suna hira. Dare ya riga ya yi, amma babu fitila a cikin dakin. Sai ya ga wannan 'dan addinin Dao ya dauki wata takarda da almakashi, sai ya yi wani wata kamar madubi wanda ya shafe a kan bango. Sai nan da nan wannan wata da aka yi da takarda ya yi haske kamar watan gaskiya. A daidai wannan lokaci, wani bako ya ce, "ga kyakkyawan dare, ga abinci mai dadi, ya kamata mu ji murna tare." Sai wannan 'dan addinin Dao ya bayar da wata tukunya cike take da giya ga dalibansu, kuma ya ce sun sha giya gwargwadon iyawarsu. Wang Qi yana tsammani cewa: dalibansa da yawa haka, yaya wata tukunyar giya ta iya ishe mu? Amma abin mamaki ya faru, daliban suna sha suna sha, amma giyar da ke cikin tukunya ba ta ragu kadan ba. Bayan 'yan mintoci kadan, wani bakon daban ya ce, "ko da yake muna da wata mai ba da haske, amma ba mu iya shan giya da murna ba, ya fi kyau an yi mana rawa." Wannan 'dan addinin Dao ya dauki wani tsinken cin abinci, ya nuna wannan wata da ya yi da takardar, sai nan da nan wata yarinya wadda tsawonta bai kai mita daya ba ta fita daga watan. Amma yayin da ta fado a kan kasa, sai ta zama kamar mutumin kullum, tana rera waka. Da ta gama wakar din, ta yi tsalle har a kan tebur, yayin da dukkan mutanen jin mamaki suke yi, wannan yarinya ta zama wani tsinken cin abinci kamar a da. Ganin haka Wang Qi ya ji mamaki kwarai da gaske. Wani bako ya ce, "ina murna sosai a wannan dare, amma tilas ne zan tafi gida." Sai bakin nan biyu suka shiga cikin watar da aka yi da takarda. A tashi a hankali, watan nan ba ta yi haske ba, daliban sun dauki fitila, sai sun ga malaminsu a zaune yake shi kadai, ba a san inda bakon suka nufi ba.

Watan daban ya wuce, amma malamin bai koyar da Wang Qi ko wane rufa ido ba, sai Wang Qi ya tambaya malaminsa cewa, "ni na zo daga wurin nisa, idan ba zan iya koyon rufa ido ta yadda ba zan mutu ba, amma ya kamata ka koyar mini wasu kananan rufa ido, in more." Wannan 'dan addinin Dao yana murmushi, amma bai amsa ba, ganin haka Wang Qi ya ce, "malam, ko wace rana na tashi da alfijer, na dawo da dare, na yi kirare na yi ciyawa, a gidana ban taba cin wadannan wahaloli ba." Malamin yace, "tun da na sani, ba ka iya hadiye wahala ba, yanzu na ga gaskiya ne. Sai gobe da safe, ka dawo gidanka." Wang Qi ya roki malamin cewa, "don Allah ka koyar mini karamin rufa ido." Malamin ya ce, "wane irin rufa ido kake so?" Wang Qi ya ce, "na ga ka iya tafiya sosai, har katanga ba ta iya hana ka ba, ina son wannan iri." Sai malamin ya kirawo sa a gaban wani katanga, kuma ya gaya masa wasu sambatu. Bayan da Wang Qi ya karanta sambatu da malamin ya gaya masa, malamin ya ce, "shiga cikin katangar", amma Wang Qi yana jin tsoro, bai iya ba. Wannan 'dan addinin Dao ya sake cewa, "sai ka gwada, shiga cikin katanga." Wang Qi ya tafi ya tsaya har sau da dama, malamin bai ji murna ba, ya ce, "kada ka daga kanka, sai tafiya kawai, shiga cikin takangar!" Da jin haka, Wang Qi ya tafi da sauri, bai sani ba ya riga ya wuce katangar. Wang Qi yana jin murna sosai, ya nuna godiya ga malaminsa. Wannan 'dan addinin Dao ya yi masa gargadi cewa, "bayan da ka koma gida, ya kamata ka yi zamanka da sahihiyar zuciya, in ba haka ba, ba za ka iya yin irin wannan rufa ido ba."

Isowar Wang Qi gidansa ke da wuya, sai ya gaya wa matansa cewa, "ni na gamu da mala'ika, na riga na koyi har na iya rufe ido, har katanga ba za ta iya hana ni ba." Amma matansa ba ta gaskata wannan magana ba ko kadan, ta ce a cikin duniya bai kasance da irin wannan batu ba. Sai Wang Qi ya karanta sambatu da malamin ya gaya masa, yana tafiya da sauri a gun wata katanga. Amma bai wuce ba, a maimakon haka, kansa ya buga wa katangar, ya fadi a kan kasa. Matansa ta ga wani kurji a kansa, sai ta ce, "ko da ya kasance da rufe idon a duniya, ba za a iya koyonsa ba cikin watanni biyu ko uku kamar kai." A ganin Wang Qi, a hakika ne ya wuce katanga a wannan dare, sabo da haka yana shakkar cewa, wannan 'dan addinin Dao ya yi ba'a da shi a daren, sai ya yi zage-zagen wannan 'dan addinin Dao. Tun daga nan ne, ya ci gaba da zamansa mai karamin sani.

Labarin wani malami da kura

Akwai wani mutumin da ake kira Malamin Dongguo, ko da yake ya iya karanta littattafai sosai, amma shi ba mai hikima ba ne. Wata rana, shi da jakinsa wanda wata jakka cike take da littattafai ke bayansa suna tafiye-tafiye zuwa wani wuri mai suna 'kasar Zhongshan' domin neman wani mukami. Ba zato ba tsammani, wata kurar Turai da ta ji rauni ta gudu a gabansa, ta ce, "malami, yanzu wani mafarauci ke bi na da gudu, ya harbe ni har sauran kadan na rasa raina. Na roke ka, ka sa na boye cikin jakarka, a nan gaba tabbas ne zan saka maka da alheri." Ko da yake Malamin Dongguo ya sani kura ta kan cuci mutane, amma ya ga wannan kura tana jin rauni, sai ya ce, "idan na yi haka, zan bata wa mafaraucin rai. Amma tun da kin roke ni, sai zan yi dabarar ceton ka." Bayan da ya fadi haka, sai ya sa kurar ta shiga cikin jakarsa.

Bayan lokaci kadan, wannan mafarauci ya gudu har zuwa a gaban Malamin Dongguo, ya tambaye shi, "ko ka ga wata kura da ta ji rauni?" Malamin Dongguo ya ce, "ni ban ga kura ba, sabo da akwai hanyoyi da yawa a wurin, mai yiwuwa ne ta tsira zuwa wata hanya daban." Mafaraucin ya gaskata abin da Malamin ya fada, sai ya bi wata hanya daban. Da kurar da ke cikin jaka ta ji mafaraucin ya yi nisa, sai ta ce, "don Allah malamin, ka sake ni, ka sa na yi tsira." Malamin Dongguo mai kirki ne, ya gaskata maganar da Kurar ke yi, ya sake ta. Amma abin da ba mu iya tunawa ba ya faru, wannan kura ta yi ihu ga Malamin Dongguo cewa, "ko da yake Malamin ka yi abin kirki ka ceci raina, amma yanzu na ji yunwa sosai, sai ka sake yin abin kirki, ka sa na cinye ka." Da kurar ta ce haka, ta yi tsalle wajen Malamin Dongguo.

Malamin Dongguo ya yi fada da kurar ba tare da wani abu cikin hannunsa, kuma ya ce, "kada ki manta da abin kirki da na yi miki", a daidai wannan lokaci, wani tsohon manomi ya ratsa ta wurin da wata fartanya, sai Malamin Dongguo ya hana shi cikin gaggawa, kuma ya gaya masa yadda ya ceci kurar, amma kurar za ta cinye shi. Da jin haka, kurar ta musunta cewa, Malamin Dongguo bai cece ta ba. Da wannan tsohon manomi ya yi tunani kadan, sai ya ce, "ba zan gaskata dukkan maganganu da kuka yi ba ko kadan. Jakar Malamin Donguo da karama, yayya aka shigar da kurar mai girma haka? Sai kurar kin sake shiga cikin jakar, bari in ga yadda aka yi haka." Kurar ta yarda da dabarar da wannan manomi ya yi musu, sai ta sake shiga cikin jakar. Da ganin haka, wannan tsohun manomi ya ja bakin jakar da hannunsa nan da nan, ya ce Malamin Dongguo, "irin wannan namun daji su kan cuci mutane, kuma ba za su canza halinsu ba ko kadan. Idan ka yi abin kirki gare su, ka zama wawa." Da ya gama maganarsa, ya buga jakar inda kurar ke ciki da fartanyarsa har kurar ta mutu.

A lokacin nan, Malamin Dongguo ya san dabarar da tsohun manomin ya yi, sai ya yi masa godiya sosai da sosai domin manomin ya ceci ransa cikin lokaci. Amma har yanzu, "Malamin Dongguo" da "Kurar da ke kasar Zhongshan" sun zama kalmomin harshen Sinanci da a kan yi amfani da su sosai. Kalmar "Malamin Dongguo" ta bayyana mutunin da ke jin tausayi ba tare da yin la'akari ba, kalmar "Kurar da ke kasar Zhongshan" ta bayyana mutumin da ke mantawa da abin kirki da aka yi masa, kuma ya aiwatar da mugun abu gare shi.

Labarin 'rashin hanya'

A zamanin yakekeniya na kasar Sin, akwai dauloli da yawa a kasar, kuma ko wace daula tana son zama shugaba a kasar Sin. Sarkin Daular Wei yana son zama shugaban duk kasar Sin, sai ya yi shirin kai hari ga birnin Handan, babban birnin Daular Zhao. Wani jami'in Daular Wei mai suna Ji Liang yana daular daban domin aikinsa, amma da zarar jin wannan labari, sai ya koma Daular Wei. Isarsa ke da wuya, ba shi da lokacin canza tufaffinsa, sai ya gana da sarkin Wei.

Sarkin Wei yana shirin yadda zai kai hari ga Daular Zhao, yayin da ya ga Ji Liang yake cikin gaggawa haka, sai ya ji mamaki. Ya tambaye shi, "ko kana da wani abun gaggawa har ba ka canza tufaffinka ba ko kadan?" Ji Liang ya ce, "Ranka ya dade! A kan hanya, na gamu da wani abun mamaki. Shi ya sa na zo nan domin sanar da kai." Sarkin Wei yana jin mamaki sosai, ya ce me ya faru. Ji Liang ya bayyana cewa, "dazun nan na ga wani keken doki, an tuka shi zuwa arewa. Sai na tambaye shi, 'Ina za ka?' Ya ba da amsa cewa, 'Zan je Daular Chu.' Da jin haka, na ji mamaki sosai, na sake tambayarsa, 'Daular Chu a kudu yake, yaya kake nufin arewa?' Amma ya ce, 'Ba kome, dokina yana da nagarta, ya iya tafiya sosai har Daular Chu. Sai na kara jin mamaki, na tambaye shi, 'ko da yake dokinka na da kyau, amma ba ka nufi Daular Chu ba!' Ya sake cewa, 'ba damuwa, ni ina da kudi mai dimbin yawa.' Amma na yi shakka sosai, na gaya masa cewa, 'na sani kana da kudi, amma hanyar da kake bi ba ta yi daidai ba.' Amma ya barke da dariya, ya ce, 'ni ina da fasahar tuki sosai.' Ranka ya dade, bai ji maganar da na yi masa ba, ya ci gaba da tafiya zuwa arewa." Da jin haka, Sarkin Wei ya bushe da dariya, ya ce, "ko akwai wawa kamar haka a duniya?" Ji Liang ya ci gaba da cewa, "Ranka ya dade! Na sani, kana son zama shugaban duk kasar Sin, sai da farko ya kamata ka yi dabarar samun amincewa daga duk kasa. Amma yanzu kana son kai hari ga Daular Zhao domin kara karfafa kwarjininka. Amma idan ka yi haka, za ka nisanta makasudinka, kamar yadda mutumin da ke tuka mota da muka ambata a sama, yana son neman Daular Chu da ke kudu, amma ya bi hanyar da za ta kai shi arewa, ta yadda ya kara nisanta makasudinsa sosai."

Da jin haka, sarkin Wei ya fahimci abin da Ji Liang ke fadi, ashe, Ji Liang yana lallashinsa ne ta hanyar ba da labari mai dadin ji. Sai ya yi tunani har mintoci da dama, ya ga maganar da Ji Liang ke yi na da ma'ana sosai, sai ya bar shirinsa na kai hari ga Daular Zhao.

Daga wannan labari, an yi wata almara 'rashin hanya'. A da, ma'anarta ita ce, ana son neman wani wuri da ke kudu, amma ya bi hanyar da ke nufin arewa. A halin yanzu dai, ta bayyana cewa, wani ya dauki matakai wadanda suke adawa da makasudinsa.

>>[Labarin Wurare Masu Suna]

Labarin Dutsen Wutai

A kasar Sin akwai sanannun duwatsu 4 na addinin Buddah, wato dutsen Wutai da Dutsen E'mei da Dutsen Putuo da kuma Dutsen Jiuhua inda a zamanin da mutane suke cewa, manyan Bodhisattva hudu masu bin addinin Buddah wato Wenshu da Puxian da Guanyin da Dizang ke zama a can. A halin yanzu dai, sun zama shahararrun wuraren yawon shakatawa na kasar Sin.

Dutsen Wutai yana cikin lardin Shanxi da ke tsakiyar kasar Sin, kuma yana kunshe ne da kananan duwatsun da yawansu ya kai biyar. Ko wadanne kananan duwatsu biyar ana da koli mai lebur, kamar wani dandalin da aka yi da kasa, shi ya sa ake kiransu dandalin gabas da na yamma da na arewa da na kudu na kuma na tsakiya, wato 'dandali biyar'. Dutsen Wutai ba wanda ya fi shi tsayi a arewacin kasar Sin.

A da da can, sunan Dutsen Wutai shi ne Dutsen Wufeng, ana samun mugun yanayi a can, a lokacin dari, ana sanyi sosai; a lokacin bazara, akwai rairayi da yawa; a lokacin zafi, ana tsanannin zafi; sabo da haka ne, manoman wurin ba su iya yin aikin gona ba ko kadan. Ana haka nan ana haka nan, sai wata rana wani Bodhisattva mai suna Wenshu ya yi bayyanan addinin a can, da ganin mutanen wurin ke shan wahala haka, sai Wenshu ya yanke shawarar canza yanayin wurin.

Wenshu ya san cewa, sarkin dodo da ke tekun gabas yana da wani dutsen sihiri mai suna 'dutsen da dodo ke hutawa a kansa', wannan dutse ya iya canza mugun yanayi da ya zama mai kyau. Sabo da haka ne, Wenshu ya canza jikinsa har ya zama wani sufi domin yana son aron duwatsun.

Isowarsa a Tekun gabas ke da wuya, sai ya ga wani babban dutse a gaban kofa ta fadar sarkin dodo, yana jin sanyi sosai. Da Wenshu ya gana da sarkin dodo, ya bayyana nufinsa. Amma sarkin dodo ya ce, "ka iya ari ko wane abu na fadata, amma ba ka iya aron wannan dutse ba. Dalilin shi ne muna tonansa har shekaru darurruwa, sai mun same shi, yana da sanyi sosai, banyan da 'ya'yana suke kawo karshen aikinsu, sai su kan tuhu a kan dutsen. Idan ka ari wannan dutse, sai su rasa wurin hutawa."

Ko da yake Wenshu yana kokari ya ce shi ne wani sufi da ke zama a Dutsen Wufeng, kuma ya nemi wannan dutse ne domin ba da alheri ga jama'a, amma sarkin dodo ba ya son ranta dutsensa ga sufin, sai yana tunanin dabarar da take hana tsohon sufin da ya aron dutsen. Sai ya ce, "wannan dutse yana da nauyi sosai, amma babu wanda ke iya taimake ka; idan ka iya dauke shi, sai ka tafi da shi."

Wenshu ya nuna godiya ga sarkin dodo, sai ya zo gaban dutsen, ya yi magana, sai dutsen ya zama wani karamin rairayi, ya tafi da shi. Da ganin haka, tsohon sarkin dodo na jin makaki sosai da sosai, ya yi da-na-sani, amma ba amfani.

Yayin da Wenshu ya dawo Dutsen Wufeng, ana zafi sosai, ba a yi ruwan sama ba cikin dogon lokaci, jama'ar wurin ke shan wahala sosai. Amma yayin da Wenshu ya sa wannan dutse a cikin wani kwari, sai abin mamaki ya faru: Dutsen Wufeng ya zama wani dausayi mai ni'ima nan da nan. Banyan wannan al'amarin, an nada wa kwarin suna 'kwari mai sanyi', haka kuma an gina wani gidan ibada mai suna 'gidan ibada mai sanyi', Dutsen Wufeng kuma ya canza sunansa da ya zama 'Dutse mai sanyi'. Har yanzu, ana kiran Dutsen Wutai 'Dutse mai sanyi'.

Dutsen Wutai shi ne wurin yawon shakatawa na matsayin kasa, yana da kayayyakin al'adu da wurare masu ban sha'awa. Yana da gidajen ibada da yawansu ya kai 42, ciki har da gidan ibada mai suna Nanzong da Foguang wadanda aka gina su a gidan sarautar Tang, ya zuwa yanzu ya kai shekaru dubu daya da dari biyu. Ba kawai ya bayyana yadda addinin zamanin da da al'adunsa suka bunkasa ba, har ma ya bayyana yadda aka gina gidaje a zamanin da.

Ban da wadannan da muka ambata a sama kuma, akwai duwatsu masu mamaki da ruwa mai kyau tare da kyawawan itatuwa da ciyawa a Dutsen Wutai. Sabo da a duk shekara, ya kasance da kankara mai taushi a kolin Dutsen Wutai, shi ya sa ko da yake a lokacin zafi, ana jin sanyi sosai a wurin, ta yadda ya zama wani wuri mai kyau da aka magance zafi.

Labarin Dutsen Wutai

A kasar Sin akwai sanannun duwatsu 4 na addinin Buddah, wato dutsen Wutai da Dutsen E'mei da Dutsen Putuo da kuma Dutsen Jiuhua inda a zamanin da mutane suke cewa, manyan Bodhisattva hudu masu bin addinin Buddah wato Wenshu da Puxian da Guanyin da Dizang ke zama a can. A halin yanzu dai, sun zama shahararrun wuraren yawon shakatawa na kasar Sin.

Dutsen Wutai yana cikin lardin Shanxi da ke tsakiyar kasar Sin, kuma yana kunshe ne da kananan duwatsun da yawansu ya kai biyar. Ko wadanne kananan duwatsu biyar ana da koli mai lebur, kamar wani dandalin da aka yi da kasa, shi ya sa ake kiransu dandalin gabas da na yamma da na arewa da na kudu na kuma na tsakiya, wato 'dandali biyar'. Dutsen Wutai ba wanda ya fi shi tsayi a arewacin kasar Sin.

A da da can, sunan Dutsen Wutai shi ne Dutsen Wufeng, ana samun mugun yanayi a can, a lokacin dari, ana sanyi sosai; a lokacin bazara, akwai rairayi da yawa; a lokacin zafi, ana tsanannin zafi; sabo da haka ne, manoman wurin ba su iya yin aikin gona ba ko kadan. Ana haka nan ana haka nan, sai wata rana wani Bodhisattva mai suna Wenshu ya yi bayyanan addinin a can, da ganin mutanen wurin ke shan wahala haka, sai Wenshu ya yanke shawarar canza yanayin wurin.

Wenshu ya san cewa, sarkin dodo da ke tekun gabas yana da wani dutsen sihiri mai suna 'dutsen da dodo ke hutawa a kansa', wannan dutse ya iya canza mugun yanayi da ya zama mai kyau. Sabo da haka ne, Wenshu ya canza jikinsa har ya zama wani sufi domin yana son aron duwatsun.

Isowarsa a Tekun gabas ke da wuya, sai ya ga wani babban dutse a gaban kofa ta fadar sarkin dodo, yana jin sanyi sosai. Da Wenshu ya gana da sarkin dodo, ya bayyana nufinsa. Amma sarkin dodo ya ce, "ka iya ari ko wane abu na fadata, amma ba ka iya aron wannan dutse ba. Dalilin shi ne muna tonansa har shekaru darurruwa, sai mun same shi, yana da sanyi sosai, banyan da 'ya'yana suke kawo karshen aikinsu, sai su kan tuhu a kan dutsen. Idan ka ari wannan dutse, sai su rasa wurin hutawa."

Ko da yake Wenshu yana kokari ya ce shi ne wani sufi da ke zama a Dutsen Wufeng, kuma ya nemi wannan dutse ne domin ba da alheri ga jama'a, amma sarkin dodo ba ya son ranta dutsensa ga sufin, sai yana tunanin dabarar da take hana tsohon sufin da ya aron dutsen. Sai ya ce, "wannan dutse yana da nauyi sosai, amma babu wanda ke iya taimake ka; idan ka iya dauke shi, sai ka tafi da shi."

Wenshu ya nuna godiya ga sarkin dodo, sai ya zo gaban dutsen, ya yi magana, sai dutsen ya zama wani karamin rairayi, ya tafi da shi. Da ganin haka, tsohon sarkin dodo na jin makaki sosai da sosai, ya yi da-na-sani, amma ba amfani.

Yayin da Wenshu ya dawo Dutsen Wufeng, ana zafi sosai, ba a yi ruwan sama ba cikin dogon lokaci, jama'ar wurin ke shan wahala sosai. Amma yayin da Wenshu ya sa wannan dutse a cikin wani kwari, sai abin mamaki ya faru: Dutsen Wufeng ya zama wani dausayi mai ni'ima nan da nan. Banyan wannan al'amarin, an nada wa kwarin suna 'kwari mai sanyi', haka kuma an gina wani gidan ibada mai suna 'gidan ibada mai sanyi', Dutsen Wufeng kuma ya canza sunansa da ya zama 'Dutse mai sanyi'. Har yanzu, ana kiran Dutsen Wutai 'Dutse mai sanyi'.

Dutsen Wutai shi ne wurin yawon shakatawa na matsayin kasa, yana da kayayyakin al'adu da wurare masu ban sha'awa. Yana da gidajen ibada da yawansu ya kai 42, ciki har da gidan ibada mai suna Nanzong da Foguang wadanda aka gina su a gidan sarautar Tang, ya zuwa yanzu ya kai shekaru dubu daya da dari biyu. Ba kawai ya bayyana yadda addinin zamanin da da al'adunsa suka bunkasa ba, har ma ya bayyana yadda aka gina gidaje a zamanin da.

Ban da wadannan da muka ambata a sama kuma, akwai duwatsu masu mamaki da ruwa mai kyau tare da kyawawan itatuwa da ciyawa a Dutsen Wutai. Sabo da a duk shekara, ya kasance da kankara mai taushi a kolin Dutsen Wutai, shi ya sa ko da yake a lokacin zafi, ana jin sanyi sosai a wurin, ta yadda ya zama wani wuri mai kyau da aka magance zafi.

Labarin Fadar Yonghe

A cikin birnin Beijing, babban birnin kasar Sin, ya kasance da tsofaffin gine-gine masu yawan gaske, amma ginin da ke da alamun kabilun Han da Man da Meng da kuma Zang shi ne Fadar Yonghe kawai.

Fadar Yonghe shi ne wani shahararen gidan ibada na darikar Zang ta addinin Buddah. Fadinta ya zarce muraba'in mita dubu 60, kuma tana da dakunan da yawansu ya zarce dubu daya. Da ma Fadar Yonghe ita ce gidan da sarki na biyu na Daular Qing Kang Xi ya yi wa 'dansa na hudu wato Yin Zhen a shekarar 1694, wanda ya zama sarkin Daular Qing a shekarar 1723. Sabo da haka ne, ya shiga cikin Fadar sarki kuma ya yi zama a nan. Sai ya kebe rabin Fadar Yonghe inda ta ci gaba da zama wurin hutawarsa, wani rabin daban ya ba da wani sufi mai suna Zhang Jiahutuketu kamar wata kyauta, wanda ya zama gidan ibada na addinin Huang.

Addinin Huang wata darikar addinin Lama ce wanda wani mutum mai suna Luobuke Zhakeba ya kafa shi. Luobuke Zhakeba ya zama wani sufi ne a lokacin da shekarunsa ya kai 8 da haihuwa, da ya kai shekarunsa 17 da haihuwa, ya je lardin Xizang na kasar Sin domin yin nazarin addinin Lama har ya zama shugaba. Sabo da mabiyansa su kan sa tufaffin wadanda launinsu rawaye ne, shi ya sa ake kiran addinin Lama addinin rawaya wato addinin Huang a bakin sinawa.

A cikin Fadar Yonghe, akwai kayayyakin al'adun zamanin da masu yawan gaske tare da wasu tsofaffin gine-gine. Amma wadanda suka fi yin suna a kasar Sin da waje su ne kayayyakin al'adun zamanin da da yawansu ya kai uku.

Daya da ke cikinsu shi ne dutsen Luohan da ke cikin karamar fadar Falun. Tsayinsa ya yi kusan mita hudu, kuma tsawonsa ya zarce mita uku. An yi shi ne da katako, a kansa ya kasance da kyawawan itatuwa da kwari da hasumiya da rami mai zurfi da kananan hanyoyi da ruwa da gada da dai sauransu. Abin lura shi ne, akwai Luohan wato mutanen da ke bin addinin Buddah da yawansu ya kai dari biyar a tsakaninsu, amma wani yaki ya sa Luohan da ke dutsen ya bace har ya kai 449 kawai a halin yanzu.

Na biyu da ke cikinsu shi ne surar da aka yi wa wani mai bin addinin Buddah wato Maitreya da ke cikin karamar fadar Wanfu. Suna daban na karamar fadar Wanfu shi ne Dafolou, ba wanda ya fi shi girma a Fadar Yonghe. Tsayinsa ya zarce mita 30 wanda aka yi shi ne da kurmi. Tsayin surar Maitreya ya kai mita 26, wanda mita 8 nasa an bine shi ne a karkashin kasa, nauyinsa ya yi kusan ton 100, har a duk duniya babu wanda ya fi shi nauyi.

Uku da ke cikin kayayyakin al'adun zamanin da shi ne surar Sakyamuni da aka yi da jan karfe. A ko wane gefenta, akwai wata sanda wadda ya kasance da dodanni da yawansu ya kai 99 a kewayenta. Wadannan dodannin da aka yi su yi kamar gaskiya, wannan ya sa mutane da yawa sun yi mamaki sosai.

Ban da wadannan kayayyakin al'adun zamanin da uku da muka ambata a sama, gine-gine da kayayyakin ado da ke cikin Fadar Yonghe suna da alamu na kansu. Kamar dai karamar fadar Falun, akwai hasumiya da yawansu ya kai biyar a kan kolinta da dai sauransu.

Tun daga aka bude kofar Fadar Yonghe ga duk duniya a shekarar 1981, ko wace shekara mutane sinawa da wadanda suke zo daga kasashen waje da yawansu ya zarce miliyan daya su kan zo nan domin aikin girmama wa addinin Buddah ko shan iska. A halin yanzu dai, Fadar Yonghe ba kawai ta zama wani wuri mai tsarki na addinin Buddah ba, har ma ta zama wani wurin da ke da al'adun kabilun Han da Man da Meng da kuma Zang, wanda ya bayyana hadin kai da kabilu daban daban na kasar Sin suke yi.

Hasumiyar da aka yi da kurmi a gundumar Ying ta jihar Shanxi na kasar Sin

A wurare daban daban na kasar Sin, ya kasance da hasumiyoyi masu yawan gaske da ke da salon addinin Buddah da kuma salon gine-gine na kasar Sin. Hasumiyar da aka yi da kurmi a gundumar Ying ta jihar Shanxi na kasar Sin ita daya da ke cikin shahararrun hasumiya ta irin nan.

A shekatar 1056, daular Liao ta fara gina hasumiyar, sai an kawo karshen aikin bayan shekaru 140. An gina ta a kan wata tashar da tsayinta ya kai mita hudu, tsayin hasumiyar kuma ya kai mita 70. Domin aikin ginawar hasumiya, an yi amfani da kyawawan itatuwa da yawansu ya kai cubic mita dubu uku wanda nauyinsu ya kai ton dubu uku.

Wajen sigarta, an koyi salon kabila da ake yi a daular Han da ta Tang, sabo da haka ne ta kasance mai fasaha kuma kyakkyawa. Tana da hawa tara, a kan ko wace hawa, an yi wata kararrawa a kai, sabo da haka ne, idan iska ta buga, sai an ji ita da kyau.

