logo

HAUSA

Babi14: Tarihi

2020-10-30 10:07:54 CRI

Babi14:Tarihi

>>[Daulolin Kasar Sin]

Daular Xia

Daular Xia ta zama daula ta farko cikin tarihin kasar Sin, ta kasance ne wajen karni na 21 zuwa karni na 16 na kafin bayyanuwar Annabi Isa,Alaihissalam, wadda ta na da sarkuna 17 da ke cikin zuriya 14, daular Xia tana kasancewa cikin wajen shekaru 500. Cibiyar daular Xia, wato wurin da karagar mulkin take tana kudancin lardin Shanxi da yannacin lardin Henan na yanzu.

Wanda ya kafa daular Xia Da Yu shi ne wani mazan jiya na tarihi wanda ya hana yaduwar ambaliyar ruwa domin kiyaye kwanciyar hankalin jama'a. An ce dalilin da ya sa Da Yu ya sami goyon bayan daga wajen jama'ar kabilarsa, saboda ya yi nasarar yin gyara ga rawayen kogin da yakan yin ambaliyar ruwa cikin shekara da shekaru, a karshe dai ya kafa daular Xia. Kafuwar daular Xin ta alamanta zaman al'umma mai mallakar dukiyarta ta maye gurbin zaman al'umma na farko wanda ya dauki dogon lokaci, daga lokacin nan kasar Sin ta shiga cikin zaman al'umma na lokacin bayi.

A karshen daular Xia, an yi siyasa mai yamutsi cikin iyalin sarkin Xia, kuma sabane-sabanen ajujuwa sun tsananta kowace rana. Musamman bayan sarki na karshe Xia Jie ya hau kujerar sarki, bai yi aikin gyare-gyare ba, ya nuna girman kai da alumbazzaranci da saukin nuna soyayya, shi kuma ma'abucin jima'i ne har fiye da kima. Har a duk rana tare da kwakwararsa mai suna Mei Xi wadda yake sonta sosai, sun yi nishadi da shan giyya, ko kusa basu lura da wahalhalu da matsalolin jama'a ba. Duk wani Wazirinsada ya gabatar da banbancin ra'ayi, zai kashe shi. Saboda haka, kananan kasashen da ke karkashin daular Xia, bi da bi ne suka ci amanar daular. Sai a daidai lokacin nan, wata kasa daya daga cikin kananan kasashe Shang yi amfani da damar nan ta kai hari kan sarkin Jie, a karshe dai Shang ta ga bayan rundunar sojojin Xia Jie, bayan Jie ya gudu, ya mutu a wani wuri mai suna Nan Chao, daga nan dai daular Xia ta halaka.

Takardun bayyanai na dangane da daular Xia zuwa yanzu da ake iya nazarinsu, kalilan ne, sai ya zuwa yanzu cikin da'irar nazarin tarihi, an kasance da gardama kan ko an kasance da daular Xia ko a'a cikin tarihin kasar Sin. Amma cikin wani shahararen littafin tarihi an rubuta tsarin zuriyar Daular Xia. Masu binciken tarihi su ma suna so cikin aikin binciken kayayyakan tarihi su sami al'adun kayayyakin da daular Xia ta bari, ta yadda za a sake maido da tarihi na daular Xia. Tun shekarar 1959, masu aikin binciken kayayyakin tarihi na kasar Sin sun soma yin bincike a wuri mai suna Xia Xu, daga nan dai an soma bude wani sabon shafi wajen binciken al'adun Xia. Yanzu galiban masana sun nuna ganinsu cewa, al'adun Er Li Tou wanda aka nada sunan bisa wurin tarihi na Er Li Tou na birnin Yanshi na lardin Henan, ya zama abun da ake yin binciken al'adun Xia. an kiyasta cewa, lokacin kasancewar al'adun wajen shekaru 1900 na kafin bayyanuwar Annabi Isa Alaihissalam ne, kuma lokacin yana cikin shekaru na daular Xia. Yanzu koda yake ba a sami shaidu na kai tsaye wajen tabbatar da cewa al'adun Er Li Tou shi ne al'adu na daular Xia ba, amma azurtattun takardun binciken tarihin da aka gabatar, sun sa kaimi ga aikin binciken al'adun daukar Xia sosai.

Kayayyakan aikin gona da aka haka a wurin tarihi na al'adun Er Li Tou , galibansu kayayyakin dutse ne, kuma an yi amfani da kayayyaki na kashi ko kahon dabbobbi da na kumba, a wajen harsashin gidaje da randar da aka haka da bangon kabari, an ga wurin da aka haka kasa da wani irin kayayyakin

aiki na katako mai suna Leisi. Jama'a masu aikin karfi na lokacin can sun yi amfani da kayayyaki marasa ci gaba, sun yada hazikancinsu sun yi himma wajen hana yaduwar ambaliyar ruwa don kiyaye kasa, sun sami sakamakon bunkasa aikin gona. Koda yake ya zuwa yanzu ba a sami kayayyakin tagulla masu girma a tsoffin wuraren tarihi na daular Xia ba, amma daga cikin kayayyakin tarihi da ke cikin al'adun Er Li Tou, an sami wasu kayayyakin aiki da kayan yaki da kayan shan giya kamar wuka da chisel da kayan yaki da tulu , a sa'an nan kuma an gano wani wurin tsara kaya da tagulla, an haka abun yin kayan fadi ka mutu da diddigar tagulla. Daga wadannan waje, an kuma fitar da wasu kayayyakan da aka yi da wani irin dutse mai daraja, har an yi ado kan jikin kayayyakin da wani irin dutse mai launin kore, da wani kayan kida mai suna Shi Qing, daga wadannan kayayyakin da aka fitar daga karkashin kasa, an gane cewa, fasahar yin kayayyaki ta kara samun ci gaba.

A wajen takardun bayyanai na tsohon zamanin da, abin da ke jawo hankulan mutane shi ne kalanda ta daular Xia. Wani bayani mai suna Xia Xiaozhen da ke cikin wani littafi mai lakabi Dadai Liji, wanda ya zama wani muhimmiyar takardar da ke kasancewa yanzu dangane da kalandar daular Xia, daga ciki an bayyana cewa mutane na lokacin can suna iya tabbatar da watanni duk bisa yadda tauraruwa ta nuna, wannan ne kalandar tun da cancan na kasar Sin. Kalandar ta bi watanni 12 na kalandar daular Xia, ta rubuta halayen tauraro da fasalin yanayi da sabbin abubuwan halittu, har da aikin gona da ya kamata a yi har da harkokin mulki na cikin kowace wata filla filla. Kalandar ta bayyana matsayin da daular Xia ta samu wajen bunkasa aikin gona, inda kuma an kare ilimin kimiyya mai daraja na tsohon zamanin da na kasar Sin.

Daular Shang

A cikin gagga masu binciken tarihi na kasar Sin, daular Xia ta zama daula mafi tsufa na tsohon zamanin can da na kasar Sin, amma galiban takardun tarihi dangane da daular Xia, an same su ne daga takardun bayyanai na bayan daular wadanda ake rubuta, har ma ya zuwa yanzu ba a sami manyan shaidu daga cikin abubuwan binciken tarihi ba. Daular Shang ta zama daula ta tsohon zamanin can da na kasar Sin da aka sami amintattun shaidu daga cikin binciken tarihi, to yanzu bari mu gabatar muku da bayanai kan daular nan da ke da rubutu a tarihin kasar Sin.

An kafa daular Shang a karni na 16 na kafin bayyanuwar Annabi Isa Alaihisallam! Ya zuwa karni na 11 kafin bayyanuwar Annabi Isa daular ta halaka, lokacin da daular ta ci ya kai wajen shekaru 600. A farkon lokaci na Shang, an yi ta kaurar da fadar daular, a karshe an yi kaura zuwa wani wuri mai suna Yin wato na kusa da birnin Anyang na lardin Henan na yanzu. Bisa binciken tarihi da aka yi an ce, a farkon lokacin daular Shang, wayin kai na kasar Sin ya sami bunkasawa ya zuwa wani babban matsayi , wasu muhimman abubuwa su ne rubutun da aka sassaka a 'ko'kon bayan kunkuru da kayakkan tagulla.

An tarar rubutun da aka sassaka a'ko'kon bayan kunkuru,a farkon lokaci na karni na 20, manoma na wani kauye mai suna Xiao Tun da ke arewa maso yamma na birnin An Yang na lardin Henan, sun same kokon bayan kunkuru ko kashin dabbobi, sai sun sayar da su kamar magungunan gargajiya, sai masana suka tarar, ashe a kan kokon kunkurun an kasance da rubuce-rubuce, sai nan da nan aka rubanya karfi don yin bincike, bayan haka ba da dadewa ba, masanan binciken rubuce- rubucen tsohon zamani na kasar Sin sun tabbatar da cewa, rubuce-rubucen da aka sassaka a kan 'ko'kon bayan kunkuru da kashin dabobbi, rubutu ne na daular Shang, bayan haka an tabbatar da cewa, kauyen Xiao Tun shi ne fadar daular shang da aka rubuta cikin littafin tarihi wato Yin Xu.

An gano Yin Xu ta hanyar yin bincike, ya zama aikin binciken kayayyakin tarihi da ke karkashin kasa mafi muhimmanci cikin kasar Sin a karni na 20. Tun karo na farko da aka yi bincike a shekarar 1928, daga wurin an fitar da tarin kayayyakin tarihi masu daraja sosai ciki har da rubuce-rubucen da aka sassaka a kan 'ko'kan bayan kunkuru da kayayyakan tagulla. Rubuce-rubucen da aka sassaka a kan 'ko'kon bayan kurkuru su ne rubutu na tsohon zamanin da da aka sassaka kan 'ko'kon bayan kunkuru da kashin dabbobi. Cikin daular Shang, kafin sarki ya yi komene abu, yakan yi addu'a domin neman jagora daga wajen Allah. Kokon bayan kunkuru shi ne kayan da sarkin ke amfani da su don neman jagora daga wajen Allah. Kafin a soma yin amfani da kokon bayan kunkuru, dole ne a yi musu gyara, wato da farko a cire tsoka da jini da ke 'ko'kon, sai a goge shi don ya yi laushi. Daga baya a cikin kokon bayan kunkuru ko na kashin dabobbi , an yi amfani da wuka don sassaka dogayen layuka gida-gida , an jera wadannan luyuka daya bayan daya. Mai yin aikin nan shi ne malamin duba, ya kan sassaka sunansa da ranakun yin addu'a da tambayoyin da ake bukatar sani kan kokon bayan kunkuru, sai a gasa luyukan da ke kan kokon bayan kunkuru. Saboda zafin wuta, sai luyuka su barke, irin barakar da ke kan 'ko'kon bayan kunkuru su ne ? Zhao ?. Sai malamin duba su binciki barakar da aka gani kan kokon bayan kunkuru, daga nan dai za a sami sakamakon addu'a, kuma za a duba ko addu'a ya yi daidaici kan 'ko'kon bayan kunkuru. In addu'a da aka yi ta yi daidai, sai wadannan kokon bayan kunkurun da aka sassaka addu'a sun zama takardun bayyanai na hukumar kuma an tanada su.

Ya zuwa yanzu an yi bincike kan 'ko'kon bayan kunkuru wajen dubu 160. Wasu daga cikinsu cikakku ne, wasu guntu-guntu ne ba a sassaka kome ba. Bisa hasashen da aka yi an ce, adadin rubutu iri daban daban da ke kan kokon bayan kunkuru ya kai dubu 4 ko fiye, dubu 3 daga cikinsu, masana sun yi nazari sosai, daga cikinsu masana sun bayyana gaba daya wato sun sami ra'ayi daya kan ma'anarsu wajen dubu ko fiye. Sauransu ko ba a gane ma'anarsu ba, ko masana suna da bambancin ra'ayi kan ma'anarsu. Koda yake, ta rubutu sama da dubu, mutane sun iya gane halayen da ke cikin daular Shang a fannin siyasa da tattalin arziki da al'adu. Littafin binciken rubuce-rubucen da aka sassaka a kan 'ko'kon bayan kunkuru shi ne Malam Liu E ya rubuta a shekarar 1931 wato ? Tiye Yun Can Gui ?. Wani littafi mai suna ? yin binciken rubuce-rubucen da aka sassaka a kan kokon bayan kunkuru ? da Malam Guo Moruo wani shahararen mai binciken tarihi da kwararai na fannin adabi ya rubuta a shekarar 1929, ya zama wani babban littafi. Yanzu cikin kasar Sin masu fadi a ji kan bincike rubuce-rubucen da aka sassaka a kan 'ko'kon bayan kunkuru su ne shehun malami Qiu Xigui na jami'ar Beijing, da shehun malami Li Xueqing na cibiyar binciken tarihi ta kasar Sin.

Daidai kamar sassaka rubuce-rubuce a kan kokon bayan kunkuru, kayayyakin tagulla su ne kayayyakin da ke da halin wakilci na cikin daular Shang. A cikin daular Shang,an kai babban matsayin fasaha wajen narke da yin kayayyakin tagulla , yawan kayayyakin tagulla da aka yi bincike daga wurin da ake kira Yin Xu ya kai sama da dubu, ciki, wata tukunya mai kusurwa hudu mai suna SiMuWu wadda aka hako daga wannan wurin na Yin Xu a shekarar 1939, tana da nauyin kilo 875, tsawonta senti-mita 133, tsayinta senti-mita 110 , fadinta senti-mita78, sifarta mai girma ce, wadda ta zama kaya mai kyau sosai na cikin tsohon zamanin da na kayayyakin tagulla na kasar Sin.

Binciken tarihi da gano kayayyaki har da nazarin tarihi, duk sun tabbatar da cewa, a daular Shang, an kasance da kasa, kuma an kafa tsarin masu zaman kansu, tun daga lokacin, tarihin kasar Sin ya shiga lokacin wayin kai.

Daular 'Xizhou' da daular 'Dongzhou'

Bayan daular `Xia` da daular `Shang`,daular `Zhou` ita ce daula ta uku ta zamanin da na kasar Sin,an kafa ta ne a shekarar 1027 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam,a shekarar 256 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam,daular Qin ta tumbuke ta,tsawon mulkinta ya kai shekaru fiye da 770.Saboda dalilin babban birninta,an rarraba daular `Zhou` da zamani biyu,wato zamani na farko ita ce daular `Xizhou`,zamani na biyu ita ce daular `Dongzhou`.Aka kuma rarraba daular `Dongzhou` da zamani biyu,zamani na farko ita ce daular `Chunqiu`,zamani na biyu ita ce daular `Zhanguo`.

Daular `Xizhou` ta fara ne daga shekarar 1027 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam zuwa shekarar 771 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam,tsawonta ya kai wajen shekaru 257.Sarki na farko na daular `Zhou` wato sarki Wu ya kafa babban birninsa a birnin Gao,bayan wannan,ya shugabanci hadaddun sojoji don kai hari ga daular Shang,daga baya,ya kafa daular `Zhou`.Bayan sarki Cheng na daular `Zhou` ya gaji mulki,bai iya rike mulki ba saboda yana karami,saboda haka,karamin sarki na daular `Zhou` Dan,dan`uwa na babansa ya rike mulki maimakonsa.A karkashin shugabancin karamin sarki na `Zhou` Dan,aka dauki matakai a jere don inganta sakamakon da aka samu.A lokacin da sarki Cheng da sarki Kang suke rike mulki,daular `Xizhou` ta sami bunkasuwa da saurin gaske,masanan ilmin tarihi sun kira wannan lokaci kamar `zamanin Cheng da Kang`.

Tsarin kasa na daular `Zhou` yana da tsarin musamman,abubuwa mafiya muhimmanci sun kumshi:tsarin gonaki masu siffar rijiya da tsarin doka da sauransu.

Daga shekarar 770 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam zuwa shekarar 476 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam,shi ne daular `Chunqiu`.Bisa bunkasuwar tattalin arziki da karuwar yawan mutane,manyan kasashe sun fara yin kazamin yaki tsakaninsu.Halin zamantakewar al`umma ya sami manyan sauye-sauye.A cikin aikin kawo albarka na sha`anin noma,aka fara yin amfani da kayan tama,a kai a kai ne aka fara yin amfani da shanu,kuma aka fara gina ayyukan madatsan ruwa,daga nan,yawan hatsin da aka samu ya kara karuwa.

An haifi malam Confucius,masanin tunani na farko a kan tarihin kasar Sin kuma shahararren masanin ba da ilmi na kasar Sin ne a daular `Chunqiu`.Malam Confucius ya takaita al`adu da tunani na da,bisa tushen nan,ya gabatar da ra`ayoyinsa a jere game da matsalar zamantakewar al`umma da matsalar siyasa,daga nan ya kafa kungiyar ilmin `Ru` na zamanin da.

Daular `Zhanguo` wato daga shekarar 403 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam zuwa shekarar 221 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam,ita ce wani zamani da kananun sarakuna suka yi kazamin yaki.

Ya zuwa daular `Zhanguo`,halin da kasar Sin ke ciki ya sami manyan sauye-sauye,wato kananun kasashe da yawan gaske sun riga sun bace sabosa aka mamaye su,saura kasashe bakwai wadanda suke kumshi `Qin` da `Chu` da `Yan` da `Han` da `Zhao` da `Wei` da Qi`sun fi girma wato sun zama muhimman kasashe na kananun sarakuna na zamanin `Zhanguo`.A wancen lokaci,bi da bi ne kasashe daban daban sun yi gyare-gyare,wanda a ciki,malam Shang Yang na kasar Qin ya fi kawo tasiri ga kasarsa.

Kodayake an yi ta yin yaki a zamanin `Zhanguo`,amma wannan bai kawo mugun tasiri ga bunkasuwar al`adu na zamanin da na kasar Sin ko kadan ba,masana a fannoni daban daban sun yi yawan gaske,wannan ya kara ingiza wadatuwar al`adu da ilmomi a wancen lokaci.A lokacin nan,al`adu da tunani na zamanin da na kasar Sin sun kai wani matsayin koli da a taba ganinsa a da ba.Daga cikinsu,rukunin ilmin `Ru` na Confucius da Mencius da rukunin ilmin `Dao` na Laozi da Zhuangzi da Liezi da rukunin ilmin `Fa` na Hanfei da rukunin ilmin `Mo` na Mozi sun fi yin suna.Duk wadannan rukunonin ilmi sun kara ingiza wadatuwar fannin tunani na zamanin `Zhanguo`.Ba ma akwai duk wadannan sun ingiza bunkasuwar siyasa da tattalin arziki a wancen lokaci ba,har ma sun kawo tasiri mai zurfi ga tunanin jama`ar kasar Sin na yanzu,wato sun ba da babban amfani ga kasar Sin wajen tunani.

A shekarar 230 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam,sarki Ying Zheng na kasar Qin ya fara yin babban aikinsa na dinkuwar kasa,a cikin shekaru 9,bi da bi ne kasar Qin ta mamaye sauran kasashe shida,kuma ta tabbatar da dinkuwar kasa a shekarar 221 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam.Daga nan,an kawo karshen halin baraka da kasar Sin ke ciki a cikin shekaru kusan dari shida.

