Babi04: Harkokin Waje
2020-10-30 10:06:45 CRI
>>[Takaitacen bayani kan harkokin waje]
Takaitacen bayani kan harkokin waje
Jamhuriyar jama'ar Sin da ta kafu a shekarar 1949 ta bude wa kasar Sin sabon shafi wajen huldar da ke tsakaninta da kasashen waje.
Daga shekarar 1949 har zuwa karshen shekarun 1950 na karnin da ya wuce, kasar Sin ta kulla huldar diplomasiya a tsakaninta da kasar Tarayyar Soviet da sauran kasashe masu mulkin gurguzu dabam daban da kuma raya huldar sada zumunta da hadin guiwa a tsakaninsu. Bayan taron Bandung da aka yi tsakanin kasashen Asiya da Afrika a shekarar 1955 a kasar Indonesiya, wasu kasashen Asiya da Afrika sun kulla huldar diplomasiya da kasar Sin. Ya zuwa shekarar 1956, yawan kasashen da suka kulla huldar diplomasiya da kasar Sin sun kai 25.
Tun daga karshen shekarun 1950 zuwa karshen shekarun 1960, bi da bi ne kasar Sin ta daddale yarjejeniyoyin sada zumunta da yarjejeniyoyin yin hadin guiwar tattalin arziki da fasahohi tare da kasar Guinea da Ghana da Mali da Kongo da Tanzaniya da sauran kasashe, ta goyi bayan gwagwarmayar da kasar Angola da Guinea Bisau da Mozambique da Zimbabwe da Namibiya da sauran kasashe suka yi da makamai don neman mulkin kan kasa da gwagwarmayar da jama'ar Afrika ta kudu suka yi don yin adawa da bambancin kabila da fararen fata suka yi . sa'anan kuma bi da bi ne ta daidaita matsalolin iyakar kasa da aka bari a tarihi a tsakaninta da kasar Myanmar da Nepal da Mongoliya da Afghanistan , da kuma daddale yarjejeniya kan iyakar kasa a tsakaninsu, ta kuma daddale yarjejeniyar iyakar kasa da kasar Pakistan game da shiyyoyin tsaron kasa da jihar Xinjiang ta kasar Sin da kasar Pakistan suka sarrafa a hakika. Ta daidaita batu dangane da pasport na kasashe biyu da Sinawa ke zaune a kasar Indonesiya suka samu. Ya zuwa shekarar 1969, yawan kasashen da suka kulla huldar diplomasiya da kasar Sin ya kai 50.
Kasar Sin ta samu babban sauyi a wajen harkokin waje ne a watan Oktoba na shekarar 1971. A wancan lokaci, bisa goyon bayan da dimbin kasashe masu tasowa suka ba ta, babban taro na 26 na Majalisar Dinkin Duniya ya zartas da kuduri mai lamba 2758 bisa kuri'u masu rinjaye don mayar da dukkan halallen hakkin Jamhuriyar Jama'ar Sin a cikin Majalisar Dinkin Duniya, kuma nan da nan ne aka kori wakilan rukunin jam'iyyar Guomindang daga Majalisar Dinkin Duniya da dukkan hukumominta. Sa'anan kuma, kasar Sin ta kulla huldar diplomasiya da yawancin kasashen Yamma, saboda haka an bullo da babban tashe na karo na uku ga kasar Sin wajen kulla huldar diplomasiya da kasashen waje .
Tun daga karshen shekarun 1970 zuwa karshen shekarun 1980, bisa jagorancin tunanin Deng Xiaoping dangane da harkokin waje, kasar Sin ta yalwata huldar da ke tsakaninta da kasar Amurka da Japan da kasashen yammacin Turai yadda ya kamata, ta kuma kyautata huldar da ke tsakaninta da kasar Tarayyar Soviet, ta raya huldar da ke tsakaninta da kasashe masu tasowa daga dukkan fannoni. Ta kyautata da kuma yalwata huldar da ke tsakaninta da kasashen da ke kewayenta da dimbin kasashe masu tasowa. Don daidaita batun Hongkong da na Macao yadda ya kamata, ta hanyar shawarwari da ta yi da kasar Britaniya da Portugal kan harkokin waje, bi da bi ne kasar Sin da wadannan kasashen biyu sun bayar da hadadiyyar sanarwa a watan Disamta na shekarar 1984 da watan Afril na shekarar 1987, inda suka tabbatar da cewa, Gwamnatin Jamhuriyar jama'ar Sin za ta sake aiwatar da ikonta na mallakar Hongkong a ran 1 ga watan yuli na shekarar 1997 da kuma sake aiwatar da ikonta na mallakar Macao a ran 20 ga watan Disamba na shekarar 1999.
Tun daga shekarun 1990, rukunin shugabanni na zuri'a ta uku na kasar Sin da ke karkashin jagorancin Mr Jiang Zemin ya gado da kuma aiwatar da tunanin Deng Xiaoping dangane da harkokin waje da manufar harkokin waje ta rike mulkin kai ba tare da tsangwama ba cikin lumana bisa halin kagowa, kuma sun yi himmar raya huldar sada zumunta da hadin guiwa da ke tsakaninta da kasashe dabam daban na duniya bisa tushen ka'idoji biyar na yin zaman tare cikin lumana, kuma sun gaggauta kafa sabon tsarin siyasa da tattalin arziki na kasa da kasa cikin hadin guiwa. Bi da bi ne kasar Sin ta sake tabbatar da huldar diplomasiya da ke tsakaninta da kasar Indonesiya, ta kulla huldar diplomasiya da kasar Singapore da Brunei da Korea ta Kudu,sa'anan kuma ta sake mayar da huldar da ke tsakaninta da kasar Vietnam da Mongoliya yadda ya kamata.
A shekarar 1996, shugaban kasar Sin Mr Jiang Zemin ya kai ziyara a kasashe uku na kudancin Asiya, ta hanyar shawarwari, kasar Sin da kasar Indiya sun kulla huldar abokantaka mai amfani don fuskantar karni na 21, kasar Sin da kasar Pakistan sun kulla huldar abokantaka ta yin hadin guiwa daga dukkan fannoni don fuskantar karni na 21, kasar Sin da kasar Nepal sun kulla huldar abokantaka da ke tsakaninsu ta irin makwabtaka masu abuta da juna daga zuri'a zuwa zuri'a. Kasar Sin ta yalwata huldar da ke tsakaninta da kasashe na Asiya da Afrika da Latin Amurka da na Turai ta gabas da ta tsakiya. Sa'anan kuma huldar da ke tsakaninta da kasashen Afrika da ke kudancin Sahara ta kara ingantuwa da karfafuwa. Huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Latin Amurka ta kara samun ci gaba. Yawan kasashen Latin Amurka da suka kulla huldar diplomasiya da kasar Sin ya kara karuwa har zuwa 19. Wasu kasashen da ba su kulla huldar diplomasiya da kasar Sin ba har yanzu suna soma tunanin raya huldar da ke tsakaninsu da kasar Sin.
'Yan Adam sun shiga cikin sabon karni, muhimman alamu da aka yi su ne, an kafa bangarori da yawa a duniya, tsarin bai daya da duk duniya take aiwatarwa wajen tattalin arziki yana ta kara samun bunkasuwa, kasar Sin kasa ce mai tasowa da ke da mutane mafi yawa a duniya, kasar Sin ba za ta iya kebantar da ita daga duniya wajen samun bunkasuwa ba, hakan kuma duniya tana bukatar kasar Sin wajen samun bunkasuwa. Da sahihiyar zuciya ce kasar Sin ta yi fatan a kara inganta hadin guiwa da samun bunkasuwa gaba daya da ke tsakaninta da dukkan kasashe da jihohi bisa tushen ka'idoji biyar na yin zaman tare cikin lumana.
>>[ Manufar harkokin waje]
Manufar harkokin waje ta kasar Sin
Kasar Sin tana tsayawa tsayin daka tana aiwatar da manufar harkokin waje ta zaman lafiya na rike mulkin kai ba tare da tsangwama ba cikin lumana, babban makasudin aiwatar da manufar nan shi ne don kiyaye mulkin kan kasa da mallakar kan kasa da cikakken yankin kasa na kasar Sin, da kuma kago wani muhallin kasashen duniya mai kyau ga kasar Sin wajen bude wa kasashen waje kofa da yin gyare-gyare da zamanintar da kasa da kuma kiyaye zaman lafiyar duniya da sa kaimi ga samun bunkasuwa gaba daya. Muhimman abubuwa da aka tanada sun hada da:
A kodayaushe, tana aiwatar da ka'idar rike mulkin kai ba tare da tsangwama ba, kuma ba ta kulla kowane irin kawance da kowace babbar kasa ko rukunin kasashe, kuma ba ta shiga rukunin soja da gasar jan damara, ba ta kara habaka karfin soja ba.
