Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya jaddada bukatar shigar da mata cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya
2019-10-30 10:52:24        cri
Zaunannen wakilin Kasar Sin a MDD, Zhang Jun, ya nanata muhimmancin karfafawa mata da kuma shigar da su cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Da yake jawabi ga kwamitin sulhu na MDD, Zhang Jun, ya jaddada bukatar taimakawa mata samun ci gaba daidai da takwarorinsu maza da kawar da talauci a tsakaninsu da kuma samar musu da ingantaccen ilimi, wadanda suka kasance muhimman sharrudan damawa da su a ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Wakilin na kasar Sin ya bayyana haka ne yayin taron kwamitin kan mata da zaman lafiya da tsaro. Da farko, kwamitin ya amince da kuduri mai lamba 2493 domin sake karfafa ajanda kan mata da zaman lafiya da tsaro, gabanin cikarta shekaru ashirin.

A cikin kudurin mai lamba 2493, kwamitin ya bukaci kasashe mambobin MDD su aiwatar da ajandar da tanadinta, ta hanyar tabbatarwa da inganta ba mata cikakkiyar dama mai ma'ana kuma bisa daidaito da takwarorinsu maza a dukkan ayyukan wanzar da zaman lafiya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China