Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Taron manyan jami'an Sin da Afirka ya yi kira da a zurfafa hadin gwiwar yaki da COVID-19
2020-08-12 10:29:33        cri

Manyan jami'ai da masana daga kasashen Sin da Afirka, sun gana ta kafar bidiyo jiya Talata, inda suka yi kira da a kara zurfafa hadin gwiwar sassan biyu a yakin da suke yi da annobar COVID-19 a nahiyar Afirka.

Taron ya kuma samu halartar manyan jami'ai da masana daga bangarorin biyu, ciki har da jami'ai daga hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka(AU) da hukumar MDD mai kula da tattalin arzikin Afirka(UNECA), da cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta Afirka(Africa CDC) gami da jami'ai daga Sin da wasu kasashen Afirka.

A jawabinsa yayin taron, mataimakin shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka(AU) Kwesi Quartey, ya jaddada cewa, yadda gwamnatin kasar Sin da kamfanoni kasar suke taimakawa kasashen nahiyar, sun taimakawa kokarin kasashe da ma nahiyar a yakin da suke yi da annobar COVID-19.

Jami'in ya nanata cewa, matakin kasar Sin na fara gina hedkwatar cibiyar Africa CDC kafin lokacin aka tsara a wannan shekara, ya sake nuna karfin alakar shugabannin Sin da Afirka da abokantar dake tsakanin kasashen Sin da Afirka a fannin kiwon lafiyar al'umma.

Shi ma a nasa jawabin, jakadan kasar Sin a kungiyar tarayyar Afirka Liu Yuxi, ya jaddada cewa, a yayin da kasar Sin ke yaki da wannan annoba, AU da shugabannin Afirka, sun aiko mata da taimako na kudi da kayayyakin, duk da matsin da suke fama da shi.

Jakada Liu Yuxi, ya ce bayan da annobar ta barke a nahiyar Afirka, kasar Sin ta kasance a kan gaba wajen taimakawa da ma tsayawa tare da al'ummomin kasashen Afirka. Yana cewa, kasar Sin ta tura ma'aikatan lafiya masu yaki da annoba zuwa kasashen Afirka 11, baya ga taimakon kayayyakin kiwon lafiya ta baiwa kasashen na Afirka da kungiyar AU, da shirya tarukan bidiyo da bangaren Afirka, da musayar kwarewa kan jinyar marasa lafiya da sauransu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China