Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zhang Jun ya yi kira ga kasashen duniya da su tallafawa matasa wajen tunkarar kalubalen da COVID-19 ke haifarwa
2020-04-28 12:02:13        cri

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bukaci kasashen duniya da su tallafawa matasa, a fannin tunkarar kalubalen da COVID-19 ke haifarwa a duniya baki daya.

Zhang Jun, wanda ya yi wannan tsokaci yayin taron kwamitin tsaron MDD da ya gudana jiya Litinin ta kafar bidiyo, ya ce ya dace mahukunta su taimakawa matasa, ta yadda za su kai ga taka muhimmiyar rawa a fannonin wanzar da zaman lafiya da ci gaban duniya.

Yayin taron mai lakabin "Tabbatar zaman lafiya da tsaron duniya: Gudummawar matasa, a fannin zaman lafiya da tsaro", jami'in na Sin ya ce, akwai bukatar kasa da kasa su aiwatar da daukacin kudurorin MDD masu nasaba da wannan jigo, su kuma maida hankali wajen aiwatar da manufofin yadda ya kamata.

Zhang Jun ya kara da cewa, Sin na dora muhimmancin gaske, ga ajandar shigar da matasa cikin harkokin wanzar da zaman lafiya da tsaro. Ya ce kasar sa na farin ciki matuka da ganin irin ci gaban da aka samu a fannin aiwatar da kudurorin MDD masu nasaba da hakan.

To sai dai kuma, ya nuna damuwa, game da yawan matasa a kasashe da yankunan duniya da dama, wadanda ke shiga mawuyacin hali sakamakon tashe tashen hankula. Wanda hakan ke haifar musu da wahalhalu na talauci, da rashin ayyukan yi da dai sauran su. Yayin da wasu ma ke fuskantar barazanar fadawa ayyukan ta'addanci. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China