Daular Qin

A shekarar 221 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam,bayan da aka aiwatar da tsarin bayi a cikin shekaru fiye da dudu biyu,an kafa daular Qin ta mulkin gargajiya ta farko a kan tarihin kasar Sin,daular Qin ita ce daula daya mai mulkin tsakiya ta farko a kan tarihin kasar Sin.Kafuwar daular Qin tana da muhimmiyar ma`ana ga tarihin kasar Sin.

Daga shekarar 255 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam zuwa shekarar 222 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam,zamanin `Zhanguo` wato yaki ne a kan tarihin kasar Sin,shi ma lokacin karshe ne na zamantakewar al`ummar tsarin bayi na kasar Sin.A wancan lokaci,ya kasance da kananun kasashe masu `yancin kai da yawan gaske,sun yi yaki da juna,daga karshe dai,kasashe bakwai sun fi gima,ana kiransu `kasashe bakwai`,wato su ne `Qin` da `Qi` da `Chu` da `Wei` da `Yan` da `Han` da kuma `Zhao`.Daga cikinsu,kasar Qin wadda ke shiyyar arewa maso yammancin kasar Sin ta yanzu ta aiwatar da gyare-gyaren aikin soja da sha`anin noma,saboda haka karfin kasar Qin ya kara karfafuwa da saurin gaske.A shekarar 247 kafin haihuwar Annnabi Isa alaihissalam,Ying Zheng wanda ke da shekaru goma sha uku da haihuwa kawai ya hau kan kujerar mulkin kasar Qin,ya zama sarki Qin.Lokacin da Ying Zheng ya kai shekaru 22 da haihuwa,sai ya fara rike mulki da kansa,daga nan ne,sarki Qin ya fara kai hari ga sauran kasashe shida,yana so ya mamaye dukkansu.Sarki Qin ya yi kokari don neman samun kwararrun mutane a fannoni daban daban,duk wanda yake da basira,sarki Qin zai yi amfani da shi.Alal misali.ya taba aikawa da malam Zhengguo,mai leken asiri na kasar `Han` da ya haka `kogin Zhengguo`,ta yadda za a sa gonaki masu sauruka wajen kadada fiye da dubu 40 na kasar Qin da su zama gonaki masu ni`ima,wannan ya kago isashen sharadi mai kyau ga kasar Qin wajen dinkuwar kasa.Daga shekarar 230 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam zuwa shekarar 221 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam,wato a cikin shekaru tara,bi da bi ne Ying Zheng ya mamaye sauran kasashe shida wato ya mamaye kasar `Han` da kasar `Zhao` da kasar `Wei` da kasar `Yan` da kasar `Chu` da kasar `Qi`,ya kammala babban sha`aninsa na dinkuwar kasa.Daga nan an kawo karshen barakar kasa a kan tarihin kasar Sin,kuma an kafa daular Qin daya tak.Ying Zheng ya zama sarki mai ikon kasashe da yawa na farko a kan tarihin kasar Sin,ana kiransa `sarkin kasa na farko`.

Sarkin kasa Qin ya dinke kasar Sin daya,wannan yana da babbar ma`ana ga tarihin kasar Sin.Da farko dai,a fannin siyasa,sarki Qin ya rarraba kasar Sin zuwa larduna talatin da shida,a karkashinsu,an kafa gundumomi,sarki Qin ya zabi kuma ya nada dukkan jami`ai na gwamnatin tsakiya da na kananun gwamnatocin wurare da kansa.Wannan tsarin lardi da gunduma da sarki Qin ya kafa ya zama tsari na mulkin gargajiya na kasar Sin a cikin shekaru fiye da dubu biyu.Kawo yanzu,sunayen gundumomin kasar Sin da yawan gaske sun zo ne daga sunayen da daular Qin ta tsara yau da shekaru fiye da dubu biyu da suka shige.

Wani amfani daban na dinkuwar kasar Sin a daular Qin shi ne dayantakar rubutu.Kafin daular Qin,kasashe daban daban suna da rubutu na kansu,wannan ya kawo mahani ga cudanyar al`adu.Bayan dinkuwar daular Qin,an tanadi cewa,rubutun Han irin na salon `Xiaozhuan` na kasar Qin ya zama rubutu na duk kasa,wannan ya ba da babban amfani ga ci gaban tarihi da al`adu na kasar Sin.

Ban da wannan kuma,daular Qin ta sa ma`auni iri daban da ya zama guda daya,alal misali,tsawo da fadi da nauyi da sauransu,wannan ya ingiza bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri.A sa`i daya kuma,sarki na farko na daular Qin ya sa kudi da doka da su zama guda daya,wannan ya kago sharadi ga bunkasuwar tattalin arziki a duk fadin kasar,shi ma ya kara karfafa matsayin ikon mulki na gwamnatin tsakiya.

Don kara karfafa mulki a kan tunani,a shekarar 213 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam,sarki na farko na daular Qin ya ba da umurni da a kone dukkan litattafan tarihi da na ilmin `Ru` na sauran kasashe,wanda a ciki ba su kumshi littafin `tarihin daular Qin` ba,kuma ya kashe mutane wadanda suka ajiye wadannan litattafai.A sa`i daya kuma,don hana harin da kananan kabilun dake arewancinta suka kai mata,sarki na farko na Qin ya ba da umurni da a sake gina babbar ganuwa da kasar Qin da kasar Zhao da kasar Yan suka gina,daga nan tsawon babbar ganuwa ya karu,wato yammancinta ya fara ne daga hamada,kuma gabashinta ya kai bakin teku.Sarki na farko na Qin shi ma ya ware kudi da yawan gaske don gina babban kabari a Lishan,yawan maginarsa ya kai fiye da dubu dari bakwai,wannan shi ne kabari na Qin da soja da doki da aka binne tare da mutanen da suka mutu wadanda suka yi suna sosai a duniya a halin da ake ciki yanzu.

Bayan dinkuwar kasar Sin a daular Qin,kasar Sin ta bude wani sabon shafi a kan tarihinta.

Daular Han

Daga shekarar 206 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam zuwa shekara ta 8 shi ne zamanin `Xihan` a kan tarihin kasar Sin.Sarki na farko na daular Han malam Liu Bang ya kafa daular Han,babban birninta shi ne Chang`an.

A lokacin da sarki Liu Bang yake rike da mulki a cikin shekaru bakwai,ya kara karfafa mulkinsa kuma ya tsara manufofin siyasa a jere game da `bai wa jama`ar kasa lokacin hutu`,wannan ya inganta mulkinsa.A shekarar 159 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam,sarki na farko na daular Han malam Liu Bang ya riga mu gidan gaskiya,daga baya,sarki Hui ya gaji mulkinsa,amma a wancan lokaci,a hakika dai,madam Lu Zhi,mata ta farko ta sarki Liu Bang ta rike mulkin kasa.Gaba daya madam Lu Zhi ta rike mulki har shekaru 16,ta zama daya daga cikin `yan mata wadanda suka rike mulkin kasa a kan tarihin kasar Sin.A shekarar 183 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam,sarki Wen ya gaji kujerar sarki Han.Sarki Wen da `dansa wato sarki Jing wanda ya rike milki daga shekarar 156 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam zuwa shekarar 143 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam sun ci gaba da aiwatar da manufar da sarki Liu Bang ya tsara game da `bai wa jama`ar kasa lokacin hutu`,sun rage harajin da aka buga wa jama`ar kasarsu,wannan ya sa tattalin arzikin daular Han ya sami bunkasuwa da saurin gaske,masanan ilmin tarihi sun mayar da wannan zamani a matsayin `zamanin Wen jing` wato zamanin da sarki Wen da sarki Jing suka rike mulki.

Bayan wannan,a kai a kai ne karfin kasa na daular Han ya kara karfafuwa.A shekarar 141 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam,sarki Wu ya rike mulki.Sarki Wu ya taba ba da umurni ga janar Wei Qing da janar Huo Qubing da su kai hari ga wuraren dake arewancin daular Han,kuma sun sami nasara,bayan wannan,sarki Wu ya habaka yankin kasarsa,shi ma ya tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki da al`adu na wurare dake arewancin daular Han.Daga baya,sarki Wu ya daina yin yaki kuma ya mai da hankali kan sha`anin noma,kokarin da ya yi ya ciyar da tattalin arzikin daular Han gaba sosai.Daga baya,sarki Zhao ya hau kan kujerar sarkin daular Han,ya ci gaba da nuna kwazo da himma don bunkasa tattalin arziki,kuma ya sami sakamako mai faranta ran mutane.

Bayan da sarki Zhao da sarki Xuan suka aiwatar da manufar `bai wa jama`ar kasa lokacin hutu` a cikin shekaru 38,karfin kasa na daular `Xihan` ya kara karfafuwa,amma a sa`i daya kuma,karfin wurare shi ma ya kara karfafuwa,wannan ya kawo babban tasiri ga mulkin daular `Han`.A shekara ta 8,Wang Mang ya tumbuke daular `Han`,kuma ya hau kan kujerar sarkin kasa,ya canja sunan kasa da `Xin`,daga nan daular `Xihan` ta kawo karshen mulkinta a kasar Sin.

Daular `Xihan` ita ce daya daga cikin dauloli mafiya karfi a kan tarihin kasar Sin.A kullum daular `Xihan` tana aiwatar da manufar `bai wa jama`ar kasa lokacin hutu`,jama`ar kasa suna da isashen abinci da sutura,kuma suna jin dadin zaman rayuwarsu,shi ya sa a kullum siyasar daular `Han` ta zauna da gindinta.Sarki Wu ya dauki shawarar da babban minista Dong Zhongshu ya gabatar masa game da `a kawar da sauran tunani,a nuna biyayya ga tunanin `Ru` kawai`,daga nan,addinin `Ru` da ilmin `Ru` sun zama tunanin tafiyar da harkokin kasa na kasar Sin.

Saboda harkokin siyasa da tattalin arziki suna tafiya kamar yadda ya kamata,shi ya sa sana`ar hannu da kasuwanci da zamantakewar al`adu da fasaha da kimiyyar hallitu dukkansu sun sami bunkasuwa da saurin gaske.Bisa bunkauswar kimiyya da fasaha,sana`o`in hannu kamarsu narke karfe da saka na daular `Xihan` sun sami yalwatuwa bisa babban mataki,bunkasuwar sana`ar hannu ta ingiza wadatuwar kasuwanci,kuma an kafa cudanyar dake tsakanin kasar Sin da kasashen dake yammancin Asiya a fannin diplomasiya da na kasuwanci da ciniki ta hanyar cinikin siliki.

Daga shekara ta 25 zuwa shekarar 220,zamanin daular `Donghan` ne na kasar Sin.sarki Guangwu wato Liu Xiu ne ya kafa ta.

A shekara ta 25,a karkashin taimakon sojojin `Lulin`,Liuxiu ya lallasa Wang Mang,ya hau kan kujerar sarki,kuma ya maido da sunan kasa da `Han`,amma ya mayar da birnin Luoyang a matsayin babban birninsa.A shekara ta biyu ta Jianwu,sarki Guangwu ya ba da umurni cewa za a yi gyare-gyare ga tsohuwar manufar da Wang Mang ya aiwatar daga dukkan fannoni,ya kafa mukamai na `Shangshu` shida saboda su tafiyar da harkokin kasa tare,wannan ya rage ikon manyan ministoci uku wato `Taiwei` da `Situ` da `Sikong`,ya kawar da `Guangnu`,kuma ya yi binciken kasa,a kai a kai ne zaman rayuwar jama`ar kasa ya sami kyautatuwa.Ya zuwa tsakiyar karni na farko,bayan kokarin da sarki Guangwu da sarki Ming da sarki Zhang suka yi,a kwana a tashi daular `Donghan` ta kara karfafuwa kamar yadda daular `Han` ta da ta yi,ana mayar da wannan zamani a matsayin `zamanin wadatuwa na Guangwu`.

A farkon daular `Donghan`,saboda mulkin kasa ya kara karfafa,huldar dake tsakanin gwamnatin tsakiya da sauran wurare tana tafiya yadda ya kamata,shi ya sa tattalin arziki da al`adu da kimiyya da fasaha da sauran fannoni dukkansu sun sami yalwatuwa cikin sauri har sun fi matsayi na daular `Xihan`.A shekarar 105,`dan kimiyya Cai Lun ya kyautata fasahar kera takarda,wannan ya sa kasar Sin ta shiga zamanin rubuta kan takarda amma ba kan gora kamar yadda aka yi a da ba,a sa`i daya kuma,fasahar kera takarda ita ma ta zama daya daga cikin fasahohin kera kayayyaki hudu na zamanin da na kasar Sin.A fannin kimiyyar halittu,kwararrun mutane na fannin ilmi na daular `Donghan` sun sami sakamako mai faranta ran mutane,wanda a ciki,malam Zhang Heng ya fi.Zhang Heng ya kera wani inji mai binciken girgizar kasa da ake kiransa `Huntianyi` da `Didongyi`.Ban da wannan kuma,wani shahararren likita da ake kiransa `Hua Tuo` shi ne likita na farko wanda ya yi amfani da maganin hana jin zafin tiyata a duniya.

Daular Wei da ta Jin

Zamanin Wei da na Jin sun kasance ne tsakanin shekarar 220 da shekarar 589 AD.A karshen karni na biyu bayan bayyanuwar Innabi Isa,aka kawo karshen daular Donghan,daga nan kasar Sin ta shiga halin baraka cikin dogon lokaci a tarihi.Da farko aka sami dauloli uku watau Wei,Shu da Wu (daga shekarar 189 zuwa shekarar 265) wadanda suka yi gaba da juna,daga baya daular Xijin ta cinye su gaba daya ta sa aya ga halin baraka,amma mulkin daular Xijin bai dade ba(265-316AD) aka sake shiga baraka.A kudancin kasa wani dangin sarkin Xijin ya kafa daular Jin ta gabas (317—420 AD),a arewacin kasa aka shiga rikice rikicen kabilu aka samu kasashe sha shida.

A wannan zamani,tattalin arzikin kudancin kasa ya samu babban cigaba.Mutanen kananan kabilu dake arewa da yammaci sun kaurata zuwa cikin kasa,kabilu daban daban sun hadu da juna.A fannin al'adu,darikar Xuanxue ta fi yaduwa,Addinan Buddha da Tao sun yi yaduwa da cigaba cikin gwagwarmayar gaba da juna da aka yi,amma masu mulkin mallaka sun kan kare darikar Buddha.A fannin adabi,aka sami kwararu bakwai a shekarun da ake kira "jianan",da marubuci Tao Yuanming,da masu kwarewa wajen rubuta sinanci kamar Wang shizhi da masu iyawa zane kamar Gu Kai,da fasahohin ramuka kamar ramukan Dunhuang,dukkansu kayayyakin tarihi ne masu daraja a kasar Sin.

A fannin kimiyya da fasahohi,malami Zu Chongzi ya zama mutumnin na farko da ya gano the circumference of a cirle to its diameter a duniya.Littafin "Qiminyaosghu" da marubuci Jia Sixie ya rubuta babban littafi ne na aikin gona a tarihi a duniya.

Daulolin arewa da na kudu sun shimfidu ne tsakanin shekarar 420 da 589 AD.A cikin daulolin arewa da akwai dauloli na Wei na arewa da na gabas da na yamma da kuma Qi na arewa da Zhou na arewa,a cikin daulolin kudu da akwai dauloli na Song da na Qi da na Liang da na Chen.

A zamanin dauloli na arewa da na kudu,tattalin arzikin kudancin kasa ya fi samun cigaba.Mutanen dake tsakiyar kasa sun kwararowa zuwa kudancin kasa,aka samu kwadago da yawa a kudancin kasa,fasahohin da aka shigo su ma sun sa kaimi ga cigaban tattalin arzikin kasa,yankin dake kawaye birnin Yangzhou,yanki ne mafi cigaban tattalin arziki a zamanin daulolin kudu.

A fannin al'adu,abun da ya fi jawo hankali shi ne cigaban salon tunanin Xuanxue,rikice rikicen da aka samu sun kawo sharuda masu kyau ga 'yancin tunani,Cigaban da aka samu a fanningadabi kuma shi ne wakoki.

A wannan zamani mu'amala da aka yi tsakanin kasar Sin da kasashen waje ta samu bunkasuwa sosai har ta shafi Japan da Korea a gabas da Asiya ta tsakiya da Daqing(Rome) da bangaren kudu maso gabashin Asiya.

Tun lokacin da aka murkushe daular Jin ta gabas,dauloli na arewa da na kudu sun zama wani halain baraka ne na tsakanin arewa da kudu a tarihin kasar Sin wanda ba a safai ganinsa ba .Da ya ke tattalin arzikin kasa ya kasance cikin halin koma baya,haduwar al'ummai dake bangaren rawayar Kogi ya samu cigaba da ba a taba ganin irinsa ba saboda mallakar kanana kabilu suka yi a tsakiyar kasar Sin.Bisa wannan halin da ake ciki,kanana kabilu da yawa dake arewancin kasar Sin sun hada kansu daga bisani sun zama al'umma daya.Sabo da haka halin baraka dake cikin daulolin arewa da na kudu ya taka muhimmiyar rawa wajen samun al'umma daya,haka kuma wani muhimmin mataki ne maras makawa wajen cigaban al'ummar kasar Sin baki daya.

Daular Sui da ta Tang

A shekarar 581 AD,Yang Jian ya kafa daular Sui ha ya zama sarki Wen,a shekarar 618 aka yi wa sarkin Yang na daular Sui Yang Guang rataye da aka kawo karshen daular Sui mafi karancin zama na shekaru 37 ne kawai a tarihi.Sarki Wen ya fi saura bayar da taimako.Na farko ya sabunta tsarin hakimai,ya soke tsarin hakimai da aka bi a daular Beizhou,ya kafa nasa sabo watau ya kafa sashen sakatariya da ma'aikatu daban daban.Na biyu sarkin Wen ya kafa sabbin dokoki wadanda ba su yi tsananni kamar na dauloli na da ba.Na uku ya kafa wani tsarin daukar hakimai ta hanyar jarrabawa.watau ya sabunta hanyar zabar hakimai.Sarki Yang bai kawo wani abin alheri ga jama'a ba ban da wata magudanawar ruwa da aka haka domin jin dadin zamansa.Sarki Yang sarki ne mafi rishin imani da tasku a tarihi,ya debi haraji fiye da kima daga jama'a,har ma ya fusanta jama'a,daga baya jama'a suka yi masa rataye a birnin Jiandu,ya girba mugunta da ya shuka,daga nan aka kawo karshen daular Sui.

