Fadin kasa, Albarka da Yawan mutane
2020-10-30 10:05:04 CRI
A arewa,yankin kasar Sin ya fara ne daga layin tsakiya na kogin Helongjiang dake arewancin Mohe,a kudu,ya fara ne daga Zengmu`ansha dake kudancin tsibirin Nansha,daga arewa zuwa kudu,nisansa ya kai wajen kilomita dubu biyar da dari biyar.A gabas,yankin kasar Sin ya fara ne daga wurin da kogin Helongjiang da kogin Wisuli suka hadu,a yamma,ya fara ne daga tuddan Pamil,daga gabas zuwa yamma,nisansa ya kai wajen kilomita dubu biyar.
Layin iyakar kasa na kasar Sin ya kai kusan kilomita dubu ashirin da biyu da dari takwas,a gabashinta ita ce Korea,a arewacinta ita ce Mongolia,a arewa maso gabashinta ita ce Rasha,a arewa maso yammacinta su ne Kazakhstan da Kyrghyz da Tajikstan,a yamma da kuma kudu maso yammacin kasar Sin su ne Afghanistan da Pakistan da Indiya da Nepal da Bhutan da sauransu,a kudu kuma su ne Myama da Laos da Vietnam.A gabas da kuma kudu maso gabashin kasar Sin,wato bayan teku su ne Korea ta kudu da Japan da Philipines da Brunei Darussalam da Malaysia da Indonesia.