Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka tana zama mai rusa cudanyar sassa daban daban
2020-09-04 20:17:42        cri

Madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yau Jumma'a a nan Beijing cewa, yanzu haka kasar Amurka tana zama mai rushe cudanyar sassa daban daban, da barnata ka'idojojin kasa da kasa da tsarin duniya.

An ruwaito cewa, a kwanan baya, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya sanar da sanya takunkumi kan wasu jami'an kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya, saboda kotun tana bin bahasin kan tuhumar da ake yi wa sojojin Amurka da aikata laifukan yaki a Afghanistan. Dangane da lamarin, kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya ta ce, abun da Amurka ta yi, ya ci karo da ka'idojin Rome, tsarin hukunta manyan laifuffukan kasa da kasa da tsarin shari'a. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China