Daular Tang ta shafe shekaru 289 tun lokacin da kafuwarta a shekara ta 618 AD har zuwa lokacin da Zhu Li ya murkushe ta.Zamanin daular Tang ya kasa matakai biyu,Bore da An Lushan da Shi Siming suka ja ragamar yi ya zama iyaka,na gaba matakin samun bunkasuwa,na baya matakin tabarbarewa.Sarki Gaozong ya kafa daular Tang,sarki Taizong Li Shimin ya ja ragamar rundunar soja ya hada kasar Sin baki daya cikin shekaru goma.Bayan da aka yi juyin mulki a Xuanwumen,Li Shimin ya dara kan karagar mulki,ya yi iyakacin kokarinsa ya dukufa wajen mai da kasa ta zama babba mai karfi,ta haka kuwa daular Tang zama kasa mafi wadata a cikin tarihin kasar Sin aka shiga kyakkyawan zamani da ake kira Zhenguang,watau daular Tang tana gaban duniya wajen harkokin siyasa da tattalin arziki da kuma al'adu da sauran fannoni.A zamanin da Sarki Xuanzong Li Longji ke mulki,aka shiga zaman jin dadi da alheri a shekarun da ake kira "kaiyuan",watau kasa ta zama mai karfi jama'a na cikin zaman alheri,zaman jin dadi ya sake bullowa.Duk da haka aka sami boren da madugai An Lushan da Shi Siming ke jagora yayin da sarki Xuanzong Li Longji ke mulki,daga nan daular Tang ta yi tabarbarewa.

A zamanin daular Sui da ta Tang,an samun cigaba wajen kafa dokoki da kundayen ka'idoji kamar su tsarin shirya ma'aikatun gwamnatin tsakiya,da tsarin daukar hakimai ta hanyar jarrabawa,da tsarin buga harji a fannoni biyu,dukkansu suna da tasiri mai zurfi ga zamanin baya baya.A zamanin daular Sui da Tang,aka bi manufar bude kofa ga kasashen waje,mu'amala tsakanin dauloli a tarihin kasar Sin da kasashen waje ta fi bunkasuwa.A fanin adabi,wakokin daular Tang sun fi shahara har wa yau dai mutane ke son karatunsu.Wakilai mawaka su ne Chen Ziang a mataki na farko na daular Tang,Li Bai da Du Fu a matakin samun bunkasuwa,Bai Juyi da Yuan Zhen a mataki na tsakiya,Li Shangyin da Du Mu a matakin karshe.Han Yu da Liu Zongyuan wadanda suka kaddamar da kamfen bin salon rubutu na zamanin da sun fi jawo tasiri ga zuriyar baya baya.Fasahar rubutun sinanci na malami Yan Zhenqing da zane zane na manyan mallamai su Yan Liben da Wu Daozi da Li Sixun da Wang Wei,da raye raye kamar "rawar Nishangyuyiwu" da kide kide da kuma fasahohin kayayyakin da aka gano a ramuka har wa yau dai ana iya same su a kasar Sin.A fanning kimiyya da fasahohi,daga cikin abubuwa guda hudu da mutanen kasar Sin suka kago,fasahar dab'I da albarushi aka kago su a ne a wannan zamani.

Da aka shiga matakin karshen daular Tang aka shiga rikici a cikin harkokin siyasa na daular Tang.Daga lokacin da jam'iyyar Niu Zengru ta yi gardama da jami'iyyar Li Deyu har zuwa lokacin da marmata masu bautawa sarki ke mallaka ikon kasa,an yi ta samun boren manoma,daga baya an sami boren Huang Cao,da farko wani jagaba naboren manoma Zhu Wen ya cin amanar daular Tang,ya nada kansa sarkin Tang har ya kafa gidan sarauta na Liang na baya daga cikin gidajen sarauta biyar a tarihin kasar sin.

Daular Song

A cikin shekara ta 960 ta AD,Zhao Kuangyin ya tayar da boren soja a wurin Chenqiao,ya sami nasarar kafa daular Song ya zama sarkin Taizu na daular nan,daga nan aka sa aya ga halin baraka wanda a ciki akwai gidajen sarauta biyar da kasashe guda goma.A shekara ta 1279 ta AD,Daular Yuan ta cinye daular Song,kasancewar daular Song ta shafe shekaru 319.Zamanin daular Song ya kasa kashi biyu,watau daular Song dake arewa,da daular Son dake kudu.A zamanin da daular Song dake arewa ,da akwai wata kasar Liao da mutanen Khitan suka kafa a arewancin kasar Sin(947-1125),da kasar Xixia da mutanen Dangxiang suka kafa a arewa maso yammaci(1038-1227);A shekara ta 1115,mutanen Nuzhen suka kafa kasar Jin(1115-1234).A shekara ta 1125,daular Jin ta cinye kasar Liao,a shekara ta 1127,sojojin daular Jin suka kai hari ga birnin Kaifei,babban birnin daular Song,suka kwace sarakuna Huizong da Qinzong,daga nan daular Song dake arewa ta wargaza.A wannan lokaci wani sarkin Gaozong da ake kira shi Zhao Gou daular Song ya kama karagar mulki a wurin Yingtianfu dake Nanjing(yau ake kira shi Shangqiu na lardin Henan),daga baya ya tsere zuwa Linan(watau Hangzhou a yau),ya tsugunar da kansa cikin dogon lokaci a kudancin Kogin Yangtse ya kafa daular Song dake kudu.A zamanin Song,zamani ne da kasashe hudu watau Song,Liao,Xia da Jin ke gaba da juna,zamanin daular Song dake kudu,zamani ne da wannan daular ke tabarbarewa.

Bayan da daular Song ta hada arewancin kasar Sin,zamantakewar jama'a da tattalin arziki da kuma al'adu sun samu cigaba,haka kuma ciniki tsakanin kasar Song da kasashen ketare ya sami bunkasuwa.Da ya ke daular Song ba ta cimma burinta na kafa wata daula mai wadata da karfi ta dogon lokaci ta hanyar aiwatar da sabon tsarin mulki da malami Fan Zhongyan ya kawo a shekarar da ake kira "Qingli"( wajen shekara ta 1041 ) da garambawul da malami Wang Anshi ya yi wa tsarin mulkin kasa ba,amma an warware wasu matsalolin dake cikin zamantakewar jama'a na wannan zamani.Boren manoma da Fang La da Song Jiang ke ja ragama ya nuna adawarsu ga mulkin danniya yayin da Huizong ke karagar mulki.Bayan da daular Jin ta cinye daular Song dake arewa,wani sarkin daular Song ya tsugunar da kansa a kudancin kasar Sin,ba shi da dogon burin hada arewancin kasa ba.A wannan zamani,mutanen Khitan sun kasar kasar Liao(947—1125) a arewancin kasar Sin,mutanen Dangxiang suka kafa kasar Xixia (1038-1227)a arewa maso yammacin kasar Song.Kasashen Song da Liao da kuma Xixia suka kasance cikin halin gaba da juna.A shekara ta 1115,mutanen Nuzhen suka kafa kasar Jin(1115-1234)a arewa.A shekara ta 1125, daular Jin ta cinye kasar Liao,a shekara ta 1127,sojojin daular Jin sun shiga birnin Kaifeng,babban birnin daular Song da hari,sun kwace sarakuna Huizong da Qinzong,daga nan daular Song dake arewa ta wargaza.Sarkin Gaozong Zhao Gou ya hau kan kujerar mulki a wurin Yingtianfu a Nanjing(watau Shangqiu na lardin Henan a yau),daga baya ya tsere zuwa Linan(watau Hangzhou a yau),ya tsugunar da kansaa kudanci cikin dogon lokaci,a ganin sarakunan daular Song,yunkurin da shahararen janar Yue Fei ke yi na neman sake hada arewancin kasa da adawa da daular Jin ba kome ba ne illa kare daular Song dake kudu ne kawai.A karshen zamanin daular Song dake kudu,wani babban waziri Jia Sidao ya cin karensa ba babaka cikin harkokin siyasar kasa ,tahaka kuwa aka kara saurin hallaka daular Song dake kudu.

A wannan zamani,nasarorin da aka samu a fanning kimiyya da fasahohi sun jawo hankula,kamar su kamfas(wato agogon nuna arewa),da fasahar dab'I da albarushi,muhimman abubuwa guda uku ne da mutanen kasar Sin suka kirkiro,daga cikinsu fasahar dab'I ta fi ta kasashen Turai dadewa da shekaru 400;Wani irin abun da malami Su Song ya kirkiro domin duba yanayi wajen sufurin kan tekuna,abun nan na farko a duniya;da wani littafin da ake kira "Mengxibitan" da Sheng Kuo ya rubuta suna da muhimmiyar daraja a tarihin kimiyya da fasahohi.A fanin al'adu,darikar neo-Confucian ta fi yaduwa,an samu shahaharun masu bin darikar nan kamar su Zhu Xi da Lu Jiuyuan,darikar Taoist da Buddha da sauran addinan waje su ma suna yaduwa.A zamanin daular Song dake arewa,malami Ouyang Xiu ya wallafi wani littafin tarhi dake kira "Xintangshu",ya ba da babban taimakonsa ga tanadin tarihin daular Tang.Littafin "Zizhitongjian" da malami Sima Qian ya shirya ya zama abun misali wajen rubuta tarihi bisa shekaru.A fannin adabi,an samu marubuta masu farin jini kamar su Ouyang Xiu da Su Shi da mawaka a rubuce kamar su Yan shu da Liu Yong da Zhou Bangyan da Li Qingzhao da Xin Qidi.A zamanin daular Song da Jin an fi samun kagaggun labarai da wasannin kwaikwayo;zane zanen da aka yi su kan siffanta duwatsu da koguna da furanni da tsuntsaye,daga cikinsu wani zane da shahararen malami Zhang Zeduan ya zana dangane da "kasuwar Shanghe a yanayin bazara" har wa yau dai yana da farin jinni a fanning zanezane kasar Sin.

Daular Ming

A shekarar 1368 ta bayyanuwar annabi Isa , Zhu Yuanzhang ya hau kujerar sarki a birnin Nanjing, kuma ya kafa daular Ming. Zhu Yuanzhang ya kasance a kan kujerar nan cikin shekaru 35, ya yi iyakacin kokarinsa don kara inganta ikon da ke karkashin shugabancin tsakiya wanda ke aiwatar da tsarin kama karya na mulkin gargajiya, ya kashe wadanda ke samar da sakamakon bajinta, kuma ya kawar da wadanda ke nuna masa bambancin ra'ayi da kuma kara daga karfin ikonsa na sarki da danne kungiyoyi masu adawa da shi. Bayan mutuwar sarkin nan na farko na daular Ming, jikarsa mai suna Jian Wendi ya hau kujerar sarki, sa'anan kuma ya ci hasara bisa sanadiyar farmakin soja da baffansa mai suna Zhu Lei ya kai masa, daga nan Zhu Lei ya hau kujerar sarki, ana kiran shi "Min Chengzu". A shekarar 1421, an kaura da hedkwatar daular Ming zuwa birnin Beijing.

Kodayake daular Ming ta kara karfin ikon da ke karkashin shugabancin tsakiya, amma wasu sarakuna da yawa sun yi sakaci da aiki, ko kuma wasu suna cikin lokacin yarantaka, ba su iya kula da harkokin mulki sosai, sai wadanda suka yi wa sarakuna aikin hidima sun saci ikon mulki. Sun ci hanci da rashawa, sun yi wa wazirai nagari wulakaci, saboda haka an yi almubazalunci wajen aiwatar da harkokin mulki a kowace rana, kuma sabanin da ke kasancewa a zamantakewar al'umma sai kara tsanani ya ke yi . A tsakiyar lokacin daular Ming, manoma sun yi ta yin tawaye har sau da yawa, amma an danne su duka.

A daular Ming, da akwai wani shahararen dan siyasa da ake kira shi "Zhang Juzheng", domin shawo kan sabanin da ke kasancewa a zamantakewar al'umma da kuma ceton mulkin daular Ming, ya soma yin gyare-gyare. Ya daidaita mulkin da jami'an kananan hukuma suke aiwatarwa da kuma farfado da aikin noma da kiwon tsutsan siliki da gyara hanyoyin koguna, dadin dadawa kuma ya hada da harajoji iri iri da aka buga don su zama iri daya kawai, saboda haka an rage nauyin da ke bisa wuyan jama'a.

A daular Ming, an sami bunkasuwa wajen aikin noma in an kwatanta wannan da na sauran daulolin da suka gabata, kuma sana'ar yin sakar siliki da kera kayayyakin fadi-ka-mutu wato tangaran da haka ma'adinan karfe da yin kayayyaki ta hanyar zuba ruwan tagulla da yin takarda da kera jiragen ruwa da sauransu su ma sun sami yalwatuwa. An kuma sami bunkasuwa wajen yin musanyar tattalin arziki da al'adu da kasashen waje . Wani kwararren zirga-zirgar teku mai suna Zheng He ya yi zirga-zirga zuwa tekun kasa da kasa har sau 7, ya kuma yada zango a kasashe da jihohi fiye da 30. Amma bayan tsakiyar lokacin daular Ming, kasar Sin ta taba shan hare-haren da kasar Japan da Spain da Portugal da Holand da sauran kasashe suka kai mata.

A daular Ming, tattalin arzikin hajoji ya sami bunkasuwa,kuma an soma samun ra'ayin jarin hujja. A farkon shekarun daular Ming, da akwai kungurmin filaye masu yawa da ba a noma ba, kuma ba wanda ke mallake su a zamantakewar al'umma, Sarkin Zhu Yuanzhang wato sarkin farko na daular Ming ya tattara wadanda suke yin zaman galabaita, kuma ya rage harajin da aka buga musu ta yadda yawan manoma da suka yi aikin noma su da kansu suka kara karuwa, kuma bi da bi ne aka shigo da sabbabin ire-iren amfanin gona kamar ganyayen taba da dankali da masara da gyada da sauransu daga kasashen waje. A wannan lokaci, sana'ar hannu tamkar sana'ar yin tangaram da ta saka da sauransu sun riga sun sami bunkasuwa bisa babbam matsayi a kasar Sin. Musamman a wajen sana'ar saka, an samu masu gida da ke da injunan saka fiye da goma da kuma masu sarrafa injunan saka da aka iya hayarsu musamman, wannan ya bayyana cewa, a kasar Sin ra'ayin jari hujja ya soma bullowa. A daular Ming, ana yin hajjoji iri iri da yawa, kuma an yi musanyarsu sosai, sa'anan kuma an kafa cibiyoyin kasuwanni manya da kanana da yawa a wuraren da ke fitar da kayayyaki iri iri da yawa da kuma samun hanyoyin da suka iya hade da sauran wurare masu yawan gaske. Dadin dadawa kuma an sami garuruwa masu wadata da yawa tamkar yadda birnin Beijing da Nanjing da Suzhou da Hangzhou da Kwangzhou da saruansu suke yi.

A daular Ming, an aiwatar da tsarin samun jami'an mulki masu jiran gado ta hanyar jarrabawar rubuta wani irin bayani bisa wani salon gargajiya, wato "Ba Gu Wen". A wannan lokaci, an rubuta kaggagun littattafai masu yawan gaske, wadanda suka hada da littafin da ake kira "Shui Hu Zhuan" , wato sunan littafin nan cikin turanci ake cewa "Heroes the Marshes or Water Margin" da littafin da ake kira "San Guo Yan Yi" kamar dauloli uku ,wato sunansa cikin Turanci ake cewa "The Romance of the Three Kingdoms" , da littafin "Xi You Ji" kamar a ce tafiya zuwa yamma da sunansa cikin Turanci ake cewa "Pilgrimage to the West or Journey to the West" da littafin " Jin Ping Mei" da sunansa cikin Turanci ake cewa "Plum in the Gold Vase" da sauransu. Sa'anan kuma akwai littafin da aka rubuta dangane da yanayin kasa mai suna "Xu Xiake's Travel Notes" cikin Turanci, da Sinanci ake cewa "Xu Xiake You Ji", da kuma littafin da Li Shizhen ya rubuta dangane da ilmin likitanci mai suna "Compendium of Materia Medica" da sinanci ake cewa "Ben Cao Gang Mu" da kuma littafin da Xu Guangqi ya rubuta dangane da aikin noma mai suna "Complete Treatiseon Agriculture " da Sinanci ake kira "Nong Zheng Quan Shu" da littafin da Son Yingxing ya rubuta dangane da ilmin fasaha mai suna " Tian Gong Kai Wu" ko ma ake cewa binciken ayyuka halitta , cikin turaci ake cewa sunansa "Exploitation of the Works of Nature" da kuma wani kamus da ake kira "Yong Le Da Dian" wato babban kundin sani na daular Ming , cikin turanci ake cewa "Great Encyclopaedia of Yongle of the Ming Dynasty" da sauran shahararrun littattafai.

Bayan karshen daular Ming, halin da ake ciki na tattara gonaki a hannun wasu mutane na da tsanani sosai, gonaki na fadar sarki da na kananan sarakuna sun shimfidu a koina a kasar Sin, harajin da gwamnati ta buga sai kara yawa yake yi a kowace rana, sabanin da ke kasancewa a cikin zamantakewar al'umma sai kara tsanani yake , wasu jami'ai da sauran wasu masu fasaha suna son shawo kan sabanin da ke kasancewa a zamantakewar al'umma, sun nemi a kayyade ikon musamman na jami'an da suka yi wa sarakuna hidimar aiki da na manyan rukunoni , sun ba da lacca da kuma tattauna harkokin siyasa, ana kira su da cewa " 'yan Donglin Clique", amma wadanda suka yi wa sarakuna hidimar aiki suka yi musu wulakanci mai tsanani sosai, wannan ya kara kawo rashin kwanciyar hankali a zamantakewar al'umma.

Gwagwarmayar da aka yi a kauyyuka ita ma tana kara tsanani, a shekarar 1627, an barke da bala'I a hardin Sha'anxi, jami'ai sun tilasta wa mutane su biya harajin da aka buga musu, saboda haka jama'a farar hula sun tashi tsaye sun yi tawaye. Jama'a masu fama da 'yunwa dubu daruruka sun kafa rundunonin soja daban daban don yin tawaye. A shekarar 1644, rundunar soja ta manoma masu yin tawaye sun kai hari kuma sun shiga cikin birnin Beijing, sai sarki mai suna Chong Zheng ya kashe kansa.

Daular Qing

Daular Qing tana da tsawon shekaru daga 1644 zuwa 1911.Tun daga lokacin da Nurhachi ya soma hawa kujerar sarki har zuwa lokacin sarkin daular Qing na karshe wato Aisin Gioro Puyi, yawan sarakuna ya kai 12. In ana yin kidayya daga lokacin shigar su daga wurin da ake kira "Shanhaiguan", wato shiga cikin babban yankin kasar Sin, ana iya cewa, yawan sarakunan daular Qing ya kai goma ke nan, yawan shekaru da daular Qing ta kasance cikin kasar Sin ya kai 268.