Tun daga aka gina hasumiyar har shekaru fiye da dari tara, ta gamu da kalubale da yawa. Bisa abubuwan da aka rubuta a cikin littattafan tarihi, an ce, yayin da aka gina ita har shekaru dari uku, an yi girgizar kasa da karfinta ya kai awo 6 da digo 5 bisa ma'aunin Richter har kwanaki bakwai, har dukkan gine-ginen da ke kewayenta sun murkushe, amma ita tana tsayawa a wurin. 'Yan shekarun nan, yawancin girgizar kasa da aka yi a gundumar Ying da ke Jihar Shanxi na kasar Sin sun sa hasumiyar ta yi rawa, amma ba su iya halaka ita ba. Yayin da kungiyoyin dakarun azzalumai na wuri-wuri na kasar suke yaki da juna, an taba kai mata farmaki da albarusan Igwa da yawansu ya zarce dari biyu, amma ba a iya canza sigarta ba ko kadan. Shahararrun hasumiya masu yawan gaske da aka gina a zamanin da babbar tsawa da walkiya su kan halaka su, amma hasumiyar da aka yi da kurmi a gundumar Ying ta jihar Shanxi na kasar Sin ta iya magance haka. Ina dalilin da ya haddasar wannan?

Sigarta akwai fasaha kuma ta taka wata muhimmiyar rawa a kan haka. Na farko, tana da hawa da yawansu ya kai tara, sabo da haka ne, ba za a iya girgizar ita da sauki ba. Na biyu, an gina ita da kurmi wanda sigarsa ba mai canzawa ba ne. Ban da wadannan abubuwa da muka ambata a baya, an yi wata sarka da karfe, wadda aka ajiye wani sashenta a kolin hasumiyar tare da dasa sashenta daban cikin kasa, shi ya sa tsawa da walkiya ba su iya halaka ita ba.

Hasumiyar da aka yi da kurmi a gundumar Ying ta jihar Shanxi na kasar Sin a matsayin hasumiyar da aka kula da ita da kyau da ke da siga mai fasaha da kuma ta siffa mai kyau, ta bayyana manyan fasahohin da masu aikin gine-gine na zamanin na kasar Sin da suka samu wajen magance tsawa da walkiya da hana girgirzar kasa da dai sauransu.

Fadar Potala

A kan tudun Qinghai da Tibet akwai wata kyakkaywar fada mai girma da ake kira Fadar Potala, fada ce mafi tsayi da girma a duk duniya gaba daya, wadda 'yan Tibet masu bin addinin Buddhism suka gina ta.

Sarkin Tibet Srong-brtsan-sgam-po ne ya gina fadar Potala a karni na 7 bayan haihuwar Annabi Isa don aurar da gimbiya Wencheng ta daular Tang. An fassara 'Potala' daga wani tsohon harshen kasar India wato Sanskrit a turance, ma iya fasara shi zuwa 'Putulo' ko kuma 'Putuo', da ma ma'anarsa ita ce tsibiri ne da Bodhisattva Guanyin a bakin Turawa ke zama, saboda haka a kan kira fadar Potala 'dutsen Potuo na biyu'. An gina fadar Potala a kan tsaunin Ja wato Red Hill na Lhasa na Tibet, tsayinta ya kai mita dubu 3 da dari 7 daga leburin teku. Tana dogara ga duwatsu, muraba'inta ya kai mita fiye da dubu dari 3 da sittin, an raba ta kashi 2 ne wato fadar Ja da ke tsakiyarsa, da kuma fadar Fari da ke kewayen fadar Ja. Saboda haka launin fadar Potala yana da kyau sosai.

Sarkin Tibet Srong-brtsan-sgam-po ya gina wani daki a tsakiyar fadar Potala, inda ya kan yi nazarin ilmin addinin Buddhism, An gina shi kamar wani kogon dutse, an ajiye mutum-mutumi na Srong-brtsan-sgam-po da gimbiya Wencheng da gimbiyar Nepal Chijun da kuma shahararren minista na Tibet Ludongzan a ciki, duk wadannan mutum-mutumi kayayyakin fasaha ne masu daraja na lokacin tsohon gwamnatin 'yan Tibet, wato karni na 7 bayan haihuwar Annabi Isa.

Ko da yake fadar Potala gini ne da 'yan Tibet masu bin addinin Buddhism suka gina, amma a sa'i daya kuma akwai halin musamman na kabilar Han a fanin gine-gine, wannan sakamako ne na yin aurantaka tsakanin mutanen Tibet da Han a shekaru dubu 1 da dari 3 da suka wuce, haka kuma alama ce ta yin hadin gwiwa tsakanin al'ummonin Tibet da Han a tarihi. Ko a Tibet ko kuma a wuraren da mutanen kabilar Han suke zama, labari mai ban sha'awa da ya faru a shekaru dubu 1 da dari 3 da suka zarce yana bazuwa a ko ina.

A cikin karni na 7 bayan haihuwar Annabi Isa, lokacin tsohon gwamnatin Tibet wato Tubo take mulkin kasar, sarkin Tibet Srong-brtsan-sgam-po yana himmantu ga harkokin siyasa kuma yana so jama'arsa sosai, karfin kasarsa sai karuwa yake ta yi. Don kafa dangantakar sada zumunta a tsakanin kasarsa da daular Tang, da kuma shigar da fasahohi da al'adu masu kyau, sarki Srong-brtsan-sgam-po ya yanke shawarar neman aurar gimbiya Wencheng ta daular Tang. Manzon musamman don neman auren Ludongzan ya je birnin Chang'an, fadar gwamnatin daular Tang tare da kyauta masu yawa. Bayan da ya sauka Chang'an, ya ji an ce, kasashen da ke makwabtaka da daular Tang su ma sun aika da manzanninsu don neman aurar gimbiya Wencheng. Sarki Taizong na daular Tang ya yanke shawarar gudanar da gasar wayo a tsakanin wadannan manzanni, ya ba da tambayoyi guda 3, ba zai auri gimbiya Wencheng ba, sai wani ya amsa dukan tambayoyi guda 3 daidai.

Tambaya ta farko ita ce: an ajiye katoko guda 10 a cikin lambu, kai da saiwa na ko wane katako duk daya ne, wajibi ne manzannin su bambance saiwoyinsu. Ludongzan yana da wayu sosai, ya ajiye katako a cikin ruwa, katako yana yin tudu saboda yawan saiwa ya fi yawa, shi ya sa ya bambanci saiwarsa.

Tambaya ta biyu ita ce: tilas ne manzannin su sa wani siririn zare ya wuce wani dutsen jade, da kyar a zare ya wuce jade saboda an lankwashi cikin jade din nan. Ludongzan ya rufe jade da zuma a wani gefe, daga baya ya daure wani tururuwa da zare, ya ajiye tururuwan nan a bakin jade, da zarar sansanin kamshin zuma, tururuwan ya fara tafiya cikin jade, don sa kaimi kan tururuwan da ya ci gaba da tafiya, Ludongzan ya yi ta busa a bakin jade, a karshe dai, tururuwan ya fita tare da zare. Ludongzan ya sake ci nasara.

Tambaya ta karshe ita ce: sarki Taizong ya sa godiyoyi 100 da dukusai 100 su zama tare, tilas ne a bambance mamarsu. Manzannin sun yi dabara da yawa, amma dukansu sun ci tura a karshe. Ludongzan ya rufe wadannan godiyoyi da dukusai dai-dai, kashegari da safe, ya saki godiyoyin nan daya bayan daya, da zarar ganin mamarsu, sai dukusai sun gudu wajen mamarsu don shan nono, jim kadan kuma, Ludongzan ya bambanci mamar ko wane dukushi lami lafiya.

Ludongzan ya amsa dukan tambayoyi guda 3, sarki Taizong ya yi murmushi, sai ya ba da tambaya ta hudu: tilas ne ya zabi gimbiya Wencheng daga 'yan mata dari 5 tare da fuskarsu a rufe. Dukan manzannin ba su taba ganin gimbiya Wencheng ba, da wuya ne sosai su zaba ba. Duk da cewa Ludongzan ya san cewa, gimbiya Wencheng tana so wani iri kamshi sosai, kudajen zuma ma suna so irin wannan kamshi sosai. A lokacin zaben gimbiya Wencheng, Ludongzan ya dauki wasu kudajen zuma tare da shi a asiri, ya saki dukan kudajen zuma, wadannan kudajen zuma sun tashi zuwa gimbiya Wencheng da ke da kamshi na musamman. Ludongzan ya ci nasara a karo na 4. Sarki Taizong ya yi tsammani cewa, minista na sarki Srong-brtsan-sgam-po yana da wayo haka, tabbas ne sarki shi kansa wani mutum ne mai haziki, a sabili da haka ne, ya yarda da sarki Srong-brtsan-sgam-po da ya auri gimbiya Wencheng.

Sarki Srong-brtsan-sgam-po ya yi farin ciki sosai da sosai, ya ba da umurnin gina wata babbar fada da ke kunshe da dakuna 999 don maraba da gimbiya Wencheng, ta haka an gina fadar Potala a birnin Lhasa. A sa'i daya kuma, an yi zana a kan bangon fadar Potala game da labarin Sarki Srong-brtsan-sgam-po, wato ya aika da Ludongzan da ya nemi aurar gimbiya Wencheng.

Gidan ibada na Xuan Kong na Shanxi wato 'Suspended Temple' a turance

Kowa ya sani, a yawancin lokutai a kan gina gidan ibada a doran kasa, amma a lardin Shanxi da ke arewacin kasar Sin, akwai wani gidan ibada da aka gina a kan bangon dutse, wai shi 'Gidan ibada na Xuan Kong', ko kuma 'Suspended Temple' a turance. An gina wannan gidan ibada a kusa da birnin Datong na arewacin lardin Shanxi a shekaru 1400 da suke wuce, gidan ibada ne kurum inda aka bauta wa Buddhism da Taoism da kuma Confucianism tare.

Gidan ibada na Xuan Kong yana cikin wani kwari. An gina shi a kan bangon dutse kamar an rataya shi a kan bangon dutse, idan wani ya hange shi daga nesa, yana da hadari sosai. Gidan ibada na Xuan Kong yana kunshe da dakuna da hasumiyoyi manya da kanana guda 40 gaba daya. An sa wasu katako a cikin bangon dutse, an mayar da wadannan katako bim ne na gidan ibada na Xuan Kong, ban da wannan kuma, an sa ginshikai na ice a karkashin gidan ibadan nan. An hada wadannan dakuna da hasumiyoyi guda 40 da hanyoyi, idan wani ya sa kafarsa kan wadannan hanyoyi, yana jin tsoron ko suna da karfi sosai , har ya hallaka gidan ibadan nan. Amma gidan ibadan nan ya dade yana kan bangon dutse lami lafiya. Wannan abin mamaki ne kwarai.

Nisan da ke tsakanin gidan ibada na Xuan Kong da kasa ya kai mita 50, ta haka ya iya gudu daga ambaliyar da ta kan mamaye dukan abubuwan da ke cikin kwarin. Wani katon dutse ya bullo daga bangon dutse, yana a kan gidan ibadan nan daidai, kamar gidan ibadan ya sa wata hula a kansa, wannan ya iya kiyaye gidan ibada na Xuan Kong daga ruwan sama da kuma hasken rana mai tsanani. An ce, ko a cikin lokacin zafi, rana tana yin awoyi 3 kawai a ko wace rana tana ba da haskenta a kan gidan ibada na Xuan Kong. Saboda haka ko da yake an gina gidan ibadan nan da katako, amma ya dade yana tsaye a nan lami lafiya.

Yawancin masu yawon shakatawa suna ganin cewa, gidan ibada na Xuan Kong yana dogara ga ginshikan da ke karkashinsa, amma a zahiri, a maimakon wadannan ginshikai, katakon da aka sa su cikin bangon dutse sun daure wa gidan ibadan nan gindi. Wasu ginshikan da ke karkashin gidan ibadan sun yi balas ne kawai, wasu kuma za su aiki idan akwai nauyi a kansu. Katako da ginshika wadanda aka yi amfani da su mai tauri ne kwarai. Kafin a yi amfani da su wajen gina gidan ibadan, sun jiku a cikin mai tukuna, saboda haka suna da karfi matuka, har sun iya gudu daga ruwan sama da kuma tururuwa.

An shirya manyan dakuna da kyau, an yi amfani da siffar bangon dutse yadda ya kamata. Yawancin dakunan kanana ne, ta yadda mutum-mutumin da ke cikinsu kanana ne. Amma babban daki na Sanguan yana da girma, saboda an haka wasu koguna a kan bangon dutse. Masu shakatawa suna tafiya kan hanyoyin da ska hada dakuna, kamar yadda suka tafiya a cikin wani labyrinth, har ma za su bata hanya.

Mutane sun ji mamaki donme aka gina gidan ibada a kan bangon dutse. Ashe, dalilin shi ne saboda hanyar da ke karkashin gidan ibada na Xuan Kong tana da muhimmnci sosai a fannin tafiye-tafiye a lokacin nan, mazaunin gidan ibadan nan ya dace da mutane masu kaiwa da kawowa da su kai ziyara da yin addu'a. Sa'an nan kuma yana kasancewa da wani kogi a gaban gidan ibada na Xuan Kong, a da can, a kan yi ruwan sama a wurin, ambaliya ta kan mamaye kome da kome, kowa da kowa ya ji tsoro. Mutane suna jita-jita cewa, wani dodo ya aikata wannan mummunan abu, shi ya sa aka gina gidan ibada a kan bangon dutse don hana wannan dodo.

Gidan ibada na Xuan Kong yana da girma matuka. Har ma an haka kalmomin sinanci guda 4 'Gong Shu Tian Qiao' a kan bangon dutse, ma'anarsu ita ce, babu wanda ya iya gina irin wannan gidan ibada mai kyau, sai Gongshu Ban ne kawai. Gongshu Ban shahararren mai zanen gine-gine ne da ya yi zama a kasar Sin a shekaru fiye da dubu 2, wanda a idon mutane, malami ne na dukan masu zanen gine-gine na kasar Sin. An yi amfani da wadannan kalmomi don girmamawar mutanen da suka gina gidan ibada na Xuan Kong.

Fadar sarakuna na daular Qing da ke birnin Shenyang

A cikin gine-gine masu sarauta da suke kasancewa a yanzu a kasar Sin, fadar sarakana na daular Qing da mazauninta a birnin Shenyang na arewa maso gabashin kasar Sin fada ce ta biyu a fannonin girma da kuma halin da take ciki a yanzu, in ana kwantanta ta da fadar sarakuna na Beijing, wato Forbidden City a turance. Bambancin da ke tsakaninta da shahararriyar fadar Forbidden City shi ne sarakuna na kabilar Manchu suka gina fadar sarakuna na daular Qing ta Shenyang, amma sarakuna na daular Ming suka gina fadar Forbidden City, sarakunan kabilar Manchu suka gyara ta, saboda haka ne ma fadar sarakuna ta Shenyang ta jawo hankulan mutane sosai domin tarihinta da kuma tsarin gine-gine na kabilar Manchu mai cikakken bambanci.

Fadar sarakuna ta Shenyang tana zauna a tsakiyar tsofaffin unguwoyi na birnin Shenyang, fadar gwamnatin lardin Liaoning da ke arewa maso gabashin kasar Sin, fada ce ta farko da sarakunan daular Qing suke zama tun daga shekarar 1616 zuwa shekarar 1911. Tarihinta yana da ban mamaki. A farkon karni na 17, makiyaya 'yan kabilar Manchu sun kafa gwamnatinsu a arewa maso gabashin kasar Sin, sarkinsu Nurhachi ya mayar da Shenyang kamar fadar gwamnatinsa, ya kuma fara gina fadarsa a wurin, bayan da ya mutu, dansa Huangtaiji ya gaje shi ya canja sunan daular Houjin da ya zama daular Qing, ban da wannan kuma ya kammala gina fadarsa, wato fadar sarakuna ta Shenyang. Sarakuna 2 na farko na daular Qing wato Huangtaiji da dansa Fulin sun hau kujerun mulkin kasarsu a fadar nan. Daga baya sojojin daular Qing sun lashe sojojin daular Ming, sun kafa sabuwar gwamnatin kasar Sin, sa'an nan kuma sun kaurar da fadar gwamantinsu zuwa nan birnin Beijing, tun daga nan ne sarakuna na daular Qing ya fara zama a cikin fadar sarukuna ta Beijing wato Forbidden City.

Maraba'in fadin fadar sarakuna ta Shenyang ya kai misalin mita dubu 60, akwai gine-gine fiye da 70 da kuma dakuna fiye da dari 3, bambancin da ke tsakaninta da fadar gargajiya ta kasar Sin shi ne tsarin gine-gine na kabilar Manchu mai cikakken bambanci. An raba fadar sarakuna ta Shenyang kashi 3 ne, wato gine-gine na tsakiya da na gabas da na yamma. Gine-gine na gabas sun fi nuna halin musamman na makiyaya. Sun hada da babban daki na Dazheng da kuma Ten-prince Pavilion a bakin turawa. Babban daki na Dazheng wani wuri ne da sarki ya kaddama da ayyukansa na yau da kullum da kuma aka yi manyan bukukuwa. Ten-prince Pavilion ofis ne na muhimman ministocin daular Qing. Babban daki na Dazheng da kuma Ten-prince Pavilion sun yi kama da tantunan da 'yan kabilar Manchu suka yi amfani da su a da. Canje-canjen gine-ginen kabiliar Manchu ya nuna canje-canjen bunkasuwar al'adun kabilar Manchu.

Yana kasancewa da kayayyakin kabilar Manchu masu yawa a cikin fadar sarakuna ta Shenyang, sun nuna al'adun gargajiya na 'yan kabilar Manchu matuka. Ga misali, wani dogon sanda da tsayinsa ya kai kusan mita 7 ya tsaya a gaban babbar kofar fadar Qingning. An ajiye wani faranti a kansa. Dogon sanda nan da ake kiransa 'Suolun' yana da muhimmanci sosai ga 'yan kabilar Manchu wajen hadaya. Bisa al'adun gargajiya na kabilar Manchu, a kan ajiye abinci a cikin farantin nan don kiwon hankaki. An fara yin wancen al'ada saboda wani labari mai ban mamaki. A can can can da an taba bin Nurhachi an nemi a kashe shi, Nurhachi ya rasa abin da zai yi, sai ya kwanta a wani kwalbati. A lokacin nan wasu hankaki sun sauka a kan jikin Nurhachi ba zato ba tsammani, sun rufe Nurhachi sosai, a sakamakon haka, Nurhachi ya gudu daga idanun masu binsa, hankaki sun ceto ransa. Bayan da ya zama sarki, Nurhachi ya ba da umurnin ga farar hula 'yan kabiliar Manchu da su ajiye wani dogon sanda tare da wani faranti a kansa a tsakiyar yadinsu don kiwon hankaki. Ban da wannan kuma, tsayin dakin kwana ya fi dakin falo a fadar nan.

A sa'i daya kuma a farkon daular Qing, sarakunan sun fara koyon al'adun kabilar Han, shi ya sa al'adun kabilar Han ta ba da tasiri a cikin fadar sarakuna ta Shenyang a bayyane. Alal misali, an yi amfani da tsarin gine-gine na daular Song wajen gina babban dakin Dazheng; sarakunan daular Qing sun nada sunauen dakunan kwana kamar yadda sarakunan kabilar Han suka yi, kamarsu fadar Guanju da kuma fadar Linzhi, wadannan sunaye sun zo daga sharararren littafi mai suna 'Shijing' na kabilar Han.

An fara gina fadar sarakuna ta Shenyang a shekarar 1625, an yi shekaru 10 ana gina ta. Daga bisani sarakuna Kangxi da Yongzheng da kuma Qianlong sun gyara ta da kuma hakaba ta, wannan ya dauki shekaru fiye da dari daya da hamsin, an hada tsarin gine-gine na kabilun Han da Manchu da Mongol da Hui da kuma Tibet gaba daya wajen gina fadar sarakuna ta Shenyang. Ma iya cewa, fadar sarakuna ta Shenyang ta zama wata muhimmiyar alama ce ta dinkuwar kasar Sin daya da kuma kasa mai yawan kabilu.

s

Labarin manyan kwazazzabai 3 na kogin Yangtze wato Sanxia na kogin Yangtze

Kogin Yangtze kogi ne na farko a kasar Sin, kuma na 3 ne a kasashen Asiya a fannin girma. Kwazazzabai guda 3 na kogin Yangtze suna shahara ne a duk duniya saboda shimfidarsu masu ban mamaki ne da kuma kyan shimfidar wurin. Kwazazzabai guda 3 su ne kwazazzabai na Qutang da Wuxia da kuma Xiling.

A mashigar kwazazzabon Qutang akwai wani shahararren birnin da ake kiransa 'birnin Baidi', wato White King City a bakin turawa. An samu sunansa daga wani labari na gaskiya a tarihi.

A shekarar 25, an yi juyin juya hali a kasar Sin. Manoma 'yan juyin juya hali sun hambarar da gwamnatin daular Xihan, amma ba su kafa sabuwar gwamnatin kasar ba tukuna. Wani janar wai shi Gongsun Shu yana mulkin kudu maso yammacin kasar Sin, yana jiran dama.

An ce, wata rana, Gongsun Shu ya yi mafarki, inda wani ya gaya masa cewa, zai yi shekaru 12 yana hau kujerar sarki. Bayan da ya farka, ya ji mamaki kwarai. Kashegari da safe, lokacin da yana yawo a lambu, ya ga farin hayaki ya fito daga wata rijiya, kamar wani farin dragon ya tashi daga rijiya zuwa sararin sama. Gongsun Shu yana ganin cewa, wannan alama ce da ke nufin cewa, zai zama sarki. Shi ya sa, ya shirya wani biki, yana kiran kansa sarki, ana kiransa sarkin Bai, ban da wannan kuma, an nada birnin da aka kafa a bakin kwazazzabon Qutang da sunan 'Birnin Baidi' wato 'birnin sarki Bai'.

Ma Yuan abokin arziki ne na Gongsun Shu, yana haziki sosai, da ya ji labarin nan, ya je wajen Gongsun Shu don neman samun aiki a gwamnatin Gongsu Shu. Amma Gongsun Shu ya ba da umurnin samar da wata rigar farar hula ga Ma Yuan, daga baya ya gana da Ma Yuan a fadarsa, inda ya nada masa marquis a bakin turawa, zai iya shugabancin dukan sojojin kasar. Masu bin Ma Yuan sun ji farin ciki matuka, suna alla-alla su kama aiki a gwamnatin Gongsun Shu. Duk da haka, Ma Yuan ya yi musu bayani cewa, 'yanzu ba a kwantar da kurar yake-yake a kasar Sin ba tukuna, babu wanda zai iya dinke kasar Sin gaba daya. Gongsun Shu bai yin shawarwari da kwararrun mutane kan manufofin kasar ba, a maimakon haka, ya fi mai da hankalinsa kan kananan abubuwa, shin zai iya jawo mutane masu hankali da su taimaka masa? ' Daga baya ya bar shi.

A lokacin nan, Liu Xiu ya riga ya kafa gwamnatin Donghan a birnin Luoyang, ya aika da wata wasika zuwa ga Gongsun Shu, inda ya yi bayani kan halin da kasar take ciki a lokacin nan, ya kuma shawo kansa da ya mika wuyansa. Amma a ganin Gongsun Shu, shi ne sarki, yaya zai mika wuyansa, saboda haka ya ki shawarar Liu Xiu. A shekarar 37, sojojin Liu Xiu sun kai wa Gongsun Shu hari, a karshe dai Gongsun Shu ya ci tura, har ya mutu.

Gongsun Shu ya yi shekaru 28 yana mulkin kudu maso yammacin kasar. A lokacin nan, an samu kwanciyar hankali a yankin, yake-yake ba su ba da tasiri a wurin ba. Ban da wannan kuma, Gongsun Shu ya bunkasa aikin noma da kuma aikin yin amfani da ruwa, ya kawo wa mutanen wurin alheri. A sakamakon haka ne, bayan da Gongsun Shu ya mutu cikin yaki, mutane sun gina gidan ibada mai suna Baidi a cikin birnin Baidi, don tunawa da Gongsun Shu.

Ban da birnin Baidi kuma,, akwai labaru da shahararrun wurare masu yawa a Sanxia na kogin Yangtze.

Yanzu ana yin aikin yin amfani da ruwa mafi girma a Sanxia na kogin Yangtze, wasu gine-gine da wurare sun nitse a karkashin ruwa, amma a sa'i daya kuma, masu yawon shakatawa za su ga wasu sababbin gine-gine da wuraren shakatawa a Sanxia na kogin Yangtze.

Kabari na Qianling da kuma alamar kabari ba tare da kalma a kanta ba

Kabarin Qianling da mazauninsa a arewacin kogin Wei na lardin Shaanxi na yammacin kasar Sin kabari ne daya tak da aka binne sarakuna 2 tare a cikin tarihin kasar Sin mai shekaru fiye da dubu 2. An binne sarki Li Zhi na daular Tang da kuma sarauniya Wu Zetian na daular Zhou tare, su ne sarakuna kuma miji da matarsa. Sarauniya Wu Zetian sarauniya ce daya tak da ta taba mulkin kasar Sin a cikin tarihin kasar Sin, dukan rayuwarta tana jawo hankali sosai. Bayan mutuwarta, an kafa wata babbar alamar kabari a gaban kabarinta, amma ba a rubuta kalma a kanta ba, ta haka ana kiranta 'alamar kabari maras kalma' wato 'Wordless Tombstone' a turance. Yanzu kabarin Qianling yana neman zama kayayyakin al'adu na tarihi na duniya.

An haifi madam Wu Zetian a shekarar 624, ta zama daya daga cikin matan sarki Taizong, sarki na biyu na daular Tang, lokacin da take shekaru 14 da haihuwa. Tun tana karama, madam Wu ta nuna kwarewarta. A lokacin nan sarki Taizong yana da wani dokin da babu wanda zai iya horar da shi, madam Wu ta gaya masa cewa, 'zan iya horar da shi, amma ina bukatar wata karfen bulala da wata wuka. Da farko a tsala masa bulala, idan ba ta da amfani, to, a bugi kansa, in ba a iya horar da shi ba, to, za a yanke makogwaronsa da wuka.' Da jin haka, sarki Taizong ya yi mamaki sosai kuma dan fushi, a ganinsa, bai kamata wata matarsa ta yi bayani haka ba, tilas ne ta bi da'a. Amma yarima Li Zhi yana so Wu Zetian a asirce, ko da yake ta fi shi girma da shekaru 4 da haihuwa.

Bayan da sarki Taizong ya riga mu gidan gaskiya, bisa dokokin da'a da aka tsara, an tilasta wa madam Wu Zetian da ta zama wata sista, Li Zhi ya hau karagar mulkin kasar a matsayin sarki Gaozong. Li Zhi ya dade yana tunawa da madam Wu, shi ya sa ba da dadewa ba ya dauko ta a fadarsa, ta haka madam Wu ta zama matar Li Zhi. Madam Wu ba ta gamsu da halin da take ciki a yanzu ba, tana neman zama sarauniya, wato 'queen' a turance, ta tuna da wata dabara. Sarauniyar sarki Gaozong madam Wang tana so yara kwarai da gaske saboda ba ta iya haihuwa ba. Wata rana, madam Wang ta ziyarci 'yar da madam Wu ta haifa ba da dadewa ba, tashinta ke da wuya, sai madam Wu ta shake 'yarta da kanta, daga baya ta rufe ta da bargo. Lokacin da sarki Gaozong ya cire bargo don kallon 'yarsa, ya gano cewa, ta riga ta mutu, yana firgita sosai, madam Wu ta yi ta kuka har ta suma. Sarki Gaozong ya yi wa baranyoyi tambaya cewa, wane ne ya kai ziyara dazu nan? Wata baranya ta ce, madam Wang ke nan. Sarki Gaozong ya ji fushi matuka, yana ganin cewa, madam Wang ta kashe wannan jaririya, tun daga lokacin nan ya fara kin jinin madam Wang. Bayan haka, madam Wu ta kulla wata makarkashiya daban, a karshe dai sarki Gaozong ya kori madam Wang daga mukamin sarauniya, ya nada madam Wu da ta zama sarauniya.

Bayan da madam Wu ta zama sarauniya, ta yi watsi da dokokin gargajiya da aka tsara wa mata, wato kada su sa baki cikin harkokin siyasa, ta fara daidaita ayyukan kasa, sa'an nan kuma, ta fara wulakanta Li Zhi sannu a hankali. Daga bisali, madam Wu ta maye gurbin mijinta Li Zhi wajen daidaita dukan ayyukan kasa.

