Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta sake sanyawa ofishin jakadancin Sin da ke Amurka da ma'aikatan diplomasiyyar Sin tarnaki
2020-09-03 20:42:08        cri

Madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yau Alhamis a nan Beijing cewa, tun daga watan Oktoban shekarar bara, ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta rika sanyawa ofishin jakadancin kasar Sin dake Amurka da kuma yadda ma'aikatan diplomsiyyar Sin suke gudanar da ayyukansu tarnaki. Abubuwan da Amurka ta yi sun saba wa dokokin kasa da kasa da manyan ka'idojin raya hulda a tsakanin kasa da kasa, sun kuma kawo cikas ga bunkasa dangantaka a tsakanin Sin da Amurka da kuma yadda suke mu'amala a tsakaninsu.

An ruwaito cewa, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar a ranar 2 ga wata cewa, tilas manyan jami'an diploasiyyar kasar Sin dake Amurka su mika takarda domin samun iznin ma'aikatar idan suna son ziyartar jami'o'in Amurka da ganawa da jami'an sassa na Amurka, ko idan an shirya wata harkar al'adu da za ta hallara mutane fiye da 50 a wani wurin da ba a cikin ofishin jakadacin kasar Sin a Amurka ba. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China