Yawan fadin yankunan da ke karkashin mulkin daular Qing ya kai murraba'in kilomita 1200 ko fiye a lokacin da fadin taswirarta ya fi girma a tarihi. A shekarar 1616, Nurhachi ya kafa daular Jin ta karshe. A shekarar 1636, Huangtaiji ya gyara sunan kasar don ta zama sunan Qing. A shekarar 1644, rundunar sojoji manoma ta Li Zicheng ta tumbuke mulkin daular Ming, kuma sarkin daular Ming wato Chong Zheng ya kashe kansa. Saboda haka rundunar soja ta daular Qing ta sami damar fatattakar rundunar sojoji manoma, sa'anan kuma ta kafa hedkwatar kasar a birnin Beijing. Bi da bi ne fadar Qing ta danne tawayen da manoma na wurare daban daban suka yi da dagiya da dakaru na daular Ming ta kudancin kasar Sin suka yi wa daular Qing, a kai a kai ne ta dinke duk kasar Sin gu daya.

A farkon lokacin daular Qing, an aiwatar da manufar nuna yabo ga wadanda suka sari sabbabin gonaki da kuma rage harajin da aka buga don sassauta sabanin da ke tsakanin rukuni rukuni, tattalin arziki da aka yi a babban yankinta da iyakacin kasar su ma sun sami bunkasuwa . Ya zuwa tsakiyar karni na 18, tattalin arziki na mulkin gargajiya ya sami bunkasuwa har zuwa wani sabon matakin koli a tarihi ,an bayyana cewa, wannan lokaci ya zama lokaci ne na samun wadatuwa sosai a karkashin mulkin sarkin Kangxi da Yongzheng da Qianlong. Tsarin kama karya na tattara ikon mulki a karkashin shugabancin tsakiya ya kara tsanani, kasar kuma ta kara karfi, kuma odarta ta kara kasancewa cikin zaman karko, ya zuwa karshen karni na 18, yawan mutane na daular Qing ya kai wajen miliyan 300.

A shekarar 1661,Zheng Chenggong ya jagoranci jiragen ruwan yaki don ketaren teku zuwa zirin Taiwan, ya fattataki 'yan mulkin mallaka na Holand wadanda suka mamaye Taiwan a cikin shekaru 38 da suka wuce. A farkon shekara ta biyu, 'yan mulkin mallaka na Holand sun ba da kai, daga nan Taiwan ta komo a karkashin mulkin kasar mahaifa.

A karshen karni na 16, "Tsarist Russia" ya kara habaka zuwa gabashinsa. Lokacin da rundunar soja ta daular Qing ta shiga cikin babban yankin kasar Sin daga wurin da ake kira "Shanghaiguan", "Tsarist Russia" ya sami damar mamayen wurin da ake kira Yakesa da Nibuchu da sauran wurare. Ba sau daya ba ba sau biyu ba gwamnatin Qing ta nemi 'yan mamaye na"Tsarist Russia da su janye jikinsu daga yankunan kasar Sin. A shekarar 1685 da shekarar 1686, Sarki Kangxi ya ba da umurni ga rundunar soja ta daular Qing don kai farmaki har sau biyu kan rundunar soja ta "Tsarist Russia" da ke Yakesa, rundunar soja ta Rasha ta ga tilas ne ta yarda da daidaita batun iyakar kasa da ke yankin gabas na tsakanin kasar Sin da Rasha ta hanyar yin shawarwari . A shekarar 1689, wakilan bangarori biyu wato Sin da Rasha sun yi shawarwari a wurin da akr kira Nibuchu, kuma sun daddale yarjejeniyar farko kan iyakar kasa wato yarjejeniyar Nibuchu.

A tsakiyar lokacin mulkin sarkin Qianlong, an wargaza tawayen da 'yan a-ware na Ge Erdan na rukunin Zhungeer da 'yan rukunin kabilar Hui manya da kanana da Zhuo suka yi, sa'anan an dinke jihar Xinjiang, kuma an tsara manufofi a jere, an raya tattalin arziki da al'adu da sufuri a jihar Xinjing.

Kafin sarkin Daoguang na daular Qing, sakamakon da aka samu wajen al'adu na da yawan gaske. An samu wasu shahararrun masana kamar su Wang Fuzi da Huang Zongxi da Gu Yanwu da Dai Zhen da sauransu da kuma shahararrun mawallafa da masu fasaha da suka hada da Cao Xueqin da Wu Jingzi da Kong Shangren da Shi Tao da sauransu. Sakamakon da aka samu wajen ilmin tarihi na da yawan gaske, shahararrun masanan binciken mafarin haifar da abubuwa suna ta fitowa daga zuri'a zuwa zuri'a, kuma an rubuta littafin da ake kira"Complete Library In the Four Branches of Literature" da "Collection of Books Ancient and Present da sauran manyan littattafai wadanda hukumar gwamnati ta shirya mutane da su rubuta su. Wajen kimiyya da fasaha, an kuma samu sakamako da yawa, daga cikinsu, sakamakon da aka samu daga wajen ayyukan gine-gine ya fi sauransu ci gaba.

A daular Qing, tattalin arziki yana dogara bisa aikin noma, wato an mai da ayyukan noma a matsayin ginshikin kasa. A wajen al'adu da tunani, an gabatar da muhimman abubuwa da suka ba da jagora ga ladabin da aka bi na irin mulkin gargajiya, kuma ba sau daya ba ba sau biyu ba an kafa "Imprisonment or Execution of an Author for Writing Sth"; Wajen huldar harkokin waje, ta rufe kofarsa ga kasashen waje,kuma ta nuna girman kai sosai da sosai.

Bayan tsakiyar daular Qing, sabane-sabanen da ke kasancewa a zamantakewar al'umma sai kara bullowa ke yi a kowace rana, gwagwarmayar da aka yi don yin adawa da mulkin daular Qing tana ta kara tsanani, daga cikinsu tawayen da aka yi bisa akidar addinin Bailian ya kawo karshen lokacin samun wadatuwa na daular Qing.

A shekarar 1840 da aka yi yakin Opium da hare-haren da kasashe masu kama karya suka yi bayan yakin nan, fadar daular Qing ta daddale yarjejeniyoyi da yawa ba bisa adalci ba tare da mahara, ta yi amfani da yankunanta don biyan kudadden diyya , ta bude hanyoyin kasuwanci da tashoshin ruwa, a kai a kai ne kasar Sin ta zama zamantakewar al'ummar aiwatar da guntun mulkin gargajiya da guntun mulkin mallaka. A karshen lokacin daular Qing, an yi alumbazzaranci wajen siyasa, tunani kuma ya ki ci gaba, kuma an kasance cikin rashin karfi da rashin karfin gwiwa, kai,daular ta shiga lokacin tabarbarewa da gurguntaka .Jama'a sun kasance cikin fama da mawuyacin hali, saboda haka an bullo da gwagwarmaya da yawa a jere don yin adawa da kasashe masu kama karya da mulkin gargajiya, kamar harkar "Taiping Tian Guo" wato " Taiping Heabenly Kingdom" da ake kira cikin Turanci da tawayen da rundunar soja ta Nian ta yi da dai sauransu. Don ceton ransu, rukunoni masu mulkin kasa sun soma gyare-gyare a jere a cikinsu, wato "Westernization Movement" da "Reform Movement of 1898" da sauransu, sun yi fatan kasar Sin za ta kama hanyar samun wadatuwa tare da 'yancin kai ta hanyar yin gyare-gyare daga sama zuwa kasa, amma a karshe dai sun ci harasa dukka. Jarumai da masana masu yawan gaske sun yi fama tare da zuba jini don ceton kasar Sin daga rikicin al'umma, suna ta ci gaba da fama ba tare da kasala ba. Suna yin aikace-aikacen kishin kasa da ba a taba ganinsu ba a cikin tarihin zamanin da muke ciki. A shekarar 1911, an tumbuke mulkin daular Qing, daga nan an kawo karshen mulkin da sarakuna na gargajiya suka yi a cikin shekaru fiye da dubu 2, kasar Sin ta shiga cikin wani sabon mataki a tarihi.

>>[Mashahuran Littattafan Tarihi]

'Dabarun yaki na Malam Sunzi'

Littafi mai suna "Dabarun yaki na Malam Sunzi" wani littafi ne mai girma da ke bayyana hasashen sha'anin soja na tsohon zamanin da, wanda kuma ya zama daya daga cikin litattafai na tsohon zamanin da na kasar Sin da ke da babban tasiri cikin gamayyar kasa da kasa kuma ke yaduwa sosai. Dabaru da ilimin falsafa da aka bayyana cikin littafin nan, an yi amfani da su kan fannoni da yawa, kamar sha'anin soja da siyasa da tattalin arziki.

Kafin shekaru 2500 ne aka buga littafi mai suna "Dabarun yaki na Malam Sunzi", ya zama wani littafi na bayyana hasashen sha'anin soja na tun wurwuri cikin gamayyar kasa da kasa wanda kuma ya zo wajen shekaru 2300 kafin wani littafi mai suna On War da Malam Clausewitz na Turai ya wallafa.

Mawallafin littafin "Dabarun yaki na Malam Sunzi" malam Sunwu, shi wani babban dan sha'anin soja na daular Chun Qiou na kasar Sin, an yi masa girmamawa da kiransa "mai kasaitan soja" ko " mai kasaitar yaki" cikin tarihin kasar Sin. A shekarun can da, domin gujewa yake-yake, Malam Sunwu ya yi gudu zuwa kasar Wu, sai sarkin daular Wu ya nada shi da ya zama babban janar , malam Sunwu ya shugabanci sojoji wajen dubu 30, sun ga bayan sojoji masu yawan dubu 200 na kasar Chu, daga nan dai sunansa ya shahara cikin sauran kananan kasashe. Malam Sunwu ya takaita fasahohin da aka samu cikin yaki a karshen shekarar daular Chun Qiou na da, ya wallafa littafi mai suna "Dabarun yaki na Malam Sunzi", wanda a ciki ya nuna dokokin sha'anin soja a jere , har ya gabatar da wani cikakken tsarin hasashen sha'anin soja.

Littafin " Dabarun yaki na Malam Sunzi" yana da babbaku sama da dubu 6, wanda ya kasa bayanai guda 13, cikin kowane bayani an bayyana wani babban hasashe. Alal misali, cikin bayani mai suna ? Dabaru ?, an bayyana batu na ko za a iya yin yaki. Cikin bayanin an nuna dangantakar da ke tsakanin yaki da halin siyasa da tattalin arziki, da gabatar da manyan abubuwa guda 5 da ke kudura samun nasara ko cin hasarar yaki, wato siyasa da lokaci mai dacewa da wuraren da ake samun saukin yin yaki da hafshoshi da dokokin shari'a, abu na farko daga cikinsu shi ne siyasa. Bayanin mai suna ? Yin yaki ?, ya bayyana ta yaya za a yi yaki. Cikin bayani mai suna ? Dabarun kai farmaki ? , an nuna ta yaya za a kai farmaki ga kasar makiya. Malam Sunwu ya tsaya a kan cewa a yi sadaukarwa kankani don samun nasara mai girma, wato a nemi samun nasara ba tare da yin yaki ba, a kwace garin makiya amma ba a kai farmaki sosai ba, a ga bayan kasar makiya, amma ba a yi yaki na dogon lokaci ba. Domin cim ma burin nan, musamman ya tisa magana kan a yi dabaru don samun nasara, ya nuna cewa, dabara mai kyau wajen shugabancin sojoji ita ce samun nasara ta dabarun siyasa, na biyu shi ne ta hanyar diplomasiyya, na uku shi ne samun nasara ta nuna karfin tuwo, dabara ta karshe ita ce kai farmaki. In ana son aiwatar da ? dabarun kai farmaki ? ba ma kawai sun san hakikanin karfi na kansa ba, har ma wajibi ne a san halayen bangaren abokan gaba. Cikin bayani mai suna ? Cin gajiyar 'yan lekan asiri ?, Malam Sunwu ya nuna cewa, in da farko ana son sanin halin da makiya ke ciki, to a fi mai da hankali kan tura 'yan lekan asiri don samun labari na fannoni.

Cikin littalin ? Dabarun yaki na malam Sunzi ? an bayyana wasu tunanin falsafa masu daraja. Alal misali, maganar da ke cewa, a san makiyi kuma a san kansa sosai, ta haka za a iya cin nasara har cikin yakin da aka yi sau da yawa , sai maganar ta zama mutane sukan fadi yau da kullum. A cikin ? Dabarun yaki na Malam Sunzi ? an bayyana azurtattun tunani na karin harshe, cikin littafin an yi tattaunawa kan abubuwan da ke da sabani da kuma wanda ke canzawa dangane da yaki, kamar makiyi da gefe nawa, masauki da baki, masu yawa da marasa yawa, masu karfi da marasa karfi, kai farmaki da yin tsaro, samun nasara da kwasar hasara. Littafin ? Dabarun yaki na Malam Sunzi ? ya gabatar da babban tsare-tsare da dabaru na yaki duk bisa sanadiyar yin bincike kan sabane-sabane da halayen sauyawarsu. Daga ciki an bayyana tunanin karin harshe wanda ya dauki wani muhimmin matsayi da aka samu cikin tarihi na falsafa na gargajiya na kasar Sin.

Littafi ? Dabarun yaki na Malam Sunzi ? ya tattauna kan sojoji da yaki, ya tattara sakamako na dabarun yaki da na makirci, wadanda masanan sha'anin soja sukan yi amfani da su, wasu sunayen dabaru da tatsuniyoyin tsohon zamani da ke cikin littafin, har mata da yara cikin kasar Sin sun san su sosai. A cikin littafi ? Dabarun yaki na Malam Sunzi ? an bayyana cikakkun tsarin soja da tunanin falsafa, da hasashen falasafa masu zurfi, da dabarun yaki da na babban tsare-tsare da ke sauyawa sosai, sabili da haka akan yi nazari, kuma akan kara fahimtarsu, har littafin ya yi babban tasiri cikin darikar tunanin sha'anin soja na gamayyar kasa da kasa, kuma na samun kwar jini sosai. An fassara littafin nan zuwa harsuna 29, kamar Turanci da Rashanci da Jamusanci da Japansanci, yanzu an kasance da littafin da aka daba'a sama da dubai cikin gamayyar kasa da kasa. Har wasu kwalijin soja na wasu kasashe sun dauki littafin ? Dabarun yaki na Malam Sunzi ? da ya zama littafin darusa. An bayar da labari cewa, har cikin lokacin yin yakin Parisa a shekarar 1991, bangarorin da ke yakekeniya , sun nazari littafin ? Dabarun yaki na Malam Sunzi ?, don su tsamo tunanin soja daga ciki ta yadda za a yi jagorancin yakin.

A da'irori da yawa kamar zamantakewar al'umma da kasuwanci, an kuma yi amfani da tunani na cikin littafin ? Dabarun yaki na Malam Sunzi ?. Wasu masana'antu da 'yan kasuwa na kasar Sin da na gammayar kasa kasa sun sa tunanin da ke cikin littafin ? Dabarun yaki na Malam Sunzi ? cikin aikin kula da harkokinsu da sayarwa cikin kasuwanci, littafin soja ke ba da amfani kan aikin kasuwanci, wato ya ba da gudumawa sosai.

'Bayanai Na Tarihi'

'Bayanai na Tarihi', wani babban littafi ne a cikin tarihin kasar Sin, kuma wani kasaitaccen littafi ne na rubutaccen tarihin rayuwar wani mutum, wanda kuma ya ba da tasiri mai zurfi ga adabi na bayan ziriyoyin kasar Sin. An rubuta wannan littafin ' Bayanai Na Tarihi' a zamanin Han ta Yamma na hijira ta farko kafin bayyanuwar Annabi Isa alaihim salam, wanda ya kunshi abubuwa na tsawon shekaru dubu uku na can zamanin da a fannin siyasa, da tattalin arziki, da al'adu da kuma na tarihi.

Kafin mu bayyana babban sakamakon da wannan littafi na ' Bayanai na Tarihi' ya bayar adabin kasar Sin, bari mu dan gutsura muku wani gajeren bayani game da marubucinsa Malam Si Maqian. Malam Si Maqian, dan ilmin tarihi kuma mawallafi ne na zamanin Han ta Yamma na kasar Sin. An haife shi ne a cikin wani iyalin masanin ilmin tarihi ; babansa wani karamin jami'i ne na daular Han ta Yamma. Malam Si Maqian yana da kaifin ido tun yana yaro, wato yakan fito da ra'ayi irin na musamman kan wassu mutane da lamura na tarihi. Lokacin da yake saurayi, Malam Si Maqian ya yi zirga-zirga ko' ina na daular, inda ya sa ido kan halayen gargajina na wuri daban daban da kuma yanayin zamantakewar al'umma, da tattlin arziki da kuma na aikin kawo albarkar noma ; Ban da wannan kuma Malam Si Maqian yakan ziyarci ni'imtattun wurare da kuma shahararrun wuraren tarihi, inda yakan dauki labarai dangane da mashahuran mutane da al'amuran tarihi. Daga baya dai, Malam Si Maqian ya gaji sha'anin babansa ya zama wani jami'i na dakin sarauta. A wannan lokaci ne ya kuduri aniyar rubuta wani babban littafin tarihi. Amma kuwa an yanke masa hukuncin daurin rai cikin dakin sarauta sakamakon wassu lamuran siyasa da suka wakana. Lallai wannan ya barana lafiyar jikinsa da kuma bata halin ziciyarsa ainun. Ko da yake daga baya an sake ba shi babban mukami, amma babu sha'awar zama jami'I gare shi, wanda a ganinsa cewar abu mafi muhimmanci shi ne kammala aikin rubuta littafin ' Bayanai Na Tarihi'. Malam Si Maqian ya shafe shekaru goma sha uku yana rubuta wannan littafi wanda ke da babi dari da uku da kuma babbaku dubu dari da hamsin.

Malam Si Maqian ya kasa babban littafin nan cikin kashi biyar. Kashi na farko, shi ne tarihin farfadorwar sarakuna da muhimman al'amuran tarihi ; Kashi na biyu, shi ne manyan matsalolin da suka wakana a kowane lokacin tarihi ; Kashi na uku, shi ne bayanan musamman kan ilmin taurari, da dokokin kalanda, da ayyukan tsare ruwa, da tattalin arziki da kuma al'adu da dai sauransu ; Kashi na hudu, shi ne harkoki da kuma abubuwan yabo na masarautun dauloli na da ; Kashi na biyar wato na karshe, shi ne rubutaccen tarihin rayuwar wassu shahararrun mutane na da'irori daban daban na dauloli na da.

Har kullum akan kira littafin ' Bayanai na Tarihi' a kan cewa littafin ' Hakikanan bayanai, wanda kuma ya kunshi abubuwa da yawa kamar na siyasa, da tattalin arziki, da sha'anin soja, da al'adu, da ilmin taurari da labarin kasa, da kuma na abubuwan gargajiya da dai sauran makamantansu. Lallai littafi ya kasance tamkar wata duniyar tarihi mai ban sha'awa. Abun da ya cancanci a yi yabo a kai, shi ne a cikin littafin nan Malam Si Maqian ya gatsa wa rukunonin mulkin koli na daular Han yayin da yake bayyana yadda dimbin jama'a suka yi dagiya da mulkin dauloli masu keta ; Dadin dadawa, Malam Si Maqian ya nuna yabo kwarai da gaske ga wassu ' yan kishin kasa da jarumai.

