Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana adawa da matakin Amurka na yada "cutar siyasa" a kwamitin sulhu na MDD
2020-09-10 13:24:37        cri
A jiya ne, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Geng Shuang, ya nuna adawa da yunkurin kasar Amurka na neman bata suna da ma shafa ma kasar Sin kashin kaji.

Geng Shuang ya jaddada a yayin taron da kwamitin sulhu na MDD ya kira kan annobar cutar numfashi ta COVID-19 da aka yi ta kafar bidiyo cewa, ya kamata kasar Amurka ta mai da hankali kan kiyaye lafiya da tsaron al'ummominta, a maimakon dora laifi kan wasu.

A wannan rana, wakilin kasar ta Amurka ya zargi kasar Sin cewa, wai tana boye bayanai game da cutar numfashi ta COVID-19, da kasa daukar matakan dakile yaduwar cutar COVID-19 yadda ya kamata, ikirarin da ya sabawa ainihin abin da ya faru. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China