Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi kira da a magance rashin kudi da nahiyar Afrika ke fuskanta
2020-10-10 17:39:38        cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a yi kokarin magance rashin isassun kudi da nahiyar Afrika ke fuskanta saboda annobar COVID-19.

A cewarsa, babu wata kasa da ta tsira daga annobar, inda ya ce annobar ta haifar da tsananin rashin kudi musammam ga kasashen Afrika. Sannan kudaden da ake kashewa sun zarce kudaden shiga, lamarin da ya haifar da gibi. Ya ce ya zuwa watan Yuni, nahiyar Afrika ce ke da kasashe 7 cikin 8 da suke cikin matsanacin hali saboda bashi, haka zalika 12 daga cikin kasashe 23 dake cikin hadarin fadawa wannan yanayi.

Idan babu managartan matakai, kalubalen ka iya komawa mai tsanani ta yadda kamfanoni za su durkushe.

Ya kara da cewa, yanayin annobar na ba zata, na bukatar a ware adadin da ya zarce wanda aka samar a shekarar 2009 lokacin da aka fuskanci matsalar kudi. Ya na mai kira da a samar da akalla dala biliyan 500 ga karin kadarorin ajiya na SDR. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China