Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Afirka za su hada hannu don samar da al'umma mai makoma daya don ci gaban al'adu
2020-10-27 19:14:19        cri
Bana shekaru 20 ke nan da kafuwar dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka. A Jiya ne kuma, aka bude bikin matasan Sin da Afirka karo na biyar a nan birnin Beijing, biki mafi shahara a karkashin tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka.

A yayin taron manema labarai da aka saba yi a yau Talata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya gabatar da nasarorin da Sin da Afirka suka cimma a fannin musanyar al'adu cikin shekaru 20 da suka gabata.

Ya ce a cikin shekaru 20 din da suka gabata, dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, ya ci gaba da karfafa hadin gwiwa a fannin al'adu, wanda kuma ya jagoranci musayar ra'ayi da ilmantarwa ta fuskar wayewar kai tsakanin bangarorin biu, kuma an ci gaba da karfafa tushen ra'ayin jama'a na sada zumunci a tsakanin Sin da Afirka. Bisa tsarin dandalin tattaunawar, an bullo da wasu muhimman tsare-tsare da dandamali na musayar al'adu daya bayan daya, ciki har da babban bikin matasa na Sin da Afirka, dandalin tattaunawar masana, da dandalin hadin gwiwar kafofin yada labarai da dai sauransu. Hadin gwiwar Sin da Afirka ta fuskar al'adu, ilimi, aikin jarida da sauran fannoni, tana bunkasuwa yadda ya kamata, kuma ana ta kara mu'amala a tsakanin matasa, mata, kungiyoyi masu zaman kansu da masana ilimi na bangarorin biyu. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China