Ko shakka babu babban littafi na ' Bayanai na Tarihi' yana da daraja sosai ga aikin wallafe-wallafe, wanda kuma ya kasance babbar nasara ce da aka samu wajen rubutun littattafan tarihi na kasar Sin.

>>[Zamanain da aka samu yalwa a cikin tarihin kasar Sin]

Zamanai biyar da aka samu yalwa a cikin tarihin kasar Sin

A cikin tarihi na tsawon shekaru dubu biyu ko fiye na mulkin gargajiya na kasar Sin, an taba samun zamanai guda biyar da aka samu yalwa a tarihi, wato zamani na daya shi ne lokacin mulki na sarki Wu na daular Han ; Na biyu shi ne lokacin mulki na Kai Yuan na daular Tang ; Na uku shi ne lokacin mulki na Yongle da na Xuande na daular Ming ; Zamani na hudu shi ne lokacin mulki na sarki Kangxi da na sarki Yongzheng da kuma na sarki Qianlong na daular Qing ; Na biyar wato na karshe, shi ne lokacin mulki na Zhangguo, wanda ba safai akan ji labarinsa a da.

Wadannan zamanai guda biyar da aka samu yalwa a tarihin kasar Sin, dukansu sun kasance cikin lokutan da sabbin dauloli matasa suke mallaka bayan rikici-rikicen da aka yi a tsoffin dauloli ; kuma wadannan zamanai suna da sigar musamman iri daya, wato samun dinkuwar kasa daya, da bunkasuwar tattalin arziki, da kyakkyawan yanayin siyasa, da zaman lafiya mai dorewa na zamantakewar al'umma, da kasa mai kasaita da kuma yalwatuwar al'adu.

Tuni a zamanin Chun Qiu, ' Komai na tabarbarewa'. Malam Confucius yana kiran zamanin nan a kan cewa ' Zamani Mai Rikici' ; Amma irin wannan halin da ake ciki a zamanin ya shaida, cewa za a haifar da sabon tsari maimakon tsohon tsari. A zamanin Zhanguo, shahararrun ' yan siyasa Li Kui da Wu Qi sun yi kwaskwariman dokoki bi da bi a kasashen Wei da Chu ; A tsakiya da kuma karshen zamanin nan, kasashen Qin, da Han, da Qi, da Zhao da kuma Yan su ma sun zama kasashe masu kasaita sakamakon kwaskwariman dokoki da suka yi, musamman ma kwaskwariman dokoki da shahararen dan siyasa Shangyang ya yi a kasar Qin daga dukan fannoni, wadda kuma ta fi sauran kasashe shida kasaita, a karshe dai ta hadiye su. Ko da yake ya kasance da bambancin matsayin kwaskwariman dokoki da aka yi a wadannan kasashe, amma duk da haka, sun kammala kwaskwarimar tsarin zamantekewar al'ummarsu, wato ke nan sun kafa tsarin mulkin gargajiya maimakon tsarin bauta.

Kasar Qin ta hadiye sauran kasashe shida wato ta kasance wata babbar kasa kacal, wadda sarki Yingzheng ke mallakarta. Wannan dai sakamako ne na ci gaban tarihin zamanin Chunqiu da na Zhanguo.

Bayan kasar Qin ta hadiye kasashe shida, sai sarki Yingzheng na kasar ya yi watsi da tsarin kananan masarautu da kuma aiwatar da tsarin kafa gundumomi, wato shi kansa ne ke mallakar harkokin duk kasar. Lallai sarki Yingzheng ya tabbatar da hasashen ' dinkuwar kasa gaba daya', wanda ake ba da shawarar aiwatar da shi tun daga zamanin Chunqiu. Daga baya dai, maganar dinkuwar kasa gaba daya da jawo mata baraka ta zama daya daga cikin ka'idojin da akan bi wajen yanke shawara kan yalwatuwar zamantakewar al'umma. Amma duk da haka, kada a ce duk wanda ke neman dinkuwar kasa yana da gaskiya kuma duk wanda ya jawo baraka laifi ne ya yi. A'a, ba haka ba. Idan wata daular sarauta ta lalace sosai wadda kuma ta kawo cikas ga bunkasuwar aikin kawo albarka, to dole ne manoma sun yi bore, wato ke nan sun ' jawo baraka' ga dinkuwarta gaba daya; Labuddah wanna ya zama wajaba, kuma ya kamata a amince da shi ko a iya cewa wannan dai ' wani al'amari ne mai kyau'. Marigayi shugaba Mao Tsedong ya taba nuna yabo sosai ga amfani mai yakini na boren da manoman kasar Sin suka yi; Babu tantama, dinkuwar kasa gaba daya za ta taso bayan da aka jawo mata baraka kamar yadda aka fadi cewa ' Haduwa ta zama wajaba bayan rabuwar da aka yi cikin dogon lokaci', wannan dai doka ce ta yalwatuwar tarihin kasar Sin. Dalilin da ya sa aka amince da hasashen ' dinkuwar kasa gaba daya' shi ne domin ya samar da wani kyakkyawan muhallin zamantakewar al'umma da kuma taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa aikin kawo albarkar kasa da kuma kyautata zaman rayuwar jama'a.

Lokacin mulkin sarki Wen a hijira ta 179 zuwa 157 kafin haihuwar Annabi Isa alaihi salam, da lokacin mulkin sarki Jing a hijira ta 156 zuwa 141 kafin haihuwar Annabi Isa alaihi salam da kuma lokacin mulkin sarki Wu na daular Xi Han a hijira ta 140 zuwa 87 kafin haihuwar Annabi Isa alaihi salam, lokaci ne na yadada yankunan kasa.

An samu habakawa daban a daular Tang bayan daular Han. A wancan zamani, sojojin daular Tang sun hallaka sojojin Turkstan ta Gabas dake arewa maso yammacin kasar; ban da wannan kuma sun murkushe sojojin Korea a arewa maso gabashin kasar; Saboda haka ne, aka tabbatar da dinkuwar kasa gaba daya a daular Han da daular Tang, wanda ba a taba ganin irinsu ba a cikin tarihi. Wadannan dauloli, muhimman zamanai ne guda biyu da aka habaka girman kasar Sin.

Ina ma'anar zamanin da aka samu yalwa na Kai Yuan? Bari mu dan gutsura muku wani gajeren bayani kan tarihin sarki Li Longji na daular Tang. A wancan zamani, sarki Li Longji yana so ya zama wani sarki mai idon basiri. Bayan ya hau kan kujerar sarkin daular, sai ya dukufa wajen tafiyar da harkokin kasa don gwada gwanintarsa a fannin siyasa; Ban da wannan kuma ya yi namijin kokari wajen rage yawan hukumomi da jami'ai na daular da kuma yin jarrabawar masaurata. To, bayan da sarki Li Longji ya yi gyare-gyare cikin himma da kwazo, sai aka kyautata halayyar masaurata wadanda kuma suke cikin kuruciya; Sakamakon haka, dukkan hukumomin daular suna tafiyar da harkokin kasa kamar yadda ya kamta; Ban da wannan kuma sarki Li Longji ya ba da umurnin rarraba wa talakawa gonakan da wassu masaurata suka kwace ba bisa doka ba. Da yake sarki Li Longji ya dauki tsauraran matakai a jere, shi ya sa aka samu babban ci gaban sha'anin noma. Ga manoma suna aikin noma tare da nuna himma, wadanda kuma sukan samu girbi mai armashi a kowace shekara. Bugu da kari kuma, aka samu wadata a fannin kasuwanci, da sana'ar hannu ,da al'adu, da kuma na kimiyya da fasaha. Dadin dadawa, dimbin ' yan kasuwa da manzannin musamman na kasashen waje ciki har da kasar Iran sukan zo daular Tang domin yin ziyarar sada zumunta. Yayin da sarki Li Longji yake kyautata harkokin gida da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa, ya kuma yi matukar kokari wajen jan damara don tsaron kasa. Bayan da sarki Li Longji ya shafe shekaru fiye da goma yana tafiyar da harkokin kasa, sai daular Tang ta zama wata kasa mai wadata wadda kuma ta shahara a duk duniya kuma jama'a suna zaman alheri.

A daular Ming, an kai farmaki kan sojoji ' yan asalin daular Yuan daga arewa da kuma arewa maso gabashin kasar, a karshe dai sun sarrafa wuraren dake kudanci da kuma arewancin babbar hamada; Ban da wannan kuma, kasashen da suka yi makwabtaka da ita kamar su Annan, da Seluo da kuma Korea dukansu kasashe ne dake cikin hannun daular Ming. Amma, daga wancan gefe, kasar Mongoliya ce ta sarrafa wuraren dake arewa da kuma arewa maso yammacin Babbar Ganuwa ta kasar. Bisa abubuwan da aka rubata cikin littafin tarihi, an ce, ban da daular Yuan, sai daular Qing ita ce kadai ta kasance dinkuwar kasa mai fadi ainun. Sarki Yongzheng na daular Qing ya yi alfaharin cewa ' ya kasance da daula tawa ita kadai mai kasaita kamar haka ko a cikin gida ko a kasashen ketare tun shekaru aru-aru da suka shige'. Amma a zahiri dai, sai sarki Qianlong na daular Qing ne ya kwantar da kura a shiyyar Zhun Ger da ta hada da lardin Qinghai da sashen kudu da na arewa na jihar Xin Jiang da kuma jihar Tibet, a karshe dai ya mallaki harkokin duk kasar wadda ke da kabilu da yawansu ya zarce hamsin.

Sarki Kangxi da sarki Qianlong na daular Qing sun yalwata hasashen ' Dinkuwar kasa gaba daya' bayan sun yi watsi da tsohuwar akida. Sarki Kangxi ya yi watsi da aikin gina Babbar Ganuwa tun bayan ya hau kan kujerer mulkin Daular Qing. Sakamakon haka ne, aka kawar da katangar da ta kasance cikin shekaru dubu biyu da suka shige, wato ke nan ya tabbatar da dinkuwar kasa gaba daya. Yin haka, ya aza harsashi ga zana taswirar kasar Sin ta zamanin yanzu da kuma kafa wata kasa mai yawan kabilu.

A kowane zamanin da aka samu yalwa a cikin tarihin kasar Sin bisa shararin ' Dinkuwar kasa gaba daya', an tabbatar da samun zama mai dorewa na zaman al'umma, da garbi mai armashi da kuma makudan kudade. Littafin tarihi ya ce, daga daular Tang da daular Ming zuwa daular Qing, jama'a suna da isasshen abinci da sutura.

>>[Abubuwan mamaki na tsohon zamani]

Me ya sa Mr.Xu fu na kasar Sin ya je kasar Japan

Bayan da Qin Shihuang ya hau karagar mulkin sarki, sai yana son ci gaba da kuruciya har abada, wato ba ya son yi tsuffa ko ya mutu, yana matukar kokari neman wani magani da hana mutun ya tsuffa ko mutuwa. Da ya ji labarin cewa, a tekun dake gabashin kasa, akwai wani tudu mai ban al'ajabi, kuma a kan wannan tudu akwai wani ciyayyin magani, in an ci wannan magani shi ba zai yi tsuffa ba har abada, sai wannan babban sarki ya aike da wani karamin jami'in da ya je tekun nan don neman samu ciyayyin magani, amma shi bai gano wannan wuri ba. Har yanzu dai a wani lambun shan iska dake birnin Qinhuan dao, ana iya gani wurin tunawa da bakin shiga teku da Qin Shihuang yake neman ciyayyin maganin tsuffa. A shekara ta l992, a wurin nan ne mutane suka kafa wani babban sakakken dutsen Qin Shihuang tsawonsa daga kasa zuwa sama ya kai mita 6.

Kodayake wannan karamin jami'I bai gano wurin kasance da ciyayyin maganin tsuffa ba, amma Qin Shihuang yana son ci gaba da nemawa, sai ya aike da wani karamin jami'I daban mai suna Xu fu don ci gaba da neman wannan ciyayyin magani. A karo na farko ne Mr.Xu fu ya je wannan teku sai ya dawo ya gaya wa wannan Qi Shihuang cewa, ya riga ya gano wannan ciyayyin magani dake wani tudu na teku, ya kuma hau wannan tudu, amma wani mutu na al'ajabi ya gaya masa cewa, in an so samu magani ya kamata a mika masa tsaraba da yawa,Kuma dole ne a zabi nagartattun maza da mata da masu sakake da aike su zuwa wurin nan. A lokacin da Qin Shihuang ya ji haka, sai cike da farin ciki, kuma nan da nan ya zabi nagartattun yara maza da mata da wadansu ma'aikata masu fasahar sakakke dake karkashin jagorancin Mr.Xu fu don je wannan wurin neman magani. Amma bayan da wannan mutun mai suna Xu Fu ya yi zagaya a kan teku, shi bai samu irin magani ba, sai ya gaya wa Qin Shihuang cewa, dalilin da ya sa a wannan gami shi bai samu irin magani domin a cikin teku akwai wani babban kifi da ya hana jiragen ruwa namu da mu yi kusa da wannan babban tudu mai ciyayyin magani. Da Qin Shihuang ya ji haka, sai ya amince da maganarsa, ya sake tura masu harbe da makamai da yawa, kuma shi kansa ya ba da jagora ga mutanensa don je wannan teku da neman samu magani. A daidai wannan lokaci ne wannan Qin Shihuang ya yi wani mafarki cewa, shi ya yi fama da wannan babban kifi wato kaman dodo. Amma a lokacin da gwanon jiragen ruwa ya zo wurin kusa da wani tsibiri sai ya gamu da wani babban kifi kaman dodo, sai wannan Qin Shihuang shi kansa ya harbe wannan babban kifi. A kan haka ne a kan hanyarsa babu wani mahani ba, amma wannan mutun mai suna Xu Fu har yanzu bai gano wani wurin dake kasance da irin ciyayyin maganin tsuffa ba, sai wannan mutun ya yi tsoro sosai domin bai samu magani kuma yana tsoron sake koma wurin Qin Shihuang, sai ya ba da jagora ga nagartattun yara mata da maza da wadansu ma'aikata masu fasahar sakakke dubu uku sun je kasar Japan, a wurin can ne suke yin zaman rayuwarsu daga zuri'a zuwa zuri'a, a karshe dai wannan mutun mai suna Xu Fu ya mutu a babban tudu mai suna Fushi na kasar Japan.

A kasar Japan akwai tatsuniyoyyi da yawa game da wannan tsohon mutun mai suna Xu fu, mutane na kasar Japan suna barbaza wannan labari daga zuri'a zuwa zuri'a. Har wadansu kwararru suna gani cewa, Mr.Xu Fu shi ne shahararren sarkin kasar Japan. Kuma mutane na kasar Japan sun mai da wannan mutun mai suna Xu fu da ya zama mutun mai girmamawa a cikin zukatansu.

Kuma har wa yau dai, an iya gani kabarin marigayi Xu Fu da fadarsa da dutsen da aka yi masa suna Xu fu da abin tunawa da wannan mutun.

A shekara ta l991, a wata gundumar dake kusa da babban tudu mai suna Fushi, jama'a na kasar Japan sun kafa wani lambun shan iska mai suna "hanyar Xu Fu". A yanayin kaka na kowace shekara,jama'a na wannan gunduma sukan yi addu'a a gaban kabarin Xu Fu. Kuma a bayan shekaru 50 da suka shige a kowane gami, mutane na kasar Japan sukan shirya kasaitaccen aikin yin addu'a don tunawa da marigayi Xu fu.

Me ya sa an hake rami a kan bangon tudu

mai suna Mogao na wurin DunHuang

Babban ramin Mogao dake wurin dake kira Donhuang shi ne wurin addinin Budah mafi girma da ajiya mafi kyau a duk duniya. Me ya sa aka gina wannan babban siton ajiye kayayyakin fasaha dake jawo hankulan mutane na duk duniya a kan wani bangon tudu dake babbar hamadar arewa maso yammacin kasar Sin?

Bisa labarin tarihin da aka rubuta an ce, wani limamin Budah shi ne ya zabi wannan wuri don yin hake hake kan bangon tudun nan dake babbar hamada. A shekara ta 366,wani limami ya yi yawon shakatawa har ya zo wurin dake gaban babban tudu, da magariba ya yi yana neman wurin kwana, amma babu wurin da zai iya zaunawa ba, sai ya ga babban tudun dake gabansa akwai hasken zinariya sosai, Sai ya yi mamaki sosai, yana tsammani cewa, wurin nan ne mai daraja sosai, a karshe dai ya tattara mutane da yawa don sassaka a kan bangon tudun nan, yawan ramukan da suka hake suna nan suna kara yawa sosai, har zuwa daular Tang yawan ramukan da suka hake sun kai fiye da dubu daya.

Bayan da kwararru suka bincike har cikin dogon lokaci, sai an cem dukkan ayyukan hakawa da aka yi suna wakiltar hikimmar mutane na tsohon zamani na da. Dalilin da ya sa an zabi wurin nan ne domin ana son yin zaune a waje da wuraren da mutane ke cukunshe, wannan ya bayyana cewa, masu bin addinin budah suna son zaman rayuwa cikin kwanciyar hankali sosai,wato suna son yin zama tare da halitta. Ga wurin nan dake gaban babban tudu, a wani gefe daban kuma akwai wani karamin kogi mai ruwa. A kewayen wannan babban tudu akwai itatuwa da yawa, har sun yi layi layi. Duk tsawon ramuka daga kasa zuwa sama ba su wuce mita 40 ba. Kodayake a yanayin hunturu akwai bababr isaka, amma a bayan wannan tudu ne isaka mai karfi yakan bugawa, kuma a yanayin rani, kodayake akwai ruwan sama, amma a gaban ramuka akwai babban tudun da ya hana ruwan sama da ya shiga cikin ramuka, saboda haka ne wannan wurin da aka yi hake hake suna cikin lafiya sosai, wato ba iska ba ruwa, har ya zama busashen wuri ne mai ajiye kayayyaki da kyau sosai.

Sabo da haka ne ko da yake wadannan manyan ramukan da aka hake sun sanda shekaru fiye da dubu, amma dukkan mutunmin mutunmin da aka saka a cikin manyan ramuka suna cikin lafiya da kyau, jimlar daulolin da wadannan ramuka sun sanda a tarihi sun kai ll, kuma yawan ramukan da aka haka sun kai 402, a cikin wadannan ramuka akwai zane iri iri da aka zana, kuma da sassakakkun duwatsun da aka yi suna da yawa sosai,duk wannan ya bar duk duniya kayayyakin gargajiyar al'adu na tarihi.

Yanzu ina kayayyakin gargajiya na Lambun shan iska mai suna Yuanmingyuan suke

A shekara ta l860, hadaddiyar rundunar soja ta kasar Ingila da ta Faransa sun kawo wa birnin Beijing hari, har sojojinsu sun shiga cikin lambun shan isaka na Yuanmingyuan, a karshe dai sun kwace dukkan kayayyaki na wannan wuri. Dukkan kayayyaki masu daraja da suka kwace daga wannan lambun shan iska sun kai nawa? Har yanzu ba a iya yin lisafi ba, daga cikinsu, yawan kayayyaki masu daraja sosai da sojojin Faransa suka mika wa sarkin kasar Faransa sun wuce dubu dari. Yanzu, in ka so kana neman ganin wadannan kayayyaki masu daraja sosai na tarihi sai ka je kasar Ingila da kasar Faransa.