Bayan da sarki Gaozong ya bakunci Lahira, madam Wu ta daidaita dukan ayyukan kasa da kanta ita kadai, ta kori sarakuna 2 na daular Tang daga mukaminsu baya bayan daya, ban da wannan kuma, a lokacin shekarunta 67 da haihuwa, ta hau kujerar mulkin kasar Sin a hukunce, ta zama 'sarki', ta canja daular Tang da ta zama daular Zhou.

Bayan da ta fara mulkin kasar Sin, madam Wu ta kashe dukan wadanda suke adawa da ita, har da 'ya 'yansa masu jiran hawan kujerar mulkin kasar.

Tsohon jami'in tsaro na daular Tang Xu Jingye da Luobin Wang, wani shahararren marubuci a fannin waka sun tayar da yaki don nuna wa madam Wu kiyaya. Luobin Wang ya rubuta wani abu kan laifuffukan da madam Wu ta aikata don yin kira a kai wa madam Wu Zetian hari. Madam Wu ita ma ta karanta abun nan, da ta gama, ta yi murmushi, ta yaba wa marubucin da ya rubuta abun nan saboda kwarewarsa. Ta ce, 'wannan marubuci ya gwada gwanintarsa sosai, amma ba ya aiki a gwamnatimmu, kai, wannan kuskure ke nan da waziri ya yi.' Nan da nan ta aika da sojojin da yawansu ya kai dubu dari 3 don kashe 'yan tawayen.

Amma a wani bangare daban kuma, madam Wu Zetian ta mai da hankali kan aikin noma, ta yi jarabawa a duk kasarta don zaben mutane masu kwarewa, ban da wannan kuma ta yi kokarin daga matsayin mata. Madam Wu ta yi shekaru 15 tana kan kujerar wata sarauniya, amma ta yi shekaru 50 tana mulkin kasar a zahiri. Lokacin take mulkin kasar, karfin kasar Sin sai karuwa take ta yi, an samu kwanciyar hankali da bunkasuwar tattalin arziki, kowa da kowa ya ji dadin rayuwarsu.

Madam Wu Zetian ta bakunci Lahira lokacin da shekarunta ya kai 82 da haihuwa, an binne ta da mijinta sarki Gaozong na daular Tang tare a cikin kabarin Qian Ling, kuma an kafa wata 'alamar kabari maras kalma' a gaban kabarinsu. Alamar kabarin nan tana da kyaungani sosai, amma ba a sassaka kalma a kanta ba.

Game da dalilan da suka sa madam Wu ba ta sassaka kalma a kan alamar kabarinta ba, mutane na da ra'ayi daban daban. Wasu suna ganin cewa, dalilin haka shi ne saboda madam Wu ta yi takama, tana tsammani nasarorin da ta samu ba za a iya rubuta su ba; wasu sun yi la'akari cewa, madam Wu ta hambarar da tsarin gargajiya na kasar Sin, wato maza suna mulkin kome da kome, ta ji kunya sosai, ba ta da jaruntakar sassaka kalma a kan alamar kabarinta; a ganin wasu kuma, dalilin shi ne madam Wu ba ta san ko ta yi amfani da 'sarauniyar daular Tang, matar sarki Gaozong' ko kuma 'sarauniyar daular Zhou Wu Zetian', shi ya sa ba ta rubuta kalma ba. Amma a idon yawancin mutane, madam Wu tana da wayo sosai, ba ta rubuta kalma a kan alamar kabarinta ba, ko ana sonta ko a'a, kowa da kowa ya iya fadi albarkatun bakinsa.

Labarin babban dutsen Lushan

Babban dutsen Lushan yana cikin lardin Jiangxi na kudancin kasar Sin, shimfidar wurin tana da kyau matuka, kuma jawo hankulan mutane. Tun da can babban dutsen Lushan yana shahara a duniya gaba daya ne saboda tsayinsa da kwazazzabai masu tsayi da magangarar ruwa mai kyangani. Mawaka da masana masu ilmin al'adu da ba a iya kidaya yawansu ba sun yi ta zuwa babban dutsen nan, inda suka rubuta wakoki, wato poems a turance, da kuma yi zane-zane. Wani shahararren mawaki na daular Song Su Shi ya sha ziyarar Lushan, ya taba rubuta cewa, yaya wanda ya yi bayani kan gaskiyar yadda babban dutsen Lushan yake, lokacin da yake cikin babban dutsen nan?

Ana kiran babban dutsen Lushan 'Kuanglu' ko kuma 'babban dutsen Kuang'. An ce, lokacin daular Zhou na karni na 4 kafin haihuwar Annabi Isa, wani malam wai shi Kuang Su ya yi nazarin ilmin Daoism a babban dusten Lushan, sarki na daular Zhou ya ji haka, sai ya sha gayyatarsa don ya zama wani jami'i na gwamnatinsa, amma malam Kuang Su ya ki karbar gayyatar da ya yi masa. Daga baya ya bace, ana jita-jita cewa, ya zama wani wanda ba ya mutuwa, saboda haka, tun daga lokacin nan ana kiran wannan babban dutse 'Lushan' ko 'Kuangshan' ko kuma 'Kuanglu'.

A lokacin daular Dongjin ta shekarar 381, wani sufi masi suna Hui Yuan ya je babban dutsen Lushan tare da sufaye masu binsa, ya gina gidan ibada na Donglin tare da taimakon gwamna na Jiangzhou, daga bisali ya fara ba da ilmi na darikar Pure Land na addinin Buddhism a nan, sannu a hankali gidan ibada na Donglin ya zama cibiya ne da aka ba da ilmin addinin Buddhism a kudancin kasar Sin. Sufi Hui Yuan ya yi shekaru 36 yana shugabancin gidan ibada na Donglin, ya bi addinin Buddhism kuma yana da ilmin addinin Buddhism masu yawa, kowa da kowa ya nuna masa girmamawa.

Akwai labaru daya game da gidan ibada na Donglin da sufi Hui Yuan har yanzu. An ce, a lokacin gina gidan ibada na Donglin, saboda karancin katako, Hui Yuan ya yi ta zulumi kan wannan. Wata rana da dare, ba zato ba tsammani ana tsawa ana walkiya, jin kadan ana babban ruwa, an tilasta wa dukan sufaye a dakinsu kawai. Kashegari ruwa ya dauke, suyafe sun ji farin ciki sosai saboda ganin wani dan tabki ya bullo a gaban dakinsu. Hui Yuan yana ganin cewa, Allah ne ya ba su wadannan katako don gina gidan ibada na Donglin. Shi ya sa ya sa a gina babban daki da wadannan katako, kuma ya nada wannan babban daki 'Shen Yun', wato 'God-Send Hall' a turance, ma'anasa ita ce Allah ne ya bayar da wannan babban daki, ban da wannan kuma Hui Yuan ya nada dan tabki inda katako suka bullo 'dan tabki na gidan katako', wato 'Wood's home Pond' a bakin turawa.

A gaban gidan ibada na Donglin yana kasancewa da wani dan tabki daban da cike yake da furen farin Lotus. An ce, malam Xie Lingyuan na daular Dongjin ne ya haka wannan dan tabki. Malam Xie Lingyuan tattaba-kunne ne na shehararren dan siyasa na daular Dongjin Xie Xuan, kuma dan wa ne na Wang Xizhi, wanda ya yi suna ne a fannin chirography a turance, ko da yake yana da haziki sosai, amma yana da girman kai. Ya je babban dutsen Lushan don shiga kungiya mai suna farin Lotus da Huiyuan ya kafa. Amma Hui Yuan ya ki shigar da shi, ya gaya wa malam Xie Lingyuan cewa, kana da girman kai sosai, to, ka haka 'yan tabki guda 3 tukuna, ba za ka shiga kungiyata ba, illa ka kwantar da hankalinka. Ba yadda zai yi, sai Xie Lingyuan ya haka 'yan tabki guda 3, daga baya an amince da shigarsa cikin kungiya wai ita farin Lotus. Hui Yuan da Xie Lingyuan sun kan yi hira da juna, sannu a hankali, sun girmama juna sosai, sun sada zuzmunta a tsakaninsu. Bayan Hui Yuan ya bakonci Lahira, Xie Lingyuan ya ji bakin ciki kwarai, ya je babban dutsen Lushan daga birnin Jiankang (wato birnin Nanjing na yanzu) don rubuta taken tunawa a kan kabarin Hui Yuan.

Yanzu babban dutsen Lushan ya zama shahararren wurin shakatawa ne a kasar Sin, a ko wace shekara mutane daga wurare daban daban na gida da na waje sun yi ta zuwa babban dutsen Lushan ziyara.

Labarin babban dutsen Huangshan

Babban dutsen Huangshan da ke kudu maso tsakiyar kasar Sin wurin yawon shakatawa ne da ya yi suna a duk duniya, yana daya daga cikin kayayyakin tarihi na duniya a fannin gandun daji. Da can ana kiran Huangshan 'Youshan', saboda duwastun da ke wannan babban dutse suna da baki makil. Amma don me ake kiransa 'Huangshan' a maimakon 'Youshan'?

Sarki Huangdi kakan kaka ne na kabilar kasar Sin a cikin tastuniyar da aka watsa a kasar Sin, an ce, ya yi shekaru fiye da dari yana mulkin kasar Sin, farar hula suna sonsa kuma suna girmamawarsa sosai. Lokacin ya yi tsufa, ya mika mukamin sarki ga wani saurayi wai shi Shaohao. Sarki Huangdi mutum ne mai son jin dadin rayuwa, ba ya so ya yi tsufa har ya mutu, shi ya sa ya yanke shawarar neman samun wata hanyar da idan zai bi, ba zai yi tsufa ba kuma ba zai mutu ba. Ya yi koyi daga wajen Rong Chengzi da kuma Fu Xiugong da suke bin addinin Dao, yana koyon ilmin samar da magani wato ilmin alchemy a turance, don neman kada ya tsufa da mutu ba.

Addinin Dao addini ne da ya samu asalinsa a kasar Sin, a cikin farkon tarihinsa, mutanen da suke bin addinin nan su kan sarrafa magani don neman ba zai mutu ba. Tilas ne a sarrafa magani a wurin da ya fi kyau. Shi ya sa sarki Huangdi da kuma Rong Chengzi da Fu Qiugong sun je neman wurin da ya fi dace da sarrafa magani.

Sun yi ta tafiya sun yi ta tafiya, har sun ziyarci dukan wuraren kasar, a karshe dai sun isa babban dutsen Youshan da ke kudu maso tsakiyar kasar. Akwai manyan duwatsu da yawa a wurin, wadanda suke da tsayi sosai, gajimare suna kewayen wadannan duwatsu a duk rana; haka kuma kwari cike yake da gajimare masu yawa. Huangdi da 'yan rakiyarsa suna tsammani wannan ne wurin da ya fi dacewa da sarrafa magani.

Sun cire itatuwa sun tsinke ganyayen magunguna a ko wace rana, ko ana iska ko ana ruwa, ba su daina ba. An ce, tilas ne a sarrafa magani har sau 9, in ba haka ba, ba zai fara aiki ba. Sun yi ta sarrafawa, ko da yake sun kara fuskantar matsala, amma Huangdi ya kara nuna niyyarsa. Sun yi shekaru 480 suna himmantu kan wannan. A karshe dai sun ci narasar samar da magani. Huangdi ya sha wani magani, nan take ya ji kamar yana iya tashi kamar tsuntsu. Ban da wannan kuma, gemunsa da gashinsa ya zama baki, amma fatansa ya yi kamar yadda ya yi a da, bai canza ba.

A lokacin nan a tsakiyar wani babban dutse sai wani jan ruwa, ya bulla yana da zafi kuma yana da kamshi. Shi ya sa Fu Qiugong ya gayyaci Huangdi da ya yi wanka a cikin wannan ruwa. Huangdi ya yi kwanaki 7 yana yin wanka a ruwan, 'yan tamoji da ke fuskarsa sun bace saboda ruwan. Huangdi ya sake samun kuruciya, ta haka ya zama mala'ika, ba zai damuda zai tsufa ko zai mutu ba. Saboda Huangdi ya zama mala'ika a nan, shi ya sa ake kiran wannan babban dutse 'Huangshan' a maimakon 'Youshan'.

Wani ginshikin dutse da ke babban dutsen Huangshan ya shahara a duniya. Akwai babbban ginshiki na dutse a wani kwari, yana da tsayi sosai, sai ka ce wani alkalami na Sinnawa, wato brush Pen a turance, wani itace yana zama a kan wannan ginshiki, in a hangi daga nisa, sai ka ce an fid da fure a kan wannan ginshiki, shi ya sa Sinnawa suna kirar wannan ginshiki 'Miao Bi Sheng Hua'.

A da can, shahararren marubucin mawaki na kasar Sin Li Bai ya yi wani mafarki a wata rana da dare, ya sauka wani babban dutse tare da iska. Ba zato ba tsammani wani babban alkalami na Sinnawa ya bullo daga tekun gajimare, Li Bai yana so ya yi amfani da wannan alkalami ya rubuta dukan abubuwan da yake so. A lokacin nan ya ji kide-kide masu dadin ji, ya ga haske mai launuka daban daban ya bullo daga wannan alkalami, daga baya an sami fure mai launin ja a alkalamin nan. Sannu a hankali alkamali mai dauke da jan fure ya matsa masa, da zarar ya mika hannunsa, sai ya farke, ashe, wani mafarki ne kawai.

Bayan hakan, Li Bai ya yi ta tafiya a duk kasar Sin don samun wurin da ke cikin mafarkinsa. A karshe dai ya isa Huangshan, ya ga wannan babban ginshikin dutse, ya fara gano cewa, ashe, alkalamin da ya yi ta nema yana nan ne.

Bayan da ya ga wannan ginshikin dutse, Li Bai ya fara gwada gwanintarsa, ya rubuta wakoki masu kyau da yawa.

Labarin gidan ibada na tunawa na Jin

Kowa ya sani cewa, gine-gine da lambuna na gargajiya na kudancin kasar Sin sun shahara a duk duniya gaba daya, amma a arewacin kasar Sin akwai wani shahararren gidan ibada na gargajiya, wato gidan ibadan tunawa na Jin da ke kewayen birnin Tai Yuan na lardin Shanxi.

Gidan ibada na tunawa na Jin yana gindin dutsen Xuan Weng da ke kudu maso yammacin birnin Taiyuan, inda kogin Jin Shui ya fara malala. Idan wani mutum ya shiga wannan gidan ibada na tunawa, sai ka ce ya shiga wata zana, har ya manta da dawowa. An baza labarai da yawa game da gidan ibada na tunawa na Jin, wato memorial temple Jin.

A shekarar 1064 kafin haihuwar Annabi Isa A.S., bayan shekaru 2 da ya hambarar da gwamnatin daular Shang, sarki Wu da ya kafa daular Zhou ya bakunci Lahira, dansa Ji Song ya gaje shi, ya zama sarki Cheng na daular Zhou a tarihin kasar Sin. An ce, lokacin da ya hau kujerar mulkin kasar, sarki Cheng yaro ne kwarai, a ko wace rana ministansa Zhou Gong ne ke goya shi a bayansa zuwa fadarsa, inda ministoci suke yin fadanci. Saboda sarki Cheng yana karami, shi ya sa Zhou Gong ya goyi bayansa ya sa hannu cikin harkokin siyasa na yau da kullum. Zhou Gong wani amintaccen mutun ne, ya kwantar da tawaye a jere, kuma ya himmantu ga koyar da sarki Cheng ilmin mulkin kasa.

Wata rana, sarki Cheng da dan'uwansa Shu Yu suna yi wasa a lambun fada, ya yanke wani ganye ya ba dan'uwansa, ya ce, 'Zan nada kai da ka zama gwamnan wani wuri.' Zhou Gong ya san wannan abu. Bayan 'yan kwanaki, Zhou Gong ya roki sarki Cheng da ya nada Shu Yu da ya zama gwamna. Sarki Cheng ya yi murmushi ya ce: 'kai, na yi barkwanci da shi.' Amma Zhou Gong ya ce: 'kada sarki ya yi barkwanci, tilas ne ministan tarihi ya dauki maganganun da sarki ya fadi, haka kuma mawaka su yi waka a kansu, ministocin kasar su aiwatar da su.' Saboda haka sarki Cheng ya canja ra'ayinsa, ya ba Shu Yu wani wuri mai suna Tang.

Wurin Tang na lokacin nan garin Yi Cheng ne na yanzu da ke lardin Shanxi. Bayan da Shu Yu ya yi girma, ya je Tang yana mulkin wurin, ya raya aikin noma da kuma aikin yin amfani da ruwa, ta yadda sannun a hankali, farar hula na wurin sun ji dadin rayuwarsu, sun yaba wa Shu Yu sosai. Daga baya dansa Xie Fu ya canja sunan wurin zuwa Jin a maimakon Tang, saboda kogin Jin da ke wurin ya kawo wa farar hula alheri, saboda haka ne, ake kiran Shanxi 'Jin' a takaice. Mutane sun kafa gidan ibada na tunawa kusa da idon ruwa na kogin Jin don tunawa da Shu Yu, ana kiransa gidan ibada na tunawa na Shu Yu ko kuma na Jin.

Ba a iya tabbatar da lokacin da aka gina gidan ibada na tunawa na Jin ba. An gano sunanasa ne a karo na farko a cikin wani littafi wai shi na daular Bei Wei da aka rubuta tsakanin shekarar 466 da 572. A sabili da haka ne, an kiyasta cewa, an gina gidan ibada na tunawa na Jin a daular Bei Wei, ya yi shekaru fiye da dubu daya yana zama a wurin. A cikin shekaru masu yawa da suka wuce, an taba yin kwaskwarima da kuma kyautata gidan ibada na tunawa na Jin sau da yawa. a shekarar 646, sarki na biyu na daular Tang Li Shimin ya ziyarce shi, ya rubuta wata shahararriyar waka, ya kuma ba da umurnin kara girman wannan gidan ibada na tunawa. A karni na 11, sarkin daular Song ya gina babban dakin tunawa da Shengmu Yi Jiang, mamar Shu Yu. Ta haka an fara samar da manyan gine-ginen da ke kewayen babban dakin Shengmu sannu a hankali.

Ba ma kawai akwai gine-ginen da aka gina a dauloli daban daban na kasar a gidan ibada na tunawa na Jin ba, har ma akwai wadanan itatuwa guda 2 a nan. An ce, an dasa itacen cypress a daular Xi Zhou (tsakanin karni na 11 kafin Annabi Isa da karni na 8 kafin Annabi Isa), ya yi shekaru kusan dubu 2 yana zama a hagu da babban dakin Shengmu. Haka kuma shekarun wani itace daban ya kai dubu daya da wani abu da haihuwa, an dasa shi a daular Sui ta kasar Sin. Ko da yake sun yi tsufa sosai, amma suna da kuruciya a yanzu. Idan ka kai ziyara a lardin Shanxi, to, tabbas ne ka ziyarci gidan ibada na tunawa na Jin.

>>[Tatsuniyoyi]

Ko da yake yana da wayo a lokacin kanana, amma watakila ne ba zai ci nasara ba bayan da ya girma

Confucius wani shahararren kwararre ne a fannonin tunani da aikin ba da ilmi, wanda ya yi zamani a karni na 6 kafin haihuwar Annabi Isa. Wasu tattaba-kunnensa sun yi suna kamar yadda Confucius ya yi. Kong Rong tattaba-kunne ne na Confucius. Kong Rong wani masani ne da ya yi zama kasar Sin a lokacin daular Han na karni na 2 bayan haihuwar Annanbi Isa. Saboda iyalansa, tun lokacin da yana kanana, Kong Rong yana da wayo sosai, musamaman ma yana gwada gwanintarsa a fannoni daban daban, ko da yake yana kanana, amma ya yi suna.

Labarin da aka gabatar game da shi aka samu ne daga wani shahararren littafi na gargajiya na kasar Sin wai shi 'Shi Shuo Xin Yu', wato 'New Account of Tales of the World' a turance.

A lokacin da shekarun Kong Rong ya kai 10 da haihuwa, babansa ya kai shi birnin Luoyang don ziyarar gwamnan wurin Li Yuanli. Li Yuanli wani masani ne mai suna kuma mai alfarma, ko wace rana mutane da yawa sun je wayensa don yin masa gaisuwa, amma idan mai kai ziyara mutum ne da bai yi suna ba, to, kamar yadda ya kan yi kullum mai gadi zai hana shi shiga.

Kong Rong yana alla-alla yin wa wannan masani gaisuwa. Wata rana ya je kofar gidan Li Yuanli, ya roki mai gadi da ya yarda da shigarsa. Amma a idon mai gadi, shi yaro ne kawai, shi ya sa ya kore shi. Kong Rong ya yi dabara, ya gaya wa mai gadi cewa, ni ne wani dangi na malam Li, tabbas ne zai gana da ni.

Da Li Yuanli ya ji haka, ya yi mamaki sosai, saboda ba ya da irin wannan dangi. Duk da haka yana so ya gana da Kong Rong.

Da ganin yaron nan, Li Yuanli ya yi masa tambaya cewa, 'shin mene ne dangantakar da ke tsaknina da kai, kai ne dangina?'

Kong Rong ya amsa cewa, 'ni ne zuriyar Confucius, kai ne zuriyar Lao Zi. Kowa da kowa ya sani, Confucius ta taba koyon ilmin da'a daga wajen Lao Zi, shi ya sa su dalibai na da malami, saboda haka ne iyalanka da iyalina mun kafa dangantakar abokantaka a tsakanin 'ya yansu.'

Ashe, a tarihin kasar Sin, a lokacin Confucius, akwai wani shahararren mai falsafa da ake kiransa Lao Zi. An ce, Confucius ya taba koyon ilmin da bai sani ba daga wajen Lao Zi, ya kira kansa dalibi.

Li Yuanli da bakinsa sun ji mamaki sosai game da amsar Kong Rong, ko da yake yana kanana, amma yana da ilmi a fannoni daban daban, kuma yana da wayo kwarai.

A lokacin nan wani mutum mai suna Chen Wei ya je gidan Li Yuanli. Shi ma wani shehun malami ne mai suna. Bakin da suke gidan Li Yuanli, sun gaya masa abin da ya faru a dazun nan. Amma Chen Wei ya gaya wa Kong Rong cewa, 'ko da yake wani mutum yana da wayo kwarai a lokacin yarantakarsa, amma bai ci nasara bayan da ya girma ba.' Nan take Kong Rong ya ce, 'ina tsammani lokacin yarantakarka, tabbas ne malam Chen kana da wayo matuka.' Nufin Kong Rong a zahiri shi ne Chen Wei mutum ne banza a yanzu. Chen Wei ya ji kunya kwarai da gaske saboda maganar Kong Rong.

Ban da wannan kuma, akwai wani labari mai suna a kasar Sin game da Kong Rong a fannin da'a. A lokacin da Kong Rong yake karami, iyalansa sun ci 'ya 'yan itatuwa tare, ya kan ba masu gabansa babban 'ya 'yan itatuwa, shi ya zabi kananan, ya yi ladabi da biyayya yadda ya kamata.

Bayan da Kong Rong ya yi girma, ya kara gwada gwanintarsa sosai, har ya zama wani gwamna. Amm a lokacin nan an fara kawo baraka ga kasar Sin, Kong Rong ya kan nuna damuwarsa da rashin jin dadinsa a cikin abubuwan da ya rubuta kan halin da kasarsa take ciki, a karshe dai wani shahararren dan siyasa na lokacin nan Cao Cao ya kashe Kong Rong.

Idan wani ya yi amfani da kwarewarsa yadda ya kamta, in akwai dama zai ci nasara.(A Crow That Shocks All)

Karni na 9 kafin haihuwar Annabi Isa A.S. zuwa karni na 5 kafin haihuwar Annabi Isa A.S., a lokacin kananan dauloli na Sin suna yaki da juna, wato lokacin Warring States a turance, yana kasancewa da kananan dauloli goma gomai, idan suna so su ci gaba da zamansu, to, tilas ne su mai da hankulansu kan aiwatar da nagartattun manufofi na gida da na waje, a sakamakon haka, masu ba da shawara ga sarakuna sun kaddamar da ayyukansu. Wadannan mashawarta suna da ra'ayoyi kan falsafa da mulkin kasa, musamman ma sun yi amfani da labaru masu ban sha'awa kamar shawarwari don shawo kan sarakunansu. A maimakon fushi, sarukuna sun karbi shawarwarin.

Akwai wani labari game da wani mashawarci wai shi Chun Yukun ya shawo kan sarkinsa.

Sarki Qiwei sarki ne da bai dade yana mulkin kasar Qi ba. Lokacin da yake jiran hawan kujerar sarki a matsayin yarima, ba ma kawai ya koyi ilmi cikin himma da kwazo ba, har ma ya mai da hankali kan hanyoyin mulkin kasa, yana fatan zai gina kasar Qi da ta zama wata kasa mai karfi bayan da ya zama sarki. Amma bayan da ya hau karagar mulkin kasar, ya gano cewa, sarki ya iya mulkin kome da kome, ya fi jin dadin rayuwarsa sosai. Lokacin da suke fadanci a ko wace rana da safe, ministocinsa suna keyawansa, lokacin da yake fadarsa, ya iya ci abinci mai kyau, mata masu kyangani suna kewayensa, sannu a hankali, ya yi watsi da fatansa.

Shekaru 2 sun wuce, sarki Qiwei ya kara mai da hankalinsa kan shan giya da yin wasa da mata, abin da kurum yake yi a ko wace rana shi ne shan giya da farauta, ya bar dukan ayyuka ga ministocinsa. Shi ya sa siyasa ya fara lalacewa, jami'ansa sun fara cin hanci da rashawa, karfin daular Qi sai raguwa yake yi, daulolin da ke makwabtaka da ita sun yunkuri kai mata hari. Jami'ai masu kyau da farar hula sun nuna damuwarsu sosai, amma sun ji tsaron ba da shawara ga sarki Qiwei, suna jin fargabar a yi musu laifuffuka.

Wani mashawarci mai suna Chun Yukun mutum ne mai fasahar magana sosai, ya kan yi amfani da almara mai ban sha'awa lokacin da yake mahawara da saura. Lokacin da ya ji labarin cewa, wai sarki Qiwei yana son yin amfani da almara don nuna wayonsa, shi ya sa ya yanke shawarar neman wata dama don shawo kansa.

Wata rana Chun Yukun ya yi wa sarki Qiwei gaisuwa, ya ce, 'ranka ya dade, ina da wani ka-cinci-ka-cinci.' Sarki Qiwei ya ce, 'to, fadi in ji.'

Chun Yukun ya bayyana cewa, 'akwai wani babban tsuntsu a cikin wata kasa, ya yi shekaru 3 yana zama a fadar sarki, amma bai kada fikafakai ba, kuma bai rera waka ba, abin kurum da ya kan yi kullum shi ne kwanta a cikin kejinsa, ranka ya dade, shin ka san wannan tsuntsu?'

Da zarar jin haka, sai sarki Qiwei ya san Chun ya yi masa suka saboda shi ne sarki amma bai dauki alhaki bisa wuyansa ba. Amma ya zai ba da amsa?

Ya yi zulumi kan amsarsa, daga baya ya gaya wa Chun Yukun cewa, 'kai ba ka sani ba? Wannan babban tsuntsu idan yana so ya kada fikafikansa, to, zai tashi zuwa sararin sama, idan yana so ya rera waka, to, kowa da kowa zai ji wakarsa sosai, ka jira ke nan.'

Tun daga lokacin nan, sarki Qiwei ya yanke shawarar daidaita kuskuren da ya yi a da, zai yi ayyukansa don kawo wa jama'arsa alheri. Da farko, ya dauki matakai wajen tafiyar da ayyukan gwamntinsa yadda ya kamata, ya gana da dukan jami'ansa, ya ba da kyauta ga wadanda suka dauki nauyinsu, a sa'i daya kuma ya yanke wa masu cin hanci da rashawa hukunci. Daga bisani a fannin aikin soja, ya dauki matakai don kara karfin soja. Daular Qi ta samu kyautatuwa sosai cikin sauri, jama'ar wurin suna jin dadin zamansu kwarai. Dukan daulolin da suke son kai wa daular Qi hari sun yi mamaki matuka da jin haka, sun kwatanta sarki Qiwei da babban tsuntsu, yana da karfi sosai, idan yana so, zai iya tashi zuwa sararin sama.

Tun daga nan, a kan kwatanta cewa, idan wani mutum yana da kwarewa, muddin ya yi amfani da ita yadda ya kamata, to, zai ci nasara.

