Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yankin cinikayya mara shinge na nahiyar Afrika zai samar da karin damarmaki ga hadin gwiwar Sin da Afrika
2020-07-22 10:27:36        cri

An bayyana yankin ciniki mara shinge na nahiyar Afrika, a matsayin wanda zai samar da sabbin damarmaki ga hadin gwiwar Sin da Afrika.

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Gedion Jalata, babban mashawarcin shirin raya kasashe na MDD kan hadin gwiwar kasashe masu tasowa, kuma tsohon jami'in tuntuba na hukumar kula da tattalin arzikin nahiyar Afrika ta MDD, ya ce yankin na bukatar ingantattun ababen more rayuwa da za su hada fadin nahiyar, yana mai cewa wannan wani bangare ne da ake matukar bukatar taimakon kasar Sin.

Ya kuma dora alhakin rashin cinikayya mai karfi tsakanin kasashen nahiyar da karancin ababen more rayuwa dake hada kasashen na Afrika, yana mai cewa, kasar Sin na taimakawa kasashen ta hannun shawarar "ziri daya da hanya daya".

Sai dai, Gedion Jalata ya ce kasashen Afrika na bukatar karfafa yaki da sabbin kalubalen da za su kawo cikas ga cimma muradun yankin, kamar cutar COVID-19, wanda ya ce galibin kasashen nahiyar na yaki da ita da taimakon kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China