Tana adawa da ra'ayin nuna fin karfi da kiyaye zaman lafiyar duniya da kuma tsayawa kan ra'ayin cewa, kasashe ko manya ko kanana, ko masu karfi ko marasa karfi ko masu fama da talauci ko masu wadata, dukkansu su ne mambobin da ke cikin gamayyar kasa da kasa bisa matsayin zaman daidai wa daida. Ya kamata kasa da kasa su daidaita rikici da gardama da ke tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari cikin lumana, bai kamata ba su yi wa juna karfin makamai ko yi wa juna kurari da karfin makamai, sa'anan kuma kada su yi shisshigi a cikin harkokin sauran kasashe bisa aron baki.
Tana yin himmar sa kaimi ga kafa sabon tsarin siyasa da tattalin arziki na kasa da kasa bisa adalci da dacewa. Ya kamata ka'idoji biyar na yin zaman tare cikin lumana da sauran ka'idojin huldar tsakanin kasa da kasa da aka amince da su a duniya su zama tushe na kafa sabon tsarin siyasa da tattalin arziki na kasa da kasa.
Bisa tushen girmama wa juna mallakar kan kasa da cikakken yankin kasa da rashin kai wa juna hari da rashin tsoma baki cikin harkokin gida na sauran kasashe da yin zaman daidai wa daida da samun moriyar juna da ka'idoji biyar na yin zaman tare cikin lumana, ta kulla huldar sada zumunta da hadin guiwa da dukkan kasashe.
Tana aiwatar da manufar bude wa kasashen waje kofa a dukkan fannoni, tana son yin cudanyar ciniki da hadin guiwar tatalin arziki da fasahohi da musanya kimiyya da al'adu da kasashe da jihohi dabam daban na duniya bisa tushen ka'idar zaman daidai wa daida da samun moriyar juna don sa kaimi ga samun wadatuwa gaba daya.
Ta shiga ayyukan harkokin waje a tsakanin bangarori da yawa ciki himma da kwazo , kuma ita ce tsayayyen karfi na kiyaye zaman lafiyar duniya da zaman karko na shiyya shiyya.
Tun daga ranar kafuwar sabuwar kasar Sin a cikin shekaru fiye da 50, ta hanyar kara abubuwa da yin daidaituwa da yalwatuwa, manufar harkokin waje ta kasar Sin ta kara samun kyautatuwa kuma ta kafa cikakkiyar al'adar harkokin waje da ke da tsarin musamman na kasar Sin. In ana hangen nesa, halin da ake ciki na samun bangarori da yawa a duniya da aiwatar da tsarin bai daya na raya tattalin arziki a duk duniya na ci gaba da samun bunkasuwa , huldar da ke tsakanin kasa da kasa tana nan tana kasancewa cikin daidaituwa mai zurfi. Neman zaman lafiya da hadin guiwa da kuma sa kaimi ga samun bunkasuwa muryar kirari iri daya ce da jama'ar kasashe dabam daban suka yi. A lokacin shiga cikin sabon karni, kasar Sin ta sami dama mai kyau a wani fanni, a wani fanni daban kuma ta gamu da kalubalen da aka yi mata wajen harkokin waje , kullum ya kamata mu natsu, kuma mu kara tunani kan abin damuwa da bala'i da tsaron lafiya da magance sauye sauye. Ya kamata mu ci gaba da fahimtar kuma mu sarrafa muhallin kasa da kasa da kasarmu take kasancewa a ciki bisa babban halin sauyawa da kasashen duniya ke ciki , muna amfani da damar da aka samar wa kasar Sin da kuma fuskantar kalubale don samun moriya da kawar da lahani. Dole ne mu ci gaba da zurfafawar nazari kan tunanin Deng Xiaoping dangane da harkokin waje, a karkashin jagorancin kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin wadda aboki Hu Jintao ke shugabanta, muna aiwatar da manufar harkokin waje ta zaman lafiya cikin mulkin kai ba tare da tsangwama ba, muna ta bude sabon shafi ga aikin diplomasiya don kara kyautata muhallin zaman lafiya na kasashen duniya ga aikin zamanintar da kasarmu mai mulkin gurguzu da kuma ba da gudumuwarmu ta kanmu ga sha'anin zaman lafiya da samun bunkasuwa na duniya.
>>[Huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen waje]
Huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka
A watan Fabrairu na shekarar 1972, shugaban kasar Amurka Mr Nixon ya kawo ziyara a kasar Sin, bagarori biyu Sin da Amurka sun bayar da hadadiyyar sanarwa a tsakaninsu wato "Sanarwar Shanghai", wannan ya alamanta cewa, halin da kasar Sin da kasar Amurka suke ciki na rashin yin cudanya a cikin shekaru fiye da 20 ya kawo karshe. A ran 16 ga watan Disamba na shekarar 1978, kasashen biyu Sin da Amurka sun bayar da hadadiyyar sanarwa game da kulla huldar diplomasiya a tsakanin Jamhuriyar Jama'ar Sin da The United States Of America. A ran 1 ga watan Janairu na shekarar 1979, kasar Sin da kasar Amurka sun kafa huldar diplomasiya bisa matsayin jakadanci. A ran 17 ga watan Augusta na shekarar 1982, kasar Sin da kasar Amurka sun bayar da sanarwar a ran 17 ga watan Augusta, inda suka tsai da kuduri na daidaita matsala game da Amurka ta sayar wa Taiwan makamai a mataki mataki har zuwa karshen samun daidaituwa.
A watan Janairu na shekarar 1984, firayim ministan kasar Sin ya kai ziyara a kasar Amurka, kuma shugaban kasar Amurka Mr Ronald Reagan ya kawo ziyara a kasar Sin. A watan Yuli na shekarar 1985, shugaban kasar Sin Mr Li Xiannian ya kai ziyara a kasar Amurka. Wannan ne karo na farko da shugaban kasar Sin ya kai ziyara a kasar Amurka.
A watan Janairu na shekarar 1998, ministan tsaron kasa na kasar Amurka Mr William Cohen ya kawo ziyara a kasar Sin, bangarorin biyu Sin da Amurka sun sa hannu kan yarjejeniya game da kafa tsarin yin tattaunawa kan kara inganta tsaron zaman lafiya da karfin soja a teku a tsakanin ma'aikatar tsaron kasa ta Sin da ta Amurka. Ran 25 ga watan Mayu, shugaba Jiang Zeming da shugaba Bill Clinton karo na farko ne suka yi magana kai tsaye ta hanyar wayar tarho cikin asiri a watan nan a tsakanin shugabannin kasashen biyu, kuma sun yi tattaunawa kan halin da ake ciki a kudancin Asiya da huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka.
Daga ran 25 ga watan Yuni zuwa ran 3 ga watan Yuli na shekarar 1998, bisa gayyatar shugaba Jiang Zemin ne, shugaban kasar Amurka Mr Bill Clinton ya kawo ziyarar aiki a kasar Sin. Shugaba Jiang Zemin da shugaba Bill Clinton sun yi shawarwari a tsakaninsu, bangarorin biyu sun yarda da kara karfafa yin tattaunawa da hadin guiwa a kan manyan matsalolin kasashen duniya a tsakanin kasashen biyu Sin da Amurka; Bangarorin nan biyu sun yarda da ci gaba da kokari tare don kara saurin dosawa gaba bisa manufar kafa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare mai amfani a tsakanin Sin da Amurka don fuskantar karni na 21. Bangarorin biyu sun tsai da cewa, ba za su harba wa juna makaman nukiliya na manyan tsare-tsare da kowanensu ya sarrafa su ba; Bangarorin biyu sun yarda da cewa, za su kara karfafa tattaunawa a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare a kan tattalin arziki da harkokin kudi don ba da gudumuwa mai yakini don sa kaimi ga raya tattalin arzikin duniya da harkokin kudi na kasa da kasa yadda ya kamata.
A ran 1 ga watan Janairu na shekarar 1999, Shugaba Jiang Zemin da shugaba Clinton sun aika wa juna wasikun taya murnar ranar cika shekaru 20 da kulla huldar diplomasiya a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka. Daga ran 6 zuwa ran 14 ga watan Afrilu na shekarar , firayim ministan kasar Sin Mr Zhu Rongji ya kai ziyarar aiki a kasar Amurka. Wannan ne karo na farko da firayim ministan kasar Sin ya kai ziyara a kasar Amurka a cikin shekaru 15 da suka wuce.