A cikin babban dakin ajiye kayayyaki masu daraja sosai na tarihin kasar Sin na birnin London na kasar Ingila, yawan kayayyaki masu daraja sosai da ake ajiye da su a ciki sun hada da kayayyaki masu daraja sosai na dauloli daban daban na tarihin kasar Sin. Daga cikinsu akwai wani hoton da aka zana a daular

Dongjin wannan shahararren hoto ne da ya shahara a duk duniya. A wancan lokaci, takanas ne shugaban kasar Faransa ya gina dakunan ajiye kayayyaki masu daraja na tarihin da sojojin kasar Faransa suka mika masa bayan da suka kwace daga lambun shan isaka na Yuanmingyuan na kasar Sin, Yawansu sun kai fiye da dubu. Daga cikinsu akwai sassakakkun duwatsu masu daraja da hagoran giwa da sauran kayayyaki masu daraja sosai da sosai. A cikin wani dakin ajiye kayayyakin tarihi na kasar Faransa akwai kayayyaki masu ma'anar musamman wato a lokacin da sarkin daular Qin ya yi bikin murnar cikon shekaru 66 da haihuwa, kayayyaki masu daraja da yawa da aka mika masa, sai sojojin Faransa sun kwace sun mika wa sarkinsu.

kayayyakin gargajiya na Lambun shan iska mai suna Yuanmingyuan

kayayyakin gargajiya na Lambun shan iska mai suna Yuanmingyuan

kayayyakin gargajiya na Lambun shan iska mai suna Yuanmingyuan

kayayyakin gargajiya na Lambun shan iska mai suna Yuanmingyuan

Ban da haka kuma akwai kayayyaki masu daraja da yawa da suke cikin hannayen mutane na kasar Faransa da na kasar Ingila dukkan wadannan kayayyakin da ba a iya yin lisafi ba.

Kafin watan Mayu na shekara ta 2000,a gun taron yin gwanjon kayayyaki da aka yi a shiyyar HongKong, kayayyaki masu daraja sosai wato kai na dabobbi hudu da aka sassaka da tgulla kaman na sa da na birida sauransu suna da daraja sosai har ba a iya yin lisafin kudinsu ba. Ban da haka kuma akwai wani agogo mai ban mamaki sosai, a da sarkin kasar Sin ne ya yi amfani da shi a cikin fadar sarki.

A gun wannan taron yin gwanjon kayayyaki, darajar kan damisa ta kai kudin Amurka dolla miliyan l4, kudin kan sa sun kai dolla miliyan 7, kuma kan biri kudinsa ya kai dollar Amurka miliyan 7.4. abin mafi farin ciki shi ne yanzu an dawo da wadannan kayayyaki guda uku a nan kasar Sin

Ina wurin da ake boye da fossil na kokon kai

na mutumin farko na birnin Beijing

Kafin a batar da fossil na kokon kai na mutun birnin Beijing wanda ya shahara a duk duniya, har kullun ne an ajiye wannan fossil na kokon kai na mutun birnin Beijing a cikin akwatin inshora na asibiti mai suna Xiehe na Beijing.

Amma, kafin aukuwar yake yake na tekun Pacific, wani shahararren masani mai zurfin ilmin bincike fossil yana gani cewa, ko asibiti mai suna Xiehe wuri ne maras kwanciyar hankali, kuma ya ba da shawara cewa, za a kaurar da wannan fossil na kokon kai zuwa kasar Amurka don ajiyewa da kyau.

Ta haka ne aka shigar da wannan fossil na kokon kai na mutane guda 5 a cikin wasu akwatuna,A cikin wadannan akwatuna an ajiye tarwatsatsun kayayyaki da yawa na mutane 5, kuma akwai kashin kafada da damtse da cinya da sauransu, wato jimlarsu sun kai l47,An yi amfani da takardu da zanen auduga don nadesu, har an jidar da su zuwa kasar Amurka, amma bayan wancan lokaci har zuwa yanzu, ba a sake gani su ba. Dukkan wadannan kayayyaki masu daraja sosai da sosai a duk duniya, an rasa su.

Daga baya, labarai iri iri da aka barbaza cewa, wai a lokacin da wani jirgin ruwa ya dauke da wadannan kayayyaki masu daraja har a kan teku ya yi karo da wani jirgin ruwa daban, sai wannan jirgin ruwa ya nutse.

Wani labari daban da aka bayar ya ce, a lokacin da wannan jirgin ruwa yake dauke da wadannan kayayyaki, har ya gamu da sojojin kasar Japan, sai sojojin Japan suka kwace wadannan fossil na mutane, har wa yau dai ba a gano wurin da aka boye wadannan kayayyaki masu daraja sosai ba.

Bayan an gama yake yaken duniya na karo na biyu, a kasar Japan,sojojin kasar Amurka sun nemi ko ina amma ba a gano ba. A shekara ta l972, wani mai arziki wato mai kudi da hannun shudi na kasar Amurka ya gabatar da sanarwa cewa, shi zai mika kudade da yawa don neman gano wadannan fossil na mutane, ko da yake ya sami labarai da yawa, amma ba a gabatar da hakikanin abin shaida ba. A shekara ta l970, wata mace dake birnin New york ta buga waya ga wani sashen da abin ya shafa cewa, mai gidanta ya taba ajiye wadannan fossil mutane, bayan da wani shahararren mai zurfin ilmin bincike fossil ya ga hotunan da wannan mace ta gabatar sai ya ce, haka ne dukkan wadannan hotuna na fosill na mutanen Beijing. Amma ba da dadewa ba, sai wannan mace ta bace.

A shekara ta l991, wani babban jami'I na rundunar sojan ruwa kuma mai zurfin bincike tarihi ya sami wasikar da aka rubuta masa cewa, shi ya riga ya yi cudanya tare da wani docter wanda yake da dangantakar dake tsakaninsa da wancan mace da ta fadi cewa ta san ina wurin da aka ajiye wadannan fossil na mutanen Beijing, kuma yana fatan za a gano wadannan kayayyaki tun da wuri, amma a yanayin kaka na shekara ta l992, wannan docter ya mutu.

A karshen shekara ta l970, wata jaridar kasar Amurka ta buga labari cewa, wani likita na kasar Amurka yana son yin tallar cewa, shi yana rike da labaru guda uku game da wurin ajiye wadannan fossil na mutanen Beijing, Na farko kila an ajiye wadannan fossil na mutanen Beijing cikin bankin da kasar Swees ya kafa a birnin Tianjin na kasar Sin, na biyu kuma an ce, an ajiye wadannan fossil na mutanen Beijing cikin wani bankin da kasar Faransa ta kafa a birnin Tianjin, Na uku kuma an ce, a cikin gidan wani amini ne an taba ajiye wadannan kayayyaki. A kan haka ne, takanas ofishin kiyaye kwanciyar hankali na birnin Tianjin ya kafa wata karamar kungiyar masu bincike don bin bahasin wannan al'amari.

A cikin juyin juya halin al'adun da aka yi, wani mutun ya rubuta wani karamin littafi cewa, ba a fitar da wadannan fossil na mutanen birnin Beijing ba, amma daga baya, ba a gano wannan marubcn wannan karamin litafi ba, sai ya rasu. Ba da dadewa ba, an sami wani labari cewa, kafin aukuwar yake yaken tekun Pacific, wani mai gadi na ofishin jakadan kasar Amurka dake kasar Sin ya ga mutane biyu sun rataya wani babban akwati kuma sun binne wannan akwati a karkashin wurin bayan ofishin jakadancin kasar Amurka, sai ya yi tsammani cewa, mai iyuwa ne wannan akwati yana boye da wadannan fossil na mutanen birnin Beijing. Koda yake an riga an gano wannan wuri, amma a kan wurin nan, akwai dakunan da aka gina, ba a tone ba tukuna.

Rasa fossil na mutanen Beijing cikin shekaru gomai da suka shige, har wa yau dai ba a gano wurin dake boye da wadannan fossil ba tukuna. Marigayi Zhou Enlai tsohon firayim minista na kasar Sin ya taba cewa, mutanen kasar Sin sun mika wa mutanen kasar Amurka fossil na mutanen Beijing don neman ajiye su, amma cikin hannayen mutanen kasar Amurka ne suka bace, ya kamata 'yan kimiyya masu kirki su yi kokarin dawo da su.

Wane wuri ne da marigayiya Yang Guifei ta zauna har zuwa karshen rayuwarta

Sunan malama Yang Guifei Yu huan ita ce uwar gidan dan sarki mai suna Tang Xuanzong na daular Tang, saboda tana kyan gani sosai sai sarki ya shigar da ita cikin fadar sarki. Wannan sarki ya ba ta wani suna Tai Zhen, kuma fadarta mai suna Tai Zhen, daga baya ta bar wannan fadar Tai Zhen sai sarki ya daga matsayinta, har ta zama matsayin yin daidai da na uwar gidan sarki. A wancan lokaci, shekarun wannan sarki 56 da haihuwa, amma shekarun wannan malama Yang Yuhuan 22 kawai da haihuwa.

Wannan malama Yang Yuhuan ba ma kawai tana da kyakyawan gani ba, hatta ma ga jikinta mai kiba mai kyau sosai,Kana kuma ta iya rera wakoki da yawa da kuma ta iya raye raye masu kyau. A lokacin da wannan sarki ya mika mata wata waka mai babbar ma'ana kuma mai zurfin ilmi, sai ta karanta sau daya ne ta iya rerawa da wannan waka mai dadin ji sosai. Sai wannan sarki ya yi mata babban yabo, ya fada mata cewa, jikinki ya fi fure kyan gani sosai. Daga baya, in mutane sun nuna yabo ga wata mace mai kyan gani sai a yi amfani da wannan karin magana, wato jikin mace ya fi fure kyan gani sosai.

Sabo da wannan sarki ya nuna kaurarsa kwarai ga wannan malama, sai dukkan danginta sun sami kaura daga wannan sarki. Misali, 'yan uwa mata guda uku nata dukkansu sun kama matsayin daidai da na uwar gidan sarki. Kuma 'yan uwa maza nata dukkansu sun kama manyan mukamai.

Amma wannan sarki kullun yana son mata masu kyan gani sosai da shan giya da yawa, sai siyasarsa tana nan tana kara lalacewa, kuma sabani iri iri da suka bullo tsakanin sassa daban daban. A karshe dai wani hargitsi ya bullo. Sai wannan sarki ya gudu da sauri don neman fakama, da rundunar sojoji ta wannan sarki sun zo wani karamin tudu, sai sojojinsa sun tada bore sun kashe wani dangin wannan malama sunasa Yang Guozhong, sun kuma nemi wannan sarki da ya kashe wannan malama wato uwar gidansa, a karshe dai wannan malama ta yi ritaya kan wani babban ice, A wancan lokaci shekarunta 38 da haihuwa. An kuma ba da labari cewa, a lokacin da ake tafiyar da gawarta sai takalma tata guda daya ta fadi, bayan haka sai wata tsohuwa ta sami wannan takalma har ta sami kudade da yawa har ta zama mai arziki sosai.

Amma game da mutuwar wannan malama, akwai labaru iri iri, wadansu mutane suna gani cewa, wannan malama ba ta mutu ba, sai wata yarinya daban da ta mutu don maimakon wannan uwar gidan sarki. Wani shahararren mai zurfin ilmi na kasar Sin yana gani cewa, wannan malama ta gudu har ta je kasar Japan. Kuma akwai danginta da suka gudu tare zuwa kasar Japan.

An ce, har wa yau dai akwai kabarin marigayiya Yang Guifei a kasar Japan.

A shekara ta l963, wata yarinya ta kasar Japan ta mika wa 'yan kallo na tashar TV takardar shaida sunayen asalin iyalin marigaya Yang Guifei. Har ta ce marigaya Yang Guifei kakani kakaninta na tsohon zamani.

A kasar Japan an barbaza tatsuniyar game da marigaya Yang Guifei iri iri, An a lokacin da ake nemi malama Yang Guifei da ta kashe kanta, sai wata yarinya daban ce da ta yi mutuwa don maimakon malama Yang Gui fei, amma Yang Guifei ita kanta ta gudu zuwa kasar Japan.

Har yanzu dai akwai kabarin Yang Guifen a kasar Japan, kuma mutane na kasar Japan suna son yin addu'a a gaban kabarin Yang Guifei, an ce, in an yi haka ne za a iya samu yarinya mai kyakyawan gani. Yanzu, kasar Japan tana shirin mai da wurin kabarin Yang Guifei da ya zama wurin yawon shakatawa ga duk duniya.

Kabarin Sarki na farko na Daular Qin

Kabarin Sarki na farko na Daular Chin yana nan ne a Kauyen Yanzhai dake wurin da ke nisan kilomita 5 daga Gabashin gundumar Lintong ta Lardin Shaanxi. Kudancin kabarin ya dogara bisa Tudun Lishan . Arewacinsa kuma yana fuskantar Kogin Weishui . Daga sararin sama ana ganin cewa, Kabarin kamar wani babban dala wato Al Ahram.

Fasalin kabarin Sarki na farko na Daular Chin ya kwaikwayi zayyane-zayyane da gine-ginen birnin Xianyang, hedkwatar Daular Chin . Babbar Fadar dake karkashin kasa ta alamanta Fadar Sarki mai haske . Fadin kabarin ya kai muraba'in kilomita 66.25 wanda ya ribanya fiye da sau daya kan umguwar birnin Xi'an ta yanzu .。

Sarki na farko na Daular Chin ya fara gina kabarinsa tun bayan da ya hau kujerar sarki a lokacin shekarunsa 13 da haihuwa. Da ya dinke kan kasashe 6 , ya tattara mutane fiye da dubu 100 daga wurare daban daban don su ci gaba da gine-ginen kabari har ya mutu yana da shekaru 50 da haihuwa . Wato an yi shekaru 37 kafin a gama aikin gina kabarinsa . Bisa lattafin tarihin da aka rubuta , an ce , an haka farfajiyar Kabarin a karkashin ruwan marmaro, sa'an nan kuma an karfafa shi da tagulla. A cikin fadar kabarin an ajiye lu'u lu'ai da kayayyaki masu daraja da yawa . Don hana yi masa sata , a cikin dakin kabarin an sa wani kayan baka da kibiya wanda a kowane lokaci in an yi motsi sai kibiya ta tashi .

A kewayan kabarin an ajiye gumakan dawaki da mutum-mutumin sojoji da yawa. Zayyanar kabarin ta bayyana babban iko da martabar Sarki na farko na Daular Chin .

A shekarar 210 kafin hijira , Sarkin ya mutu a wurin da ake kira Pingtai na Lardin Hebei. A watanni biyu bayan mutuwarsa aka kai gawarsa zuwa birnin Xianyang kuma an yi bikin jana'iza .

Lokacin da ake binne gawar Sarkin , Hu Hai , sarki na biyu na Daular Chin ya ba da umurnin cewa , a binne dukannin matan Sarki na farko tare da mijinsu . Mutanen da suka haka kabarin kuma za a binne su don kare asiri .

A bayan shekarar 1949, masu binciken abubuwan tarihi na kasar Sin sun yi binciken kabarin Sarki na farko na Daular Chin . A kewayan fadar karkashin kasa sun haka koguna fiye da 200 , sa'an nan kuma sun gano koguna biyu wadanda barayi suka haka. Daya yana arewa maso gabashin Kabarin. Daya kuma yana yammacin kabarin. Yanzu an riga an rufe kogunan.

>>[Labaran Tarihi na Kasar Sin]

Nawa ne hanyoyin siliki na kasar Sin

Hanyar siliki muhimmiyar hanya ce wadda wayewar kai ta kasar Sin a zamanin da ta yadu zuwa kasashen yamma . Kuma gada ce mai hade da tattalin arziki da al'adu na kasar Sin da kasashen yamma .

Hanyar silikin da kullum ake cewa ita ce hanyar babban yanki wadda Zhang Jian na Daular Han ta yamma ya bude kuma ta fara daga Changan a gabas zuwa Lome a yamma . Wannan hanyar babban yanki ta ratse gida biyu a kudu da arewa . Hanyar Kudu ta fara daga Dunhuang zuwa Yangguan , sa'an nan kuma ta kai shiyyar arewa maso gabashin Afganistan da Ansi (wato kasar Iran ta yanzu), a karshe dai ta kai Daular Rome . Hanyar arewa ta fara daga Dunhuang zuwa Matsatsar Yumen , sa'an nan kuma ta kai Kangju (wato shiyyar Asiya ta tsakiya ta Rasha ta yanzu). A karshe dai ta hade da hanyar kudu a kudu maso yamma . Wadannan hanyoyi biyu kullum ake kiransu hanyar silikin babban yanki .

Ban da wadannan hanyoyi biyu kuma akwai hanyoyin siliki biyu daban ba a san su ba . Daya ce hanyar siliki ta kudu maso yamma. Ta fara daga lardin Sichuan zuwa lardin Yunnan , sa'an nan kuma ta ratsa Kogin Irowadi zuwa Menghong dake arewacin kasar Mianmar . Kana kuma hanyar ta zuwa Mopal dake arewa maso gabashin India . A karshe dai ta kai Tsaunukan kasar Iran. Wannan hanyar siliki ta fi dadewa bisa hanyar silikin babban yanki.

Ya kasance da wata hanyar siliki daban . Ita ce daga birnin Guangzhou ka dau jirgim ruwa zuwa Zirin Malacca . Sa'an nan kuma ya zuwa Srilanka da India , a karshe dai ya isa Afrika ta gabas. Wannan hanyar ruwa ana kiran Hanyar siliki kan teku. Kayayyakin tarihin da aka fitar daga kasar Somalia dake gabashin Afrika sun tabbatar da cewa , wannan hanyar siliki ta haddasa a lokacin Daular Song ta kasar Sin .

Wannan hanyar siliki kan teku ta hade da kasar Sin da manyan kasashe masu wayewar kai na duniya . Kuma ta hanzarta musanyar tattalin arziki da al'ada a wadannan shiyyoyi. Bisa littafin tarihin da aka rubuta , an ce , a zamanin da Marco Polo ya zo kasar Sin ne ta hanyar siliki kan teku. Lokacin da ya koma wa kasarsa, shi ma ya dau jirgin ruwa daga birnin Quanzhou na Lardin Fujian, ta wannan hanyar ta isa Vinis .

Sunayen matsatsun Babbar Ganuwar Kasar Sin masu ban sha'awa

A muhimman wuraren Babbar Ganuwa an gina matsatsu masu yawa. A cikinsu wasu matsatsu sun sami sunaye masu ban sha'awa.

