Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Jumia na fatan yin hadin gwiwa da karin kamfanonin Sin masu samar da hajoji don bukasa cinikayya ta yanar gizo
2020-10-16 12:53:33        cri
Kamfanin Jumia dake hada hadar sayar da hajoji ta yanar gizo a nahiyar Afirka, ya bayyana fatan fadada hadin gwiwa da karin kamfanonin Sin masu samar da hajoji don bukasa cinikayyar sa.

Da yake bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Alhamis, a gefen bikin kaddamar da alkaluman wadatuwar abinci a nahiyar Afirka, babban jagoran kamfanin a kasar Kenya Sam Chappatte, ya ce kasar Sin na da ikon samar da hajoji da duniya ke bukata, kuma kamfanin su na da burin gabatarwa masu sayayya a Afirka, damar samun kayayyaki masu inganci.

Mr. Chapatte ya ce har yanzu, hada hadar saye da sayarwa ta yanar gizo a nahiyar Afirka ba ta yi karfi ba, idan an kwatanta da yanayin a sauran sassan duniya, kasancewar ba ta ma kai kaso 2 bisa dari na jimillar kayan sari da ake hada hadar su ba, kasa da abun da ake samu a kasar Sin.

Jami'in ya ce bullar cutar COVID-19 a sassan duniya, ta taimaka wajen fadada hada hadar cinikayya ta yanar gizo a sassan nahiyar Afirka. Kuma matakan da gwamnatocin kasashen nahiyar ke dauka, don dakile yaduwar annobar, sun taimaka wajen ingiza al'ummar nahiyar, rungumar hidimomi ta yanar gizo, wanda hakan ke da sauki da kuma arha. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China