A ran 8 ga watan Mayu na shekarar 1999, da asuba da karfe 5 da minti 45 (Agogon birnin Beijing), Kungiyar Nato da ke karkashin shugabancin kasar Amurka ta harba wa ofishin jakadan kasar Sin da ke wakilci a kasar Yogoslaviya harsassai guda biyar na makamai masu linzami daga kusurwoyi dabam daban, nan take manema labaru na kasar Sin su uku suka mutu bisa sanadiyar nan a yayin da ma'aikatan ofishin fiye da 20 suka ji rauni, sa'anan kuma an rushe ginin ofishin sosai. Jama'ar kasar Sin sun yi fushi sosai da sosai saboda mugun aikin nan da kasar Amurka ta yi, shi ya sa an kawo tasiri ga huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka bisa wani mataki.
Ran 11 ga watan Satumba, shugaba Jiang Zemin da shugaba Clinton sun yi ganawa a tsakaninsu a lokacin da aka kira kwarya kwaryar taron shugabannin kungiyar hadin guiwar tattalin ariki ta Asiya da tekun Pasific a Auckland na kasar New Zealand, kuma sun sami sakamako mai yakini.
A shekarar 2000, cudanya da hadin guiwa da kasar Sin da kasar Amurka suka yi a fannoni masu yawa a tsakanin manyan shugabanni sai kara yawa suke yi. A ran 15 ga watan Disamba na wannan shekara, Majalisar Amurka ta zartas da dokar ware kudadde a dukkan fannoni, inda aka yi shirin ba da diyyar da yawanta ya kai kudin Amurka dolla miliyan 28 domin hasarar kayayyaki da ofishin jakadan kasar Sin da ke wakilci a kasar Yogoslaviya ya samu bisa sanadiyar farmakin da Amurka ta kai masa.
A shekarar 2001, ran 1 ga watan Afril da safe, wani jirgin saman yaki mai leken asiri kuma mai lamba EP-3 na Amurka yana leken asiri a sararin samaniya da ke haddin ruwa na kilomita 104 na kudu maso gabashin tsibirin Hainan na kasar Sin , ya yi karo kuma ya rushe wani jirgin sama mai lamba Qian-8 na bangaren kasar Sin wanda ya bi sawon jirgin Amurka don sa ido a kai, saboda haka Wang Wei ,matukin jirgi na kasar Sin ya rasa ransa. Bayan da jirgin sama na Amurka ya haddasa al'amarin nan, sai ya kutsa kai cikin sararin samaniya na kasar Sin ba tare da samun izni ba, sa'anan kuma ya sauka a filin jirgin sama na soja na Lingshui na tsibirin Hainan. A ran 11 ga watan Afrika, ministan harkokin waje na kasar Sin Mr Tang Jiaxuan ya karbi wasikar neman afuwa da wakili mai cikakken iko na gwamnatin Amurka kuma jakadan Amurka da ke wakilci a kasar Sin ya mika masa a madadin gwamnatin Amurka dangane da al'amarin da jirgin saman soja mai leken asiri na Amurka ya yi na yin karo da kuma rushe jirgin saman soja na kasar Sin.
A ran 11 ga watan Satumba, Jihar New York da Washington na kasar Amurka sun gamu da farmakin ta'adanci da aka yi da karfin tuwo, shi ya sa an sha babbar hasarar kayayyaki da kuma sa mutane da yawa suka mutu ko suka ji rauni . A ran 19 ga watan Oktoba, shugaba Jiang ya gana da shugaba George W.Bush a birnin Shanghai, inda suka yi musayan ra'ayoyinsu a kan huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka da nuna adawa da ta'addanci da sauran manyan matsaloli, kuma sun sami ra'ayi daya mai muhimmanci, gaba daya ne bangarorin biyu sun yarda da yin kokarin raya huldar hadin guiwa mai amfani a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka.
A shekarar 2002, huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka ta sha fitina, amma tana kasancewa cikin halin samun bunkasuwa da kyautatuwa daga dukkan manyan fannoni. Daga ran 21 zuwa ran 22 ga watan Fabrairu, bisa gayyatar da shugaba Jiang Zemin ya yi, shugaba W.Bush ya kawo ziyarar aiki a kasar Sin , shugabannin kasashen biyu sun sake ganawa, kuma sun kara zurfafa tattaunawa kan huldar da ke tsakanin bangarorin biyu da halin yanzu da kasa da kasa suke ciki, kuma gaba daya ne suka yarda da kara inganta tattaunawa da hadin guiwa a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka da kuma daidaita sabanin da ke tsakaninsu yadda ya kamata, kuma sun sa kaimi ga kara bunkasa huldar hadin guiwa mai amfani da ke tsakanin kasashen nan biyu cikin hadin guiwa. Shugaba Jiang ya karbi gayyatar da shugaba Bush ya yi masa, ya kuma kai ziyara a kasar Amurka a watan Oktoba kafin ya tafi kasar Mexico don halartar taron yin hadin guiwar tattalin arziki a tsakanin Asiya da tekun Pasific. Shugaba Jiang ya karfafa wa shugaba Bush muhimmancin daidaita batun Taiwan yadda ya kamata ga raya huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka. Shugaba Bush ya sake jaddada cewa, kasar Amurka tana aiwatar da manufar Sin daya tak a duniya, kuma ta yi biyayya ga hadadiyyar sanarwa guda uku a tsakanin Sin da Amurka, wannan manufar kullum ce da gwamnatin Amurka take aiwatarwa cikin dogon lokaci, ba za a sauya ta ba.
Huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Japan
A wajen siyasa, a ran 2 ga watan Oktoba na shekarar 1971, kasar Sin ta gabatar da ka'idoji guda uku dangane da sake tabbatar da huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Japan, wato Jamhuriyar Jama'ar Sin ita ce gwamnati ta halal daya tak da ke wakilcin kasar Sin ba; Taiwan wani kashi ne da ba za a iya belle shi daga Jamhuriyar Jama'ar Sin; Yarjejeniyoyi da aka daddale tsakanin kasar Japan da Chiang Kaishek ba su bisa doka ba, kuma ba su da amfani, dole ne a soke su. A ran 25 ga watan Satumba na shekarar 1972, firayim minista Tanaka Kakuei ya kawo ziyara a kasar Sin, ran 29 ga wannan wata, gwamnatin Sin da ta Japan sun bayar da hadadiyyar sanarwa, daga nan kasar Sin da kasar Japan sun sake tabbatar da huldar diplomasiya da ke tsakaninsu.
Yanzu, huldar da ke tsakanin kasashen nan biyu tana kasancewa cikin halin samun yalwatuwa daga dukkan fannoni, an sami sakamako mai yakini wajen yin hadin guiwar hakikanin aiki a fannoni dabam daban. Amma a wani fanni daban kuma, firayim ministan Japan Koizumi Junichiro ya halarci shagalin tunawa da fursunonin yaki a Haikalin Yasukuni sau da yawa a jere, wannan ya zama babban batun da ya ba da tasiri ga huldar siyasa da ke tsakanin kasar Sin da kasar Japan a halin yanzu.
A wajen tattalin arziki, kasar Sin da kasar Japan kowacensu ta mayar da juna bisa matsayin abokiyar ciniki mai muhimmanci . A cikin shekaru goma a jere, kasar Japan ta zama babbar abokiyar ciniki ta kasar Sin, kasar Sin ta zama babbar kasa ta biyu da kasar Japan ta ke ciniki da ita a duniya da kuma babbar kasuwa ta biyu ta fitar da kayayyakinta zuwa kasashen waje.
Wajen yin hadin guiwar kimiyya da ba da ilmi da al'adu da kiwon lafiya, bayan da kasar Sin da kasar Japan suka tabbatar da huldar diplomasiya a tsakaninsu yadda ya kamata, bangarorin biyu sun kafa huldar yin hadin guiwar kimiyya da fasahohi a tsakanin gwamnatocinsu, kuma sun daddale "Yarjejeniyar yin hadin guiwar kimiyya da fasahohi a tsakanin kasar Sin da kasar Japan" a watan Mayu na shekarar 1980. Sa'anan kuma, musanyar kimiyya da fasahohi da yin hadin guiwa a tsakanin kasashen nan biyu sun kara yalwatuwa da saurin gaske, matakansu sai kara habakawa suke yi, kuma an bayyana halin da ake ciki na shigar da jami'an gwamnati da jama'a gaba daya ta hanyoyi dabam daban.