Harbi wani ganye da nisan taki dari (wato Shoot An Arrow Through A Willow Leaf A Hundred Paces Away)

A can can da a kasar Sin, a cikin lokacin Zhanguo, lokacin da daulolin kasar Sin suke yaki da juna wato shekarar 403 zuwa shekarar 221 kafin haihuwar Annabi Isa A.S., an kasance da kananan dauloli da yawa. Akwai shahararrun mutane da suka yi zamani a wadannan kananan dauloli, ya zuwa yanzu labaransu na bazuwa.

Akwai wani shahararren janar a daular Qin, wanda sunansa Bai Qi, ya iya yin yaki kwarai. Saboda ko kusa bai ci tura a cikin dukan yake-yaken da yake jagoranci ba, shi ya sa ana kiransa 'sarkin yaki'. Wata shekara, sarkin daular Qin ya aika da Bai Qi da ya shugabanci sojojinsa don kai wa daular Wei hari. Idan daular Qin ta ci daular Wei, to, za a haddasa al'amura da yawa a tsakanin wadannan kanana dauloli, shi ya sa mutane masu yawa sun nuna damuwarsu sosai kan wannan.

An ba da umurni ga wani mai ba da shawara Su Li da ya shawo kan Bai Qi da kada ya kai hari ga kasar Wei. Su Li ya yi dabara don yi wa Bai Qi gaisuwa, ya gaya masa wani labari kamar haka:

Akwai wani mutum da ya iya harba kibiya sosai, sunansa Yang Youji. Tun lokacin da yake karami, ya fara koyon harba kibiya, ya iya harbin wani ganyen ice daga inda ke nisan taki dari. A lokacin nan kuma, akwai wani mutum daban da shi ma ya iya harba kibiya, sunansa Pan Hu. Wata rana sun yi gasa, mutane da yawa sun tsaya suna kallo.

An kafa wani abin bara da nisan da ke tsakaninsa da maharba ya kai taki 50. An sa wani digo ja a tsakiyar abin bara. Pan Hu ya harba kibiyoyi guda 3, ko wanensu ya kai buzaye daidai, mutane, 'yan kallo sun yi ta tafi.

Yang Youji ya waiwayi nan, ya waiwayi can, a karshe ya ce, 'abin bara nan ya yi kusa sosai, kuma ya faye girma. To, ya fi kyau mu harbi ganyayen da ke kan icce, ga shi nisan da ke tsakaninsa da mu ya kai taki 100.'

Ya sa a zabi wani ganyen da ke kan iccen, ya shafe shi ja. Daga baya, ya harbi wata kibiya, wannan kibiya ya zarce tsakiyar ganyen nan daidai.

Kowa da kowa ya yi mamaki sosai. Pan Hu ya gane ba ya da irin wannan kwarewa, amma bai gaskata cewa, Yang Youji zai ya harba ganyaye da ko wace kibiyarsa ba, shi ya sa ya matsa wa wannan icce, ya zabi ganyaye guda 3, ya rubuta lamba a kansu da launuka iri guda 3, daga baya ya gaya wa Yang Youji da ya harbi wadannan ganyaye 3 baya bayan daya.

Yang Youji ya je wajen iccen, ya dudduba lambar da ke kan ganyayen, daga bisani, ya koma baya, ya harbi kibiyoyi guda 3 a jere, kai, ko wanensu ya zarce tsakiyar ko wane ganyayen. A sakamakon haka, mutane suna ban tafi da babbar murya, Pan Hu kuma ya girmama Yang Youji sosai.

Ana cikin wannan hali ne, amma wani mutumin da ke kusa da Yang Youji ya bayyana cewa, 'idan ka iya harbin ganye daga nesa kamar haka, to, zan koya maka.'

Yang Youji ya ji fushi saboda maganarsa, ya juya baya ya ce, 'shin yaya za ka koya mini?'

Wannan mutum ya ce, 'ba zan koya maka fasahohin harbi ba, a maimakon haka, zan tuna maka yadda za ka kare girmamawar da ake nuna maka wajen harbi. Ko ka taba yin la'akari da cewa, idan karfinka ya kare, ko kuma ka yi kuskure kadan, muddin ka ci tura, to, wannan zai ba da babban tasiri maras kyau kan sunanka. Idan wani ya iya harbi sosai, ya kamata ya mai da hankali wajen kiyaye girmamawar da ake nuna masa.'

Bayan labarin nan, Su Li ya gaya wa Bai Qi cewa, 'ana kiranka 'sarkin yaki', amma daular Wei ba wata daular da ka iya lashe ita cikin sauki ba, idan ba ka ci nasara nan da nan ba, to, wannan zai kawo illa ga sunanka. Da jin haka, Bai Qi ya gane idan yana so ya kiyaye suna na 'sarkin yaki', to, zai yi yaki bayan ya yi la'akari da abubuwa da yawa, a sabili da haka ne, ya nemi wata hujja ta wai ya kamu da ciwo, to, shi ke nan an daina kai wa kasar Wei hari.

Zuwan Chang'e a duniyar wata

Ranar murnar wani muhimmin bikin gargajiya ne na Sinawa, wanda a kan yi shi a tsakiyar watan Agusta, bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato lokacin da aka samu cikakken wata. A ran nan, iyalai su kan taru, suna cin wainar wata tare da 'ya'yan itatuwa. Yanzu, ga wani labari dangane da bikin nan.

Chang'e wata kunkiya ce ta duniyar wata, kuma mijinta Houyi wani jarumin yaki ne, wanda ke da tsananin kwarewa wajen harba kibiya. A lokacin, dodanni masu yawa sun fito a duniya, wadanda suka kawo wa dan Adam barna. Bayan da sarkin gumaka ya sami labarin, sai ya aika da Houyi zuwa kasa don ya murkushe wadannan dodanni.

To, shi ke nan Houyi ya sauka a kasa tare da kyakkyawar matarsa Chang'e. Sabo da jaruntakarsa, da sauki ne ya kashe wadannan dodanni. Amma, a daidai lokacin da ya kammala aikinsa, rana guda har goma sun fito a sararin sama.

Lalle ne, wadannan rana guda goma 'ya'ya ne na sarkin gumaka, kuma sun fito tare ne don barkwanci. Amma sabo da aikinsu, an fara zafi sosai, har ma bishiyoyi da amfanin gona duk sun kama wuta, koguna sun bushe, an iya ganin gawawwaki ko ina.

Tausayi ya kama Houyi, sai ya lallashe su da su fito daya bisa daya a maimakon su fito tare. Amma su ki bin shawararsa, har ma da gangan ne su kara kusa da kasa, sabo da haka, kasa ma ta kama wuta.

Ganin irin mugun aikin da 'yan uwan rana suke yi, Houyi ya fusata, ya yi ta yin hakuri, amma daga karshe ya kasa, sai ya sa kimiya a bakansa, ya yi ta harbarsu har guda 9, daga nan, rana ta karshe ta ba da kai ta yi ta rokon gafara, sai Houyi ya huce takaici.

Amma duk da haka, Houyi ta bata wa sarkin gumaka rai, sabo da 'ya'yansa ne aka kashe. Ya ji fushi sosai, har ma ya hana Houyi da matarsa su koma aljana.

A cikin irin wannan hali ne, sai Houyi ya yanke shawarar zama a kasa, don bauta wa dan Adam. Amma a nata bangaren, matarsa ba ta ji dadin zama a duniyar mutane ba, ta yi ta zargin mijinta da cewa, bai kamata ya kashe 'ya'yan sarkin gumaka ba.

Daga baya, Houyi ya sami labarin cewa, akwai wata gunkiya da ke zaune a dutsen Kunlun, kuma tana da wani irin magani mai ban mamaki, wanda idan a sha, sai za a shiga aljanna. Sai Houyi ya tashi zuwa dutsen nan, ya yi ta tafiya, ya ketare kogona masu yawan gaske, duwatsun da ya hau ma ba su lisaftuwa, ya sha wahala sosai, daga karshe ya isa wurin, kwalliya ta biya kudin sabulu ke nan. Amma abin bakin ciki shi ne, maganin da ya samo ya ishe mutum daya kawai. Houyi ba ya so ya je gidan gaskiya ba tare da matarsa ba, amma a sa'i daya, ba ya so matarsa ta bar shi kadai a duniyar mutane. Shi ya sa bayan da ya koma gida, ya boye maganin.

Amma daga bisani, Chang'e ta iske maganin, ko da yake tana son mijinta, amma ta fi son zama a aljanna. Sabo da haka, a ran 15 ga watan Agusta, bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato lokacin da wata ta fi haske, sai Chang'e ta sha maganin a yayin da mijinta ba ya gida. Da zarar ta sha maganin, sai ta fara tashin sama, ta yi ta sama ta yi ta sama har zuwa duniyar wata. Bayan da Houyi ya koma gida, ya ji bakin ciki sosai, sabo da matarsa ta bar shi.

Ko da yake Chang'e ta cika burinta, amma duk da haka, ba ta ji dadi ba. Sabo da babu kowa a wata, sai dai wani zomo wanda ke daka magani da kuma wani tsohon da ke sarar itatuwa. Musamman ma, a ran 15 ga wata na takwas na ko wace shekara, Chang'e ta kan tuna da zamanta a da mai dadi.

Labarin "neman shimkafa a birnin Chang'an"

Dongfang Shuo wani mutum ne mai hikima na zamanin da wanda babu wanda bai san shi ba a kasar Sin. labarunsa ma sun shahara sosai a tsakanin jama'ar kasar Sin.

Yana zaune ne a daular Han a karni na uku kafin kafin haihuwar annabi Isa. Ya kware sosai wajen rubuce-rubuce, kuma shi mutum ne mai son yin barkwanci. Da farko dai, Dongfang Shuo wani karamin jami'i ne a birnin Chang'an. A lokacin, wadanni ne suke kiwon dawakin sarki. Ko da yake dukansu kananan jami'ai ne, amma su kan sami damar kusantar sarki. Dongfang Shuo yana son jawo hankalin sarki don a ciyar da shi gaba, sabo da haka ya yi dabara.

Wata rana, Dongfang Shuo ya fada wa wani wada cewa, "kwanan baya, sarki ya ce, ku wadanni, gajeru ne, ba ku fi saura ko a wajen aikin noma ko kuma a fannin fada ba, kuma kuna cin arzikin kasa a banza, sabo da haka yana shirin kashe dukan wadannin kasar."

Jin haka, sai wadan ya barke da kuka sabo da tsoro.

Dongfang Shuo ya ce, "Na ba ka dabara. Ya kamata ka hada kai da sauran wadanni, idan kun gamu da sarkin, sai ku durkusa a gabansa, ku yi ta rokon gafara daga wajensa."

Wadan ya nuna masa godiya sosai.

Daga baya, dukan wadanni su kan durkusa a gaban sarki suna rokon gafararsa, idan suka gan shi. To, sarkin ya ji mamaki. Sai wadannin sun ce, "Dongfang Shuo ya ce za ka kashe mu."

Sai sarkin ya kira Dongfang Shuo, ya tambaye shi me ya sa ya yi karyar?

Dongfang Shuo ya ce, "ranka ya dade, kai mai martaba, wadannan wadanni tsayinsu bai fi mita daya ba, amma ko wane wata, ana ba su jakar shinkafa daya da kuma yuan 200. Ga shi tsayina ya kusan kai mita biyu, amma abin da aka ba ni daidai ne da nasu. Sakamakon haka, wadannin su kan koshi har keya, amma ni na kan ji matsananciyar yunwa. Abin nan ba shi da adalci. Idan kai mai martaba, ka yarda da abin da na fada, to, sai ka gyara halin da ake ciki."

Sarkin ya bushe da dariya. Amma Dongfang Shuo ya sami biyan bukatarsa. Daga bisani, sarkin ya ciyar da shi gaba.(Lubabatu Lei)

Labarin wasa da kananan sarakuna ta hanyar nuna musu alamar yaki

A daulolin gargajiya na kasar Sin, sarki mutum ne wanda ke da ikon koli na mulkin kasa. Amma idan sarki ya yi wasa da mulkin kasa, ya yi abin da ya ga dama, to, lalle ne, kamar yadda Hausawa su kan ce, abin da mutum ya shuka, shi zai girbe.

Sarkin You sarki ne na karshe na daular Zhou a karni na takwas kafin haihuwar annabi Isa. Kullum bai kula da harkokin kasa ba, sai dai yana wasa da matansa a fada yana kece raini. Daga cikin matansa, ya fi son wata mai suna Baosi, kome take so, sai ya biya bukatarta. Amma abin mamaki shi ne kullum Baosi ba ta jin farin ciki, tana murtuke fuskarta. Sarkin You ya yi ta yin dabaru da dama don sa Baosi ta yi murmushi, amma ba dama.

Wata rana, sarkin You ya je yawon shakatawa tare da Baosi. Lokacin da suka isa hasumiyar nuna alamar yaki da ke dusten Li, sarkin You ya yi wa Baosi bayani a kan amfanin hasumiyar cewa, wannan gini ne da ake amfani da shi wajen bayar da labarin aukuwar yaki. A lokacin, a kan yi gine-gine irin wannan tun daga hedkwatar kasa har zuwa can karkara. Idan an kai hare-hare a kan iyakar kasar, to, sojojin da ke girke a hasumiyar za su kunna wuta a hasumiyar nan da nan, sa'an nan sojojin da ke girke a wata hasumiyar daban da ke da dan nisa za su gani, su ma za su kunna wuta don ci gaba da ba da labarin yaki ga wata hasumiya daban. Hakan nan, jim kadan, a hedkwatar kasar, za a sami labarin da ke aukuwa a kan iyaka. Kuma idan an kai hari a kan hedkwatar kasar, to, za a kunna wuta a hasumiyar ba da labarin yaki dake dutsen Li, don neman taimako daga wajen kananan kasashen da suka nuna biyayya ga daular Zhou.

Bayan da Baosi ta ji maganar sarkin You, ba ta yi imani da cewa, za a kirawo sojoji daga wurin da ke nisan kilomita dubbai ta hanyar kunna wuta kawai ba. Domin neman faranta wa Baosi rai, sai sarkin You ya umurci sojoji da su kunna wuta. To, kananan sarakuna da ke kasashe daban daban sun sami labarin, kuma suna tsammani, lalle ne an kai wa hedkwatar kasa hari. Sabo da haka, sun shugabanci rundunonin sojoji zuwa Lishan don ba da gudummawarsu.

Amma yayin da suka isa wurin, sun ga sarkin You yana shaye-shaye tare da matarsa, yana jin dadi kawai, babu kowa da ya kai farmaki. Wato sarkin ya zambace su ke nan, amma sai suka yi hakuri, suka koma tare da sojojinsa. Da Baosi ta ga abin nan mai ban dariya, sai ta yi dan murmushi. Da sarkin You ya ga mowarsa ta yi murmushi, sai ya yi matukar farin ciki, har ma ya umurci sojojinsa da su sake kunna wuta, sabo da haka, kananan sarakuna sun sake zuwa tare da sojojinsu cikin gaggawa. Da sarkin You da Baosi suka ga an sake yi wa kananan sarakuna zamba, sai suka barke da dariya tare. Hakan nan sarkin You ya yi ta kunna wuta, don zambatar kananan sarakuna. Daga karshe, ba wanda ya zo idan aka kunna wuta.

Zuwa can, gaskiya ne an kai hari kan daular Zhou. Sai sarkin You ya ba da umurnin kunna wuta don neman taimako daga wajen kananan sarakuna. Amma kananan sarakunan ba su ci gaba da amincewa da shi, ba wanda ya zo don ba da taimako. Sabo da haka, ba da dadewa ba, an mallake daular Zhou, an kashe sarkin You, kuma an kama Baosi. Daular Zhou ta wargaje.

Labarin cin mutumcin Han Xin

Han Xin wani mashahurin kwamandan soja ne na kasar Sin a zamanin da. Iyayensa matalauta ne, kuma sun riga shi gidan gaskiya tun lokacin da yake karami. A lokacin, bai iya yin ciniki ba, kuma bai iya yin aikin noma ba, ga shi kuma babu arziki a gidansa, shi ya sa yana zama irin na matalauta, bayan da ya sami cin abincin rana, bai san inda zai ci abincin dare ba.

Sabo da haka, a garin Han Xin, wasu matasa su kan raina shi. Wata rana, wani saurayi ya gamu da Han Xin, yana tsammani Han Xin matsoraci ne, sabo da ko da yake shi kato ne, amma yana dauke da takobi. Shi ya sa ya dakatar da shi, ya ce, "idan kana da bajinta, sai ka cire takobinka, ka soke ni; idan kuma kai matsoraci ne, sai ka wuce a karkashin wandona." Kowa ya sani yana neman cin mutumcin Han Xin da gangan ne. Han Xin ya yi ta tunani, daga bisani ya wuce a karkashin wandon wannan mutum ba tare da ko yin magana ba. Dukan mutanen da ke kallo a wurin sun barke da dariya, suna ganin Han Xin matsoraci ne maras jaruntaka.

Amma a hakika, Han Xin mutum ne mai gwaninta a wajen aikin soja. A zamaninsa, ana kokarin neman hambarar da sarki na biyu na daular Qin sabo da mugun mulkinsa, manoma sun yi ta ta da tarzoma a wurare daban daban na kasar, Han Xin shi ma ya shiga wata rundunar soja mai karfi, shugaban rundunar kuma mutum ne da ya hambarar da mulkin daular Qin daga baya ya kuma kafa wata sabuwar daula, sunansa Liu Bang. Da farkon fari, Han Xin ya zama wani karamin jami'i mai kula da sufurin abinci kawai. Daga baya, ya gamu da wani mutumin da ake kira Xiao He, shi mai ba da shawara ne ga Liu Bang, su biyu su kan tattauna harkokin siyasa da aikin soja tare. Xiao He ya gane cewa, Han Xin mutum ne mai gwaninta sosai, shi ya sa ya yi ta nuna babban yabo a kan Han Xin a gaban Liu Bang, amma duk da haka, Liu Bang ya ki dora wa Han Xin babban nauyi.

Sabo da haka, Han Xin ya sami karayar zuciya. Wata rana, ya gudu daga rundunar, Xiao He ma ya bi shi. Liu Bang ya sami labarinsu, sai ya yi tsammanin sun gudu ne tare. Amma bayan kwanaki biyu, Xiao He da Liu Bang sun dawo, Liu Bang yana jin mamaki kuma yana murna. Ya tambayi Xiao He me ya faru. Xiao He ya ce, "na je komo da gwani ne." Liu Bang ya ji mamaki, ya ce, " da ma akwai janar da dama da suka gudu, me ya sa ka bi Han Xin kawai?"Xiao He ya ce, Han Xin gaskiya gwani ne da wuya ake iya samun irinsa, ba za ka iya samun mutumin da ya fi shi idan kana son kwace mulkin kasar ba." sabo da haka, Liu Bang ya yarda da ciyar da Han Xin gaba a matsayin babban kwamandan soja." Daga nan, Han Xin ya zamo wani babban kwamandan soja daga wani karamin jami'I mai kula da sufurin abinci. Kuma daga baya, ya ci manyan nasarori da dama a yake-yaken da aka yi na neman kwace mulkin daular Qin.(Lubabatu Lei)

Labarin dila na aron kwarjinin damisa

A wajen karni na biyar zuwa na uku kafin haihuwar annabi Isa alailissalan, zamanin yake-yake ne a kasar Sin, sabo da a lokacin, ya kasance da kananan kasashe masu yawa a yankin kasar Sin, kuma fada ya kan barke tsakaninsu.

Kasar Chu tana daya daga cikin kasashen da suka fi karfi a lokacin. A kasar, akwai wani babban janar mai gwaninta sosai a karkashin jagorancin sarkin Xuan na kasar Chu, sunansa Zhao Xixu. Amma a hankali a hankali ne, sarkin Xuan ya tarar cewa, an fi jin tsoron Zhao Xixu a maimakonsa. Sabo da haka, ya ji mamaki sosai. Sai ya tambayi ministocinsa.

A lokacin, akwai wani minista mai suna Jiang Yi, ya bai wa sarkin wani labari cewa,

Akwai wani damisa a wani dutse, wata rana ya je yin farauta sabo da yunwa. Jim kadan, sai ya ga wani dila, sai ya zabura ya kama shi. Amma a yayin da damisa ya bude baki zai cinye dila, wannan dila mai wayo ya ce, "haba, kana tsammani kai ne sarkin dabbobi, har za ka cinye ni. Ba ka sani ba, Allah ya riga ya nada ni a matsayin sarkin halittu. Duk wanda ya ci ni, to, Allah zai yi masa hukunci mai tsanani."

Bayan da ya ji maganar dila, sai ya yi mamaki, kwarjininsa ma ya dakushe sosai. Amma duk da haka, bai yi imani da maganar dila sosai ba.

Yayin da damisa ke duban bakin gatari, sai dila ya kara da cewa, "kai ba ka gaskata abin da na fada ba? To, yanzu sai ka bi ni, mu zaga a daji, ka ga ko dabbobi suna jin tsoron gamuwa da ni." Damisa ya yi tsammanin dabara ce mai kyau, sai ya bi dila.

To, shi ke nan, dila yana tafiya a gaban damisa gaba gadi. Zuwa can, sai suka gamu da wasu kananan dabbobin da ke kiwo a daji, da zarar sun ga damisa a bayan dila, sai su tsorata, nan da nan su zura a guje, su watse.

Ganin haka, damisa ma ya fara jin dan tsoro, amma bai sani ba, shi kansa ne ake jin tsoro.

Bayan da sarki Xuan ya ji labarin nan, sai ya yi ta tunani, ya gane cewa, ashe, shi ne ake jin tsoro a maimakon Zhao Xixu, ya kuma rage karfin ikon Zhao Xixu.

Tun daga nan, dila ya ari kwarjini daga damisa ya zama wani karin magana na kasar Sin, don sifanta mutane irin dila.(Lubabatu Lei)

Labarin Fan Zhongyan na kokarin karatu cikin mawuyacin hali

Fan Zhongyan nagartaccen dan siyasa da kuma marubuci ne a tarihin kasar Sin, wanda ba dai kawai ya ba da babban taimako a fannin siyasa ba, har ma ya kware sosai a fannonin adabi da aikin soja. Yanzu zan gaya muku wani labarinsa na kokarin karatu cikin mawuyacin hali.

Fan Zhongyan yana zaune ne a daular Song da ke karni na 10. Babansa ya riga shi gidan gaskiya a yayin da shekarunsa bai kai uku ba, gidansa ya yi tsiya sosai. Da shekarunsa ya kai fiye da goma, sai ya je mashahuriyar makarantar Yingtianfu don yin karatu. A lokacin, yana zama ne a cikin mawuyacin hali. Sabo da rashin isashen kudi, a cikin lokaci mai tsawo, babu wani abinci gare shi sai kunu. Ko wace rana da safe, sai ya dama kunu, bayan da kunun ya daskare, sai ya yanke shi cikin kashi uku, to, wannan shi ne abincinsa a duk rana.

Wata rana, Fan Zhongyan yana cin abinci, sai wani abokinsa ya zo wurinsa. Da ya ga abincin Fan Zhongyan ba shi da kyau, sai tausayi ya kama shi. Sabo da haka, ya ba wa Fan Zhongyan kudi don neman kyautata zaman rayuwarsa. Amma Fan Zhongyan ya ki karba. A cikin irin wannan hali ne, ba yadda zai yi, sai kashegari abokin nan ya kawo wa Fan Zhongyan abinci masu dadi da yawa.

Bayan 'yan kwanaki, abokinsa ya sake kai ziyara a wurin Fan Zhongyan. Ya ji mamaki sosai yayin da ya tarar abincin da ya kawo wa Fan Zhongyan a 'yan kwanankin da suka gabata duk sun rube, ko kadan Fan Zhongyan bai taba su ba. Sabo da haka ya fusata, ya ce, "kai ne ka fi nuna girman kai, ba ka amshi duk abubuwan da aka ba ka ba. Ka bakanta abokinka rai."

Fan Zhongyan ya yi murmushi ya ce, "ka rasa fahimtata. Ba wai ba na son ci ba ne, sai dai ina jin tsoron cinsu. Ina damuwar kyamar kunu da zan yi bayan da na ci abinci masu dadi da ka kawo mini. Kada ka yi fushi."

Fan Zhongyan ya taba bayyana burinsa cewa, "burina shi ne in zama wani likita mai kyau ko kuma wani waziri mai kyau. Sabo da likitoci suna warkad da masu cuta, a yayin da waziri ke kulawa da harkokin kasarsa. Daga baya, Fan Zhongyan ya zama waziri da kuma shahararren dan siyasa na daular Song.

Fan Zhongyan ya mayar da bunkasa aikin ba da ilmi da yin kwaskwarima a hukumomi a matsayin muhimman fannoni biyu na kara karfin kasa. Ya yi ta kokarin kafa makarantu a duk fadin kasar, don horar da kwararru iri daban daban da kasar ke tsananin bukata.

Bayan aikin da ya sha a fannin siyasa, ya kuma yi kokari ainun a fannin adabi, har ma ya fitar da kyawawan rubuce-rubuce da dama.(Lubabatu Lei)

Labarin Tian Ji game da sukuwa

A karni na hudu kafin haihuwar annabi Isa Alaihissalan, akwai dauloli da dama a kasar Sin wadanda suka sha yin fada da juna. A lokacin, akwai wani jami'in daular Wei wanda ake kira Sun Bin, sabo da takwaransa ya cuce shi, shi ya sa ya tsira da ransa zuwa daular Qi bayan da manzon kasar Qi ya kubutad da shi.

Daga baya, manzon daular Qi ya gabatar da Sun Bin ga babban janar Tian Ji, Tian Ji ya shawarce shi a kan dabarun yaki, Sun Bin ya shafe kwana uku yana masa bayani, sabo da haka, Tian Ji ya girmama shi kwarai, har ma ya dauke shi a matsayin babban bako. A nasa bangaren, Sun Bin shi ma ya nuna babbar godiya ga Tian Ji, ya kan ba shi dabara.

Sukuwa wasa ne mai farin jini tsakanin sarakai na daular Qi. Daga sarki har zuwa dogari su kan yi sukuwa domin nishadi, har ma su kan yi caca a kansa. Sau tari ne Tian Ji ya yi caca tare da sarki da dai sauran masarauta a kan sukuwa, amma kullum yana shan kashi. Wata rana, Tian Ji ya sake shan hasara a sukuwa, ya koma gida yana bakin ciki. Shi ya sa Sun Bin ya ba shi hakuri ya ce, 'idan an sake yin sukuwa, bari in taimake ka.'

Yayin da aka sake yin sukuwa. sai Sun Bin ya bi Tian Ji zuwa filin sukuwa. Masarauta da kuma talakawa su ma sun zo suna kallo. A lokacin, a kan karkasa dawaki cikin gida gida bisa saurinsu na gudu, kuma a kan bambanta dawaki na gida kala kala bisa ado da aka yi musu. Idan dawakin wani mutum sun ci nasara har sau biyu a cikin gasa uku, to, sai mutumin nan ya ci gasar.

Bayan da Sun Bin ya dudduba, ya ga ba bambanci sosai tsakanin dawakin Tian Ji da na saura, sai dai akwai matsala a kan dabaru ne kawai. Sai ya gaya wa Tian Ji cewa, 'janar, kwantar da hankalinka, za ka yi nasara.' Shi ya sa Tian Ji ya yi farin ciki, ya sa kudin caca da yawa don gayyatar sarki da ya yi sukuwa da shi. Dawakin sarki ba su ko taba shan kashi a cikin sukuwa ba, shi ya sa sarki ya yarda.

Kafin sukuwa, bisa shawarar da Sun Bin ya ba shi, Tian Ji ya yi wa dokinsa mai kyau ado iri na kyawawan dawaki, don ya yi tsere da kyakkyawan doki na sarki. Bayan da aka fara sukuwa, sai a ga dokin sarki ya yi gaba da sauri, a waje daya kuma, dokin Tian Ji ya ja da baya kwarai, shi ya sa sarki ya bushe da dariya. A cikin sukuwa ta biyu kuwa, Tian Ji ya yi amfani da dokinsa mai kyau don yin sukuwa da dokin sarki mai matsakaitan inganci , har ma dokin Tian Ji ya ci nasara. Hakan nan kuma, a cikin sukuwa ta uku kuma, Tian Ji ya yi amfani da dokinsa mai matsakaitan inganci don yin sukuwa da dokin sarki maras kyau, dokin Tian Ji ya sake zarce na sarki, dawakin Tian Ji sun lashe dawakin sarki da ci biyu da daya ke nan.

