Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci Amurka da ta daina bata sunan ofisoshin jakadancinta dake kasar
2020-09-26 16:09:29        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a jiya Jumma'a cewa, kasar Sin ta nemi Amurka, da ta daina bata sunan ofisoshin jakadancinta da jami'ansu dake kasar.

A ranar 24 ga wata ne, ministan harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce, kasarsa ta rufe ofishin jakadancin kasar Sin dake birnin Houston ne bisa laifin leken asiri da wasu jami'an ofishin suka aikata. Ya kara da cewa, ofishin jakadancin kasar Sin dake birnin New York ma, yana gudanar da wasu ayyuka masu nasaba da leken asiri. Kana, ma'aikatar shari'a ta Amurka, za ta gabatar da karin kara kan batun.

Dangane da wannan batu, Wang Wenbin ya ce, ofisoshin jakadancin kasar Sin dake Amurka, da kuma dukkanin jami'ansu, suna gudanar da ayyukansu bisa yarjejeniyar dangantakar diflomasiya ta Vienna, da yarjejeniyar dangantakar jakadu ta Vienna, da kuma yarjejeniyar diflomasiyya tsakanin Sin da Amurka, kana suna gudanar da ayyukan diflomasiyya yadda ya kamata.

Ya ce, kasar Sin ta nemi gwamnatin Amurka, da ta daina bata sunan ofisoshin jakadancinta dake kasar, da kuma kiyaye ka'idojin dokokin kasa da kasa da abin ya shafa, da yarjejeniyar diflomasiyya tsakanin Sin da Amurka, da kuma nuna goyon baya ga ofisoshi da jami'an diflomasiyyar kasar Sin dake kasarta yadda ya kamata. Kana, idan akwai bukata, kasar Sin za ta mai da martani kan Amurka dangane da dukkanin abubuwan da ta yi wa ofisoshi da jami'an diflomasiyyarta. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China