Ran 6 ga watan Disamba na shekarar 1979, kasashen biyu Sin da Japan sun sa hannu kan "Yarjejeniyar musanyar al'adu a tsakaninsu", inda suka tabbatar da cewa, za su kara yin musanya a tsakaninsu wajen al'adu da ba da ilmi da kara wa juna ilmi da wasannin motsa jiki da sauran fannoni. A shekarar 2002, gwamnatocin kasashen biyu sun tsai da kuduri na shirya "Shekarar al'adun kasar Sin" da "Shekarar al'adun kasar Japan" Ban da wannan kuma, bangarorin biyu sun kuma shirya "Shagalin yanayin zafi na tsakanin samari da yara na kasar Sin da Japan da Korea ta kudu" da "Gasar da ke tsakanin kasashen nan uku kan ilmin TV da dandalin tattalin arziki na Sin da Japan" da dai sauransu.
Yanzu, wajen huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Japan, da akwai matsaloli da yawa da suka jawo hankulan mutane wadanda kuma ya kamata a daidaita su cikin tsanaki:
Da farko, matsalar yadda za a fahimci abubuwan da suka faru a tarihi. Wannan batun siyasa ne da ya jawo hankulan mutane wajen huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Japan .Tun daga shekarar 2001 har zuwa yanzu, an yi ta samun matsaloli saboda kasar Japan ta yi biris da hakikanan abubuwan da suka faru a tarihi wajen gyara littattafan karatu na tarihi da kuma gyara tarihin da ya danganci yadda japan ta kawo wa kasar Sin hari, da kuma batun ziyarar da firayim ministan kasar Japan Koizumi Junichiro ya yi don shiga shagalin tunawa da fursunonin yaki a Haikalin Yasukuni, wannan ya kawo fitina mai tsanani ga huldar da ke tsakanin kasar Sin da Japan.
Na biyu, matsalar Taiwan. Matsayin da bangaren Sin ya dauka kan huldar da ke tsakanin Japan da Taiwan yana bayyanuwa sosai, wato ba ya nuna bambancin ra'ayi kan cudanyar da ke tsakanin jama'ar Japan da Taiwan , amma ya tsaya tsayin daka ya nuna kiyayya ga cudanyar da ke tsakanin hukumomin gwamnati ta kowace hanya , da kuma kago Sin biyu ko Sin daya Taiwan daya, ya nemi bangaren Japan da ya yi alkawari a bayyane cewa, Taiwan ba ta cikin da'irar yin hadin guiwar tsaron kai a tsakanin kasar Japan da kasar Amurka .
Na uku, matsalar tsibirin Diaoyu. Tsibirorin Diaoyu suna haddin ruwa na gabashin teku da ke nisa da arewa maso gabashin birnin Jilong na lardin Taiwan na kasar Sin da mil 92 na teku, su ne ke karkashin tsibirin Taiwan, suna kunshe da tsibirin Diaoyu da karamin tsibirin Huangwei da karamin tsibirin Chiwei da karamin tsibirin kudu da na arewa da sauran manyan duwatsu. Tsibirorin Diaoyu sun zama yankunan kasar Sin tun fil azal, su da Taiwan dukkansu wani kashi ne da ba za a iya raba su daga babban yankin kasar Sin ba. Kasar Sin tana da mallakar kai da ba a iya gardama a kai ba kan tsibirorin Diaoyu da haddin ruwa da ke kusa da su.
Matsayin nan na kasar Sin na da cikakkun shaidu na tarihi da na dokokin shari'a . A watan Disamba na shekarar 1943, kasar Sin da kasar Amurka da kasar Britaniya sun bayar da "Sanarwar Alkahira", inda aka tsai da cewa, Kasar Japan za ta mayar wa kasar Sin yankunan da ke kunshe da shiyyar arewa maso gabashin kasar Sin da Taiwan da tsibirorin Penghu. A shekarar 1945, "Sanarwar Potsdam" ta tsai da cewa, dole ne a aiwatar da sharudan "Sanarwar Alkahira". A watan Augusta na wannan shekara, kasar Japan ta amince da "Sanarwar Potsdam" kuma ta ba da kai ba tare da kowane sharadi ba, wannan ya bayyana cewa, kasar Japan za ta mayar wa kasar Sin Taiwan da tsibirin Diaoyu da sauran tsibirori da ke karkashinsa.
Na hudu, matsalar yin hadin guiwar tsaron kai a tsakanin kasar Japan da Amurka. A shekarar 1996, kasar Japan da kasar Amurka sun bayar da "Hadadiyyar sanarwar yin hadin guiwar tsaron kai" , kuma bisa sanarwar nan ne, suka soma gyara "ka'idar yin hadin guiwar tsaron lafiya da aka tsara a shekarar 1978. A watan Satumba na shekarar 1997, kasar Japan da kasar Amurka sun soma tabbatar da sabuwar ka'idar yin hadin guiwar tsaron lafiya. A ran 24 ga watan Mayu na shekarar da muke ciki, majalisar dokoki ta kasar Japan ta dudduba kuma ta zartas da sabbin daftarin kudurai da suke shafar ka'idar tsaron zaman lafiya a tsakanin Japan da Amurka., wannan ya alamanta cewa, sabon tsarin yin hadin guiwar tsaron lafiya da kasar Japan da Amurka suka karfafa a kai ya kafu. Game da wannan, wani muhimmin abu da kasar Sin ta mai da hankali a kai shi ne, na farko, matsalar da ta shafi Taiwan, na biyu manufar soja ta kasar Japan. Ya zuwa yanzu, ta hanyoyi dabam daban, kasar Sin ta bayyana matsayinta da abin ya shafa kuma ta mai da hankali sosai a kai.
Na biyar, matsalar ba da diyyar yaki. A lokacin da aka yi shawarwari kan sake tabbatar da huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Japan a shekarar 1972, gwamnatin Japan ta bayyana sosai cewa, ta yi bakin ciki da jin babban hakkin da ke wuyanta sosai saboda yakin da ta tayar wa jama'ar kasar Sin kuma ta nemi afuwa a kan wannan. Bisa sharadin nan, bisa babbar moriyar kasar, gwamnatin kasar Sin ta tsai da kuduri na yin watsi da bukatarta ta neman biyan diyyar yaki daga wajen Japan, kuma an rubuta wannan a cikin "Hadadiyyar sanarwa da ke tsakanin kasar Sin da kasar Japan" wadda kasashen nan biyu suka daddale a shekarar 1972. A shekarar 1978, zama na uku na zaunannen kwamiti na biyar na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya zartas da "Yarjejeniyar zaman lafiya da sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasar Japan", wannan ya sake tabbatar da kudurin yin watsi da bukatar neman biyan diyyar yaki daga Japan ta hanyar takardun dokokin shari'a.
Na shida, matsala game da makamai masu guba da kasar Japan ta bari a kasar Sin. A lokacin da kasar Japan ta kai wa kasar Sin hari, kiri da muzu ne ta keta yarjejeniyar kasa da kasa, ta yi amfani da makamai masu guba, ta sa jama'a farar hula da sojoji da yawa suka mutu ko suka ji rauni bisa sanadiyar shan guba . Bayan da sojojin Japan suka ci hasara a cikin yaki, sai suka binne ko kuma bar makamai masu guba da yawa a wurin da suke girke. Ya zuwa yanzu, a wurare fiye da 30 na larduna da manyan birane da jihohi masu ikon aiwatar da harkokinsu fiye da goma na kasar Sin , an gano makamai masu guba da kasar Japan ta bari. Dayake wadanda makamai masu guba sun lalace sosai saboda cikas da iska da ruwan sama suka kawo musu a cikin rabin karnin da ya wuce, shi ya sa ba zato ba tsammani suna kan fitar da iska mai guba, wannan ya kawo kurari mai tsanani ga rayukan jama'ar Sin da dukiyoyinsu da muhallin hallita. A karshen shekaru 1980 na karnin da ya wuce, gwamnatin kasar Sin ta yi ma'amala da gwamnatin Japan a hukunce, inda ta nemi gwamnatin Japan da ta daidaita matsalar nan. A ran 30 ga watan Yuli na shekarar 1999, a birnin Beijing ,gwamnatin kasar Sin da ta Japan sun daddale "Takardar fahimtar juna game da rushe makamai masu guba da kasar Japan ta bari a cikin kasar Sin . A cikin takardar nan, gwamnatin Japan ta bayyana cewa, za ta tuna muhimman abubuwa da ake tanade a cikin "Hadadiyyar sanarwa da ke tsakanin kasar Sin da Japan" da "Yarjejeniyar zaman lafiya da sada zumunta a tsakanin Sin da Japan" sosai da sosai, ta fahimci abin gaggawa da za ta yi ga daidaita wannan matsalar , kuma ta yi alkawarin aiwatar da hakkinta na sa kai na rushe makamai masu guda da aka tanada a cikin "Yarjejeniyar hana makamai masu guba".Yanzu, sassan da abin ya shafa na gwamnatocin kasashen nan biyu suna nan suna yin shawarwari a kan yadda za a yi hakikanin aiki don lalata makamai masu guba da Japan ta bari tun da wurwuri bisa daftarin takardar nan.
