Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bada gudunmuwar kayayyakin kiwon lafiya da na ofis ga kungiyoyin kwadago na Afrika
2020-07-15 10:09:27        cri

Hadaddiyar kungiyar kwadago ta kasar Sin (ACFTU), ta bada gudunmuwar kayayyakin lafiya ga kungiyoyin kwadago na nahiyar Afrika, domin taimakawa yaki da cutar numfashi ta COVID-19 a tsakanin ma'aikatan nahiyar.

Gudunmuwar da aka mika ga hadaddiyar kungiyar kwadago ta nahiyar Afrika (OATTU), ta kuma kunshi kayayyakin ofis domin taimakawa ayyukan kungiyar a fadin nahiyar.

Kayayyakin kiwon lafiyar sun hada da makarin baki da hanci 20,000, da sinadarin tsaftace hannu 1,000 da na'urar buga rubutu da kananan kumfytoci, wadanda za a raba ga kungiyoyin kwadago dake fadin nahiyar.

Sakatare Janar na hadaddiyar kungiyar ta Afrika, Arezki Mezhoud, ya ce gudunmuwar daga abokan huldarsu na kasar Sin, za ta taimaka wajen kare ma'aikatan nahiyar daga annobar COVID-19.

Ya kara da cewa, wannan ya nuna irin goyon bayan dake tsakanin Sin da Afrika da kuma ci gaban hadin gwiwa tsakanin ma'aikatan Afrika da takwarorinsu na Sin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China