2020-05-04 22:00:05 cri |
Karkashin laimar wannan rana, matasan da suka shiga adama da su, sun koyi wasu darussa daga nasarorin da wadanda aka karrama da lambobin yabo albarkacin ranar suka cimma. Lambobin da aka baiwa matasan dai su ne mafi martaba da ake baiwa matasa da suka yi fice.
Kaza lika matasa, sun saurari labarun matasa da suka taka rawar gani a yaki da cutar numfashi ta COVID-19, da ma yadda suka koma bakin aiki bayan annobar.
Har ila yau, kafofin watsa labarai sun zanta da matasa kai tsaye, an kuma gabatar da makaloli, da nune nune game da muhimman al'adun kasar Sin. (Saminu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China