Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bikin ranar mata ta MDD ya yi kira a samar da daidaito tsakanin al'umma
2020-03-07 17:01:11        cri
Hukumar kula da harkokin mata ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi bikin murnar ranar mata mai taken "Zuri'armu mai daidaito: cimma muradun mata" a jiya Jumma'a, inda ta yi kira ga kasa da kasa su ci gaba da bunkasa harkokin da suka jibanci mata, a wani kokari na cimma burin samar musu daidaito.

A nasa bangaren, babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga mata su tashi tsaye da nuna hazaka domin tinkarar kalubalen sauyin yanayi da fadace-fadace da har yanzu ke addabar duniya.

Kana, shugaban babban taron MDD karo na 74, Tijjani Muhammad-Bande, ya yi jawabi ta kafar bidiyo inda ya ce, ya kamata kowa ya nace ga tabbatar da daidaiton jinsi, saboda wannan shi ne muhimmin sharadin da ya wajaba wajen kare hakkin dan Adam. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China