Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cika shekaru 20: An gudanar da dandalin nazarin sakamako da makomar FOCAC
2020-10-29 11:39:10        cri

Yayin da dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen nahiyar Afirka wato FOCAC ke cika shekaru 20 da kafuwa, a jiya Laraba an gudanar da taron nazartar sakamako, da ma makomar dandalin na FOCAC ta yanar gizo. Dandalin ya hallara wakilai daga kasashen Sin da Afirka ta Kudu da Botswana da Najeriya

Cikin wata sanarwa da ya fitar game da dandalin, mataimakin darakta a hukumar kula da harkokin wallafa littattafan harsunan waje na kasar Sin Lu Cairong, ya ce karkashin inuwar wannan dandali, hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka na kara zurfafa.

Jami'in ya ce ana samun sabbin nasarori a fannonin raya ababen more rayuwa, da ilimi da horaswa, da fannin kasuwanci da cinikayya, da bangaren raya kiwon lafiya da musaya tsakanin al'ummu, wanda hakan ke amfanar dukkanin sassan dake cudanyar, da ma sauran bangarorin duniya baki daya.

A nasa tsokaci kuwa, daraktan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin a Najeriya Charles Onunaiju, cewa ya yi cikin shekaru 20 da suka gabata, dandalin FOCAC ya zamo dandalin aiwatar da kudurorin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Ya ce a gabar da nahiyar Afirka ke fuskantar kalubalen gina salon ta na raya tattalin arziki, dandalin na sharewa nahiyar fagen bunkasa cinikayya tsakanin sassan ta, da ma karin dama ta hade sassan wuri guda. Har ila yau, dandalin na aiki tare da shawarar ziri daya da hanya daya, wajen taimakawa dunkulewar Afirka wuri daya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China