Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabanin Afrika mata sun bukaci a kawar da bambanci a tsarin kiwon lafiya yayin da ake fama da annobar COVID-19
2020-10-15 11:30:43        cri

Shugabanni mata daga kasashen Afirka a yankin kudu da hamadar Sahara sun bukaci gwamnatoci da su shawo kan matsalar karuwar rashin daidaito a fannin kiwon lafiya wanda ya kara kamari a yayin da ake fama da annobar cutar numfashi ta COVID-19.

A jawabin da suka gabatar ta kafar bidiyo a taron koli kan batun kiwon lafiya, shugabanin Afirka mata da 'yan gwagwarmaya sun bayyana cewa, akwai bukatar a samar da manufofi da dokokin da za su taimaka wajen shawo kan manyan matsalolin cutukan dake damun mata da yara mata a nahiyar Afrika.

Monica Geingos, mai dakin shugaban kasar Namibia ta ce, annobar COVID-19 ta kara bijiro da matsalar rashin daidaito a tsakanin jinsi a fannin kiwon lafiya a Afrika, inda aka dakatar da yin haihuwa da ayyukan hidimar shirin tsarin iyali a asibitoci.

Gomman shugabannin Afirka mata da masu tsara manufofin kasa, da masu fafutuka, sun halarci taron kolin shugabanni mata kan batun kiwon lafiya ta kafar bidiyo, wanda wata kungiyar wayar da kai ta kasa da kasa mai suna kungiyar tallafawa lafiyar mata ta shirya.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China