Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Akwai bukatar zuba jari don kyautata rayuwar matan karkara
2020-10-16 11:55:30        cri

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi kira ga sassan masu ruwa da tsaki, da su kara azama wajen zuba jari, don kyautata rayuwar matan dake zaune a yankunan karkara, ta yadda hakan zai sa su iya jure kalubalolin rayuwa dake ritsawa da su.

Cikin wani sako da ya gabatar albarkacin ranar matan karkara ta kasa da kasa, wadda aka yi bikin ta jiya Alhamis, Mr. Guterres ya ce, "cikin hadin gwiwa, muna iya zuba jari da zai baiwa matan karkara dama ta samun ingantaccen tsarin kiwon lafiya, da na zamantakewa, da hidimar muhimman bayanai a fannin noma."

Jami'in ya ce, "Dole ne mu kawar da gibin da dabarun zamani suka kawo, mu samar da muhimman hidimomi masu baiwa matan na karkara kariya daga cin zarafi". "Kaza lika mu kawar da nunawa mata bambanci a dokokin gado, da sauran sassa dake haifar musu asarar hakkokin su na samun kudaden shiga".

Babban magatakardar MDDr ya kara da cewa, "Albarkacin wannan rana, ya kamata mu sabunta himmar mu, ta kare matan karkara a duk inda suke, mu kara azama wajen tallafawa rayukan su, a gabar da ake ci gaba da fama da tasirin cutar COVID-19".

Mr. Guterres ya ce, matan karkara na taka rawar gani a muhimman fannoni na noma, da samar da isasshen abinci, da kula da filaye da sauran albarkatu, amma kuma da daman su, na fuskantar wariya da cin zarafi, karkashin manufofi na nuna wariyar launin fata da mamayar talauci.

Daga nan sai ya yi nuni da yadda cutar COVID-19 ta shafi sama da rabin daukacin mata manoma dake rayuwa a dukkan sassan duniya, ciki har da hana su damar fita, da rufe kantuna da kasuwannin su, tare da datse hanyoyin su na gudanar da hada hada. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China