Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda suka mutu sanadiyyar COVID-19 a Afrika na dab da kai wa 40,000
2020-10-20 11:18:16        cri
Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Afrika, ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a fadin nahiyar ya kai 1,644,780, zuwa yammacin jiya Litinin, haka kuma adadin wadanda ta yi ajalisnu ya kai 39,738.

Cibiyar Africa CDC ta kara da cewa, zuwa yanzu, yawan mutanen da suka warke daga cutar a fadin nahiyar, ya kai 1,356,239.

A cewarta, Kasashen da cutar tafi Kamari la'akari da yawan wadanda ta harba, sun hada da Afrika ta kudu da Morocco da Masar da Habasha da Nijeriya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China