Matsatsar Shanhaiguan wadda ake kiran matsatsa ta farko ta Babbar Ganuwa tana iyakar tsakanin Lardin Hebei da Lardin Liaoning . Ita mafari ne na Babbar Ganuwa. Matsatsar tana dogara bisa Tuddun Yanshan a arewa kuma tana gabar Tekun Bohai a kudu . Saboda yana da hali mai ni'ima kuma tuddu yana hade da teku , shi ya sa an ba ta sunan matsatsar Shanhaiguan.

Shahararen janar Xu Da na Daular Ming ta kasar Sin ya fara gina matsatsar Shanhaiguan . A lokacin da wannan janar wanda yake da idon basira kan aikin soja ya fara gina matsatsar Shanhaiguan wadda ta iya mallakar tuddu da teku . Matsatsar tana da kofofi guda 4 . A kofar gabas an rataye wani babban kyale wanda aka rubuta kalmomin Sinnanci "Matsatsa ta farko a duniya" a kansa . Duk kyalen yana da tsayin mita 5.9 , fadinsa

ya kai mita 1.6 . A cikinsu kalma tana da tsayin mita 1.45, fadin kalmar ya kai mita 1.09 . Xiao Xian wanda ya sami digiri na uku kuma shahararen marubuci ya rubuta wadannan kalmomi.

Matsatsar Jiayuguan dake mafarin yammacin Babbar Ganuwa tana birnin Jiayuguan na Lardin Gansu . An gina shi a shekarar 1372. Saboda an gina ta kan tudun Jiayu , shi ya sa an ba ta sunan matsatsar Jiayuguan . Sa'an nan kuma ba a yi yaki a wannan wuri ba , shi ya sa an ba ta sunan Matsatsar zaman lafiya .

Matsatsar yarinya dake Gundumar Pingding ta Lardin Shanxi tana da labarin kasa mai ban mamaki , kuma da sauki an kiyaye ta , da kyar an kai mata farmaki , shi ya sa an ba ta sunan Babbar kofar Sanjin . A farkon daular Tang , Gimbia Pingyang , diya ta uku ta Sarki Li Yuan ta taba jagoranci sojoji dubu dubai don kiyaye wannan masatsar . Saboda Gimbia Pingyang tana da kwararrun fasahohin soja , kuma sojojin da take jagoranci suna da karfi , shi ya sa an ba ta sunan Matsatsar Yarinya .

Matsatsar Yumen dake karamin birnin Fangpan dake arewa maso yammacin Gundumar Dunhuang ta Lardin Gansu ta sami suna ne sabo da a zamanin da an jigilar da lu'u lu'ai daga Hetian na Jihar Xinjiang zuwa wuraren cikin kasar Sin ta wannan matsatsar .

Sunayen Wurare Masu ban sha'awa na Taiwan

A cikin tarihi aka yi kira Taiwan da jihar Yi da tsibirin Liuqiu da Dongfan da Dayuan da sauransu . Daga baya bisa halin musamman nasa an ba shi sunaye masu kyau , kamar tsibiri mai daraja da tsibirin furen Haitan da tsibirin bazara da tsibirin malam-bude-littafi da tsaibirin rake . 'Yan mulkin mallaka na Turai sun taba kiran Taiwan da Fumossa wato ma'anarsa ita ce tsibiri mai kyaun gani. Wasu mutane kuma sun kira shi da tsibiri na masu sana'ar su .

Tsibirin Taiwan yana da kyau , sunayensa kuma suna da kyau . Wani mawaki ya rubuta kyallen kalmomi masu balas wadanda ake rataye a bangarori biyu na babbar kofa da dukkanin sunayensa. A cikinsu akwai kalmomin tsibiri mai launin kore da Tudun Yangming da dankalin furanni da ruwan zaki da kogin soyyaya da sauransu .

Ban da wannan kuma , akwai sauran kyalle wanda aka rubuta kalmomi da sunayen wurare 14 na Taiwan . Shi ma haka ya bayyana yanayin musamman na tsibirin Taiwan kamar 'kwalluwar budurwa.

Zuriyar Dragon

Sinawa su kan ce su zuriyar Dragon ne, wannan muna iya samun asalinsa daga gunki da tatsuniya na da.

A can can can da, kafin wani sarki da ake kira Huang ya harhada kasar tsakiya, 'yan kabilarsa suna bauta wa wata dabba mai suna bear. Amma daga baya, sarki Huang ya cimma nasarar yaki kan wani mutum mai suna Chiyou, sai ya fara bauta wa wani dodo a maimakon wannan dabba ta bear don neman samun sulhu da kabilun da suka ba da kai. Wannan dodo shi ne dragon, wanda ke da kan bear da jikin maciji, wanda kuma ya bayyana tarihin bunkasuwar al'ummar kasar Sin da kuma harhaduwar kabilu daban daban.

Daga baya, alamomin dragon da ke alamanta al'ummar kasar Sin sun soma bullowa a kan zane-zane iri daban daban, har ma an samu rubutunsa. Ana iya samun rubutun dragon daga kalmomin da aka sassaka a kan kashi da kokunan bayan kunkuru wadanda aka tonu su daga kufayin karkashin kasa na wuraren daular Yinshang, haka kuma an iya ganin zane-zanensa a burbushin tangaran na can can can da.

Dragon ya zama gunkin da kaka da kakannin Sinawa suka bautawa, shi ya sa al'ummar kasar Sin suka soma hulda da dragon. Sabo da haka, tatsuniyoyi da dama game da dragon sun fito, inda aka ce, wata mace da ake kira Deng ta haifi sarki Yan ne sabo da dragon ya ji tausayinta, haka kuma Fubao ta haifi sarki Huang sabo da tauraro da ake kira 'Big Dipper' cikin Turanci ya tausaya mata. Ban da su biyu kuma, an haifi Yao da Shun ne sabo da tausayi ya kama 'jan dragon'. To, tun da yake kakannin kakannin Sinawa asalinsu na dragon ne, to, dole ne, jikokinsu su kasance zuriyar dragon.

Sunayen Sinawa

Kowa ya sami sunansa tun yake jariri, wanda daga baya zai bambanta shi da sauran mutane cikin zamantakewar al'umma. Amma a shekaru aru aru da suka wuce, a kasar Sin, amfanin sunaye ya wuce haka sosai.

A cikin tarihi mai tsawo, al'adun suna na Sinawa ya taka muhimmiyar rawa a fannin siyasa da al'adu da kuma harkokin zamantakewar al'umma. Bisa nazarin da aka yi, an ce, Sinawa sun riga sun yi shekaru sama da miliyan suna zaune a kasarsu. Amma sun soma samun sunayen iyali, wato "xing" a bakin Sinawa, tun shekaru dubu 5 zuwa dubu 6 da suka wuce ne kawai, wato tun lokacin al'ummar da ke karkashin jagorancin mata. A lokacin, mata ne ke kula da harkokin kabilarsu. Bugu da kari kuma, a lokacin, an yi auratayya ne tsakanin kabilu daban daban, kuma an hana yin aure tsakanin 'yan kabila daya. Sabo da tsarin nan na yin aure tsakanin kabilu daban daban, ya zama tilas kowa ya samu sunan iyalinsa wato "xing" don bambanta asalin mutane.

Bisa nazarin da wani masanin kasar Sin na daular Qing da ake kira Gu Yanwu ya yi, an ce, akwai sunayen iyalai 22 wadanda suka fi tsufa a kasar Sin. Amma mai yiwuwa ne za a kara samun irin wadannan sunaye idan ba su bace cikin tarihi tare da mutuwar kabilunsu ba. Amma fa duk da haka, an samu manyan sauye-sauye a sunayen da aka ci gaba da amfani da su. A kimanin shekaru dubu 4 zuwa dubu 5 da suka wuce, wato bayan zamanin al'ummar da ke karkashin jagorancin mata da kuma daga baya zamanin da maza ke jagora, an fara shiga al'umma mai tsarin aji aji wanda muhimmin halinsa shi ne, kabilun da ke bin asalai daban daban sun yi ta kawo wa juna tasiri kuma sun sha fama da juna. Irin tsarin al'umma ya haifar da ajin shugabanni da ajin da suke shugabanta, wato wadanda suka samu nasara sai an ba su wani yanki , kuma an yarda da su tafi yankin nan tare da iyalansu da kuma fursunonin da suka kama a yaki don su fara zama a wurin. Wadannan mutane da suka tafi wurin sun zo ne daga kabilu da dama. Bayan da suka fara zama a sabon matsugunansu, sun samu wani sabon suna dangane da wurin da suke zaune, wato 'Shi' da ake maganarsa cikin Sinanci.

Ya zuwa karni na uku kafin hijira, bayan da sarkin Qin Shihuang ya harhada kasar Sin gaba daya a karkashin jagorancinsa, an fara dayantar da 'Xing' da aka samo daga al'ummar da ke karkashin jagorancin mata da kuma 'shi' daga al'ummar da ke karkashin jagorancin maza. Daga baya, a cikin al'umma mai mulkin mallaka ta kasar Sin ta tsawon shekaru 2000, wata daula ta tashi, sa'an nan ta wargaje, daga baya wata daban ta tashi, an yi ta yin haka, ko wane lokacin da wata sabuwar daula ta bayyana, sai an ba da sababbin yankuna, wadanda suka kawo sabbin sunaye tare da su. Sabo da haka, sunaye sun zama alamar matsayin mutum, kuma Sinawa sun samu wata irin al'adar musamman dangane da sunaye. Daga baya, 'ya'yansu sun yi ta gadon al'adar nan daga zuriya zuwa zuriya. Ainihin ra'ayin bin asali da Sinawa ke riko ke nan.

Har zuwa yanzu, Sinawa da suke zaune a kasashen ketare su kan zo babban yankin kasar Sin don bin al'adar nan ta neman asalinsu. Sunayen Sinawa sun zama muhimmin abin da ya kamata a karanta idan ana so a sami ilmi game da dogon tarihin kasar Sin. A takaice dai, sunayen Sinawa sun bayyana muhimman halaye da dama na al'ummar Sin a can can can da, wannan kuma shi ne muhimmin abin da ya yi ta jawo hankulan masana.

Yaya kasashen Turai ta Yamma suka sami sakamakon

kiwon tsutsar siliki daga kasar Sin

An ce, yau sama da shekaru 5,000 ke nan Madam Leizu, matar sarkin kasar Sin mai suna Huang Di ta koya wa jama'a sana'ar kiwon tsutsar siliki a nan kasar Sin. Daga cikin rubutun Sinanci da aka sassaka a kan kashi ko kwaryar bayan kunkuru a nan kasar Sin tsakanin karnin 16 zuwa na 11 kafin bayyanuwar Annabi Isa (A.S.), akwai kalmomi kamar siliki da zaren ziliki da tsutsar siliki da kuma itacen tsutsar siliki da kuma makamantansu. A cikin babban littafin wakoki na farko da aka buga a nan kasar Sin, an wallafa wata wakar yabon sana'ar kiwon tsutsar siliki. An rubuta wannan wakar cewa, rana ta haskaka a yanayin bazara, kananan tsuntsaye suna kuka a kan bishiyoyi, 'yam mata suna tafiye-tafiye a kan rairayi, rike da dogayen kwanduna, suna zuwa wurin cire ganyayen bishiyoyin tsutsar siliki. Daga wannan wakar, an shaida cewa, tun can shekaru aru-aru, kasar Sin ta riga ta kware wajen kiwon tsutsar silili da yin abawar zaren siliki da sakar siliki.

Bayan da marigayi Zhang Qian na zamanin daular Xihan wato tsakanin shekarar 206 kafin bayyanuwar Annabi Isa (A.S.) zuwa ta shekarar 25 ya yi doguwar tafiya zuwa kasashe da ke yammacin kasar Sin, sai aka fara jigilar kayayyakin siliki na kasar Sin zuwa nahiyar Turai. Da Turawa suka ga irin wadannan kyawawan kayayyakin siliki masu haske da taushi, sai sun dauke su kamar kayayyaki masu daraja kwarai, sun yi cinikinsu sosai. An ce, a zamanin da yayin da sarkin kasar Roman ya shiga cikin gidan tiyata don kallon wasan kwaikwayo sanye da babbar rigar siliki ta kasar Sin, sai duk 'yan kallo suka yi sha'awar rigarsa ainun. Haka nan a lokacin da marigayi Columbus, shahararren mai zirga-zirga a kan teku yake tafiya mai ban mamaki a kan teku, ya gaya wa abokan tafiyarsa cewa, idan wani ya zama na farko wajen gano babban yanki, to, zai ba shi kyautar wata rigar siliki. Amma a wancan zamani, farashin kayayyakin siliki ya yi kunnen doki da na zinariya, har illa yau gwamnatin daular Roma ta samu gibin kudi saboda makudan kudade da ta biya wajen sayen kayayyakin siliki daga kasashen waje. Da ganin haka, sai majalisar dattijai ta zartas da wata doka musamman domin hana sayar da tufafin siliki na kasar Sin da kuma sanya su, amma dokar nan ta gamu da babbar kiyewa daga wajen manyan masu mulki na wannan daular wadanda ke sha'awar kayayyakin siliki na kasar Sin ainun, daga bisani, daular Roman ta ga tilashi ta soke wannan dokar.

Tun can farko, Turawa ba su san irin wadannan kayayyakin siliki da kasar Sin ta saka ta hanyar kiwon tsutsar siliki. A ganinsu, an sami zaren siliki ne daga bishiyoyi, kuma an jikar da su cikin ruwa. Bayan da suka fahimci cewa, an sami zaren siliki ne daga bawon tsutsar siliki, sai sun dau aniyar koyon sana'ar kiwon tsutsar siliki daga kasar Sin kuma ba tare da tsoron sadaukar da kome ba.

A karni na 6, sarkin daular Roman ya taba kiran wani mishan wanda ya taba zuwa kasar Sin, ya kuma turo shi zuwa kasar Sin don satar sakamako da kasar Sin ta samu wajen kiwon tsutsar siliki. Bayan saukarsa a lardin Yunnan na kasar Sin, wannan mishan ya gane cewa, ashe, an yi dashe-dashen bishiyoyin tsutsar siliki ne da 'ya'yan bishiyoyin nan, kuma tsutsar siliki ma an same su ne bayan da aka shafe mako daya ana kyankyashe su a cikin aljihun gaban kirji na mutane a yanayin bazara. Da aka same su, sai aka yi kiwonsu da ganyayen bishiyoyin tsutsar siliki, bayan da tsusar siliki suka soma girma sun yi kwasfa, sai an sami zaren siliki daga jikin kwasfan nan.

Bayan da wannan mishan ya sami wannan sakamako, kuma ya yi satar wasu 'ya'yan tsutsar siliki da na bishiyoyin tsutsar siliki, sai ya koma da su gida don neman samun lambobin yabo. Amma wani abu ya faru ba zato ba tsamani, wato wannan mishan ya yi kuskuren daukar 'ya'yan tsutsar siliki a matsayin 'ya'yan bishiyoyin tsutsar siliki, ya binne 'ya'yan tsutsar siliki a cikin kasa, ya sanya 'ya'yan bishiyoyin tsutsar siliki a aljihun gaba na rigarsa don neman kyankyashe su, amma ina, me ya faru, asirinsa ya tonu, kowa ya gane. Daga baya, sarkin daular Roman ya sake turo mishan biyu masu basiri zuwa nan kasar Sin don satar sakamako da kasar Sin ta samu wajen kiwon tsutsar siliki cikin fakewa da yadada addini. Wadannan mishan biyu sun tsamo darasi da aka samu a da, sun tuna da hanyar da ake bi sosai wajen dashen bishiyoyin tsutsar siliki da kyankyashe kananan tsutsar siliki, sun boye 'ya'yan tsutsar siliki da na bishiyoyin tsutsar siliki cikin holokon kwagiri, sun koma da su kasar Roman. Ta haka dai ne aka yadada sakamako da kasar Sin ta samu wajen kiwon tsutsar siliki a kasashen Turai ta yamma.

An ce, yau sama da shekaru 5,000 ke nan Madam Leizu, matar sarkin kasar Sin mai suna Huang Di ta koya wa jama'a sana'ar kiwon tsutsar siliki a nan kasar Sin. Daga cikin rubutun Sinanci da aka sassaka a kan kashi ko kwaryar bayan kunkuru a nan kasar Sin tsakanin karnin 16 zuwa na 11 kafin bayyanuwar Annabi Isa (A.S.), akwai kalmomi kamar siliki da zaren ziliki da tsutsar siliki da kuma itacen tsutsar siliki da kuma makamantansu. A cikin babban littafin wakoki na farko da aka buga a nan kasar Sin, an wallafa wata wakar yabon sana'ar kiwon tsutsar siliki. An rubuta wannan wakar cewa, rana ta haskaka a yanayin bazara, kananan tsuntsaye suna kuka a kan bishiyoyi, 'yam mata suna tafiye-tafiye a kan rairayi, rike da dogayen kwanduna, suna zuwa wurin cire ganyayen bishiyoyin tsutsar siliki. Daga wannan wakar, an shaida cewa, tun can shekaru aru-aru, kasar Sin ta riga ta kware wajen kiwon tsutsar silili da yin abawar zaren siliki da sakar siliki.

Bayan da marigayi Zhang Qian na zamanin daular Xihan wato tsakanin shekarar 206 kafin bayyanuwar Annabi Isa (A.S.) zuwa ta shekarar 25 ya yi doguwar tafiya zuwa kasashe da ke yammacin kasar Sin, sai aka fara jigilar kayayyakin siliki na kasar Sin zuwa nahiyar Turai. Da Turawa suka ga irin wadannan kyawawan kayayyakin siliki masu haske da taushi, sai sun dauke su kamar kayayyaki masu daraja kwarai, sun yi cinikinsu sosai. An ce, a zamanin da yayin da sarkin kasar Roman ya shiga cikin gidan tiyata don kallon wasan kwaikwayo sanye da babbar rigar siliki ta kasar Sin, sai duk 'yan kallo suka yi sha'awar rigarsa ainun. Haka nan a lokacin da marigayi Columbus, shahararren mai zirga-zirga a kan teku yake tafiya mai ban mamaki a kan teku, ya gaya wa abokan tafiyarsa cewa, idan wani ya zama na farko wajen gano babban yanki, to, zai ba shi kyautar wata rigar siliki. Amma a wancan zamani, farashin kayayyakin siliki ya yi kunnen doki da na zinariya, har illa yau gwamnatin daular Roma ta samu gibin kudi saboda makudan kudade da ta biya wajen sayen kayayyakin siliki daga kasashen waje. Da ganin haka, sai majalisar dattijai ta zartas da wata doka musamman domin hana sayar da tufafin siliki na kasar Sin da kuma sanya su, amma dokar nan ta gamu da babbar kiyewa daga wajen manyan masu mulki na wannan daular wadanda ke sha'awar kayayyakin siliki na kasar Sin ainun, daga bisani, daular Roman ta ga tilashi ta soke wannan dokar.

