Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ina dalilan tashe-tashen hankula a yammacin kasashen Afirka
2020-10-27 14:21:25        cri

A makon jiya, an yi ta fama da sauyin yanayin siyasa, da tashe-tashen hankula a wasu yammacin kasashen Afirka da suka hada da kasar Guinea, da kasar Cote d'Ivoire, da kuma tarayyar Nijeriya da sauransu. Lamarin da ya haddasa rasuwar mutane kimanin dari daya, wanda hakan ya janyo hankulan gamayyar kasa da kasa.

Wasu masana sun ce, an samu wadannan tashe-tashen hankula ne sakamakon sabanin ra'ayi game da babban zabe, da yadda 'yan sanda suke aikata ba daidai ba. Sai dai kuma wasu na ganin hakan a matsayin sakamako na matsalolin karancin aikin yi, da talauci, sakamakon barkewar cutar numfashi ta COVID-19.

A sa'i daya kuma, sabani a tsakanin kabilu daban daban, da masu bin addinai daban daban, shi ma ya kasance babban tushen haddasa wadannan rikice-rikice.

Ga karin bayani da Maryam Yang ta hada mana:

A ranar 18 ga watan Oktoba ne aka gudanar da babban zaben shugaban kasa a kasar Guinea. Sa'an nan a ranar 19 ga wata, kafin kwamitin babban zabe mai zaman kansa ya kammala aikin kididdigar kuri'u, dan takarar jam'iyyar adawa, kana shugaban jam'iyyar kawancen karfin dimokiradiyya na kasar Guinea, Cellou Dalein Diallo ya sanar da lashe babban zaben da kansa, inda kuma ya sanar da cewa, akwai wasu da suka tafka magudi a babban zaben. Sabo da haka, masu goyon bayan jam'iyyar adawa a sassan kasar Guinea suka fara zanga-zanga, inda tashe-tashen hankula suka barke a tsakaninsu da 'yan sandan kasar.

A kasar Cote d'Ivoire kuma, rikici ya barke sakamakon babban zaben shugaban kasa. Bisa shirin kasar, za a gudanar da babban zabe a ranar 31 ga wata, amma, biyu daga cikin 'yan takara guda hudu, wato tsohon shugaba Henri Konan Bedie, da tsohon firaminista Affi N'Guessan, sun ki halartar yakin neman zabe, kana sau da dama, sun yi kira ga magoyon bayan jam'iyyun adawa da su gudanar da zanga-zanga, domin nuna kiyayya ga shugaban kasar na yanzu Alassane Ouattara, kuma kada su halarci babban zaben shugaban kasan dake tafe.

Bisa labarin da kafofin watsa labaran kasar suka fidda, a ranar 24 ga wata, rikici ya barke tsakanin magoyon bayan bangarorin biyu, wanda ya haddasa rasuwar matane 16, yayin da mutane 67 kuma suka jikkata.

A tarayyar Najeriya kuma, an gabatar da wani bidiyo ta yanar gizo, da ya nuna yadda 'yan sandan kasar SARS suka kashe, ko gallazawa wadanda suke tuhuma, lamarin da haifar da bore a sassan kasar, domin neman bin hakkin wadanda rundunar 'yan sandan SARS ta kashe ko ta ci zarafi.

Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bayyana a ranar 23 ga wata cewa, tarzomar da masu bore suka yi, ta haddasa rasuwar mutane 69.

Dangane da wannan lamari, shehun malamin jami'ar koyon harkokin watsa labarai ta kasar Sin Xu Tiebing ya bayyana cewa, ban da wasu dalilai na kai tsaye, da suka haddasa wadannan rikice-rikice, matsalolin rashin aikin yi, da talauci, da barkewar cutar numfashi ta COVID-19, sun kasance muhimman dalilan da suka haddasa rashin amincewar al'ummomi da gwamnatocinsu, sun kuma tunzura tashe-tashen hakula a wadannan kasashe na yammacin nahiyar Afirka.

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta nahiyar Afirka, ta fidda rahoton dake cewa, ya zuwa ranar 25 ga wata, mutane sama da miliyan 1.7 sun kamu da cutar COVID-19 a duk fadin nahiyar, yayin da mutane sama da dubu 41 suka rasa rayukansu. Sakamakon barkewar cutar, adadin rasa rayukan yi a nahiyar ya karu matuka, kana, akwai mutane masu yawa da suka shiga kangin talauci, wadanda suka kawo barazana matuka ga zaman takewar al'umma.

Bisa rahoton da bankin duniya ya fidda a watan Oktoba, raguwar tattalin arzikin Afirka zai kai 3.3%, lamarin da ya kasance raguwa ta farko cikin shekaru 25 da suka gabata. Kuma, a watan Mayu, MDD ta fidda rahoto mai taken "hasashen tattalin arzikin duniya na shekarar 2020", inda ta ce, barkewar cutar COVID-19 za ta shigar da mutane miliyan 34.3 cikin kangin talauci a shekarar 2020, kuma kaso 56% daga cikinsu, za su faru ne a nahiyar Afirka.

Haka kuma, shehun malami a jami'ar Abuja dake Najeriya Dr. Shariff Ghali Ibrahim ya bayyana cewa, an rufe kamfanoni da dama a Nijeriya sakamakon barkewar cutar COVID-19, lamarin da ya kara adadin masu rasa ayyukan yi a kasar, don haka zanga-zanga ita ce hanyar da wadanda suka rasa aikin yi suke iya bi domin nuna fushi da rashin amincewarsu.

Ban da haka kuma, sabanin dake tsakanin 'yan kabilu daban daban da masu bin addinai daban daban, shi ne wani muhimmin dalili ne da ya haddasa rikice-rikice a kasashen.

Xu Tiebing ya ce, galibin mutanen dake arewacin kasar Cote d'Ivoire da arewacin kasar Nijeriya Musulmi ne, yayin da galibin mutanen dake kudancin kasashen biyu Kirista ne, a wadannan kasashen biyu, akwai kabilu daban daban, inda kuma ake sa samun rashin cimma matsayi daya game da wanda zai rike madafun mulkin kasa a wadanan kasashen biyu.

Bugu da kari, shugaban kungiyar ilmin siyasa ta kasar Guinea ya ce, masu goyon bayan jam'iyyun siyasan kasar Guinea, su kan fito ne daga kabilu mabambanta, amma a halin yanzu, yakin dake tsakanin jam'yyun siyasa yana sauyawa, zuwa yakin dake tsakanin 'yan kabilu daban daban a kasar.

Bayan barkewar rikice-rikice a wadannan kasashe, MDD da kungiyar AU, da ma wasu kungiyoyin kasa da kasa sun yi Allah wadai da lamurran da suka auku, inda suka kuma yi kira ga bangarori daban daban, da su kai zuciya nesa, da karfafa shawarwarin dake tsakaninsu, domin samar da yanayin siyasa mai dacewa, na farfado da tattalin arziki gabanin yaduwar cutar numfashi ta COVID-19. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China