Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Asusun IMF ya yi hasashen tattalin arzikin yankin kudu da hamadar Sahara zai karu da kaso 3.1 a shekarar 2021
2020-10-23 10:58:50        cri

Asusun bada lamuni na duniya IMF ya yi hasashen tattalin arzikin kudu da hamadar sahara, zai raguwa zuwa kaso 3.0 a bana, yayin da kuma zai farfado ya kai kaso 3.1 a shekarar 2021.

Cikin sabon hasashen da ya yi kan tattalin arzikin yankin kudu da Hamadar Sahara, IMF ya ce hasashen ya dogara ne da juriyar tasirin COVID-19 da samun tallafin kudi daga ketare da kuma samar da riga kafi mai inganci da araha da kuma aminci.

Ya kara da cewa, abubuwan da za su ingiza ci gaban a badi, sun hada da ingantuwar fitar da kayayyaki da farashinsu yayin da duniya ke farfadowa, da kuma farfadowar sayayya a cikin gida da zuba jari.

Daraktan sashen kula da nahiyar Afrika na asusun, Abebe Aemro Selassie, ya ce nahiyar na kuma gwagwarmaya da matsalolin lafiya da tattalin arziki.

A cewarsa, harkoki sun fara farfadowa a kasashen Afrika a hankali, kuma kasashen na neman dabarun sake farfadowa yayin da ake fama da matsin tattalin arziki da zaman takewa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China