Sarki sai bude baki yake kawai, bai san daga ina ne Tian Ji ya sami dawaki masu kyaun haka. Sai Tian Ji ya gaya wa sarki cewa, ba wai dawakinsa na kyau ne, an yi dabaru ne kawai. Sa'an nan ya gaya wa sarki dabarun Sun Bin, sai nan da nan sarki ya kirawo Sun Bin zuwa fada. Daga baya sarki ya nada Sun Bin a matsayin babban mai ba da shawara ga rundunar sojoji. Kuma Sun Bin ya taimaki Tian ji wajen kyautata dabarun yaki, rundunar sojojin kasar Qi ta yi ta samun nasarori da dama a yake-yaken da aka yi tsakaninta da rundunonin soja na sauran kasashe.(Lubabatu Lei)

Labarin gashi daya na shanu tara

Sinawa su kan sifanta abu maras muhimmanci kaman wani gashi ne daga shanu 9. An samo wannan karin magana ne daga wani shahararren masanin tarihi na kasar Sin mai suna Si Maqian.

An haifi Si Maqian ne a shekarar 145 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihissalan. Babansa wani jami'i mai kula da tarihi ne a fadar sarki. Sabo da tasirin mahaifinsa a kansa, Si Maqian yana matukar sha'awar tarihi tun da yake karami. Ya karanta littattafai da dama, kuma ya fara zaga a wurare daban daban na kasar Sin tun da shekarunsa ya kai 20 da haihuwa, don yin bincike a kan mutane da labarin kasa da al'amura da aka rubuta a littafi. Sabo da haka, ya sami ilmi da yawa. Daga baya ya zama wani jami'i a wurin sarki.

A lokacin, yaki ya barke tsakanin kabilar Xiongnu na arewa maso yammacin kasar Sin da daular Han. Shi ya sa sarki Liu Che ya umurci babban janar Liling da ya shugabanci rundunar sojoji zuwa fagen yaki don yin fada da kabilar Xiongnu.

Sabo da haka, Liling ya shugabanci sojoji 5000 zuwa fagen yaki. Da farkon fari, an yi ta samun bishara daga wurin yaki. Ministoci ma sun yi ta taya wa sarki murna. Amma ba da dadewa ba, sojojin Xiongnu dubu gomai sun yi wa sojojin Liling zobe, an yi fada har kwanaki 8 tsakanin bangarori biyu, daga karshe, an kusan kashe dukan sojojin daular Han, kuma janar Liling shi ma ya ba da kai.

Bayan da sarkin daular Han ya sami labarin, sai ya fusata. Ministoci ma sun fara zagin Liling. Sai Si Maqian shi kadai ne ke yin shiru. Sai sarki ya tambayi Si Maqian mene ne ra'ayinsa game da al'amarin. Si Maqian ya fadi albarkacin bakinsa cewa, Liling yana da dakaru dubu 5 ne kawai, amma sojojin Xiongnu dubu 80 ne suka yi zobe, bayan fada ta kwanaki da dama, sabo da rashin samun abinci da makamai ne, shi ya sa ya daina fadar, ba wai gaskiya ne ya ba da kai.

Bayan da sarki ya ji maganar Si Maqian na neman kare Liling, sai ya ji fushi sosai, har ma ya tasa keyarsa zuwa gidan kurkuku. Daga baya, an yi tsegumi cewa, Liling ya zama mai horar da sojojin Xiongnu. Sai sarki ya kara jin fushi, har ma ya sa a yi wa Si Maqian wanda ya taba tsaron Liling hukunci mai tsanani. Si Maqian ya sha wahala sosai, sabo da haka, ya tuna da kisan kai. Amma ya yi tsammanin cewa mutum kamarsa in ya mutu kamar shanu tara sun rasa gashi daya ne kawai, ba za a ji tausayinsa ba, har ma za a yi masa dariya. Sai Si Maqian ya yanke shawarar yin hakuri da tsara wani shahararren kundin tarihi.

Sai Maqian ya aika wa abokin arzikinsa wata wasika dangane da ra'ayinsa. Daga baya, an tsamo maganarsa a wasikar "shannu tara sun rasa gashi daya" zuwa wani karin magana "gashi daya na shannu tara".

Si Maqian ya sha wahala ainun, kuma ya yi ta yin kokari shekara da shekaru, daga karshe ya cimma nasarar rubuta wani kundin tarihi mafi muhimmanci na kasar Sin.(Lubabatu Lei)

Hade madubi a gu daya

A karnin 9, ya kasance da wata babbar daula mai karfi a arewacin kasar Sin mai suna Sui. A sai daya kuma, ya kasance da wasu kananan dauloli a kudancin kasar Sin, daular Chen ita ce daya daga cikinsu. Daular Sui kullum tana neman kai hari ga kananan daulolin da ke kudu, ta yadda za ta hada kasar Sin a gu daya.

A lokacin, akwai wani mutum da ake kiransa Xu Deyan, shi wani jami'in kasar Chen ne wanda ya rufa wa sarkin kasar baya, kuma ya auri kanwar sarki. Shi da matarsa na kaunar juna kwarai. Amma manyan jami'an kasar Chen na ta almubazzaranci. Xu Deyan ya gano cewa, wata rana za a mamaye kasarsa. Wannan ya kan tsunduma shi cikin damuwa.

Wata rana, yana bakin ciki sosai, ya gaya wa matarsa cewa: "Ina ganin cewa za a ta da yaki nan ba da dadewa ba. A lokacin, ina da alhakin kiyaye sarki, shi ya sa ke da ni za mu rabu da juna. Amma idan muna raye ba mu mutu ba, sai Allah ya sa mu sake saduwa da juna. Yanzu ya kamata mu shirya wani abin musamman, wanda zai iya ba da taimako yayin da muke neman juna."

Matarsa ta yarda da ra'ayinsa da shawararsa. Shi ya sa Xu Deyan ya kawo wani madubin tagulla, ya raba shi kashi 2, daya ya ba matarsa, dayan kuma shi kansa ke rike da shi. Ya gaya wa matarsa cewa, 'Bayan da muka rabu da juna, a ran 15 ga watan Janairu na ko wace shekara, sai ki sa a yi tallar rabin madubi naki a kasuwa. Idan ina raye a lokacin, zan je nemanki.'

Ba da dadewa ba, sai daular Sui da ke arewa ta kai hari ga daular Chen. Sojojin Sui sun mamaye kasar Chen, kuma sun kashe sarkin kasar. Xu Deyan ya yi gudun hijira, matarsa kuma an kama ta, an mai da ita da ta zama kishiyar wani janar daular Sui, mai suna Yang Su.

Xu Deyan da ke gudun hijira ya samu labarin cewa matarsa tana babban birnin daular Sui, sai ya tafi zuwa can. Ko wace rana da dare, ya kan duba rabin madubinsa, ya yi ta tuna zaman rayuwarsa tare da matarsa. Matarsa kuwa, ko da yake tana zaman jin dadi a cikin fada, amma tana begen mijinta sosai.

Wannan rana ran 15 ga watan Janairu ne. Xu Deyan ya yi yawo a kasuwa, sai ya ga wani tsoho wanda ke tallar rabin madubin tagulla, kuma kudin madubin ya yi tsada sosai. Xu ya dubi madubin, gaskiya ne na matarsa ne. A hakika ma, wannan tsoho bara ne wanda ke aiki a cikin fadar Yang Su, ya zo kasuwa ne domin ba da taimako ga matar Xu Deyan a wajen neman mijinta. Shi ya sa Xu ya rubuta wata waka, ya ba tsoho, inda ya rubuta cewa, 'Da ma matata ta bar ni tare da madubi, yanzu ga shi madubi ya dawo, amma ina matata ?'

Da matarsa ta ga rabin madubi na mijinta da wakar da ya rubuta, ta yi kuka, ta yi kuka, har ba ta son cin abinci. Da Yang Su ya sami labarin, sai ya kirawo matan, ya tambaye ta dalilin da ya sa ta yi bakin ciki kamar haka. Sai matar ta gaya wa Yang Su labarin rabin madubin tagulla. Labarin ya burge Yang Su sosai. Sai ya kirawo Xu Deyan, ya mayar masa matarsa, kuma ya ba shi kudi da kayayyaki da yawa. A karshe dai, Xu da matarsa sun sake zaman tare.

Sabo da labarin, a kan yi amfani da "hade madubi a gu daya" domin sifanta sake haduwar miji da mata, bayan da suka rabu da juna.

Labarin Cao Zhi

A tarihin kasar Sin, akwai wani sanannen iyali, mahaifinsa Cao Cao shi masani ne wajen harkokin soja da kuma wakoki, 'ya 'yansa biyu wato Cao Pi da Cao Zhi su ma kwararru ne wajen adabi, amma a cikinsu Cao Zhi ya fi sauran biyu wajen adabi.

Cao Pi shi ne mai ba da sharhi a kan adabi, wani littafi mai suna 'Dianlun.Lunwen' ya yi suna sosai a kan tarihin sharhohin adabi. Cao Zhi shi mawaki ne da ba a fi shi ba a zamaninsa.

Da Cao Pi ya zama sarki, ya yi hasadar gwanintar Cao Zhi sosai wajen adabi. A wani karo, sabo da wani karamin abu, Cao Pi yana shirin kai naushi ga 'dan uwansa Cao Zhi , ko Cao Zhi ya iya yin wata waka mai kyau cikin wani gajeren lokaci. Cao Zhi ya sani sosai, 'dan uwansa na son kai masa naushi, amma Cao Pi ya riga ya zama sarki a waccen lokaci, babu wani abu da Cao Zhi zai iya yi sai ya bi umurnin da Cao Pi ya ba shi. Sai ya yi namijin kokarinsa, da ya tuna da 'dan uwansa na adawa da shi, ya ji fushi sosai. Sai ya tsara wata waka kamar haka : 'Ana tafasa wake, ana kone gararsu ; wake suke kuka a cikin kwano, suke cewa, tun da mu 'yan uwa ne, me ya sa muke yin adawa da juna ?' Bayan sarki Cao Pi ya ji wannan waka, sai ya daina kai wa Cao Zhi naushi.

Cao Zhi ya sami sanara sosai a kan adabi. A cikin zamaninsa na dauloli uku, an yi ta yin yaki, farar hula sun sha wahala sosai. Amma Cao Zhi a matsayin 'dan uwan sarki ya nuna tausayi sosai ga farar hula, wadanda suka rasa gidajensu. Haka kuma yaki ya sa Cao Zhi yana kaunar kasarsa sosai, ya ce, 'ina son in sadaukar da rayuwata domin kasa kamar na zo gida.'

Ko da yake Cao Zhi ya sami nasara sosai a kan adabi, amma yana son gudanar da aikinsa a fannin siyasa, wannan ya sa sarki Cao Pi ya yi shakkarsa, kuma ya kan yi adawa da shi, sabo da haka ne, Cao Zhi ya sha wahaloli masu yawan gaske a zaman rayuwarsa. Cao Zhi ya kan rubuta wakoki domin bayyana fushinsa, amma yana tsoron rubuta haka a fili, sai ya rubuta 'yan mata da yawa masu kyaun gani a cikin wakokinsa, kamar waka mai suna ''yan mata kyawawa' da 'akwai wata yarniya mai kyaun gani a kudancin kasa' da dai sauransu. 'Yan mata da ya rubuta masu kyaun gani ne, kuma su gwanaye ne wajen adabi. Kuma mun ga wata waka mai suna Luoshenfu. Luoshui wani kogi ne da ke dab da birnin Luoyang, babban birnin daular Wei, sarkin kogin da ake kira Mi Fei na da kyaun gani sosai, marubuci na kaunarta, amma ba su iya fahimar juna domin Cao Zhi 'dan Adam ne, amma Mi Fei tana cikin kogi ne. Wannan waka ta yi suna sosai, har ana ta yabonta cikin shekaru dubu.

Kwararren mawaki Cao Zhi ya rasu a yayin da shekarunsa ya kai 41 kawai da haihuwa, amma ya ba da muhimmin tasiri sosai a kan tarihin adabin kasar Sin. Wakarsa da ya yi dangane da wake ta zama wata almara, wadda ta bayyana wani mutumin da ya samu gwaninta sosai a kan adabi.(Danladi)

Labarin Su Qin

A zamanin yakekeniya na karni na biyar kafin bayyanuwar Annabi Isa(A.S), kasar Sin ta kasance da daulolin da yawansu ya kai 7, wato su ne daulolin Qin da Yan da Zhao da Qi da Chu da Han da kuma Wei. Daular Qin da ke arewa masu yammacin lardin Shaanxi na yanzu na kasar Sin ta fi karfi a sakamakon gyare gyaren da ta yi a kan siyasa da tattalin arzikinta, sabo da haka ne, ta kan kai hari ga sauran dauloli shida. A cikin wannan hali, sarakunan dauloli shida sun zama bangarori biyu, bangare daya yana ganin cewa, ya kamata su raya kyakkyawar dangantaka a tsakaninsu da daular Qin, kada a fusata daular Qin da ta sami wata damar kai musu yaki. Amma bangare daban yana ganin cewa, ya kamata dauloli shida su hada kansu domin yaki da daular Qin.

A zamanin nan da muka ambata tun farko, akwai masu ba da shawara da yawa, wadanda suke ta lalashin sarakunan daulolin da su bi shawararsu. To, idan aka karbi shawarar da suka gabatar, za su zama mayan jami'ai, to za su yi suna sosai a kwana daya. Su Qin shi ne daya daga cikin irin wannan masu ba da shawara.

Da farko dai, Su Qin ya zo daular Qin, ya lallashi sarkin Qin cewa, ya kamata daular Qin ta raya dangantakar abuta a tsakaninta da sauran dauloli shida, bayan haka sai ta cinye sauran dauloli daya bisa daya. Amma sarkin Qin bai yarda da haka ba, ya ce, daular Qin ba ta da ra'ayin kai wa sauran dauloli hari. amma a zahiri dai, daular Qin ba ta da karfin cinye sauran dauloli ne a waccen lokaci. Da Su Qin ya rasa dabarar da zai yi, ya ga kudinsa na karewa, sai ya koma gidansa da ke birnin Luoyang.

Da iyalansa suka ga haka, sun san cewa Su Qin bai sami nasara ba, sai mahaifi da mahaifiyarsa ba su son magana da shi, matarsa ta ki kallonsa sam sam. Ya roki kanwarsa da ta dafa masa abinci, amma kanwar ta ki , haka kuma ta ce Su Qin ba shi da amfani. Da ganin haka, Su Qin ya shiga bakin ciki sosai, sai ya yi namijin kokarinsa wajen karatu da nazarin dabarun da aka yi amfani da su wajen yaki.

Su Qin yana ta yin karatu da kuma nazarin halin da ake ciki a lokacin, a karshe dai ya sami nasara wajen lallashin sauran dauloli shida da su hada kansu domin yaki da daular Qin. Su Qin kuma ya zama babban hafsan hafsoshi na sojojin sauran dauloli shida. Da daular Qin ta ga haka, sai ba ta iya kai hari ga ko wace daular da ta hada kanta da sauran daulolin ba. An kasance cikin hali ne cikin kimanin shekaru 15 bayan haka, har sarki Qinshihuang ya dinke kasar Sin.

Bayan da Su Qin ya zama babban hafsan hafsoshi, ya kasance babban mutum a daulolin shida. A wani karo, ya zo gidansa. Amma kafin haka, jami'an wurin sun share hanyoyi domin maraba da shi. Uba da uwarsa suna jiransa a bakin hanya. Da ya zo gida, matarsa tana jin tsoronsa sosai har ba ta iya magana ba. Kanwarsa ta yi ladabi da biyayya ga Su Qin. Ganin haka, Sai ya yi murmushi ya tambayi kanwarsa cewa, 'A da kun raina ni, amma yanzu kun nuna girmamawa. Yaya haka ?' Kanwarsa ta ce, 'A halin yanzu dai, ka zama babban jami'i, ka yi dukiya sosai, muna tsoron daukan matakai kamar da gare ka.' Da jin haka, Su Qin ya yi tunani sosai, ya ce, 'Idan wani yana fama da talauci, to, ko iyayensa ma za su raina shi; idan ka zama babban mutum, to, dangoginka za su ji tsoronka. Wannan shi ne dalilin da ya sa mutane su kan nemi mukami da dukiya !'(Danladi)

Labarin tsinke furanni a lambun Qujiang

A karni na takwas, lokaci ne na daular Tang da ta Sui a kasar Sin. A lokacin, sarki ya kafa tsarin jarabawa don neman fitar da kwararrun da za su kula da harkokin kasa, wato za a yi jarrabawa daga darussa zuwa darussa, kuma duk wanda ya ci jarrabawar da aka yi masa, to, zai iya zama jami'in gwamnati.

A lokacin, an karkasa wannan tsarin jarrabawa cikin digiri uku, kuma duk wanda ya ci jarrabawa ta digiri na uku, to, mai yiwuwa ne za a nada shi a matsayin babban jami'in gwamnati. Shi ya sa masana suke kokarin neman cin wannan jarrabawa ta digiri na uku, amma sabo da haka, wannan jarabawa ya fi wahala, a kan dauki mutane 10 zuwa 20 daga cikin 100 da suka shiga jarrabawar, shi ya sa, akwai mutane masu yawa da ba su samu nasarar jarrabawar ba har duk tsawon rayuwarsu, kuma ba abin mamaki ba ne wani mutum ya ci jarrabawar a yayin da yake da shekaru sama da 50 da haihuwa.

A lokacin, a kan yi jarrabawa ta digiri na uku a birnin Chang'an, wato hedkwatar daular Tang. Kuma a kan yi jarrabawar a watan Janairu na ko wace shekara, sa'an nan a watan Faburairu, za a bayyana sunayen mutanen da suka ci jarrabawar. Daga baya, sarki zai kira liyafa a lambun shan iska na Qujiang, don nuna yabo ga mutanen da suka ci jarrabawa ta digiri na uku.

Lambun Qujiang yana kudu maso gabashin birnin Chang'an. A wurin, akwai wani babban tabki, a kewayen lambun kuma, akwai wasu kyawawan lambuna. Ban da wannan, ana iya samu shahararren haikalin Ci'eng da hasumiyar Dayan da kuma ta Xiaoyan. Sarki da ministocinsa da kuma 'yan gidan sarauta su kan je wurin don shakatawa, kuma mawaka ma suna son zuwa wurin don yin wake-wake.

A gun liyafar da sarki ya kira a lambun Qujiang, masanan da suka ci jarrabawa ta digiri na uku su kan ajiye kofin da ke dauke da giya a kan kogin Qujiang, sa'an nan kofin ya yi shawagi a kan kogin, har zuwa wani masani daban, to, shi wannan masani zai sha giyar da ke cikin kofin, kuma zai yi waka. A sa'i daya kuma, za a aika da biyu daga cikin wadannan masana wadanda suka fi karancin shekaru da kuma kyaun gani zuwa lambu, don su tsinke furanni masu daraja, sa'an nan za a baiwa ko wane masani fure daya. Sabo da haka, a kan kira wannan irin liyafa liyafar tsinke furanni.

Wata shekara, bayan da aka kammala liyafar, sai masana suka je haikalin Ci'eng don shan iska. Da suka isa wurin, sai wani daga cikinsu ya rubuta sunansa a kan jikin wani dutsen da ke wurin, daga baya kuma, wannan ya zamo wata al'ada, bayan da aka kammala liyafar, a kan zabi wani masani da ke iya rubutu sosai, don ya zane sunan dukan masana a jikin dutsen. Daga baya kuma, idan wani daga cikinsu ya zama waziri, to, za a canja launin sunansa zuwa ja.

Har zuwa yanzu dai, ana iya ganin sunayen masanan da suka ci jarrabawar digiri na uku a jikin wani dutsen da ke hasumiyar Dayan.

Tsarin jarrabawa na daular Tang, ya bai wa kananan masana damar sa hannu cikin harkokin siyasa na kasa, kuma ya kyautata aikin gwamnati na kula da harkokin kasa.(Lubabatu Lei)

Mutane uku suna iya sa saura gaskata karya

Idan an yi ta barbaza karya ko tsegumi tsakanin jama'a, to, za a mayar da karya da ta zama gaskiya. A kasar Sin ma, ana iya samun wani labari dangane da wannan.

A wajen karni na biyar kafin haihuwar annabi Isa alaihissalam, ya kasance da kananan dauloli da dama a kasar Sin, kuma a kan yi yake-yake tsakaninsu, ba a samu kwanciyar hankali ba, sabo da haka, masu nazarin tarihi su kan kira wannan lokaci kamar zamanin yakekeniya

A lokacin, akwai kasashe biyu da ke makwabtaka da juna, su ne daular Wei da ta Zhao, kuma sun kulla yarjejeniyar sada zumunta tsakaninsu. Don neman amincewa da juna, ta yadda za a tabbatar da yarjejeniyar, sai sun aika wa juna mutane don a yi garkuwa da su. Sabo da haka, sarkin Wei ya aika da dansa zuwa birnin Handan , hedkwatar kasar Zhao don a yi garkuwa da shi. Amma don tsaron lafiyar dansa, sarkin daular Wei ya kuma tura wani minista mai suna Pang Cong zuwa daular Zhao don yi wa dansa rakiya.

Pang Cong mutum ne mai gwaninta a daular Wei. A lokacin, wasu jami'an gwamnati su kan nuna hamayya gare shi, shi ya sa yana damuwa idan ya bar sarkin daular Wei, za a cuce shi. Sabo da haka, kafin ya tashi, ya ce wa sarkin daular Wei, 'Idan wani ya ce, damisa ya zo kan titi, ko za ka gaskata?'

Sarkin Wei ya ce, 'Ba zan gaskata ba. Yaya damisa zai zo kan titi?'

Sai Pang Cong ya ci gaba da tambaya, 'To, idan mutane biyu suka ce damisa ya zo kan titi tare, ko za ka yi imani da wannan.'

Sarkin Wei ya amsa da cewa, 'lalle ne, idan mutane biyu sun ce hakan, za a fara dan gaskatawa.'

Sai Pang Cong ya sake yin tambaya, 'to, shi ke nan. Idan har mutane uku sun ce maka wani damisa ya zo kan titi, yaya za ka yi?'

Sarkin Wei ya ce, 'I, to, idan har mutane uku sun gaya mini wannan, ba yadda zan yi sai in gaskata su.'

Da ya ji maganar sarkin Wei, sai Pang Cong ya kara damuwa, ya ce, 'ranka ya dade, kai mai martaba, kowa ya sani, damisa ba za ta zo kan titi ba, amma sabo da mutane uku sun ce haka, sai aka gaskata hakan. Akwai nisa sosai tsakanin birnin Handan da babban birninmu, kuma ba wai mutane uku kawai za su yi mini tsegumi ba.'

Sarkin daular Wei ya gane abin da Pang Cong ke nufi, sai ya kada kai ya ce, 'kwantar da hankalinka, na san abin da kake nufi.'

Sai Pang Cong ya raka dan sarkin Wei zuwa daular Zhao. Daga bisani, gaskiya ne an sha yi wa Pang Cong tsegumi a gaban sarkin Wei. Da farkon fari dai, sai sarkin Wei ya yi ta kare shi daga kagen da ake yi masa. Amma abin bakin ciki shi ne, bayan da tsegumin da sarkin Wei ya sha sauraro dangane da Pang Cong, ya yi ta karuwa, sai shi ma ya fara yin imani da su. Har ma, bayan da Pang Cong ya dawo daga daular Zhao, sarkin Wei ya ki ganinsa.

To, mutane uku sun iya mayar da karya da ta zama gaskiya. Kun ga karfin tsegumi.(Lubabatu Lei)

Labarin Xiang Yu

A shekarar 202 kafin haihuwar Annabi Isa A.S., sarki Qin Shi Huang ya kafa daula ta farko a tarihin kasar Sin, wato daular Qin.

Saboda sarakunan daular Qin suna son kece raini fiye da kima, musamman ma sarki Qin Shi Huang ya gina fada mai girma da kuma kushewa, ya kuma kashe kudi mai yawan gaske wajen zaman yau da kullum, shi ya sa ya ci da gumin jama'a sosai, farar hula sun yi ta yin tawaye. A karshe dai, bayan shekaru 15 da aka kafa daular Qin, an hambarar da gwamantin daular Qin, rundunonin soja guda 2 suna yin fama da juna don neman samun jan ragamar mulkin kasar, wata runduna tana karkashin shugabancin Xiang Yu, Liu Bang yana jagorancin wata daban.

Xiang Yu wani janar ne daga garin Chu, ya gwada gwanintarsa wajen aikin soja. Kafin aka hambarar da gwamnatin daular Qin, Liu Bang wani karamin hafsa ne, yana da dan wayo, amma ya iya yin amfani da kwararru yadda ya kamata. Lokacin da suka yi yakin kin gwamnatin daular Qin, sun yin alkawarin zama 'yan uwa, suna goyon bayan juna. Amma bayan da aka hambarar da gwamnatin daular Qin, sun yi fama da juna.

Da farko, Xiang Yu ya sami rinjaye. Ya nada kansa 'sarkin Chu', ya nada Liu Bang 'sarki Han' da ke karkashin shugabancinsa. Don kiyaye karfinsa, Liu Bang ya amince da mukamin Xiang Yu, amma ya nemi kwararru a asirce, ya bunkasa sojojinsa. Sannu a hankali, sun yi kunnen doki.

Xiang Yu da Liu Bang sun yi shekara da shekaru suna yaki da juna, ana kiran wannan yaki 'yakin tsakanin Chu da Han'. Wata rana Xiang Yu ya lashe Liu Bang ya kuma yi garkuwa da baban Xiang Yu da matarsa. Ya bukaci Liu Bang da ya mika wuyansa, ya yi barazanar cewa, idan Liu Bang ba zai ba da kai ba, to, zai kashe baban Liu Bang ya yi miya da shi. Amma Liu Bang ya gaya wa Xiang Yu cewa, 'lokacin da muke yaki da sojojin daular Qin, mu ne 'yan uwa, babana babanka ne, idan ka yi miya da babanmu, to, kada ka manta da ni, ka ba ni wasu.' Ba yadda zai yi, sai Xiang Yu ya saki baban Liu Bang da matarsa.

Xiang Yu da Liu Bang sun yi yaki na karshe a wani gari mai suna Gaixia( da ke lardin Anhui a yanzu). Bayan da suka yi dauki ba dadi mai tsanani, sojojin Liu Bang sun yi wa Xiang Yu da sojojinsa garkuwa. Duk da cewa, Liu Bang bai iya lashe Xiang Yu daga duk fannoni ba, saboda Xiang Yu yana da sojoji da yawansu ya kai dubu dari.

Wata rana da dare, Xiang Yu da sojojinsa sun ji wakar gargajiya da suka saba da shi. Ashe, waka ce daga garin Chu. Sautin wakar ta zo ne daga sansanin sojan Liu Bang. Xiang Yu da sojojinsa sun ji mamaki sosai, suna ganin cewa, Liu Bang ya ci garinsu, sun kama dangoginsu, kirar wakar nan ta sa sojojin Xiang Yu su tuna da garinsu da kuma iyalai da dangoginsu kawai. Nan take aka tayar da kura a sansanin Xiang Yu, sojojinsa sun guda bi da bi, a karshe dai sojoji darurruka kawai sun ci gaba da zama a sansanin.

A zarihi dai, Liu Bang ya yi dabara. Ya ba da umurni ga sojojinsa da su rera wakar garin Chu don ta da hankali a sansanin sojan Xiang Yu.

A karshe dai Liu Bang ya ci nasara a kan garin Gaixia, an tilasta wa Xiang Yu ya kashe kansa. Daga baya Liu Bang ya kafa daular Han, wadda ta fi jawo hankulan mutane wajen tattalin arziki da al'adu.

Makwabciyar Song Yu ta leka shi a asirce ta bango

A cikin tarihin adabin gargajiya na lokacin da na kasar Sin, akwai wani shahararren marubuci wanda ake kiransa Song Yu, an ce wai shi saurayi ne mai kyan gani sosai. An taba rubuta wasu labaru game da Deng Tuzi wanda yake da jaraba, labarin "makwabciyar Song Yu ta leka shi a asirce ta bango" shi labari ne na ban sha'awa da ke daya daga cikinsu.

Song Yu da Deng Tuzi dukkansu su manyan jami'ai ne na kasar Chu, su da sarkin Chu su abokan arziki ne. Deng Tuzi ya yi kishi da zurfin ilmi na Song Yu, shi ya sa kullum ya kan yi maganganu masu cin zarafi a kansa a gaban sarkin Chu. A wani karo kuma, Deng Tuzi ya gaya wa sarkin Chu cewa:" ranka ya dade, Song Yu yana da kyan gani da kuma ilmi mai zurfi, ban da wannan kuma yana da jaraba, shi ya sa kada ka amince da shi da ya raka ka zuwa gidanka. Kana da mata masu kyan gani da yawa, idan sun gan shi, watakila ne za a haddasa matsaloli."

