Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jagororin Masar da na Afirka ta Kudu sun tattauna game da madatsar ruwan GERD
2020-10-15 10:47:23        cri

A jiya Laraba, shugaba Abdel-Fattah al-Sisi na kasar Masar, ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, game da batun madatsar ruwan GERD da kasar Habasha ta gina a kogin Nilu.

Wata sanarwar da fadar shugaban kasar Masar ta fitar ta ce, yayin zantawar tasu, shugaba Al-Sisi ya jaddada matsayar kasar sa game da wannan batu, yana mai cewa, Masar na fatan ita da Habasha da Sudan, za su kai ga kulla cikakkiyar yarjejeniya bisa doka, mai kunshe da ka'idojin cike madatsar ruwan, da yadda za a yi amfani da ita.

Daga nan sai shugaban na Masar ya bayyana rashin amincewar sa da duk wani mataki, ko tsari da zai tauye hakkin kasar sa na cimma moriyar albarkatun ruwa daga kogin Nilu.

Shi kuwa a nasa bangare, shugaba Ramaphosa cewa ya yi, zangon rikon mukamin shugabancin AU na shekara daya da ya fara, yana mai da hankali matuka ga hadin gwiwa da Masar, ta yadda za a kai ga cimma yarjejeniya cikin adalci, game da wannan batu na madatsar ruwan GERD. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China