Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Sin da Senegal sun taya juna murnar cika shekaru 20 da kafuwar dandalin FOCAC
2020-10-12 10:43:10        cri
Yau ranar Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Senegal Macky Sall, sun taya juna murnar cika shekaru 20 da kafuwar dandalin tattauna hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC ta wayar tarho.

Shugabannin biyu sun bayyana cewa, cikin shekaru 20 da suka gabata, dandalin FOCAC ya zama babbar alamar hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa. Bangarorin biyu sun tsaya tsayin daka wajen raya al'ummominsu, da kuma dukufa wajen inganta dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu. Kuma, sakamakon da aka cimma cikin tarukan FOCAC sun ba da tallafi matuka ga al'ummomin Sin da Afirka. A shekarar 2018, an cimma babbar nasarar gudanar da taron kolin dandalin FOCAC da aka yi a birnin Beijing, inda Sin da Afirka suka cimma matsayi daya wajen karfafa dunkulewar al'ummominsu, lamarin da ya ba da jagoranci ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka.

Haka kuma, sun ce, matsalar cutar COVID-19 babbar matsala ce dake gaban dukkanin bil Adama, wadda ta haddasa babbar asarar tattalin arzikin duniya. Sin da Afirka suna son hada gwiwa domin fuskantar wannan kalubale tare, ta yadda hadin gwiwarsu za ta kasance abin misali ta fuskar raya hadin gwiwar dake tsakanin bangarori daban daban don cimma moriyar juna, da ba da gudummawa a fannin kare yanayin adalci na duniya.

Bugu da kari, sun ce, suna fatan hada kan mambobin dandalin FOCAC domin kyautata tsarin taron bisa ka'idojin mu'amala tare da aiwatarwa tare, da cimma sakamako tare, ta yadda dandalin zai ba da jagoranci yadda ya kamata ta fuskar raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, da inganta dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a tsakanin bangarorin biyu zuwa wani sabon matsayi, da karfafa dunkulewar al'ummomin Sin da Afirka domin tallafa musu, da samar musu wata kyakkyawar makoma. Sun kara da cewa, suna da cikakken imani kan cewar, taron dandalin FOCAC da za a kira a kasar Senegal a shekarar 2021 mai zuwa, zai taimakawa Sin da Afirka wajen cimma burinsu na bai daya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China