Tun can farko, Turawa ba su san irin wadannan kayayyakin siliki da kasar Sin ta saka ta hanyar kiwon tsutsar siliki. A ganinsu, an sami zaren siliki ne daga bishiyoyi, kuma an jikar da su cikin ruwa. Bayan da suka fahimci cewa, an sami zaren siliki ne daga bawon tsutsar siliki, sai sun dau aniyar koyon sana'ar kiwon tsutsar siliki daga kasar Sin kuma ba tare da tsoron sadaukar da kome ba.

A karni na 6, sarkin daular Roman ya taba kiran wani mishan wanda ya taba zuwa kasar Sin, ya kuma turo shi zuwa kasar Sin don satar sakamako da kasar Sin ta samu wajen kiwon tsutsar siliki. Bayan saukarsa a lardin Yunnan na kasar Sin, wannan mishan ya gane cewa, ashe, an yi dashe-dashen bishiyoyin tsutsar siliki ne da 'ya'yan bishiyoyin nan, kuma tsutsar siliki ma an same su ne bayan da aka shafe mako daya ana kyankyashe su a cikin aljihun gaban kirji na mutane a yanayin bazara. Da aka same su, sai aka yi kiwonsu da ganyayen bishiyoyin tsutsar siliki, bayan da tsusar siliki suka soma girma sun yi kwasfa, sai an sami zaren siliki daga jikin kwasfan nan.

Bayan da wannan mishan ya sami wannan sakamako, kuma ya yi satar wasu 'ya'yan tsutsar siliki da na bishiyoyin tsutsar siliki, sai ya koma da su gida don neman samun lambobin yabo. Amma wani abu ya faru ba zato ba tsamani, wato wannan mishan ya yi kuskuren daukar 'ya'yan tsutsar siliki a matsayin 'ya'yan bishiyoyin tsutsar siliki, ya binne 'ya'yan tsutsar siliki a cikin kasa, ya sanya 'ya'yan bishiyoyin tsutsar siliki a aljihun gaba na rigarsa don neman kyankyashe su, amma ina, me ya faru, asirinsa ya tonu, kowa ya gane. Daga baya, sarkin daular Roman ya sake turo mishan biyu masu basiri zuwa nan kasar Sin don satar sakamako da kasar Sin ta samu wajen kiwon tsutsar siliki cikin fakewa da yadada addini. Wadannan mishan biyu sun tsamo darasi da aka samu a da, sun tuna da hanyar da ake bi sosai wajen dashen bishiyoyin tsutsar siliki da kyankyashe kananan tsutsar siliki, sun boye 'ya'yan tsutsar siliki da na bishiyoyin tsutsar siliki cikin holokon kwagiri, sun koma da su kasar Roman. Ta haka dai ne aka yadada sakamako da kasar Sin ta samu wajen kiwon tsutsar siliki a kasashen Turai ta yamma.

Bisa wani labari daban da aka samu daga mutanen zamanin da dangane da yadda aka yadada sakamako da kasar Sin ta samu wajen kiwon tsutsar siliki a kasashen Turai ta yamma, an ce, a cikin wani littafi da marigayi Xuanzang, shahararren babban limanin limaman addinin Buddah na zamanin daular Tang na kasar Sin ya wallafa, an ce, wata karamar kasa mai suna Jusadanna da ke a yammacin kasar Sin tana son samun sakamako da aka samu wajen kiwon tsutsar siliki, sai ta bukaci wata karamar kasa da ke gabashinta da ta koya mata, amma kasar nan ta yi watsi da bukatunta, kuma ta kara tsananta yin bincike-bincike a tashoshi da ta kafa a kan bakin iyakar da ke tsakanin kasashen nan biyu don hana a aika da 'ya'yan tsutsar siliki da na bishiyoyinsu zuwa kasashen waje. Daga bincike da kwararru suka yi, an gano cewa, mai yiwuwa ne, wannan karamar kasa wata kasa ce mai suna Beiwei wadda kuma take daya daga cikin kananan kasashe da suka hadu suka zama kasar Sin ta yanzu. A cikin irin wannan hali ne, sai wata dabara ta fado cikin zuciyar sarkin kasar Jusadanna, wato ya bukaci wannan karamar kasa da ta ba shi gimbiya don ya aura duk cikin fakewa da kara dankon aminci a tsakanin kasashensu biyu, daga baya dai ya cim ma burinsa. A yayin da zai karbi amarya, sai wannan sarki ya aika da manzonsa na musamman zuwa wurin gimbiya don neme ta da ta je kasarsa tare da wasu 'ya'yan tsutsar siliki da na bishiyoyin tsutsar siliki. Gimbiyar nan ta yi na'am da bukatu da sarkin kasar nan ya yi mata. Kafin tashinta daga wannan karamar kasa, gimbiyar ta boye 'ya'yan tsutsar siliki da na bishiyoyin tsutsar siliki a cikin hula. Da za ta fita daga bakin iyakar kasa, jami'ai sun yi bincike-bincike kan duk suturanta, amma ba su binciki hularta ba sabo da tsoro da suka ji. Ta haka, an tafi da 'ya'yan tsutsar siliki da na bishiyoyin tsutsar siliki zuwa wannan kasar, daga wannan kasar an yadada sakamako da kasar Sin ta samu wajen kiwon tsutsar siliki zuwa kasashen yammacin Turai.

Wani Bature dan kasar Hungary ya tabbatar da wannan labari mai daraja da marigayi Xuanzang ya rubuta a cikin littafinsa, bayan da ya gano wani tsohon zane a jihar Xinjiang ta kasar Sin. A kan tsakiyar wannan tsohon zane, an zana wata mace mai arziki, sanye da tufafi masu kyau da wata hula a ka, haka nan kuma an zana mata barori biyu wadanda ke tsaye a ko wane gefe nata, wata bara da ke tsaye a gefen hagunta na nuna wa hularta da yatsa. Wannan mace mai arziki ita ce gambiyar wannan karamar kasa da ta yadada 'ya'yan tsutsar siliki da na bishiyoyin tsutsar siliki daga kasar Sin zuwa kasashen yammacin Turai.

Asalin rubutun Sinanci da sauye-sauyensa

Rubutun Sinanci yana daya daga cikin tsofaffin rubuce-rubuce da mutane mafiya yawa ke amfani da su. Kago rubutun Sinanci da yin amfani da shi ba ma kawai sun gaggauta yalwata al'adun kasar Sin ba, hatta ma sun kawo tasiri mai zurfi ga yalwatuwar al'adun duniya.

Yau kimanin shekaru 6,000 da suka wuce, an riga an fara rubuta alamu ko abubuwan shaida wadanda yawan ire-irensu ya wuce 50 a wani wurin tarihi mai suna "Banpo" na kasar Sin. Haka nan kuma an rubuta wadannan alamu ko abubuwan shaida daki-daki kuma bisa ka'idoji, sabili da haka, an ce, lalle, suna da halayen musamman na kalmomi masu saukin fahimta, kwararru suna ganin cewa, mai yiwuwa ne, wadannan alamu ko abubuwan shaida su ne asalin rubutun Sinanci.

An kafa tsarin rubutun Sinanci ne a zamanin daular Shang ta kasar Sin wato karni na 16 kafin bayyanuwar Annabi Isa (A.S.). Daga binciken da aka yi a kan kayayyakin tarihi, an gano cewa, a farkon zamanin daular Shang, kasar Sin ta riga ta kai wani babban matsayin wayin kai, tsofaffin kalmomi da aka sassaka a kan kashi da kwaryar bayan kunkuru sun samar wa kasar Sin wani halin musamman na wayin kanta. A zamanin daular Shang, kafin sarkin kasa ya yi wani abu, sai ya nemi sa'a, kashi da kwaryar bayan kunkuru kayayyakin aiki ne da ya kan yi amfani da su wajen neman sa'a.

  Kafin a sassaka kalmomi a kan kashi ko kwaryar bayan kunkuru, a kan gyara su. A farkon farko, a kan cire nama da ke kan kashi da kwaryar bayan kunkuru, daga nan an sa zarto an yayyanka su kuma an goge su. Bayan haka an yi amfani da wuka wajen huda kananan ramuka gida-gida a kan bayan kashin da bayan kwaryar bayan kunkuru. Malaman duba sun sassaka sunayensu da ranar neman sa'a da tambayoyi a kan wadannan kashi da kwaryar bayan kunkuru, daga nan sai su sa wadannan ramuka da suka sassaka a kan kashi da kwaryar bayan kunkuru a kan wuta, ta haka sai wadannan ramuka su tsage. Bisa bincike da masu duba suka yi a kan hanyar da suka tsaga, sai su sami sakamakon duba. Haka nan kuma an sassaka bayani kan ko an tabbatar da sakamako da aka samu ko a'a a kan kashi ko kwaryar bayan kunkuru. Bayan da aka tabbatar da sakamakon duba, sai a ajiye wadannan kashi ko waryar bayan kunkuru da aka sassaka kalmomi bisa matsayin takardun fayil na hukuma.

Ya zuwa yanzu, yawan wadannan kashi da kwaryar bayan kunkuru da masu binciken kayayyakin tarihi suka gano ya wuce dubu 160. Daga cikinsu akwai cikakken kashi da kwaryar bayan kunkuru masu kyau da aka sassaka kalmomi a kai, sauransu kuwa sun farfashe. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, jimlar babbaku iri dabam daban da aka sassaka a kan wadannan kashi da kwaryar bayan kunkuru ta wuce 4,000. Daga cikinsu, akwai kimanin babbaku 3,000 wadanda aka tabbatar da su bisa bincike da masu nazarin kayayyakin tarihi suka yi. Haka nan kuma daga cikin wadannan babbaku 3,000, akwai babaku 1000 wadanda kwararru suka sami ra'ayi daya wajen bayyana ma'anarsu. Ta hanyar wadannan babaku 1,000, aka gano yawancin abubbuwan zamanin daular Shang a fannin siyasa da tattalin arziki da al'adu da sauransu. Kalmomi da aka sassaka a kan kashi da kwaryar bayan kunkuru wani irin cikakken rubutu ne mai kyau, kuma sun aza harsashi ga yalwata rubutun Sinanci.

Rubutun Sinanci kamar zane-zane ne. Jimlar babbakun Sinanci ta kai misalin 10,000. Daga ciki akwai misalin babbaku 3,000 wadanda a kan yi amfani da su a kullum. Ana iya yin amfani da wadannan babbaku 3,000 wajen rubutun kalmomi masu dimbin yawa har ba su iya lissaftuwa. Sa'an nan ana iya yin amfani da kalmomin nan wajen rubuta jimloli iri dabam daban.

Bayan da aka kago rubutun Sinanci, ya yi tasiri mai zurfi ga kasashe da ke makwabtaka da kasar Sin. An kago rubutun Japananci da na Vietnam da Korea da kuma sauran kasashe ne duk bisa ginshikin rubutun Sinanci.

Babbar kararrawa mai suna "Yongle" na tashi

zuwa wuri mai nisan kilomita 45

A cikin gidan babbar kararrawa da ke a birnin Beijing na kasar Sin, akwai wata babbar kararrawa mai suna "Yongle" wadda nauyinta ya kai ton 46.5, tsayinta ya kai mita 6.75, kuma tsawon dari'arta ya kai mita 3.3. Yau sama da shekaru 500 ke nan da aka yin wannan babbar kararrawa. An yi ta ne ta hanyar haka wani babban rami mai siffar kararrawa cikin kasa. Yayin da ake yinsa, an hura wuta a kasan tukwanen narke jan karfe wadanda yanwansu ya wuce goma, bayan da aka sami ruwan jan karfe mai zafi kwarai daga wadannan tukwane, sai a zuba su cikin babban ramin nan da aka haka, bayan da ruwan jan karfe ya sanyaya, sai a sami wannan babbar kararrawa. Wannan fasahar yin kararrawar ta kai matsayin ci gaba sosai.

Bayan da aka sami wannan babbar kararrawa, an taba ajiye a wurare daban daban, sai a zamanin daular Qing wato a shekarar 1751, an kaurar da ita zuwa haikali mai suna " Juesheng", daga baya an canja sunan haikalin nan zuwa Gidan Babbar Kararrawa. Tun bayan da aka ajiye babbar kararrawar nan a wannan wuri har zuwa yanzu, ba a canja wurinta ba.

Muryar Babbar Kararrawa mai suna Yongle tana da dadin ji kwarai. Daga cincike da kwararru suka yi, an gano cewa, muyarta tana iya tashi zuwa wuri mai nisan kilomita 45, tsawon lokacin sautin muryar karshenta ya kai mintoci biyu, lale wannan ya ba mutane mamaki kwarai.

A kan buga wannan babbar kararrawa ne a ranar sabuwar shekara. Ko da yake an yi shekaru 500 da 'yan doriya ana buga wannan babbar kararrawa, amma ya zuwa yanzu dai tana da inganci sosai kamar ba a taba ta ba. Bisa bincike da 'yan kimiyya da fasaha suka yi a kan wannan babbar kararrwa, an gano cewa, karfunan babbar kararrawar nan suna hada da tagula da kuza da karfe da Magnesium da zinariya mai nauyin kilo 18.6 da kuma azurfa mai nauyin kilo 38. Bisa bincike da kwararru suka yi, an ce, kayayyakin tagulla mai gauraye da zinariya suna iya maganin tsatsa, haka nan kuma kayayyakin tagulla mai gauraye da azurfa ma suna kara inganci sosai, daidai da wannan ko da yake yau da sama da shekaru 500 da aka fitar da wannan babbar kararrwa mai suna Yongle, amma an kiyaye ta da kyau. Haka zalika muryarta ma tana da dadin ji ainun.

Wani kwararre a fannin narkewar karfuna ya bayyana cewa, " nasarar da aka samu wajen fitar da babbar kararrawa mai suna "Yongle" abu mai al'ajabi ne ga tarihin duniya kan narke karfuna, dalilin da ya sa haka shi ne domin ko da yake an sami ci gaba sosai a fannin kimiyya, amma duk da haka da kyar ake iya fitar da irin wannan babbar kararrwa.

An gano sabbin abubuwa masu ban al'ajabi

na tsohon garin Beijing ta hanyar zamani

An gina birnin Beijing ne a tsakanin shekarar 1403 zuwa ta 1425. Tun can da, kyakkyawan fasalin birnin Beijing da gine-ginensa masu kayantarwa sun shahara a duk duniya. Daga hotunan birnin Beijing da 'yan kimiyya da fasaha suka dauka daga sararin samaniya ta hanyar zamani a cikin shekarun nan da suka wuce, an gano zane-zane kamar manyan dodanni biyu da ake kira "Dargons" cikin Turanci a unguwoyin birnin Beijing, da zanen wani mutum mai tsayi da ke zaune tare da kafafunsa biyu a kanannade. Wadannan zane-zane suna da kayatarwa kwarai, har ila yau sun zama sabbin abubuwa masu ban al'ajabi na birnin Beijing, kuma an yi mamaki da su ainun.

A kan hotuna masu launi da aka dauka daga nesa ta hanyar zamani, an ga wadannan "Dragons" biyu sun ratsa garin daga arewa zuwa kudu, suna tafiya tare. Daya daga cikinsu ya tashi daga "Tian'anmen" zuwa wani ginin gargajiya mai suna Zhonggulou, haka nan kuma gine-gine na zamanin da ne suka haifar da siffarsa. Sauran daya kuwa ya tashi daga tafki mai suna Nanhai zuwa tafki mai suna Shishahai, kuma koramu ne suka fitar da siffarsa.

Ya zuwa yanzu dai, ba a san ko masu tsara fasalin ne suka wasa kwakwalwa suka tsara fasalin wadannan "Dragons" biyu masu kayatarwne, ko Allah ne ya halace su ba.

Ban da wannan kuma wani abu mai ban al'ajabi dabam shi ne siffar zanen Lambun Shan Iska mai suna "Jingshan" da ke birnin Beijing. Wannan zane yana siffanta wani mutum mai tsayi da ke zaune, idanunsa a rufe, kuma kafafunsa a kanannade sosai. A da, Lambun Shan Iska mai suna "Jingshan" laumbun sarkin kasar Sin ne, kuma yana arewancin fadar gargajiya na sarakunan kasar Sin. Ko an wasa kwakwalwa ne aka tsara fasalin wannan lambun shan iska , ko a'a? Wannan ma ka-cici-ka-cici ne.

Wadannan sabbin abubuwa masu ban al'ajabi biyu da aka gano a birnin Beijing sun sa birnin Beijing ya kara baiwa mutane mamaki.

Allurar kashi da kayayyakin aladu na mutanen da can can a kauyen Zhoukoudian da ke a karkarar birnin Beijing

Yau kimanin shekaru 50 da suka wuce, sai dan adam sun fara iya yin allura da kuma yin amfani da ita. An yi irin wannan allura ne da siririn kashi. Masu binciken kayayyakin tarihi sun taba gano allurar kashi a wani tsohon wuri na nahiyar Turai, amma fasahar yinta tana kan matsayin koma baya. Bamban da haka wata allurar kashi da aka gano a tsohon wuri mai suna Zhoukoudian na kasar Sin, fasahar yinta ta kai matsayin ci gaba, don haka ta sami babban yabo daga wajen mutane.

Tsayin wannan allurar kashi mai kyau ya kai millimetre 82, tsawon "diameter" ya kai millimetre 3. Wato ke nan ta fi tsinken ashana girma, jikinta ya dan lankwashe kadan, fuskatar ta yi sumul-sumul, kanta mai kaifi ne kwarai, haka kuma ramin ya fito sosai, da ka gani sai ka ce an huda ramin nan ne da wani kayan aiki mai tsini, amma abin bakin ciki shi ne, da aka tono ta daga karkashin kasa an bata wannan ramin.

Da allura da zare, amma da kyar za a tono zare daga karkashin kasa. Bisa bincike da kwararru suka yi, an ce, zare da mutanen da can can na kauyen Zhoukoudian na Beijing suka yi amfani da shi, ba a saka shi da zare kamar su rama ko auduga da makamantasu ba, mai yiwuwa ne an yi amfani da jijiyar tsohuwar barewa da ba safai a kan iya samunta ba wajen yin zaren nan wanda tsawonsa ya iya kai centimetre 50, launin zaren nan fari fat kuma mai siriri ne daidai kamar zaren siliki, lalle, wannan jijiyar barewa ta cancanci zaman zare.

An kimanta cewa, tun da yake mutanen da can can na kauyen Zhoukoudian na birnin Beijing sun sami allura da zare, sai sun iya yin amfani da su wajen dinkin tufafi , saboda haka mutanen nan sun sanya tufafi.

Yau sama da shekaru 18,000 da suka wuce, mutanen da can can na kauyen Zhoukoudian na Beijing sun riga sun iya yin kayayyakin alatu da sanya su a jiki. Masu binciken kayayyakin tarihi sun gano abin wuya da mutanen nan suka yi a wurin da suka taba zama. Wadannan mutanen da can can sun goga kwayoyin dutse da hakoran namun daji da kashin kifaye da na kififfiya da kumba masu launi iri iri, sun yi rami, sun zura zare a cikinsu, daga karshe dai sun sami kayayyakin al'adu.