Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi musayar kwarewar da ta samu a yaki a COVID-19 a taron mata na MDD
2020-08-06 10:06:43        cri

Mata a MDD, wani sashe ne na hukumar MDD dake fafutukar samar da daidaito tsakanin jinsi da kuma kyautata rayuwar mata, a ranar Laraba ta gudanar da taron tattaunawa ta kafar bidiyo domin nazarin samun cigaba game da batun samar da daidaito a tsakanin jinsi yayin da ake fama da annobar cutar numfashin ta COVID-19. Jami'ar dake kula da al'amurran mata ta kasar Sin Huang Xiaowei, ta gabatar da jawabi a lokacin taron.

Huang, mataimakiyar shugabar kwamitin kula da al'amurran mata da kananan yara na kasa dake karkashin majalisar gudanawar kasar Sin kana mamba ta farko ta kungiyar dukkan matan kasar Sin, ta yi musayar kwarewar da kasar Sin ta samu wajen tafiyar da ayyukan dakile annobar COVID-19 da farfadowar tattalin arziki da kuma kyautata zaman rayuwar al'umma.

A jawabin da ta gabatar yayin taron, Huang ta ce, a lokacin da ake fama da cutar COVID-19, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin Sin sun baiwa rayuwar al'umma da lafiyarsu muhimmanci sama da komai, kuma sun zaburar da dukkan jama'ar kasa da su shiga a dama da su wajen yaki da annobar COVID-19. Huang ta gabatar da shirin gwamnatin Sin na tabbatar da bada kariya ga rayuwa da lafiyar mata da yara a yayin da ake tsaka da yaki da annobar da kuma irin gudunmawar da kungiyar dukkan matan kasar Sin ta bayar wajen yaki da cutar COVID-19 da samun farfadowa daga tasirin annobar.

Huang ta bukaci a kara samun goyon baya a tsakanin kasa da kasa wajen yaki da annobar, kana a kara kokarin cimma nasarar samar da daidaito a tsakanin jinsa da kuma ci gaban rayuwar mata daga dukkan fannoni. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China