Da jin haka, sarkin Chu ya kirawo Song Yu domin tabbatar da maganganun da Deng Tuzi ya fada. Song Yu ya ce:" lalle ina da kyan gani, wannan Allah ya ba ni, kuma gaskiya ne ina da ilmi mai zurfi, wannan sabo da na yi iyakacin kokari kan karatu, amma game da cewa ina da jaraba, wannan ba gaskiya ba ne."

Sarkin Chu ya ce:" wane ne zai iya shaida abin da ka fada?"

Song Yu ya ce:" game da mata masu kyan gani, an fi samu su a cikin kasar Chu. Amma a cikin kasar Chu kuma, an fi samun mata masu kyan gani a cikin garina wanda ake kiransa Chenli. Mace mafi kyan gani a cikin garina ita ce makwabciyata. Wannan mace tana da kyan gani da kuma kyan kira. Idan ta yi murmushi, to nan da nan ne dukkan maza sai su ji farin ciki. Amma macen ta kan leka ni ta bango har shekaru uku, ban amince kaunarta ba. sabo da haka yaya za a ce ni mutum ne mai jaraba? A hakika dai, Deng Tuzi ne yake da jaraba sosai."

Sarkin Chu ya ce:" ina dalili?"

Song Yu ya ce:" matar Deng Tuzi ba ta da kyan gani sam, amma da ya ganta a karo na farko, sai nan da nan ne ya nuna mata soyayyarsa, kuma sun haifi'ya'ya biyar." Da jin haka, sarkin Chu bai san me ya fada ba.

To, wannan shi ne labari game da makwabciyar Song Yu ta leka shi a asirce ta bango.

>>[Labarin Basira]

Na'urar tsinkayar girgizar kasa ta kasar Sin

A lokacin daular Han ta Gabas a kasar Sin, a kan yi girgizar kasa a kewayen birnin Luoyang, wato hedkwatar daular. A cikin shekaru sama da 50 tun daga shekara ta 89 har zuwa ta 140, gaba daya an samu girgizar kasa da yawansu ya kai 33. Musamman ma a shekarar 119, an yi girgizar kasa masu karfi har sau biyu, wadanda suka shafi gundumomi fiye da goma, inda gidaje da yawa suka wargaje tare kuma da mutane da kuma dabbobi masu yawa da suka mutu ko ji rauni. Sabo da haka, jama'a sun tsorata. Sarki na lokacin yana tsammanin an bata wa aljanu rai, shi ya sa ya kara karbar haraji daga hannun jama'a, don yin ibada. A lokacin, akwai wani mai ilmin kimiyya wanda ake kira Zhang Heng, bai yi imani da camfe-camfe game da girgizar kasa ba, a ganinsa, girgizar kasa bala'i ne daga indallahi, sai dai dan Adam ba su sami ilmi sosai a kanta ba. Sabo da haka, ya kara yin nazari a kan girgizar kasa.

Daga baya, ya yi kokarin nazarin abubuwan da suka kawo girgizar kasa. Bisa gwaje-gwajen da ya yi shekara da shekaru, a shekarar 132, a karo na farko ne ya kirkiro wata na'urar tsinkayar girgizar kasa a kasar Sin har ma a duk duniya baki daya.

Wannan na'ura ta kasance tamkar wata babbar tukunya, an yi ta ne da tagulla. Akwai dodanni 8 bi da bi a gabas da kudu da yamma da arewa da arewa maso gabas da kudu masu gabas da arewa maso yamma da kuma kudu maso yamma da ke kewayenta, kuma ko wannensu yana rike da wani karamin kwallon tagulla a bakinsa. Ban da wannan, akwai wani kwado da ke tsugune a karkashin ko wane dodon. Kwadon ya daga kansa, kuma bakinsa a bude, don karbar kwallon da zai fada daga bakin dodo. Wannan na'ura tana da ban sha'awa, kamar kwadi suna wasa ne tare da dodanni. Idan an yi girgizar kasa a gabas, to, dodon da ke gabas zai buda bakinsa, kwallon da ke bakinsa ma zai fada cikin bakin kwadon da ke tsuguna a karkashinsa, don bayar da labarin aukuwar girgizar kasa, ta yadda gwamnati za ta bayar da agaji. Hakan nan ma idan an yi girgizar kasa a yamma ma, dodon da ke yamma zai bude bakinsa.

A shekara ta 133, an yi girgizar kasa a birnin Luoyang, wannan na'urar da Zhanghen ya kirkiro ya ci nasarar tsinkayarta. A cikin shekaru 4 bayan wannan ma, an yi girgizar kasa har sau uku a yankin Luoyang, ko waccensu na'urar ba ta kasa ba da bayani ba. A watan Faburairu na shekara ta 138, dodon da ke yamma ya buda bakinsa, kwallon ya fada cikin bakin kwadon da ke tsugune a karkashinsa, amma duk da haka, ba a ji girgizar kasa ba, sabo da haka, an fara shakkar wannan na'urar tsinkayar girgizar kasa. Bayan kwana uku ko hudu, manzon lardin Gansu wanda ke yamma da birnin Luoyang ya zo tare da labarin cewa, an yi girgizar kasa a can. Ashe, gaskiya ne an yi girgizar kasa. Tun daga nan, an fara yin amfani da na'ura don yin nazarin girgizar kasa a kasar Sin.(Lubabatu Lei)

Peach biyu sun kashe barade uku

A wajen karni na bakwai kafin haihuwar annabi Isa alaihissalan, ya kasance da dauloli da dama a kasar Sin. Daular Qi tana daya daga cikinsu. A daular, akwai barade uku masu matukar jaruntaka, wadanda suka sami goyon baya sosai daga wajen sarki. Sabo da haka, baraden nan uku su kan nuna girman kai. A lokacin, akwai wani mutum mai suna Chen Wuyu, yana son mayar da wadannan barade uku a karkashin jagorancinsa, don hambarar da mulkin sarkin daular Qi.

Ganin haka, wazirin daular Qi, Yanying ya damu sosai. Don neman samun kwanciyar hankali a kasar, Yanying ya yanke shawarar kashe wadannan barade uku. Amma yaya za a kashe barade uku masu tsananin jaruntaka haka? Wata rana, sarkin daular Lu ya kai ziyara a daular Qi, sabo da haka, sarkin daular Qi ya kira liyafa a fadarsa. Yanying da baraden uku da sauran jami'ai su ma sun halarta. Yanying ya ba da shawarar diban wasu peach don ba wa baki su ci. Sarki ya yarda. Sai Yanying ya diba peach shida daga wajen lambu. Ya ba wa ko wane sarki da waziri na dauloli biyu peach daya. Sauran biyu kuwa, sai Yanying ya ba da shawarar ba wa jami'an da suka fi ba da taimako don nuna yabo gare su.

Sarki yana ganin dabara ce mai kyau. Sai ya nemi ko wane jami'i da ya bayyana taimakon da ya bayar. Wani daga cikin baraden uku mai suna Gong Sunjie ya fito, ya ce, 'Da ma na bi sarki zuwa farauta. Na taba kashe wata damisa, ko wannan babban taimako ne?' Yanying ya ce, 'gaskiya ne ka ba da babban taimako, ya kamata ka sami yabo.' Sai ya ba shi peach daya. Gongsun Jie ya ji dadi.

Ganin haka, wani barde daban da ake kira Gu Yezi ya tashi ya ce, 'Me aka yi da kashe damisa?Na taba kashe wani babban kunkuru a rawayen kogi, don kubutad da sarki.' Sarkin ya yarda da shi, shi ya sa ya ba shi sauran peach daya.

Lalle ne barade na karshe mai suna Tian Kaiqiang bai ji dadi ba. Sabo da ya taba samun manyan nasarori a yake-yake da dama, amma ga shi an kyale shi. Ya fusata, har ma ya cire takobi, ya kashe kansa. Ganin haka, barde na farko Gongsun jie ya ji kunya, ya ce, 'taimakon da na bayar bai kai na janar Tian ba, amma na sami yabo, wannan ba adalci.' Sabo da haka, shi ma ya kashe kansa. Barde na karshe Gu Yezi shi ma ya fito, ya ce, mu uku mun taba yin rantsuwar mutuwa tare, ga shi yau su biyu sun riga ni gidan gaskiya, to, yaya zan rayu ni kadai ba tare da su ba?' sabo da haka, shi ma ya yi kisan kai.

A cikin dan lokaci, baraden uku duk sun mutu, ko hana su sarki bai iya yi ba, baki ma sai bude baki suka yi kawai. Yanying ya yi amfani da hikimarsa, ya kashe wadannan barade uku da peach biyu kawai.(Lubabatu Lei)

Labarin Ximen Bao

Ximen Bao wani mutum ne da ya yi zamani a karni na biyar kafin haihuwar Annabi Isa. Sabo da gwanintarsa, sarki ya nada shi a matsayin magajin garin Yedi. Bayan da Ximenbao ya kama aikinsa, sai ya tambayi wasu tsoffin dattawa na wurin, me ya fi kawo wa jama'ar gundumar wahala? Sun amsa da cewa, ba abin da ya fi kawo wa jama'a wahala, sai a aura wa aljanin kogi mata da a kan yi a ko wace shekara.

Ashe garin Yedi yana dab da rawayen kogi. Akwai wata tatsuniya wadda ta sami karbuwa sosai tsakanin jama'ar garin cewa, akwai wani aljani da ke zaune a cikin rawayen kogi, idan ba a aura masa mata ba, zai ta da ambaliyar ruwa, don hallaka jama'ar garin baki daya. Sabo da haka, gwamnati da mayu na wurin suna kokarin aura wa gunkin kogi mata.

Dattawa sun ci gaba da cewa, ko wace shekara, idan lokaci ya zo, sai wata mayya za ta zaga a garin, da ta ga wata kyakkyawar yarinya daga gida mai talauci, sai ta ce,'To, ya kamata ta auri aljanin kogi.' Sai a tafi da yarinyar, a tilasta ta da ta zauna ita kadai, a dinka mata sabbin tufaffi, a ba ta abinci masu kyau. Bayan kwana goma, yarinyar za ta ci ado, sa'an nan za a sa ta zauna a kan wata tabarma, a jefa tabarma cikin kogin. Lalle ne yarinyar ta nitse cikin kogi tare da tabarma. Sa'an nan mayu za su yi biki, don bayyana cewa, aljanin kogi ya sami mata. Bayan da Ximen Bao ya ji abin, bai ce uffan ba.

To, rana ta zo da za a sake aura wa aljanin kogi mata. Bayan da Ximen Bao ya sami labarin, sai ya zo gefen kogi da wuri wuri tare da sojoji. Ba da jimawa ba, sai aka ga masu hannu da shuni na garin da jami'an gwamnati sun zo tare da yarinyar da aka zaba, tare kuma da wata mayya tsohuwa mai shekaru kaman saba'in da wani abu.

Ximen Bao ya ce, 'bari in dubi yarinyar, ko tana da kyaun gani.' Sai a zo da yarinyar, Ximen Bao ya dudduba ta, ya ce, ba ta kai ga aurar aljanin kogi ba. Amma tun da aljanin kogi yana jira, sai mayya ki je cikin kogi don sanar da aljanin cewa, za a nemi wata kyakkyawar yarinya daban. Ba a fahimci abin da ya faru ba, sai sojoji sun jefa tsohuwar cikin kogin. Jim kadan, Ximen Bao ya ce, 'me ya sa mayya ta dade ba ta komo ba? Bari mu aika da wata 'yar koyo, don ta matsa mata lamba.' Hakan nan an jefa 'yan koyo har uku cikin kogi.

Kowa ya firgita. Amma ga shi Ximen Bao yana mai cike da sahihanci da biyayya, tamkar gaskiya ne yana jiran sakon aljanin kogi. Zuwa can, sai Ximen Bao ya ce, lalle ne, aljanin kogi yana matukar son baki, ga shi ya dakatar da manzannin da muka tura. To, mu sake aikawa da wani.' Masu hannu da shuni da jami'an gwamnati na garin wadanda suka shirya abin dukansu sun tsorata, sun durkusa suna rokon afuwa.

Ximen Bao ya daga murya, ya ce, 'aura wa aljanin kogi abu ne da ke cutar jama'a, nan gaba duk wanda ya shirya abin, sai a jefa shi cikin kogi.' To, daga nan an kawo karshen aura wa aljanin kogi mata, kuma jama'a sun ji dadin zama a gundumar.(Lubabatu Lei)

Labarin Tian Ji game da sukuwa

A karni na hudu kafin haihuwar annabi Isa Alaihissalan, akwai dauloli da dama a kasar Sin wadanda suka sha yin fada da juna. A lokacin, akwai wani jami'in daular Wei wanda ake kira Sun Bin, sabo da takwaransa ya cuce shi, shi ya sa ya tsira da ransa zuwa daular Qi bayan da manzon kasar Qi ya kubutad da shi.

Daga baya, manzon daular Qi ya gabatar da Sun Bin ga babban janar Tian Ji, Tian Ji ya shawarce shi a kan dabarun yaki, Sun Bin ya shafe kwana uku yana masa bayani, sabo da haka, Tian Ji ya girmama shi kwarai, har ma ya dauke shi a matsayin babban bako. A nasa bangaren, Sun Bin shi ma ya nuna babbar godiya ga Tian Ji, ya kan ba shi dabara.

Sukuwa wasa ne mai farin jini tsakanin sarakai na daular Qi. Daga sarki har zuwa dogari su kan yi sukuwa domin nishadi, har ma su kan yi caca a kansa. Sau tari ne Tian Ji ya yi caca tare da sarki da dai sauran masarauta a kan sukuwa, amma kullum yana shan kashi. Wata rana, Tian Ji ya sake shan hasara a sukuwa, ya koma gida yana bakin ciki. Shi ya sa Sun Bin ya ba shi hakuri ya ce, 'idan an sake yin sukuwa, bari in taimake ka.'

Yayin da aka sake yin sukuwa. sai Sun Bin ya bi Tian Ji zuwa filin sukuwa. Masarauta da kuma talakawa su ma sun zo suna kallo. A lokacin, a kan karkasa dawaki cikin gida gida bisa saurinsu na gudu, kuma a kan bambanta dawaki na gida kala kala bisa ado da aka yi musu. Idan dawakin wani mutum sun ci nasara har sau biyu a cikin gasa uku, to, sai mutumin nan ya ci gasar.

Bayan da Sun Bin ya dudduba, ya ga ba bambanci sosai tsakanin dawakin Tian Ji da na saura, sai dai akwai matsala a kan dabaru ne kawai. Sai ya gaya wa Tian Ji cewa, 'janar, kwantar da hankalinka, za ka yi nasara.' Shi ya sa Tian Ji ya yi farin ciki, ya sa kudin caca da yawa don gayyatar sarki da ya yi sukuwa da shi. Dawakin sarki ba su ko taba shan kashi a cikin sukuwa ba, shi ya sa sarki ya yarda.

Kafin sukuwa, bisa shawarar da Sun Bin ya ba shi, Tian Ji ya yi wa dokinsa mai kyau ado iri na kyawawan dawaki, don ya yi tsere da kyakkyawan doki na sarki. Bayan da aka fara sukuwa, sai a ga dokin sarki ya yi gaba da sauri, a waje daya kuma, dokin Tian Ji ya ja da baya kwarai, shi ya sa sarki ya bushe da dariya. A cikin sukuwa ta biyu kuwa, Tian Ji ya yi amfani da dokinsa mai kyau don yin sukuwa da dokin sarki mai matsakaitan inganci , har ma dokin Tian Ji ya ci nasara. Hakan nan kuma, a cikin sukuwa ta uku kuma, Tian Ji ya yi amfani da dokinsa mai matsakaitan inganci don yin sukuwa da dokin sarki maras kyau, dokin Tian Ji ya sake zarce na sarki, dawakin Tian Ji sun lashe dawakin sarki da ci biyu da daya ke nan.

Sarki sai bude baki yake kawai, bai san daga ina ne Tian Ji ya sami dawaki masu kyaun haka. Sai Tian Ji ya gaya wa sarki cewa, ba wai dawakinsa na kyau ne, an yi dabaru ne kawai. Sa'an nan ya gaya wa sarki dabarun Sun Bin, sai nan da nan sarki ya kirawo Sun Bin zuwa fada. Daga baya sarki ya nada Sun Bin a matsayin babban mai ba da shawara ga rundunar sojoji. Kuma Sun Bin ya taimaki Tian ji wajen kyautata dabarun yaki, rundunar sojojin kasar Qi ta yi ta samun nasarori da dama a yake-yaken da aka yi tsakaninta da rundunonin soja na sauran kasashe.(Lubabatu Lei)

Labarin Chulong na lallashin uwar sarki

Karni na biyar kafin haihuwar Annabi Isa lokacin yake-yake ne na kasar Sin. A lokacin, uwar sarki Zhao tana kan kujerar mulkin daular Zhao. Akwai kuma wata daular da ake kira Qin, a shirye take za ta kai hari kan daular Zhao. Sabili da haka, daular Zhao ta nemi taimako daga wajen daular Qi, amma daular Qi ta nemi uwar sarki Zhao da ta aika da autarta Chang'an zuwa daular Qi don a yi garkuwa da shi, in ba haka ba, ba za ta tura sojoji masu ba da gudummawa ba. Sabo da matukar son autarta, shi ya sa uwar sarkin Zhao ta yi ta duban bakin gatari. A nasu bangaren kuma, ministocinta sun yi ta lallashinta da ta aika da Chang'an zuwa daular Qi domin neman tsaron kasarsu. Sakamakon haka, uwar sarkin Zhao ta fusata, ta ce, nan gaba, duk wanda ya tabo maganar aika da Chang'an zuwa daular qi don a yi garkuwa da shi, zan ci masa mutumci.

Wata rana, wani minista mai martaba da ake kira Chulong ya je wurin uwar sarki Zhao, uwar sarki ta yi tsammanin Chulong ya zo ne don lallashinsa, shi ya sa ta fusata. Amma abin da Chulong ya ce kawai shi ne, 'na dade ban zo don gai da uwar sarki ba, shi ya sa na ce bari in zo in gaishe ki.'

Uwar sarki ta ce, 'kwanan nan ban motsa jiki sosai ba, kuma ban ci abinci da yawa ba.' Chulong ya ce, 'ni ma ba na son cin abinci sosai, amma na yi kokarin yawo a ko wace rana, ta yadda zan kara cin abinci, don lafiyar jikina.' To, a cikin gaishe-gaishen da suka yi wa juna, uwar sarki ta fara huce takaici.

Sai Chulong ya ce, 'sunan autana shi ne Shuqi, ina kishinsa kwarai, amma ga shi na tsufa, shi ya sa nake son ya zo nan fada ya zama wani dogari, abin da ya kawo ni yau ke nan.' Uwar sarki ta tambaya, 'shekarunsa nawa ne?' Chulong ya amsa da cewa, '15, ina so in danka shi a hannunki kafin na kai takarda.' Uwar sarki ta ce, 'lalle ne maza ma suna kishin auta.' Chulong ya ce, 'mai yiwuwa ne maza su fi mata son auta.' sai uwar sarki ta bushe da dariya. Da Chulong ya ga an sassauta ran uwar sarki, sai ya kara da cewa, 'sabo da kishin 'ya'yansu, ya kamata iyaye su yi hangen nesa domin makomarsu. Uwar sarki ba ta gane ba. Sai Chulong ya bayyana cewa, 'A ganina, ba ki yi hangen nesa a kan makomar danki ba. Sabo da tun can can can da, ba a samu 'ya'yan sarki masu yawa da su cimma gadon mahaifinsu zuriya zuwa zuriya ba. Dalili shi ne ba su ba da babban taimako ga kasarsu ba. Yanzu ki ba Chang'an gonaye da dukiyoyi, amma ya fi kyau ki ba shi damar ba da taimako ga kasar, ta yadda zai zaunad da gindinsa a daular Zhao bayan da ki riga shi gidan gaskiya.'

Bayan da uwar sarki ya ji maganar Chulong, sai ta fara gane cewa, ashe, shi ma yana lallashinta ne, amma ga shi ya cimma nasara. Shi ya sa uwar sarki ta shirya dawaki da barori, ta aika da dansa zuwa daular Qi. Daular Qi ita ma ta yarda da tura sojoji masu ba da taimako zuwa daular Zhao.(Lubabatu Lei)

Labarin aron kibiyoyi da kwale-kwale

A wajen karni na 3 kafin haihuwar annabi Isa Alaihissalan, ya kasance da dauloli uku a yankin kasar Sin, daga cikinsu, daular Wei tana arewa, daular Shu kuma tana kudu maso yammacin kasar, an kuma sami daular Wu a kudu. Daular Wei ta tura sojoji masu yawa su bi kogi don kai hari kan daular Wu wanda ke bakin kogin Yangtse. To, ba da dadewa ba, sojojin daular Wei suka iso wurin da ke kusa da daular Wu, kuma sun girke a wurin, don neman kofar kai kari.

A lokacin, babban kwamandan rundunar kasar Wu shi ne Zhouyu, bayan da ya yi nazari a kan rundunar sojojin daular Wei, sai ya yanke shawarar yin amfani da kibiyoyi don yaki da mahara. Amma abin tambaya shi ne yaya za a shirya kibiyoyi dubu 10 da ake bukata a cikin gajeren lokaci? A lokacin, a kalla dai ana bukatar kwana goma don kera kibiyoyi masu yawan haka. Amma wannan ya fi tsawo ga tsaron daular Wu.

A lokacin, mai ba da shawara kan aikin soja na daular Shu, Zhu Geliang yana ziyara a daular Wu. To, shi Zhu Geliang mutum ne mai matukar hikima, shi ya sa Zhou Yu ya shawarce shi a kan yadda za a cimma burin kera kibiyoyi dubu goma cikin dan lokaci. Zhu Geliang ya ce, kwana uku ya ishe mu. Ana tsammanin Zhu Geliang yana cika baki ne kawai. Amma Zhu Geliang ya dauki alwashin cewa, idan bai kammala aikinsa cikin lokaci ba, to, sai a gille kansa.

Bayan da Zhu Geliang ya dauki nauyin nan, bai damu ba. Ya fada wa ministan daular Wu Lu Su cewa, ba za a cimma burin kera kibiyoyi masu yawan haka ta hanyar kullum ba. Sa'an nan, ya nemi Lu Su da ya shirya kwale-kwale 20, kuma ko wane kwale kwale a tura sojoji 30, kuma a ajiye ciyayi masu yawa a kan kwale-kwale. Lu Su ya shirya kamar yadda aka bukata, amma bai san me za a yi da abin da aka shirya ba.

To, shi ke nan, da ma Zhu Geliang ya yi alkawarin kera kibiyoyi dubu goma cikin kwana uku, amma a ranar farko, bai yi kome ba, a rana ta biyu kuwa, haka yake. Ga shi rana ta uku ta kusanto, amma ba a samu ko kibiya daya ba. Kowa na nuna damuwarsa. A rana ta uku da daddare, Zhu Geliang ya kirawo Lu Su cikin wani kwale-kwale, Lu Su ya ce, 'me ya faru'. Zhu Geliang ya ce, 'mu je mu debo kibiyoyi.' Lu Su ya dimauta. To, shi ke nan, Zhu Geliang ya umurci a harhada wadannan kwale-kwale da igiya, sa'an nan su kama hanyar zuwa sansanin rundunar sojojin daular Wei.

A ran nan da dare, an yi hazo sosai, har ma ba a iya ganin kome ba. Lokacin da kwale kwale suka kusanci sansanin soja din, sai Zhu Geliang ya sa a jejjera kwale-kwale a layi daya, sa'an nan ya umurci sojojin da ke kan kwale-kwale da su buga ganguna kuma su yi ihu.

To, bari mu leka me ya faru a sansanin sojojin daular Wei bayan da suka ji karar. Kwamandan rundunar sojojin Wei Cao Cao ya tattara janar cikin gaggawa don su tattauna yadda za a fuskanci al'amarin. Daga karshe, sun yanke shawarar harba kibiyoyi daga bakin kogi ne kawai, tun da ba a san yadda abokan gabansu suke ba sabo da hazo. To, rundunar sojojin Wei ta tura sojoji kimanin dubu 10 zuwa bakin kogi don su rika harbar kibiyoyi. Kibiyoyi sun yi cul cul cul kamar ruwan sama. Ba da dadewa ba, an sami kibiyoyi marasa lisaftuwa a duk jikin ciyayi da ke kan kwale kwale. To, sai Zhu Geliang ya sa a juya kwale kwale, don a harba kibiyoyi a gefe daban. Bayan da aka samu isassun kibiyoyi, sai Zhu Geliang ya ba da umurnin dawowa.

Bayan da ayarin kwale-kwale na Zhu Geliang ya koma sansanin sojan Wu, an kirga kibiyoyi da aka samu, kash, har ya wuce dubu goma. Babban kwamandan rundunar Wu, Zhou Yu ma ya girmama Zhu Geliang kwarai. Amma yaya Zhu Geliang ya sani

za a yi hazo a ran nan da dare. Ashe, Zhu Geliang ya kware ne a wajen nazarin yanayi. Haka nan Zhu Geliang ya yi amfani da hikimarsa ya ari kibiyoyi dubu goma daga wajen makiya.(Lubabatu Lei)

Labarin Mozi

An haifi Mozi a cikin karni na biyar kafin haihuwar Annabi Isa A.S., kuma a wancan lokaci, kasar Sin wata kasa ce da ta hada da kasashe da yawa. Kasar Chu ita ce daya daga cikinsu, wadda wata babbar kasa ce, kasar Song kuwa ita ce wata karamar kasa.

A daidai wancan lokaci, wani shahararren mai sana'a na kasar Chu wanda ake kiransa Gong Shuban ya kago wani sabon makami mai suna kwaranga mai tsawo domin yin amfani da ita kan kai wa ganuwar abokan gaba hari. Bayan da aka gama yin kwaranga mai tsawo, sai kasar Chu tana cikin shirin kai wa kasar Song farmaki don gwada karfin wannan sabon makami.

Da Mo Zi ya ji labarin nan, sai nan da nan ya tashi, bayan kwanaki goma, ya isa babban birnin kasar Chu, ya gana da Gong Shuban domin hana wannan yakin da za a yi. Da ya gamu da Gong Shuban, ya ce :"wani ya wulakanta ni, ina so in yi amfani da karfinka don kashe shi." Gong Shuban bai san wannan wayo ne da ya yi ba, da jin haka, yana bakin ciki, amma bai ce kome ba. Mo Zi ya ci gaba da cewa :"idan ka amince da rokona, to zan ba ka kudade da yawa." Gong Shuban ya amsa cewa :"ina da da'a, ba zan kashe mutane don kudi ba." Mo Zi ya ce :"kasar Chu kasa ce mai girma, ko da ba ta da mutane da yawa, amma tana da manyan yankunan kasa. Yanzu tana cikin shirin kai wa karamar kasar Song hari, wannan yaki ne maras adalci. Ko da yake ka ce ba za ka kashe mutane ba, amma idan yaki ya tashi, fararen hula masu yawa za su mutu sakamakon sabon makamin da kuke yin amfani da shi, to ina bambancin da ke tsakanin wannan da kashe mutane da kanka?"

Gong Shuban bai san yadda ya kamata ya fada ba, sai ya ce shirin kai wa kasar Song hari shi ne kudurin da sarkin kasar Chu ya tsai da, shi ya sa Mo Zi da Gong Shuban sun je domin yin wa sarkin Chu gaisuwa. Bayan da suka gan shi, Mo Zi bai ce kome game da yaki ba. Ya ce :"ranka ya dade, ina da wata tambaya, wani mutum shi kansa yana da wani kyakkyawan jirgi, amma ba ya so, yana so ya saci jirgin makwabcinsa maras kyau, kuma yana da tufafi masu kyan gani, amma ba ya so, yana so ya saci tufafin makwabcinsa marasa kyau, a ganinka shi wane iri mutum ne ?" Sarki kasar Chu bai san wannan wayo ne da ya yi ba, sai ya amsa nan da nan, cewa :"shi ne mutum maras kyau, barawo ne." Mo Zi ya yi amfani da wannan zarafi mai kyau, ya ci gaba da cewa:" kasar Chu tana da manyan yankunan kasa, amma kasar Song wata karamar kasa ce kawai, kamar wani kyakkyawan jirgi da wani jirgi maras kyau. Kuma kasar Chu tana da albarkatun kasa, amma kasar Song ba ta da shi, kamar tufafi masu kyau da na marasa kyau, shi ya sa ina ganin cewa, idan kasar Chu za ta kai wa kasar Song hari, to ita kamar wancan barawo ne." Sarkin kasar Chu bai san yadda ya kamata ya amsa ba, shi ya sa ya ce ba tare da jin kunya :"abubuwan da ka fada dazun nan sun yi daidai, amma tun da Gong Shuban ya riga ya kago kwaranga mai tsawo, dole ne zan kai wa kasar Song hari." Mo Zi ya ce :"kwaranga mai tsawo ba ta da matukar karfi kamar yadda kake tsamani, in ba ka gaskatad da wannan ba, to ni da Gong Shuban za mu nuna maka." Sabo da haka sarkin kasar Chu ya shirya musu kayayyaki, wadanda suke hade da ganuwa da makamai masu kare gari da kwaranga mai tsawo da sauran makaman kwaikwayo. Gong Shuban ya kai hari ga ganuwar kasar Song, ko da yake ya canja dabaru da yawa, amma bai ci nasara ba.