Huldar da ke tsakanin kasar Sin da Rasha
Ran 2 ga watan Oktoba na shekarar 1949, kasar Sin da tarayyar Soviet sun kulla huldar diplomasiya a tsakaninsu. A watan Augusta na shekarar 1991, Tarayyar Soviet ta wargaje, ran 27 ga watan Disamba, kasar Sin da kasar Rasha sun sa hannu kan muhimman bayanonin da aka tanada kan shawarwarin da ke tsakanin kasashen biyu, kuma sun daidaita matsalolin da suka shafi huldar diplomasiya da ke tsakanin kasar Sin da tsohuwar Tarayyar Soviet. A shekarar 2001, huldar abokantaka ta taimaka wa juna tsakanin kasashen nan biyu bisa manyan tsare-tsare ta sami bunkasuwa kuma ta kai wani sabon matsayi. Amincewa da bangarorin biyu suka yi wa juna wajen siyasa sai kara karfi take yi, kuma manyan shugabanninsu sun kara yin cudanya a tsakaninsu. A cikin shekara daya, shugaba Jiang Zemin da shugaba Vladimir Putin sun gana da juna har sau uku da kuma buga wa juna wayar tarho har sau 6. Yarjejeniyar yin hadin guiwar sada zumunta a tsakanin kasashen biyu da ke makwabta da juna kuma abuta da juna wadda shugabannin kasashen biyu suka sa hannu a kai a shekarar 2001 da kuma hadadiyyar sanarwa da suka bayar sun tabbatar da tunanin sada zumunta a tsakanin kasashen biyu da jama'arsu daga zuri'a zuwa zuri'a da kuma har abada ba tare da yin adawa da juna ba ta hanyar dokokin shari'a.
Daga ran 26 zuwa ran 28 ga watan Mayu na shekarar 2003, shugaban kasar Sin Mr Hu Jintao ya kai ziyarar aiki a kasar Rasha.
A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, huldar tattalin arziki da ciniki da hadin guiwar tattalin arziki da fasahohi a tsakanin bangarorin biyu sai kara yawa suke yi a kowace rana. Sa' anan kuma musanya da hadin guiwa da ke tsakanin kasashen biyu wajen al'adu da kimiyya da fasaha da ba da ilmi da sauran fannoni su ma sun kara yawa , a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kungiyar wake-wake da raye-raye ta kasar Sin da ta jihar Xinjiang da kungiyar wakilan mawallafa ta kasar Sin da kungiyar wasan Ballet ta fadar Kremlin da kungiyar wasan ballet na tsohon salo na Moscow da kungiyar kidan Orchestral ta St.Petersburg da kungiyar kidan symphony ta gwamnatin kasa ta Moscow da sauran kungiyoyin 'yan wasannin fasaha da al'adu na kasashen biyu sun kai wa juna ziyara.
Game da matsalar iyakar kasa. Yawan tsawon iyakar kasa da ke tsakanin Sin da Rasha na da kilomita 4370. Ya kasance da matsalar iyakar kasa da aka bari a tarihi a tsakanin kasashen biyu. Yanzu, bisa tushen yarjejeniyoyin da abin ya shafa da ke tsakanin kasashen biyu kan matsalar iyakar kasa da kuma ka'idojin kasa da kasa da kowa ya amince da su da manufar yin shawarwari bisa zaman daidai wa daida da yin hakuri da juna, bangarorin biyu sun yi shawarwari a cikin shekaru da yawa, sa'anan kuma sun tabbatar da layin iyakar kasa na kashi 90 cikin dari.
Yanzu, ba a tabbatar da layin iyakar kasa da ke tsibirin Hexiazi da wani wuri wato wurare guda biyu da ke gabashin iyakar kasa da ke tsakanin kasar Sin da kasar Rasha, bisa tushen adalci da zaman daidai wa daida da yin hakuri da juna , bangarorin biyu za su daidaita matsalolin da har yanzu ba su daidaita ba a kan iyakar kasa tun da wurwuri.
>>[Kungiyoyin Duniya da Kasar Sin]
Kungiyar Asean da kasar Sin
Kungiyar Asean ta fito daga kawancen kudu maso gabashin Asiya da aka kafa shi a ran 31 ga watan Yuli na shekarar 1961. A watan Augusta na shekarar 1967, kasar Indonesiya da Thailand da Singapore da Philippines da Malasiya wato kasashe biyar ke nan sun kira taro a birnin Bangkok, sun kuma bayar da sanarwar Bangkok, sun yi shelar kafuwar kawancen kasashen kudu maso gabashin Asiya, a takaice dai ana kiranta kungiyar Asean. Sa'anan kuma, kasar Malasiya da Thailand da Philippines sun kira taron a birnin Kuala Lumpur bisa matsayin minista, inda suka tsai da kuduri cewa, kawancen kasashen kudu maso gabashin Asiya ya mayar da gurbin kawancen kudu maso gabashin Asiya.
Manufarta:
Bisa halin yin zaman daidai wa daida, su yi kokarin tare don sa kaimi ga samun karuwar tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al'umma da raya al'adu a shiyyar da suke zama.
Yin biyayya ga adalci da ka'idojin kasa da kasa da tsarin ka'idojin Majalisar Dinkin Duniya don ciyar da zaman lafiya da zaman karko na shiyyar nan gaba.
Sa kaimi ga yin hadin guiwa da samar wa juna taimako wajen tattalin arziki da zamantakewar al'umma da al'adu da fasahohi da kimiyya da sauransu.
Samar wa juna taimako wajen ba da ilmi da ba da horo ga sana'o'i da fasahohi da harkokin hukumomi da gine-ginen yin nazari da sauransu.
kara yin hadin guiwa mai amfani wajen yin amfani da sha'anin gona da masana'antu da kara habaka ciniki da kyautata sufuri da zirga-zirgan ababan hawa da kuma daga matsayin zaman rayuwar jama'a.
Sa kaimi ga kara wa juna ilmi a kan matsalolin kudu maso gabashin Asiya.
Ci gaba da yin hadin guiwa sosai da samun moriyar juna da kungiyoyin kasa da kasa da na shiyya shiyya wadanda suke da manufofi da buri da suke daya da na kungiyar, kuma neman hanyar da za a bi wajen kara karfin hadin guiwar nan.
Mambobinta:
Kungiyar Asean tana da kasashe goma da suka hada da kasar Brunei, Kampuchea, Indonesiya, Laos, Malasiya, Myanmar, Philippines, Singapore, Thailand da Vietnam .
Huldar da ke tsakaninta da kasar Sin:
Kasar Sin ta riga ta kulla huldar diplomasiya a tsakaninta da dukkan kasashe mambobin kungiyar Asean, kuma ta zama kasar abokantaka da yin tattaunawa da kungiyar Asean daga dukkan fannoni.
Kungiyar yin hadin guiwa ta Shanghai da kasar Sin
A watan Yuni na shekarar 2001,shugabannin kasar Sin da Rasha da Kazakhstan da Kirghiziastan da Tajikistan da Uzbekstan wato kasashe 6 ke nan sun yi shawarwari a birnin Shanghai, kuma sun sa hannu kan "Sanarwar kafa kungiyar yin hadin guiwa ta Shanghai". Sun kuma shelanta cewa, kafa sabuwar kungiyar yin hadin guiwa a tsakanin bangarori da yawa a shiyya shiyya bisa tushen tsarin kasashe biyar na Shanghai, wato kungiyar yin hadin guiwa ta Shanghai. Manufar kungiyar nan ita ce haka: kara inganta amincewar juna da zumuncin da ke tsakanin kasashen da ke makwabtaka da juna da kuma abuta da juna a tsakanin kasashe mambobin kungiyar , himmantar da kasashe mambobi dabam daban da ke cikin kungiyar wajen yin hadin guiwa mai amfani a fannin siyasa da tattalin arziki da ciniki da kimiyya da fasahohi da al'adu da ba da ilmi da makamashi da tafiye-tafiye da kiyaye muhalli da sauransu, Gaba daya ne suka yi yunkurin kiyaye da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da zaman karko na duniya da na shiyya shiyya, kafa sabon tsarin siyasa da tattalin arziki na kasa da kasa bisa dimokuradiya da adalci da dacewa. Bangarori dabam daban sun tsai da kudurin kafa sakatariyar kungiyar a nan birnin Beijing.