Gong Shuban ba ya so ya amince da faduwarsa ba, ya fada wa Mo Zi cewa :"ina da wata dabara daban, amma ba zan gaya maka ba." Mo Zi ya ce :"ni ma ina da wata dabara daban, amma ba zan gaya maka ba." Sarkin kasar Chu ya tambayi Mo Zi mene ne dabararsa, Mo Zi ya ce :"nufin Gong Shuban shi ne yana so ya kashe ni. Sabo da a ganinsa, idan ya kashe ni, to babu 'yan kasar Song da za su tsare kasar yayin da kasar Chu ta kai wa kasar Song hari. Amma na riga na koyar da dalibana yadda ya kamata a tsare kasar, ko da an kashe ni, amma ba wanda zai iya shiga ganuwar kasar Song ba."

Ganin haka, sarkin kasar Chu ya ce :"ba zan kai wa kasdar Song hari ba." shi ya sa kasar Song ta magance wani hadari saboda basira da jar zuciyar Mo Zi.(Kande Gao)

Labari game da shirin daukan tsaurarrun matakai don kare raunin da ake da shi

Zhu Geliang wani shahararren mutum ne da kowa ya sani a kasar Sin. Idan wani mutum yana da basira, sai Sinawa su kan ce:" kai shi kamar Zhu Geliang ne." To, yanzu muna so mu gabatar muku wani labari game da Zhu Geliang.

A cikin karni na 3 kafin haihuwar Annabi Isa A.S., ya kasance da manyan kasashe uku a cikin kasar Sin, wato kasar Wei da ta Shu da kuma ta Wu. A kan kiran lokacin da suna "zamanin kasashe uku". A kan ta da yaki tsakanin kasashen uku, amma ko wane bai iya halaka sauran biyu ba. Zhu Geliang shi ne mashawarcin sojoji na kasar Shu, ya yi suna sosai domin kwarewarsa wajen yaki.

A wani karo, kasar Wei ta sami wani labarin cewa, kasar Shu ba ta girka sojoji masu karfi da yawa a wani muhimmin wurinta bisa manyan tsare-tsare wanda ake kiransa birnin Xicheng, yawan sojojinta bai kai dubu goma ba, shi ya sa kasar Wei ta aika da wani babban janar mai suna Si Mayi da ya shugabanci sojoji fiye da dubu dari domin kai wa kasar Shu hari. Da kasar Shu ta sami wannan labari, sai nan da nan ne sarkin kasar da sojojin kasar suka ji tsoro sosai. Saboda kasar Shu tana da sojoji dubu goma kawai, idan wadannan sojoji sun yi fada da abokan gaba fiye da dubu dari, ko shakka babu za su fadi. Kuma ba su da isasshen lokaci da su tura sojoji daga sauran wurare domin ba su taimako. Birnin Xicheng yana cikin wannan mawuyacin hali, kowa yana fatan mashawarcin sojojin kasar Zhu Geliang zai nemi wata dabara mai kyau.

Zhu Geliang ya yi ta yin tunani, a karshe dai ya tuna da wata dabara mai kyau sosai. Ya ba da umurni ga dukkan fararen hula da sojoji na Xicheng da su janye jikinsu daga birnin da kuma boye kansu a wani wuri mai lafiya, daga baya kuma a bude kofar birnin domin jiran abokan gabansu. Ba da dadewa ba Si Mayi, babban janar na kasar Wei da sojojinsa suka yi wa birnin Xicheng kawanya, amma abin mamaki shi ne, ba wanda ke tsaron kofar birnin, kofar bude take, wani tsoho ne kawai yake shara da tsintsiya. A daidai wannan lokacin da ba ya san yadda zai yi ba, sai ya ga wani mutum ya taho a kan ganuwar birnin, shi ne abokin gabansa Zhu Geliang. Daga baya kuma Zhu Geliang ya fara yin kide-kide. Dukkan sojojin kasar Wei sun ji mamaki kwarai da gaske, sabo da a daidai wannan lokaci mai muhimmanci, mai ba da shawara kan aikin soja na kasar Shu yana yin kide-kide, ba su san mene ne ya faru ba.

Fuskantar kofar birnin da ke budewa da kuma Zhu Geliang wanda ke yin kide-kide, Si Mayi bai san yadda zai yi ba, sabo da tun da ya san Zhu Geliang yana da basira sosai, amma yanzu ya bude kofar birnin domin jiran sojoji fiye da dubu dari, wannan ya wuce abin da ya tunani a da. Sabo da haka, yana ganin cewa, dole ne an girke sojoji masu yawa a boye a cikin birnin. A daidai lokacin, Zhu Geliang ya fara yin kide-kide da sauri, kamar za a yi ruwan sama mai tsanani. Da sauraron kide-kiden, sai Si Mayi ya ji abu maras kyau zai faru, yana shakkar cewa, kide-kiden nan sako ne da Zhu Geliang ya yi domin gaya wa sojoji da su fara yaki, sabo da haka ya ba da umurnin janye sojojinsa. Nan da nan sai sojojin da yawansu ya zarce dubu dari suka janye jiki da sauri, kuma domin wannan, an tsaron birnin Xicheng ba tare da yin amfani da ko soja guda ba. Wannan shi ne shirin daukan tsaurarrun matakai don kare raunin da ake da shi.(Kande Gao)

>>[Labarin Soja]

Zhou Yafu ya kwantar da kurar da sarakuna bakwai suka tashi

Kamar yadda sinawa su kan ce : "zakunan da wani rago ke shugabanta za su fadi idan suka yi fada tare da ragunan da wani zaki ke shugabanta." Wannan ya shaida cewa, shugaba yana da muhimmanci sosai a cikin yaki.

A cikin karni biyu kafin haihuwar Annabi Isa, an kafa daular Han ta kasar Sin. Gwamnatin daular Han da kabilar Hun da ke yammacin kasar Sin sun kiyaye zaman lafiya ta yin aurantaka tsakaninsu, kuma bangarorin biyu ba su ta da babban yaki tsakaninsu ba. Amma daga baya sarkin kabilar Hun ya amince da tunzura da aka yi masa, shi ya sa ya karya dangantakar da ke tsakaninta da daular Han. A cikin shekarar 158 kafin haihuwar Annabi Isa, sojojin kabilar Hun sun yi ta kai hari ga yankunan bankin iyakar daular Han, sun kashe mutane da kuma kwace kayayyaki. Sabo da haka, sarkin Han mai suna Wen Di ya aika da janar guda uku da su shugabanci rundunonin sojoji uku don yin dagiya da su. Haka kuma domin tsaron birnin Chang'an, babban birnin daular Han, ya aika da sauran janar uku da su tare da sojojinsu suka zauna a wuraren da ke kewayen birnin Chang'an. Janar Liu Li ya zauna a Bashang, Janar Xu Li ya zauna a Jimen, kuma Janar Zhou Yafu ya zauna a Xiliu.

A wani karo, sarki Wen Di ya je wuraren nan uku don kai ziyara ga sojoji da kuma yin bincike a kansu. Da farko ya isa Bashang, ganin zuwan sarki, nan da nan Liu Li da sojojinsu sun shirya babban biki don maraba da shi. Yayin da sarki da 'yan rakiyarsa suka shiga sansanin soja, ba wanda ya hana su. Jim kadan sai sarki ya tafi, janar da sojoji sun yi musu ban kwana. Daga baya kuma, sarki ya isa Jimen, sojojin nan kuwa sun shirya babban biki kamar na Bashang suka yi domin maraba da shi. A karshe dai sarki ya isa Xiliu, yayin da sojar sansanin sojojin Zhou Yafu ya ga wasu mutane da suka zo daga nesa, nan da nan ya gaya wa Zhou Yafu. Dukkan sojoji sun sa sulke kamar za su fara yaki da abokan gaba. Wasu 'yan rakiyar sarki a gaba sun isa kofar sansanin soja, wadanda suke tsaron kofar sun hana su, ba su amince da su shigo ba, sun ce :"a cikin sansanin soja, mu bi umurnin janar kawai. Idan janar bai ba mu umurni ba, to ba za mu yarda da ku shigo ba." Lokacin da 'yan rakiyar sarki suke yin zagi-zagi tare da sojojin da ke tsaron kofar, sarki ya iso, haka kuma wadanda ke tsaron kofar su ma sun hana shi shigowa a cikin sansani. Sarki bai san yadda zai yi ba, sai ya aika da bawansa da ya nuna musu alamar sarki da kuma tura wani da ya gaya wa Zhou Yafu, cewa zai shiga sansanin soja domin ziyarci sojoji. Bayan da Zhou Yafu ya ba da umurni, sai sojoji sun bude kofar.

Bayan da sarki ya gama yin ziyara ga sojoji, ya bar Xiliu. A kan hanyar dawo wa birnin Chang'an, bayin sarki sun yi fushi sosai, suna tsammanin cewa, Zhou Yafu ba ya girmamawa sarki. Amma sarki ya yi ta yi masa yabo, ya ce :"Zhou Yafu shi ne janar na gaskiya. Sojojin Bashang da na Jimen ba su da kyau, idan abokan gaba sun kai musu hari a boye, ko shakka babu za su fadi. Amma idan su gudanar da sojoji kamar Zhou Yafu, ko abokan gaba za su suka kai musu hari?" A cikin wannan binciken da sarkin Han Wen Di ya yi, yana ganin cewa, Zhou Yafu kararre ne a fannin soja.

A cikin shekara ta biyu, wato shekarar157 kafin haihuwar Annabi Isa A.S., ciwo mai tsanani ya kama da sarki Wen Di. Kafin ya tafi gidan gaskiya, ya tura wani da ya kira dansa wato yarima a gabansa, ya gaya masa cewa :"idan za a ta da hargitsi a cikin kasar, dole ne ka aika da Zhou Yafu da ya shugabanci rundunar sojoji, shi mutum ne da ya dace da yin aikin." Bayan da sarki Wen Di ya mutu, dansa Liu Qi ya zama sabon sarki, wato Sarki Jing Di. Sabo da wannan sabon sarki saurayi ne, shi ya sa sarakunan wurare bakwai sun yi amfani da damar, sun ta da rikici domin neman samun karagar sarki. Sarki Jiang Di ya bi wasiyyar ubansa ya aika da Zhou Yafu da ya kwantar da kurar da suka tashi. Fuskantar kawancen sojojin sarakuna bakwai masu karfi, Zhou Yafu ya dauki mataki kan sanar da tsaro kawai. Sau da yawa sarki ya ba da umurni kan kai farmaki ga sojoji 'yan tawaye, amma ya ki bin umurnin, sabo da ya sani ko da yake 'yan tawaye suna da karfi, amma domin yakin da suka ta da ba na adalci ba ne, shi ya sa tabbas ne ba za su yi shi cikin dogon lokaci ba. Ashe, haka ne, ba da dadewa ba, 'yan tawaye ba su kiyaye hakuri ba, sun fara hare-hare, amma Zhou Yafu bai mayar da martani kan wannan ba.

A karshe dai, ba yadda za su yi ba, sai 'yan tawaye sun yanje jikinsu, Zhou Yafu ya yi amfani da damar ya aika da wasu sojojinsa masu kyau don kai musu hari, kuma sun ci nasara a kansu. Ganin halin da ake ciki, sarakunan bakwai sun kashi kansu bi da bi.

Kwantar da kurar da sarakuna bakwai suka tashi da Zhou Yafu ya yi ta kiyaye dinkuwar daular Han da kuma karfafa karfin tsakiyar gwamnatin kasar.(Kande Gao)

Kai wa kasar Wei hari domin ceton kasar Zhao

Sun Bin shi ne wani sahararren masanin soja na zamanin Zhanguo a cikin tarihin kasar Sin. Shi da Pang Juan sun taba koyon dabarun soja tare, daga baya kuma sun bayar da gudummowarsu tare ga kasar Wei. Pang Juan ya yi hassada da kwarewar aiki ta Sun Bin, shi ya sa ya zalunce shi, har an yanke gwiwarsa. Daga baya kuma, babbar janar ta kasar Qi Tian Ji ya kubutad da Sun Bin cikin asiri. Labarin kai wa kasar Wei hari domin ceton kasar Zhao shi ne wani yakin da ke tsakanin Sun Bin da Pang Juan.

A cikin karni na hudu kafin haihuwar Annabi Isa, an yi gyare-gyaren siyasa da sojoji a cikin kasar Wei, wanda ya sa kasar tana ta kara karfinta, kuma ta mallake wasu kananan kasashe marasa karfi. A wancan lokaci, kasashe wadanda karfinsu suka yi daidai da kasar Wei su ne kasar Qi da kuma kasar Qin. Kasar Zhao da karamar kasar Wei wadanda suke makwabta da kasar Wei su kasashe ne marasa karfi sosai.

A cikin shekarar 368 kafin haihuwar Annabi Isa A.S., domin samun goyon baya daga kasar Qi, kasar Zhao ta kai wa karamar kasar Wei hari, wadda ta dogara ga kasar Wei. Sarkin kasar Wei ya aika da babbar janar kasar Pangjuan da ya shugabanci sojoji kusan dubu dari domin kai hari ga birnin Handan, babban birnin kasar Zhao. Ba abin da za a yi sai kasar Zhao ta roki kasar Qi domin neman taimako daga wajenta.

Zou Ji, minista na kasar Qi ya tsaya kan ra'ayin cewa, ba za ta ba da taimako ga kasar Zhao ba, sabo da yin haka zai raunana karfin kasar kanta. Amma Duan Ganlun, wani minista daban na kasar yana ganin cewa, idan kasar Wei ta yi nasara kan kasar Zhao, to wannan zai kara karfafa karfin kasar Wei, kuma wannan zai yi barazana wa kasar Qi, shi ya sa ya yarda da ba da taimako ga kasar Zhao.

Sarkin Qi ya karbi shawarar da Duan Ganlun ya bayar, shi ya sa ya aika da Tian Ji a matsayin babbar janar da kuma Sun Bin a matsayin mashawarcin soja da su shugabanci sojoji dubu tamanin domin ba da taimako ga kasar Zhao.

Bayan da Sun Bin ya yi nazari kan halin da ake ciki, yana ganin cewa, sojojin kasar Wei suna da karfi sosai, idan an yi yaki da su kai tsaye, to, kasar Qi za ta sha hasarori da yawa, shi ya da ya kamata sojojinta su kauce wa rundunar abokan gaba kuma su karya lagonsu. Kamar yanzu rundunar kasar Wei mai kyau ba ta cikin birnin Daliang, babban birnin kasar Wei, shi ya sa ya kamata a yi amfani da wannan dama domin kai wa babban birnin kasar hari, ganin haka tabbas ne sojojin Wei za su koma birnin Daliang domin kubutad da shi, ta haka kasar Zhao za ta fita daga mayuwacin halin da take ciki.

Domin neman tsayawa kan matsayi mai amfani, Sun Bin ya tsai da kudurin rude hankalin makiya da su yi tsammanin rundunar kasar Qi ba ta da karfi sam. Shi ya da da gangan ne ya aika da wani hafsa maras kwarewa wajen aiki da ya shugabanci wasu sojoji domin kai wa muhimmin birni na kasar Wei wajen soja Pingzhen hari, a karshe dai sojojin Qi sun fadi. Sabo da haka babban janar kasar Wei Pang Juan ya yi tsammanin cewa, sojojin Qi ba su da karfi sam, za a iya cinsu da yaki cikin sauki, shi ya sa ya kara kai wa kasar Zhao hari.

A sa'i daya kuma, Sun Bin shi da kansa ya shugabanci sojoji masu nagarta sosai da su kai wa birnin Daliang hari. Da Pang Juan ya sami labarin nan, nan da nan ne ya janye dukkan sojojinsa daga filin daga mai nisa domin kare babban birnin kasar. Sabo da dukkan sojoji da dawaki suna jin gajiya sosai, kuma Sun Bin da sojojinsa sun riga sun jiransu cikin dogon lokaci, a karshe dai sojojin Wei sun fadi.

Sojojin kasar Qi sun kauce wa rundunar abokan gaba kuma su karya lagonsu, wannan ba kawai ya kubutad da kasar Zhao ba, har ma ya raunana karfin kasar Wei, kuma ya ba da tasiri mai muhimmanci ga nan gaba.(Kande Gao)

Yakin Jingxing

A cikin shekara ta 206 kafin haihuwar Annabi Isa A.S., an rushe daular Qin, kasar gargajiya ce ta farko wadda ta dinke kasar Sin gaba daya a cikin tarihin kasar Sin, sabo da haka an bude wani sabon shafi na tarihin kasar Sin. A wancan lokaci, ya kasance da sabbin rukunonin soja biyu, wato Xiang Yu, sarkin kasar Xichu da Liu Bang, sarkin kasar Han, domin samun mulkin kasar Sin, sun fara kai wa juna farmaki. A cikin yakin da ke tsakaninsu na kusan shekaru biyar, babban janar na kasar Han wanda ake kiransa Han Xin ya nuna gwaninsa wajen sha'anin soja, yakin Jingxing shi ne abin misalin gwanintarsa.

A watan Oktoba na shekara ta 204 kafin haihuwar Annabi Isa, Han Xin ya shugabanci sojoji fiye da dubu goma da aka dauke su cikin soja ba da dadewa ba domin kai wa kasar Zhao hari, wadda karamar kasa ce a karkashin shugabancin Xiang Yu. Sarkin Zhao mai suna Xie da Chen Yu, babban hafsan hafsoshi na sojojin Zhao sun tara sojoji dubu dari biyu, kuma sun girke su a cikin wani wurin ketare dutsen Taihang mai kunci wanda ake kiransa Jingxing don yin yaki tare da Han Xin.

Jingxing wani tsugugi mai hadari ne da tilas ne sojojin Han za su ratsa shi, idan suna so su kai wa sojojin Zhao farmaki. A wancan lokaci, sojojin Zhao sun isa Jingxing da farko, kuma sun sarrafa da shi domin jiran sojojin Han.

Wani masharwacin sojojin Zhao mai suna Li Zuoche ya ba babban janar Chen Yu shawara, wato a wani bangare, yawancin sojoji sun yi yaki tare da sojojin Han, a daya bangare kuma, wasu sojoji sun yi kawanya ga abokan gaba, daga baya kuma dukkan sojojin sun kai wa sojojin Han farmaki gaba da baya domin kama Han Xin da rai. Amma Chen yu ya fi son kai wa abokan gaba hari a gabansu, shi ya sa bai karbi shawarar da Li Zuoche ya bayar.

Han Xin ya sani bambancin da ke tsakain bangarorin biyu wajen karfin sojoji ya yi yawa, idan sun kai wa abokan gaba kai tsaye, ko shakka babu za su fadi. Shi ya sa ya girke sojojinsa a wurin da ke nesa da Jingxing, ya yi ta yin nazari kan Jingxing da yadda aka girke sojojin Zhao. Yayin da Han Xin ya samu sakon leken asiri kan cewa, Chen Yu bai mai da hankali a kan abokan gaba ba, kuma yana so a gama yin yaki cikin sauri, nan da nan ne ya jagoranci sojojinsa da su zaune a wurin da ke kilomita 15 na Jingxing.

A cikin tsakar dare, Han Xin ya zabi sojoji da suka fi inganci dubu biyu wadanda ko wanensu ya dauki wata tutar Han, sun bi karamar hanya ta dutsen zuwa wurin da ke bayan sansanin sojojin Zhao don yin musu kawanya. Idan sojojin Zhao sun tashi daga sansanin soja kashegari don yaki, to za su kutsa kai cikin sansanin sojojin Zhao domin kafa tutar Han cikin kasa.

Daga baya kuma, Han Xin ya ba da umurni ga sojojinsa da su nufi sojojin Zhao. Yayin da suka kusa da Jingxing, gari ya waye. Dukkan sojojin Zhao su ma sun shirya domin fara yaki. Da Chen Yu ya ga Han Xin yana da sojoji marasa yawa, kuma yana sarrafa muhimmin wuri, nan da nan sai ya ba da umurnin kai wa sojojin Han farmaki. Suna ta yin yaki har dogon lokaci, amma sojojin Zhao ba su ci nasara ba.

A daidai wannan lokaci, sojoji da dama ne suka zaune a cikin sansanin sojojin Zhao, sojojin Han dubu biyu da Han Xin ya girke sun kutsa kai cikin sansanin, sun kafa tutocin kasar Han, daga baya kuma sun buga ganga da kuma ihu. Ba zato ba tsammani, sojojin Zhao da suke cikin yaki sun iske cewa, sansaninsu cike yake da tutocin sojojin Han, nan da nan ne sun bata ransu. Han Xin ya yi amfani da wannan halin da ake ciki don mai da farmaki, sojojin Zhao dubu dari biyu sun fadi, an kashe hafsan hansoshi Chen Yu da kuma kama sarkin Zhao da rai.(Kande Gao)

Yakin Feishui

A cikin farkon karni na hudu, an rushe gwamnatin tsakiya ta wancan lokaci, kuma an kafa mulki biyu a cikin kasar Sin, wani yana kudancin kasar Sin, wani kuma yana arewacin kasar. Kasar Dongjin, mulkin siyasa na kabilar Han da ke kudancin kasar Sin ya sarrafa yankin kogin Yangtsi, babban birninsa shi ne Jiankang, wato birnin Nanjing na yanzu, haka kuma kasar Qianqin, mulkin siyasa na kabilar Di da ke arewacin kasar Sin ya sarrafa da yankin kogin Huanghe.

Sarkin daular Qianqin Fu Jian shi mutum ne na karewar aiki, ya mai da hankali kan yin amfani da masu ba da shawara na kabilar Han da yin gyare-gyare kan tsarin jami'ai da karfafa ikon tsakiyar gwamnatin kasar da kuma gudanar da manufofin tattalin arziki wajen raya sha'anin noma, a sa'i daya kuma ya dora muhimmanci kan sojoji, yana fatan zai hallaka kasar Dongjin domin sake dinka kasar Sin gaba daya.

A cikin shekarar 383, Fu Jian ya dauki 'yan kabilu daban daban da yawansu ya kai dubu dari takwas da saba'in da su nufi kudu domin kai wa kasar Dongjin hari. Bisa labarin leken asiri da aka samu, an ce, kasar Dongjin tana da sojoji fiye da dubu dari kawai, shi ya sa Fu Jian ya ce ba tare da tsoro ba, " muddin sojojina su jefa bulalar doki a cikin kogi, sai kogin ba zai kwarara ba, shi ya sa abin tabbbas ne zan hallaka kasar Dongjin."

Yayin da kasar Dongjin ta san sojojin Qianqin sun riga sun nufi kudu, cikin gaggawa ne ta aika da Xie Shi da Xie Xun da su shugbanci sojoji masu kyau dubu tamanin domin yin dagiya da abokan gaba. A cikin daidai wannan lokaci, sojoji a gaba na kasar Qianqin sun riga sun isa birnin Luojian da ke kusa da kasar Dongjin, wato gabashin birnin Huainan da ke jihar Anhui ta kasar Sin yanzu, kuma sun hana ayyukan tafiye-tafiye na kogin Huaihe, halin da ake ciki yana da tsanani sosai. Xie Shi da Xie Xuan sun tura sojoji dubu biyar da su kai wa abokan gaba da ke birnin Luojian farmaki a asiri, kuma sun ci nasara sosai, sabo da haka an karfafa zuciyar sojojin Dongjin, sun ci gaba da tafiya har zuwa kogin Feishui da ke tsakiyar jihar Anhui ta kasar Sin yanzu.

Sanin faduwar sojoji a gaba ke da wuya, sai nan da nan Fu Jian ya je filin daga don sa ido. Yayin da ya hawa kan kofar ganuwa don duba sojojin Dongjin da ke gabashin gabar kogin Feishui, sai ya ga tantuna da yawa a gabar da ke gabansa, bugu da kari kuma ya saurari muryar ganga, da jin haka, ya ji tsoro sosai, sai ya juya baya, ya yi wa 'yan rakiyarsa cewa:" sojoji da dawaki na kasar Dongjin sun yi yawa, a hakika dai su abokan gaba masu karfi sosai, don me kuka ce su marasa karfi ne?"

A daidai wannan lokaci, ta yin nazari, Xie Shi da Xie Xuan suna ganin cewa, ko da yake kasar Qianqin tana da sojoji masu yawa kwarai, amma dukkansu an dauke su daga kalibu daban daban ba tare da na sa kai ba, sabo da haka tabbas ne zukatansu ba su yi daya ba ne, bugu da kari kuma rundunar sojojin Qianqin ta yi girma, kuma sun riga sun yi tafiya da yawa, shi ya sa dukkan sojoji da dawaki sun ji gajiya kwarai, shi ya sa ya kamata sojojin Dongjin sun yi amfani da dabarar yin hare-hare cikin sauri. Ganin haka, Xie Shi da Xie Xuan sun mika wa Sarki Fu Jian wasika, inda suka bukaci sojojin kasar Qianqin da su janye jikinsu daga gabar kogin Feishui domin sojojin Dongjin su wuce kogin don fara yaki tsakaninsu. Fu Jian ya yi riya a zuciyarsa cewa, idan mu yi amfani da damar wuce kogi da sojojin Qianqin ke yi domin kai musu hari, to dole ne za mu ci nasara. Shi ya sa ya ba da umurin janye sojoji daga gabar kogin. Amma abin da ya fi tsammaninsa shi ne dukkan sojojin Qianqin ba su so su yi yaki ba, sanin umurnin janye jikinsu ke da wuya, sai sojojin da ke baya suka yi tsammanin cewa, dole ne sojoji a gaba sun ci hasarar yaki, shi ya sa suka gudu, nan da nan ne rudunar sojojin kasar Qianqin ta rude. Sojojin Dongjin sun yi amfani da damar su wuce kogin Feishui don kai musu farmaki. A daidai wannan lokaci, wasu daga cikin sojojin Qianqin sun yi ihu cewa :"kasar Qianqin ta fadi, kasar Qianqin ta fadi." Da jin haka, sojojin sun fi rudewa. Cikin gajerren lokaci ne, sojojin Qianqin dubu gomai sun taka juna, yawan mutuwa ba a iya lisaftuwa ba, har ma Sarki Fu Jian ya ji rauni. Sabo da haka, kasar Qianqin ta fadi sosai, kuma ba ta farfado da kasa ba, bayan shekaru biyu ke nan an rushe kasar Qianqin.(Kande Gao)

Yakin Changping

A cikin zamanin Zhanguo na kasar Sin, wato karni na hudu kafin haihuwar Annabi Isa A.S., kasar Qi ta dinga karfafa karfinta ta yin gyare-gyare cikin kasar. Yayin da sarkin Qin Zhao Wang ke kan karagar mulin kasar, kasar Qin ta riga ta zama kasa mafi girma a cikin manyan kasashe bakwai. Yakin Changping shi yaki ne mafi shahara kafin kasar Qin ta dinke duk kasar sin.

Kasashen Han da Wei da Yan da Zhao kasashe ne da ke makwabtaka da kasar Qin, kuma sun kulla dangantakar kawance da ke tsakaninsu domin hana mamayewar kasar Qin. A cikin kasashen hudu, kasar Zhao kasa ce mafi karfi, kasar Wei kasa ce mafi maras karfi. Tun daga shekara ta 268 kafin haihuwar Annabi Isa, da farko dai kasar Qin ta kai wa kasar Wei hari, wanda ya sa kasar Wei ke karkashin jagorancin kasar Qin. Daga baya kuma kasar Qin ta kai wa kasar Han farmaki, sarkin Han ya ji tsoro sosai, shi ya sa ya aika da wani da ya shiga kasar Qin don bayyana ra'ayinsa kan mika wa kasar Qin wani gari mai suna Shangdang domin neman samun zaman lafiya a kasar. Amma Feng Ting, magajin garin ba ya so ya yi haka, ya mika garin ga kasar Zhao don bunkasa hadin gwiwar kasashen Han da Zhao kan yin dagiya da kasar Qin tare.