Bisa matsayin daya daga cikin wadanda suka ba da shawarar kafa kungiyar hadin guiwa ta Shanghai na farko da kuma matsayinta na mai taimakawa wajen ciyar da ita gaba ba tare da kasala ba, kasar Sin ta yi himmantu wajen shiga dukkan aikace-aikacen da aka shirya bisa tsarin kungiyar, bugu da kari kuma ta gabatar da ra'ayoyi da ka'idoji masu amfani da yawa don raya kungiyar da kuma kara girmarta, kuma ta ba da gudumowa mai muhimmanci sosai.
Majalisar Dinkin Duniya da kasar Sin
A ran 25 ga watan Afril na shekarar 1945, wakilai da suka zo daga kasashe 50 sun kira taron Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kasa da kasa a birnin San Fransisco na kasar Amurka. Ran 25 ga watan Yuni, an zartas da tsarin ka'idojin Majalisar Dinkin Duniya. Ran 26 ga wannan wata, bayan da kasar Sin da kasar Faransa da kasar Tarayyar Soviet da Britaniya da Amurka da sauran yawancin kasashen da suka sa hannu a kai suka mika takardar ba da izini, sai tsarin nan ya fara aiki nan da nan, Majalisar Dinkin Duniya ta kafu. A shekarar 1947, Babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya tsai da kuduri cewa, ran 24 ga watan Oktoba rana ce ta Majalisar Dinkin Duniya.
Manufar Majalisar Dinkin duniya ita ce haka: kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali na kasa da kasa; raya huldar sada zumunta a tsakanin kasa da kasa bisa tushen girmama hakkin jama'ar kasashe dabam daban na yin zaman daidai wa daida da ka'idar yanke shawara kan harkokinsu na kansu; da yin hadin guiwa a tsakanin kasa da kasa ta yadda za a iya daidaita matsalolin da suke jibintar tattalin arziki da zamantakewar al'umma da al'adu da jinkai a tsakanin kasa da kasa, kuma sa kaimi ga girmama hakkin duk 'Yan Adam da walawarsu. Ya zuwa watan Satumba na shekarar 2002, Majalisar Dinkin Duniya tana da kasashe mambobi da yawansu ya kai 191, ciki har da kasashe 49 da suka fara kafa Majalisar. Babbar hedkwatar Majalisar tana birnin New York na kasar Amurka, kuma an kafa hukumominta a birnin Geneva na kasar Switzerland da birnin Viena na kasar Austria da birnin Narobi na kasar Kenya da birnin Bangkok na kasar Thailand.
Kasar Sin babbar kasa ce mai tasowa, kuma kasa ce ta din din din da ke cikin kwamitin sulhu, kullum tana tsayawa kan ka'idoji da nuna adalci a cikin harkokin kasa da kasa, tana da matsayin musamman mai muhimmanci a dakalin Majalisar Dinkin Duniya da na kasa da kasa. Yanzu, amfani da Majalisar Dinkin Duniya za ta ba da ga gaggauta kafa sabon tsarin siyasa da tattalin arziki na kasa da kasa bisa adalci da dacewa ya zama muhimmin abu ga gamayyar kasa da kasa da suke mai da hankali a kai. Ra'ayin kasar Sin game da kafa sabon tsarin siyasa da tattalin arziki na tsakanin kasa da kasa da kiyaye zaman lafiya da sa kaimi ga samun bunkasuwa da yin adawa da ra'ayin nuna fin karfi ya karfafa hadin guiwa da daidaituwa a tsakanin kasashen din din din biyar da ke cikin Majalisar Dinkin Duniya ta yadda za a ba da taimako ga samun zaman lafiya da bunkasuwa a duniya.
Kungiyar hadin guiwar tattalin arziki
ta kasashen Asiya da tekun Pasific da kasar Sin
A watan Janairu na shekarar 1989, a lokacin da firayim ministan kasar Australiya Mr.Hawk ya kai ziyara a kasar Korea ta kudu, ya gabatar da "Shawarar Seoul" , inda ya ba da shawarar kiran taron shiyyar Asiya da tekun Pasific bisa matsayin minista don yin tattaunawa kan yadda za a kara inganta hadin guiwar tattalin arziki. Ta hanyar yin shawarwari da kasashen da abin ya shafa, a birnin Canberra, hedkwatar kasar Australiya, kasar Australiya da Amurka da Japan da Korea ta kudu da New Zealand da Canada da kasashe 6 na tsohon kawancen Asean sun kira taron farko na kungiyar yin hadin guiwar tattalin arziki a tsakanin shiyyar Asiya da tekun Pasific bisa matsayin minista, daga nan kungiyar APEC ta kafu.
A watan Nuwamba na shekarar 1991, a gun taro na uku na kungiyar APEC da aka kira a birnin Seoul bisa matsayin minista, an zartas da "Sanarwar Seoul", inda aka tabbatar da manufofi da buri na kungiyar, wato kiyaye karuwa da yalwatuwar tattalin arziki domin moriya daya na jama'ar wurin ; Sa kaimi ga yin dogaro da juna a tsakanin mambobin kungiyar a fannin tattalin arziki; Kara karfafa tsarin yin ciniki a tsakanin bangarori masu yawa wanda ke budewa sauran kasashe kofa; rage katangogi da aka gitta wajen yin ciniki da zuba jari a shiyya shiyya.
Kungiyar tana da mambobi 21.
Huldar da ke tsakaninta da kasar Sin:
Tun daga shekarar 1991 da kasar Sin ta shiga cikin kungiyar APEC, ta halarci aikace-aikace dabam daban da kungiyar ta shirya cikin himma da kwazo, wannan ya kago muhalli mai kyau daga waje ga kasar Sin wajen yin gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa, kuma ya sa kaimi sosai ga yalwata huldar bangarori biyu da ke tsakanin kasar Sin da mambobin kungiyar da abin ya shafa. Tun daga shekarar 1993, a kowace shekara, shugaban kasar Sin ya kan halarci kwarya kwaryar taron shugabannin kungiyar, kuma ya gabatar da ra'ayi da matsayin ka'ida na kasar Sin a daidai da batutuwan da aka gabatar a gun taron, ta kuma ba da gudumuwa mai amfani kuma mai yakini ga samun nasarar kiran taruruka. A shekarar 2001, kasar Sin ta yi nasarar shirya kwarya kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC a birnin Shanghai.
Kungiyar ciniki ta duniya wato WTO da kasar Sin
A gun taron da aka kira kan babbar yarjejeniyar kwastan da ciniki wato GATT bisa matsayin minista a watan Afril na shekarar 1994 a birnin Marrakesh na kasar Morocco, an tsai da kudurin kafa kungiyar ciniki ta duniya. A ran 1 ga watan Janairu na shekarar 1995, kungiyar ciniki ta duniya wato kungiyar WTO ta kafu. Babbar manufar kungiyar ita ce sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki da ciniki ta yadda za a kara daga matsayin zaman rayuwa da ba da tabbaci ga samar da cikakkiyar damar samun aikin yi da kuma ba da tabbaci ga kara samun karuwar hakikanan kudadden shiga da biyan bukatu mai amfani da ake yi . Bisa burin samun ci gaba mai dorewa , ya kamata a yi amfani da albarkatan duniya yadda ya kamata da kara habaka aikin fitar da kayayyaki da hajjoji da na ba da hidima; daddale yarjejeniyar samar wa juna gatanci da moriyar juna; Rage da kuma kawar da harajin kwastan da sauran katanga da aka gitta ga ciniki da kuma kauda bambancin gatanci a cikin cinikin da ake yi tsakanin kasa da kasa. Yawan mambobin kungiyar ya kai 144, hedkwatarta yana birnin Geneva.
Tun daga shekarar 1986 da kasar Sin ta gabatar da bukatarta ta mayar da matsayinta na uwar kasar da ta daddale babbar yarjejeniyar kwastan da ciniki wato GATT, kasar Sin ta yi kokari ba tare da kasala ba don neman shiga cikin yarjejeniyar kwastan da ciniki wato kungiyar ciniki ta duniya. Daga watan Janairu zuwa watan Satumba na shekarar 2001, kungiyar aiki ta kasar Sin ta kungiyar ciniki ta duniya ta kira taro har sau hudu, kuma ta kammala shawarwarin da ke tsakanin bangarori da yawa kan shigar da kasar Sin cikin kungiyar ciniki ta duniya da kuma zartas da takardun dokokin shari'a game da shigar da kasar Sin cikin kungiyar. Daga ran 9 zuwa ran 14 ga watan Nuwamba na wannan shekara, an kira taro na hudu na kungiyar ciniki ta duniya bisa matsayin minista a Doha, hedkwatar kasar Qatar, Ministan tattalin arziki da cinikin waje na kasar Sin Mr Shi Guangsheng ya ja ragamar kungiyar don halartar taron, ran 11 ga wannan wata, kasar Sin ta sa hannu kan yarjejeniyar shigarta cikin kungiyar. Daga ran 19 zuwa ran 20 ga watan Disamba na shekarar nan, bisa matsayinta na mambar kungiyar, kasar Sin ta shiga cikin babbar majalisar kungiyar WTO.
>>[Ministocin Kasar Sin]
Zhou Enlai
Zhou Enlai, ya zama ministan harkokin waje na kasar Sin daga shekarar 1949 har zuwa shekarar 1958.
Zhou Enlai shi ne babban dan juyin juya hali da masanin siyasa da na soja da na harkokin waje na rukunin talakawa, sa'anan kuma yana daya daga cikin manyan shugabannin Jam'iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin da Jamhuriyar Jama'ar Sin , kuma yana daya daga cikin wadanda suka soma kafa runduanr sojan suncin kai ta jama'ar kasar Sin. Garinsa yana birnin Shaoxing na lardin Zejiang, an haife shi a ran 5 ga watan Maris na shekarar 1898 a birnin Huai'an na lardin Jiangsu. Ya bar duniya a watan Janairu na shekarar 1976 a birnin Beijing.
Zhou Enlai ya halarci aikin tsara manyan manufofin harkokin waje na kasar Sin da yawa da kuma shi kansa ya aiwatar da su. A shekarar 1954, ya halarci taron Geneva. A gun taron , an daidaita batun Indochina, kuma ya sa gamayyar kasa da kasa ta amince da 'yancin kai da kasar Vietnam (ban da kudancinta) da Laos da Kampuchea wato kasashe uku ke nan suka samu. A madaddin kasar Sin, ya gabatar da shawarar kafa ka'idoji biyar na yin zaman tare cikin lumana, wadda ta zama ka'idar huldar da ke tsakanin kasa da kasa. A shekarar 1955, a gun taron Bandung da aka kira a kasar Indonesiya a tsakanin kasashe 29 na Asiya d Afrika , ya tsaya tsayin daka kan ra'ayin yin zaman tare cikin lumana da yin adawa da mulkin mallaka da gabatar da shawarar neman ra'ayi daya tare da kasancewar sabani da kuma yin shawarwari cikin hadin guiwa. Bi da bi ne ya kai ziyara a kasashe fiye da goma na Turai da Asiya da Afrika, kuma ya yi marhabin da shugabanni da mutane da yawa masu abuta da mu da suka zo daga kasashe dabam daban na duniya, wannan ya kara dankon zumuncin da ke tsakanin jama'ar kasar Sin da jama'ar duniya.
Chen Yi
Chen Yi ya zama ministan harkokin waje na kasar Sin daga shekarar 1958 zuwa shekarar 1972.
Chen Yi yana daya daga cikin wadanda suka soma kafa rundunar sojan suncin kai ta jama'ar kasar Sin, shi masanin harkokin soja ne, kuma mashal na Jamhuriyar jama'ar Sin. Bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, bi da bi ne ya dau mukamin mataimakin firayim ministan kasar Sin, kuma ministan harkokin waje da mataimakin shugaban kwamitin soja na tsakiya da sauran mukamai.
Daga shekarar 1958, bisa matsayinsa na mataimakin firayim minista kuma ministan harkokin waje ne ya aiwatar da tunani da manufa na Mao Zedong da Zhou Enlai kan harkokin waje cikin himma da kwazo, kuma ya halarci aikin tsara ka'idojin manyan tsare-tsare na harkokin waje na kasar Sin na dogon lokaci, sa'annan kuma ya taimaka wa Zhou Enlai wajen halartar manyan aikace-aikacen harkokin waje a jere. A watan Oktoba na shekarar 1952, bisa matsayin mamban kungiyar wakilan Jam'iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin, ya hallarci babban taro na 19 na wakilan Jam'iyyar Kwaminis Ta Tarayyar Soviet, ya gana da Stalin. A watan Oktoba na shekarar 1954, ya ja ragamar kungiyar wakilan jam'iyyar kwaminis da gwamnati ta kasar Sin zuwa Jamhuriyar dimokuradiya ta Jamus don yin ziyara, a wannan gami kuma, ya ziyarci kasar Poland. A watan Afril na shekarar 1955, bisa matsayinsa na babban mai ba da taimako ga Zhou Enlai da mamban kungiyar wakilan gwamnatin kasar Sin ne , ya je Bandung don halartar taron Asiya da Afrika. A watan Fabrairu na shekarar 1958, bisa matsayinsa na mataimakin firayim minista kuma ministan harkokin waje, a karo na farko ,ya rufa wa Zhou Enlai baya wajen yin ziyarar sada zumunta a kasar Korea ta Arewa, kuma ya tsara shirye-shirye sosai ga rundunar sojojin sa kai ta jama'ar kasar Sin don komawa gida yadda ya kamata. A shekarar 1960, bi da bi ne ya raka Zhou Enlai ko shi kansa ya ja ragamar kungiyoyi don yin ziyara a kasar Myanmar da Indiya da Nepal da Kampuchea da Mongoliya da Afghanistan da sauran kasashe kuma ya daddale yarjejeniyar sada zumunta da yarjejeniyar tattalin arziki a tsakanin kasar Sin da kasar Nepal, da kuma daddale yarjejeniyar sada zumunta da rashin kai wa juna hari a tsakanin kasar Sin da kasar Kampuchea da yarjejeniyar sada zumunta da ba da taimakon juna a tsakanin kasar Sin da kasar Mongoliya da yarjejeniyar sada zumunta da rashin kai wa juna hari a tsakanin kasar Sin da kasar Afghanistan.
Ji Pengfei
Ji Pengfei ya zama ministan harkokin waje na kasar Sin daga shekarar 1972 zuwa shekarar 1974.
Mr Ji Pengfei ya taba daukar mukamin shugaban kungiyar harkokin waje na kasar Sin da ke wakilci a Jamhuriyar dimokuradiya ta Jamus bisa matsayin jakada da kuma jakadan farko da ke wakilci a Jamhuriyar dimokuradiya ta Jamus da mataimakin ministan harkokin waje da kuma ministan harkokin waje. Bayan shekarar 1979, ya zama ministan sashen yin cudanya da kasashen waje na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin da mataimakin firayim minista da babban sakatare na majalisar gudanarwa ta kasar Sin . A lokacin da ya zama direkta na ofishin kula da harkokin Hongkong da Macao na Majalisar gudanarwar kuma ya zama daya daga cikin direktocin kwamitin rubuta babban tsari na yankin musamman na Hongkong na Jamhuriyar Jama'ar Sin da na Macao , cikin himma da kwazo ne ya aiwatar da manufofi da ka'idojin da gwamnatin kasar Sin ta tsara bisa tunanin da aka yi na Sin daya amma tsarin mulki iri biyu don daidaita batun Hongkong da Macao cikin lumana, sa'anan kuma ya halarci bikin sa hannu kan hadadiyyar sanarwar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Britaniya a kan batun Hongkong.
Qiao Guanhua
Qiao Guanhua ya zama ministan harkokin waje na kasar Sin daga shekarar 1974 zuwa shekarar 1976.
Qiao Guanhua mutumin birnin Yancheng na lardin Jiangsu ne. A da, ya taba dalibta a kasar Jamus, kuma ya sami digiri na uku na ilmin philosophy. A lokacin yakin kin harin Japan, muhimmin aikinsa shi ne aikin yada labarai da kuma rubuta bayanai da sharhi kan al'amuran kasa da kasa. A yanayin kaka na shekarar 1942, ya je aiki a jaridar Xinhua Ri Bao da ke birnin Chongqing don shugabantar shafin musamman na kasa da kasa, har zuwa ranar samun nasarar yakin kin harin Japan. Bayan kafuwar Jamhuriyar jama'ar Sin, ya zama mataimakin direkta na kwamitin tsara manufofin harkokin waje na ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin da mataimakin ministan harkokin waje da kuma rike da sauran mukamai. A cikin ayyukan harkokin waje na yau da kullum, ya kan rubuta ko ja ragamar rubuta muhimman takardun harkokin waje, bayan shekarar 1976, ya dau nauyin mai ba da shawara ga hadadiyyar kungiyar sada zumunta da kasashen waje ta jama'ar kasar Sin. Manyan littattafai da ya rubuta sun hada da littattafan da ke kunshe da sharhohin da ya rubuta kan al'amuran kasashen duniya da bayani mai suna daga Munich zuwa Dunkirk da dai sauransu.