Sabo da kwadayinsa da kuma rashin hangen nesa, sarkin kasar Zhao ya karbi garin nan, wanda ya fusata kasar Qin. A cikin shekara ta 261 kafin haihuwar Annabi Isa, sarkin kasar Qin ya ba da umurni ga babban janar Wang Qian da ya shugabanci sojoji domin kai wa garin Shangdang hari. Sojojin Zhao da ke Shangdang ba su fi sojojin Qin karfi ba, shi ya sa sun janye jikinsu har birnin Changping. Da sarkin Zhao ya ji wannan batu, sai ya aika da babban janar Lian Po da ya shugabanci sojojin Zhao masu karfi zuwa birnin Changping domin neman sake kwace Shangdang daga hannun sojojin Qin.

Bayan da sojojin Zhao suka isa birnin Changping, nan da nan ne sun fara kai wa sojojin Qin farmaki. Sabo da karfin wadannan sojojin Zhao sun fadi sau da dama a jere, shi ya sa Lian Po ya canja sitatiji, wato sojojinsa sun yi tsaro kawai, sai sun yi jira har sojojin Qin suka ji gajiya. Lalle dabarar nan ta ba da amfani sosai, an rage yawan hare-haren da sojojin Qin suka yi, ko wane na bangarorin biyu bai iya ci nasarar yakin nan.

Domin karya halin kaka ni ka yi da ake ciki, sojojin Qin sun aika da wani da ya je birnin Handan, babban birnin kasar Zhao domin ba da kudade da yawa ga manyan jami'an kasar domin su iza kiyaya a tsakanin Lian Po da Sarkin Zhao, wato sun yada jita-jita cewa, dalilin da ya sa Lian Po ya yi tsaro kawai bai kai wa sojojin Qin hari shi ne sabo da yana so ya mika wuya ga sojojin Qin, kuma mutumin da sojojin Qin suka fi jin tsoro shi ne Zhao Kuo, wani babban janar kasar Zhao daban. Da jin haka, nan da nan ne sarkin Zhao ya ba da umurni ga Zhao Kuo domin ya maye gurbin Lian Po, ya zama sabon shugaban sojojin Zhao.

Zhao Kuo ya karanta littattafan soja masu yawa, amma bai taba shiga ko wane yaki ba. Isawarsa a birnin Changping ke da wuya, sai ya canja sitatijin Lian Po.

A sa'i daya kuma, kasar Qin ta canja shugaban sojojinta a asiri, wato Bai Qi, babban janar mafi kyau ya maye gurbin Wang Qian. Bai Qi ya dauki matakin soja kan cewa dukkan sojojin Qin sun nuna kamar sojojin Zhao za su iya ci nasara a kansu cikin sauki, da haka sun janye jikinsu, har sun yaudari abokan gaba da su shiga tarko da suka yi musu. Sojojin Zhao da Zhao Kuo ke shugabanta sun yi iyakacin kokarinsu domin keta kawanyan da sojojin Qin suka yi musu, amma sun kasa. Kuma Zhao Kuo ya mutu don kibiya da aka harbe shi. Dukkan sojojinsa sun mika wuyansu.

Bayan yakin nan, kasar Qin ta kara karfafa karfinta wajen sojoji.(Kande Gao)

Cao Gui ya yi dagiya da kasar Qi

A zamanin Zhanguo na tarihin kasar Sin, ya kasance da kananan kasashe da yawa a cikin kasar Sin, wasu daga cikinsu wadanda suke da karfi suna so su zama sarki mafi girma, wato sauran kasashe suna karkashin jagorancinta. Kasar Qi ita ce daya daga cikinsu. Bisa sojoji masu karfi da sarkin kasar Qi Huan Gong ya dogara a kansu, kasar Qi ta kai wa kasar Lu maras karfi farmaki a cikin shekara ta 684 kafin haihuwar Annabi Isa. Kuma sarkin kasar Lu Zhuang Gong ya tsai da kudurin yin dagiya da kasar Qi ba tare da jin tsaro ba.

Sanin harin da kasar Qi ta yi wa kasar Lu, dukkan jama'ar kasar Lu sun fusata sosai. Wani farar hula wanda ake kiransa Cao Gui yana cikin shirin yi wa sarki Zhuang Gong gaisuwa domin rokon shiga yakin yin dagiya da kasar Qi. Wani ya lallashe shi cewa :"wannan babban al'amari na duk kasar manyan jami'ai su damu da shi, ina ruwanka?"

Cao Gui ya ce :"manyan jami'ai ba su da hengen nesa, kila ba su da dabara mai kyau. Yanzu kasarmu tana cikin hali mai tsanani, ya kamata mu mai da hankali a kanta." Shi ya sa ya je kofar fadar sarki domin neman ganin sarki.

Da Cao Gui ya yi gaisuwa ga sarki Zhuang Gong, ya gaya masa bukatarsa kan shiga yakin yin dagiya ga kasar Qi, kuma ya tambayi sarki cewa:" kasarmu ba ta fi kasar Qi karfi ba, to mene ne ka dogara domin yi dagiya da sojojin kasar Qi?"

Sarki ya ce :"a cikin zaman yau na kullum, idan ina da abinci mai kyau ko tufafi masu kyaun gani, to zan ba su ga saura. Sabo da haka a ganina, mutanena za su goyi bayata." Da jin haka Cao Gui ya kada kai don nuna kin yarda, cewa :"Wannan karamar riba ce, kuma babu mutane da yawa sun ci ribar, shi ya sa fararen hula ba za su goyi bayanka don wannan."

Sarki ya ce :"kullum na ba da gaskiya sosai ga gunki."

Cao Gui ya yi murmushi, ya ce :"gunki ba zai ba ka taimako ba."

Sarki ya yi tunani, kuma ya ce :"game da batun kai kara, ko da ya ke ban iya yin bincike sosai kan ko wane batu, amma na yi iyakacin kokarina domin daidaita su."

Da jin haka, Cao Gui ya kada kai, ya ce :"madalla, wannan batu ne da ya iya samu zukatan fararen hula, a ganina a iya godara bisa batun domin yaki da kasar Qi."

Cao Gui ya roki sarki domin tafi filin daga tare, sarki ya ga lalle Cao Gui yana da dabara mai kyau, shi ya sa ya amince da rokonsa. Daga baya kuma mutanen biyu sun tashi a cikin keken doki na soja guda tare da sojoji.

Bisa al'adar gargajiya ta kasar Sin, a cikin zamanin da, idan rundunonin sojoji biyu suna son yin yaki tsakaninsu, kullum bangare A ya buga ganga domin tayar da yaki, kuma bangare B shi ma ya buga ganga domin nuna amincewarsa wajen tayar da yaki. Idan bangare B bai buga ganga domin amsa kirar A wajen tayar da yaki, kullum bangare A zai fara kai wa B farmaki bayan ya buga ganga har sau uku.

An girka rundunonin sojoji na kasashen biyu na Qi da Lu a birnin Changshao da ke jihar Shandong ta kasar Sin yanzu, sojojin Qi sun yi tsammanin cewa, yawansu ya fi yawa, shi ya sa sun fara buga ganga domin tayar da yakin da ke tsakaninsu da abokan gaba. Da jin haka, sarkin kasar Lu ya shirya ba da umurnin fara yaki, Cao Gui ya hana shi, ya fadi cewa :"kada ka fara yaki cikin gagawa, lokacin yaki bai isa ba tukuna."

Yayin da sojojin Qi suka buga ganga na sau biyu, kamar yadda ya yi a da, Cao Gui ya hana sarkin Lu. Ganin haka, dukkan sojojin Lu sun fusata sosai, amma sabo da ba su da umurnin sarki, ba abin da zai yi sai sun jira kawai.

Janar sojojin Qi ya ga sojojin Lu ba su yi kome ba, shi ya sa ya ba da umurnin buga ganga na sau uku. Sojojin Qi sun yi tsammanin sojojin Lu sun jin tsoro, shi ya sa sun fara kai wa sojojin Lu hari ba tare da hankali ba.

A daidai wannan lokaci, Cao Gui ya gaya wa sarkin Lu cewa :" ranka ya dade, yanzu kana iya ba da umurnin fara yaki."

Sojojin Lu sun fara buga ganga, nan da nan ne an yi wa dukkan sojojin kwarin gwiwa, sun fara kai wa sojojin Qi hari kamar damisa. Abin da ya faru a gaban sojojin Qi ya zarce abubuwan da suka yi tsammani a da, domin marasa karfi sun fadi, sabo da haka sun fadi.

Lokacin da sarkin Lu ya ga sojojin Qi sun fadi, nan da nan sai ya so ya ba da umurnin ci gaba da ba su kashi. Cao Gui ya ce :"kada ka yi haka yanzu." Ya yi tsalle daga motar soja, ya ga alamar sawun keken doki na soja na sojojin Qi, daga baya kuma ya tsaya a kan keken doki, ya hengi abokan gaba da ke janye jikinsu, ya ce :"don Allah ranka ya dade, ya ba da umurnin ci gaba da ba su kashi."

Da sojojin Lu sun ji umurnin, kowa ya cika da karfi, sun ci gaba da kore su har waje na kasar Lu.

Sojojin Lu sun ci nasara a ciki yakin, sarki ya yi wa Cao Gui yabo. Bayan suka dawo wa fada,sarki ya tambayi Cao Gui, cewa :"don me ba ka yarda da mu amsa yaki ba yayin da sojojin Qi suka buga ganga har sau biyu?"

Cao Gui ya amsa cewa :"karfafa zuciyar sojoji yana da muhimmanci sosai yayin da ake yin yaki. Da abokan gaba suka buga ganga a karo na farko, sojojinsu suna da karfi sosai, yayin da suka buga ganga a karo na biyu, an rage karfin sojoji kadan, kuma lokacin da suka buga ganga a karo na uku, an riga an rage dukkan karfin sojoji. A daidai wannnan lokaci, sojojinmu suna da karfi sosai, ko shakka babu za su ci nasara."

Daga baya kuma sarki ya tambaye shi dalilin da ya sa ba a ci gaba da ba su kashi nan da nan. Cao Gui ya ce :"ko da yake sojojin Qi suka janye jikinsu don fadi, amma kasar Qi wata kasa ce mai girma, tana da sojoji masu karfi, shi ya sa ina ganin cewa, watakila ne sun yi yaudara kamar sun fadi, kuma sun jira mu a wani wuri, sabo da haka ya kamata mu mai da hankali a kan wannan. Daga baya kuma, na ga tutarsu ta fadi, alamar sawun kekunan doki nasu a barkatai suke, to na iya tattabar da cewa, gaskiya ne sun fadi, shi ya sa na roke ka kan ba da umurnin ci gaba da kai musu farmaki.

Jin haka, sarki Zhuang Gong ya gane cewa, ashe, haka ne, ya yi ta yi wa Cao Gui yabo.(Kande Gao)

Yakin Baiju

Kasar Wu da kasar Chu kasashe biyu ne da ke cikin zamanin Chunqiu na kasar Sin, wato karni na shida kafin haihuwar Annabi Isa. Domin neman zaman sarki mafi karfi, a cikin shekaru 79, wato daga shekara ta 584 zuwa ta 514 kafin haihuwar Annabi Isa, bangarorin biyu sun yi ta yin yaki tsakaninsu har sau goma. A cikin shekara ta 515 kafin haihuwar Annabi Isa, yarima He Lu na kasar Wu ya hau kujerar sarkin kasar. Bayan da ya zama sarkin kasar Wu, ya yi ajiyar zuci cewa, zai dinke duk kasar Sin gaba daya. Sabo da haka ya raya tattalin arziki, kuma ya mai da hankali a kan sha'anin soja, ya nada shahararren kwararre a fannin soja, wato Sun Wu da ya zaman babban janar domin koyar da dabarun soja, duk kasar Wu ta yi wadata sosai.

Kasar Chu wata babbar kasa ce daban a kudancin kasar Sin, a cikin dogon lokaci ta riga ta mallaka sauran kasashe mafi yawa. Amma tun bayan da Zhao Wang ya zaman sarkin kasar Chu a cikin shekara ta 516 kafin haihuwar Annabi Isa, karfin kasar Chu tana ta raguwa sakamakon cin hanci da rashawa na siyasar gida da kuma yin yaki tare da kasashe masu makwabtaka da ita. A cikin shekara ta 512 kafin haihuwar Annabi Isa, bi da bi ne sarki He Lu ya murkushe kananan kasashen Xu da Zhongwu wadanda suke karkashin shugabancin kasar Chu, daga baya kuma yana so ya yi amfani da wannan dama mai kyau domin kai wa kasar Chu hari.

Sun Wu yana ganin cewa, dukkan yawan mutane da yawan yankunan kasar Chu sun fi na kasar Wu yawa, shi ya sa ko da yake karfin kasar Chu yana ta lalacewa, amma sojojinta suna da karfi sosai. Kuma kasar Wu ta yi yaki cikin shekaru da yawa a jere, an kashe kudi da kayayyakin soja da yawa, shi ya sa ya kamata a jira zarafi mai kyau domin kai wa kasar Chu hari. Ban da wannan kuma Sun Wu ya ba da shawara kan cewa an raba sojojin kasar Wu cikin kashi uku domin suna ta ba wa sojojin Chu haushi daya bayan daya.

Sarkin Wu ya karbi shawarar da Sun Wu ya gabatar. A lokaci lokaci, kasar Wu ta aika da wata rundunar sojojinta domin kai wa yankunan bakin iyakar kasar Chu farmaki. Har kullum sarkin Chu ya aika da sojoji da yawa don yaki. Amma idan sojojin Chu suka tashi, to sojojin Wu za su janye jikinsu. Janye sojojin Chu daga yankunan bakin iyakar kasar ke da wuya, to runduna ta biyu ta sojojin Wu za ta sake kai wa kasar Chu hari. Kasar Wu ta yi ta yin haka har shekaru shida, wanda ya haddasa gajiyar sojojin kasar Chu sosai da kuma kashewar kudi da kayayyakin sojojin kasar Chu masu yawa, kasar Chu ta fi samun lalacewa.

A cikin shekara ta 506 kafin haihuwar Annabi Isa (A.S.), kasar Wu ta yi tsammanin cewa, lokaci ya yi da za su kai wa kasar Chu hari. Sabo da har wancan lokaci, yawan sojojin kasar Chu sun ninka na kasar Wu, shi ya sa Sun Wu ya tsai da kuduri kan daukar matakin kai hari cikin sauri. Ya zabi sojoji mafi kyau fiye da dubu domin su nufi bakin iyakar kasar Chu cikin sauri a asiri.

Sarkin Chu wanda bai shirya kome ba ya sami labarin, cikin gagawa ne ya aika da manyan janar-janar Nang Wa da Shen Yinshu da su jagoranci dukkan sojojin kasar don gamu da sojojin Wu. Bangarorin biyu sun tsai da fara yakin da ke tsakaninsu a birnin Baiju, wurin da ke kusa da birnin Anlu na jihar Hubei da ke kasar Sin yanzu. Shen Yinshu ya gabatar wa Nang Wa wata shawara kan cewa, Nang Wa ya shugabanci yawancin sojoji don yin tsaro a gaban abokan gaba, shi da kansa kuma ya jagoranci wasu sojoji don yin kawanya ga abokan gaba, daga baya kuma sun kai musu farmaki tare. Wannan hanya ce mafi kyau da sojojin Chu za su bi don cin nasara kan sojojin Wu. A farko dai, Nang Wa ya amince da shawarar da Shen Yinshu ya bayar.

Amma bayan da sojojin da Shen Yinshu ke shugabanta suka tashi, domin jin maganar cin zarafi da mutanensa ya yi kan cewa, wai idan suka ci nasara, to sarki zai fi nuna wa Shen Yinshu yabo domin dabarar yaki da ya gabatar, shi ya sa Nang Wa shi da kansa ya tsai da kudurin canja dabarun da aka tsara a da, wato ya fara kai wa sojojin hari shi kadai, a karshe dai sojojin Chu da yake shuganta sun fadi. Da Shen Yinshu ya san labarin nan, nan da nan ne ya shugabanci sojojinsa don ba su taimako. A karkashin shugabantar Sun Wu, sojojin kasar Wu sun yi kawanya ga sojojin Shen Yinshu. Ganin haka, Shen Yinshu ya yanke kansa domin ba da sarkin Chu. Da sarkin Chu ya ji labarin faduwar sojojinsa a cikin yakin da ke tsakanin kasashen Chu da Wu, ya bar babban birnin kasar tare da iyalinsa a asirce. Da sojojin da ke filin daga suka ji labarin, nan da nan sai suka bata ransu. Sabo da haka sojojin Wu sun shiga babban birnin kasar Chu. Daga baya kuma, wani ministan kasar Chu Mai suna Shen Baoxu ya yi gudun hijira har zuwa kasar Qin, wata kasa mai karfi daban. Sabo da rokon da ya yi wa kasar Qin, a karshe dai kasar Qin ta yarda da tura sojoji domin kai wa kasar Wu hari, sabo da haka kasar Wu ta janye sojojinta daga kasar Chu.(Kande Gao)

Yakin Chibi

Labarin yakin Chibi labari ne mafi shahara a cikin tarihin kasar Sin, domin a cikin yakin da aka yi a zamanin Kashshe Uku na tarihin kasa Sin, wato karni na biyu, sojoji marasa karfi sun ci nasara kan masu karfi sosai.

Bayan da Cao Cao, sarkin kasar Wei ya sarrafa da yankin arewacin kasar Sin, sai ya shugabancin sojojinsa da su nufi kudu domin kai wa kasar Shu hari, kuma ya mamaye birnin Jingzhou sakamakon cin nasara kan Liu Bei, sarkin kasar Shu. Ba yadda zai yi ba sai Liu Bei ya janye sojojinsa har zuwa birnin Xiaokou. Domin kwadayinsa na cin nasara kan kasashen Shu da Wu tare, sarki Cao Cao ya nufi kudu tare da sojojinsa masu karfi dubu dari biyu har zuwa gabar kogin Yangtsi da ke kusa da yankin bakin iyakar kasar Wu. Sabo da haka kasashen Shu da Wu sun kulla dangantakar kawance da ke tsakaninsu domin yin dagiya da Cao Cao.

Ko da yake yawan sojojin Cao Cao ya ninka sau hudu da na kawancen sojojin kasashen Shu da Wu, amma sojojin Cao Cao ba su saba da yin yaki a kan kogi. Sabo da haka sun janye jikinsu da kuma tsugunewa a arewacin gabar kogin Yangtse domin yin gaba da kawancen sojoji a bakin kogin.

Zhou Yu, shugaban sojojin kasar Wu da kwararre a fannin soja na kasar Shu Zhu Geliang sun tsai da kudurin kunar kwalekwalen fada na sojojin Cao Cao. Da farko dai, sun yi dabara kan nuna kamar Huang Gai, wani tsohon janar na kasar Wu ya mika wuya ga kasar Wei. Don cimma burin nan, da gangan ne Huang Gai ya yi fada tare da sarki Zhou Yu. Daga baya kuma, Huang Gai ya je wurin Cao Cao, ya gaya masa cewa, yanzu ya riga ya canja tunaninsa yana so ya bayar da gudummowarsa ga sarki Cao Cao tare da dukkan kwalekwalen fada nasa. Ganin haka, Cao Cao ya yi dukkan imaninsa ga Huang Gai.

A daidai wannan lokaci, wani kwararre mafi shahara daban a zamanin a fannin soja wanda ake kiransa Pang Tong ya zo domin yi wa sarki Cao Cao gaisuwa, ya ba shi wata shawara cewa, idan an daure dukkan kwalekwalen fada tare da igiya, to sojoji za su iya tsaya kan kwalekwale domin fada da abokan gaba kamar yadda suka saba yi a da a kan kasa. Jin haka, Cao Cao yana murna ya zuba ruwa a kasa ya sha, ya ce :" Lalle, wannan dabara ce mai kyau sosai." Amma a hakika dai Pang Tong shi ne abokin arziki na Zhu Geliang, shi ya sa da gangan ne ya gaya wa Cao Cao dabarar. Wani mashawarcin soja na kasar Wei ya ce:" ranka ya dade, lalle daure dukkan kwalekwalen fada tare da igiya wata dabara ce mai kyau, amma idan abokan gaba sun kai mana farmaki da wuta, yaya za mu yi ?" Cao Cao ya ce :" ba damuwa. Muna arewa, suna kudu. Yanzu lokacin dari ne, har kullum iska ta kan buga ne daga arewa maso yamma, tabbas ne ba za a busa iska daga kudu maso gabas ba. Idan sun kai mana hari da wuta, to za su kona kansu." Da jin haka, dukkan sojojin Cao Cao sun yi ajiyar zukatansu.

Amma ba kamar sanin kowa ba, a ran 20 ga watan Nuwamba, ba zato ba tsammani an busa iska daga kudu maso gabas. Kuma a daidai wannan rana, an mika wa Cao Cao wata wasikar da Huang Gai ya rubuta shi, inda Huang Gai ya ce, zai mika wuyansa tare da dukkan kwalekwalensa ga Cao Cao a ran nan. shi ya sa Cao Cao da manyan janar-janar nasa sun tsaya a kan kwalekwale don jiransa. Gaskiya ne, sun ga Haung Gao ya nufe su tare da kwalekwalen fada fiye da goma. Cao Cao ya ji murna sosai. Cikin sauri ne dukkan kwalekwalen nan sun zo a gaban Cao Cao. Kwaram an kunna musu wuta, ashe dukkan kwalekwalen nan cike suke da mai da ciyayi. Domin iska daga kudu maso gabas, kwalekwalen sun kutsa kansu a cikin sojojin Cao Cao, nan da nan dukkan kwalekwalen fada na sojojin Cao Cao sun kama wuta. Sabo da abin da yake faruwa ya wuce abin da Cao Cao yake tsammani a da, shi ya sa an halaka yawancin kwalekwalensa, haka kuma cikin sauri ne wutar ta yadu har bakin kogi na arewa, wato sansanin sojojin Cao Cao, sojojin Cao Cao sun fadi sosai.(Kande Gao)

Labarin liyafar cin abinci a garin Hongmen

A shekaru 221 kafin bayyanuwar Annabi Isa(A.S), an sami dinkuwar daular mulkin gargajiya ta farko a tarihin kasar Sin wato Daular Qin. Sabo da shugabannin Daular Qin su kan ci da gumin jama'a, shi ya sa jama'a sun yi ta yin tawaye. A cikin jama'ar da suka yi tawaye, akwai sojoji biyu suna da karfi sosai, daya daga cikinsu babban manaja mai suna Xiang Yu ke shugabanta, wani daban kuma wani karamin jami'i wanda ake kira Liu Bang ke shugabanta.

Xiang Yu ba ya son jin ra'ayin sauran mutane ba, amma ya iya yaki sosai, shi ya sa ya yi suna sosai a kasar Sin; Liu Bang mai wayo ne kamar barawo, amma ya iya yin amfani da mutane sosai. Sabo da dukkansu sun yi tawaye ne domin murkushe mulkin Daular Qin, shi ya sa suka zama wani kawance, sun ba da taimako ga juna. Xiang Yu da Liu Bang sun daddale wata yarjejeniya inda suka yarda da cewa, wanda ya iya shiga cikin birnin Xianyang, babban birnin Daular Qin da farko, sai aka nada shi da ya zama shugabansu.

A shekaru 207 kafin bayyanuwar Annabi Isa, Xiang Yu ya lashe sojojin Daular Qin a birnin Julu, amma a daidai wannan lokaci, Liu Bang ya riga ya lashe sojojin da Daular Qin ke jibgewa a birnin Xianyang. Bisa shawarar da aka kawo shi, Liu Bang ya girke sojojinsa a garin Bashang da ke dab da birnin Xianyang, amma bai shiga cikin birnin Xianyang ba. A maimakon haka, ya rufe fadar Daular Qin, ya yi abin kirki ga jama'a. Farar hula sun ga Liu Bang ya yi abin kirki gare su, kuma sojojinsa na bin doka sosai, shi ya sa sun jin murna sosai, suna fata Liu Bang zai zama shugaban kasa.

Da Xiang Yu ya ji haka, sai fushi yake ji, ya shugabanci sojojinsa da yawansu ya kai dubu 40 zuwa garin Hongmen da ke dab da birnin Xianyang, yana shirin shiga cikin birnin. Mai ba da shawara gare shi wato Fan Zeng ya ce ya kamata ya lashe Liu Bang da farko, ya ce, "a da, Liu Bang mutum ne mai kwadayi kuma mai son mata ne sosai, amma har yanzu ba ya kwace dukiya, kuma ba ya neman mata masu kyaun gani. Wannan ya bayyana cewa, yana da hangen nesa. Sabo da haka ne, ya kamata ka kashe shi tun da bai bunkasa sosai ba."

Da Liu Bang ya ji labarin, ya tambayi mai ba da shawararsa Zhang Liang, Zhang Liang yana ganin cewa, a halin yanzu dai, yawan sojojin da Liu Bang ke shugabanta shi ne dubu goma kawai, ba su iya yin fada da sojojin da Xiang Yu ke shugabanta ba. Shi ya sa Zhang Liang ya kirawo abokinsa kuma kawun Xiang Yu wato Xiang Bo da ya je garin Hongmen domin rarrashin Xiang Yu kada ya yi fada da Liu Bang. Bayan haka, Liu Bang da Zhang Liang da wani babban janar mai suna Fan Kuai sun je garin Hongmen, sun gaya wa Xiang Yu cewa, suna nan ne suna gadin birnin Xianyang, suna jiran Xiang Yu da ya zo ya zama shugaba. Xiang Yu yana tsammani maganar da suka yi gaskiya ne, sai ya yi liyafar cin abinci ga Liu Bang. Fan Zeng a gaban Xiang Yu yake, sau da yawa ne ya gaya wa Xiang Yu cikin sirri da ya kashe Liu Bang, amma Xiang Yu bai yarda da wannan ba. Sai Fan Zeng ya sa babban janar mai suna Xiang Zhuang da ya yi rawa a gaban Liu Bang, amma ya rike da takobi a hannunsa, ashe yana son kashe Liu Bang. Da ganin haka, kawun Xiang Yu wato Xiang Bo ya tashi da sauri, shi ma ya yi rawa a gaban Liu Bang, nufinsa shi ne kare Liu Bang. Zhang Liang ya ga yadda ake cikin halin gaggawa, sai ya fita ya yi magana da Fan Kuai. Sai nan da nan, Fan Kuai ya rike da wata garkuwa da wani takobi, ya shiga cikin wurin da ake yin liyafa, ya zargi Xiang Yu cewa, "Liu Bang ya lashe sojojin Xianyang, amma bai nada masa shugaba ba, ya girka sojojinsa a garin Bashang, yana jiranka. Amma kana son kashe Liu Bang wanda yake kamar 'dan uwanka!". Da Xiang Yu ya ji haka, sai ya ji kunya. Liu Bang ya ce zai je bayangida, amma ya tsira zuwa sojojinsa. Da ganin haka, Fan Zeng ya ji fushi sosai, ya ce, "Xiang Yu ba za ka gudanar da sha'ani mai girma ba. Tabas ne Liu Bang zai zama shugaban duk kasa."

Wannan shi ne shahararren labarin "liyafar cin abinci a garin Hongmen" a tarihin kasar Sin. Xiang Yu yana tsammani shi mai karfi ne, sai ya amince da abubuwan da Liu Bang ya fada, wannan ya sa Liu Bang ya tsira. Bayan haka, yayin da Xiang Yu yake ta yaki a waje, Liu Bang ya shiga birnin Xianyang, sai sun fara yaki da juna. Ko da yake da farki dai sojojin da Xiang Yu ke shugabanta sun yi na Liu Bang yawa, amma ba ya son jin ra'ayin sauran mutane, sojojinsa kuma su kan kashe farar hula, su kan tayar da wuta a ko ina, ta yadda Xiang Yu ya rasa goyon baya da farar hula ke nuna masa. Amma Liu Bang ya ci gaba da yin abin kirki ga jama'a, ya yi amfani da wasu kwararru, da karshe dai ya sami rinjaye a gun fadar da yake yi da Xiang Yu. A shekaru 202 kafin bayyanuwar Annabi Isa, sojojin da Liu Bang ke shugabanta sun kewaye Xiang Yu a garin Gaixia inda Xiang Yu ya kashe kansa bisa tilas. Sai Liu Bang ya zama shugaba, ya kafa Daular Han: dinkuwar daular mulkin gargajiya ta biyu a tarihin kasar Sin.