Huang Hua
Huang Hua ya zama ministan harkokin waje na kasar Sin daga shekarar 1976 zuwa shekarar 1982.
Bayan da aka mayar wa kasar Sin kujerarta ta halal a cikin Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 1971, an nada Mr Huang Hua don ya zama wakilin farko na din din din na kasar Sin da ke wakilci a Majalisar Dinkin Duniya da kwamitin sulhu na majalisar; A shekarar 1976, ya zama ministan harkokin waje, ya taba jan ragamar kungiyoyin wakilan kasar Sin don halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya na 29 da na 32 da na 33 da na 35 da na 37. A watan Augusta na shekarar 1978, tare da ministan harkokin waje na kasar Japan ne ya sa hannu kan yarjejeniyar sada zumunta da shimfida zaman lafiya a tsakanin Jamhuriyar jama'ar Sin da kasar Japan a birnin Beijing. A shekarar 1978, ya shugabanci shawarwarin kulla huldar diplomasiya da aka yi da wakilan kasar Amurka, a shekarar 1982, tare da sakataren harkokin kasa na kasar Amurka, wato ministan harkokin waje na kasar Amurka Mr.Hague ya sa hannu kan sanarwar ran 17 ga watan Augusta kan daidaita batun sayar wa Taiwan makamai da Amurka ta yi. Daga shekarar 1985 zuwa shekarar 1995, ya halarci taron shekara shekara na majalisar aikin kasa da kasa. Yanzu ya dau nauyin shugaban kungiyar yin nazari a tsakanin aminanmu na kasa da kasa na kasar Sin da shugaban kungiyar yin cudanyar sada zumunta a tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin da shugaban kungiyar ba da taimakon jin dadin jama'a da kuma shugaban asusun Son Qingling.
Wu Xueqian
An nada Wu Xueqian don ya zama ministan harkokin waje daga shekarar 1982 zuwa shekarar 1988.
Mr Wu Xueqian ya taba zama mataimakin firayim ministan Jamhuriyar jama'ar Sin da mamban majalisar gudanarwa ta kasa kuma ministan harkokin waje. A lokacin da ya dau nauyin mamban majalisar gudanarwa ta kasa kuma ministan harkokin waje, ya taba yin ziyara a kasar Korea ta Arewa da Malasiya da Japan da Masar da Kenya da Zambiya da Romaniya da Faransa da Tarayyar Jamus da Amurka da Canada da Argentina da Brazil da sauran kasashe na Asiya da Afrika da Turai da nahiyar Amurka, wato yawansu ya wuce kasashe 50.
Qian Qichen
Qian Qichen ya zama ministan harkokin waje na kasar Sin daga shekarar 1988 zuwa shekarar 1998.
An haifi Qian Qichen a watan Janairu na shekarar 1928, shi e mutumin Jiading na birnin Shanghai ne, a watan Oktoba na shekarar 1942 ya shiga Jam'iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin kuma ya yi aiki domin jam'iyyar, matsayin ilminsa ya yi daidai da matsayin ilmin da aka samu a jami'a. Daga shekarar 1942 zuwa shekarar 1945, a lokacin da yake karatu a makarantar sakandare da ke karkashin Jami'ar Datong ta birnin Shanhai, ya shiga cikin Jam'iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin kuma ya zama shugaban karamar kungiyar jam'iyyar da kuma sakataren kwamitin reshin jam'iyyar. Daga shekarar 1954 zuwa shekarar 1955, ya je karatu a makarantar horar da 'yan kungiyar samarin kwaminis ta kwamitin tsakiya na Tarayyar Soviet. Daga shekarar 1955 zuwa shekarar 1963, ya zama sakatare na matsayi na biyu na ofishin jakadan kasar Sin da ke wakilci a kasar Tarayyar Soviet da mataimakin direktan ofishin kula da harkokin daliban da ke dalibta a kasar da direktan ofishin yin nazari ,daga shekarar 1963 zuwa shekarar 1966, ya zama shugaban sashen kula da harkokin daliban da suke dalibta a kasashen waje na ma'aikatar jami'ai da kuma mataimakin shugaban sashen yin cudanya da kasashen waje, daga shekarar 1966 zuwa shekarar 1972, a cikin "babban juyin juya hali kan al'adu" da aka yi, ya sha wulakanci, sa'anan kuma an tura shi zuwa makarantar ma'aikatan hukuma na "ran 7 ga watan Mayu" don yin aikin lebura. Daga shekarar 1972 zuwa shekarar 1982, ya zama karamin jakadan kasar Sin da ke wakilci a Tarayyar Soviet da jakadan da ke wakilci a kasar Guinea da shugaban sashen watsa labarai na ma'aikatar harkokin waje. Daga shekarar 1988, ya soma zama ministan harkokin waje da sakataren kwamitin Jam'iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin a ma'aikatar harkokin waje da mamban majalisar gudanarwa ta kasa. Daga shekarar 1993, ya soma zama mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin da kuma mataimakin firayim minista kuma ministan harkokin waje.
Tang Jaixuan
Tang Jiaxuan ya zama ministan harkokin waje daga shekarar 1998 zuwa shekarar 2003.
An haifi Tang Jiaxuan a birnin Shanghai a watan Janairu na shekarar 1938, kuma shi mutumin birnin Zhenjiang na lardin Jiangsu ne, ya shiga cikin Jam'iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin a shekarar 1973. Bayan da ya kammala karatu a makarantar sakandare , sai ya je karatu a sashen koyon harshen Ingilish na Jami'ar Fudan ta birnin Shanghai .daga shekarar 1970 zuwa shekarar 1978, ya dau nauyin shugabancin kungiyar jama'ar Sin ta sada zumunta da kasashen waje da mamban majalisar sada zumunta a tsakanin kasar Sin da Japan da mataimakin direkta na kungiyar jama'ar Sin ta sada zumunta da kasashen waje. Daga shekarar 1988 zuwa shekarar 1991, ya zama karamin jakada da jakada na ofishin jakadan kasar Sin da ke wakilci a kasar Japan. Daga shekarar 1991 zuwa shekarar 1993, ya zama mataimakin ministan harkokin waje. Daga watan Maris na shekarar 1993 zuwa watan Maris na shekarar 1998 ya zama mataimakin ministan harkokin waje. A watan Maris na shekarar 1998, ya zama ministan harkokin waje. A watan Maris na shekarar 2003, ya zama mamban majalisar gudanarwa ta kasa.
Li Zhaoxing
Li Zhaoxing ya zama ministan harkokin waje daga shekarar 2003 har zuwa yanzu.
An haifi Li Zhaoxing a watan Oktoba na shekarar 1940 a lardin Shangdong, ya kammala karatu a Jami'ar Beijing a shekarar 1964. Daga shekarar 1970 zuwa shekarar 1977, ya taba zama ma'aikaci da jami'i a ofishin jakadancin kasar Sin da ke wakilci a Jamhuriyar Kenya. Daga shekarar 1985 zuwa shekarar 1990, ya zama mataimakinshuga da shugaba na sashen watsa labaru na ma'aikatar harkokin waje da kuma kakakin ma'aikatar harkokin waje. Daga shekarar 1993 zuwa shekarar 1995, ya zama wakili din din din da jakada mai cikakken iko na Jamhuriyar Jama'ar Sin da ke wakilci a Majalisar Dinkin Duniya. Daga shekarar 1998 zuwa shekarar 2001, ya zama jakadan musamanna Jamhuriyar Jama'ar Sin a Amurka . A watan Maris na shekarar 2001 zuwa shekarar 2003, an nada shi don ya zama mataimakin ministan harkokin waje, a watan Maris na shekarar 2003, ya zama ministan harkokin waje.
>>[Muhimman ajiyayyun takardun kasar Sin dangane da aikin diplomasiya]
Muhimman ajiyayyun takardun kasar Sin dangane da aikin diplomasiya
Sin da Amurka
(Sanarwar Shanghai) (1972)
(1978)
(1982)
Sin da Japan
(1972)
(1978)
(1972)
Sin da Rasha
(2002)
Sin da Britaniya
(1984)
(1998)